An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
KAMBUN
KARFE
NAFI'U SALISU
IBN SALIS
NAHIYAR SAIFANA
ska ma'abociyar sanyi mai dan ratsawa cikin Ijiki na kadawa a hankali, gabas, yamma,
kudu, arewa, rassan dogayen bishiyoyi na rangaji
gwanin ban sha'awa, kunnuwan su na fado zuwa
bisa shimfidaddiyar kasar da Ubangijin sammai da
kassai ya shimfida a doron duniya, yayin da kukan
tsuntsaye da na wasu daga cikin namun daji ke
wanzuwa a daidai lokacin.
Nahiyar na da fadin gaske, dauke take da
duwarwatsu da tsaunika ma'abota girma, akwai
bishiyoyi masu tsawo da kauri, sannan akwai
koramu ma'abota gudanar da ruwa a cikinsu, wanda
hakan na daya daga cikin abin da ya sa wannan
nahiya ke da sanyi wuri.
Kwal!Kwal!!Kwal!!! Sautin bugun karfe ke
bayyana daga gindin wani dogon tsauni dake cikin
wannan nahiya, ga duk wanda ya saurara da kyau ya
ji karar dukan dake bayyana, zai fahimci ana dukan
karfe da karfe nc daga can in da sautin karar ke
fitowa.
Daga kudu da wannan dogon tsauni in da karar
dukan karfe ke fitowa, sai ga wani mahayin Doki ya
fito haye kan wani bakin Dokinsa ma'abocin karfin
kafadu. Wanda ke kan dokin, saurayi ne mai cikar
zatin halitta, ma'abocin kwarji. Iskar dake kadawa
tana shawagi a'sararin duniya a wannan lokaci, ta na
5
kada gashin kanshi ma'abocin yalwataccen baki mai
ban sha'awa. Ya na sanyc da wata rigar gashi, akwai
wani dogon takobi a jikinsa, sannan ga wata
garkuwa a bayansa ya goya ta, a kafadar haggunsa
kuma kwari da baka ne a rataye, kai kace wani
mafara uci ne yayin da ya fito farauta cikin dokar
daji.
Idan ka yi masa kallon natsuwa, za ka fahimci
akwai jarumtaka a tare da shi, haka nan idan ka kalli
kirar jikinsa, za ka fahimci jan gwarzon saurayi ne.
Dokinsa kuwa Ingarma ne. A hankali ya doso in da
karar dukan wannan karfe ke bayyana. Yayin da ya
kusanto wannan tsauni, sai ya hango Dattijon shi da
matarsa, da ya sake matsiwa sosai sai ya ga matar
na juya irin karfen nan na zuga wutar makera, can
gefe guda kuma tartsatsin wuta ne ke tashi, shi
kuma wannan Dattijon yana dukan wani karfe dake
kan wani katon karfe da wata katuwar gudumar
karfe dake hannun damarsa. Da matashin saurayin
nan ya sakc yin duba can gefe guda, sai ya hango
wani karamin yaro zaune ya na wasa, Shekarun
yaron ba su wuce uku zuwa hudu ba. A wuyan
yaron akwai wata azurfa da aka daura masa mai
haske da daukar idanu.
Dattijon nan ya waiwaya wajen matarsa mai yi
masa zugar wutar makerar lokacin da ya ji ta daina
juya abin zugar wutar. Ga mamakinsa sai ya ga tana
kallon wani waje daban, cikin mamaki da yanayin
da ya ganta, ya tambayc ta.
"Aisamatu me ki ke kallo ne haka.?"
Maimakon ta amsa masa tambayar da ya yi ma
ta, sai ta nuna mashi in da take kallo da bakinta.
Dattijon ya waiga a hankali domin ganewa
idanunshi abin da ya dauke wa Aisamatu hankali
daga barin zugar wutar makerar. A nan ya yi ido
hudu da matashin saurayin dake kan doki, har ya iso
inda suke tsattsaye ba dauke idanunsa daga gare shi
ba.
Dattijon nan bai yi magana ba, har sai bayan
da matashin ya sauka daga kan dokin nasa, yayin da
ya nufo wurinsa cikin natsuwa tare da sakin fuska
cikin fara'a.
"Barka da zuwa ya kai wannan ma'abocin
kyawun halitta." In ji wannan Dattijon
Kafin Dattijon ya gama rufe bakinsa, matashin
saurayin ya iso gare su yana murmushi tare da amsa
sannu da zuwan da Dattijon ya yi masa.
Dattijon ya aje kayan kirar dake hannunsa,
sannan ya yi wa matashin nan jagora zuwa cikin
tsaunin nan in da a nan gidansa yake.
Bayan sun kadaice a cikin wani kogo wanda
fadinsa ya kai girman dakin kwanciya. Saurayin
nan ya gabatar da kansa ga Dattijon nan, bayan ya
bukaci hakan. 7
"Sunana Amar bin Zubaid, na samu labarinka
a wajen Kakana Sarkin bokayc, yayin da na ziyarce
shi da wata bukata tawa. Wannan bukata tawa kuwa
ita ce, ya kai wannan Dattijo ma'abocin sanin sirrin
kira, ban wanzu gare ka ba face dan wata babbar
bukatata, kuma karama a wajenka.
Na kasance daya daga cikin mutanen da suke
son mallakar Gimbiya Anisa 'yar Sarki Haiman
wadda mahaifinta ya yi alkawarin zai aurar da ita ga
duk wanda ya sanar da shi yanda za ayi amfani da
sihirtaccen kambun nan na bakin karfe wanda ya sa
aka dauko masa a karkashin dutse, dake ajiye a
gidan sarautar kasar Sarki Haiman din, DaulatulSakaf, don haka ina so a bisa basira da kware irin
wadda Allah ya yi maka, ka kera min irin wannan
kambu ya kasance kamarsa da wancan komai iri
guda, don haka da na je wurin Kakana ya buga min
alkalumma, ya sanar da ni cewa kai kadai ne wanda
zaka iya kera min irin wannan kambu a duk
makeran duniya ba ki daya, idan ka yi haka, zan
mallaka maka dukiya mai tarin yawa, wadda kai
kanka sai ka yi mamaki da ita."
Lokacin da Amar bin Zubaid ya kai aya a
zancen nasa, sai Dattijon nan mai suna Abusamar ya
dube shi sosai yana mai cewa.
"Lallai Amar ka zo gare ni da al'amari mai
girma, a rayuwata kai ne mutum na farko da ka taba
zuwa garc ni da abin da na ji shi kamar a mafarki.
Anya kuwa kai kana da labarin Kambun nan na
gidan. sarauta? Idan kuwa haka ne, to lallai
rayuwarka na fuskantar wahala da kunci idan ka ce
zaka nemi sanin yadda ake amfani da wannan
kambu, domin karshe ma dai zaka iya rasa
rayuwarka gaba daya, idan har ka ce sai ka binciko
domin ba kai ba ma dan Adam, ko matashin Aljanin
Kakana Huzaid ya gagare shi." Shi ma Dattijon
Abu-samar da yazo nan a zancensa, sai ya saurara
ya na kallon kofar kogon da suke ciki. Matarsa
Aisamatu ta shigo dauke da wani gora na jar fata, ta
aje kusa da Amar da ya zo wajen maigidanta.
Amar ya juyo suka fuskanci juna shi da
Aisamatu, ya yi gaisuwa cikin girmamawa a gare ta,
ya na mai farin cikin kawo masa wannan ruwa da ta
yi. Ba tare da ta tsaya wajensu ba, ta fito daga
kogon wanda za'a iya cewa daki ne guda.
Abu-Samar ya shafi gemansa da hannunsa na
haggu, sannan ya kalli Amar ya na mai sauraran
abin da zai sake fitowa daga bakinsa.
Amar ya ce "Ya kai Abu-Samar, ka yi sani
cewa, mu mun kasance ma'abota tarin dukiya, kuma
jinin sarauta, don haka idan har zaka iya kera min
irin wannan kambu, to lallai zan mallaka maka
dukiya mai tari yawa, bayan haka za ka iya fadin
duk abin da ka ke so, na rantse da rana ma'abociyar
haske, sai na mallaka maka shi, in dai har bai f
Karfina ba."
A lokacin da Dattijo Abu-Samar ya ji wannan
batu, sai ya yi murmushi ya sake shafar gemunsa,
sannan уа сс.
"Na ji abin da ka fada ya Amar, amma idan har
haka ne, to ina bukatar yin nazari akan wannan
al'amari, don zai iya kasancewa nima wani tashin
hankali ya shafe ni a sakamakon haka, saboda haka
ka tafi izuwa saurare na har tsawon kwana bakwai,
sannan ka dawo."
Amar ya ji dadi tare da farin ciki sannan ya
kawo zinare saba'in masu nauyi ya ba shi, kafin
daga nan ya yi masa sallama tare da godiya a gare
shi ya tafi.
Dattijo Abu-Samar, ya kasance mutum ne mai
shekaru da dama a duniya, kuma ya kasance mutum
mai sha'awar zaman ciki dokar daji shi kadai, don
haka ne ma ya kasance cikin daji tare da iyalinsa.
Sana'arsa ta kira kuwa, ya gajcti ne a wajen
Kakansa da har yanzu yana raye, sai dai kuma
tsufansa ya yi nisa sosai. Abu-Samar ya kware to
fuskar iya kira, domin a wannan lokacin masana
bincike sun gudanar da bincike akansa, sum kuma
gune babu wani mutum da ya ke yin kira wanda ya
10
kai shi kwarewa, domin lokuta da dama ya kan kera
wasu abubuwan ban mamaki, haka nan idan ka zo
ka ce ya kera maka takobi irin na Sarki wane, ko
sarauniya wance, kambun sarauta ko zoben sarauta
da dai sauransu, to zai yi maka irin sa. Yana da
wani kundi wanda a cikinsa ya ke dauke da
rubutattun sunayen abubuwa da suka shafi kayan
sarauta na sarakuna, haka nan kuma duk wani
takobi, zobe, kambu, da wani mai mulki ya mallaka
na sihiri ko kuma mai kudi na ban mamaki, to
akwai sunayensu da tarihinsu a rubuce cikin wannan
kudi. Abu-Samar da matarsa Aisamatu, basu taba
haihuwa ba tunda suke a rayuwarsu, don haka sai
suka dauko dan kaninsa domin su rene shi, wanda a
yanzu yake wajensu.
BAYAN SATI GUDA
Da kwanaki bakwai suka cika, a cikin kwana
na takwasa, sai ga Amar ya dawo izuwa ga AbuSamar kamar yadda ya yi masa umarnin cewa bayan
kwanakin bakwai ya dawo domin jin in da aka
kwana game da bukatarsa. A wannan lokaci sai
Abu-Samar ya fara ba Amar labarin.
BABI NA DAYA
A
wani lokaci, a wani zamani, shekaru aruaru da suka shude (wuce), a cikin
Kasashen Larabawa. An yi wani sadauki ma'abocin
nauyin kafadu, kuma ma'abocin karfin damtse da
kwarcwa wajen iya yaki. Babban kafiri ne amma
daga baya ya yi imani da Allah (daya) ta dalilin
wasu isharori da suka wanzu gare shi na ban
mamaki da al'ajabi, don haka sai ya shiga
Musulunci tare da wasu daga cikin mutane da ya ke
tare da su.
Kafin wannan lokaci, wannan Sadauki mai
suna Haidar sai da ya yaki rundunar sarakuna da
sarakai daban-daban, a bisa jagorancin mahaifinsa
wazirin Sarki Lamrud da ke mulkar birninsu, a ciki
har da wani babban Sarki wanda ya so karbar
addinin Musulunci, sai dai kafin wannan lokaci
Haidar ya shirya rundunar makafirta suka yaki
wancan sarkin shi da jama'arsa.
An yi kiyasin cewa, a wancan lokacin duk
wani Sadauki ba ya nuna shi sadauki ne, matukar
Haidar ya na nan, yanzu ya karar masa da numfashi.
Takobin Haidar, shi ne takobin da, idan ya kai
sara ko da bai samu wanda zai sara da takobin ba, to
iskan takobin kadai sai ya ji wa mutum rauni. Haka
nan idan kuma ya samu mutum to lallai sai dai
gawarsa. Aljannu kuwa konewa suke idan takobin
12
ya taba jikinsu. Hatta karfe idan ya sare shi da shi,
to sai ya lalace.
Bayan Haidar ya karbi Addinin Musulunci, sai
nan da nan labari ya iskc Sarakuna daban-daban,
wanda mafiya yawa daga cikinsu kafirai ne, don
haka sai bakin ciki ya kama su, takaici ya shiga
addabarsu, su kuwa Sarakunan masallata, sai farin
ciki ya wanzu a zukatansu, murna da farin cikin
wannan al'amari ya sa su cikin walwala da nishadi,
fargaba da yawan damuwar zaluncin da Haidar yake
a da, ya gushe daga zukantansu. Har ma sai da aka
samu wani Sarki daga cikin Sarakunan Musulmi ya
ba shi aurcn diyarsa kyauta.
A wannan lokaci nc, Sarakunan kafirai suka
dinga aikawa da sauran makwabtansu labarin
Musuluntar Sadauki Haidar, wannan kuma shi ne
abin da ya zama fargaba a zukatan Sarakunan
kafirai, mazansu da matansu. Don haka tun ba aje
ko'ina ba, sai suka fara shawarwarin yadda zasu
Gullo wa lamarin, in da a karshe suka yanke
shawarar shirye-shiryen makircc-makircen yadda za
su hallakar da Sadauki Haidar.
**
Sarki Ukashatu, wani makafirci, kuma daya
daga cikin manyan sarakuna a wancan lokacin, yana daya daga cikin sarakunan kafiran da suka sha
13
alwashin ganin bayan Sadauki Haidar, don haka sai
ya jefa gaba da kiyayya mai tsanani tsakaninsa da
mutanensa maza da mata, kowa a garin ya zama mai
kyama da kin Sadauki Haidar, sabanin baya kafin
musuluntarsa da duk wani kafiri yana sonshi,
musamman ma ta fuskar kisan gillar da yakc yi wa
Musulmi, duk da cewa akwai wasu da yawa da
bautar su ba daya ba ce da ta Haidar. Akwai masu
bautar wuta, kogo, gumaka, rana, taurari da wata,
darc, dutsc, dabba, da sauransu.
Wata rana Sarki Ukashatu, ya bukaci ganin
bokansa wanda yake sanar da shi al'amuran yau da
kullum ta fuskar sihiri, ya wanzu tare da shi, sai ya
ce da shi.
"Ya kai wannan Boka ma'abocin sanin kafar
sihiri, ina so ka wanzu cikin ilimin bokancinka, ka
kuma tabbatar ka samar da wani sharri wanda zai
zamo sanadiyar mutuwar Amirul Jihad (kamar
yadda wasu da yawa suke kiransa) Haidar kenan,
"Ya kasancc ba zai yi wani yawancin kwana ba,
sannan kada ka bari jininsa (da ko dan uwa) daga
ahlinsa ya wanzu cikin rayuwa mai dadi a doron
kasa, facc ka wanzar da shi cikin kunci da wahala.
Wannan shi ne babbar bukatata." Da kammala
wannan magana, sai bokan nan ya yi murmushi,
sannan ya tabbatar masa da cewa, wannan an yi an
gama. 14
Tun daga lokacin da Sarki Ukashatu suka rabu
da Boka Ashfar, bayan da ya koma gida, a cikin
wannan yini ya fara kullc-kullin abubuwan sharri da
makirci ta hanyar siddabaru da sihiri wanda zai
cutar da Sadauki Haidar, bisa cika umarnin Sarki
Ukashatu.
BAYAN WASU SHEKARU
Sai ga takarda daga wani babban sarki, shi
kuma wannan Sarki ya kasance mai bautar gumaka
shi da jama'arsa. Yayin da wannan takarda ta iso ga
Haidar, sai ya ga tana dauke da neman gayyatarsa
zuwa walima a kasar wannan Sarki, wanda ake kira
da suna Sarki Ushaibat.
Haidar ya yi farin ciki da ganin wannan
takarda, sannan ya amsa a rubuce cewa, zai ziyarci
kasar Sarki Ushaibat (wato kasar da yake mulki
Hubar). Yayin da wannan takarda da Haidar ya sa
aka rubuta ta amsa gayyatar da aka yi masa ta riski
Sarki Ushaibat, sai murna da farin ciki suka wanzu
cikin zuciyarsa, ya kuma aikawa sauran sarakunan
makafirta cewa, ga abin da ya shirya na son hallaka
Sadauki Haidar, kuma shigaban sadaukai. Ya shirya
tuggu da makirci domin hallakar da Sadauki Haidar,
wanda wannan ya faru ne saboda ganin jarum taka
irin tasa idan ya shirya jakar wanda ya yi niyya to fa
15
lallai sai ya cimma burinsa, to suna tsoron ya zama
sarki.
Bayan haka, al'umma da dama sun shiga
addinin Musulunci ta dalilin şhiriyar Haidar izuwa
bautar Allah Ta'ala, don haka yana da jama'a sosaí,
kuma ya bi gari-gari yana wa'azantar da mutane
daga barin bautar wanin Allah (Shirka), da su dawo
izuwa babban rabo, (Addinin Islam). Sannan da
yawa daga cikin mutanensa su ma, sun kasance
sadaukai masu nauyin kafadu, idan suka sara ko
suka ko harbin kibiya da sauransu to lallai sai
mutum ya dandani ukuba, imma ba sauran shan
ruwan mutum a gaba, sai ya mutu.
**
Al'amari ya gabato, dangane da amsar gayyatar
da Sadauki Haidar zai yi a birnin Hubar (wato
birnin Sarki Ushaibat), don haka sai Haidar ya fara
zikiri ga Ubangiji (Madaukakin Sarki) akan neman
nasarar wannan tafiya cikin sa'a da neman a
kammalá komai lafiya ya dawo tare da Jama'arsa
lafiya.
Haka ya wanzu yana addu'o'i a turakarsa, bai
gushe ba har sai da ya kwana goma sha biyar, a rana
ta goma sha shida ne, bayan ya wanzu yana zikirin
Allah, kamar yadda ya saba, sai wani nannauyan
bacci da bai taba jin irinshi ba ya wanzu garc shi.
16
rijiyoyin nan, sannan wasu mayaka daga cikin
sadaukai su ja tunda a kowacce kuskurwa, .da zarar
Haidar ya afka cikin rijiya, sai su bi sauran mutanen
da yake tare da su da sara, yayin da za su yi kokarin
komawa baya idan sun fahimci haka
Nan da nan Baraden Sarki Ushaibat suka
bazama ko'ina a cikin birnin Hubar, wasu, akan
Dawakai, wasu kuma a kafa, wasu dauke da
garkuwa da makamai majiya karfi akan dawakai
suka samu wurin labewa, kai ka ce dama can an
aiko masu ne da shirin gwabza yaki
Shiru, babu motsin wani abu mai giftawa, a
cikin birnin sai dai iska kawai ma'abociyar
wanzuwa a sararin duniya. Birnin Hubar ya yi shiru
tamkar babu wani bil-Adama a cikinsa!
Da adadin sa'a guda ta cika, sai ga kura ta
turnuke ta yi sama daga can wajen gari, wannan
alama ce ta cewa Haidar da mutanensa sun iso
birnin Hubar. Nan da nan labari ya isa kunncn Sarki
Ushaiba, ya yi dariyar mugunta sannanya tashi
yayo hawa da wasu daga cikin mutancnsa domin ya
zo ya ganewa idanunshi abin da zai wakana.
A gefen damansa, wazirinsa ne sai kuma haggunshis
Bokayc hudun da suka yi wa rijiyoyin shiri ne cikin
wata shiga, kai ka cc Iblisai ne, don Isananin muni,
sai kuma babban sadaukin Sarki Ushaibat da wasu
masu bin bayansa a tsaye su ma daga dama kusa da
25
daya. Nan take Haidar ya yi kabbarar shi ma kafin
ya rufe baki sai ya nuna saitin wadannan rijiyoyi da
takobinsa, nan take sai wani haske gami da iska mai
karfi suka bayyana a wurin, nan da nan sia ga kasa
tana tsagewa mutanen Sarki Ushaibat suna afkawa
ciki. Ganin wannan abu sai hankalin Sarki da duk
wanda ke wajen ya tashi, nan take ya juya shi da
wasu da dama daga cikin mutanensa da nufin
komawa cikin birnin. Kafin su ankara tuni rijiyoyin
nan masu bakunan sihiri sun cika da mutanen Sarki
Ushaibat, ihunsu da karaji kawia ake ji. Zuwa can
kuma sai wurin ya zama ya shafc, nan da nan
Haidar ya kalli jama'arsa tare da basu umarnin su
biyo bayansa. Yayin da suka shiga tsakiyar birnin
Hubar, sai Haidar ya sakc rikontakobinsa
ma'abociyar kaifi da kyalkyali kamar madubia
cikin rana, ya daga murya yayin da sautin maganar
ke fita da karfi har ya na amsa kuwwa cikin birnin
Hubar, ya na mai cewa.
"Kaiconku makafirta, kaiconku, ashc ba ku
zamo masu cika alkawari ba sai ku kasance
masharranta ga bayin Allah? Hakika da kunsan abin
da ba ku sani ba, da ba ku kasance masu shirya
tuggu da makirci ga bakin ku ba.Toina mai
tabbatar wa a gare ku, ba za ku zamo masu rinjayc a
gare mu ba, da sannu Ubangijinmu (Allah) zai
kubutar damu daga bakin tarkonku na makirci.
27
Haidar ya daga kai sosai ya kalli kowa, tun
daga kan Dakarun Sarki har zuwa kan Sarki
Ushaibat da wazirinsa, ya girgiza kai, sannan ya
fara da cewa.
"Kaiconku makafirta, lallai kun yi kuskure
game da abin da ku ka kasance kuna aikatawa a
gare mu na yaudara, to ku yi sani cewa,
Ubangijinmu (Allah Ta'ala) shi ne wanda zai karre
mu da kariyarsa daga duk wani makirci naku
Ba mu zo gare ku da nufin yaki ba face mun
zo ne bisa amsa gayyatar ku, wanda ku ka yi haka
domin cutar dani daga zaluncinku, to tunda ba yaki
ya wanzar damu a birninku ba, kuma babu
alkawarin yakin a tsakaninmu, to lallai mu masu
kiyayewa ne a bisa zaman lumana. Amma da sannu
zan wanzu a wannan birni naku, ba zamu juya baya
gare ku ba, face kun zama kararru a cikin wannan
birni naku, idan har kuwa muka juya baya gare ku,
to sai dai idan har kun kasance masu yin mubaya'a a
gare mu tare da yin Imani da Allah da kuma
Manzonsa (S.A.W)."
Haidar na kammala wannan jawabi nasa, ya
juya wajen jama'arsa ya kuma yi umarni a gare su a
wannan lokaci da su juya domin komawa garinsu,
kafin kiftawar idanu, sai duk kowa ya juya kan
Dokinsa da nufin komawa. 30
"Haidar." Muryar Sarki Ushaibat ta yi kiran
sunan Sadauki Haidar, shi kadai ya tsaya bisa
dokinsa tare da juyowa, suka hada ido da Sarki
Ushaibat durkushe da guiwowinsa bisa kasa ya na
mai cewa.
"Ka yafe ni ya kai wannan Sadauki ma'abocin
kadaita Ubangijinka mai girma. Ma za ka sanar da
ni kalmar Shahada, lallai na yi alkawari a gare ka
zan ba da gaskiya da Ubangijinka da kuma Ma'aiki
(S.A.W)." Da jin haka, sai nan da nan Haidar ya yi
wa mutanensa umarni da su dakata, Haidar ya iso ga
Sarki Ushaibat yana mai farin ciki, nan take ya
sanar da shi kalmar shahada, ya fada tare da
nanatawa har sau uku, wanda hakan yasa sauran
jama'ar Sarki da dama suka mika wuya su ma.
Wannan shi ne abin da ya faru na dangane da
makircin Sarki Ushaibat ga Haidar. Maimakon
makircinsa ya kama Sadauki Haidar sai hakan ya
zama sanadin Imaninsa da Allah Makadaici tare da
jama'arsa. Don haka Haidar da jama'arsa suka dawo
cikin birnin Hubar aka sha shagali har na tsawon
kwana bakwai, sannan daga baya Haidar da
mutanenshi suka yi wa Sarki Ushaibat da jama'arsa
sallama suka bar birnin. 31
BABI NA UKU
H
aidar ya zama Sarki a garin su, yayin da
mutanensa suke girmama shi, suke ganin
darajarsa da kuma kimarsa, sai dai duk da cewa
yanzu ya zama sarki ya na kan gadon sarauta,
babban abin da ke damunsa bai wuce na rashin
sanin in da dansa yake ba.
Idan dai mai karatu bai manta ba, tun lokacin
da Haidar ya daura wa dansa Sayyar zoben nan a
wuya, iska ta dauke shi ta tashi sama dashi, har
zuwa yanzu rabonsa da shi kenan. To me ya faru da
shi bayan rabuwarsu.?
Duk da cewa Haidar ya na kan karagar mulki
yanzu, to amma abin da yake tunani shi ne, idan ya
mutu wanene zai gaje shi? Ya san dai babu wanda
ya fi cancanta da ya maye gurbinsa bayan ya kwanta
dama tamkar dansa na cikinsa da ya haifa, sai dai
kuma ga yadda ta kasace a gare shi.
Mahaifiyar Sayyar Aisamatu kuwa, wannan
al'amari ya jefa ta cikin tsananin bakin ciki,
musamman ganin cewa Sayyar shi kadai ne dan da
Allah ya basu, ba su kuma sake haihuwar wani dan
bayan shi. To amma a duk lokacin da ta yi Sallah,
tana rokon Allah da ya bayyana mata yaron nata
32
kafin lokacin da zata koma zuwa ga Mahaliccinmu
Allah.
Haidar ya samu shekaru da dama yana mulki,
yayin da mutane suke jin dadin mulkinsa, domin ya
kasance mai yin adalci a tsakanin jama'arsa, tare da
kiyayewa da kare hakkokinsu mazansu da matansu.
Kwanci tashi, wata rana aka wayi gari Sarki
Haidar ya kwanta rashin lafiya, don haka sai
wazirinsa ne ke tafiyar da harkokin mulkin kasar.
Ana cikin wannan ne, rannan sai Sarki Haidar ya
fito zuwa tsakar birninsa, inda wani matashin
dabino ya ke dashe, wanda bai fara yin 'ya'ya ba.
Anan aka yi sallar Azahar a wannan rana, bayan da
aka idar da sallar, sai Sarki Haidar ya tashi cikin
karfin hali yana yi wa mutanensa nasihohi kamar
yadda ya saba, in da daga bisa ni ya sa wazirinsa ya
miko masa takobinsa. Ya karba ya cire ta daga cikin
gidanta, sannan ya ambaci sunayen Allah tsarkaka,
ya yi kalmar shahada sannan ya soka takobin a jikin
bishiyar dabinon nan. Duk mutanensa suka bishi da
kallo cikin mamaki tare da al'ajabin abin da ya yi. A
lokacin da takobin ta shiga jikin dabinon, sai da
rassan bishiyar suka yi girgiza, sannan abin da ya fi
ba kowa da ke wajen mamaki, yadda rabin takobin
ya shige jikin bishiyar dabino. 33
Sarki Haidar ya juyo ya kalle su daya bayan daya yana mai yin murmushi, sannan ya shafi
gemunsa ya na mai cewa.
"Ya kuma mutancna, hakika nasan zaku so jin dalilin da yasa na yi haka." Ya fan dakata
Duk suka kada kai kamar kadangaru.
Sarki Haidar ya ci gaba
"Dalilina na yin haka kuwa shi ne, domin na
bar maku wasiyya da cewa, babu wani mutum da ya isa ya cire wannan takobin daga jikin bishiyar dabinon nan, face dana Sayyar, shi kaďai nc zai cire
wannan takobi daga jikin wannan bishiyar dabino, ko da bayan raina, idan aka samu wanda ya yi haka,
to kuwa shi ne dan Sayyar: Amma idan ba shi ba, to babu wanda ya isa ya cire wannan takobi daga jikin
wannan bishiyar dabino."
Yayin da mutanensa suka ji wannan batu, duk
sai suka cika da mamaki da kuma al'ajabi, don haka sai kuma suka ji dadi domin sun samu hanyar da za
su gane Sayyar dan sarkinsu a duk lokacin da hakan ta faru.
Sarki Haidar ya sake cewa.
"Sannan wasiyya ta biyu da zan bar muku ita ce........"
A daidai wannan lokaci ne wani mutu daya daga cikin mutanen garin,