ɗaukar kai tsaye wa inda basu wajan suna kallo a TV da radio.
Hakan ya sa Master ya ce.
"Yau muna cikin farin ciki wannan ma na ɗaya daga cikin nasarar da muka samu."
"Yanzu haka zan tura ma kowa 2m yaka mata a ce kuna da abin yi kamar kasuwanci ko wani abun."
"Ku sa ni wannan kuɗin da nake baku ba kuɗin nan ba ne, duk kuɗin da muka ɗauko ko muka ƙwamushe na al'umma ne, ba namu ba dan haka ku kauda idanun ku a kan wannan kuɗin."
Muhusin ne ya ce.
"Gaskiya ni bana so ba zan amsa ko biyar ba, abin da ka yi min ban da abin da zan biya ka, inason ka san ce wa ni ma ina da aikin yi."
Murmushi Master ya yi ya ce.
"Ni ba dan wani abu na baku kuɗi ba dan kyautatawa ce, dan Allah kada ku ce ba zaku amsa ba idan baku amsa ba ba zan ji daɗi ba."
"Kun san waye mahaifina? Kuma kun san mahaifiya ta? Koda bana wani aiki ba zan rasa kuɗi ba, duk abin da nake so ina samu in dai bai fi ƙarfin su ba."
Rungumeshi suka yi suna jin daɗi dan harda wasu da suka dawo daga makaranta.
Malikat
Kawu kallon sama da ƙasa ya yi ma Abba san nan ya fita bai ce komai ba.
Yana fita Malikat ta fashe da kuka ta na ce wa.
"Dan Allah Abba mai nene dalilin faɗanku da Kawu.?"
Abba ne ya fara rarrashinta ganin ta yi shiru ya ce.
"Bana son kusa ma kan ku damuwa wannan matsala ce tsakani na da ɗan uwana, idan Allah yasa za ku ji ko mai nene za kuji kada ku tada hankalin ku."
Malikat ta ce.
"In sha Allah Abba amma ba ma jin daɗin abin da ya ke faruwa."
Murmushi ya yi ma ta ya ce.
"Allah ya yi maku albarka Allah ya kare min ku, ku ta shi ku shiga ciki kun ji ƴan albarka."
Murmushi suka yi a tare san nan suka shiga cikin ɗakin su.
Malik ne kwance a kan makeken gadonshi yana yin video call dasu Ammi da ka gan shi zaka san yana cikin farin ciki.
Ammi ta ce.
"Ta samu ne naga kana ta farin ciki.?"
Dariya ya yi ya ce.
"Ana fi sa'adāh."
Tun da Ammi ta ji ya yi larabci ta san yaron na ta yana cikin farin ciki.
Suna cikin firan ne ya ji ana ƙwanƙwasa ƙofa ya san babu me wannan aikin sai Hisham dan haka ya ta shi bai tambayi waye ba ya buɗe ƙofar, yana buɗewa Hisham ya jefe shi da harara ya na ce wa.
"Ɗan rainin wayyau ka kashe waya sai da ka ta so ni."
Dariya ya yi ya ce.
"Ka san na sha aiki na ga ji wallahi."
Dariya Hisham ya yi ya ce. "Ai kam dole ka ce ka sha aiki."
Malikat suna shiga ɗaki suka fara fira suna cikin fira wayar Malikat ta yi ƙara, da kamar ta share dan ta yi tunanin company ne suka tura ma ta message ɗin da suka saba.
Amma abin mamaki ta na duba wa ta ga numbern da ku san kwana uku kenan a na tura mata message da ita kuma message ne na soyayya, ta yi duk binciken ta bata gane ba dan an kulle duk wata ƙofar da za a ga ne mai numbern.
Saƙon ta fara karantawa kamar haka Assalamu alaikum masoyiyya ta fatan kin koma gida lafiya ina son ki dai na wahala wajen binciken ko ni wane ne dan wahalar da kan ki ke, amma ki sa ni duk wani abu da ki ke yi a kan idanuwana ki ke yin shi.
Kanta ne ya kulle ita a sa nin ta babu wanda take soyayya da shi sai mutum ɗaya Usman, kuma shima baya ƙasar ya yi tafiya.
Fatima ganin yan da ƴar uwarta ta shiga damuwa lokaci ɗaya ya sa ta ce.
"Adda mai yake damun ki ne.?"
Ba zata iya ɓoye ma Fatima komai ba saboda ba tada abokiyar shawarar da ta wuce ta, dan haka ta faɗa ma ta duk abin da ya ke faruwa tare da miƙa mata wayar ta ce.
"Ki duba wannan yanzu a ka tura min shi."
Itama Fatima ta shiga damuwa bayan ta gama karantawa ta tura waye kai mai ka ke so?.
Master yau babu batun dafa abinci order yasa a ka yi musu, kowa ya faɗa abin da yake so kuma daka doso gidan za ka ji ƙiɗa na ta shi,
Yau Master ya taka rawa.
(NIKAM NA CE BA DOLE ZAKAYI RAWA BA HANKALIN KA KWANCE KANA ƘWAMUSHE MA MUTANE KUƊI)
Ƴan sanda dole ta sa suka fara harɓi dan da alama mutane sun hassala.
https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U
FUSKAR ƁOYE
BY FATIMA BINTU HUSSEN
https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
BISMILAHI RAHAMANUR RAHIM
PAGE 1️⃣3️⃣and1️⃣4️⃣
Mutane ganin ƴan sanda na harbi ya sa kowa ya fara yin ta kan shi dan ceton ran shi.
Malikat har sun fidda rai da za'a mai do masu da amsa kusan 15mnt sai suka ji ƙaran shigowar message dama wayar na kusa da Fatima ita ta ɗauka ta duba ganin abin da aka rubuta ne ya sa ta ja tsaki,
Ka da ki ta da hankalin ki wajan sa nin ko Ni waye idan lokaci ya yi za ki sa ni.
Bayan Malikat ta gani ta ce "To yan zu ya zamu yi?"
Numfasawa Fatima ta yi ta ce "Ni ina ganin ya kama ta ki ce ki na son ga nin shi."
Malikat ta ce "A kan me zan ce ya zo ina son ga nin shi?"
Fatima ta ce "Ta hakan ne zamu gane ko shi waye kin ga da ga nan sai mu san dalilin bibiyar ki."
Malikat ta ce "shawara me kyau. Yanzu ƴan da za'a yi ki tura mashi message ki ce ina son ga nin shi."
Ha ka kam a kayi Fatima ta tura ma numbern message.
Malik ba dan ya so ba haka ya tashi ya yi wanka ya shirya suka fita zuwa wajan aiki.
San da suka isa abin ya yi sauƙi dan mutane sun fara watse wa,
Ya na zuwa ganin mutane ya sa hankalin shi ta shi ya na zuwa ya tambaye abin da ya faru kamar be sani ba,
Nan Dpo ya faɗa ma shi duk abin da ya faru da rashin sa'ar da basu yi ba,
Master bayan an kawo masu abinci suka ci suka ƙo shi san nan ya ce " Wan nan karon ba gidan marayu kawai zamu taimaka ma wa ba,"
Ina son mu taimaka ma al'umma da yawa da asibitoci da ƙauye ka mu ba ma wasu jari"
Muhusin ne ya ce "Master ya maganar wannan yarinyar ta tura message a kan ta na son ta gan ka."
(TO FAH WACE YARINYA KENAN IN TAI TSAME MA JI)
Hararar shi Master ya yi kafin ya ce "Ka ce ma ta ni ban shirya haɗawa da ita ba dan yanzu."
Muhusin ya ce "haba Master me zai sa ka ce haka sai wahalar da mutane ka ke kawai ka shirya ka je ku haɗu."
Nushi ya kai mai ya ce "Dan Allah ka da ka dame ni in ce ni na gani kuma baka san dalili na na yin haka ba idan yanzu na fito ta san ko ni wa ye za ta iya shi ga hatsari."
Muhusin ya ji zafin nushin da Master ya yi mashi shi fa a wannan maganar bai ga wani abun zafi ba,
Muhusin ya ce "shi kenan."
Saudi Arabia
Ammi ce ta kalle Abbi ta ce "Gaskiya na ji daɗin ganin yaro na a cikin farin ciki na kwana biyu ban gan shi cikin wannan ya na yin ba."
Murmushi Abbi ya yi ya ce "Kin san rayuwar yau da gobe wani lokacin babu abin da a kayi maka sai ka jika cikin ɓacin rai wani lokacin kuma ka tashi da farin ciki shi ya sa ake son duk halin da ka tsin ci kan ka ka gode ma Allah."
Ammi ce ta ce "Alhamdulilahi ala kullu halin."
Da ga nan ta ce "ya ka mata mu ta shi mu leƙa wajan Fatima ka ga tunda mu ka zo bamu haɗu ba."
Abbi ne ya ce "to ya shirya su ta fi."
Dama Arfa ta na can tun ranar da suka zo Madina ɗiyar Aunty Fatiam ta zo suka tafi.
Malik ba yan ya gama sauraran komai ya ce " Yanzu wa su su shirya su tafi wajan da abin ya faru na san zuwa yanzu za'a iya samun wa ta shidar.
Wa su daga cikin su suka fara shirin komai wa can.
Malikat su na zaune a falo su ne cin abinci wayar Malikat ta yi ƙara alamar shigowar message Fatima ce ta ɗa ga ido ta kalle Malikat,
Malikat ta ma ta alama ta bari su koma ɗaki duk abin da suke Umma na kallon su,
Umma ce ta ce "Kai lafiyar ku kuwa?"
Fatima ce ta ce "babu komai Umma."
Girgiza kai Umma ta yi ba dan ta yadda da su ba.
Malik ya na ganin sun ya kalle Hisham ya ce "Kaga Malam ka zo muyi abin da ya kamata."
Hisham bai ce komai ba ya taso su ka ci gaba da abin da ya kamata sun haɗa komai ne da wasu Cameras duk abin da suke su Malik na ga ni,
Jami'ai bayan sun koma wannan dajin da abin ya faru su kai ta ƴan dube duben su can suka hango wasu jakun ku na an sagale su a saman bishiya
[10/12, 18:41] hiameera437: FUSKAR ƁOYE
BY FATIMA BINTU HUSSEN
https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U
𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝑊𝐴𝑅𝐼𝑇𝐸𝑅'𝑆 𝐴𝑆𝑆𝑂𝐶𝐼𝐴𝑇𝐼𝑂𝑁 (𝐽 𝑊 𝐴)
𝑇𝐻𝑅 𝑁𝑂𝐵𝐿𝐸 𝑊𝑅𝐼𝑇𝐸𝑅'𝑆 𝑇𝐸𝐴𝑀
NA KUƊI ME NAIRA ƊARI UKU PHONE NUMBER 09023086483
Bismilahi Rahamanur Rahim
Page 1️⃣5️⃣and1️⃣6️⃣
END OF BOOK ONE
Dpo ne ya ce "Umar ji ka dauko wain can jakun ku nan."
Umar ya ji wajan bishiyar ganin tsawan shi baya kai wa sai ya fara ƙoƙarin hawa bishiyar bayan ya hau ya cilo da jakun kun ƙasa.
Malikat
Bayan sun shiga ɗaki suka duba saƙon da aka tura ganin an rubuta,
Lokacin haɗuwar mu bai yi ba idan lokaci ya yi ba sai kin nema ba ni da kai na zan nemi ga nin ki.
Tsaki ta yi ta ce "Fatima ya zan yi da wannan mutumin? ya zamar min bala'i gashi ko na yi boloking na shi ba ya yi da na yi ya ke fita."
Fatima ta ce "Da ga yau ko ya tura kada ki ƙara kula shi na ga al'ama ɗan iska ne."
Dariya Malikat ta yi ta ce "Ko kuma na chanza sim, kin ga idan na chan za babu ƴan da za'ayi ya samu sabuwar numbern ta."
Fatima ta ce "Hakan ma ya kama ta ayi."
Jami'ai
Bayan an dauko jakun kun nan Dpo ya matso kusa da su ya ba da umarnin a beɗe,
Umar ne ya kai hannu cikin tsoro ya na tunanin abin da zai ga a ciki,
Ya na buɗe suka ga facemaks da kaya da wasu ƴan ƙa nan takardu ko wanne da photon fuska da ban da ban,
Dpo
Hannu ya kai ya dau ka takardar ya beɗe ya na karanta abin da aka rubuta kamar haka,
Ni ne Master kuma zaki da kum bar wahalar da kan ku saboda lion ya wuce tunanin ku kuma ina nan zan chanza salo ga wasu ƴan kuɗi nan ko mai kwa din ga sha wajen neman master na bar ku lafiya.
Malik
Duk abin da suke yi suna gani shi da Hisham.
Hisham
Ne ya ce " amma wallahi wannan gayen ya raina ma mutane wayo."
Wani ban zan kallo Malik ya yi mai ya ce "ka ga Malam ka bar wata magana kayi abin da ya ke gaban ka."
Hisham
Bai ce komai ba ya maida hankalin shi kan computer ya ci ga ba da abin da ya ke yi.
Jami'ai
Bayan wannan abin da suka gani suka yi binciken da zasuyi a cikin dajin basu ga komai ba haka nan suka kama hanya su ka koma barek,
Suna zuwa Dpo ya ce "A haɗa meeting Yan zu yan zu."
Babu daɗe wa haka haɗa meeting ɗin.
Dpo
Ya ce "na baku dama kowa ya kawo nashi shawarar da abin da ya ke ga ni za'a samu ci ga ba."
Umar ne ya ce "Sir ni ina ganin mai zai hana mu ba shi damar yi magana da mu domin mu san abin da ya sa ya ke wahalar da mutane kun ga zai faɗa dalilin shi na haka idan wani laifi aka yi ma shi sai mu jam'ia mu zare hannun mu akan shi."
Malik ne ya ɗaga mashi hannu al'amar jin jina.
Dpo ya ce "kai kana ganin yin hakan zai zama mafita a gare mu?"
Shuru Umar ya yi bai ƙara magana ba.
Sannan Dpo ya ce "sara wani."
Asp ne ya ce " mai zai hana mu yi mashi bara zana mu ce zamu kama kowa na shi kunga idan mukayi mashi wannan barazanan hakan zai sa hankalin shi ya tashi ya miƙa kan shi."
Jin wannan shawarar ya sa Malik ya fashe da dariya.
Da mamaki su ke kallon su al'amar me ya ke ma dariya.
Cikin dariya ya ce " yo kai in ban da hauka mutumin da ba'a san shi ba ba'a san komai na shi ba shi ne ka ke maganar ayi mashi baraza da ya ke shi sakarai ne sai ya bar wa ta hanya da za ta sa a kama shi ko."
Kowa baki ya sa ki ya na kallon shi to a wannan maganar su basu ga abin dariya.
Dpo ne ya ce "ya isa haka dame za muji muna fama da bala'i kai kuma kama yi ma mutane wata dariya ai yanzu babu abin dariya a ciki."
Malik
Ya ce "yo dole nayi dariya ma na wannan shawara haka da ya ba da."
Ba wannan karan ba ne suka saba ganin haka ba dan kai tsaye idan akayi abu bai yi ma Malik ba mutum ko shi waye kai tsaye ya ke fitowa ya nuna ga shi ko wa n shakar shi ya ke ji Saboda ba ƙara min amfani ya ke da shi a ƙasa ba.
Haka suka ƙara ci zaman su amma basu samu wata shawara ba dan yawan ci shirme suke yi har gwanda ma shawara Umar,
Daga ƙarshe Dpo ya ce "wai nan jakun ku nan ku dau ke su ku kaisu ɗauki da aka sa ba aje yi duk wani abu da ya shafe shi."
Daga nan suka ta shi kowa ya yi ta kan shi,
Master
Cikin ƙan ƙanin Lokaci ya fara ba da taimako ga mutane ya taimaka ma makaran tu da masalatai da mara sa ƙarfi dan har gida ya sai ma wasu duk wannan abin da ake yi babu wanda yasan meyi dan sai dai kawai suga an fara aiki kuma idan suka tambaya sai dai kawai a ce masu wani bawon Allah ne,
Mutane sai magana ake yi abin da yakama ta ace ƴan siyasa da gwamnati ta yi amma sun kasa sai gashi an samu wani wan da ba'a san ko waye ba ya na yi.
Sosai mutane ke yin magana suna yi mashi addu'a
Wasu ƙauye kan da kanshi ya ke zuwa haka zaka ga wasu mutanan abin tausayi har aurar wa ya yi Allah kaɗai ya san taimakon da ya yi na mutane.
Saudi Arabia
Ammi bayan su ida gidan ƴar uwar ta Fatima sosai su ka yi murnar ganin junnah mijin Aunty Fatima ne ya fito ya rungume Abbi duk da suna haɗa tun da Abbi anan Saudiya ya ke aiki.
Arfa da gudu ta fito suka gaisa da su Ammi tare da Madina Arfa ce ta ce "Ammi kinga kuɗin da akh ya tura mana ya ce wai mu ce masasa".
Dariya Ammi ta yi ta ce "kai wannan Yayan naku ya na ji da ku."
Aunty Fatima ce ta ce "Malik yanzu baya son zuwa nan sai ka ce ba ƙasar shi ba Najeria ta riƙe shi."
Dariya Ammi tayi ta ce "kin san aikin su ne babu wani hutu suke samu ba."
Aunty Fatima ta ce "Allah dai ya tsare ni wallahi ban so ya zama sojan najeria ba."
Abbi ne ya ce "to ai najeriar ma ƙasar shi ce ko? tun da ƙasar mahaifin shi ne ai shi ma ƙasar sa ce."
Dariya suka yi domin sun gane nufin Abbi kwata kwata baya san ta ji ana faɗin laifin malik.
Bayan kwana biyu
Malikat
hankalin ta ya kwanta ganin kwana kusan biyar ba'a tura ma ta wannan message ɗin ba amma abin da ke ta da mata hankali ta lura kamar akwai masu bibiyar ta dan kusan yanzu idan zata je aiki zata ga wata ɓakat mota ta na bin da har ta je ta dawo kuma ba wajan aiki ƙadai ba har a unguwa ana mata wannan abin hankalin ta ya kasa kwanciya ba ta san wanda zata faɗa ma wa ba,
Suna zau ne Umma ba tana nan suna fira ganin yan da Fatima ke ta ma ta magana amma hankalin ta kamar baya kai ya sa ta ɗan kai mata duka,
A ɗan firgice! ta ce "Fatima me ya faru za ki yi min wannan dukan?"
Fatima ta ce "na ga kwana biyun nan kamar kin cikin damuwa?"
Murmushin ƙarfin hali tayi ta ce "me ki ka gani? ni babu abin da yake damuna."
Ita ma Fatima murmushi ta yi ta ce "tabbas ni nasan da abin da yake damun ki."
Ganin dai Fatima ta gano ta ya sa ta ce "ina cikin damuwa kamar yan da ki faɗa."
Fatima ta ce "ni dama na sani, na san da abin da ke damun ƴar uwata."
Nan ta kwashe duk abin da ke damun ta ta faɗa ma Fatima.
Fatima ta ce "ni ina tunanin wannan me tura maki message ne ya sa ake bibiyar ki ai kinga kwana biyu bai turo ba."
Malikat ta ce "nima nayi wannan tunani amma ina tsoron kada su cutar da mu."
Fatima ta ce "in Sha Allah babu abin da zai faru saboda da cutar da ke zasuyi da tuni sunyi abin da suka ga dama."
Malikat ta ce "Allah kaɗai ya san komai kawai ki taya ni da addu'a."
Daga nan suka ci ga ba da firan su
Malik a gajiye ya koma gida saboda ya sha aiki babu wasa yau tun da ya je office yana kan computer sallah kawai ke tada shi.
Bayan ya shiga gida wanka ta yi ya chanza kaya ya kwanta ya ƙure ac har ya kwanta kuma ya tashi ya dauka wata ƴar ƙaramar waya ya tura message
Washe gari
Yau ƴan san sun tashi cikin tashi hankali ba ƴan san da kaɗai ba harda mutanan gari sakamakon me bama gwamna Shawara da aka wayi gari babu kuma har gidan shi aka je aka dau ke shi cikin dare,
Sunyi tunanin masu garkuwa da mutane ne amma har ƙarfe kusan bakwai na dare ba wani labari.
TOFAH ABU YA YI ƘAMARI ME BA MA GWAMNA SHAWARA GUDA AKA DAUKA
TO WAYE DA WANNAN AIKIN
WAI SHI WAYE ME BIBIYAR MALIKAT NIFA INA TSORON KADA WANI ABU YAJE YA SAME TA
NI INAGA FA KAMAR MASTER NE KE TURA MATA WANNAN MESSAGE ƊIN
GASKIYA MASTER DA ZAFIN KA YA KAMATA A BINCIKA SHI MAGANAR UMAR YA KU KE TUNA NI IDAN WANI NE YA KE SAMU WANNAN KUƊIN
NIFA NA FARA ZARGIN MALIK HARGA ALLAH SABODA WASU ABUBUWAA DA YAKE YI
WANI MESSAGE NE MALIK YA TURA
KUN LURA AKWAI ABIN DA MALIK DA HISHAM SUKE SHIRIN YI KUWA
ME YE DALILIN ƳAR TSAMAR DAKE TSAKANIN BABAN MALIKAT DA YAYAN SHI
WAYE MASTER MEYE DALILIN SHI NA HAKA
WAYE MALIK
SAI DAI MUN HAƊU A BOOK TWO
ALHAMDULILAH A NAN NA KAWO KARSHIN BOOK ONE DUK ME SO ZAI BIYA ƊARI UKU TA WANNAN BANKIN 9023086483 FATIMA HUSSAIN OPAY
MY NUMBER 09023086483 BAN DA KIA PLEASE
[10/12, 19:11] hiameera437: Ɗazu aka yi family meeting wai duk jikoki su dinga bada 2k duk wata, na ce a cire ni a familyn kawai😂😂a
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect