Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
tura mai daga nan kuma ya cigaba da game, Ya na cikin game din ne muhusin suka shigo shida Emma. Da mamaki Malik ya je kallon su Emma ne ya ce "good evening Master." Cikin mamaki master ya ce " evening yau shi ka dawo baka faɗa min ba?" Dariya Emma ya yi ya ce " yanzu na dawo shi ne na kira babban mutum ya zo ya dauko ni. Hararar wasa muhusin ya yi ma shi ta ce "wai kai baza ka dai na ce min wannan su nan ba ko?" Dariya Emma ya yi ya ce " naga da shi aka san ka ko." Master ne ya ce " ai fa yanzu zan fara raba faɗa tunda kun dawo kafin wain can kajin kuma su dawo." Dariya su ka yi su duka dan sun sa dasu Ammar sun dawo shi ke nan master ya fara ciwon kai kuma. Daga nan suka shiga fira anan ne master ya ke basu labarin bayanan ƙauyen da aka tura mashi da kuma taimako da ya ke so ya kai masu. Malikat kam ta na cikin cin abin ci Abba ya shigo gidan da sallama suka amsa mai bayan sun gaisa ya zauna ya na kallon Malikat, Ganin kallon da Abba ya ke ma ta ya sa tayi ƙasa sa kan ta da idan kaga Abba na ma mutum wannan kallo to akwai wani abu kenan? Abba ne ya kira sunan ta ta amsa. Abba ya ce " gaskiya wannan aiki ki aji ye shi kada ku jefa kan kin cikin matsala." Ji tayi gaban ta ya faɗi duniya ba bu abin da take so kamar aikin nan nata amma rana ɗaya Abba ya ce ta aji ya. Abba ganin ta faɗa tuna ni ya sa ya ce " kiyi haƙuri ba ina so na ɓata maki ba ne kinga ni ba wani hali ne da ni ba yanzu fira da kika yi da wannan mutum kin ji yan da mutane ke magana, Ni tsoro na ɗaya kada mutane su fara zargin ko kin san shine ke ce Ki ka gaiyato shi. Cikin sanyin Muryar ta ce "shi ke nan Abba tun da haka ka ce." Abba ya ce "Tom Allah ya yi maki albarka." Ta amsa da amin. Daga nan suka ciga ba da fira suna cikin firar ne Fatima ta shigo Fatima ita ke bima Malikat daga Malikat sai ita. Washi gari Ban san ya aka yi ba naga Malikat wajan aiki kuma tana zuwa ba ta daɗe ba ƴan sanda suka zo wai bincike ta ba da numbern da aka turo saƙon nan da kyar aka samu saboda ya na ƙasa. Bayan ta ba su numbern suka amsa suka ce idan da wani binciki zasu ƙara dawo wa fatan zata basu haɗin kai. Master duk wannan abin da ke faruwa ya sani dan tun a ranar da abin ya faru Mahusin ya ba shi shawara akan ya yi binciki akan ta. Kuma cikin ƙan ƙanin Lokacin aka bincika mai komai akan ta daga kan family ɗin ta har aikin da Abba ya ke anan ya ke jin labarin Abba ya hana ta zuwa aiki, Shi kuma ya san ya nda ya yi ya sa aka je wajan Abba aka ce kada ya damu akwai tsaro sosai za'a kula da ita kuma rashin zuwan ta aiki shine zai sa ma ai yi zargi a kanta, Abba kuma bai yi musu ba ya amin ce. Yau su Ammi jirgin su zai ta shi zuwa Saudiya dan haka tun da asuba Malik ya kwashe su zuwa aripot. Ba su daɗe da zuwa aripot ba jirgin su Ammi ya tashi. Malik ya kama hanya ya koma wa gida yana tafiya ya na tuna nin yan zu ne ma hankalin shi zai fi kwanciya zai guda nar da aikin shi yanda ya kamata tunda su Ammi ba su nan kuma za su dade ba su dawo ba tunda an samu holiday. Master bayan Khalid ya duba baya nan ƙauyen nan ya faɗa ma master zai shi ga gaba akan aikin, Nan take ya tura mai kuɗin da za su isa har agama. Ƴan sanda sunyi bincike akan wannan numbern da aka tura saƙo amma ba su samu komai ba dan an toshi duk wata hanya da zata sa a gane me numbern ko yanzun ma suna cikin aiki aka turo masu saƙo da wannan numbern, Dama kun dai na bincike a kaina domin waje n ayi? Kana magana a kan adalci kamar wani mutumin arziƙi. Baya master ya karan sa ya tura na su da za ka ga mutumin arziƙi gobe da misalin ƙarfe 08:30pm za'a wuce da kuɗin waje a motar shugaban ƙasa idan kun isa za ku iya zuwa wajan nikuma a gaban ku zan yi abin da nike so kuma baku isa kuyi komai akai ba. Wannan message ne fa ya tada masu hankali hakan ya sa suka fara shiri a kan gobe. FUSKAR ƁOYE BY FATIMA BINTU HUSSEN https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U https://chat.whatsapp.com/Jp93APpPrfe9IezRu9zH91?mode=ac_t NA KUSA GAMA FREE PAGES. WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE ƊARI BIYAR BABU YAWA. NUMBER WAYA NA 09023086483 ACCOUNT NUMBER 9023086483 FATIMA HUSSIN OPAY Bisimilahi Rahamanur Rahim Page 7️⃣and8️⃣ Ammi sun sauka Saudi Arabia lafiya in da suka sauka a unguwar su Al otaibiyah Abbi ne ya je ya Ɗauke wani abin mamaki shi da na ga sun shiga wa ni babban gida gidan ya haɗu ma sha Allah. Najeria Zaki tun da ya ga ya samu abin da ya ke so kawai sai ya ta shi ya shiga ɗakin shi ya na zuwa ya kunna speaker ya saki ƙiɗa da ma idan ya na cikin farin ciki ya na kunna waƙa dan har rawa ma ya iya dama gwanin ta ne. Malik bayan sun yi waya da Ammi ta faɗa ma shi sun isa lafiya. Suna gama wayan ya haɗa ina shi ina shi ya fita ya na saƙe saƙe a rai. WASHI GARI Master tun da safe suke ta shirin yan da za su fita su na so wannan aikin da zasuyi ya Girjiza jami'an tsaron ya na so su san shi Master ya wuce tuna nin su. Suma Jami'a ƴan sanda har da sojoji da sauran jami'a tunda safe hankalin su na kan aikin da zasu yi suna so a wannan karan su yi nasara ko ba komai mutane za su dai na tuna nin ya fi ƙarfin su, Wannan karan sun sa ma kan su su ne keda nasara. Malikat bayan ta gama aikin ta ta haɗa ina ta ina ta ta yi hanyar gida, Bayan me napep ya a jiye ta ta shiga gida jin muryar Yayan Baban ta ya sa ga banta ya faɗi dan ta san in dai ya zo gidan su ba alkairi ya ke kawo shi ba, Cikin sanyin jiki ta shiga da sanyin jiki bayan ta yi sallama ta duƙa har ƙasa ta gaida shi, Sama sama ya amsa ya na bin ta da kallon banza, Kaka ta ce "lafiya ka ke yi ma jika ta wannan kallon?" Kallon Kaka ya yi ya ce "Ba dole zan kalle ta ba an bar yarinya ta na ta yawo a gari ba ta a can bata a can." Kaka ta ce "Kai dai wallahi an yi mara hankali ban san yaushi ka koma haka ba. ka manta da Allah ya ke bada miji komai lokaci ne." Dariya ya yi ya ce "A ce yarinya shekara ashirin da biyu amma ta ma yawo a gari ai kamata ya yi a haɗa ta da koma wayi." Cikin takaici Kaka ta ke kallon Ɗan nata ta rasa wa ce kalar ƙi yaiya ce tsakanin Yaran nata. Malik ya na zaune a wani ɗaki da alama ɗakin da suke aiki ne dan duk computers ne a ciki shida wasu ne ya ke yin aikin, Ɗagowa ya yi ya na kallon su da murmushi shi kaɗai ya san abin da ya ke yi ma murmushi, Ɗaya daga cikin mutanen ne ya ce "ya dai Man? dan na san wannan murmushi na ka na nasara ne." Bai ba shi amsa ba sai ya ce "yanzu na tsara yanda komai zai ta fi da yanda zamu yi nasarar kama Master shi da yaran shi." Iho suka sa su na kiran sunan shi. Kallon Hisham ya yi ya ce "muje ja ka taka min dan ni nagaji zan wuce gida." Hisham ya bi bayan shi ya na murmushi. Suna zuwa suka shiga mota Malik ne ya ce "ka kula na shirya yan da komai zai tafi Ni zan wuce na fara shirina." Hisham ya ce "ai ni ban gane ba kada a zo reshi ya juye da mujiya." Murmushi Malik ya yi ya ce "ka da ka manta Malik da ƙwaƙwalwa ya ke aiki kuma ya ke tuna ni duk abin da zasu yi baza su iya cin nasara ba, Kai dai kawai ka kula kayi komai a natse. (WAI WANNAN MALIK DIN SHIKUMA DAGA INA WAI BA JAMI'IN TSARO BANE NI FA KAINA YA FARA KULLE WA.) Dariya Hisham ya yi ya ce " Wallahi na sanka amma gaskiya kai ɗin nan ba ƙara min ɗan iska ba ne." Dariya suka fashi da ita san nan Hisham ya fita daga mota ya koma ciki. Shikuma Malik ya fita da ga wajan da gudu. Master kam tun ƙarfe uku suka gama shirin su Master ya yi shigar tsofafin idan ka gan shi sai ka rantse irin tsofafin ƙauyen nan ne ya saka wannan facemaks din hada gashin baki da gemu. Shima Muhusin kusan kalar shigar Master ya yi shikuma Emma ya yi shigar baban fastor. Sai wasu da su kayi shigar irin ta ƴan wasan borin nan. Suka fito wani ya hau keke wani ya hau mashine sai su Master suka hau wata ruɓabiyar mota suka fita kai tsaye suka fara tafiya sunyi tafiya Sosai har su ka fara fita garin Katsina. Suna tafi suna haduwa da jami'an tsaro jefi jefi. Suna isa wani waje kamar gona duk ciyawa su duka suka fara noma kamar gaske ga jami'an tsoro nan ta ko ina suna jiran su ga ta inda master zai bulo. Master suna cikin wannan noma suka hango wata mota ta taho da gudu Mahusin ne ya samu wani ƙarfe ya sai ta motar da shi ƙarfe ya shiga cikin tayar motar nan tayar ta fashi. Jami'ai sun ji ƙara fashiwar abu amma basu kawo komai a ran su ba sun yi tuna nin ko wasu daga cikin su ne suka yi harɓe. Master hannu ya ɗaga ma Muhusin alamar jin jina murmushi muhusin ya yi. Suka ƙara so wajan motar irin zasu bada taimako a chanza tayar motar direban motar da Emma suna gaban motar suna koƙarin kwance tayar motar. Master da Muhusin ne su ka yi bayan motar wani abu Master ya curu ya daura a bot ɗin nan da nan ya buɗe jakun kuna ne suka gani kusan guda biyar ko buɗe wa basu tsya ba suka kwashi jakun kunan, Muhusin na tsaye Master na kai wa cikin wancan Motar ta ta su sai da suka gama sai ta komai san nan suka ɗauko wasu jakun kun nan wa wancar motar ta su suka saka su a cikin motar direban. Lokacin da suka gama musayar jakun ku nan lokacin su kuma suka gama cire tayar suka dau ko wata. Bayan sun gama sauya tayar motar direban ya yi masu godiya har da ba su kuɗi wai su ci abinci. Master har ya hango shi yana marin shi wato dan ya raina masu wayo su zai ba ma wasu kuɗi wai su sai ya abinci. Me motar ya na tafiya Master ya dauka wayar shi ƴar nokia ta gaji da tsufa dan duk an liƙe ta da lobari. Wata number ya tura ma message ya rubuta Master ya gama aikin shi ƙana nun ƙwari. Jam'i da ke can suna baza idanu ta idan za suga mota ta bul lu da kuma Master, Wata mota ce ta taho suna ganin motar suka gane ta gidan gwamnati ce hakan ya nuna masu cewa wannan motar ita ce motar da suke jira, Kuma lokacin ne message ɗin master ya shi go wayar shugaban su, Hankali a tashi ya ke nuna masu message ɗin nan suka shiga yin zufa, Master kam bayan ya tura message ɗin Muhusin ya ce "ya kamata mu wuce." Master ya ce "Ka manta zaki baya tsoro sai dai aji tsoron sa?" Muhusin shi fa ya na mamakin ƙarfin halin wannan bawon Allahn. Jami'a kam motar na iso wa suka duba suka ga ita ce nan suka shiga yi mai tambaya da kamr ya sahari su amma ya cigaba da basu amsa, Sai da suka ce ya buɗe but ɗin motar suna so su duba wani abu, Ganin kamar zai yi masu gadama shugaban jami'an ya ce "ka san Zaki?" Cikin zaro idanu ya ce "waye bai san labarin shi ba." Jam'i ya ce "to zaki nan ya na jiran ka ƙara sa ya faru ce ka." Wani ne ya ce "tun da ka taho ka haɗu da wani ko wa su?" Direba ya ce "Eh na haɗu da wasu mutane har suka taimaka min na chanza taya da tayar ta fashe." Salati wani ya ɗauka ya ce "shi kenan an gama wallahi ya yi nasara." Wannan maganar ta ƙara tada masu hankali. Nan suka buɗe but ɗin suka zuge zip ɗin ja kun ku nan abin da suka gani ne ya ta da masu hankali a me makon kuɗin Saudi Arabia dana America sai suka ga kuɗin najeria a kuɗin ma kuɗi mafi ƙaran ci Naira biyar biyar ne aka jera saba ɓi alamar an kwashi wain can. Direba kam sume wa ya yi sabo da tashin hankali wasu daga cikin jam'i an ne suka bi hanyar da ya buyo. TOFAH GASKIYA WANNAN MASTER BA ƘARAMIN JAIRI BANE WANNAN AIKI HANA TO YA ZATA KASAN CE SHIN ƳAN SANDA ZASU KAMA MASTER KO KO YA CI BANZA. FUSKAR ƁOYE BY FATIMA BINTU HUSSEN https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U https://chat.whatsapp.com/Jp93APpPrfe9IezRu9zH91?mode=ac_t https://chat.whatsapp.com/LZtufHUnlqUFvnBvvoUWs3?mode=ac_t WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE ƊARI BIYAR NE BABU YAWA A TUN TUƁENI TA WANNAN NUMBER 09023086483 Bisimilahi Rahamanur Rahim Page 9️⃣and 1️⃣0️⃣ Master ya duk wannan abin da yake faruwa akan idan shi kuma ba su kai motar ko ina ba sai suka sa ka tamfal suka rufe motar suka koma suka ci gaba da noma, Ganin ƴan sanda sun yo in da suke ya sa ya yi ma su alama da su cire facemaks ɗin da su ka sa ka kayan ma su ka cire na sama, Suka yardda akan hanya yan da ƴan sandan za su gani, Suka koma suka ci gaba da noma. Ƴan sanda su na tafiya suna harbi har suka ƙaraso in da suka ga kayan su Master da suka ajiye, A rikice suka dauka suna dubawa wani ne ya ce "wannan fuskar na gan ta tana tuƙa keke shugaban su ne ya ce "to ni duka fuskokin nan na gani har na taimaka ma wani da ga cikin su" ya faɗa ya na nuna fuskar da Master ya sa. Ganin dai wannan ba kai su zai yi ba ya sa suka ƙara so wajan wasu mutane da suke noma, Babban cikin su ne ya yi sallama suka gaisa bayan sun gaisa ya ce "dan Allah ina da tambaya?. Wani tshone ya ce "Yaro yi tambayar ka Allah ya sa na sani." Shugaban su ya ce " Dan Allah Baba baka ga wasu mutane a nan ba?. Tsohon ya ce " Yanzu na ga su sunyi can a wata mota." Ai da gudu suka yi hanyar da ya nuna masu. Master ga nin sun ta ya fashe da dariya harda dafe ciki. Malikat ganin ko ta ci gaba da tsayewa a gaban kawun na ta baƙin ciki za tai ta kwasa, Da gudu ta ruga ta shige part ɗin su ta na shiga ta faɗa cikin Umma ta sa ki wani ku ka me cin rai cikin kuka ta ke ce wa "Umma me mu ka yi ma Kawu baya san mu?" Murmushin da yafi kuka ciwo ta yi ta ce "Haba Malikat na ce in dai Kawun ku ne ki daina ta da hankalin ki har ki sama kan ki damuwa shima mahaifin ki bai tsira a wajan shi kiyi haƙuri wata rana sai labari." Fatima ce ta fito daga ɗaki ta ma ce wa "Wallahi Umma mutumin nan duk ya zubar da mutumcin shi a idona shi ya sa wani lokacin ko gashi shi ba na yi wallahi na tsane shi." Umma ce ta ɗaka ma ta tsawa! ta na ce wa "Ta na cewa ka da na sake jin irin wannan maganar a bakin ki ko ma miye ya ke yi ɗan uwan mahaifin ki ne dole za kuyi haƙuri." Suna cikin wannan maganar suka ji sallamar Kawun ya shigo, Umma ce ta amsa ta ce "Ka shigo mana." Kallon ta ya yi san nan ya shi go ta gaishe shi ko amsawa bai yi ba ya kama faɗa, A kan an bar Malikat ta na yawo a gari a kan aiki ta ke zuwa wa ma ya sani ko wani wajan ta ke zuwa ta yi iskancin ta amma a dinga ce wa ta tafi aiki. Maganar da ya jefi Malikat ta iskanci ita ce ta chaki Umma a kirji har taji ba za ta iya yin shuru ba, Cikin fusata ta ce "Haba malam ya za ka zo ka cika mu da hargagi har kana jifar Ƴata da maganar iskanci to wallahi zan dau ka ko mai amma ban jifar Yarana da munanan kalamai." Kawu ya ce "Duk abin da zaki faɗa ki faɗa bazan ji zafi ba saboda ina son ki ki ɗin rayuwa ta ce." (TA SHIN HANKALI NI KAM BAN GANE BA WAI BA YAYAN MIJIN TA BANE TO ME YA KAWO MAGANAR SOYAYA A CIKI) Fatima ce ta ce "Umma me ya ke nufi na ji ya na wa ta magana warda ban gane ba dan Allah ki faɗa mana wani abu mana." Umma ce ta ce "Ga shi nan ki tambaye shi mana Ni ban san abin da ya ke magana a kai ba." Suma cikin gaka Abba ya yi sallama ya shigo, Ya na ganin ɗan uwan na shi ya haɗe rai cikin ɓacin rai ya ce "Me ya ce me ta kawo ka nan ko ka zo ka wulaƙanta min iyali ne? To wallahi ka fita harka ta idan ba haka ba wallahi hukuma ce zata raba mu dalilin da ya sa Ni ke share ka a wa ni abin bana kulawa saboda mahaifiyar mu ne kana cin albarka cin ta, Ya haɗa hannuwan🙏🏿 sa alamar roƙu dan Allah ka fita daga rayuwa ta ka bar ni na samu salama Ni da iyali na sanin kan ka ne wa ni baya auren matar wa Ni." Master sai da suka ɗauka tsawon lokacin kafin suka bar wajan kai tsaye gidan su suka wuce, Master suna zuwa ya zauna akan kujera ya kalle Muhusin ya ce "Ya kamata mu ƙara ruɗa wain can banzayin." Muhusin ya ce "Wallahi kam in banda rashin hankali ai ya kama ta a ce mu ma sun bin cike mu amma da ya ke ƙwaƙwalwar kifi gare su amma wai a haka suke alfahi su ne masu ƙare ƙasa." Murmushi kawai Master ya yi, Wayar shi ya ɗauka ya nemo wata number ya fara rubutu kamar haka, Masu ƙare ƙasa masu kula da dukiyar ƙasa kun ce ku ke da nasara ya a kayi ku ka bar Master ya yi nasara bayan sun wuce Master ya na nona shi da yaran shi ya tura da emjo ɗin dariya🤣🤣🤣🤣 (WAI JAMA'A INA MALIK YA SHIGA NE? A TAIKAMA A LALUBU MA NA SHI) Tashin hankali Dpo na ganin wannan message ya tashi ya na huce ya daukar cup ɗin da ke gaba shi ya yi jefa da shi a nushi bango, Wain da ke ɗakin taron ne suka bishi da tambayar ko lafiya?, Wayar kawai ya meƙa ma su ya ma kasa Magana. Asp ne ya ce "yan zu ina ga yanda za'ayi a nemo Malik ƙila shi ya taimaka mana da wani abun." Su duka suka yi na'am da maganar dan haka wani ya fara kiran Malik amma wayar bata shi ga. Dpo ya ce "gaskiya wannan yaron shuman cin shi ya yi waya amma ya a kayi ma ba mu binciki wainan mutanen ba kuma abin da ya daure min kai naga wata mota a rufe wan da da alama motar ba'a daɗe da rufe ta ba ya kamata mu koma mu ƙara bincike." Nan da nan aka shirya wasu bataliya suna fitowa waje kuma su ka ga mutanan gari sun cika wajan suna so su basu amsa a kan maganar da su kai ta cika baki zasu kama Master. Kuma wani abun tashin hankali ana cikin wannan abin aka saki wani video a media wani mutum ne zaune a wani ɗaki fuskar shi rufe da ɓakin wani abu ba'a ga nin shi magana ya fa ra kamar, Hey mutanen gari nine Zaki Master ya kama ku binciki masu ƙare ƙasa ya a kayi Master ya ƙuɓuce masu ko da ya ke ai ba abin mamaki ba ne bari na faɗa maku gaskiya cin hanci na basu ya na faɗin haka ya ce a ƙintsi. 🙃TOOOFAH ANA GWARAMA SU DPO ANGA TAKAI ALLAH YA RABAKU DA MUTANAN GARI LAFIYA FUSKAR ƁOYE BY FATIMA BINTU HUSSEN https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U https://chat.whatsapp.com/Jp93APpPrfe9IezRu9zH91?mode=ac_t https://chat.whatsapp.com/LZtufHUnlqUFvnBvvoUWs3?mode=ac_t *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE ƊARI BIYAR BABU YAWA MY NUMBER 09023086483 FREE PAGES Bisimilahi Rahamanir Rahim PAGE 1️⃣1️⃣and1️⃣2️⃣ Wannan videon ne ya ƙara tada tarzoma da tashin hankali nan mutane a ka fara magana, wasu suna daukar duwatsu suna jifar ƴan sanda da su, Ta ɓangaren Master kam ya na cikin farin ciki dan duk abin da ke faruwa yana gani, musamman ya tura ƴan jarida a kan su dauka komai su ɗaura a live haka yasa a ke

Chapter 2 of 4