Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta tsugunna a wani waje. Duhun da d'akin yayi yasa ba'a ganin komai bazaka iya gane menene a ciki ba. Cikin wata irin murya kamar ba ta-ta ba tace, " Yaushe??? Taku. INDO CE.. [25/02, 10:41 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* (Masarauta) Mallakin *INDO CE..* Marubuciyar SIRRIN K'ETA. A JINI 'DAYA. 🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼 *Page~3* بسم الله الر حمن الر حيم "Yaushe ne zakiyi magana??? Meyesa bazaki bani amsa ta ba?? Sai yaushe ze zo??? Kinyi shiru ki fad'a min!!!" Tayi maganar a tsawace. Me gadin gurin ne ya shigo da fitila yana haskawa.. Wata Mace ce a tsakure a jikin bango ta had'e kai da guiwa gashin ta yayi buzu-buzu kaca-kaca ga tarin datti, Tsawar da Maharaniey, (Sarauniya) ta daka ce tasa ta d'agowa tana zuba mata firgitattun idanun ta wanda sukayi jajur,, daka ganta ka ga mahaukaciya saboda irin d'aud'ar da take jikin ta da kuma yanayin ta. Ido ta zuba mata suna kallon kallo ba tareda tayi magana ba. Maharaniey ta k'ara da cewa, "kiyi magana kafin ranki ya 'baci, ki fad'a min mana, meyesa kika dena magana ki bud'e baki kiyi min bayani" Jijjiga ta ta shiga yi tana cewa, "kiyi magana ki fad'a min yaushe ne??? Hadima Farhana ce ta matso zuciyar ta na k'una cikin 'bacin rai tace, " gaskiya ranki ya dad'e ta wata fuskar ke muguwa ce, sai yaushe zaki dena azabtar da wannan matar??? Meyesa zaki za'ba mata wannan rayuwar?? Shin menene abunda kike so daga gareta da har kika kasa jin tausayin ta dan tak'i fad'a miki?? Wannan be dace ba" Da mamakin maganganun da Hadima Farhanaa ta gaya mata ta juyo a fusace tana zazzare mata manyan idanun ta, cikin Hasala tace, "ki rufe min baki, kece zaki fad'a min abunda ya dace ne?? Yaushe ne kika samu matsayin da zaki duba tsabar idanu na ki fad'a min irin wannan maganar??? Me kika taka ne Farhanaa???????? Hadima Farhanaa tace, " ban taki komai ba tinda ni bani da mulki bani da dalilin sa, amma gaskiya ce nake fad'a miki me wannan matar tayi miki da zaki kulle ta anan shekara da shekaru?? Kuma ace bazan fad'a ba ya kamata kiyi adalci, kullum kin takura mata da tambaya, shin ranar mutuwar ki kike tambayar ta ne ko meye???? A fusace Maharaniey (Sarauniya) ta zaro wata takobi da akayi mata mazauni a jikin bangon d'akin wanda aka gina shi da zallar dutse, Cikin tsananin Fushi ta kai mata Takobin da niyar raba kanta da gangar jikin ta ba tareda tunanin kuskuren da take shirin aikatawa ba. Wani irin gurnani matar tayi tareda yunk'urawa ta mik'e tana girgiza kanta da iya k'arfin ta tana fizge fizge, tana wani irin ihu, kamar me cutar iska. Dakatawa Maharaniey, (Sarauniya) tayi jikin ta na rawa saboda tsabar 'bacin rai, ta dad'e a haka kafin tayi wurgi da takobin ta kalli Hadima Farhanaa, cikin Izza tace, "Farhanaa ki dinga banbance matsayi na da naki, karki manta nice silar zuwan ki duniya, ki dena d'aukar kanki a wata abu ke ba komai bace face baiwa ta" Daga haka tasa kai ta fice daga kurkukun a fusace, kai tsaye bayan masarautar ta nufa bakin wani k'aton kududdufi k'oramu suna ta gudana da ruwa ta ko ina ga sanyi da yake tashi a wajen tsuntsaye sai yawo suke suna lelewa, tsayawa tayi ta rungume Hannuwan ta cikin k'irjin ta tana babbaza ido, har wani lokaci kafin zuciyar ta ta fara yin sanyi. Hadima Farhanaa ce ta k'araso wajen cike da nadamar abunda ta aikata, durk'ushewa tayi kan guiwoyin ta- ta maida hannuwan ta baya ta hard'e su, kanta a k'asa tace, "Hazoor, (Ranki ya dad'e) ki gafarce ni idan har zuciyar ki zata iya hakan, idan baki huce ba ki d'auki mataki a kaina na d'auka, tabbas nayi kuskure ama sharrin zuciya ne ba da son rai na ba, kwata-kwata bani da niyar 'bata miki rai bansan hakan zata faru bane" Lumshe ido tayi tareda sauke wani zazzafan numfashi, ba tareda ta kalle ta ba tace, "ina Abdullakareem??? Hadima Farhanaa tace, " yana nan cikin kwanciyar hankali ba abunda yake damun shi" Jinjina kai tayi ba tareda tayi magana ba ta juya ta koma cikin Tajmahaal. Da tsakar dare ta tashi ta shiga wani d'aki, babu haske sosai sai kad'an-kad'an, tarkace ne na abubuwan da suka fi kama da na tarihi, kan kujerar da ke tsakiyar gurin ta zauna ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana d'an karkad'a ta a hankali, k'arewa d'akin kallo ta shiga yi kafin janyo wata akwati ta bud'e ta, zuba wa akwatin ido tayi har wani lokaci kafin ta saki murmushi, cikin wata maraitacciyar murya tace, "yaushe zaka dawo??? Meyesa zaka guje ni?? Sai yaushe zaka zo gareni??? Murmushi tayi ta k'ara cewa, " nasan zaka zo, ko ba dad'e ko ba jima, nasan fushi kake dani, nima yanzu na canja na dawo kamar yadda kake son gani na meyesa bazaka zo ba?? Ita kad'ai take y'an surutan ta har wani lokaci sannan ta tashi ta koma turakar ta. Babbar Fadar Masarautar Phurlasirie, Cike take mak'il da jama'ar masarautar yayin da kowa yake hirar sa cikin nishad'i da walwala hayaniya ce kawai ke tashi. Shiru fadar tayi kamar wucewar tsawa, sakamakon busar da ta iso cikin fadar wadda take nuna alamar Maharaniey mahalakhshmie ta doso cikin fadar, Kowa tashi yayi tsaye ya k'ame tareda sunkuyar da kansa k'asa gami da dunk'ule hannuwan su na dama suka d'ora gefen k'irjin su, ba babba ba yaro haka tsoho da tsuhuwa haka maza da mata, kowa mik'a ban girma yake gareta. Tsaye tayi a bakin fadar ta lumshe idanun ta, cikin wata irin siga take motsa bakin ta a hankali ba tareda sautin abunda take fad'a ya fito ba, sai da ta d'auki d'an lokaci a haka kafin ta bud'e idanun ta, take suka k'ara rikid'a suka k'ara wani irin kwarjini da razanar da duk wanda yayi gigin tsoma nasa idon cikin su, Idan baka lura sosai ba bazaka ta'ba cewa tana k'ifta su ba sai in kayi mata kallon k'wak'waf hakan kuwa ba kowa ne yake iyawa ba, Cikin takun ta me cike da zallar izza da gadara ta saka k'afar ta ciki tareda k'ara rarraba idanu tana kallon mutanen da suka koma kamar basa motsi,, Har sai da ta dangana da kyakkyawar kujerar mulkin ta ta zauna sannan kowa ya zauna. Kowa yayi shiru yana tsammanin abunda ze fito daga bakin. An kwashi lokaci sosai kafin tayi magana cikin d'aga murya tace, "ina buk'atar sanin duk abunda yake gudana a ciki da wajen masarauta" Da sauri Wanda suke da Alhakin hakan suka taso tareda hawa kan tudun da ke gefen kujerar wanda aka tanada saboda su. Subbhu ne yayi gyaran murya kafin yace, " Ranki ya dad'e wasu daga cikin mutanen masarauta suna cewa sun kasa gane dalilin da yasa kika rad'awa yaro Abdulkareem sannan kuma kin enta Udday fiye da ko wane bawan ki ta dalilin haihuwar wannan yaro basu fahimci meye hakan yake nufi ba, har wasu suna cewa ko dai kina da alak'a ta jini da yaron" Jinjina kai tayi tareda zubawa Hadima Farhanaa ido. Hadima Farhanaa ta sunkuyar da kai cikin sanyin jiki. Kamar baza tayi magana ba sai kuma ta mik'e, ta fara takawa cikin k'asaita hannun ta rik'e da gefen mayafin Sarin ta, Juyowa tayi tana fuskantar jama'ar ta, cikin d'aga murya tace, "abu ne me kyau kaso wanda ya so ka da gaskiya, kyautatawa ga wanda ya kyautata maka abune me matuk'ar muhimmanci, kar ku manta da waye Abdulkareem kar ku zama butulu saboda wasu y'an tsirarun mutane suna son hure muku kunnuwan, ku tsarkake zukatan ku a koda yaushe kar ku bari wani yayi tasiri a zuciyar ku, ya kasance kuna yin komai da yak'ini ba tareda bin fad'ar wani ba, idan kun kasance wanda basu san waye shi ba kuyi tambaya ga iyayen ku da kakannin ku, nasan ma ba lallai ne ace baku san da hakan ba, enta wanda ya enta ka shima abu ne me kyau, be zama dole sai wanda ka had'a jini dashi ba zaka kyautatawa, akwai su da yawa wanda su d'in jini na ne amma a hakan sune suke tunzura ku dan su jefa ku cikin wasi-wasi, Komai na yiwa udday ban biya shi ba domin kuwa shi kyautar d'an sa yayi min, har gobe shi mutum ne me daraja a idon masu daraja, yaro kuma na d'auka a matsayin d'ana ne, kuma wani abunda baku sani ba, koda bana raye ku sani Abdulkareem bin Abdulkareem shine magajin karaga ta, Yafi kyau ku maida hankali wajen kishin kanku da y'ancin masarautar ku da kuma yankin ku domin dubban halittu suna son ganin bayan Tajmahaal wadda kuka taso cikin ta tin kakannin kakannin ku, Ni dai na aminta kuma na tsaya ga al'uma ta na fansar da raina gurin kare su da basu y'ancin su, ban yarda da zalumci ko nakasu a wannan masarauta ba, duk wanda yayi k'ok'arin hakan?? Yasan meye hukuncin duk wani kaifi a fadar nan" Shiru tayi tareda k'ara taku biyu zafafa tana kallon su d'aya bayan d'aya. Shiru fadar ta k'ara yi kowa da tunanin sa, jikin su yayi sanyi matuk'a domin kuwa sun san a cikin zantukan ta babu na watsarwa. Wasu kuwa furucin ta na mallakawa Abdulkareem karaga shine ya k'ara hautsina tunanin su yayin da zuciyar su ke raya musu duk yadda akayi Abdulkareem d'an ta ne. Babbar tambayar kuma itace da wane mijin ta haifi Abdulkareem????? Kuma a yaushe???? Subbhu ne ya d'akko wata takarda yana dubawa, cikin d'aga murya yace, "ku saurari k'orafin da Shugabar mu zata saurara da kuma hukuncin da zata yanke a yanzu" A take nutsuwa ta k'ara wanzuwa a gare su kowa ya cigaba da sauraron su. Subbhu yace, "Hazoor !! ( Ranki ya dad'e) "Janela tana d'auke da juna biyu wanda ya kasance ya samu asali daga Narayan, Sakamakon keta haddin ta da yayi saboda son zuciyar sa ba tareda son ranta ba, iyayen ta sun mik'o kukan su gareki tareda sa ran samun adalci" Udday yace, "wanda suka san dasu ake su fito gaban shugaba" Fitowa sukayi suka durk'usa kamar yadda tsarin masarautar yake suna tsammani daga gareta. Zama tayi tareda lumshe ido ta sauke 'boyayyar ajiyar zuciya kafin ta bud'e su ta juye akan Narayan wanda jikin sa yake kyarma saboda tsabar tsoro da fargabar azabar shugabar tasu, a Take wani abu ya fara kwaranyowa cikin tunanin ta, Jinjina kai tayi tace, "wajibi ne auren ta gare shi bayan yayi zaman kurkuku na adadin lokacin da zata rabu da abunda yake jikin ta, kullum ze d'auki hukuncin bulalai hamsin ba tareda ya motsa ba, Bayan wata d'aya sai a koma yi masa duk mako d'aya, Ban da shan ruwa sai me zafi abinci kullum sau d'aya, Kulawa da d'an sa da matar sa ya wajabta a kansa indai ya 'bata mata rai ko ya goranta mata koda na lokaci d'aya hukuncin kisa ta hanyar jifa ya tabbata gareshi" Daga haka ta mik'e da niyar fita daga fadar jiki a muce. Tashin hankalin abunda take fad'a ya hana shi aiwatar da abunda yaso k'addamarwa akan ta, idanun sa sun kad'a sunyi jajur saboda azabar rad'ad'in da zuciyar sa take masa ya kafe ta da idanu yana wani irin huci, zuciyar sa tana raya masa irin mummunan matakin da ya dace ya d'auka a kanta. (Waye????????? Mu had'e a next page insha Allah) INDO CE.. [26/02, 8:29 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* (Masarauta) Mallakin *INDO CE..* Marubuciyar SIRRIN K'ETA. A JINI 'DAYA. 🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼 *Page~4* بسم الله الر حمن الر حيم Free page Da sauri mahaifin sa ya rik'o hannun sa wanda yake kakkarwa, cikin razani da shakka yace, "Arveen wannan be dace ba kasan wacece yarinyar nan kuwa??? Kai kad'ai ne ka rage min a yanzu dan haka karka sake kayi abunda zata cire maka kai a banza" Yana shirin yin magana ta juyo tana kallon su saboda ji a jikin ta da tayi ana firar ta. Ganin haka yasa sukayi saurin fuskewa dan gudun matsala. Kawar da idon ta tayi daga kansu kafin tace, "Arveen ka kula da hukuncin da na zartar, karka bari a samu matsala" Daga haka ta juya ta fice ba tareda ta k'ara kallon sa ba. Fizgewa yayi daga rik'on da Waziri yayi masa, a fusace yace, "wai yaushe ne har yarinyar nan tayi girman da zata iya ja dani??? A gaban mu fa aka haife ta, amma Baba ka kalla yadda kowa yake jin tsoron ta, idan haka ne meye amfanin rashin iyayen nata?? Da sauri waziri ya shiga jansa dan kuwa akwai mutanen ta a kusa,, da wani yaji abunda yake fad'e ze rattaba mata kuma yasan hukuncin baya wuce kisa, baza tayi duba da cewa d'an uwan ta bane kawai gamawa zatayi dashi. Sai da suka koma sashin su sannan ya sake shi, Yaja tsaki tareda cewa, " Arveen kana da matsala meyesa kake haka ne??? Kasan halin yarinyar nan, ina ruwan ka da zancen yarintar ta tinda dai har ta riga ta girma??. Yanzu abunda yake gaban ka shine wanda ya dace ba wai hurumin ta ba. Arveen ya zuba dogon tsaki cikin k'unar rai yace, "yarinya duk ta addabi kowa?? Kenan mu haka zamu k'are a bayin ta?? A k'a'ida ma fa sarautar tawa ce, Kaji fa abunda take cewa wai nine zan kula mata ma da hukuncin da ta yanke wa wannan yaron, saboda tsabar zalumci ai ni banga laifin shi ba, ai kuwa wata rana hakan zata faru akanta itama sai muga me dakatar dani idan zata iya" Waziri yace, "Arveen tinda dai na tabbatar baka son ta shikenan kawai kayi shagalin ka d'a na" Ya fad'a yana wani irin murmushi me cike da ma'anoni da yawa iri da kala. Cikin nutsuwa ta zauna a bakin makeken gadon ta tana maida numfashi saboda irin bugawar da zuciyar ta takeyi, cikin sassanyar murya tace, "Arjula?? " Cikin sauri Arjula ta k'araso kusa da ita ta sauka tana kallon ta. Itama kallon ta take har wani lokaci kafin tace, "Farhana" Tashi tsuntsuwar tayi ta fice daga turakar cikin sauri, Ba tareda wani 'bata lokaci ba sai gata ta dawo tareda Hadima Farhana. Da sauri ta durk'ushe a wajen tareda cewa, "Hazoor, (Ranki ya dad'e) na amsa kiran ki" Ido ta zuba mata har wani lokaci kamar wadda bata ta'ba magana ba da kyar ta iya cewa, "Abdulkareem a nomo min Hadima Urmi" Hadima Farhana ta jinjina kai ta tashi da sauri tana cewa, "yanzu kuwa Ranki ya dad'e, amma kafin na fita ya kamata kisha ruwa, abunda dai bakya so d'in ni kuma karanbani yayi min yawa bana son ganin ki cikin wani yanayi, kisha ruwa zuciyar ki zata samu salama Insha Allah" Kamar bazata kula ba sai kuma ta jinjina kai tace, "zan sha amma bayan na ganshi" Hadima Farhana tasan halin kayar ta dan haka tace, "yadda kika ce haka za'ayi, nagode da amsa tayi na" Bata kalle ta ba sai ma hannu da ta mik'awa Arjula, ita kuwa tayi d'araf akai. Basu 'bata lokaci ba suka dawo tare. Uwar Hadimai Urmi ta mik'a gaisuwar ta. Bayan ta amsa ta mik'e ta nufi hanyar fita. Hadima Farhana tace, "Uwar Hadimai Urmi Shugaba tana son ganin d'an ta ne" Hadima Urmi ta mik'e tana cewa, "zan cika aiki ya shugaba ta" Sashin gaba d'aya yara ne wasu sun tasa wasu k'ananu ne. suna ganin ta suka fara murna,, d'aya bayan d'aya suke zuwa suna ta'ba k'afar ta ita kuwa sai sa musu Albarka take, Masu kula dasu ma sai mik'a gaisuwa suke. Hadima Urmi ce tayi gaba zuwa cikin wani d'aki k'ayatacce wanda yaji ado da dukiya me yawan gaske ko ina tsaf sai walk'iya yake. Da murmushi akan fuskar ta ta shiga kai tsaye wajen d'an madai-dai-cin gadon da aka kwantar dashi yana shan baccin sa ta nufa, tsayawa tayi ta zuba masa ido tana k'ara jin k'aunar sa tana ratsa duka sassan jikin ta, a hankali tasa hannu ta shafi kansa har zuwa fuskar sa tareda furta, "Masha Allah" Ta'ba shin da tayi ne yasa yayi firgigit ya bud'e idon sa yana waro su a kanta. Yalwataccen murmushi ta sakar masa ganin yadda ya k'ara wayo ya girma, hakan ya tabbatar mata yana samun kulawar da ta dace, cikeda kulawa ta d'auke shi ta rungume shi tareda binsa da addu'o'i har wani lokaci sannan ta mik'a shi ga Hadima Urmi, Hannu tasa ta share y'ar k'wallar da ta fara k'ok'arin sakkowa daga cikin idanun ta, A zuciyar ta tana cewa, "ranar kuka bata zo ba tukunna" Ficewa tayi daga shashin ta koma nata. Ramraj ne zaune gefen k'afafun mahaifiyar sa, Kallo d'aya zakayi masa ka gane yana cikin damuwa. Rausayar da kai yayi yace, "Mama Shikenan Maharani Mahalakshimi bazata saurare ni ba??? Wani shu'umin murmushi gimbiya Sunaya ta saki kafin tace, " ina ta murna na haifi namiji, namijin da ze iya yak'ar masarautar nan dan cika muradin mahaifin sa amma sai dai kashh, be cika namijin ba, Raj a yanzu ba soyayyar ta ya kamata ka nema ba, Fansar jinin mahaifin ka ya kamata ka nema kuma ka nema masa cikar burin sa ko da ze samu salama, Idan baka sani ba Maharani Mahalakhshimiey, (Sarauniya Mahalakshmi) itace ta kashe maka Mahaifin ka ta ruguza cikar burin sa, wannan yarinyar shaid'aniya ce da suffar mutum a memakon muyi k'ok'arin kawar da ita sai kuma kace kana sonta?? Nace ka hak'ura ka k'i kaga yadda take wahalar da kai har yau tak'i saurarar ka bata ta taka ma baki d'aya, amma da Arveen ne na tabbata da zata saurare shi, Kana kallon fa idan aka zauna a fada ma wuyacin abu ne bata bashi abunda zeyi ba, kaga wannan ma matsayi ne wanda kai baka same shi ba, Mu bata d'auke mu matsayin jinin ta ba tafi ganewa Waziri da d'an sa saboda shi yafi mu nuna mata k'auna da kulawa, motsi kad'an idan kayi sai ta hukunta ka amma shi bata yi masa haka, Ka dawo nutsuwar ka Raj kisan mutum a gurin ta tamkar shan ruwa ne bana so ta kashe ka ba tareda mun cika muradin mu ba" Shiru Raj yayi maganganun Mahaifiyar sa suna ratsa shi, ya d'an d'ebi lokaci beyi magana ba sai kuma yace, "ita d'in ba wai wadda zamu kawar bace domin kuwa mutanen da suka fi mu k'arfi harda iko suna sun hakan amma sun kasa, Lakhshmie sarauniya ce wadda ta gagari duniya manyan masarautu suna da irin wannan buk'atar ta son kawar da ita dan haka idan muka kawar da ita kawai munyi yak'in ne amma ba mune da nasarar ba, sune zasu zo suyi kane kane akan komai, Fansar jinin mahaifina ta hanyar kashe ta ko nakasta ta ba shine mafi kyawu ba, sai dai ta haifa min wani,, auren ta zanyi kawai kuma yadda tsarin yake wanda ya aure ta shine da mulki dan haka wannan ne ya dace damu, Kiyi tunani akai sosai, yanzu lalla'ba ta zamuyi mu shiga jikinta sosai mu nuna mata komai ya wuce sai mu dinga binta a sannu muna hak'e jijiyoyin ta lokaci d'aya sai dai taji ta fad'a tarkon mu" Dariya sosai Gimbiya Sunaya take sai da tayi me isarta sannan ta rungumo shi tana cewa, "ashe kana da fasaha d'ana gaskiya kai jarumi ne na dena ce maka ba jarumi ba kaji ko?? Bari ma gobe zanje nace mata baka da lafiya dan haka ka zauna gobe kar kaje ko ina kaji ko?? Zanje ma na nemo sa'a" Yace, " ai kuwa ta haka zamu fara kama ta kinyi shawara me kyau" Zaune take ita da Arjula suna hira sai surutu take zuba mata duk da cewar tsuntsuwar bata magana amma hakan be hana ta zama ta fad'a mata damuwar ta ba har ta bata labari,har abunda ya wuce baya ma suna tattaunawa, Koda baza ta ce komai ba takan nuna alamar amsa ga abunda Maharani ta fad'a mata, idan na damuwa ne zata nuna alamar damuwar ta haka idan na farin ciki ne zata nuna, Tsuntsuwa ce me ban mamaki sai dai kowa kawai ganin ta yake be san sirrin dake tattare da ita ba. Kallon ta tayi tana murmushi tace, "Arjula!! Kin tuna a Fadar Maharanie Abunda ya faru? Karyar da kai tayi hakan ke nuna alamar bata tuna ba. Maharani tace, " kina nan fa Har maa take min dariya? Lokacin da yayi min.. Da sauri Arjula ta baza fuka-fikin ta tana fiki-fiki dashi, Hakan yasa Maharani tayi shiru tana kallon ta fuskar ta d'auke da murmushi tace, "Yanzu dai kin tuna ko?? Kare kanta tayi da fuka-fikin ta ta cusa shi ciki tana karkad'a jela. Dariya Maharani tayi tana cewa, " oh kunya ta ma kike ji?? Ni banji kunyar ki ba? Sassauta murya tayi tace, "Arjula na kasa manta wannan ranar tana yawan dawowa cikin tunani na ko meyesa hakan?? Rausayar da kai tayi tareda yin kalar tausayi. Maharani ta gyad'a kai kafin tace, " lokacin lek'en sirri yayi Arjula ki zagaye ko wane sashi na Mahaal kizo min da labarin abunda yake faruwa, ki tabbatar babu wanda ya ganki, ki bi iska yadda ko kusa da mutum kika je baze sani ba " Tashi Arjula tayi ta fice cike da son cika umarni. Hadima Farhana ta k'araso tana d'an murmushi tace, "Sannu da hutawa Shugaba" Bata ce komai ba sai Jinjina kai tayi ba tareda ta kalle ta ba. Hadima Farhana tace, "Ranki ya dad'e taya kike iya yin magana da Arjula? Shin tsuntsuwar tsafi ce ko kuwa?? Naga bama ita kad'ai ba kema kina iya jin maganar ta" Mik'ewa tayi daga kishingid'en da take ta d'ora k'afar ta d'aya kan d'ayar, Cikin Izza tace, "daga ina kike??? " K'asa tayi da kai tareda cewa, "ina neman afuwar shugaba, naje Sashin marayu Abdulkareem ya girma sosai, daga nan na wuce 'bangaren bayi dan kula da abunda suke aikatawa na tarar ba matsala, amma wata daga cikin manyan bayi na 'barin ciyar da mutane abinci na kama ta da laifin hantarar na k'asa da ita gami da wahalar dasu ko tayi musu horon yunwa haka kuma abincin sai son ranta take bawa mutum bata ba su wanda zasu ci ya k'osar dasu, sun bani k'orafi ne sai kuma nayi bincike na gane hakan nayi shigar bayin ne na shiga cikin su sai kuma naga hakan tana faruwa nima ta faru a kai na" Jinjina kai Sarauniya tayi a hankali ta bud'e baki tace, " kin nuna mata kanki?? Wane mataki kika d'auka?? Da sauri tace, "Maharani ban d'auki mataki ba bata san ma naje ba" Gyad'a kai tayi tace, "ki mayar da ita 'barin share share ba'a matsayin wata ba itama ta shiga cikin wanda shugabar su zata dinga basu umarni, a wajen abinci kuma ki nemi wata ki d'ora sannan ta dinga yi mata kamar yadda itama ta yiwa mutane, Bayan haka idan ta k'ara yin hakan ga wani zata kar'bi tsatstsauran hukunci" Hadima Farhana tace, "Zanyi hakan ranki ya dad'e" Wata Hadima ce tayi gyaran murya a bakin k'ofa tareda cewa, "zan iya shigowa Ranki ya dad'e??? Hadima Farhana tace, " shigo" Shigowa tayi tana d'ibar gaisuwa cike da ladabi tace, "nice Sabuwar Hadimar da zata dinga nemawa mutane iso zuwa gareki Hazoor" Jinjina kai tayi alamar ta gamsu, ta k'ara zuba mata ido alamar tana sauraron abunda zata fad'a. Godiya tayi sannan ta cigaba da cewa, "Hazoor gimbiya Sunaya matar Tsohon Galadiman wannan masarauta tazo hankali tashe tana son ganin ki" Shiru tayi na wani lokaci kafin ta gyad'a kai. Hadima Farhana tace, "a iso lafiya" Tashi tayi ta fita cikin sauri. A hargitse gimbiya Sunaya

Chapter 2 of 10