tsananin
farin ciki sannan ya sake su suka sake rugawa wajen iyayensu wato Hasilatul Kurbas da Inmal suma suka
rungumesu.
Nan fa kowa ya cika da tsananin farin cikin samun su Izaima a cikin koshin lafiya.
Bayan an gama farin cikin samun su Izaima lafiya sai suka dunguma gaba daya suka fice daga cikin wannan daki na biyu suka durfafi hanyar da za ta fitar da su daga cikin fadar. Sai da suka iso tsakiyar fadar sai kwatsam! Suka ga dakarun gidan suna ta fiffitowa ta ko ina rike da muggan
AKIN GINI
makamai iri-iri suna yi musu kawanya. Wasu makaman ma
da ke hannun Dakarun ko a labari su Kurbas basu taba jinirin su ba, kuma yawan Dakarun ya kai miliyan daya darabi, sai gashi su sadauki Kurbas sun zama 'yan mitsi-mitsitamkar an ajiye bera guda daya a tsakiyar Kyanwowi dubu.Al'amarin da ya matukar dugunzuma hankalinZuhura, Kurbas, Hasilatul Kurbas, Inmal, Lahura da su
izaima ke nan, suka kama kalle-kalle da waigc-waige ke
nan domin sun san cewa ko aikin kirga Dakarun aka basu
ba karamin jidali bane bare ace yaki za su yi da su.
Wannan shi ne abinda ya faru a can sabuwar fadarSarauniya Abidatul Azmal bayan su sadauki Kurbas sun
sami nasarar dauko jikokinsa su Izaima wadanda AbidatulAzmal tayi garkuwa da su.
*
*
A
L'AMARIN GIMBIYA Abidatul Azmal kuwa,
lokacin da ta zama wannan katon tsuntsu ta fice
daga cikin fadar ta luluka a cikin gajimare sai ta wanzu
tana mai tsala matsanaicin gudu a sararin samaniya domin
ta isa can birnin Nurul Kalbi a cikin Kankanin lokaci ta
tarwatsa birnin gaba daya ta kashe duk wani mahaluki dake cikinsa sannan ta kamo Maharaz da hannunta a raye don
ta kaishi can sabuwar fadarta inda za ta yiwa mutanensa
kisan gilla a gabansa.
Haka dai Abidatul Azmal ta wanzu tana ta tafiya harta shafe sa'a hudu. Kwatsam! ba zato ba tsammani sai ta
hango wani farin aljani daga can nesa ya durfafota yanadauke da wani bil'adama a zaune bisa kansa ya rufefuskarsa da farin rawani, idanunsa kadai ake gani, kuma
17
Taskar Tsafi = 5
Kin Gini
gaba dayan tufafin da ke jikinsa farare ne kuma ya rala
wata zabgegiyar takobi a bayansa iska na ta kada komaj
jikinsa.
Koda ganin wannan aljani da mahayinsa sai Abida
Azmal ta cika da tsananin mamakin kuma taji zuciyarıa
dan buga da karfi saboda ko kadan ba ta ga wannan alja
da mahayinśa a binciken da tayi na tsawon kwana bakw
cikin halwar tsafinta ba.
Kallo daya ta yiwa aljanin da mahayinsa ta gane c
ma'abota addinin Musulunci ne saboda ganin irin yana
kalar tufafin da ke jikinsu don haka ta tabbatar da
abokan gabatarta ne.
Tambayar da Abidatul Azmal ta yiwas kanta ita c
"Anya kuwa wannan mutum ba Sarki Maharaz ban
Ai kuwa idan shi ne a yau ne zan zare masa rub
numfashi, sannan na karasa birnin nasu na baje koma
kowa ba sai ma na kamashi na koma da shi fadata ba."
Ya yin da ya rage saura bai fi kamu goma ba tsakan Abidatul Azmal wacce ta kasance a cikin siffar Kat
tsuntsu da kuma wannan farin aljani sai duk su biyun su
tsaya cak a cikin iska aka fara kallon-kallo. Nan ta Abidatul Azmal ta rikide izuwa ainahin kamanninta sanD ta dubi wannan farin aljani ta daka masa tsawa ta c "Wane ne kai? Kuma wane ne wannan bil'adama wand kake dauke da shi? Ka hanzarta amsa mini wanna! tambaya tawa ko kuwa yanzun nan na hallaka ka kai Ubangidan naka". ال
murmushi
Lokacin da farin aljanin ya ji wannan batu sai yay sannan ya murtuke fuska ya ce, "Ya ke wannan shaidaniyar Sarauniya, ki yi sani cewa wannan ubangidan
18
a
nawa ruwane mai kashe dukkan gobara, kuma shi ne bakin
takobi mai raba masöya. Shiine mai kawar da zálunci ya
shimfida adalei,kuma shime dodon dukkanikafiran daiké
wannan &inahiyansIna maiilisanar sdard kewidewa komai
sammakonki shiia tafeyakerdomin Ubangijinsa ya sanar da
shi dukkan shirinkisd dsllA ainisi sb swoo sb ilin вisррв
Alhalin iyanzu kin boyewadansu Musulmioa can
sabuwar fadarkiu dan ke dajin Shalfur, kumaikina kan
hanyarki ne ta zuwa birnin Nurul Kalbi domin ki je kisbaje
birnin ki kashe mutanen garin kúma ki kamo Sarkinsu a
hannu a raye.T"0 t IamNA lutsbidA swoduх вy оvяwsr
a Kodamaljanin ya zo nanua jawabinsa sai Abidatul
Azmal ta lari numfashinsá tana mai Kara daka masa tsawa
ta ce, "Ban tambayeka dogon labari ba, kawai so nake ka
gabatari da kankadda kuma wandaskake daukebdasshisa
garenilA x s msb imez sn syad s on ina snioiвв
aikio Kafimaljanin ya buđerbaki ya cé wani abu sai jarumin
daakeskan aljanin ya yayesrawanin das ya rufe fuskarsa da
shi, fuskarsa ta bayyana afilizad o2 ida awoo sb lub snisT
sb sXKodá Abidatul Azmalrta ga ko waye sai ta cika da
tsananin mamaki/ Ba wani bane face Sarki Maharazlouoned
idIB Sarki Maharaz ya dubiigimbiya Abidatul Azmal
fuskarsa a murtuke babu annuri ko kadan yai ce,u"Ya ke
wannansabokiyar gaba, kiyi sani cewanyau na fito ne dà
fishina bisa dogaro da Ubangijina. Kosdai ki tuba ki karbi
addinina ko kuma na hallakaki domin kece kadai yanzu
kika zame mana matsala a wannan nahiya tamu domin gaba
dayan kafiran aljanu ma isun saduda tunda an gwada 'yar
káshi musidairsulesun ganes kurensu.s Da yawansulosun
musulunta wasu kun sun yi hijara sun bar nahiyar ma gaba
50
19
daya. Ki sani cewa a dalilinki mun yi asarar dubunnan
rayuka da dukiyoyi babu adadi. Lallai tsakaninmu da ke
babu ga maciji. Ubangijina ya nuna mini duk irin makircım
da kike kullawa, hatta mahaifiyata da jama'ata da kika sa
aka kullesu a cikin kurkuku na gani a cikin barcina. ina
tabbatar miki da cewa da izinin Allah baki isa ki cutar da su
ba. Ko yanzu na ci babbar riba akanki tunda na shiga har
cikin birninki na ci da yaki kuma na musuluntar da dukkan
jama'arki."
Sa'adda Sarki Maharaz ya zo nan a zancensa Sai
hawaye ya zubowa Abidatul Azmal ta ce, "Tabbas ka das
mini mugun bakin cikin zuciya wanda har na mutu ba zau
manta da shi ba. A dalilin haka ne na rasa mahaifin
mulkina, jama'ata da kasata. Kai ne mutumin da ya lalaia
darajata da kimata a wannan nahiya. Babba bakin cikina da
takaicina shi ne a baya na sami damar da zan hallakaka,
amma sai na fasa saboda sharrin darsuwar sonka a cikin
zuciyata. Tabbas na yi nadamar kamuwa da kaunarka a
raina duk da cewa shi So barawo ne dare daya yake sace
mutum. A yau ina mai battar maka da cewa zan kasheka da hannuna duk da cewa ina sonka a raina kuma na sani cewa
a halin yanzu ka baro amaryarka a can birnin Nurul Kalbı
tana zaune ta zuba ido ta ga komawarka. Bayan na kasheka itama zan je na kamata na kaita can kurkukuna inda za ta ci gaba da rayuwar bakin ciki a matsayin bazawara har sa wahala
ka
da bakin ciki sun zamo sanadin ajalinki. Yanzu sai shirya gani nan bisa kanka".
Koda gama fadin haka sai Abidatul Azmal ta zare takobinta ta afkawa Sarki Maharaz da aljanin da ke daukc
Taskar Tsafi 5 Madakin Gini
da shi. Cikin bakin zafin nama Maharaz ya zare takobinsaya tareta suka kacame da azababben yaki.
taAbidatul Azmal ta wanzu tana mai kai musu wannan
sara da suka cikin mugun karfi na ban mamaki wanda
kai cewa shi kansa Sarki Maharaz da kyar yake iya kareharin nata, shi kuwa aljanin da ke dauke da shi ya ma kasakare harin, a cikin dakika goma ta dankara masa kyawawansara uku a jikinsa ya shiga mugun hali ya shiga mugun haliya rinka tambal-tambal a sama zaj hantsilar da Maharaz su
rikito kasa tare. Babban abinda ya daurewa Maharaz kaishi ne ya ya aka yi Abidatul Azmal ta sami wannan sabongagarumin. karfi haka aljalin a sanin da ya yi da karfinsuyazo daya shi da ita.
Lokacin da Maharaz ya ga sun fara tambal-tambal a
sama za su rikito kasa su hallaka shi da aljanin da ke dauke
da shi sai ya fara karanta addu'o'i a cikin zuciyarsa yana
mai neman taimakon Allah.
Ana cikin haka ne Abidatul Azmal ta sokawa farinaljanin takobi a ciki. Nan take yai kalmar shahada ya sakifuka-fukansa ya sullamo kasa a lokacin da yai shahada.
Cikin hanzari Maharaz ya daka tsalle sama daga kanaljanin kawai sai ya tsinci kansa a tsaye cikin iska tamkar
yana da fuka-fuki kai ka ce tsuntsu ne. Shi kansa ya san
cewa kawai Yardar Allah ce. Itama Abidatul Azmal sai tacika da tsananin mamaki da ta ga Maharaz ya tsaya a sama
cikin iska domin duk irin gumurzun da suka yi a baya shida ita ba ta taba ganin ya yi irin wannan bajinta ba.Cikin tsananin fishi da Kunan rai ta sake afka masa suka cigaba da sabon dauki ba dadi a cikin gajimare. Wannan
karon sai fadan ya sauya yanayi domin karfi ya sake zama
21
Taskar Tsafi = 5 Madakin Gini
daya, suka ci gaba da kaiwa juna sara da suka cikin bakin
zafin
nama
Duk sa'adda takubbansu suka hadu sai dai ka ga tartsatsip
wuta yana tashi. Tsawon dakiku masu yawa suna ta
wannan gumurzu dayansu bai sami nasarar komai ba. Koda
ganin haka sai Abidatul Azmal ta ja da baya ta tsaya cak
cikin iska, kawai sai ta saki takobinta ta sallamo Kasa
sannan ta dunkule hannayenta ta ce, "Tunda mun kasa cuta
da juna da makami ai sia mu gwada 'yar kashi ko?"
Kasa.
Da jin haka sai shima Maharaz ya saki takobinsa ta
Tabbas rashin sani ya li dare duhu! Inda Maharaz
san abinda zai biyo baya da ba zai saki takobin sa he
domin Abidatul Azınal yaudararsa layi.
Koda ta ga ya saki takobinsa sai tayi wuf ta day
rigarta ta zaro wadansu masifafTun wukake guda b
masu tsananin KAIFI DA TSINI.
Kafin Maharaz ya ankara tuni ta caka masa wukak
a kirjinsa hagu da dama, wukaken suka nutse, Maharaz ba
san sa'adda ya kwallah ihu ba a lokacin da jini ya fara
kwararowa daga jikinsa.
Kafin Abidatul Azmal ta zare wukar tuni ya dok
Kirjinta da kafarsa guda da karfin gaske. Tamkar an bug
tamaula haka ta cilla da baya a sama cikin iska tay
katantanwa kuma tayi kumallon jini.
Har Maharaz ya yi nufin ya zare wadannan wukake
guda biyu daga cikin kirjinsa sai ya fasa domin tsananın zogin da yake ji, kuma ya fahimci cewa idan ya zare sun ba
karamin jini. ne zai fita daga jikinsa ba wanda zai iya janyo sanadin ajalinsa cikin kankanin lokaci saboda haka sa
22
Taskar Tsafi = 5 Madakin Gini
shima ya dunkule hannayensa da kyar kamar ma ba zai iya
ci gaba da fada ba.
Itama Abidatul Azmal a wannan lokaci tana cikin
wani irin mugun hali na galabaita sakamakon mummunan
dukan da Maharaz ya yi ma ta a kirji har idanunta na
lumshewa, shi kuwa Maharaz dishi-dishi ma yake gani har
jiri ya fara dibarsa kawai tsananin juriya da jarumtaka ne
suka sa har yanzu bai sare ba.
Nan take Abidatul Azmal ta dawo cikin haiyacinta
sosai kawai sai ta share jinin da ke bakinta ta tuntsure da
dariya sannan ta nuna Maharaz da dan yatsanta guda ta се,
"Na gama da kai ya kai masoyin raina, kuma babban
abokin gabata, domin babu yadda za a yi ka tsira daga
sharrin dafin da ke jikin wadannan wukake nawa. Da zarar
ka zare daya daga cikin wukaken daga kirjinka gudan jini
zai yi fitar burgu kuma take za ka mutu. Idan kuma ka ki
zare wukar a hankali dafin da ya shigeka zai ratsa dukkan
jinin jikinka."
Cikin karfin hali Maharaz ya tari numfashin Abidatul
Azmal ya daka ma ta tsawa ya ce, "Ya ke wannan jahila
kuma batacciya, ki yi sani cewa babu mai kashewa da
rayawa face Allah. Wannan dafi na jikin wukakenki bai isa
ya kasheni ba face da yardar Ubangijina".
Kafin Maharaz ya gama rufe bakinsa tuni Abidatul
Azmal ta sake afka masa tana mai kai masa naushi da bugu
cikin bakin zafin nama kuma tana kaiwa wukakenta cafka
domin ta zaresu daga cikin kirjinsa.
Duk da cewa Maharaz yana cikin matukar galabaita
kuma dafi na kara shiga jikinsa sai ya rinka tare hare-haren
23
Taskar
nata kuma ya hanata samun damar zare wuka daya daga
cikin guda biyun.
iaSai da suka shafe rabin sa'a cur! suna wannan artabu
a sannan ne Maharaz ya sake galabaita ainun, ya zamana
cewa idanunsa sun fara lumshewa, ya fara gani dishi-dishi
kuma Abidatul Azmal ta fara samun nasarar gabza masa
naushi a fuska. Nan da nan fuskarsa ta kumbura, ko ina jini
ya duru.
Koda Maharaz ya ga ya galabaita ainun, kuma ya
labbatar da cewa Abidatul Azmal za ta iya samun nasarar
hallakashi a ko yaushe sai ya fara kiran sunayen Allah
Tsarkaka a cikin zuciyarsa yana mai neman taimakonsa.
gsbFaruwar hakan, ke da wuya sai yaji wani irin
gagarumin karfi ya shigeshi. Nan take ya rinka jerawa
Abidatul Azmal naushi a fuskarta, kirjinta da cikinta,
Nan da nan itama fuskarta la kumbura, jini ya rinka
fita daga hancinta da bakinta. Cikin kankanin lokaci ta fita
daga haiyacinta, kawai sai ta suma ta sallamo izuwa kasa
za ta hallaka.
Cikin zafin nama Maharaz ya cafota ya rungumeta da hannayensa biyu sai gashi suna saukowa kasa, a hankali daga can kololuwar sama tamkar yana da fuka-fukai a jikinsa.
Yana cikin haka ne ya dubi fuskar Abidatul Azmal ya ga yadda ta kumbura tayi kaca-kaca da jini ba kyan gani sai yaji
mamaki
ya kamu da tausayinta. Al'amarin da ya matukar bashi
babbar abokiyar
ke nan, ya ce a ransa, "Saboda me zan ji tausayin gabata wacce take son ta hallakani? gashi ta caka Yanzu mini wadannan wukake masu dafi ina ji a
24
Taskar Tsafi =5 MadakinGmina? по в комка ку о906W NETSIM nidodel Eb коткNan take Maharaz yy yanke hök uney deikm nelursaoWardaararaaukd iurdewaAbidatulA/marwilya ldd ohin ya hie
wanzdwartala uolon Rasd kumAMUsLARiA OS Kehaniy ar sdstm kwanciyarЧghn kc 929k s1 ilst 192 каinMahara ha dhike ua pmtiyd Nidaur Azmal akanhannayensa suna a aukowykasab Rdtaruhsd Basy" tabRasa Bayai tayaIBPIV tikaP'sadhul λευκοARARPNAEABA κu2ς oR19 Shifmidekaws Kays
awa
A dai-dai wannan lokaci ne adiút
kadanukadanaishi res vkkU Banm Manarwandakeddrkashe bisa yiwoyinsa dgabanta
12 Abidatul Azmal taji kö fahnba aLEAPan Motact Hor hatash if shutagubawaa kasheta.
Har Mahara Kama li a AP& WNsai kawai sai ya kasa. Kawai sai hawaye suka zubo masa yadubeta ya ce, "Ya ke abokiyar gaba kiyi sani cewa a iyatsawon rayowata d duniya ban taba kas ya mac ha haka kitan raakeyaken
dalvathayr Cattai Kiwwba žan Tira Ba daga Kankn
i amma
kina
braalbakhefh с y nnul & sbST BIUdDN BWiY BYkan
Gama fadin hakan ke ddWüyRSA NANPAS YdUnodsnis sai yaji if уаmme.
Aa tth kumadgttd lai sahm kwarin Jikahtl sabbaw25
Taskar Tsafi = 5
haka sai ta mike tsaye a fusace. Tana mikewa tsaye tayi
arba da takobin Maharaz wacce ya saketa a can sama
sa'adda suke gumurzu ta fado kasa.
Cikin sauri Abidatul Azmal ta ruga ta dauko takobin
ta dawo kan Maharaz ta raba kafafu a kansa. Kawai sai ta
daga takobin sama da hannayenta biyu za ta caka a cikinsa.
Bisa mamaki sai taji ta kasa caka masa ta tsaya cak kawai
sai ta fashe da kuka ta koma gefe daya ta zauna tana tunani
tana mai dada ci gaba da zubar da hawaye.
Sai da ta shafe rabin sa'a guda cur! tana tunani da
kuka kuma ta kasa yankewa kanta hukunci bisa abinda ya
kamatra tayi a rayuwarta.
Nan take Abidatul Azmal ta rikida ta zama wannan
katon tsuntsu ta tashi sama ta luluka izuwa cikin gajimare
ta bar Sarki Maharaz a wannan wuri a kwance babu abinda
yake motsi a jikinsa tamkar gawa.
Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin gimbiya
Abidatul Azmal da Sarki Maharaz bayan sun yi haduwar
bazato a sararin samaniya sun fafata kazamin yaki.
*
L'AMARIN SU SADAUKI Kurbas kuwa, Alokacin da dakarun fadar gimbiya Abidatul
Azmal suka yi musu kawanya ya zamana cewa sun firgita
ainun da ganin yawan dakarun kuma sun tabbatar da cewa
babu yadda za ayi su sami nasara akan Dakarun sai Kurbas
ya yiwa Zuhura rada a kunne ya ce, "Bamu da mafita face taimakon Ubangijin Musulunci."
Da jin haka sai Zuhura ta gyada kai itama tayi masa rada a kunne ta ce, "Tabbas zancenka dutse ne don haka ga
26
Taskar Tsafi = 5 Madakin Ginı
addu'ar da ya kamata mu yi ta karantawa a zuciyarmu. Nan
take ta rada masa addu'ar kuma ta radawa Hasilatul Kurbar
ita ma sai ta radawa Inmal, shima ya radawa Lahura.
Ya yin da Dakarun gidan suka ga su Kurbas suna yin
rada a tsakaninsu sai suka bushe da mahaukaciyar dariya
wadda sautinta ya cika dodon kunnen su Kurbas ya
addabesu.
Koda ganin haka sai Zuhura ta kwallah kabbara da
karfi ta afkawa Dakarun ta' rinka saransu da sukarsu. Bisa
mamaki sai ga ta tana daddatsa sassan jikinsu tamkar tana
sassabe a gona. Ai kuwa sai Kubas, Hasilatul Kurbas,
Inmal da Lahura ma suka yi koyi da ita, suka yi ta saran
dakarun suna masu ci gaba da karanta wannan addu'a
wacce Zuhura ta rada musu.
Saboda tsananin yawan Dakarun su Kurbas basu
gama kashe su ba gaba daya sai bayan sa'a bakwai. Tunda
aka fara yakin Zuhura na goye da lzaima shi kuma Kurbas
sai ya goya dan uwanta Uhairu. Har aka gama yakin daya
daga cikin su Kurbas bai sami rauni ba, amma fa gaba
dayansu sai suka zube Kasa suna haki saboda tsananin
jigata.
Bayan sun dan huta sai suka mike tsaye suka fice
daga cikin fadar. Suna fita sai ginin fadar ya kama girgiza
yana rugujewa kuma ya rinka nutsewa izuwa karkashin Kasa.
Su Kurbas suka tsaya daga can nesa kadan suna kallon ikon Allah. Tabbas sun san cewa Allah ne Ya nutsar da wannan fada tunda wuri ne wanda ba a komai a cikinsa face sabon Allah da cutar da bayinSa.
Taskar Tsafi = 5
Bayan gidan ya gama nutsewa sai Zuhura ta dubi.
su Kurbas gaba dayansu ta ce, "Ai sai ku zo mu tafi
izuwa gida can birnin Nurul Kalbi".
Cikin tsananin mamaki su duka suka dubeta.
Kurbas ya ce, "Ta ya ya zamu nufi birnin Nurul Kalbi
a yanzu bayan daga nan zuwa can tafiya ce ta kwana
da kwanaki masu yawa, kuma gashi bamu da abin
hawa".
Koda Zuhura taji wannan tambaya sai tayi
murmushi ta ce, "Ubangijin da ya bamu nasara muka
hallaka gaba dayan dakarun da ke cikin wannan gida
shì ne zai kai mu birninmu a cikin kankanin lokaci.
Abinda nake so da ku shi ne kawai ku biyoni a baya."
Koda gama fadin haka sai Zuhura ta kama hanya
ta nausa cikin daji. Ba tare da fargabar komai ba kuwa
su Kurbas suka bita a baya da sauri su duka.
L'AMARIN SARKI MAHARAZ kuwa, Alokacin da ya farfado daga dogon suman da
ya yi sai ya tsinci kansa a cikin kwale-kwale a tsakiyar
kogi. Kwale-kwalen na tafiya da kansa babu mai
tukashi.
Cikin firgici Maharaz yai sauri ya shafi kirjinsa
sai ya ga sam babu wadannan wukake da gimbiya Abidatul Azmal ta caccaka masa kuma ko alamar rauni babu a kirjinsa a inda aka caka masa wukaken.
28
Madakin GiniAl'amarin da ya matukar bashi mamaki ke nan yamike zaune zumbur! yana hailala da godiya ga Allahda ya ga ya sami lafiya tamkar wani abu bai tabasamunsa ba. Kawai sai ya ji an yi masa sallama irin taaddinin Musulunci a bayansa.
A firgice ya juya da sauri kawai sai ya yi arba dawani mutum tsoho tukuf wanda ke dauke da farindogon gemu, babu silin bakin gashi guda daya ajikinsa. Kallo daya za ka yi masa ka san cewa ya shamiya a duniya.
Cikin tsananin tsoro Maharaz ya dubi tsohon yace, "Wane ne kai, kuma ya ya aka yi na zo nan, menene ya faru gareni?"
Koda jin wadannan tambayoyi sai tsohon ya yimurmushi sannan ya ce, "Kwantar da hankalinka yakai Maharaz...Sunana Ansarul Mauruf."
Koda jin haka sai shima Maharaz ya cika datsananin mamaki kawai sai ya rungume tsohon yanamai farin ciki ya ce, "Tabbas kafin rasuwar mahaifinaya bani labarinka kuma ya tabbatar mini da cewa kafinna bar duniya sai ka ziyarceni. Kai kuwa ina ka shiga aduniyar nan a tsawon wadannan shekaru da ka dainahidima ga mahaifina?"
Ansarul Mauruf ya yi murmushi ya ce, "Ya kaiMaharaz ka yi sani cewa yau shekarata dubu arba'inina rayuwa a wannan duniya kuma na shekara sittin dabiyar kacal ina hidima a gidajen manyan sarakunan29
MadakiIN G
Taskar Tsafi = 5
musulunci. Mahaifinka shi ne Sarki na karshe wanda
na yiwa hidima kuma na rabu da shi ne domin na tafi
yawon yada addinin Allah da JIHADI na yake-yake.
Na ziyarci nahiyoyi dubu saba'in da bakwai kuma na
yi yaki sau dubu goma sha daya da dari biyar kuma
babu wanda ban sami nasara ba na akwar da kafirci.
Akan hanyar dawowata ne na tsinceka a kwance cikin
daji magashiyan tamkar ka mutu an soke ka da
wukake guda biyu a kirji masu mugun dafi. Sai da na
karanta addu'a ta musamman sannan na zare wadannan
wukake daga kirjinka. Nan take raunikan suka warke
kuma jini bai zuba ba koda digo.
Wannan duk iko ne na Allah ba wai dabarar mu
ba. A haka yanzu abokiyar gabarka gimbiya Abidatul
Azmal ta sauka a birnin Nurul Kalbi amma ba ta kashe
kowa ba, sai dai ta ritsa matarka tana jiran ka koma gida ta kasheta a gabanka. Babu abinda zamu iya yi bisa wannan al'amari face addu'a. Da izinin Allah za
mu isa birnin Nurul Kalbi a cikin kankanin lokaci". Koda gama fadin haka sai tsoho Ansarul Mauruf ya shafi Maharaz da hannunsa nan take barci ya kwashe shi.
Maharaz bai farka ba sai a cikin birnin Nurul Kalbi kuma a cikin turakarsa akan kujera. Yana bude ido
igiya
ya
tamau
yi arba
tana
da
kuka. matarsa Salsirat daure akan gado da
ini askаi Madakin Gini
Gimbiya Abidatul Azmal ta dora takobinta akan
uls vuyanta kuma ta kura masa idany tana mai zub da
iemhawayfoYsYi
sb Cikin tsananin razana Maharaz ya durkusa bisa guiwoyinsa ya shiga rokon gimbiya Abidatul, Azmal
luteyane mai ccwa, "Kada ki kashe mini matata domin
Bgibala yi miki laifin komai ba. Na rokcki da ki kasheni a
majinakonta ita ki kyalcta".
Gimbiya Abidatul Azınal tayi shisshikar kuka
slusannanata cc, "Ya kai masoyina ka. tuna ccwa a
dalilinka na rasa ubana, mulkina, kasata da jama ata.
в ваня Babu Pa wani abu da zan yi maka domin na dauki
TRT fansa face na kashe wannan mata taka domin yanzu ne
kake son ka fara sabuwar rayuwa mafi dadi a duniya
Blare da sita kuma ka san cewa nima ina matukar
Kuanarka amma ba zan iya zama abokiyar rayuwarkа
ba a matsayinka na babban abokin gabatala
s s Koda gama fadin haka sai Sarki Maharaz ya
eed fashe da matsanaicin kuka sannan ya cc, "Na ji ba zan
iya hanaki abinda kike son aikatawa ba amma ki sani CIASI
cewa idan kika kashe matata ba ki yi mini adalci ba
tunda ni ban kashe miki miji ba abokin rayuwar da
bayan iyaye sai shi." Rsтaрej
ilar Koda jin wannan batu sai Abidatul Azmal ta
fashe da matsanaicin kuka sannan ta ce, "Ya kai
wannan Sarki kayi sani cewa taboas a yanzu na gamsu
cewa addininku shi ne addinin gaskiya tunda na ga
1
Taskar Tsafi = 5 Madakin Gini
zahiri da idanuna, wato tsafina ya kasa tasiri a kanku.
Abin kunya ne a gareni na karbi wannan addini naku
na yi watsi da wanda na gada a wajen iyayena. Ina mai
yi muku fatan alkairi da jin dadin rayuwa kai da
matarka".
Koda gama fadin haka sai gimbiya Abidatul
Azmal ta cire kaifin takobin da ke hannunta daga
wuyan Salsirat sannan ta cakawa kanta takobin. Nan
take ta sulale kasa matacciya.
Ita kanta Salsirat sai da ta fashe da kuka
sakamakon kamuwa da tausayin gimbiya Abidatul
Azmal da kuma Sarki Mabaraz wanda ya durkusa
gaban gawar gimbiya Abidatul Azmal yana ta sharar
hawaye.
a
Wannan shi ne yadda karshen kafirci ya zo a
nahiyar da birnin Nurul Kalbi yake. Kuma sannan ne
musulunci ya yadu a ko ina.
Sarki Maharaz ya ci gaba da mulki tare da
matarsa mahaifiyarsa kuwa ta auri Sadauki Kurbas
suka ci gaba da rayuwar Musulunci cikin kwanciyar hankali.
Alhamdulillah.
Karshe!.
Daga mai debe muku kewa a kullum da ko yaushe.
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is