bukaci ruwan alwala. Nan take aka kawo masa
ruwa mai tsafa ya gabatar da alwala.
Koda ya mike domin ya yi sallah sai attajiri Suhairu
ya ce, "Me zai hana ka jirani nima nayi irin abinda na ga
kayi yanzu in ya so sai mu yi ibadar tare?".
Koda jin haka sai Maharaz ya yi murmushi sannan ya
ce, "Ai ba a yin addinin Allah da jahilci, dole sai na koyar
da kai yadda ake yin komai".
Suhairu ya jinjinakai ya ce, Ai kuwa ni da iyalina
mune mutane na farko da zamu fara koyar wannan addini naka a wannan birni namu".
Kafin Suhairu ya kara fadin wani abu sai Maharaz ya fuskanci alkibla ya tayar da sallah.
shafa
Bayan
ne
Maharaz ya idar da sallah ya yi addu'o'insa ya
abinci tare.
sannan ya koyawa Suhairu Bismillah, suka ci
ce, "Yanzu
zan
Da
suka
sa a
kare cin abincin sai attajiri Suhairu y8 kaika dakinka domin ka zauna ka huta in ya so bayan mun ci abincin dare sai na kirawo iyalina domin ka koya mana yadda ake wannan addini naku kafin
18
Taskar Tsafi-4 => Madakin Gini
gari ya waye a sake tara jama'ar gari a can kofar fada ka
koyar da su".
Maharaz ya yi murmushi ya ce, "Wannan ai babu laifiyadda ka tsara ya yi kyau". Nan take Suhairu ya kirawo
wani hadimi ya yiwa Maharaz jagora izuwa wani
kasaitaccen daki wanda ke dauke da wani gado na alfarma
wanda aka tanada musamman saboda manyan baki.
Maimakon Maharaz ya kwanta akan gadon ko don ya
huce gajiyar yakin da ke jikinsa sai kawai ya zauna a kasan
dakin ya harde kafafu ya fiddo casbaha ya kama lazimi.
Shi kansa hadimin da ya rako Maharaz dakin sai ya cika da
mamaki yana mai cewa a cikin zuciyarsa.
"Wai shin wannan mutumin wane iri ne? Tun da ya
zo gidan nan bai damu da komai ba. Hatta abincin da aka
kawo musu dan kadan ya ci. Yanzu gashi a cikin tsananin
gajiya ga raunika a jikinsa amma bai ma damu da ya
kwanta ya buta ba sai bauta kawai yake ta yi".
Hajka dai wannan hadimi ya fice daga cikin dakin ya
bar Maharaz yana lazimi.
Kamar yadda attajiri Suhairu ya tsara haka al'amura
suka kasance, wato bayan sun ci abincin dare shi da
Maharaz sai Suhairu ya kirawo iyalansa suka zo suka
riskeshi a cikin turakarsa.
Iyalan Suhairu sun kasance su uku ne rak. Daga
matarsa wata kyakkyawar mace 'yar kimanin shekaru
hamsin wacce kai da ganinta ka san cewa sa'adda tana
budurwa mazaje sun sha gwagwarmaya akanta sai kuma
wani yaro wanda bai fi shekara goma sha daya ba a duniya,
sai kuma babbar 'yarsa wata budurwa wacce ita kadai ce ta
19
Taskar Tsafi-4 *> Madakin Gini
rufe fuskarta da jikinta gaba daya, idanunta kadai ake iya
gani.
Da shigar iyalan Suhairu cikin turakar sai Maharaz da
wannan budurwa suka hada idanu. Take Maharaz yaji
zuciyarsa ta buga da karfin gaske don haka sai yai sauri ya
sunkui da kansa kas cikin tunani yana mai mamaki a ransa
yana mai cewa.
"Akan wane dalili zuciyata za ta buga saboda ganin
idanun wannan mace?"
Amsar da ya kasa baiwa kansa ke nan.
"Da ganin idanun wannan mace ta kasance budurwa
kuma kyakkyawa ta gaban kwatance amma kuma ai komai
kyawunta bana zaton zai kai na gimbiya Abidatul Azmal.
ila kanta Abidatul Azmal a ranar da na fara ganinta
zuciyata bata buga da karfi haka ba Kodayake dai sai na ga
fuskar wannan budurwa sannan zan iya yanke hukunci"
Bayan iyalan Suhairu sun zauna a gefe daya kusa da
shi suna masu fuskantar Maharaz sai Suhairu ya fara
gabatar da su ya ce, "Wannan Lamirat ke nan, matata guda daya jal a duniya wacce muka yi auren saurayi da budurwa.
Wannan kuma ita ce Sharisat babbar 'yata. Kayi hakuri bata yarda aga fuskarta tunda lokacin da ta shekara bakwai а
duniya kuma ta kasance a haka bisa wani dalili. Wannan kuma
kara
shi ne Harun, kani ne ga Sharisat. Daga kansa bamu samun haihuwa ba".
Maharaz ya dago kai cikin biyayya ya gaida Lamirat kamar yadda yake gaishe da mahaifiyarsa Zuhura, sannan ya
ya
sunkui da kansa kas cikin alamun kunya. Al'amarin da burge Lamirat ke nan taji Maharaz ya burgeta. Itama
20
Taskar Tso-4 >Madakin Gini Sharisat sai ta budi baki cikin zazzakar murya mai daukar hankali ta gaishe da Mahárazon idvae nantew ind aY" Tunda Maharaz ya zo duniya bai ta6 ajin murye mai 'dadi da zaki irinta ba. Nan fa yaji zuciyarsa ta ci gabe da bugawa da sauri da sauri, yaji babu abinda ya ke so "sannan face ya ga fuskar wannan budurwa mmai zakin murya
& tse Abinda ya daurewa Maharaz kai shi ne, duk sa'edda
ya dago kansa sama sai ya ga Sharisat ta kura mnsa idenu ko kiftawa bata yi nran tsa uiad peanaw it abuR
Suhairu ya dubi Maharsz ya ce, "Yanzu sai ka shigar
da iyalina cikin wannan addini mai daraja, sannan ka fora
koyar damu yadda za a bautawa Ubangijin Musulunci? al
ab ESVBa tare da gardamar komai ba kuwa Maharaz ya
biyawa su Sharisat kalmar shahada suka karanutata sanna
ya fara koya musu wankan tsarki izuwa kan alwala da
kuma yadda ake yin sallah. Bayan haka kuma sai ya bude
jakarša ya dauko Al-Kurani mai tsarki ya shige karantesbi.
mmibb Koda fara hakan sai Suhairu da lyalansa suka ji tsiger
jikinsu ta tashi, kowannensu jikinsa ya yi sanyi domin nen
take kalmomin Al-Kurani suka rinka ratsasu, suka ji sun
gamsu da duk Zancen da suke ji, olsa inew it jed sаIковM
a
1Dyake Mabaraz yana karatun ne da karin bayani na
fassara sai kalmomin suka zamo abin fahimta sosar
garesu. Kafin Maharaz ya kai kan ayar da yake karantawa
dulkaninsu sun fara kwalla da zubar da hawaye. Lokacin
da ya kamımala karatun ya dago kai ya ga duk suna hawaye Sons & sani na sai ya cika da tsananin mamaki.
21
Taskar Tsafi-4 ya
Suhairu ya sa hannu ya share hawayensa sannan
ce, "Ya kai wannan Sarki mai daraja kayi sani cewa tundauwata ta haifeni ban taba jin kalmomi masu dadi cikinhikima da basira ba irin wadannan. Tabbas kalamin yaf
Karfin basirar dan Adam sai dai Mahaliccinsa. Hakika
da iyalina mun yi imani matuka da wannan addini AUbangijin Musulunci, bakin cikina shi ne da muka kasancaa cikin kafirci tsawon shekaru na rayuwarmu a baya sai
yanzu ne muka shigo cikin wannan rahama".
Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube SarkMaharaz ya rungume attajiri Suhairu ya ce, "Dukkasgodiya ta tabbata ga Ubangijin Musulunci wanda ke shiryarda bawansa a duk sa'adda ya so.
Daga wannan rana Maharaz ya ci gaba da koyar daiyalan attajiri Maharaz ilimin addini da kuma sauran
mutanen birnin, kuma jama'a suka tsinci kansu a cikinsabuwar rayuwa mai dadin gaske ta farin ciki da kwanciyarhankali irin wacce basu taba tsintar kansu ba a ciki.Al'amarin da ya kara musu imani da kaunar addininMusulunci ke nan a zukatansu.
Tsawon kwanaki bakwai a cikin wannan hali,Maharaz bai ji wani sako ba daga can birnin Nurul Kalbі.kuma wani iko na Allah ko sau daya bai samu damar yinIstahara ba akan matsalar gimbiya Abidatul Azmal dakuma halin da mutanen birnin Nurul Kalbi ke ciki ba.
Ba komai ne ya haddasa hakan ba face hankalinsa da yatsayar wajen ganin jama'a sun koyi addinin Allah, kuniasuna Yinsa a aikace.
Taskar Tsafi-4 -> Madakin Gini
A ranar kwana na bakwai Maharaz ya yi wani
mafarki mai ban tsoro, ya farka a firgice bai san sa'adda уa
walla kabbara da karfi ba. A wannan lokaci da sassafe ne
kuma cikin ikon Allah gaba daya mutanen gidan attajiri
Suhairu barci suke yi Sharisat ce kadai idonta biyu tana yin
wani lazimi da Maharaz ya koya ma ta.
Koda ta jiyo kabbarar Maharaz da karfi sai ta mike
zumbur a firgice cikin tsananin razana, bata san cewa
hijabinta ya fadi ba sai ta ruga da gudu izuwa can dakin
Maharaz, ai kuwa tana shiga ta iskeshi a zaune yana ta
salati da hailala. Koda ya dago kai ya yi arba da ita ya ga
tsananin kyawunta sai ya rude kuma ya kidime ya manya
da abinda ya gani a mafarkinsa kawai sai ya tsura ma ta
idanu cikin tsananin mamaki domin ya tabbatar da cewa
kyawunta ya ninka na gimbiya Abidatul Azmal sau uku.
Koda Sharisat ta ga Maharaz ya kura ma ta idanu ko
kiftawa ba ya yi sai jikinta ya bata cewa lallai bata tare da
hijabinta kuma fuskarta a bude take, haka ma jikinta.
Tabbas ya ga irin kyakkyawar kirar jikinta.
Cikin tsananin damuwa da kunya ta juya da baya da gudu
ta dauko hijabinta a dakinta ta sanya sannan ta dawo dakin
Maharz ta tsaya a gefe daya nesa kadan da inda yake ta ce,
"Ya kai wannan Sarki mai daraja mene ne ya faru gareka
ka farka a firgice haka kana irin wannan salati?"
Koda Maharaz yaji wannan tambaya sai kunya ta
kamashi ya sunkui da kansa kas sanann ya yi murmushi ya
ce, "Ki gafarceni ya ke sarauniyar kyawawan mata ta
duniya, hakika na san cewa na tasheki daga barci hakan ya
samo asali ne daga mummunan mafarkin da na yi akan 'yan
23
Taskar Tsafi-4 dakın Cini
uwana da suka tafi can birnin Nuruľ Kalbi. A cik
mafarkin nawa an nuna mini cewa suna cikin mugun ha
don haka ni yanzu hankalina ya dugunzuma ban ga ta za
ba dole nayi shiri na tafi birnin Nurul Kalbi domin na
halin da 'yan uwana ke ciki duk da cewar ban gama aik
da nake yi ba a birninku. Na fahimci cewar a cik
wadannan kwanaki bakwai da na yi tare da ku babu wane
ya sami ilimi mai yawa a wajena sama da ke saboda hak
zan bar miki wakilci na koyar da mutane wannan addie
mai albarka har Allah Ya dawo dani".
Koda jin wannan batu sai fuskar Sharisat ta juy
izuwa tsananin damuwa kaman za ta fashe da kuka sannan
ta ce, "Ya kai jarumin jarumai, kayi sani cewa kain
saurayi na farko wanda ya taba ganin fuskata da kuma
kyawun surar jikina a duniya tun daga sa'adda na cika
shekara bakwai kawo i yanzu Na yi alkawari cewa duk
saurayin da ya fara ganin fuskata ko surar jikina ba zan taba rabuwa da shi ba dai-dai da sa'a guda don haka kaine mijin
idan
aurena. Lallai tare da ni za ka yi wannan tafiya sai dai bana numfashi a doron kasa. Shin kana so na zama abokiyar rayuwarka ko kuwa baka kaunata?"
da mamaki
Lokacin
sannan
da Maharaz yaji wannan tambaya sai ya cika ya ce, "Haba ya ke tauraruwar babu wani taurari ai
tarin baiwa
da
da
daraja
namiji da zai ki ki domin Allah Ya yi miki ta kyau da kamala bugu da kari kuma gashi kin karbi addinin Musulunci. Amma ya ya za a yi na yi wannan tafiya tare da ke alhalin baki kasance matata ba kuma kin sani cewa wannan tafiya da zan yi mai tsananin
hadari ce?"
24
Taskar Isatl-4 -> Madakin Gini
Sharisat tayi murmushi ta ce, "Duk wannan mai sauki
ne idan har kana kaunata. A yanzun nan sai a daura mini
aure da kai idan ka amince. Batun hadarin da ke kan hanya
kuwa ba na tsoron komai tunda na san cewa Ubangijin
Musulunci na tare da mu".
Da jin haka sai jikin Maharaz ya yi sanyi kuma nan
take ya cika da tsananin farin ciki amma zuciyarsa tana
tsoron ya yi wannan tafiya tare da Sharisat. Har ya budi
baki zai ce wani abu sai kawai ya ga attajiri Suhairu tare da
matarsa Lamirat da Harun Kanin Sharisat sun shigo cikin
dakin fuskokinsu cike da annuri. Da zuwansu sai attajiri
Suhairu ya dubi Maharaz ya ce, "Bani sadakin 'yata yanzun
nan na daura muku aure." Cikin matukar mamaki da
damuwa Maharaz ya shafa aljihunan rigarsa yaji wayam,
sannan ya ce, "Ai kuwa ni yanzu bani da komai". Attajiri
Suhairu ya sa hannu a aljihunsa ya dauko kudi dirhami dari
ya ce, "Ga wannan na baka rance ka biya sadakin 'yata duk
sa'adda kuka dawo ka biyani".
Maharaz ya karbi dinaren cikin murna sannan ya
maidawa Suhairu. Nan take aka daura aurensa da Sharisat.
Ana gama daura auren kuwa ya yi shiri shi da matarsa
suka yi bankwana da mutanen gari ana kukan rabuwa da su.
Suka hau dawakai suka kama hanya suka tafi birnin Nurul
Kalbi.
Wannan shi ne abinda ya faru a birnin gimbiya
Abidatul Azmal bayan an ci birnin da yaki.
25
Taskar Tsafi-4 => Madakin Gin L'AMARIN SU SADAUKI Kurbas kuw AHAlokacin da suka baro Sarki Maharaz a birn
Nurul Kalbi sai suka yi ta tafiya ba sassauci. Tun safe suka fara tafiya basu tsaya ba face idan lokacin sallah ya har sai da gari ya soma duhu sannan suka ya da zango cikin daji suka kafa tantuna. Sadauki Kurbas, Zuhu Hasilatul Kurbas, Himal da Lahura na zaune a wajen to tare da wadansu tsirarun mazaje wadanda duk manyanta sun kewaye wuta suna jin dumi. Tsawon dakiku dayansu bai ce uffan ba. Duk sa'adda Kurbas dubi Zuhura sai ya ga alamun damuwa a tare da ita kuma sai ya ga tana yawan tunani.
Bisa wannan dalili ne ya mike tsaye yai kiranta suka koma gefe daya ya ce da ita, "Ya ke Ummul Maharaz wai shin mene ne yake damunki ne na fuskanci cewa kina cikin matukar damuwa da yawan tunani".
Koda jin wannan batu sai Zuhura tayi ajiyar zuciya ta ce, "Tabbas, ina cikin tsananin fargaba domin ina ji a jikina cewa abokan gaba za su kawo mana hari a ko yaushe daga yanzu. Babban tashin hankalina shi ne ta ya ya zamu iya kare wadannan raunanan jama'a wadanda daga yara sai mata sai kuma tsofaffi? Ka tuna fa cewa mu hudu ne kacal jarumai anan".
hankalinsa
Sa'adda sadauki Kurbas yaji wannan batu sai
sai
ya dugunzuma yai shiru yana tunani, daga can ya dago kai ya dubi Zuhura cikin tsananin damuwa a
lokacin da idanunsa suka kada kamar zai yi kuka, sannan ya
tare
ce,
da
"Ya ke Ummul Maharaz na sani cewa Allah Yana mu to amma fa shi ajali idan wa'adinsa ya cika babu
26
Taskar Tsafi-4 #> Madakin inda ya isa Gini
ri guda
ya kawar da shi. Ni kaina yanzu ina da sauran daya kacal a duniya".
ane
Cikin mamaki Zuhura ta dubeshi ta ce, "Kai kuwa
ga
burine da kai haka alhalin kana da 'ya har ma kuma
ina cikin
jikokinka
hadari?" duk da cewar a halin yanzu jikokin naka
Burina
Kurbas ya sake yin ajiyar zuciya a karo na biyu ya ce, da ya rage shi ne ina son kafin ajalina ya cika Allah Ya bani mata ta gari kuma kyakkyawa kamar matata da na rasa. Na hanga nayi tunani babu wata mace irin wannan matsayi a duk fadin wannan nahiya tamu face ke din nan. Shin za ki iya yi mini alfarma daya ki aureni?" Koda jin wannan batu sai Zuhura taji murmushi ya subuce ma ta, har ta budi baki za ta ce wani abu kawai sai
suka ji wata irin gagarumar iska ta taso daga can sararin samaniya ta addabesu har tantunan da suka kafa suka kama girgiza suna ciccirewa."
Koda suka daga kawunansu sama sai suka yi arba da
manya-manyan dawakai masu fuka-fuki guda dari biyu da
amsin. Zaune kan dawakai wadansu irin manyan mutane
samudawa masu tsananin kwarjini da ban tsoro kuma
ake da muggan makamai cikin shirin yaki".
Koda jin wannan muguwar runduna sai Zuhura,
arbas, Hasilatul Kurbas da Himal suka zare takubbansu
aka taresu suna masu kwalla kabbara:
Nan fa wuri ya yamutse aka kaure da azababben yaki.
Sauran jama su Zuhura dake cikin tantuna a kwance
dama tuni sun zabura a firgice tun sa'adda wannan
gagarumar iska ta taso, ai kuwa duk wanda ya fito daga
27
Taskar Tsofi-4 *> Madakin Gini cikin tantin ya yi arba da wadannan samudawan suka rinka kure musu gudu suna rafkesu. Lokacin da Zuhura ta ga ana karkashe jama'arsu a sa'adda suke kokarin guduwa sai la daka musu tsawa ta ce, "Kowa ya tsaya a waje daya". Nan take jama'ar suka taru a waje guda su kuma su Kurbas suka kewayesu aka ci gaba da dauki ba dadi a haka, ya zamana
cewa samudawan na kokarin hallaka mutanen garin su kuma su Zuhura suna hanasu. In da mutum yana nan
sa'adda ake wannan gumurzu dole ne ya fahimci cewar.
karfin addu'a be kawai yake taimakon su Kurbas domin
kuwa wadannan samudawa sun fisu karfin damtse, naci da
İya yaki nesa ba kusa ba.
Abinda Zuhura ta fahimta shi ne ko kadan
samudawan basa son su hallakasu su biyar din nan sun fi so
su kamasu a hanuu a raye, sauran jama'ar tasu suke son su
hallaka kawai.
A wannan lokaci Lahura bata da lafiya don haka ta
kasa koda tayasu yin yakin ma tana zaune a waje daya don
haka cikin ruwan sanyi samudawan suka kamata suka
daddaureta suka dorata akan doki daya daga cikinsu.
Koda ganin abinda ya faru ga Lahura sai sadan
Kurbas da Zubura suka kara zage dantse suna masu ne
taimakon Allah aka ci gaba da bakin gumurzu. Sai da
shafe sa'a uku cur ana yaki su Kurbas basu sami n
koda kashe mutum daya ba daga cikin samudawan,
kuma samudawan sun kasa kamasu kuma sun kasa ka
sauran wadannan nakasassun jama'a. A sannan ne kowanne
bangare ya gaji ainun aka ja da baya aka yi cirko-cirko ana haki da tunanin
28
mafita.
Taskar Tsafi-4
A
> Madakin Gini wannan lokaci ne Zuhura ta matso daf da sadauki Kurbas ta ce, "Ya kai babban masoyina yanzu wace dabara ce kake ganin zamu yi?"
Kurbas ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Hakika idan muka ci gaba da wannan yaki ba zamu iya kashe wadannan mutane ba, kuma suma ba za su iya kashemu ba, amma fa rayuwar jama'armu tana cikin hadari komai zai iya faruwa
a garesu tunda na fuskanci cewa suna so su kamamu su tafi damu a raye mu yi sharadi da su akan cewa zamu yarda mu ba da kanmu su tafi da mu amma sai idan za su kyale jama'armu su karasa cikin birnin Nurul Kalbi tunda daga
nan zuwa can bai wuce tafiyar rabin sa'a ba. Tabbas idan har suka isa cikin birnin Nurul Kalbi sun tsira babu wani
tsautsayi da zai samesu. Na sani cewa wadannan
samudawan Dakarun abokiyar gabar mu ne, wato gimbiya
Abidatul Azmal ba zai wuce su kai mu inda take ba kin ga
ke nan mun sami wata dama da zamu iya kubutar da
rayuwar su Izaima a can inda aka kaimu din".
Sa'adda Kurbas yazo nan a jawabinsa sai Zuhura tayi
murmushi. Nan take kuwa suka yi yarjejeniya da wadannan
samudawa suka amince aka bar jama'arsu suka ruga da
gudu suka nufi hanyar birnin Nurul Kalbi. Sai da rabin sa'a
shude sannan su Kurbas suka zubar da makamansu aka
kamasu duka aka daukesu aka dorasu akan wadannan
dawakai masu fuka-fuki aka tashi da su sama aka luluka
izuwa cikin gajimare.
ta
Taskar Tsafi-4 => Madakin Gini
A
L'AMARIN SARKI Maharaz da amaryarsa
Sharisat kuwa, sai suka wanzu suna ta tafiya a
cikin daji suka durfafi birnin Nurul Kalbi.
Bayan sun shafe doguwar tafiya ne suka iso wajen
nan inda aka fafata kazamin yaki tsakanin su Kurbas da
samudawan nan. Koda suka ga gawarwaki irin na jama'ar
su sai hankalin Maharaz ya dugunzuma ainun har ya fara
zubar da hawaye. Amma abinda ya daure masa kai shi ne,
bai ga gawar mutum daya ba daga cikin su sadauki Kurbas.
Nan take suka karawa dawakansu kaimi suka ci gaba da
tafiya don isa birnin Nurul Kalbi amma basu isa birnin ba
sai da dare ya soma rabawa. Ai kuwa da zuwansu suka
taryesu cikin matukar farin ciki kuma aka basu labarfin duk
abinda ya faru.
Koda Maharaz yaji cewar gimbiya Abidatul Azmal ta
kama mahaifiyarsa da su sadauki Kurbas sai ya fusata
'ainun ya ce, "Ai kuwa lallai a daren yau zan yi Istaraha don Allah Ya nuna mini inda Abidatul Azmal ta boye wannan
jama'a tawa domin naje mu yi yakin karshe da ita". A wannan dare dai babu wani sukuni a tsakanin
Maharaz da amaryarsa domin sai da suka kusan kaiwa asuba suna ta nafilfiloli da addu'o'in neman sa'a akan
abokan gaba sanann barci ya sacesu ma basu sani ba.
A
L'AMARIN GIMBIYA Abidatul Azmal kuwa Nitama sai da ta kwana bakwai a cikin dakin halwar tsafinta sannan ta fito ta ta iske tuni samudawanta sun kawo su Zuhura.
30
Taskar Tsafi-4 => Madakin Gini Fuskarta a murtuke ta dubi samudawan ta daka musu tsawa ta ce, "Amma dai kun cika manyan banza da wofi tunda baku cika aikinku ba. Me yasa kuka ki hallaka gaba dayan wadannan mutanen birnin Nurul Kalbi kuma in ba
don ma su sadauki Kurbas sun ba da kansu ba da ba za ku iya kamo su ba. Ai duk abinda ya faru tsakaninku da su na gani a madubin tsafina saboda haka baku da sauran amfani
a wajena".
Koda gam afadin haka sai Abidatul Azmal ta zare
takobinta ta daka tsalle sama tamkar an cillata daga cikin
kibiya. Ai kuwa sai ta hau saran wadannan samudawa tana
gididdibasu tamkar tana sassabe a gona.
Cikin kankanin lokaci sassan jikinsu ya rinka
shawagi a sama yana zubewa kasa, jini ya rinka fantsama
yana malala a kas. Nan da nan ta karar da su su duka dari
biyu da hamsin din dayansu bai tsira da rayuwarsa ba.
Al'amarin da ya matukar baiwa su Zuhura mamaki ke
nan domin su hudu sun shafe sa'a uku suna gumurzu da
samudawan basu sami nasarar kashe koda dayansu ba,
amma gashi Abidatul Azmal ta kashesu su duka a cikin
dakiku kadan.
Abin tambaya anan shi ne, "Wane irin sabon
gagarumin karfi Abidatul Azmal ta samu a yanzu?
Wannan tambaya ce wadda Zuhura, Kurbas, Hasilatul
Kurbas da Himal suka yiwa kansu a cikin zuciyoyinsu
kuma suka kasa baiwa kansu amsa.
Bayan Abidatul Azmal ta gama kashe wadannan
samudawa sai ta diro kasa tamkar tsuntsuwa bisa kafafunta
sannan ta dubi su Zuhura ta kyalkyale da dariyar mugunta
31
Taskar Tsafi-4 Madakin Gini
ta ce, "Yanzu kuma za a kaiku cikin kurkukuna a kullel
sanann na tafi har can birnin Nurul Kalbi na kas
dukkanin wani mai rai da ke cikinsa. Yanzu haka Sar Maharaz da matarsa Sharisat suna cikin brinin, lallai sai yanke musu farin cikin aurensu. A gaban Maharaz
yiwa Sharisat yankan rago sannan shi kuma na kamoshi
kawoshi nan na yi muku kisan gilla a gabansa.
Lallai sai na shafe musulmi da musulunci a wanna
nahiya gaba daya yadda har abada ba za a tuna da su ba
tarihi. Tabbas yanzu na gama gagarumin shiri wanda dole
ne ma na sami nasąra akanku makiyana!"
Koda gama fadin haka sai Abidatul Azmal ta rikida t
zama katon tsuntsu ta tashi sama ta fice daga cikin wannan fada
*SHIN ABIDATUL AZMAL ZA TA SAMI
NASARAR DAKUSHE FARIN CIKIN AUREN
MAHARAZ DA ÁMARYARSA?
*IDAN TA RISKESU A BIRNIN NURUL KALBI
WANE IRIN GAGARUMIN YAKI ZA A YI?
*WAYE ZAI SAMI NASARA TSAKANIN
ABIDATUL AZMAL DA SU MAHARAZ?
Mu hadu a littafin TASKAR TSAFI (5) kashi na biyar don jin karshen wannan labari.
Daga mai debe muku kewa a kullum da ko yaushe.
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI.
08184030720, 0706468188О.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels