lOKACIN DA SARAUNIYA Abidatul Azmal Lta shige izuwa cikin karkashin kasa tare da su
Izaima ta face bat ya zamana cewa hankalin su Sarki
Maharaz ya dugunzuma ainun sun rasa abinda za su yi,
sai dukkaninsu suka yi zugum-zugum suka yi shiru suna
tunani her izuwa lokaci mai tsawo dayansu bai ce uffan
ba. Sarki Maharaz ya dubi gawarwakin jama'arsu
musulmi maza da mata, yara da kanana, sai takaici ya
kainashi, bai san sa'adda hawaye ya zubo masa ba.
A sannan ne ya ji ya tsani Sarauniya Abidatul Azmal
fiye da komai a duniya saboda ita ce dalilin wannan
asara da aka yi ta dubunnan daruruwan rayuka.
Maharaz ya dubi Hasilatul Kurbas, Kurbas,
gimbiya Zuhura, Himal da Lahira ya ga suma gaba
dayansu duk kuka suke yi, sai zuciyarsa ta sake sosuwa
ya ci gaba da zubar da hawaye cikin matsanaicin bakin
ciki.
Daga can sai gimbiya Zuhura tasa hannu ta share
hawayenta sannan ta taso daga inda take zaune ta dawo
daf da Sarki Maharaz ta zauna tana mai dafa kafadarsa
suka dubi juna ta ce, "Ya kai dana ka kasance mai
kwarin zuciya, domin bai kamata ace jarumi kamarka ba
yana zubar da hawaye".
Koda Sarki Maharaz yaji wannan batu na
mahaifiyarsa sai ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ya ke
Ummina kiyi sani cewa ba komai bane ya sa ni zubar da
3
Taskar Tsafi-4 > Madakin Gini
wannan hawaye ba face ganin yadda aka karar da dukkan jama'armu yanzu shi ke nan birninmu na Nurul Kalbi ya
zama kango, tunda iya mu din nan ne kawai muka rage."
Da jin haka sai Zuhura tayi murmushi ta ce, "Waye
ya gaya maka jama'armu sun kare? Biyoni a baya ka ga ikon Allah".
Koda gama fadin haka sai Zuhura ta mike tsaye ta
nufi bayan karagar mulki da ke cikin fadar. Maharaz da
su Kurbaz suka mike gaba dayansu suka bita cikin
mamaki. Da isar Zuhura bayan rusasshiyar karagar sai
tasa kafarta ta doki karagar. Nan take karagar ta balle
kuma ta fadi can gefe daya, sai ga wani wakeken rami a
wajen.
A cikin ramin matane, yara da tsofaffi jingim sama
da mutum dubu ashirin a zazzaune suna ta karanta
addu'o'i.
Koda ganin wadannan jama'a sai mamaki da farin
ciki ya turnuke su Sarki Maharaz. Maharaz ya dubi
gimbiya Zuhura ya ce, "Ya ke Ummina ya ya aka yi kika
boye wannan jama'a a wannan rami a lokacin da ake ta
wannan azababben yaki?
Zuhura ta sake yin murmushi a karo na biyu ta се,
"Nima ba dabarata ba ce, taimakone kawai daga Allah".
Koda jin haka sai Maharaz ya daga kansa sama ya
yi godiya ga Allah.
Nan take suka kama fito da wadannan mutane daga
cikin ramin har aka gama fito da kowa. A sannan ne su
Tashar Tsafi-4 Madabin Glni
Maharaz suka zauna suna sa magani a jikin raunikan
jikinsu.
Bayan kowa ya gama kintsawa sai Zuhura ta dubi
Marahaz ta ce, "Ya kai dana yanzu mene ne abin yi?
Wane irin mataki ya kamata mu dauka ne akan wannan
babbar mikiyiya tamu? Ni abinda ya fi tayar mini da
hankali ma shi ne, wadanann yara su Izaima da tayi
garkuwa da su."
Ya yin da Sarki Maharaz yaji wannan batu sai
jikinsa ya yi sanyi ya dubi Zuhura cikin alamun damuwa
ya ce, "Ya ke Ummina kiyi sani cewa duk abinda ke
cikin zuciyarki shi ne a nawa. A cikin kowacce dakika
guda zuciyata ta kan buga da karfi sakamakon tsoron irin
tuggun da gimbiya Abidatul Azmal za ta iya kulla mana
a yanzu. BAbban tashin hankalina shi ne a halin yanzu
bamu san ma anda ta tafi ba da wadannan yara kuma a
koyaushe za ta iya kawo mana harin sumame, haka kuma
na tabbatar da cewa yanzu ba karamin gagarumin shiri za
ta je ta yi ba a kanmu. Ni dai abinda na yi shawara yanzu
shi ne mu tattara mu koma can birninmu na Nurul Kalbi,
idan muka nutsu sai mu ci gaba da shiryc-shiryen ci gaba
da yaki da wannan azzaluma, amma yanzu tunda Allah
Ya sa mun ci wannan birni na ta da yaki, ba zamu barshi
haka ba, zamu kafa daular Musulunci in ya so sai mu sa
wakili wanda zan shugabanci birnin".
Koda jin wannan batu sai Zuhura ta dubi Maharaz
cikin tsananin fargaba ta ce, "Yanzu kai a tunaninka wa
kake zaton daga cikinmu zai iya karbar wannan wakilci
5
Taskar Tsafi-4 => Madakin ba
Gini
Abidatul
tare da yaji tsoron komai ba tunda a koyaushe Azmal za ta iya kawo ziyarar bazata?"
suka
Kafin
ga
Maharaz ya budi baki. ya ce wani abu sai
gidajensu mutanen garin sun fara firfitowa daga cikin suna tahowa gaban wannan rusasshiyar Abidatul fada ta Azmal.
Kafin wani lokaci mai tsawo gaba daya mutanen birnin sun taru a gaban su Sarki Maharaz sun yi jugum- jugum, kallo daya za ka yiwa wannan jama'a ka fuskanci cewa assirye suke su mika wuya.
Hakika mutanen birnin sun yi matukar mamaki bisa ganin yadda akazo a ka ci gimbiya Abidatul Azmal da yaki har fadarta. Al'amarin da ko a mafarki ba su taba
zatonsa ba.
Koda yake wasu daga cikin mutanen birnin a
firgice suke saboda sanin cewa har yanzu fa akwai
sauran rina a kaba, tunda ba a kashe Abidatul Azmal ba,
amma kuma ganin ta tsere daga yakin yasa jikinsu ya yi
sanyi.
Lokacin da Sarki Maharaz ya ga jama'ar birnin sun
gama taruwa a gabansa mazansu da matansu yara da
manya, sai ya hau kan wani dogon mumbari ya
fuskancesu ya ce, "Ya ku jama'ar wannan birni kun yi
sani cewa tsawon shekara da shekaru Sarkinku da 'yarsa
suna yi muku mulkin kama karya, wato mulki na zalunci,
wanda babu mai jin dadinsa face ya kasance Basarake,
ko attajiri na jikin Sarki. Ku sani cewa Sarkinku ya
kasance gagarumin matsafi, kuma 'yarsa Abidatul Azmal
6
Taskar Tsafi-4 => Madakin Gini
ta kasance mashahuriyar BASADAUKIYA, wacce babu
kamarta a wannan nahiya gaba daya. Yanzu gashi an wayi gari mu ma'abota addinin Musulunci mun sami
nasarar yaki akansu, karfin tsafinsu da jarumtakarsu basu
basu nasara ba. Ina so ku sani cewa ba komai ne ya bamu
wannan nasara a kansu ba face taimakon Ubangijinmu
wanda shi ne Ubangijin da ya halicci sammai da kassai
da duk abinda ke cikinsu. Duk wani abu da kuke
bautawa cabaninsa ba gaskiya bane. Ina kira a gareku da
ku beyar da gaskiya ga Ubangijina nayi muku alkawari
za ku zauna a rayuwa irin wacce da talaka da Basarake
duk daya ne, babu sauran zalunci, babu ha'inci sai
karamci da kaunar juna tare da zaman lafiya, wato lislama."
Koda Sarki Maharaz yazo nan a zancensa sai gaba
dayan mutanen garin suka durkusa kasa bisa guiwoyinsu
suna masu nuna mubaya'a a gareshi.
Koda ganin haka sia farin ciki ya lullube Maharaz
da su Kurbas. Maharaz ya dubi jama'ar birnin cikin
murna ya ce, "Ku mike tsaye ai bani za ku durkusawa
ba. Abinda na kę so da ku yanzu shi ne, ku karbi
addinina. Saboda haka yanzu zan biya muku kalmar
shahada don haka sai ku biyata bayan na furta."
Nan take Sarki Maharaz ya biya kalmar shahada, ai
kuwa sai gaba dayan mutanen birnin suka amsa da
muryoyinsu a lokaci guda. Muryoyin kuwa suka cika
birnin gaba daya da amsa kuwwa har izuwa cikin
Sajida
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Aliyu Abubakar Sharfadi
Khadija Muhammad Shitu
Ismail Abdullahi
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Shehu Usman
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Ismail Abdullahi
Ismail Abdullahi
by Azizat Hamza
by Ashanty Love
by Hamida Sunusi Ahmad,HAERMEEBRAERH,Haermeebrah
by Nazir Adam Salih
by Sumayya Abdulkadir Takori
by Fatima
by Tawakaltu Abubakar
by Aisha Humaira
by Billyn Abdul
by Mai Dambu