An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Taskar Tsati
A
magd
sant Slevti
sale
ABDULAZIZ SANI MYGINI
Taskar Tsafi-4 > Madokin Gin
TASKAR TSAFI-4
lOKACIN DA SARAUNIYA Abidatul Azmal Lta shige izuwa cikin karkashin kasa tare da su
Izaima ta face bat ya zamana cewa hankalin su Sarki
Maharaz ya dugunzuma ainun sun rasa abinda za su yi,
sai dukkaninsu suka yi zugum-zugum suka yi shiru suna
tunani her izuwa lokaci mai tsawo dayansu bai ce uffan
ba. Sarki Maharaz ya dubi gawarwakin jama'arsu
musulmi maza da mata, yara da kanana, sai takaici ya
kainashi, bai san sa'adda hawaye ya zubo masa ba.
A sannan ne ya ji ya tsani Sarauniya Abidatul Azmal
fiye da komai a duniya saboda ita ce dalilin wannan
asara da aka yi ta dubunnan daruruwan rayuka.
Maharaz ya dubi Hasilatul Kurbas, Kurbas,
gimbiya Zuhura, Himal da Lahira ya ga suma gaba
dayansu duk kuka suke yi, sai zuciyarsa ta sake sosuwa
ya ci gaba da zubar da hawaye cikin matsanaicin bakin
ciki.
Daga can sai gimbiya Zuhura tasa hannu ta share
hawayenta sannan ta taso daga inda take zaune ta dawo
daf da Sarki Maharaz ta zauna tana mai dafa kafadarsa
suka dubi juna ta ce, "Ya kai dana ka kasance mai
kwarin zuciya, domin bai kamata ace jarumi kamarka ba
yana zubar da hawaye".
Koda Sarki Maharaz yaji wannan batu na
mahaifiyarsa sai ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ya ke
Ummina kiyi sani cewa ba komai bane ya sa ni zubar da
3
Taskar Tsafi-4 > Madakin Gini
wannan hawaye ba face ganin yadda aka karar da dukkan jama'armu yanzu shi ke nan birninmu na Nurul Kalbi ya
zama kango, tunda iya mu din nan ne kawai muka rage."
Da jin haka sai Zuhura tayi murmushi ta ce, "Waye
ya gaya maka jama'armu sun kare? Biyoni a baya ka ga ikon Allah".
Koda gama fadin haka sai Zuhura ta mike tsaye ta
nufi bayan karagar mulki da ke cikin fadar. Maharaz da
su Kurbaz suka mike gaba dayansu suka bita cikin
mamaki. Da isar Zuhura bayan rusasshiyar karagar sai
tasa kafarta ta doki karagar. Nan take karagar ta balle
kuma ta fadi can gefe daya, sai ga wani wakeken rami a
wajen.
A cikin ramin matane, yara da tsofaffi jingim sama
da mutum dubu ashirin a zazzaune suna ta karanta
addu'o'i.
Koda ganin wadannan jama'a sai mamaki da farin
ciki ya turnuke su Sarki Maharaz. Maharaz ya dubi
gimbiya Zuhura ya ce, "Ya ke Ummina ya ya aka yi kika
boye wannan jama'a a wannan rami a lokacin da ake ta
wannan azababben yaki?
Zuhura ta sake yin murmushi a karo na biyu ta се,
"Nima ba dabarata ba ce, taimakone kawai daga Allah".
Koda jin haka sai Maharaz ya daga kansa sama ya
yi godiya ga Allah.
Nan take suka kama fito da wadannan mutane daga
cikin ramin har aka gama fito da kowa. A sannan ne su
Tashar Tsafi-4 Madabin Glni
Maharaz suka zauna suna sa magani a jikin raunikan
jikinsu.
Bayan kowa ya gama kintsawa sai Zuhura ta dubi
Marahaz ta ce, "Ya kai dana yanzu mene ne abin yi?
Wane irin mataki ya kamata mu dauka ne akan wannan
babbar mikiyiya tamu? Ni abinda ya fi tayar mini da
hankali ma shi ne, wadanann yara su Izaima da tayi
garkuwa da su."
Ya yin da Sarki Maharaz yaji wannan batu sai
jikinsa ya yi sanyi ya dubi Zuhura cikin alamun damuwa
ya ce, "Ya ke Ummina kiyi sani cewa duk abinda ke
cikin zuciyarki shi ne a nawa. A cikin kowacce dakika
guda zuciyata ta kan buga da karfi sakamakon tsoron irin
tuggun da gimbiya Abidatul Azmal za ta iya kulla mana
a yanzu. BAbban tashin hankalina shi ne a halin yanzu
bamu san ma anda ta tafi ba da wadannan yara kuma a
koyaushe za ta iya kawo mana harin sumame, haka kuma
na tabbatar da cewa yanzu ba karamin gagarumin shiri za
ta je ta yi ba a kanmu. Ni dai abinda na yi shawara yanzu
shi ne mu tattara mu koma can birninmu na Nurul Kalbi,
idan muka nutsu sai mu ci gaba da shiryc-shiryen ci gaba
da yaki da wannan azzaluma, amma yanzu tunda Allah
Ya sa mun ci wannan birni na ta da yaki, ba zamu barshi
haka ba, zamu kafa daular Musulunci in ya so sai mu sa
wakili wanda zan shugabanci birnin".
Koda jin wannan batu sai Zuhura ta dubi Maharaz
cikin tsananin fargaba ta ce, "Yanzu kai a tunaninka wa
kake zaton daga cikinmu zai iya karbar wannan wakilci
5
Taskar Tsafi-4 => Madakin ba
Gini
Abidatul
tare da yaji tsoron komai ba tunda a koyaushe Azmal za ta iya kawo ziyarar bazata?"
suka
Kafin
ga
Maharaz ya budi baki. ya ce wani abu sai
gidajensu mutanen garin sun fara firfitowa daga cikin suna tahowa gaban wannan rusasshiyar Abidatul fada ta Azmal.
Kafin wani lokaci mai tsawo gaba daya mutanen birnin sun taru a gaban su Sarki Maharaz sun yi jugum- jugum, kallo daya za ka yiwa wannan jama'a ka fuskanci cewa assirye suke su mika wuya.
Hakika mutanen birnin sun yi matukar mamaki bisa ganin yadda akazo a ka ci gimbiya Abidatul Azmal da yaki har fadarta. Al'amarin da ko a mafarki ba su taba
zatonsa ba.
Koda yake wasu daga cikin mutanen birnin a
firgice suke saboda sanin cewa har yanzu fa akwai
sauran rina a kaba, tunda ba a kashe Abidatul Azmal ba,
amma kuma ganin ta tsere daga yakin yasa jikinsu ya yi
sanyi.
Lokacin da Sarki Maharaz ya ga jama'ar birnin sun
gama taruwa a gabansa mazansu da matansu yara da
manya, sai ya hau kan wani dogon mumbari ya
fuskancesu ya ce, "Ya ku jama'ar wannan birni kun yi
sani cewa tsawon shekara da shekaru Sarkinku da 'yarsa
suna yi muku mulkin kama karya, wato mulki na zalunci,
wanda babu mai jin dadinsa face ya kasance Basarake,
ko attajiri na jikin Sarki. Ku sani cewa Sarkinku ya
kasance gagarumin matsafi, kuma 'yarsa Abidatul Azmal
6
Taskar Tsafi-4 => Madakin Gini
ta kasance mashahuriyar BASADAUKIYA, wacce babu
kamarta a wannan nahiya gaba daya. Yanzu gashi an wayi gari mu ma'abota addinin Musulunci mun sami
nasarar yaki akansu, karfin tsafinsu da jarumtakarsu basu
basu nasara ba. Ina so ku sani cewa ba komai ne ya bamu
wannan nasara a kansu ba face taimakon Ubangijinmu
wanda shi ne Ubangijin da ya halicci sammai da kassai
da duk abinda ke cikinsu. Duk wani abu da kuke
bautawa cabaninsa ba gaskiya bane. Ina kira a gareku da
ku beyar da gaskiya ga Ubangijina nayi muku alkawari
za ku zauna a rayuwa irin wacce da talaka da Basarake
duk daya ne, babu sauran zalunci, babu ha'inci sai
karamci da kaunar juna tare da zaman lafiya, wato lislama."
Koda Sarki Maharaz yazo nan a zancensa sai gaba
dayan mutanen garin suka durkusa kasa bisa guiwoyinsu
suna masu nuna mubaya'a a gareshi.
Koda ganin haka sia farin ciki ya lullube Maharaz
da su Kurbas. Maharaz ya dubi jama'ar birnin cikin
murna ya ce, "Ku mike tsaye ai bani za ku durkusawa
ba. Abinda na kę so da ku yanzu shi ne, ku karbi
addinina. Saboda haka yanzu zan biya muku kalmar
shahada don haka sai ku biyata bayan na furta."
Nan take Sarki Maharaz ya biya kalmar shahada, ai
kuwa sai gaba dayan mutanen birnin suka amsa da
muryoyinsu a lokaci guda. Muryoyin kuwa suka cika
birnin gaba daya da amsa kuwwa har izuwa cikin
7
Taskar Tsafi-4 => Madakin Gini
dazuzzuka. Al'amarin da ya kara jefa su Sarki Maharaz
cikin matukar farin ciki ke nan.
Sarki Maharaz ya ci gaba da bayani yana mai cewa
zan zauna tare da ku a cikin wannan birni har izuwa
lokaci mai tsawo domin na baku kariya da taimakon
Allah bisa sharrin Abidatul Azmal kuma zamu koyar da
ku addinin Allah."
Koda jin haka sai farin ciki ya lullube gaba dayan
jama'ar birnin suka sami nutsuwa a cikin zukatansu. A
wannan lokaci ne Sarki Maharaz ya sauko daga kan
mumbarin da yake jawabi kawai sai ya ga Hasilatul
Kurbar, Himal da Kurbas sun taho gareshi fuskokinsu
cike da alamun firgici. Da isowarsu daf da shi sai Kurbas
ya dubeshi ya ce, "Ya kai wannan Sarki mai daraja yanzu
ke nan kana nufin anan zamu barka mu mu tafi can
birnin Nurul Kalbi? Ka sani cewa muna cikin fargaba
bisa sharrin Abidatul Azmal kuma muna cikin tashin
hankalin bisa halin da jikokina ke ciki, wato su Izaima
wadanda ke can hannun Abidatul Azmal."
Sa'adda Sarki Maharaz yaji wannan batu sai ya yi
murmushi sanann ya ce, "Ya kai wannan sadauki ina so
ku sani cewa wanda duk ya dogara da Allah to fa Allahzai iya masa duk abinda ya gagareshi. Ku fa tuni hasken
imani ya ratsa jikinku su kuwa jama'ar wannan gariyanzu ne za su san Allah. Tun da har mun sami nasara shigar da su cikin addinin Allah bai kama ta mu yi nisa da su ba kuma suna bukatar kariyarmu. Idan ban zaunatare da su ba, Abidatul Azmal za ta iya dawowa a ko8
Taskar Tsafi-4 => Madakin Gini yaushe ta dada kafirtar da su. Yanzu abin da nake so da
ku shi ne, ku yi shiri tare da sauran jama'armu ku tafi izuwa can birninmu na Nurul Karbi domin a dada raya
birnin. Abu daya za ku ruke ku sami kariya daga sharrin abokan gaba, wato addu'a. Lallai ku lizamci addu'ar
neman tsari tun akan hanyarku har ku isa can, bayan kun shiga birnin ma ku ci gaba da addu'ar kada ku sassauta
dare da rana. Albarkacin wanda aka yi duniya da lahira
dominsa babu abinda zai sameku. Ina son ku bani kwana
talatin kacal, wannan lokaci zai isheni na koyar da jama'ar wannan birni addinin Allah kuma zan ci gaba da yin istahara domin Allah Ya nuna mini irin shiryeshiryen da Abidatul Azmal ke yi a kanmu domin mu san
matakin da zamu dauka a kanta.
Ya yin da Sarki Maharaz yazo nan a zancensa sai
hankalin su Kurbas ya kwanta suka sami nutsuwa. Nan
take suka kama shirye-shiryen tafiya. Wasu daga cikin
attajiran birnin kuwa suka shiga kawo musu gudunmawa
ta ababan hawa da guzuri mai yawa har su Kasim suka yi
mamakin irin wannan karamci. Daga cikin attajiran da
suka kawo gudunmawar mafi tsoka akwai wanda ake
kira Suhairu ibini Marwasi.
Attajiri Suhairu ya kasance mutum mai tausayi da
jin kai kuma gaba daya mutanen birnin suna girmamashi
şaboda kyawawan halayensa. Tsananin hakurinsa ne
yasa mahaifin Abidatul Azma! yake saurara masa. Da
yake Allah ya yiwa Suhairu karfin arziki duk abind
9
Taskar Tsafi-4 -> Madakin Gini
Sarki yabukata a wajensa yana bayarwa bai taba musu
ba, kuma yana matukar biyayya a gareshi
Bayan su Kurbas sun gama shirein tafiya sai attajin
Suhairu ya zo wajen Sarki Maharaz ya се, "
shugabana ina neman alfarma guda daya a wajenka. Ina
son na saukeka a gidana tunda dai yanzu an rushe
wannan gidan sarauta na Abidatul Azmal babu inda za
ka zauna".
Koda fadin haka sai sauran attajiran garin suka taso
suna cewa suma za su bawa Maharaz masauki. Maharaz
ya dubesu ya ce, "Ai wanda ya fara bani masauki
wajensa zan je".
Koda jin haka sai farin ciki ya lullube attajiri Suhairu. Ba tare da bata lokaci ba Sarki Maharaz ya je wajen Zuhura domin su yi sallama, sai ya ga idanunta sun ciko da kwalla, al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa
ce, "Ya
ke nan ya dubeta cikin tsananin damuwa ya ke Ummina ina dalilin cikar kwalla a idanunki?"
subuto
Sa'adda Zuhura taji wannan tambaya sai hawaye ya ma ta sannan ta ce, "Ya kai dana ka yi sani cewa kaine
sai kai,
kadai
gashi abinda
har
ya rage mini a duniya, bani da kowa
ganin jikina. yanzu ka ki ka yi aure bare na sa ran Haka kuma kullum rayuwarka hadari take, a ko a cikin yaushe za ka iya rasa rayuwarka. mai rokonka Ina da ka nemi budurwa ta gari ka yi aure a
cikin wannan
shi ne mu
birni, domin ka cika mini burina. Fatana bar irin zuri'armu a doron kasa kafin cikar ajalinmu".
10
Taskar Tsafi-4 => Madakin Gini
Ya yin da Zuhura ta zo nan a zancenta sai
tausayinta ya turnuke Sarki Maharaz har hawaye ya zubo
masa, kawai sai ya rungumeta ya ce, "Ya ke Ummina
kiyi sani cewa a nalin yanzu babu wata tsayayyiyar mace
a zuciyata, amma zan yi kokari na bi umarninki don haka
sai ki tayani da addu'ar Allah ya hadani da wadda za ta
dace da ni. laka kuma nima ina neman alfarma guda
daya a wajenki".
Cikin matukar mamaki Zuhura ta dubi Maharaz ta
ce, "Kai kuwa wacce irin alfarma kake son nayi maka?"
Maharaz ya sunkui da kansa kas ya ce, "Ya ke Ummina
ina son ki sani cewa har yanzu shekarunki basu wuce na
yin aure ba, saboda haka ina shawartarki da kiyi aure
domin shi ne mutuncin 'ya mace, kuma samun cikar
darajarta. Idan za ki bi shawarata, me zai hana ki auri
Kurbas?.
Koda jin wannan, batu sai mamaki ya kama Zuhura ta
ce, "Me yasa kake mini sha'awar auren Kurbas?". Maharaz
ya yi murmushi ya ce, "Ai ido ba mudu bane, amma ya san
kima. Tuntuni na lura da wadansu al'amura da ke wakana
tsakaninki da shi, zan so ace Kurbas ya zamo mahaifina na
biyu a rayuwa".
Da jin haka sai Zuhura ta yi murmushi sannan ta
janye jikinta daga cikin na Maharaz ta dubeshi cikin fara'a
ta ce, "Sai ka tayani da addu'a Allah Ya zaba mini abinda
ya fi alkairi". Maharaz ya ce, "Amin".
11
Taskar Tsaofi-4 >Madahin G
Nan take su Zuhura suka hau dawakansu suk
bankwana da Sarki Maharaz suka kama hanya don fita d
cıkin brinin.
Himal da Lahura ne akan gaba bisd dawakansu a je
sannan Zuhura da Kurbas, sai sauran mutanen birnin Nur
Kalbi wadanda suka yi saura a yakin 'da aka fafata
Sarki Maharaz da sauran jama'a kuwa, suka bisu
kallo har suka fita daga cikin birnin, suka yi nisa har suk
bace musu da gani. Faruwar hakan ke da wuya sai Attaji
Suhairu ya kama hannun Sarki Maharaz ya jashilsuka taf
izuwa gidansa. A sannan ne jama'a suka watse suka kam
komawa gidajensuode dsnsy tod awao insa b пог в
Sius Wannan shi ne abinda ya faru a birnib Sarauniy
Abidatul Azmal bayan an fafata kazamin yaki anci garin da
yaki, wato Musulmai sun sami nasara bl erIBİEZRD
st Bd aut ay Aволв ве sisd nsanew gii sho
переез
SAndaM AL'AMARIN SARAUNIYA Abidatul Azmal
DRE RY kuwa, lokacin da ta nutse izuwa karkashin
avkasa dauke da Izaima, Uhairu yayan Himal,
sai tsulum! ta baiyana a cikin wani makeken daji a gaban
wani katon tsauni. Take Sarauniya Abidatul Azmal ta shafi tsaunin da hannunta na hagu sai ga wata kofa ta zinare ta abaiyana a jikin tsaunin. Sarauniya Abidatul Azmal tasa hannu ta bude kofar ta kunna kai ciki, sai ga ta a cikin wata luntsumemiyar fada wadda aka Kawatata da dukkan kayan kawa da kayan jin dadin rayuwar duniya. Fadar a cike take da kuyangi da bayi masu hidima, kuma dukkaninsu mutane ne babu aljan ko guda daya.
12
Taskar Tsafi-4 => Madakin Gini
Koda wadannan hadimai suka ga shigowar gimbiya Abidatul Azmal dauke da yara guda biyu, sai suka rinka zubewa kasa suna kwasar gaisuwa. Ko daya daga cikinsu bata kalla ba kawai sai ta ci gaba da tafiya har ta isa kan
wata kasaitacciyar karagar mulki ta zauna. Zamanta ke da wuya wani dogon mutum tsoho mai farin gemu yazo gareta
ya zube kasa ya kwashi gaisuwa ya ce, "Lale marhaban da Sarauniyar duniya. Ya shugabata lafiya kuwa kika zo mana
a wannan lokaci ba sa'adda kika saba zuwa mana ba?".
Ya yin da Abidatul Azmal taji wannan tambaya sai tayi ajiyar zuciya sannan ta dubi tsohon cikin nutsuwa ta
ce, "Ya kai Zurhus hakika zuwana wannan boyayyiyar fada
tawa a yanzu ya zo ne bisa dole ba akan shiri ba, domin
makiya sun bini har fadata sun cini da yaki. In ba don na
gudo nan ba da nima sai sun hallakani. Wadannan yara
kuwa da ka ganni da su garkuwa nayi da su domin na sami
damar daukar fansa akan yarima Himal domin shi ne ya
kashe mahaifina Sarki Asmaru".
Koda jin haka sai idanun tsoho Zarhus suka zazzaro
ya firgita ainun saboda jin cewa an kashe Sarki Asmairu.
Sarauniya Abidatul Azmal ta dubi wata kuyanga ta mika
ma ta Izaima da Uhairu ta ce, "Ki kai wadannan yara
kurkuku a tsaresu, amma a kula da abincinsu sosai, kuma
kada a basu wuya". Kuyangar ta karbi yaron ta ce, "An
gama ya shugabata".
Kawai sai ta tafi da su izuwa cikin wata kofa ta shige.
Sarauniya Abidatul Azmal tayi shiru tana mai sunkui da
kanta kas, ta shiga tunani har izuwa lokaci mai dan tsawo,
daga can sai idanunta suka ciko da kwalla ta dago kai ia
3
Taskar Tsafi-4 >Madakin Gin
dubi tsoho Zarbus ta сe, "Hakika abokan gaba sun
mutuncina kuma sun zubar mini da kimata kuma sun yan
mini farin cikina. Ya zama wajibi a gareni nayi gagarum
shiri na Karshe don ganin bayan makiyanmu"
Koda gama fadin haka sia Abidatul Azmal ta dauk
madubin tsafinta ta dorashi akan cinyaria sannan
shafeshi da hannunta na hagu sau uku. Nan take duk abind
ya faru a birnin ya baiyana akan madubin tun daga lokaciтda aka gama wannan yaki kawo izuwa sa'adda SarkMaharaz ya yi bankwana da su Kurbas suka tafi izuwabirnin Nurul Kalbi domin su sake raya birnin nasu".
Koda gama ganin wannan allamari sai gimbi
Abidatul Azmal ta takarkare ta bushe da mahaukaciyadariya. har da faduwa kasa daga kan karagar mulkiAl'amarin da ya baiwa gaba dayan badiman fadar mamak
ke nan bar ma suka tsorata. Daga can kuma sai ta miketsaye ta koma kan karagarta ta zuana ta murtuke fuskakamar an aiko ma ta da sakon mutuwa. Kawai sai ta tafahannayenta sau uku. Faruwar hakan ke da wuya sai wat
katuwar kofa ta bude, wadansu irin samudawan mutan
suka rinka fitowa daga ciki. Adadin samudawan bai wu
dari biyu da hamsin ba, dukkaninsu sun yi shigar yaki n
matukar kwarjini da ban tsoro. Su kansu hadiman wane
fada sai da suka razana ainun da ganin wadan
samudawa domin basu san da zaman su ba a cikin iad
asalima babu wanda ya taba shiga wannan daki da suka
daga ciki.
Su dai wadannan samudawa sun kasance doga
tamkar bishiyar dabino domin mutum bai isa ya iya tah
Taskar Tsafi-4 -> Madakin Gini
kafadarsu ba ma bare kawunansu, sannan suna da kauri da
kuma kirar halittar jikinsu ta sha bambam da ta bil'adama tamkar ba jinsin bil'adama ba saboda kunnuwansu dogaye
ne a tsaitsaye kamar na zomaye.
Fuskokinsu kuwa munana ne babu kyan gani tamkar
na birirrika. Abinda zai daurewa mutum kai shi ne a ina
Abidatul Azmel ta samo wadannan mutane masu kama da
Dodanni, wadanda babu irin su a doron kasa? Babu mai iya
amsa wannan tambaya face ita kanta Abidatul Azmal din.
Geba dayan wadannan samudawan sai suka jeru a
layi cikin sahu-sahu a gaban gimbiya Abidatul Azmal suka
sunkui da kawunansu kas cikin alamun biyayya kuma suka
kame tamkar sun kasance gumaka.
Abidatul Azmal ta dubi babban cikinsu mafi girma ta
ce, "Ya kai Gamzuba maza ku yi hawa kai da jama'arka ku
nufi hanyar birnin Nurul Kalbi za ku riski su sadauki
Kurbas. Ina son ku afka musu ku kashe gaba dayan jama'ar
da ke tare da su maza da mata, yara da manya. Amma lallai
ina son ku kamo mini Kurbas da Zuhura mahaifiyar
Maharaz a raye, da kuma Himal da Hasilatul Kurbas da
Lahura ko ta wane hali ku zo mini da su nan. Amma ku
tabbatar da cewa kun gusar musu da hankalinsu kafin ku
kamasu in ba haka ba kuwa ba za ku iya kama su ba".
Sa'adda gimbiya Abidatul Azmal ta zo nan a zancenta
sai shugaban samudawan Gamzuba ya risina ya ce, "An
gama ya shugabata, amma kin sani cewa wadannan mutane
da kika turamu mu kamosu ma'abota addinin Musulunci ne
kuma sun kasance shaidanun gaske. Wace dabara kike
ganin zamu yi mu sami nasara akansu farat daya?".
15
Taskar Tsafi-4 >Madakin Gini
Koda jin wannan tambaya sai Abidatul Azmel tay
murmushi sannan ta ce, "Tabbas kayi hikima da ka yi mias
wannan tambaya. Dabara daya za ku yi amfaní da ita. Kad.
ku kuskura ku afka musu lokaci guda, dole ne ku fara t
dan leken asiri garcsu domin ya ga halin da suke ciki. Idan
har suna cikin karance-karancensu na sihiri ne kada ka
kusancesu sai dai ku kusancesu a lokacin da suka yada
zango suna barci ko dai suna wani abu sabanin irin
bautarsu".
Sa'adda Gamzuba yaji wannan batu sai ya y
murmushi mai kama da kukan jaki, sannan ya juya ya daga
kansa sama ya karanta wadansu dalasiman tsafi. Nan take
kadansu manyan tagogi guda dari biyu da arba'in suka
bude sai ga manyan dawakai kosassu masu fuka-fukai sun
yi fitar burgu daga ciki. Gabadaya dawakan suka sauko
Kasa suka dira agaban samudawan, kowa ya kama nasa ya
dane a lokaci guda suka zaburi dawakan suka tashi da su
sama suka fice ta saman fadar suna masu ratea tsaunin
tamkar ratsawar haske.
A wannan lokaci duk wanda ya ga wannan runduna ta
wadannan samudawa dole ne ya razana domin kwarjininsu
ya kai su hallaka duniyar ma gaba daya ba wai gari guda ba.
Bayan bacewar wadannan samudawan ne gimbiya
nufi
Abidatul
kofar Azmal
wani
ta mike tsaye daga kan karagar mulki ta daki dabam.
ya ce,
Koda
"Ya
ganin haka sai tsoho Zarhus yai sauri ya tarets
da abokan
gabar shugabata
ya zamu
idan wadannan samudawan sun dawo yi da su?"
16
Taskar Tsafi-4 >Madakin Gini Abidatul Azmal ta ce, "Suma a kaisu kurkuku a
ajiyesu amma kada akaisu dakin da aka kai su Izaima. Nimayanzu zan shiga dain halwar tsafi ne kuma ba zan fito ba sai bayan kwana goma sha hudu domin na binciko abinda zan yi naga bayan Sarki Maharaz saboda shi kadai
ne mutumin da zai iyakawo mini cikas a cikin al'amurana." Tsoho Zarhus yai ajiyar zuciya ya ce, "Ya shugabata to me zai hana ayanzu ki tura wadannan Dakaru naki izuwa can birnin naki domin su kawar da Sarki Maharaz don kada jama'armu su ci gaba da addinin Maharaz?".
Koda jin wannan batu sai hawayen takaici ya zubowa Abidatul Azmal ta ce, "Ai na makara tunda har Maharaz ya musuluntar da jama'ata. Abinda zan iya yi kawai shi ne, na shiga wannan dakin balwa na binciko hanyar da zan bi na
ga bayan sa, a sannan ne zan yi gagarumin shirin yaki na Karshe. Ina tabbatar maka da cewa sai na sami gagarumar
nasara wacce zan kawar da musulunci da musulmi a
wannan nahiyar gaba daya". fadin hakan sai Abidatul Azmal ta Karasa cikin wannan
dakin tsafi. Tana shiga cikin dakin sai kofare dakin ta kulle da kanta.
A
CAN BIRNIN Abidatul Azmal kuwa, lokacin
Ada attajiri Suhairu ya tafi da Sarki Maharaz
izuwa gidansa sai ya shigar da shi har izuwa cikin turakarsa.
Gidan attajiri Suhairu ya kasance babban gida ne mai wuri-wuri, sannan kowanne Gangare akwai hadiman da ke
17
Taskar Tsafi-4 Madakin Gini
kula da shi. Hakika gidan ya tsaru kuma yaKawatu tamkar
sarauta. gidan
Da shigar su cikin turakar sai attajiri Suhairu ya kai
Maharaz har kan shimfidarsa ya zaunar da shi sannan ya
kirawo wata kuyanya ya umarceta da taje ta kawo musu
abinci. Cikin kankanin lokaci aka kawo musu abinci na
afarma sama da kala bakwai.
A dai-dai wannan lokaci ne Maharaz ya fuskanci
cewa lokacin sallar la'asar yayi, saboda haka sai ya ki cin
abincin ya