sai kaga sun faɗi ƙasa
magashiyan,
Amma saboda juriya irin ta zaratan
Jarumai sai suka muƙe tsaye aci
gaba da yaƙin,
Koda ganin hakan sai ta falfala da
azababban gudu izuwa kan su
Tana mai kwala kabbara da ƙarfi
tare da yiwa Annabi Sallallahu alaihi
Wasallama salati,
Domin ta kai musu ɗauki,
Cikin daƙiƙa hamsin bisa taimakon
Ubangiji mahalicci ta samu nasarar
hallaka dakarun baki ɗaya,
Faruwar hakan ke da wuya sai gaba
ɗaya gawarwakin dakarun da
HAUSABOOK.COM
78
makaman yakin gami da jinin da ya
cakuɗa da ƙasa suka ɓace ɓat
tamkar basu taɓa wanzuwa ba,
Nan take filin ya rikiɗa izuwa wata
ƙasaitacciyar faɗa,
Da aka kawata ta da nau'ikan kayan
ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar
duniya,
Bisa wani zagayayyan tudu da aka
shimfiɗe sa da wata irin Koriyar
Darduma anan aka ajiye wata
ƙasaitacciyar sanda wace akayi ta
zallar zinare kuma aka yi mariƙin ta
da zubardaju,
Sandar tana canza launi lokaci zuwa
lokaci
Kai da gani kasan aiki ne na sihiri.
Koda Husnat tayi arba da sandar sai
ta dubi Bawa hilwas tace"sai kayi
hanzari ka ɗauko mana waccan
sandar sihiri domin mu tafi izuwa
HAUSABOOK.COM
79
dajin kushuful-fannar domin ɗauko
ƙoƙon kan boka Manaf.
Ko da jin wannan umarni daga bakin
Husnat
Sai hilwas ya taka da kafafun sa har
izuwa wannan gayayyen tudu yake
ya dauki sandar sannan ya dawo
izuwa inda su Kahzib ke tsaye.
Kawai ya shige gaba ya durfafi kofar
fita daga gidan,
Sharwas, Kahzib na biye dashi
jaruma Husnat ce a karshe,
Lokacin da suka fita sai suka hango
dawakan su acan gefe suna cin
ciyayi,
A sannanne Husnat ta lura cewa
lokacin sallar la'asar ya giya,
Don haka sai tayi istigfari sannan ta
cire salkar ruwan ta ta ɗaura alwala,
HAUSABOOK.COM
80
Bayan ta kammala ne ta fuskanci
gabas ta tayar da sallah,
Sa'adda Hilwas, Kahzib da Sharwas
suka ga yadda jaruma Husnat ke
gudanar da ibadar ta nan take suka
ji addinin musulunci ya kayatar
dasu,
Domin ba su taɓa ganin addini mai
tsafta da nutsu tamkar addinin
Husnat ba,
Nan take Sharwas yaji soyayyar
Husnat ta daɗa mamaye zuciyar sa,
Da yake yamma tayi liƙis duhun
magariba ya fara kawo kai sai
hilwas ya bayar da shawarar a
kwana a dajin idan ya so da safe sai
a durfafi dajin Kushuful-fannar,
Mu haɗu a KANGIN BAUTA Littafi na
12 domin jin cigaban wannan
kasaitaccen labari,
HAUSABOOK.COM
81
Daga mai ɗebe muku kewa a kullum
da ko yaushe
Kamar yadda jarumi Hilwas ya
bayar da shawara haka al'amarin
yakasance,
In da aka kwana a wajen da dukudukun safiya bayan jaruma Husnat
tayi sallar asuba anyi kalaci kowa ya
kimtsa cikin sa,
Sai kowa ya kama dokin sa ya hau
ya sakaasa linzami aka cigaba da
tafiya,
Hilwas, Kahzib da Sharwas suna
tafiya a jere kusa da juna,
Husnat na biye dasu har a wannan
lokaci fuskar ta rufe take da rawani
idanuwan ta kaɗai ake gani,
Nan fa aka wanzu ana ratsa
duwatsu, koramu tsaunuka haɗe
kwazazzabai gami da sarƙaƙiya,
HAUSABOOK.COM
82
cikin matsanancin gudu ma keta
sa'a ,
Wasa-wasa saka gashi an shafe
tsawon Sa'a uku ana wannan
tafiya,amma ba'a haɗu da wani abu
mai cutar wa ba,
Koda kuwa miyagun yan fashi da
dakarun sumame,
Lokacin da Sa'a huɗu ta cika a dai
dai lokacin aka shigo dajin
kushuful-fannar,
Nan fa kowa yasha jinin jikin sa bisa
ganin yadda dajin yaksance dole ne
a samu miyagun halittu a cikin sa,
Kuma yakasance cikin shirin ko ta
kwana
Tsawon tafiyar Sa'a aka yi sannan
aka hango wata rijiya a can nesa,
Don haka sai aka ƙara azama domin
isa, lokacin da aka isa sai kowa yaja
HAUSABOOK.COM
83
linzamin dokin sa ya kama ya sauka
ƙasa,
Ita dai rijiyar an gina ta ne da zallar
dawatsun wuta masu kwarin gaske,
Tana ɗauke da murfi guda ɗaya jal,
da aka yi shi da zallar mulmulallan
karfe,
In da za'a sanya karti majiya karfi
mutun sattin ba zasu iya buɗe
murfin ba,
Nan fa aka yi cirko-cirko aka rasa
wanda zai buɗe murfin rijiyar.
Daga can Kahzib ya matsa izuwa
bakin Rijiyar ya sanya hannun sa
ɗaya domin ya buɗe murfin amma
sai yaji tamkar Dutse ya rike, sai da
ya tara gumi ya jiƙe sharkab amma
murfin ko gezau bai yi ba,
Amma sai da hilwas, sa Sharwas
suka gwada tasu dubarar amma
murfin bai buɗe ba,
HAUSABOOK.COM
84
Duk wannan abu dake da wakana
jaruma Husnat na tsaye a gefe guda
tana gani bata ce ƙala ba.
Koda taga kowa ya kasa buɗe wa sai
ta matsa daf da rijiyar ta karanta
ayatul-kursiyyu tare da yiwa Annabi
s'a'w salati.
Ta sanya hannun ta ɗaya ta buɗe
murfin tamkar ta yaye tufafi,
Hilwas, Kahzib da Sharwas basu san
sa'adda su ka dunga dalalar da
yawu daga bakunan su ba saboda
matukar al'ajabi.
Koda murfin ya buɗe sai akaji wani
irin mahaukacin gurnani na fitowa
daga cikin rijiya,
Daga can sai aka ga wani ɗan
wadan aljani yayo fitar burgu daga
cikin rijiyar tamkar an janyo shi da
ƙugiya.
HAUSABOOK.COM
85
Aljanin yakasance baƙi mummuna
yana ɗauke da fuka -fukai irin na
jemage, Du du du tsawon sa bai
huce kamu biyu ba,
A hannu ɗaya ana rike da wani
ƙoƙon kai, ɗayan kuwa yana ɗauke
da wani zabgeegen Gatari na zinare
yana sheƙi da walwali,
Aljanin ya bushe da dariyar
mugunta tamkar bazai daina ba
Daga bisani ya murtuke fuska
tamkar an aiko masa da wasikar
mutuwa ya ce" Kaicon ku yaku
waɗannan bil'adama ma'abota
taurin kai da GAJEREN KWANA,
kuyi sani cewa haƙiƙa kun tafka
babban kuskure da kuka kuke
tsammanin cewa zaku iya ɗaukar
ƙoƙon kan mai girma Mannaf kuma
har ku fita a raye,
Ina mai tabbatar muku dacewa
dayan ku bazai fita a raye ba,
HAUSABOOK.COM
86
Kafin aljanin ya gama rufe bakin sa
Husnat ta tari numfashin sa tana
mai daka masa tsawa tace
"Kai tsohon maketaci kuma
azzalumi la'anannan Allah kayi sani
cewa,
Ka sani cewa ai babu mai kashe wa
face Ubangijin musulunci,
Da yardar sa zamu ga bayan ka
sannan samu abinda muka fito
nema.
Sa'adda ɗan wadan aljanin yaji
wannan batu daga bakin Husnat sai
ya fusata ainun idanun shi su ka
kaɗa su ka yi jawur, gashin jikin shi
ya mimmiƙe ya dubi Husnat yace
"Na rantse da gemun mai gidana
boka Mannaf sai nayi gunduwagunduwa da sassan jikin ki ta yadda
ƙananan tsuntsaye zasu ji daɗin
tsatstsagar naman ki,
HAUSABOOK.COM
87
Domin hakan ya zamo darasi ga
bil'adama masu tsarin idanu irin ki,
Kafin Husnat ta sake cewa wani abu
Aljanin ya ɗaga gatarin sa izuwa
sama ya falfala da azababban gudu
izuwa kan ta yana ihu da kururuwa
mai firgita DANDAZON MAYAKA
Komai tsakanin yawan su,
Koda ganin hakan sai Husnat ta
kwala kabbara da ƙarfi tare da zare
takobin ta ta ruga izuwa gare shi,
Su na haɗuwa suka ruguntsume da
azababban yaƙi mai matukar
kwarjini daban sha'awa,
Su duka biyun suka wanzu suna
kaiwa juna sara da suka cikin
matuƙar zafin nama juriya da
bajinta tagaban kwatance,
Wohoho haƙiƙa masu iya magana
sunyi gaskiya da suka ce idan gwani
ya haɗu da tsohon ƙashi , juriya da
HAUSABOOK.COM
88
jarumtaka suka game a waje guda
dola ne artabu ya zamo tashin
hankali,
Gaskiyar masu iya magana da suka
ce fadan da yafi karfin sai ka koma
ɗan kallo,
Hakan ne yafaru da hilwas, Kahzib
da Sharwas domin koda suka ga
cewa Manyan GWARAZAN JIYA sun
kacame da azababban yaƙi sai suka
koma izuwa inda dawakan su suke
suna hangen abinda ke wakana, Sai
da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana
wannan fafatawa amma aljanin bai
samu nasarar taɓa jikin Husnat ba,
A zahiri ga wnada yake kallon yadda
artabun ke wakana sai tabbatar da
cewa aljanin ya nuna ka Husnat a
karfin damtse,
Sai dai ita ta fi shi salon kwarewar
yaƙi,
HAUSABOOK.COM
89
Al'amarin da ya fusata shi kenan ya
kaiwa Husnat wani bahagon sara da
gatarin sa sa nufin tsarga ta gida
biyu,
Cikin wani irin baƙin zafin nama
Husnat ta wurkila tare da zamewa,
Gatarin aljain ya sari iska, koda
aljanin yaga cewa yakasa samun
nasarar hallaka ta sai ya shiga aika
mata miyagun sihiri kamar ,kibbau,
duwatsu,mashi da sauran su,
Amma Dazarar sun doshi inda take
sai su narke su zama ruwa su ɗige a
ƙasa,
saboda addu'o'in da take karantawa
na neman tsari a a gare sa,
Da kyar da siɗin goshi ta samu ta
hallaka aljanin ta hanyar soka masa
takobi a ƙahon zuciyar sa.
Kuma ta ƙone shi ƙurmusa ta hanyar
karanta masa ayatul-kursiyyu,
HAUSABOOK.COM
90
Haƙiƙa su Bawa hilwas sun ga iko da
ƙidira ta Ubangijin talikai bisa ganin
yadda Husnat tayi masara akan
aljanin,
Bayan an fito da abin guzuri an yi
kalacin rana. Sai kowa ya sake
kama linzamin dokin sa ya hau ya
sakar masa linzmai a ka cigaba da
tafiya domin fi cewa daga dajin
kushuful-fannar.
Mu haɗu a Littafi na 12 don cigaban
wannan labari
A wannan karon da aka fara wannan
tafiya sai fira ta ɓarke tsakanin su
jarumi Hilwas,
Domin a wannan karon sun samu
nutsuwa a zukatan su cewa jaruma
Husnat za ta cika musu dukkan
burikan su bisa taimakon Ubangijin
ta,
Gaskiyar masu iya magana da su ka
ce sannu sannu bata hana zuwa sai
HAUSABOOK.COM
91
dai a daɗe ba'a je ba, sai gashi an
shafe tsawon kwanaki ashirin da
uku ana wannan tafiya,
A ranar kwana na ashirin da huɗu
ne da la'asar aka iso birnin Baitulna'im,
Tun daga nesa aka hango kofar
birnin cike da miyagun dakaru
ɗauke da miyagun makamai,
Al'amarin da ya sanya su hilwas su
ka sha jinin jikin su kenan,
Domin da gani ruwa baya tsami
banza, don haka sai hilwas ya ɗauki
sandar sihiri ya sanya ta a kirjin sa
ta yadda babu komai wanda zai iya
gane ta,
Kuma ya ɗauki ƙoƙon kan boka
Manaf ya sanya shi a cikin wata jaka
ya rataya a gadon bayan sa, Sannan
ya zare takobin sa. Da ganin hakan
sai Kahzib ya zare kwari da bakan
sa,
HAUSABOOK.COM
92
Sharwas ya ciro mashin sa ya rike a
hannu, Husnat riƙe da takobin ta
aka durfafi kofar birnin Baitulna'im,
Yayin da ya rage saura taku talatin
tsakanin su da kofar birnin. Sai
kawai aka ji wani ƙara daga cikin
birnin sai kofar ta buɗe, Sai ga sarki
shardasu, yarima kinzaru da sarkin
yaƙi hatyal, Waɗansu irin girɗa -
girɗan dakaru na take musu baya,
Bisa tsakiyar dakarun mahaifan su
hilwas me maza da mata sanye cikin
sararin baƙin ƙarfe hannu da ƙafa,
Koda ganin hakan sai su hilwas
suka ja linzamin dawakan su suka
sauko ƙasa, Suka durfafi in da su
sarki shardasu suke domin tarar
juna, Sa'adda sarki shardasu yarima
da sarkin yaƙi suka yi arba da
jaruma Husnat sai hantar cikin su ta
kaɗa da karfi tsoro ya ka masu.
HAUSABOOK.COM
93
Sarki shardasu ya tambayi kansa a
cikin ran sa shin wace ce wannan
bakuwar jaruma?
Shin ya akayi halarar tsafi na bata
bayyana mini ita ba a lokacin da na
gudanar da bincike akan su hilwas
ɗin,
Amsar tambayar da sarki shardasu
ya kasa bawa kanshi kenan, Amma
saboda kada yarima da sarkin yaƙi
su fahimci wani abu sai
Kawai ya shiga sakar wa su hilwas
murmushi mai taushi,
Amma har a lokacin zuciyar shi
bugawa take da karfi tamkar zata
faso cikin kirjin shi ta fito waje,
Abin da bai sani ba shine kamar
yadda ya kamu da tsoron haka
yarima da sarkin yaƙi su ka kamu
dashi,
HAUSABOOK.COM
94
Yayin da ya zamana an iso daf da
juna sai sarki shardasu ya dubi su
hilwas cikin annurin fuska tamkar
wanda aka bawa SARAUTAR
DUNIYA ya buɗi baki yace "lale
marhaban da zuwan JARUMAN
DUNIYA sai a yau ne na tabbatar da
cewa kun cika MAZAJENI DUNIYA
kuma GWARAZAN JIYA da babu
kamar ku a wannan KARSHEN
ƘARNI,
yaku waɗannan jarumai kuyi sani
cewa a yau ne zan cika muku
alqawarin da na ɗaukar muku na
baku yanci da mahaifan ku daga
KANGIN BAUTA a karkashin iko na,
Don haka yanzu sai ku danƙamin
sandar sihiri da ƙoƙon kan boka
Mannaf,
Koda jin wannan batu daga bakin
sarki shardasu sai hilwas ya
murtuke fuska tamkar an aiko masa
da wasikar mutuwa ya dubi Sarki
HAUSABOOK.COM
95
yace " ya shugabana ni da yan uwa
mun amince zamu damƙa maka
abubuwan da ka buƙata amma bisa
sharaɗin cewa bazaki yaudare mu
ba,
Idan kuwa har ka saɓa alkawarin
zamu bar ka tare da wannan jaruma
ta yanke maka hukunci dai dai laifin
da ka aikata,
Kuma sai mun rushe mulkin
zaluncin ka daga doran ƙasa,
Koda jin hakan sai sarki shardasu
yace na amince da sharaɗin ku,
Da jin haka sai hilwas ya ciro sandar
sihirin boka kimraz tare da ƙoƙon
kan boka Mannaf ya miƙa wa sarki
shardasu ya sa hannu ya karɓa
zuciyar cike da matukar farin ciki,
Kawai sai ya nuna dakarun dake
bayan sa da ɗan yatsan shi na hagu
take su ka ɓace ɓat kuma sasarin
HAUSABOOK.COM
96
ɗaya daure mahaifan su hilwas ya
ɓace a daga jikin su,
Cikin matukar farin ciki maral
misaltuwa hilwas, Kahzib da
Sharwas, suka ruga izuwa in da
mahaifan su suke domin tarar juna.
Yayin da ya rage saura kamar taku
goma sha biyu a tsakanin su sai
sarki shardasu ya yi nuni da hannun
sa izuwa wajen take wata ƙarama ta
tafasasshiyar darma ta bayyana a
tsakanin su ta yadda babu damar su
haɗu da juna,
Sannan sarki shardasu ya ɗauki
ƙoƙon kan boka Mannaf ya sanya
kansa take ya ya zauna a kan
tamkar ya saka hular ƙarfe.
Ya riƙe sandar sihirin a hannun sa
gami da bushewa da dariyar
mugunta, Yarima kinzaru da sarkin
yaƙi su ka yi koyi dashi,
HAUSABOOK.COM
97
Daga bisani ya murtuke fuska
tamkar an aiko masa da wasikar
mutuwa ya dubi su hilwas a lokacin
da hawayen takaici ke zuba daga
idanuwan su,
"Haƙika yaro man kaza ne bai san
wuta ba sai ta nar ka shi, kuma
tabbatar duk tsuntsun da ya ja ruwa
shi ruwa kan doka,
Yanzu kuna tsammanin cewa zan
barku a raye ne,
Ku sani cewa a halin ku da mahaifan
ku baku da wani amfani a waje na,
Yanzu batare da ɓata lokaci zan
hallaka waccan jarumar da kuke
takama da ita,
Koda Gama faɗin hakan sai sarki
shardasu ya daga sandar sihiri
izuwa sama ya kwarara wawan ihu
sannan ya falfala da azababban
gudu izuwa kan jaruma Husnat,
HAUSABOOK.COM
98
Koda ganin hakan sai bawa hilwas
ya riga izuwa kan yarima kinzaru,
Kahzib da Sharwas kuwa suka tari
sarkin yaƙi hatyal, rike da makaman
su,
Lokacin da aka haɗu da juna sai aka
ruguntsume da azababban yaƙi mai
matukar kwarjini daban sha'awa.
Ɓangarorin uku suka wanzu suna
kaiwa juna sara da suka cikin
matuƙar zafin nama juriya da
bajinta tagaban kwatance,
Wohoho haƙiƙa masu iya magana
sunyi gaskiya da suka ce idan gwani
da gwani suka haɗu a yaƙi juriya da
bajinta suka game waje guda dola
ne yaƙi ya zamo tashin hankali
daban tsoro.
Sai da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya
cur ana wannan artabu,
Tabbas a wannan rana Allah ya
nuna ikon sa domin Husnat ta samu
HAUSABOOK.COM
99
nasarar hallaka sarki shardasu ta
hanyar karya masa waya,
Amma ita ma tasha matuƙar
wahalar gaske,
Hilwas da Kahzib suma sun kashe
abokan gabar su,
Amma sai da Husnat ta kai musu
ɗauki bisa taimakon Ubangiji,
Tabbas inda ace mutum yana tsaye
a wannan waje zai ga yadda gawar
sarki shardasu ke kawance a ƙasa
cikin ƙaskanci da wulakanci dole ne
ya gode wa Allah bisa ganin yadda
ya kawo KARSHEN ZALUNCI da
azzalumai.
Koda samun wannan gagarumar
nasara sai wannan ƙorama da ta
raba tsakanin su hilwas da
mahaifan su ta ɓace ɓat tamkar bata
taɓa wanzuwa ba.
HAUSABOOK.COM
100
A sannanne su hilwas suka ruga
izuwa inda mahaifan su suke suka
rungume juna suna masu zubar da
hawayen farin cikin. Al'amarin da ya
sanya Husnat dake tsaye a gefe
guda ta kamu da matukar tausayin
su kenan har kwalla ta zubo mata,
Daga can sai ta taka da kafafun ta
har zuwa inda suke ta durƙusa kasa
bisa gwiwar ta ta dube su cikin
tausaya tace "yaku waɗannan
jarumai kuyi sani cewa a yanzu ne
zan cika alkawarin da na ɗaukar
muku na warkar da mahaifan ku
bisa taimakon Ubangiji na,
Koda Gama faɗin hakan sai Husnat
ta fito salkar ruwan ta ta kofa
ayatul-kursiyyu da falaƙi da nasi,
Ta umarci mahaifan su Kahzib maza
su shanye ruwan. Haƙiƙa tsarki ya
tabbata ga Ubangiji maɗaukakin
sarki,
HAUSABOOK.COM
101
Faruwar hakan ke da wuya sai
idanun mahaifin hilwas suka buɗe
garau yana iya ganin komai,
Mahaifin kahzib kuwa bakin ya buɗe
ya dawo yana iya magana tar-tar.
Sharwas kuwa duk kuturtar dake
jikin mahaifin shi ya warke jikin sa
yayi kyau sumul,
Batare da bata lokaci ba su hilwas
da mahaifan su suka karɓi kalmar
shahada a wajen Husnat Sannan
aka dunguma izuwa cikin birnin
Baitul-na'im aka musuluntar da
kowa dama sun gaji da mulkin sarki
shardasu,
Bayin dake kurku kuwa aka fito
dasu aka basu yanci. Nan fa gari ya
kaure da shewa da murna,
Kashe gari tun da duku-dukun
safiya aka shiga shagalin nadin
sarautar bawa hilwas a matsayin
sabon sarkin birnin Baitul-
HAUSABOOK.COM
102
na'im,tare da auren sa da gimbiya
lashmira,
Kahzib a matsayin waziri, hilwas a
matsayin sarkin yaƙi tare da daura
auren su, Kahzib da gimbiya
shuraima yar sarki Husubul-Dinar,
Sharwas da jaruma Husnat, daga
wannan rana aka rushe KANGIN
BAUTA kowa ya samu 'yanci gaba
ɗaya jama'ar birnin suka kasance
cikin matukar farin ciki maral
misaltuwa,
Hasken musulmi ya mamaye ko ina
a nahiyar baki ɗaya
Alhamdulillah
Ƙarshe
Daga mai ɗebe muku kewa a kullum
da ko yaushe MANSUR USMAN SUFI
Sarkin marubutan Yaƙi
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels