domin
komawa wajen zamansu suna
gaisawa da masoyansu Wasu kuma
na ɗaga musu hannu,
har suka isa in da kujerunsu suke
suka sake zama, zuciyoyinsu cike da
farin cikin farin ciki Maral
Bayan komai ya samu dai daita sai
kuma tsala tsalan Isalan mutanan
kuyangi suka shigo fadar dauke da
farin ciki da nau'ikan kayan abinci
mai rai da lafiya.
HAUSABOOK.COM
38
nau'i daban-daban Wadansu na
dauke da tulunan giya,
Nan take aka shiga hidimar ciye ciye
da tanɗe-tanɗe,
wani abu da zai bawa mutum
mamaki kuma ya, daure masa kai
shi ne duk tarin tsananin yawan
jama'ar da suka halarci bikin sai da
suka yi wadata da abıncı da abin
sha har suka bar shi,
sannan taro ya watse kowa yayi
kama gabansa, baki suka koma
masaukinsu
kahzib, Hilwas da Sharwas na zaune
a cikin turakarsu suna hira a
tsakanınsu domin debewa juna
ƙewa.
A cikin hirar ta su ne Sharwas ya
dube su fuskarsa cike da tsananin
damuwa ya ce "Ya 'yan uwana ku yi
sani cewa wannan farin cıkı da
muke a yanzu,
HAUSABOOK.COM
39
kawai ina nuna shine ba dan
zuciyata tana so ba, ta wata fuskar
ma wannan farın cıkin ba shi da
wani amfanı.
Cike ma maganar mamakI Hilwas ya
dubi Sharwas cikin murmushi ya ce,
"Ya abokina shin ina dalilin wannan
furici naka?"
Sharwas ya sake haɗe rai ya ce,
"Sanın kanku ne ke cewa
mahaifanmu na raye kuma mun
rabu da su tun muna yara kanana,
to ina amfanin farın cikın mu tunda
ba mu san halin da suke cikı ba.
Ko da jin wannan batun daga bakın
Sharwas sai hankalın Hilwas da
Kahzıb ya dugunzuma ainun har
kwallar takaici a zubo masu Hilwas
ya buɗi baki da ƙyar fuskarshi cike
da damuwa ya ce,
"Haƙiƙa abokina ka sosa mini in da
yake yi min Kaikayı.
HAUSABOOK.COM
40
ka sani cewa a yau yau kafin
wayewar gari sai mun gano in da
mahaifan mu suke mun gana da su.
Hakika mahaifa sune ginshiƙin
rayuwar dukkannin wani ɗa na gari.
Sa'adda Hilwas ya zo nan a
zancensa sai ya fashe da kuka,
al'amarin da ya narkar da zuciyar
Kahzib da Sharwas ke nan suma
suka fashe da kukan,
Sai da suka shafe tsawon lokaci a
cikin wannan hali sannan Hilwas ya
share hawayen da ke fuskarsa ya
mike tsaye zumbur ya fice daga
cikın turakar Kahzib da Sharwas na
bıye da shi.
Da ya ke lokacı ne na dare sai suka
huce kai tsaye izuwa kurkukun
kasar,
Duk in da suka huce sai dai ka ga
kuyangi da bayı nayi musu musujina
gamı da miƙa gaisuwa.
HAUSABOOK.COM
41
Su kuwa ko kallonsu baa yi suna
masu fice daga gidan sarautar,
Tafiyar daƙiƙa hamsin kacal suka yi
suka iso kofar kurkukun wadda ta
kasance murtukekiya da aka yi ta da
zunzurutun bakın karfe,
duk in da mutum ya kalla a sama da
ƙasan kofar tarin muggan dakaru ne
shırye cikın shigar yakı.
Hannayensu suna rike da miyagun
makamai sai mazurai suke yi suna
kai komo kamar za su ci babu,
haƙiƙa komai dakewar zuciyar
jarumi da rashin tsoronsa idan ya yi
arba da dakarun dole ne ya firgice
saboda kwarjininsu. Koda shugaban
da ke kula da kofar wani garjejen
basamuden kato ya hango su Hilwas
sai ya tako da katafunsa ya tare su
ya risına a gare su cikin
girmamawa.
HAUSABOOK.COM
42
Hilwas ya dubi basamuden ya ce,
"Ya kai Zamaru ka yi sani cewa ba
komai ne ya kawo mu nan ba sai
domin ka sanar da mu shin ina ne
mahaifanmu suke.
''Da jin wannan tambaya sai idanun
Zamaru suka zazzaro ya dubi Hilwas
cikin alamun tsananin tsoro ya ce,
"Ya shugabana na roƙe ka da ka yi
min rai. ka sani cewa ba zan iya
sanar da kai in da sarki Shardasu ya
boye mahaifanku ba, domin ina ina
tsoron ka da ya halakar da ni
Sa'adda Hilwas ya ji wannan batun
sai ya fusata ainun har idanunsa
suka kaɗa suka yi jawur,
ya dakawa Zamaru tsawa wacce ta
sanya hantar cikin Zamaru ta kaɗa,
ya dube sa ya ce "Na rantse da
rayuwar mahaifan mu idan ba ka
sanar da mu in da aka ajıye
mahaifanmu ba sai mun yi maka
kısa mafi muni ka bƙkunci barzahu.
HAUSABOOK.COM
43
Nan fa hankalin Zamaru ya
dugunzuma ainun ya rasa abin da
yake yı masa dadɗiA.
Abuna farko da ya faɗo masa a rai
shi ne, shin yanzu idan ya sanar da
su Hilwas in da aka ajıye
mahaifansu yana da tabbacın cewa
sarkı Shardasu ba zai gane cewa shi
ne ya sanar da su ba.
Sannan abu na biyu shi ne tabbas
idan bai sanar da Hilwas abin da ya
ke bukata ba zai rasa rayuwarsa a
yanzu take, Wannan fa shi ne masu
iya magana kan cewa gaba tsini
baya siyaki.
Wata zuciyar kuma ta ce da shı
koma dai dai zai zai faru gwara ka
sanar da Hilwas abin da ya bukata.
Domin ka TSIRA DA RAYUWAr ka a
yanzu. Koda barde Zamaru ya zo
nan a tunanin sa sai ya dubi Hilwas
da turɓunanniyar fuskarsa kai ka ce
murmushi bai taba wanzuwa a
HAUSABOOK.COM
44
kanta ba. Ya buɗe tafkeken bakınsa
wanda ya fi kama da kofar gari ya
ce, "Ya shugabana sarkı ya ajiye
mahaifan ku maza ne a can Wani
gida na musanman,
bayan ɗauke su daga kurkuku,
domin ka da ku yi yunƙurin zuwa in
da suke.
Shi dai gidan ya kasance a cikin
kasa, wanda i dan har aka shigar da
mutum baya taɓa fitowa face dai
mutuwarsa.
Gidan ya kasance a can ƙarshen
gidan sarauta. Mahaifan ku mata
masu suna a zaune a gidan horar da
mata sana'o'i domin samar wa da
sarkı dukiya mai tarin yawa, Ko da
jin wannan bayani daga bakin barde
Zamaru sai bawa Hilwas, Kahzib da
Sharwas suka ji sun kamu da
sananın tausayin mahaifansu bisa
jin matsanancin halin KANGIN
BAUTA da suke ciki".
HAUSABOOK.COM
45
Ba tare da ɓata lokaci ba Hilwas ya
umarci barde Zamaru ya kawo musu
ingarmun dawakai,
sannan suka kama musu linzami,
suna masu tsala azababban gudu
Kai tsaye gidan karkashin kasa suka
nufa da ke karkashın gidan sarauta
domin su fara saduwa da
mahaifansu maza, Tafiyar rabuwa
sa'a da daƙiƙa hamsin kaɗai suka yi
suka iso ɓangaren tun kafin su
karaso bakin kofar wajen suka fara
fafata yaƙi da dakarun da ke tsaro.
Lokacin da suka iso bakin kofar
kuwa sai suka cika da matukar
mamaki,
Abin da ya ba su mamakin kuwa shi
ne duk da irin yadda sararin
samaniya ta mamaye da duhu,
Amma ko ina a wajen haskake yake
da wani haske na musamman
wanda in da allura za ta faɗi a kasa
HAUSABOOK.COM
46
da zarar mutum ya duba zai ganta
Kai da gani ka san aiki ne na sihiri.
Dakarun da ke wajen kuwa sun
kasance ababan tsoro saboda
kwarjininsu sai ka rantse ka ce ba
su kasance bil'adama ba, tsananin
yawansu kuwa ya huce musali.
Yayin da suka bayyana suka yı arba
da su Hilwas sai suka zare
makamansu suka tare su aka
kacame da KAZAMIN GUMURZU mai
matuƙar muni, ban tsoro da ban
al'ajabi.
Ana fa wannan gumurzu ne dakarun
suka gane shayi ruwa ne ba abinci
mai nauyı ba, yawansu ya zamto
banza,
domin duk in da su Hilwas suka
sanya gaba sai dai ka ga
gawarwakin su na zubewa kasa, jini
kuwa ya dinga feshi, fantsama yana
malala a kasa.
HAUSABOOK.COM
47
Nan fa ya zamana cewa bangarorin
biyu sun wanzu suna kawai juna
sara da suka cikin matuƙar zafin
nama JURIYA DA BAJINTA ta ban
al'ajabi.
Ana cikin wannan yaki ne wani daga
cikin yanayin ya shammaci bawa
Hilwas ya kawo masa wani
nagartaccen sara da takobinsa
wanda zai canza masa hannu.
cikin bakin zafin nama Hilwas ya
sanya takobinsa domin ya kare
harin amma sai saran badakaren ya
rinjaye shi ya kadɗe takobin Hilwas
ta yo kasa za ta fadi. Kafin
badakaren ya sake wani yunkuri
Hilwas ya dunkule hannun sa ɗaya
ya gabza masa wawan naushi a
fuska,
kuma ya miƙa ɗayan nasa ya cafo
takobinsa saboda tsananin karfin
naushin sai da badakaren ya banke
'yan uwansa dakaru mutum shida,
HAUSABOOK.COM
48
suka zube kasa magashiyan. Tabbas
jarumta da SADAUKANTAKA baiwa
ce daga Allah, dukiya mulki ba sa
bayar da ita face Allah. Kuma duk
wanda Allah ya ba shi jarumta ya
huta.
In da a ce mutum zai ga yadda
Hilwas, Kahzib da Sharwas ke
ragargazar dakarun suna yin
MUGUWAR HALAKA dole ne ya
jinjina musu. Sai da aka shafe sa'a
daya ana fafata baƙin artabu.
sannan kuma Hilwas suka samu
nasarar halakar da dakarun ba ki
ɗaya,
suka kutsa kai izuwa cikin gidan a
nan amma sai suka yi
GWAGWARMAYA da dakaru masu
tarin yawa sannan suka samu shiga
cikin ƙarƙashin ƙasa.
Lokacin da suka shiga sai suka
kama kalle-kalle da dube-dube suna
masu duba dakunan da ke cikı
HAUSABOOK.COM
49
domin su ga in da mahaifansu suke
amina shiru babu labari sai
fursunoni da suke gani maza da
mata,
Da ƙyar da sidin goshi suka gano a
cikin mahaifan nasu suke a cikin
waɗansu kejina na karfe
hannayensu da kafafunsu ɗaure da
sarƙoƙi. Cikın matuƙar farin ciki
maral musaltuwa su Hilwas suka
ruga izuwa in da kejinan suke Koda
ya rage bai fi saura taku uku a
tsakanınsu ba kwatsam ba zato ba
tsammani sar wani wawakeken
rami ya bayyana a gabansu wata
irin gagarumar wuta na ci gangaganga a cikin ramin. Kuma wata irin
kakkausar murya ta kece da dariya
cike cike da matukar fushi da ɓacin
rai Hilwas, Kahzib da Sharwas suka
waiga bayansu domin su ga wanda
yake dariyar.
Ai kuwa koda waigawar tasu sai
suka yı turus.
HAUSABOOK.COM
50
Ba wani suka gani ba face sarkı
Shardasu shirye cikin gagarumar
shigar shigar yarima Kinzaru na
tsaye a ɓarin hannun sa na dama,
sarkın yaƙi Hatyal na tsaye a hagu.
Waɗansu gabza-gabzan samudawan
dakaru na kewaye da su cıkın shigar
yaƙi mai matuƙar kwarjini,
hannayensu rike da muggan
makamai Sai da sarki Shardasu ya yi
dariya ta ishe shi sannan daga
bısani ya murtuke fuska kamar an
aiko masa da WASIKAR MUTUWA,
ya dubi Hilwas, Kahzib da Sharwas
sannan ya buɗi baki cikin kakkausar
murya ya ce, "Ya ku jarumai masu
dauke da KAMBUN JARUMTA ku sani
cewa tun daga lokacin da kuka fice
daga cikin masaukinku har kawo
izuwa nan na ga dukkannin abin da
ya faru gare ku. Ina so ku yi sani
cewa ku da mahaifanku gaba ɗaya
kuna karkashin iko na ne har abada
ɗaya daga cikin ba zai sadu da
mahaifansa ba face ya amince da
HAUSABOOK.COM
51
biya mini wata mahimmiıyar bukata
ta. "Koda gama fadin hakan sai
sarki Shardasu ya yi nuni da hannun
sa na hagu izuwa bangaren bangon
yamma da ke wajen. Yana mai
karanto waɗansu ɗalasiman tsafi,
gama rufe bakinsa ke da wuya sai
hoton mahaifansu Hilwas mata ya
bayyana suna zaune a cikin wani
gida suna aika ce aika ce Duba ɗaya
za ka yi musu ka fahimci cewa suna
cikin damuwa Domin sun rame
matuƙa sun yi baki tufafin da ke
jikinsu ya yi datti sosai duk ya
yayyage, babu wanda zai gansu a
cikin wannan hali face ya kamu da
tsananin tausayinsu Sa'adda Hilwas,
Kahzib da Sharwas suka yi. Arba da
su a sannan ne mahaifin Kahzib da
Sharwas da ke zaune a cikin
wannan kejin suka fara zubar da
hawaye. duk da mahaifin Hilwas
idanuwansa a makance suke baya
gan abin abin da ke faruwa, amma
da ya ji kukan ɗan sa Hilwas da
HAUSABOOK.COM
52
abokanan Rauzil da Hasham sai shi
ma ya fashe da kukan. Sai da suka
shafe wani lokacı a cikin wannan
hali yarima Kinzaru na yi musu
dariyar mugunta. sannan sarki
Shardasu ya sake nuna bangon a
karo na biyu hoton bat! Kuma ya
sanya wani duhu tsakanin su da su
Rauzil ya zamana ba sa iya ganin
'ya'yansu. Sarki Shardasu ya saki
guntun murmushi ga su Hilwas da
har yanzu hawaye ke zuba daga
idanuwan su Sannan bushe da
dariyar mugunta, kana ya murtuke
fuska kamar an aiko masa da
WASIKAR MUTUWA, ya ce, "Ya ku
wadannan ZARATAN MAYAKA
ma'abota karfin damtse ku yi saji
cewa idan har kun ɗaukae mini
Alkawarin da za ku samo mini abin
da nake ji Bukata to zan 'yantaku
tare da iyayenku ba za ku kara
bauta a gare ni ba. Idan kuwa ku ka
bijirewa buƙata ta ku da mahaifan
ku za ku kasance a cikın KANGIN
HAUSABOOK.COM
53
BAUTA har ajali ya riske ku, Yanzu
dai shawara ta rage ga mai shiga
rijiya. Koda jin wannan batun daga
bakın sarki Shardasu sa hankalın
Hilwas, Kahzib da Sharwas ya
dugunzuma ainun, kuma su duka
ukun suka faɗa kogin tunani don
samun mafita. Abin da ya faɗo musu
a rai shi ne shin wace irin bukata ce
za su biyawa sarkı Shardasu? An ya
kuwa ba yaudararsu zai yı ba?
To yanzu kuma idan ba mu amince
mun biya masa bukatarsa ba za mu
ci gaba da zama a cikın kuncin
rayuwa, tare da mahaifanmu?
Amsar tambayoyın da suka kasa
bawa kansu ke nan take hankulansu
suka sake dugunzuma fiye da ko
yaushe. Hilwas ne ya katse shirun
da ya wanzu a tsakanınsu ta hanyar
buɗar bakı ya sanya hannu ya share
hawayen sa sannan ya ce "Mun
amince za mu bıya maka buƙatar
matsawar za ka ba mu FANSAR
RAYUKAN mahaifanmu. Shin mece
HAUSABOOK.COM
54
ce ake buƙatar taka?" Sarkı
Shardasu ya yi murmushi a karo na
biyu ya ce, "Abın da kawai nake
buƙata shi ne za ku tafi izuwa gidan
boka Kimraz domin ɗauko mini
SANDAR SARAUTAR shi Kafin ku isa
gidan za ku tarar da miyagun
dazuzzuka guda huɗu masu matukar
haɗari. Daji na farko ya kasance
mallakin wani gawurtaccen
matsafin dodo da ake yi masa masa
laƙabi da suna Zamzaru. Dodo
Zamzaru ya kasance gwarzon
mayaki, kaifi da tsini ba ya tasiri a
kansa, A wannan ƙarni ba ki ɗaya,
domin saboda hatsabibancinsa ne
ya zamana sarakunan da ke
makwabtaka da dajin suka yi kaura
suka bar yanayin. Kuma an ce shi
kadai ne yake rayuwa a dajin. Daji
na biyu ya kasance na waɗansu irin
tsuntsaye ne masu kama da
tsuntsun batoyi, babu wani nau'in
makami da yake tasiri a kansu face
tsagwaran KARFIN DAMTSE da
HAUSABOOK.COM
55
basirar mutum. Masana da bokaye
sun tabbatar da cewa adadin
tsuntsayen ba zai kidayu ba, Domin
kullum kara yawa suke yi. Daji na
uku na waɗansu fatalwoyi ne na
haske, mutum ba zai taba samun
nasara a kansu ba face ya kashe
shugabansu kuma dukkanninsu
suna da kamanni iri daya sak!. Babu
yadda za a yi mutum ya iya gane
wane ne shugabansu. tsakanin zafin
namansu kuwa ba zai musaltu ba
sai dai abin da ido ya gani. Na
karshe kuwa ya kasance daji ne na
waɗansu zakunan sihiri da wani
shu'umin boka ya ƙirƙira mai suna
Sultan ibn Hammar. Bayan kun
samu nasara shiga gidan boka
Kimraz kun dauko mını sandar
tsafinsa sai kuma ku huce izuwa
wanı daji da ke ıyaka da gidan ku
ɗauko mini ƙoƙon kan boka Mannaf
da ke ajiye a cikin wata tsohuwar
rijiya dake fadar Sarkin bokaye na
duniya, Sa'adda sarki Shardasu yazo
HAUSABOOK.COM
56
nan a zancen sa sai hankalinsu
Hilwas ya dugunzuma ainun,
Sharwas dubi sarki ya ce, "Ya
shugabana a wace nahiya
dazuzzukan suke?" Sarki ya ce, "Me
ku ke ci ne na baka na zuba? Ai zan
haɗa ku ne da wani hadimin aljanina
ya yi muku jagora." Koda gama
fadin haka sai sarki Shardasu ya
rintse idanunsa ya kırawo sunan
aljaninsa, wata irin kakkarfar iska
ta mamaye wurin wacce ta haddasa
gashin kansu bawa Hilwas da
rigunan jikinsu kaɗawa. Daga can
sai ga wani narkeken aljani ya
bayyana tsum! Tamkar an jefoshi
daga sararin samaniya. Aljanin ya
kasance mai matuƙar tsaho, muni,
girma gami da kwarjini. Domin duk
dakewar zuciya irin ta su jarumi
Hilwas sai suka firgita da ganin
aljanın Shi kansa sarkin yaki Hatyal
da yarima Kinzaru sun razana
matuka. sarki Shardasu ne kadai bai
tsorata ba. Aljanin ya faɗi ƙasa ya
HAUSABOOK.COM
57
kwashi gaisuwa ga sarki Shardasu.
Sarki ya dube sa ya ce, "Ya kai
Kubuzul Haiman ka yi sani cewa ban
kirawo ka nan ba sai domin ina sai
ka yiwa waɗannan jarumai rakıya
izuwa dajin Darul Hashawar.
Wannan shi ne abin da nake
bukata."
Koda jin wannan batun sai aljani
Kubuzul Haiman ya risina ya ce, "An
gama ya shugabana. Ba tare da
wani ɓata lokaci ba Hukubul Haiman
rankwafa gadon bayansa bawa
Hilwas, Sharwas da Kahzib suka hau
kan kansu suka zauna tare da
dawakansu sannan Kubuzul Haiman
ya yunkura ya tashi izuwa sararin
samaniya.
Kafin kiftawar ido ya ɓace ɓat a
cikin gajimare, nan take sarki
Shardasu, yarima Kinzaru da sarkin
yaki Hatyal suka bushe da dariyar
mugunta.
HAUSABOOK.COM
58
Wannan shi ne dalilin barowar
jarumi Hilwas, Sharwas da Kahzib
daga birninsu na Baitul Na'im,
domin su ɗaukowa sarki Shardasu
sandar sihiri da kokon kan boka
Mannal.
SHIN WADANNE IRIN MIYAGUN
MUSIBU SU HILWAS ZASU
FUSKANTA A WANNAN TAFIYA TASU
SUNA SAMUN NASARAR KETARE
MIYAGUN DAZUZZUKA HUDU HAR
SU ISA GIDAN BOKA KIMRAZ?
KUMA SUNA SAMUN NASARAR
DAUKOWA SARKI SHARDASU
SANDAR TSAFI DA KOKON KAN
BOKA MANNAF DOMIN FANSAR
RAYUKAN MAHAIFANSU?
SHIN YA SHURAIMA 'YAR SARKI
HUSUBUL DINAR DA GIMBIYA
LASHMIRA ZA SU KASANCE NA
KEWAR MASOYANSU HILWAS DA
KAHZIB?
HAUSABOOK.COM
59
TSAKANIN YARIMA KINZARU DA
GIMBIYA LASHMIRA WAYE ZAI GAJI
KARAGAR MULKIN SARKI
SHARDASU?
INA LABARIN SARKI BARSUS,
Sarkin marubutan yaƙi ANSAB DA
SARKI HULBARU DA KOWANNENSU
YA SHIRYAWA SARKI SHARDASU
BAKIN TUGGU DOMIN RABA SHI DA
KARAGAR MULKINSA, AMMA YA
TSIRA DAGA SHARRINSU?
SHIN A WANE HALI MAHAIFANSU
JARUMI HILWAS YA ZA SU KASANCE
NA RABUWA DA 'YA'YANSU?
Mu hadu a 10 KANGIN BAUTA domin
jin ci gaban wannan labarin
nayataccen labari.
Lokacin da su jarumi Hilwas suka yi
cirko cirko a kofar shiga gidan boka
kimraz Cike da matukar damuwa
bisa halin KANGIN BAUTA da suka
baro mahaifin su a ciki. Sai suka
shafe tsawon daƙiƙa arba'in Batare
HAUSABOOK.COM
60
da ɗayan su yace uffan ba. Ana cikin
wannan hali ne kwatsam bazato
babu tsammani sai suka hango wani
mahayi bisa ingarman doki fari. Ya
rataya wata sharbebiyar takobi a
gadon bayan sa ya durfafo inda
suke gadan gadan. Sai dukkanin su
suka ƙura wa mahayin idanu suna
jiran ƙarasowar sa. Sannu a hankali
mahayin ya ci gaba da kusanto su,
Har yazmana tazarar dake tsakanin
su bata huce taku biyar sannan yaja
linzamin dokin sa ya tsaya cak Yayin
da suka yi arba da mahayin sai suka
cika da matukar mamaki. Abu na
farko da ya basu mamaki shine
yadda mahayin ya yaksance ya
mace ba namiji ba,
Sannan ya akayi ta iya ketare
miyagun dazuzzukan dake baya
Wato dajin fatalwoyi na haske, dajin
dodo zamzaru da kuma dajin
zakunan sihiri masu ɗauke da fuka -
fukai ,
HAUSABOOK.COM
61
Wanda su kansu sai da suka sha
bakar wahala sannan suka samu
nasarar ketare dazuzzukan.
Amsar tambayoyin da suka kasa
bawa kansu kenan
Shi kuwa Sharwas sam bai ma san
da wannan zancen ba,
Domin tuni ya shagala da kallon
kyakkyawar budurwar, domin
lokacin da ya fara arba da ita sai
yaji zuciyar sa ta buga wa karfi
wani abu ya soki ya soki zuciyarsa a
karo na farko yaji ya kamu da
matukar kaunar ta a zuciyar sa,
Tsawon daƙiƙu ana wannan kallon
kallo tsakanin su Sharwas da
Mahayin,
Sannan daga bisani hilwas yayi
karfin hali yayi gyaran murya ya
dubi budurwar yayi gyaran murya
yace" yake wannan budurwa shin
wace ce ke ?
HAUSABOOK.COM
62
Kuma ya akayi kika ƙetare miyagun
dazuzzukan dake baya har kika iso
nan?.
Sannan mene ne ke tafe da ke izuwa
gar mu.
Sa'adda budurwar taji wannan batu
daga bakin hilwas dai tayi gyaran
murya cikin tattausar murya mai
daɗin sauraro tace" yakai hilwas
ɗan makaho rukaisu kayi sani cewa
da farko dai ni suna na Husnat bintu
abu-husein
Na fito ne daga gabashin duniya a
wani birni da ake yiwa lakabi da
Darul--imfidal,
Game da amsar tambayar ka ta biyu
kuwa shine,
Na samu nasarar ketare dazuzzukan
dake baya ne bisa taimakon
Ubangiji mahalicci,shine wanda ya
halicci duniya da Abin da ke cikin ta,
HAUSABOOK.COM
63
Amsar tambayar ta karshe ita ce
bakomai ne ke tafe dani izuwa gare
ku sai domin na taimaka muku da
izinin Ubangiji na domin ku samu
nasarar abin da kuka fito nema.
Kuma na kuɓutar da mahaifan ku
daga makircin azzalumin sarki
sharadi,
Sa'adda Kahzib, hilwas da Sharwas
suka ji wannan batu daga bakin
Husnat sai suka cika da ɗumbin
al'ajabi da mamaki,
Kahzib yace "yake wannan jaruma
taya ya za ki iya taimaka mana
wajen cimma burin mu bayan cewa
mu ɗin Jarumai ne zamu iya nasara
akan dukkan abinda muka sanya a
gaba,
Sannan naji kin ambaci wani
Ubangiji shin dama akwai wani abin
bauta bayan namu?.
HAUSABOOK.COM
64
Husnat tayi ƙaytaccen murmushi da
ya ƙarawa fuskar ta kwarjini sannan
tace " na yar da cewa tabbas ku
sadaukai ne kuka kuma zaku iya
cimma nasara akan abinda kuka
sanya a gaba
Amma ina so ku sani zan taimaka
muku ne wajen mallakar abin da
kuka fita nema cikin ruwan sanyi
batare kun sha wata wahala ba,
Sannan ina so mu haɗa karfi da
ƙarfe wajen rushe mulkin zalunci na
sarki shardasu domin ku sani cewa
koda mallaka sa abubuwan dake
bukata sai ya ci amanar ku bazai
taɓa baku fansar rayukan mahaifan
ku ba,
Sannan zan roƙi Ubangiji na ya
warkar da lalurar dake samun
iyayen ku,
Amma sai idan kun ɗaukar mini
alkawarin cewa zaki bayar da
gaskiya ga Ubangiji na
HAUSABOOK.COM
65
Sa'adda Sharwas, Kahzib da hilwas
su ka ji wannan batu daga bakin
Husnat sai jikin su yayi sanyi,
Suna masu zurfafa izuwa cikin
Kogin tunani
Daga bisani sai
Sharwas yace "Ɗan bamu Lokaci
zamu tattauna da yan uwa na,
Koda gama faɗin hakan sai shaewas
da yan uwansa suka koma gefe
guda suka yi ƙusƙus a junan su
sannan daga bisani suka dawo
izuwa inda Husnat take,
Hilwas ya dube ta yace" yake
Husnat haƙiƙa mun amince zamu
zamu karbi addinin ki,
Matukar kika cika alkawarin da kika
ɗauka na taimaka mana wajen
mallakar abubuwan da muka fito
nema,
HAUSABOOK.COM
66
Sannan idan har Ubangijin naki ya
warkar da mahaifan mu,
Munyi miki alkawarin cewa zamu
taimaka miki wajen yaɗa addinin ki
a wannan nahiya baki ɗaya,
Koda jin wannan batu daga bakin
hilwas sai jaruma Husnat ta cika da
matukar farin ciki maral misaltuwa,
Kawai sai ta kama linzamin dokin ta
ta sauko ta durfafo ƙofar gidan boka
kimraz
Da isar ta sai kawai ta sanya
hannun ta akan Mabudin kofar tayi
bismillah ta tura ƙofar bisa mamaki
sai gashi ta buɗe
Al'amarin da yayi matukar bawa su
hilwas mamaki kenan kuma ya
ɗaure musu kai,
Domin dai ko da a tarihi basu taɓa
ganin jarumin da yayi wannan bajin
ta ba.
HAUSABOOK.COM
67
Domin kofar tana da kaurin gaske
wacce in da za'a sanya karti majiya
karfi mutun sattin ba za su iya ture
ta ba,
Batare da fargabar komai ba,
Husnat ta zare sharbebiyar takobin
dake gadon bayan ta ta kunna kai
izuwa cikin gidan tana mai yafito su
hilwas da hannunta tana nuna su
biyo bayan ta,
Batare da gardamar komai ba
hilwas ya zare takobin sa ya bi
bayan ta da sauri,
Kahzib na rike da mashin sa mai
baki biyu,
Sharwas na rike da kwari da bakan
sa suka shige izuwa cikin gidan,
Wannan shi ne abinda ya faru da su
bawa Hilwas akan hanyar ta zuwa
gidan boka kimraz domin ɗauko wa
sarki shardasu sandar sihiri.
HAUSABOOK.COM
68
Acan birnin baitul-na'im kuwa
al'amarin gimbiya lshamira da
gimbiya shuraima yar sarki
Husubul-Dinar kuwa,
Tun sa'adda suka ji abinda ya da
yafaru da masoyan su wato bawa
Kahzib da hilwas,
Sai suka kasance cikin tsanin
damuwa yana zamana cewa sun
kamu da rashin lafiya domin ko
abinci basa iya ci,
Koda sarki Husubul-Dinar yaga abin
da ya samu yar sa sai ya yanke
shawarar ya tafi izuwa Birnin sa
domin yi mata magani,
Amma sai sarki shardasu yace yayi
hakuri har zuwa lokacin da zasu
samu lafiya ayi musu magani tare
da gimbiya,
Al'amarin mahaifan su Kahzib maza
da mata a cikin kurkuku kuwa sun
kasance cikin kinci da damuwa dare
HAUSABOOK.COM
69
da rana bisa tunanin halin da ya'yan
su ke ciki.
Suka ji sun tsani sarki shardasu fiye
da komai a rayuwar su .
Wannan shi ne abin da yafaru da su
gimbiya lshamira da mahaifan su
Kahzib.
Mu haɗu a KANGIN BAUTA Littafi na
11 domin jin cigaban wannan
kasaitaccen labari.
Daga mai ɗebe muku kewa a kullum
da ko yaushe
Lokacin da su jaruma Husnat dasu
bawa Hilwas suka shiga izuwa gidan
boka kimraz,
Sai suka tsinci kansu a wani
makeken fili mai tarin rairayi,
Sai suka ci gaba da tafiya Husnat
tana mai dawo bayan su,
HAUSABOOK.COM
70
Saboda ta lura yadda Sharwas ke
satar kallon ta a fakai ce,
Yayin da taga hakan sai ta dube sa
ta sakar masa tattausar murya a
lokacin da ya waigo ya haɗa idanu
da ita ɗin.
Koda yaga irin murmushin da
Husnat ke yi masa sai yaji zuciyar
sa ta buga da karfi,
Kawai ya mayar da duban sa zuwa
kan hanya yana mai tambayar kansa
a cikin ran sa yana mai cewa shin
Mene ne ma'anar wannan murmushi
da Husnat tayi mini shin ko ita ma
ta kamu da soyayyata ne.
Amsar tambayar da Sharwas ya
kasa bawa kansa kenan.
Haka dai aka cigaba da tafiya sai da
aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana
tafiya batare da an haɗu da wani
abu mai cutar wa ba,
HAUSABOOK.COM
71
Ana cikin wannan hali ne kwatsam
bazato babu tsammani sai aka ga
waɗansu irin dakaru na taso wa
daga cikin rairayin tamkar yadda
danshi ke tsattsafowa daga cikin
ƙasa,
Dakarun sun kasance girɗa-girda
tamkar samudawan farko suna
dauke da siffa guda biyu,
Tsagin jikin su na dama na karfe ne
tsagin hagun kuwa na na haske ne
Suna dauke da miyagun makamai
masu barazana ga rayuwar
bil'adama,
Suna dauke da idanuwa jajur kwaya
ɗaya jal a tsakiyar goshin su,
Hancin su da bakunan su irin na
gwaggwan biri ne,
Haƙiƙa waɗannan dabaru sun
kasance munana kuma ababan
tsoro,
HAUSABOOK.COM
72
Babu wata halitta mai numfashi
walau mutum ko aljan da zayi arba
da miyagun dakarun face tayi
nadamar wanzuwar ta a doran ƙasa,
Sa'adda su jarumi Hilwas sukayi
arba da dakarun sai suka ɗimauce,
Tamkar ace kyat su zura da
gudu,amma saboda juriya irin ta
zaratan Jarumai sai suka dake,
Jaruma husnat ce kaɗai bata razana
ba ita ma saboda tana karanta
sunayen Ubangiji tsarkaka ne a
cikin ran ta yasa hakan,
Yayin da dakarun suka kammala
yiwa su hilwas ƙawanya sai aka fara
kallon-kallo tsakanin su,
Daga can sai dakarun su ka zare
makaman su suka yi ihu da
kururuwa mai firgitar wa suka ruga
izuwa kan su.
HAUSABOOK.COM
73
Ko da ganin hakan sai jaruma
Husnat ta zare takobin ta ta kwala
kabbara da karfi ta ruga izuwa kan
dakarun,
Sharwas, Kahzib da hilwas sukayi
koyi da ita ta hanyar zare makaman
su,
Lokacin da aka haɗu sai aka
ruguntsume da azababban yaƙi mai
matukar kwarjini muni daban tsaro,
Kowa ne ɓangare su ka wanzu suna
kaiwa juna miyagun hare hare cikin
matuƙar zafin nama juriya da
bajinta tagaban kwatance,
Wohoho ana fara wannan artabu ne
wani abun mamaki ya fara guda
domin kuwa duk irin zafin nama na
su jarumi Hilwas yazama abanza,
Domin kuwa duk sa'adda suka sari
jikkunnan dakarun da makaman su
sai suji tamkar dutse suka sara
domin wani irin tartsatsin wuta ne
HAUSABOOK.COM
74
yake tashi gami da kara marar daɗin
sauraro.
Al'amarin da yayi matukar
dugunzuma hankalin su kenan suka
fahimci cewa idan aka Cigaba da
wannan artabu a haka dakarun zasu
iya samun nasarar hallaka su.
Abangaren jaruma Husnat kuwa
tuni labari yasha bambam,
Domin kuwa Husnat ta zamo
gagarabadau a tsakiyar dakarun,
Duk in da ta sanya a gaba sai dai
kaga dakarun na zubewa ƙasa
matattu tamkar tana sassabe a
gonar auduga.
Tabbas jarumtaka baiwa ce daga
Ubangijin halitta ba'a siyan ta kuɗi
ko mulki,
Komai hassadar Mutum idan ya ga
Yadda Husnat ke ragargazar
dakarun doka ne ya jinjina mata ya
HAUSABOOK.COM
75
tabbatar dacewa ta cika mace mai
kamar maza kuma jarumar Asali,
Nanfa ƙarar karafniyar ƙarafa,ihun
mazaje haɗe da kururuwar dakaru
ta cika dodon kunne,
Sassan jikkunnan dakarun suka
dinga shawagi a sararin samaniya
suna zubowa ƙasa tamkar ana
ruwan su ne daga saman,
Jini kuwa ya dinga kwaranya,
tsartuwa gami da feshi yana zubar a
ƙasa tamkar an balle Teku,
Sai da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya
ana wannan fafatawa babu
sassauci,
A sannanne dakarun suka fahimci
cewa Husnat tayi musu muguwar
barna.
Domin ta kashe fiye da rabin su,
Nan fa hankalin su ya dugunzuma
ainun,kuma suka fusata ainun
HAUSABOOK.COM
76
zukatansu suka dunga tafarfasa
tamkar zasu kone,
Kawai sai suka zage damtse suna
cigaba da kaiwa Husnat hare hare ta
ko ina,
Al'amarin su Bawa hilwas kuwa
sa'adda su ka ga irin gagarumar
bajintar da Husnat ke yi sai suka
cika da matukar mamaki suka ce a
cikin ransa anya kuwa Husnat
bil'adama ce,
Taya ya za'ayi ce zaratan Jarumai
kamar mu mun kasa samun damar
hallaka koda badakare ɗaya amma
Husnat ta kashe fiye da rabin su,
Lokacin da sa'a biyu ta shuɗe ana
wannan fafatawa a dai dai wannan
lokacin ne Husnat ta hallaka ba ki
ɗaya dakarun dake gaban ta, Kuma
ta hango irin mawuyacin halin da su
Bawa hilwas ke ciki,
HAUSABOOK.COM
77
Domin dakarun sun galabaitar dasu
basa iya mayar da martani sai dai
ƙoƙarin kare kansu.
Wasu lokutan idan dakarun suka
kawo musu hari suka kare da
makaman su