An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
HAUSABOOK.COM
1
HAUSABOOK.COM
2
Kangin Bauta
Littafin yaki Rubuta
labari
Mansur Usman Sufi
Kyawawan samari ne majiya karfin
damtse su uku, mai matukar
kwarjini da ban tsoro. Na farkonsu
yana rataye da waɗansu zaratan
takubba guda biyu a gadon
bayanshi kuma ya kasance mai
matuƙar kaurin jiki fiye da 'yan
uwanshi. Saurayi na biyu yana
dauke da wani irin KWARI DA BAKA
mai daukar hankali,jikinsa a murde
yake ya tara kwanji,
kallo daya zakayi masa kafahimci
cewa ya fi sauran yan uwansa kirar
sadaukantaka.
HAUSABOOK.COM
3
Na ukun kuwa yana ɗauke da dauke
da dogon nashi mai baki biyu,
bakin yakasance daga farkon sa
yayi fadi daga karshe yayi tsini ya
fitar da baki biyu.
Babu abin da zai burge ka ga
samarin sama da yadda suka yi
shigar yaƙi iri daya sak,
kuma suna zaune abisa jajayen
dawakai ingarmu.
Samarin uku suna tafiya ne acikin
wani daji ma,abincin dogayen
bishiyoyi,koramu,
tare da kwazazzabai.gaba daya
yanayin dajin ya banbanta da
sauran dazuzzukan da idanuwa
suka saba gani.
Domin hatta kwari da tsuntsayen
dake cikin sa abin tsoro ne.awasu
lokutan sai kaga tsuntsaye na dauke
da fuskokin bil,adama,hatta
HAUSABOOK.COM
4
bishiyoyin dajin suna canza launi
zuwa launi,
Tabbas dajin yana da matukar
kwarjini ga duk jarumin daya tsinci
kansa acikin sa dolane ya razana
Haka dai zaratan samarin uku suka
cigaba da tafiya adajin Babu alamun
razani atattare da fuskokinsu
Lokacin da suka shafe tsawon sa,a
daya da dakika talatin suna tafiya
acikin dajin,a dai dai wannan lokaci
ne suka fara hango wani katafaren
gida kwaya daya jal adajin,
Al,amarin da yayi matukar basu
mamaki kenan suka ce acikin
zukatan su.taya za,ace wannan
kasurgumin daji ace an gina
wannan kerarrran gida a cikinsa.
Amsar tambayoyin da suka kasa
bawa kansu kenan, suka cigaba da
tafiya,
Da isar su bakin gidan suka tarar da
gidan ya kasance tankameme
HAUSABOOK.COM
5
Tamkar gari guda.gaba daya ginin
anyi shine da waɗansu manyan
duwatsun wuta wadanda ido bai
taba gani ba,
Katangun gidan sun kasance masu
tsawon gaske.akwai ƙatuwar kofa
guda daya jal mai tsawo da kauri
inda za,a sanya karti majiya karfi
mutum hamsin bazasu iya ture ta.
Nanfa samarin suka yi cirko-cirko
suna nazarin kofar tsawon dakika
arba,in dayansu bai ce uffan ba.
Daga can sai daya daga cikin su
wanda ake kira da suna Hilwas yayi
gyaran murya yace "yaku 'yan
uwana yanzu mene ne abinyi?
Gashi yanzu mun iso gidan boka
kimraz,naji ajiki na cewa dukkan
baiwar da muke da ita bazata yi
mana wani amfani ba face muyi
Amfani da fasahar da muke da ita."
HAUSABOOK.COM
6
Koda jin wannan batu sai sharwas
yayi caraf ya tari numfashin Hilwasa
yace"Ni shawarar dazan bamu muyi
tunanin hanyar da zamu bude
Wannan kofa,
kunsan masu iya magana na cewa
abari ya huce shi ke kawo rabon
wani, kuma da zafi-zafi a kan daki
karfe."
Duk wannan tattaunawa da akeyi
kahzib yayi shiru bai ce kala ba.
Fuskar sa cike da damuwa,
Kahzib yayi gyaran murya
yace"yaku abokaina nifa ba wannan
abu ne damuwata ba.
shin kun mantane cewa rayuwar
iyayenmu tana hannun sarki
shardasu.
A cikin ku wane yake da tabbacin
sarki shardasu zai cika alkawarin
daya daukar mana idan muka
mallako masa abubuwan da yake
HAUSABOOK.COM
7
buƙata na bamu fansar rayukan
iyayemu.
meyasa baza muyi tunani me yasa
baza muyi tunani akan nemo musu
maganin dazai warkar da lalurar
dake samun su ba?
Sa,adda kahzib ya zo daidai nan
azancen sa sai jikin Hilwasa da
sharwas yayi sanyi.
Kuma hankalinsu ya dugunzuma
ainun suka zurfafa izuwa kogin
tunani,
Su dai wadannan samari sun fito ne
daga Wani birni da akewa lakabi da
BAITUL-NA'IM.
dalilin daya baro dasu daga gida
shine kamar haka:- *
Birnin baitul-na,im yakasance
kasaitaccen birni daya shahara a
fannin noma, kasuwanci.
HAUSABOOK.COM
8
wanda ya haɗar da attajirai da
manoma.kuma suna da ZARATAN
MAYAKA masu juriya a filin daga.
Sarkin da yake rike da Sarautar
wannan birnin ana kiransa da
shardasu ibn furais,
Sarki shardasu yakasance Gwarzon
mayaki mai tarwatsa maza afilin
fama.
mutum ne mai son abin duniya
.dadin dadawa kuma yakasance
AZZALUMI nagaban kwatance.
Domin duk shekara a birnin sa ana
noma abinda bokaye da masu
hasashe suka tabbatar da cewa zai
iya ciyar da kasashen dake nahiyar
na tsawon shekaru biyu amma
saboda zaluncin sa sai dai ya siyar
da abincin ga manyan kasashen da
ke wata nahiyar daban Duk yawan
abin da mutum ya noma zai kasashi
gida Biyar ya dauki daya kaso
hudun na sarki shardasu ne.
HAUSABOOK.COM
9
hatta dabbobi bai kyale ba duk
shekara a kwai kason sa aciki, Sai
da ya Zamo duk faɗin nahiyar babu
attajiri kamarsa.
Mahaifan Waɗannan samari uku sun
kasance bayi ne ga sarki shardasu
asali sarki shardasu ne ya cinye
kasar su da yaki ya ribato su a
matsayin fursunonin yaki.
A tarihin samartakar su ba,a samu
jarumai kamar su ba a can ƙasar su
Mahaifan su sun samu lalurar dake
jikin sune saboda bautar da suke yi
a karkashin sarki shardasu.
Mahaifin Hilwasa ana kiransa da
suna Rukaisu , Rukaisu ya samu
lalurar makantane saboda aikin ƙera
dukkan nau,ikan kayan
yaki,kofuna,da sauransu abubuwan
da ake sana'anta su da zinariya da
jauhari. Tunda Rukaisu yake
Wannan aiki nasa ba,a taba samu ya
HAUSABOOK.COM
10
ƙera wani abu ba yadda sarki ya
buƙata ba amma
saboda wata rana an samu akasi ya
kera wadansu kofuna ba yadda aka
umarta ba ya sanya aka soke masa
idanu da wasu kibiyoyi na wuta
idanunsa suka makance kuma aka
aikashi izuwa kurkuku.
Mahaifin sharwas kuwa ana kiransa
da suna Rauzil ya kamu da ciwon
kuturtane a hannayen sa da
ƙafafuwan sa saboda aikin dafa
sarki shardasu ruwan wanka wata
rana rauzil ya kammala dafawa
sarki ruwan zafi a bahon wanka
bayan ya kammala zuba turaruka da
sabulai masu kanshi,
sai ya umarci wadansu kuyangi da
sukai ruwan izuwa kewaye.
Jim kadan sai ga sarki shardasu ya
fito daga kewayen fuskarsa a
murtuke tamkar an aiko masa da
sakon mutuwa. kawai sai ya damki
HAUSABOOK.COM
11
gashin kan Rauzil yana janshi akasa
har izuwa inda wani ƙaton kasko
yake a turakar sa.
Kaskon yana dauke da wani
tafashasshan ruwan zafi mai kauri
baƙi baƙi.
kawai sai sarki shardasu ya kama
hannayen Rauzil ya tsomasu acikin
kaskon.
Tun Rauzil yana kwarara ihu har
takai bana iyawa sai dai hawaye
kawai yake zuba a idanunsa.lokacin
daya fito da ƙafafuwan take naman
jikinsu ya zagwanye Babu tausayi
afuskar sarki shardasu ya damki
hannayen Rauzil ya motsa akaskon,
Hakika komai rashin imanin mutum
idan yaga yadda Rauzil yake
kwarara ihu yana zubar da hawaye
dolane ya tausaya masa sai da
naman jikin hannayen ya zagwanye
sannan ya yi jifa dashi gefe guda
HAUSABOOK.COM
12
Rauzil na fitar da numfashi samasama tamkar zai sheka barzahu
daga nan aka kaishi izuwa kurkuku
yazamo gurgu baya iya tafiya sai dai
rarrafe
Mahaifin kahzib kuwa ana kiransa
da suna Hashim Shi kuma ya samu
lalurar kurumtane
saboda wani laifi da ya yi wa Sarki
shardasu ya dunga dura masa
garwashin wuta a baki yana
hadiyewa
Matayen su hasham kuwa sai suka
kasance cikin matukar bakin ciki
tare da kewaye mazajen su dare da
rana Bayan shudewar wannan
al,amari ne da kwanaki arba'in sai
sarki shardasu na zaune a fadar sa.
Fadar ta kasance makekiya mai
tsawo da fadi.an kawatata da
dukkan kayan kyale kyalen alatun
jin dadin duniya.
HAUSABOOK.COM
13
Duk inda mutum ya kalla bayi ne da
kuyangi suna ta hidima,
kowacce kusurwa a fadar dakarun
ne atsaitsaye cikin matsananciyar
shigar yaƙi mai matukar kwarjini da
ban tsoro hannayen su rike da
miyagun makamai Domin tabbatar
da cikekken tsaro.
Sarki shardasu Sarki shardasu na
zaune a bisa kan ƙasaitacciyar
karagar mulki da akayi da farin lu,u
lu,u da jauhari.
Ajikinsa yana sanye da yar karamar
rigar Koriya mai gajeran hannu a
hannun sa na hagu yana rike da
wata ƙasaitacciyar sanda irin ta
hamshakan sarakai sanye a kansa
akwai kambun sarauta na zinare.
A ƙafarsa yana sanye da takalmi
baki da aka yi masa ado da nau,ikan
gashin dawisu. A wannan lokacin
ana tafiyar da harkokin mulki cikin
kwanciyar hankali kwatsam sai aka
HAUSABOOK.COM
14
hango Wani badakare ya shigo fadar
yayin da rage tsakaninsa da karagar
mulki bai huce taku goma ba sai
kawai ya zube kasa ya kwashi
gaisuwa.
sannan daga bisani ya dago da
kansa yayi gyaran murya yace"ya
shugabana labari ya riskeni cewa
matayen su hasham sun sauka
lafiya,
kuma dukkanninsu sun haifi yaya
maza, Koda jin wannan batu daga
bakin bawa Durshuf sai fuskar sarki
shardasu ta faɗa ɗa da murmushi
tamkar wanda aka bawa SARAUTAR
DUNIYA
kuma ya mike tsaye tsam daga kan
karagar sa daga bisani ya murtuke
fuska tamkar an aiko masa da sakon
mutuwa ya dubi Bawa Durshuf
yace"ina so kayi mini jagora izuwa
inda matayen suke"
HAUSABOOK.COM
15
Sarki na gama faɗin hakan sai bawa
Durshuf ya shige gaba sarki
shardasu yabi bayansa take dakarun
Sa suka mara masa baya.
Suna fita wajen fadar aka kawo
keken doki sarki Yakamata ya hau
aka cigaba da tafiya.
Tafiyar dakika talatin da hudu, su
badakare Durshuf kadai su kayi
suka iso wani bangare da bayi suke
a cikin Gidan sarautar,
Shi dai wannan bangare akalla yana
dauke da dakuna fiye da talatin
kuma musamman an Gina nasa ne
domin bayi mata masu dauke da
juna biyu. Da isowar su durshuf
Sai wani badakare ya rugo izuwa
inda suke tsaye ya sauke
matattakalar keken dokin take Sarki
shardasu ya taka matattakalar
keken dokin Ya sauko kasa Sannan
badakaren ya zube kasa Ya kwashi
HAUSABOOK.COM
16
gaisuwa cikin ladabi yace"ya mai
duniya ai Sai ku shigo izuwa ciki
Sarki shardasu Ya karewa matayen
kallo da nazarin jariran dake
hannayen su na wani dan lokaci
Sannan daga bisani ya mayar da
dubansa ga shugaban dake kula da
Gidan wani garjejen kato yace dashi
cikin kakkausar murya yakai Larbus
kayi Sani cewa ban zo wannan gida
ba Sai don na baka wani umarni.
Abin da nake bukata shi ne ka kula
da lafiyar wadannan mataye da
jariran su.
Tabbas nan gaba zasu zamo masu
amfani agareni". Koda gama
wannan jawabin Sai Sarki shardasu
Ya juya ya nufi kofar fita daga gidan
dakarun sa na take masa baya.
yana fita ya hau bisa keken dokin
Sa, Ya nufi hanyar da zata mayar
dashi izuwa fada.
HAUSABOOK.COM
17
Tun daga wannan rana matayen su
Hasham suka kasance cikin kulawa
ta musamman.
Amma dai-dai da rana daya basu
taba daina begen masoyan su ba,
Gaskiyar masu iya magana da su
kace sannu-sannu bata hana zuwa
Sai dai adade ba,a je ba Sai gashi
jariran su Hasham sun shekara
goma,
tun a wannan lokaci Sarki shardasu
Ya umarni sarkin yaki Hatyal ya
dauke su ya kaisu izuwa gidan
horan yaki Nan fa yazamo cewa su
sharwas sun kware ainun a fagen
salon yaki iri daban-daban.
A bangaren mahaifan su Hilwas
kuwa tun da aka tafi da Yaya yen su
Sai izuwa gidan horar da mayaka
Sai Ya zama na sun kasance cikin
KANGIN BAUTA Ya zama na duk
wata kulawa da ake basu lokacin da
suka haihu an dai na yi musu ,
HAUSABOOK.COM
18
domin a wasu lokutan dakyar suke
samun abinda zasu ci.
Kasaitacciyar turaka ce da aka
kawata ta da nau'ikan kayan kawa
da alatun jin dadin rayuwar duniya.
Babban abinda ya kara fito da
kyawun turakar shi ne wadansu
fararen kushin na alfarma da aka
kewaye turakar dasu kowacce
kusurwa a turakar an kawata ta da
wasu kawatattun fitulu na azurfa.
idan mai kallo ya yi duba daga
bangaren yamma a turakar bisa
kayatattun kujerun zai yi arba da
wani sadauki zaune shirye cikin
gagarumar shigar yaki Mai matukar
kwarjini da ban tsoro Duba daya
zaka yi masa ka kawar da fuskar ka
saboda tsananin munin sa, A bisa
wata karaga ta alfarma wani mutum
ma,abocin kyawun fuska da
kwarjini, yana sanye da tufafin
sarauta na alfarma sun yi matukar
yi masa kyau kai da gani kasan yana
jin dadin duniya. Shiru ne ya wanzu
HAUSABOOK.COM
19
a tsakanin su Sai Daga bisani ne
Sarki shardasu Ya katse shirun da
ya wanzu ta hanyar budar baki yayi
gyaran murya yace "yakai dirkar
birnin baitul-na,im kayi Sani Sani
cewa ban kirawo ka nan ba Sai
domin na tunasar dakai cewa
lokacin gudanar da GASAR JARUMTA
ya gabato nan da kwana talatin
kacal! Lallai ina so a fara shirye
shiryen wannan gasa. Kasani cewa
awannnan karon akwai manayan
sarakunan nahiyoyi hudu da zasu
halarci wannan Gasa Sannan salon
gasar zai canza izuwa rukuni uku
.wato fadan takobi, Sai kuma na
KWARI DA BAKA da kuma ta
KARFIN DANTSE. Koda Sarki
shardasu Ya zo nan azancensa Sai
Ya zira hannun sa aljihunsa na Riga
ya dauko wata doguwar takarda ya
mikawa sarkin yaki, Cikin biyayya
ya sa hannayen sa ya karba Sannan
ya warware ta yafara karanta
abinda ke kunshe a cikinta. Koda
HAUSABOOK.COM
20
kammala karantawar Sai yaji
zuciyar sa yayi bakikkirin bakomai
ne ya sanya shi cikin wannan hali ba
Sai domin a cikin sunayen jaruman
gasar da aka bashi yaga sunan
yarima kinzaru Wanda tsakanin su
akwai rashin jituwa, Saboda sarkin
yaki yana matukar kaunar kanwarsa
gimbiya lashmira Tsakanin lashmira
da yarima kinzaru akwai rashin
jituwa saboda kowannen su na
kwadayin ya gaji karagar mulki,
Sa,adda Sarki yaki Ya zo dai dai nan
a tunanin sa Sai ya cika da matukar
bakin ciki yana cikin wannan hali ne
Sai ya lura akwai sauran rubutu a
ayan takardar. Cikin matukar farin
ciki ya juya takardar ai kuwa Sai
yayi arba da sunan gimbiya
lashmira,Bawa Hilwas, sharwas da
bawa kahzib, saboda farin ciki bai
San sa,adda murmushi ya subuce
masa ba, yayin da ya hada idanu da
Sarki shardasu sai ya sunkui da
kansa kasa cikin alamun rashin
HAUSABOOK.COM
21
gaskiya Sarki shardasu Ya dubi
sarkin yaki da duban dake nuna
fahimtar wani abu game da
murmushi nasa Sannan yayi gyaran
murya yace
" ya dirkar birnina kayi Sani cewa
inaso ka gaggauta sanar da dukkan
Wanda sunan sa ke kunshe a cikin
wannan takardar jaruman Gasa
kuma a tabbatar da cikekken tsaro
daga yanzu har izuwa bayan gasa
domin wannan gasa ce ta
musamman. Koda gama fadin hakan
sai Sarki shardasu Ya mike tsaye
tsam! daga kan kujerar sa ya taka
da kafafunsa ya nufi wata har
siririyar kofa a turakar.
Yana tafiya cikin kasaita da BAKAR
IZZA! yana isa bakin kofar wadansu
ZARATAN MAYAKA na sihiri suka
bayyana su kimanin arba,in shirye
cikin gagrumar shigar yaki suka
Mara masa ba ya har ya kule izuwa
cikin Gidan sarautar. Hakika Sarki
HAUSABOOK.COM
22
shardasu Ya zurfafa acikin ilimin
tsafi da kamo kafar shi sai mutum
yayi da gaske.
Nan take Sarki yaki Ya mike tsaye
ya fice daga turakar zuciyar sa cike
da tunane - tunane iri - iri.
Sarki Barsus na kwance bisa gado a
cikin masaukinsa sanye da riga
falmaran da dogon wando marar
nauyi irin na hamshakan attajirai,
kawai sai ya ji wani kwankwasa
masa kofar shigowa turakar nan
take ya mike tsaye tsam daga kan
gadon ya je ya bude kofar. Wani
saurayi
kyakykyawa sanye cikin sulken yaki
ya yi ido biyu da shi,
Barsus ya yi guntun murmushi a
gare shi.
Saurayin ya zube kasa ya kwashi
gaisuwa sannan ya budi baki cikin
ladabi ya yi gyaran murya ya ce,
HAUSABOOK.COM
23
"Ya shugabana tuni kyaumu sun iso
tare da shugaban barayin wannan
nahiya, kuma tuni ma sun fara yin
kyau da ayy kyau, domin isa in da
turakar sarki Shardasu da gimbiya
Lashmira take. Koda jin wannan
batun daga bakin saurayin sai sarki
Barsus ya bushe da dariyar
mugunta, a lokaci guda kuma ya
turbune fuska kamar an aiko masa
da WASIKAR MUTUWA.
Cikin kakkausar murya ya ce,
"Tabbas na yarda da kai ya kai
Huzmal ina mai tabbatar maka da
cewa da zarar burina ya cika na
ganin bayan sarki Shardasu da
gimbiya Lashmira a gobe za a yi
nadin sarauta ta tare da yi maka
wazirina,
Koda jin hakan daga bakin sarki
Barsus sai Huzmal ya sake zubewa
kasa ya kwashi gaisuwa,
HAUSABOOK.COM
24
sannan ya tashi ya juya ya ficc daga
cikin turakar zuciyarsa cike da farin
ciki,
koda ficewar Huzmal sai sarki
Barsus ya janyo kofar turakar ya
rufe ta ruf,
ya kashe fitulun da ke ciki, sannan
ya kwanta bisa kan gadonsa domin
ya samu ya huta.
Sa'adda gimbiya Lashmira ta yi arba
da fuskar mahayin sai ta cika abin
mamaki mamaki, ba komai ne ba ya
ba ta mamaki ba sai bisa ganin
gimbiya Shuraima 'yar
sarki Husubul Dinar,
Kallo ne ya wakana tsakanin
gimbiya Lashmira da Shuraima na
dan wani lokaci,
har Lashmira ta budi baki da kyau ta
ce wani abu sai Shuraima ta matso
daf da ita ta rike hannunta ta tashe
ta tsaye,
HAUSABOOK.COM
25
ta yagi wani yanki a tufafinta ta
goge mata jinin da ya zuba a
bakinta suka shirya juna. Sannan
Shuraima ta budi baki cikin
tattausar muryar ta ce,
"Ya Lashmira ina ncman afuwarki
bisa ZUBAR DA JININ da na yi miki
tabbas ban yi hakan domin kaskanta
daraja da martabarki ba sai domin
kare zuciyar ki daga kudurun da ke
tattarc a al'adar.
ki yi sani ccwa na san ba wani abu
ne ya fito da ke a cikin wannan dare
ba fuskantar tsananin soyayyar
bawa Hilwas da ta addabi zuciyarki.
Tabbas, matsalarmu irn daya ce,
domin ni ba komai ne ya fito da ni a
dai-dai wannan lokaci ba sai bisa
kamuwar da zuciyata ta yi da kyau
kaunar bawa Kahzib, irin son da ban
taba yuwa wani da namiji ba,
Saboda haka kinga yanzu
tsakaninmu sai dai mu hada kai
HAUSABOOK.COM
26
domin saduwa da masoyanmu kafin
wayewar gari. Koda jin wannan
doka daga bakin gimbiya Shuraima
sai Lashmira ta saki tattausan
murmushi, a gare ta sannan ta budi
baki cikin annurin fuska ta ce
"Ya ke Shuraima ki yi sani cewa
tabbas na gamsu da dukkan
bayaninki domin na san a cikin
sarakunan da suka halarci GASAR
JARUMTA mahaifin ki ne kadai ba
shi da wani mummunan kudiri a
zuciyarsa a kaina da abbana.
Amma sai dai kafin mi ci gaba da
tafiyar mu ina so ka amsa mini
tashin tambayoyi kamar haka: -
Shin kuna yakinin cewa bawa
Kahzib zai amince da soyayyarki?
Tambaya ta karshe ita ce a ina ki ka
samu irin tufafin da na sanya?
Da jin wannan tambayar sai
Shuraima ta yi murmushi ga
Lashmira sannan ta dube ta ta
HAUSABOOK.COM
27
hanyar gyaran lallausan muryar ta
kawo gwauron nunfashi ta ajiyc ta
ce,
"Game da tambayarka ta farko, ki
yin sani cewa duk da cewa bawa
Kahzib bai furta min cewa yana
kaunata ba tabbas na ga alamun
hakan a kan fuskarsa,
a lokacin da muka hada idanuwa da
shi a filin gasa,
kin san masu iya magana na ccwa
LABARIN ZUCIYA a tambayi
fuska Sannan game da tufafin da na
sanya mai kama da naki kuwa labari
ne mai tsawo,
akwai bukatar mu samu lokaci mu
zauna. Sa'adda Lashmira ta ji amsar
wadannan tambayoyin sai mamaki
ya turnuke ta ta ce a cikin ranta.
"Shin wace alaka ce ke tsakanin
tufafina da na gimbiya Shuraima,
HAUSABOOK.COM
28
Kawai sai ta bar abin a cikin ranta
su ka ci gaba da tafiya suna masu
sakc rufe fuskokinsu da rawanin har
suna hira kamar sun dadec da sanin
junansu har suka iso masaukinsu,
bawa Kahzib ba su hadu da wata
matsala ba, sai da kyar da sidin
goshi suka sadu da masoyansu.
Wato bawa Hilwas da Kahzib kuma
suka samu damar taron a ranar,
ashe su ma da kyau Sun sun kamu
da soyayyarsu.
Kashe gari tunda duku-dukun safiya
fadar sarki Shardasu ta cika ta
batse da jama'a,
duk in da mutum ya kalla kawunan
bil'adama ne rututu babu masaka
tsinke Babu abin da zai bawa
mutum mamaki kuma iya daure
masa kai fuska ganin yadda
sarakunan da suka halarci taron ba
su yi wani jinkirin fitowa ba,
HAUSABOOK.COM
29
da yawa daga cikin jama'a a nan
suka same su.
Ana cikin wannan hali ne sai aka
jiyo bushin algaita hade da bugun
tambura,
alamun sarki Shardasu na kan
hanya.
Kwatsam! Sai aka hango sarki
Shardasu da tawagarsa sun shigo
fadar sarki ne a kan gaba, gimbiya
Lashmira tsaye aɓangaren hagu
yarima Kinzaru a dama dukkansu
sun caba ado mai girma daukar
hankali, dakaru rike da kyau na take
musu baya.
Koda ganinsu sai gaba daya jama'ar
da ke fadar suka mike tsaye domin
girmamawa a gare su,
domin masu iya magana kan ce ba a
sarki biyu a masarauta daya,
sai da sarki da su yarima suka
zauna a wajen da aka tanadar musu
HAUSABOOK.COM
30
sannan kowa ya zauna, fadar ta yi
shiru kamar mutuwa ta kawo
Ziyara.
Aɓangaren da aka tanadarwa
sarakuna kuwa
sa'adda sarki Hukubul Ansab ya yi
arba da tufafin da ke sanye a jikin
sarki Shardasu sai takaici da bakin
ciki suka suka mamaye zuciyar shi
ya ji kamar ya kurma ihu daboda
takaici.
Ba wani abu ya sanya shi hakan ba
face bisa ganin wannan dukkan
kayan sarakunan masarautar daya
sace a dakin masarauta domin ya
samu nasar yiwa sarki Shardasu
JUYIN MASARAUTA sarki Shardasu
na sanye dasu wato alkyabba,
kambu, takalmi da sauransu.
Sarki Hukubul Ansab ya ce a ransa
Shin yanzu duk wahalar da na sha
ta tashi a banza, tabbas sarki
Shardasu ya cika hatsabibi a ilimin
HAUSABOOK.COM
31
tsafi, kuma wannan shi ne masu iya
magana ke cewa kifi na ganiqnka
mai jar koma. Sa'adda sarki
Hukubul Ansab ya zo nan a tashinsa
sai hankalinsa ya dugunzuma ainun
fiye da ko yaushe. Kamar hadin baki
sarakunan da suka gabatar a
bayyane suka mike daga kan
kujerun zamansu suka je suka zube
a gaban sarki Shardasu suka kwashi
gaisuwa,
sarki Shardasu ya karbi gaisuwar
fuskarsa babu yabo babu fallasa.
Duk wanda ya kalla daga cikin
sarakunan sai ya ji hantar tasiri ta
kada, ya sunkui da kansa kasa shi
kuwa sarki Shardasu sai ya yi
guntun murmushi a gare shi,
sarki Husubul Dinar ne kadai bai ji
wani abu a ransa ba har ya mayar
wa da sarki Shardasu martanin
murmushin,
HAUSABOOK.COM
32
Sarakunan suka sake mikewa tsaye
suka koma wajen zamansu suna
yiwa junansu wani irin kallo mai
tattare da kyayyar juna.
Bayan kamar shudewar dakika
talatin sai aka hango su bawa
Hilwas sun shigo fadar dakaru na
dauki musu baya,
su duka ukun shigar korayen tufafi
suka yi farin rawani, farin takalmi.
Shigar da tayi kyau fito da tsantsar
kyawunsu. Koda shigowarSu ya
zauna gaba daya fadar ta ruɗe da
shewa masu tafi da jinjina na yi su
Hilwas na daga musu hannu, sai da
suka zauna a wajen zamansu bayan
sun kwashi gaisuwa ga sarki
Shardasu sannan fadar ta sake yin
shiru A karo na biyu, sarkı Shardasu
ya katse shirun da ya wanzu ta
hanyar miƙewa tsaye ya fuskanci
jama'a Sannan ya yi gyaran murya
ya ce,
HAUSABOOK.COM
33
"Hakika na girma jin dadi bisa ganin
yadda jama'a suka bayar da hadin
kai wajen halartar wannan fada mai
albarka, domin ganin yadda za a
bayar da manyan kyaututtuka ga
jaruman da suka samu nasarar
lashe gasar gasa rukuni uku da aka
sake a jiya.
Yanzu sai kowa ya saurara, domin
ya ji sauraran bayanı. "Gama fadin
hakan sai sarki ya koma kan
kujerarsa ya zauna sarkin yaki
Hatyal ya miƙe tsaye ya yi gyaran
murya ya ce," Da farko yanzu muna
bukatar ganin jarumi Hilwas wanda
shi ne ya lashe kallon yaki da
takobi, bayan ya samu nasara a kan
abokin gwaminsa yarima Kinzaru.
"Koda jin an ambacı Hilwas sai
fadar ta rude da ya Koda hayanıya
magoya bayansa na yi masa jinjina,
har sai da je ya tsaya a da akc
bukata.
HAUSABOOK.COM
34
Koda tsayawar ta shi sai wani
badakare va iso da wata
madaidaiciyar akwatu ta bakin karfe
ya ajiye ta gaban sarkin yaki a bisa
tcburin da ke gabansu.
Sarkin yakı ya bude akwatun ya
dauko wata takobi da aka yi ta da
zubar daji haɗe da wani kambu ya je
ya risina a gaban sarki ya miƙa masa
ya karba, shi kuma ya mike tsaye ya
sanyawa bawa Hilwas kambun
kuma ya damka masa takobin,
Sannan ya rike hannun hilwas ɗayan
ya saka a nasa ya daga sama.
Nan take fadar ta rude da shewa
gami da tafi, wasu ma har da kida
da rawa, domin nuna farin ci kınsu
bisa ba wa gwaninsu KAMBUM
JARUMTA na gwarzon shekara. A
bangarcn gimbıya Lashmira kuwa
saboda tsananin muna ba ta san
sa'adda ta mike tsaye ba tana yıwa
masoyinta tafi da jinjina.
HAUSABOOK.COM
35
Al'amarin da ya harzuka zuciyar
yarima Kinzaru ke nan takama
tafarfasa kamar zuciyar tasa za ta
ƙone
ya ji kamar ya zare takobi ya sare
wuyan bawa Hilwas.
Fadar ba ta samu nutsuwa ba sai da
sarkı Husubul Dinar da sarki
Hulbaru suka ba wa Hilwas kyutar
dukiya mai yawa da adadinta ya kai
dinare miliyan shida da ɗoriya
sannan yaje ya zauna a kan
kujerarsa a cikin yan uwansa
Sharwas da Kahzib Sannan sarkin
yaki Hatyal ya yi gyaran murya ya
dora demunsa a kan takardar da ke
magana game da shi,
Jarumai na Kahzib da ya lashe
zaben harbin KWARI DA BAKA, sai
arumi Sharwas da ya lashe kallon
jifa da mashi A lokaci guda tsakanin
Kahzib da Sharwas suka mike tsaye
suka nufi in da karagar mulki take
HAUSABOOK.COM
36
sai nan take fadar ta sake kaurewa
da shewa da tafi, gimbiya Shuraima
kuwa farin cikin da ke zuciyarta ba
a tonawa bisa ganin abin Kaunarta
bawa Kahzib.
Sa'adda ya rage bai fi sauran taku
uku ba da girma da karagar mulki
sai suka zube kasa suka kwashi
gaisuwa ga sarkı Shardasu sannan
wannan mummunan halin ya sake
daukar manyan akwatu guda biyu
ya ajiye su gaban sarkin yakı
Hatyal,
shi kuma ya bude ya dauko wata
kasaitacciyar KWARI DA BAKA a
cikin akwatu daya ya sake mikawa
sarkı Shardasu shi kuma ya
dankawa Kahzib, sannan sarkın yakı
ya sake bude akwatu ta biyu ya
dauko wani dogon mashi mai bakı
biyu mai kyau launi da daukar ido
ya mikawa sarki a karo na biyu, shi
kuma ya damkawa Sharwas.
HAUSABOOK.COM
37
Take fadar ta sake rudewa fiye da
ko yaushe, a wannan lokaci ne
Kahzib ya hango gimbiya Shuraima
'yar sarki Husubul Dinar,
kawai sai ya ga ta jefe shi da wani
inn tattausan mumushi mai tattare
da tsantsar so da Kauna.
Ai kuwa shi ma bai san sa'adda ya
mayar mata da maratanin
murmushin ba.
Kahzib da Sharwas suka juya