Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 5
su Abbanku su ka zo da maganar aure, bayan su Babban mu sunyi shawarar ba shi, sai ga wani zance ya fito. Wai Mus'ab yana dauke da wata cuta, kuma duk macen da ya aura za ta sha wahala a kan wanan cutar tashi, dan Allah ki faWamun gaskiyya, nasan ba zaki Soye ba, sanan kin san Yayata ba wani kiSa gare ta ba, kuma wallahi ba xan taSa cewa daga bakinki na ji ba, ko a gidanmu." Tsuru-Tsuru nayi da idano, tabbas nasan komai da ta faWa gaskiyys ne, Amma idan na fad'a mene makoma ta, nayi munafunci, ko nayi taimako?. "Wallahi, Salma ba zan ta Sa cewa a bakin ki naji ba." Wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke, sanan na ce."Kin san bani da alak'a kyakyawa da Mus'ab, abubuwan shi ba su shafe ni ba, kuma ba na saka kaina, domin nasaka SAKATA na kulle duk wata ofa da za ta had'a wani abu tsakani na da abinda ya shafi Mus'ab." "Nasani, Amma ba zaki rasa sani wani abu a kai ba, bani zaki yiwa ba Salma, 'yar uwata da rayuwarta." Shiru nayi ina tunani a cikin zuciyata, mai zai sa na Soye gaskiyyar nan, mene ruwana da tonan asirinsa, idan ma na rufa mai aairi ban tsane shi ba, gwanda na to na masa asiri ko mutuwa ne ma yayi, karewa. "Duk abinda na fad'a miki, idan har kika fad'awa wani ni ce na fad'a miki. Ubangiji ya gama ki da Masifa a rayuwa." da sauri ta gyad'a kai sanan ta ce. "Na yarda wallahi, babu wanda zaiji ke ce kika fad'amun." "Eyh, tabbas Mus'ab na dauke da cutar da ni kaina ban ma san sunan ta ba. Amma ta danganci iyali, itace wacce ke sa mata su rame sosai. Yanzu shigowarki zaki ga ina dariya, ganin ki ne yasa na tuno yayarki shine nay dariya." Shiru tayi, ni kam sai a lokacin na tu na SaranSaramar da niya, daman ni a kwai mugun surutu, da fad'i ba a tambayeka ba."Shikenan na gode, kuma insha Allahu babu wanda zai ji maganar nan da ga bakin ki ta fito." "Shikenan na gode." daga haka ta tashi ta fice, ni kuma na maida hankali kan abinda nake kafin ta shigo. Haka na zauna a jin sukuku, idan wani Sangarena zuciyata ya nuna mum abinda nayi ba dai-dai ba ne, sai wani b'arin ya ce. "Kinyi d'in, shi dai-dai yake miki." Muna tashi daga makaranta mu ka yo gida, ni dai burinah naje nayi waya da Vida.mia nah, ya fi mun wanan zancen Mus'ab Win. Sai dai ina shiga Wakin Ummanah ta aika ni Snagren sa, na kai mai Abinci. "Wai Ummah ke ce kike da hain ciyar da Mus'ab ne?." Wani banzan kallo ta watsa mun wanda ya sani ficewa, ni ban san me Mus'ab kewa Ummanah ba ta ke mugun son sa haka. angaren Hajja na fara zuwa, bakina Wauke da Sallamah na shiga Wakin na ta. Ciki-ciki ta amsa mun, ni kam bai dame ni ba. "Ya na nan?." "Waye?." ta tambayeni, kamar ba ta san wanda nake nema ba. "Mus'ab." na faWa a daile. "Allah magani maoci maye ni uwar su Yunusa matar Galadima, wanan yarinyar baki yi ba wallahi." "Yana nan?." Na sake fada. "Yana Sangaren uwarsa." Murgu Wa baki nayi na huge, har na fita sai naji ban kyauta ba, Hajja fa ba ita ta kemun abinda Mus'ab ke mun ba, dawowa nayi na ajiye plast Win sanan na zo inda take na zauna."Hajja." na kira sunanta. "Na'am Uwatah." ta faWa. "Hajja, kin ware mutum Waya cikin jikokin, kin nuna shi kaWai kike so, kika damu da shi, kuma hakan kan haifar da tsana cikin zuri'ar ki." kallona tayi sanan ta ce. "Salame ai ni kin nuna mun ban isa da ke ba, kin nuna mun ke ware cikin jikokina, sabida kin dauki tsanar duniya kin Wora a kan wanda kika kamar na damu da shi." ganin Hajja ba zata fahimci abinda na ke so ta fahimta ba, yasa na kwashe afafuna nayi waje. Ji nake kamar kar na shiga Sangaren nasu, sabida nasan Maman ciki ba ta nan, walida kuma ba ta dawo ba, har na kai bakin ofa wani Sangarena na zuciyata yace da ni."Yanzu fa yunwa yake ji, kuma yana jiran abincin nan, ke baki da hankali zaki kai masa yaci yayi maganin yunwar, kinga fa kin taimakeshi kenan." Da sauri na ce."Allah kar kasa ko rana daya na zama mai taimako ga Mus'ab." ina fadin haka na canja hanya zuwa Sangaren su Sadiya, a zauren su na Soye plast din kar a gani, nasan da zarar angani topa sai nai kai mai. Sadiya na zaune tsakar gida na shiga, washe baki nayi ganin wayar Anty a hannunta, a fili na ce. "Antyn ba ta nan?." "Yanzu ta je gidan Anty Nadra, wai ta kawo kayan kitchen." "Su amarya, ni Wan a ramun minti Waya nayi waya." Na faWa, ban jira cewarta ba na dau wayar, a zuwa yanzu na haddace lambar Masrur tas a kaina, kira na danna bayan na loda lambar. Kamar ko yashe bugu Waya ya Wauka tare da faWin."Fulani nah." Wani sanyi naji a raina, sanan na ara yardarwa raina Masrur soyayyar gaskiyya yake mun, domin dana kirashi yake gane nice. "Na'am Vida mia." "Fulani, yau nayi kewarki sosai." "Nima haka, na si kiranka da safe amma ban sami lokaci ba har na tafi makaranta." "Nima Fulani na tanadi morning messages Wina, sai kuma na tuna wayar Ummanah ce." dariya nayi jin ya faWi Ummanah kamar yadda nake faWa."Me ya baki dariya haka?." ya tambayeni, murya cike da so da auna, wanda ban san lokacin da na fara gane su ba. "Wai Ummanah, irin yadda nake faWa." Dariyar yayi shima sanan ya ce. "To ba Ummnah ba ce." da sauri na ce. "Eyh, Ummanah ni kaWai." "Wallahi ban yadda ba." ya faWa kamar zaiyi kuka, dariya yabani, ai kuwa na shiga yin abata babu ko aautawa, sai da na gama sanan ya ce. "Dariya kike mun ko?." shima dai kamar zaiyi kukan. "Ni kai ne ka ban dariyan." "To me nayi na baki dariya?." "Kana magana kaman za kayi kuka." "To ai kukan zan miki, tun da kina rabani da Ummanah." "Ni dai ba zan baka Ummanah ba gsky." na fada, kuka har cikin raina da gaske."Shekrar ki nawa?." Naji ya tambaye ni. "Sha takwas da wata Waya." dariya yayi sanan ya ce. "Menen wata Waya?, sha takwas kawai hajiya." "Hajiya kuma?." na tambayeshi."Eyh mana, Hajiyata, Fulanita." "Wai nikam suna nawa ne da ni?." "Dubu biyu." ya bani amsa, kamar yasan tambyar da zan masa kenan. "To faWo su muji." "Tom ki shirya." "Na shirya ai." Na bashi amsa a matse. "Fulani." "aya." yayi dariya sanan ya ce. "Gimbiya." na c e. "Biyu." ya k'arayin dariya, sanan ya ce. "Mai gadon zinare." "Uku." "ki daina lissafawa." na ce. "Thom." "Habibiya, Hajiya, Uwar 'ya'yana, Matata, mai Waki na, abar auna, wacce nake so." Dariyar da nayi ce ta tsayar dashi. "Mai ya baki dariya?." Shiru nayi sanan na ce. "Duka kuma wa'yanan nawa ne?." "Ai baki taaya na gama ba." bude baki nayi da niyar yin magana, naji sallamar Anty, sai a lokacin na tuna inda aka aiki ni, da sauri na ce."Kasan aike na akayi?." "Ta ina zan sani baki fad'an ba, ina zaki." "Wai Mus'ab a ka ce na kaiwa abinci, tun Wazu." "Maza-maza tashi ki kai ma sa." Tashi nayi ina fad'in. "idan na dawo zan kira ka, ko a wayar Ummanah ne." Sanarwa! Ranar litinin zamu fara posting paid pages, posting kullum, za'a fara siyar da complt ma ranar litinin, zaku iya fara payemnt tun yanzu Payment via. 8129553971 OpaY Sani Muhammad lawan. Shaidar biya. 08165383931. ci gaba "Shikenan sai anjima, love you." A jiye wayar nayi tare da fitowa, kai tsaye nayi Sangarensu. Da sallama na shiga Sangaren na su, sanin Walida ba ta dawo ba, kuma tun safe Maman ciki ta fita yasa na nufi Wakin na shi, yana zaune kan kujera yana faman lallatsa da laptop Win shi, daman kowa yasan Mus'ab da aiki da na'ura, domin ko aikin da ya ke yi na na'ura ne. Suna da babban kamfani, wanda suke aiki da na'ura mai kwakwalwa sanan ma aika cin farin kaya ne, na hukumar yai da cin hanci da rashawa EFCC. Ciki-ciki nayi sallama, yayi kamar bai ji ni ba, nima kuma ban sa ke maimaitawa ba. Ajiye plast Win abincin nayi tare da juyawa, sai dai kiran suna na da yayi yasa ni tsayawa, ba tare da juyowa ba."Ke Salame." bantaSa jin ya faWi suna na ba, idan an tambayeni ma zance ba lallai yasan sunan, ashe shima salamen yake cewa, sunan da na tsana. in amsawa nayi jin Salame ya ce, na ci gaba da tafiya. "Ba da ke nake ba." ya faWa a fusace amma cikin sanyin murya. "Ai ba suna na Salame ba." Na faWa, zuciyata namun wani tuwii domin ko kalma Waya bana aunar ta haWani dashi. "Ke ya dama wanan, Wauki tsintsiya ki sharemun Waki." a wane sukwane na juyo nayi mai wani kallon. "Kana shaye-shaye ne?." Ganin ina ta kallonsa, idanu na kamar sa faWo asa tsabagen harara ne yasa shi cewa. "Ba da ke nake ba, ko baza kiyi ba ne?." "Wallahil azeem ba zan ba." na faWa a fili, kallo na yake cike da mamaki, rashin kunyar tawa har ta kai nan kenan?."A karo na arshe, ki Wau tsintsiya ki sharemun nan." "Mitcheww." naja wani dogon tsaki, tare da yin gaba. Sai dai ban kai ofa ba naji an riomun hannu, ina juyowa a ka Wauke ni da mari, wanda nima banyi wani dogon tunani ba, na Wauke shi da nawa marin. Sai arar ya bada Tas! Tas Legends pen. (08165383931/ 08129553971). Daga page 10 zamu gama free pages, mu shiga paid pages, 500 kacal ne sai kuma masu buatar complete 1000. Payment via. 8129553971 OpaY Sani Muhammad lawan. Shaidar biya. 08165383931. *SAKATA*d'& <;Stroy and written<; By Sayyid writer (Legend) ' *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)=؋=* SHAFI NA TARA (P.09). (3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE "Mitcheww." na ja wani dogon tsaki, tare da yin gaba. Sai dai ban kai ofa ba na ji an rio mun hannu, ina juyowa a ka Wauke ni da mari, wanda nima banyi wani dogon tunani ba, na Wauke shi da nawa marin. Sai arar ya bada Tas! Tas. Da mugun mamaki ya Wago ya kalleni, ni kuwa sai haki nake kamar wata zakanya, banyi au ne ba kuwa naji ya kwarfeni da afarsa na faWi asa Tim!, ai kuwa ya bini da duka. Ya fusa ta iya fusa ta, nima kuma na fusa ta iya fusa ta domin baki na bai mutu ba, faWi na ke. "Shege, mugu, azzalumi, kuma wallahi zai ka ga gatana, wallahi sai munyi shari'a da kai." shi kuwa duka na ya ke amma da afa, cikin sa'a na rie kafar ta sa, na gan tsara masa wani mugun cizo, kuma nak'i ci kawa har sai da na had'o da fata, da sauri ya janye k'afar tare da matsawa, nan take zuciyata ta ce mun. "FaWan bai k'are ba." ai kuwa na tashi da mugum guda na Wane bayan shi kamar wata biranya, na shiga gantsara masa cizo a wuya, shi kuwa faWi ya ke. "Baki da hankali ne?, sauka a kai na." Salatin da Ummanah ta saki ne ya sa jiki na wani irin mutuwa, kirjina ya shiga bugawa da k'arfi-k'arfi. "Sannu 'yar biri." sai a lokacin na fara oarin dirga asa, idanunta suka kai kan afarshi da ke fitar da jini, ga kuma shatun haorana a wuyansa. "Kashe shi zakiyi kenan." miri-miri nayi da idanu tare da fad'in. "Ina shigowa ya kifa mun mari." Ba ta ko kula ni ba ta shigo Wakin tare da kama hannuna ta shiga jana a asa, kamar kayan wanki. "Nashiga uku na lalace." kawai nake iya fad'a a raina domin nasan yau na bushe har hanjina. "Ummanah dan Allah kiyi hauri, wallahi shine ba shi da gaskiyya, wai sai na share masa d'aki daga na ce bazan share ba shine ya mare ni." Sai da na fad'a kuma, na tuna Saran-b'aramar da nayi, ni a rayuwata kwata-kwata ban iya arya ba, komai gaskiyya nake fad'a kai na tsaye. "Shine kika fara gantsara masa cizo ko, ke ga mahaukaciya, karya ko?." "Wallahi Ummanah ba haka ba ne, mari na yayi." ban arasa rufe baki ba, naji saukar mari tare da bulala, ina ihu ina kororoto amma Umma ara zanbad'a mun ta ke. Daman Ummanah kwata-kwata ba ta iya duka ba, duk lokacin da ta dake ni sai tayi mun rauni, shi yasa Abbanah yayi mun fad'a kan na kiyaye abinda zai Sa ta ma ta rai, to lokacin da ta da ke ni ma na arshe a kan Mus'ab ne, kai Mus'ab ya zama masifa a rayuwata. Tun ina kuka da bata hauri, har na yi shiru gaba Waya duk wani arfina ya are, sai da ta ga ji dan kan ta sanan ta kyale ni tare da fice wa, ta bar ni kwance ina kuka. Nayi kusan minti goma a zau ne, zuciyata na ta saka mun abubuwa kala-kala, ta ce mun "in je ina bu ga masa dutse a kai, sai dai ko mene ayi mun.", ta ce mun."In je in a re mai tana di, zagi ta uwa ta uba" ko hakan zai kawo karshen zumuncin nan." abubuwa kala-kala, arshe na yanke mafita guda d'aya na tarka ta na bar gidan baki daya, na je gidansu Masrur ko a 'yar aiki ya kai ni, daga baya mu yi aurenmu. A b'angaren Ummanah kam, ta na ga ma duka na ta nufi Sagarensu Mus'ab, ya na zaune kan kujera ya rasa mai ke masa dadi, sallama tayi d'akin ya amsa. "Yanzu kai Mus'ab yarinya k'arama za ka tsaya har ta mare ka, ba ka b'abbalata." "Ummah kiyi hak'uri, bana son na dake ta nayi mata rauni." "Da ba ka ballataba, ai ko shi Abban na ku idan yazo ya ji abinda ta yi sai ya Sallata, kuma ya na dawo zan faWamai." "Ummah dan Allah kiyi hakuri, laifina ne da nasa ta sharar." "To wallahi daga yau, har zuwa ranar da zaka bar gidan nan ita zata ke maka sharar Wakin, kuma ka ci abinci idan zaka ci." ta faWa ta na ta shi, alamun shi ma ya Sata ma ta rai,a tsakar gida su ka haWu da Maman ciki, ganin yanda ran Ummanah ke haWe Maman ciki ta ce."To mai kuma ya faru da 'ya'yan naki?." "Bari ke dai, lamarin Salma ya fara isa ta, yarinyar nan kullum rashin arziinta ara gaba ya ke." "Salma yarinya ce fa har yanzu, wai bakya tuna lokacin da aka haife ta ne?." wata harara Ummanah ta watsa Maman ciki, sanan ta ce."A'a ban haife ta ba, yawo nake da ita a ciki." "Allah yabaki hauri, yanzu ta na ina?." "Ta na can ta na jinyar jikinta." daga haka Ummanah ta huce, tabar Maman ciki da sakkaken baki, Waki ta nufa ta ajiye jakar ta tare da shiga bayi, sauri-sauri take ta fito tazo Sangaren namu. Ni kam tun da na yanke shawarar barin gidan, na shiga haWa kayana, bayan na cika akwatina sanan na jawo wata katuwar jaka na shiga zuba wasu kayan ciki, har da jaka da takalmi na. Bayan na gama na shiga d'akinta, inda take ajiye kudinta na nufa, naira dubu uku na dauka, sai kuma nayi tunanin dubu uku tayi mun yawa, nan da Gwari avenue baifi 2500, haka yasa na ajiye dari biyar na fito, ina kokarin janyo jaka da akwati na ta shigo, kallo na kawai tayi ba tare da ta ce."Ci kan ki ba." ta huce ciki, ni kam na ci gaba da jan kayana. Ina daf da bakin ofa naji an cafke ni, juyuwar da xanyi na ganta da wayar charger ta computer Abbanah, ba wata-wata ta hau zabga mun, ni kuma ina rusa ihu. Mamam ciki ta shigo da sauri ta na fad'in."Innullahi wainna illahir rajiun, Menene haka dan Allah?." "Barni na targad'a yarinyar nan, nayi mata rau ni." "Kiyi ma ta rau ni, sabida me, haba dan Allah." Nikam narkewa na arayi a jikin Maman ciki, ina faWin."Wallahi sai na bar gidannan ba za'a kasheni ba." "kiyi shiru ke kuma." Maman ciki ta faWa, Ummanah kam ajiye bulal tayi tare da shigewa Wakin, kallona Maman ciki tayi sanan ta ce. "Je ki mai da kayan, kuma kar ki sake irin wanan abun ko da wasa." "Wallahi Mama bazan ko ma ba, duka na zata ci gaba, ni kawai a bar ni." "Ki je ki mayar na faWa mi ki." Maman ciki ta sake faWa. "Wallahi ko kin mayar sai na dake ki, kuma har can Sangaren zan zo." Kuka na fara, maman ciki ta ce. "To ai ba Sangarena zan kai ki ba, muje." tunda ta ce haka, Sangaren Hajja zata kai ni. Ai kuwa can Winne, Hajja na gani na haka ta fara sababi. "Amma wanan uwarta ki ba ta da hankali, to wallahi ahir Winta." Ni kam wata tsanar Mus'ab ce sabuwa ta sake fidda rashe a cikin zuciyata, a kan shi anyi mun dukan da ba'a taSa kwatanta mun ba, an kira mahaifiyata sa mara hankali, duk a kan Mus'ab, kai Mus'ab ya zama tauraruwa mai wutsiya a inda nake." Maman ciki ce tai ta ba Hajja hauri, sai da ta ga tay shiru sanan ta ta shi ta tafi. "Tashi ki haWa ruwan Wumi." Hajja ta faWa tana kallona, bayan fitar Maman ciki, ba musu na mie nayi Kitchen, a heater na Wora ruwan Wumin, sai da yayi sanan na sauke na shiga na watsa ruwa, naji daWi sosai a jikina, na zo nabi lafiya kujera na kwanta, banko sassauta da tsinewa Mus'ab, har bacci ya Wauke ni. Sai wajen la'asar sanan na tashi, zaune na ganshi kan Waya kujera dake kallon tawa, amma hankalinshi na kan wayarsa yana dannawa, inaga ma baisan ni ce kwance kan Waya kujerar ba, miewa nayi ina turu baki, ina hararshi asa-asa, Allah ya gani na tsani Mus'ab, bana ko aunar ganinshi domin a yanzu na fuskanci Mus'ab so yake ya rabani da Ummanah, domin a kwanciyar nan ta wa na ara tabbatar da hakan, indai nasamu saSani da Ummanah tofa a kan lamarin Mus'ab ne, ko mene ribarsa oho, wani Sari na zuciyata ya ce. "Mutumin da baya sonki, mene ribarsa idan bai rabaki da iyayenki ba?." a fili na furta. "Kurwata kur, mai Wa ya ci Wanshi mara Wa ya ci oon tsuliyarshi." Wani kallo ya watsamun, sanan ya ci gaba da danna wayarsa, nima na mayar mai da kallon da hausawa suke cewa. "Harara a duhu." tun da bai san inayi ba. Bayi na shiga na Waura alwala, na fito na ta da sallah, har na kamalla yana zaune, yana danna waya."Mai bautar waya." na faWa a raina, tare da shiga Wakin da Hajja ke ciki. "Hajja abinci." Na faWa daga tsaye. "Ke fa matsalata dake rashin kunya da rashin mutunci, haka ake yi a gidanku." na cuno baki gaba sanan na ce. "Ke kuma matsalal ki mita da sababi." "Nayi mita nayi sababin, na rantse yanzu zaki ficemum a Sangare." Shiru nayi nasan zata aika, kaddam ne daga aikin Hajja."To yanzu Hajja mai zan ci?." "Shiga kitchen, ki dafa taliyar yara ina da ita lodi-lodi." Kicin Win na nufa, na shiga haWa indomie na, ina mamakin yadda Hajja ke cin indomie, a yanzu haka akwai sama da katan biyar a cikin kicin Win, ina tsaye har ta kamalla, na juye a faranti na dawo falon, yana nan zaune kaman mutun-mutumi, yana faman bautar waya. Bayan na ajiye na shiga Waki, nayi narai-narai da fuska na ce. "Hajja tawa." Baki buWe take bina da kallo, kamar ta ga sabuwat hallita. "Hajjana, dan Allah wayarki zaki bani, na kira malamin mu na sanarshi bani da lafiya ya sa banzo ba." ita Hajja ba ta wami damu da waya ba, kuma kullum wayarta cike da katin waya, haka su Sadiya za su zo da Walida suyi ta Wauka suna kiran samarinsu, ni kam bantaSa ba sai yau, ko da yake yanzu na fara soyayyar. Dawo falon nayi, sabida naji ana cewa."Waya sa saurayi kana cin ainci tafi tsargawa." Nan da nan na danna masa kira kamar ko yaushe, sai dai yau kiran na shiga ya katse, kafin na gama tantance mai ya faru naga kiranshi ya shigo, murmushi nayi tare da kai lomar indomie baki na, bayan na Waga kiran."Fulani mai lambobi da yawa." Ya faWa bayan na Waga."Mijin Fulani, mai gane Fulani a ko yaushe." Na faWa cikin wani irin salon magana, dani ban ma san na iya ba, ko dan Mus'ab na nanne? Oho mun. "Fulani, yau kuma wayar wa aka samu?." Ya tambaya cike da kulawa kamar ko yaushe."Wayar Hajja ta ce." Na bashi amsa cikin cool voice, wanda ni dai ban san lokacin da na iya ba."Uhm, Ummanki, Hajjanki, to ni wai wa za'abani?." "Salma Galadima mana, ita za su baka, ni dai kabarmun Hajjana, da Ummanah." "Ai kam na barsu, tun da zasu bani abinda nafi auna." Dariya nayi na ce."Zasu baka mana, mussaman Ummanah." "Yau mai Fulani ke ce?." Dariya na arayi, sanan na ce. "Indomie Win Hajja na dafa." "Yau kina Sangaren Hajja ne?." "Can zan kwana, ilama na dawo nan." "Kai Fulani, ai Umma ba za taji daWi ba." "Uhm, zataji mana. Ai yanzu munafukai sun shiga tsakanina da ita." Dariya yayi, har ana jiyo sautin shi sosai ta waje, sanan ya ce."Fulani munafukai kuma." "Uhm, munfukai masu bacci da ido Waya." Na faWa ina ara kai indomie bakina, gaskiyya na yarda waya da saurayi ana cin abinci tafi tsargawa."Su waye haka to?." ya tambayeni. "Na ce maka masu bacci da ido Waya." "Su ba su da suna?." "Uhm..." "La'ila ha ilallahu muhammadu rasulillahi, amma Salame baki da mutunci, Mus'ab Win na zaune kika saka taliyar yaran gaba kika cinye, shi dayake kawo wa baki zuba masa ba." Muryar Hajja ta tare ni daga niyar bawa Masrur amsa, dariya yayi ta cikin wayar tare da ce wa. "Fulani sai anjima." ban iya bashi amsa ba ya kashe wayarsa, sakamakon wani abu da yatsayamun a maoshi yaki tafiya, jin wai Mus'ab ke kawo wa Hajja indomie Win da nake ci yanzu, yau nice naci abinda Mus'ab ya kawo. Da wani mugun sauri na tashi na nufi banWaki, domin kwararar da indomie din da naci, amma ina ciki na yarie ta katamau, duk yunuri na amai yai fita, a dole na wanke bakina na koma Wakin, ina ta faman cika da batsewa."Ke lafiyanki?." Hajja ta tambayeni. "Haba Hajja ai sai ki ce mun ga wanda ya kawo indomie Win, amma kika barni na ci haram." "Uwariyanki Salame, abincin ne haram?." "Habba Hajja, Haba Hajja ni dai baki kyauta mun ba." Sallama Babban ciki naji, sai kuma Abbanah ya na ta faman faWa, ban ma iya arasa tantance abinda yake faWa ba, na tashi nayi Wakin Hajja da nasan Ummanah ce ta faWa masa abinda nayi ya zo Sallani. "Har mu mutanen nan zasu mayar ananan mutane, har mu za'ayi wanan cin fuskar." Abbanah yake faWa, shi dai Babban ciki yayi shiri ya zauna kan kujera, Alhaji arami da kawu Madu ne suka shigo sai Yaya ilyasu, babu Abinda nake tamaimaitawa a raina sai. "Innullahi wa inna illahir rajiun, yau kashi na ya boshe. Duka wanan taron a kai na." "Lafiyanku wai?." Hajja ta tamabaya, bayan su gama zama. "Iyayen yarinyar da Mus'ab zai aura ne suka aiko, wai sun gano yana da wata cuta dan haka sun fasa bashi aurenta." Legends pen. (08165383931/ 08129553971). Daga gobe zamu gama free pages, mu shiga paid pages, 500 kacal ne sai kuma masu buatar complete 1000. Payment via. 8129553971 OpaY Sani Muhammad lawan. Shaidar biya. 08165383931. *SAKATA*d'& <;Stroy and written<; By Sayyid writer (Legend) ' *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)=؋=* SHAFI NA GOMA

Chapter 4 of 5