a yanda nakeso da ki rayu a yanda kika zaɓa"....
Sudai basu kulata ba domin sun fuskanci Ruƙa'a kullum ƙara dulmiya takeyi, haka suka shiga motarsu suka nufi gida, babu abinda yake cin zuciyar Samha kamar sunan Ruth da mahaifiyarta take kiranta dashi, koda sukaje gidan bata da wata walwala duk sanda ta kaɗaice kalaman mahaifiyarta na dawo mata, tunda dake da Mom bata taɓa ma rayuwarta kyakkyawan fata ba.
Idan ya tuna wannan abin sai kuka ya ƙwace mata haka zata tottoshe bakinta don kada kakarta me sonta tajiyota haka a daddafe ta wayi gari da safen juyi tayitayi a gadon tunani da dama suna zuwar mata wasu suna ce mata ta haƙura da wannan tafiyar bakin da Mahaifiyarta tayi wannan tafiya tata mai girma ne wata kuma tana faɗa mata kar ta soma komai yana faruwa ne cikin rubutun Allah, idan Allah bai hukunta mata abinda Mom ta furta ba bazai Sameta ba domin ba zunubi ta aikata ba..........
*👑 HARIJIN SARKI 👑*
*Oum Hairan*
*Regular 500, VIP 1k, V-VIP 2k via 9031307566 Fauziyya Tasiu Umar Opay Evidence of payment 09031307566*
*Ga masu son a tallata musu hajojinsu ƙofa a buɗe take zamu tallata muku kasuwancinku cikin aminci da rahusa, kudai ku tuntuɓi wannan number 09031307566.*
https://arewabooks.com/u/oumhairan1
*Page 5-6*
Wayewar garin tazo mata da wani yanayi na sanyin jiki da mutuwar gaɓoɓi tunda tayi sallah take zaune saman sallaya batasan me takeyi ba addu'a ko kuma zaman banza, 5:45am wayarta ta fara rurin neman agaji Miƙewa tayi cike da zullumi ta sani mutum ɗaya ne me kiranta yanzu domin kuwa shine suke da alƙawari dashi, shi ɗin ne kuwa ta danna accept yace “Ina kofar gidanku jirgin mu zai tashi shida da rabi ne Samha" amsa masa tayi da “to Yallaɓai" ba wani ɓatawa kanta lokaci tayi ba shigar tayi ta gargajiya ta gyara gashinta ta yafa mayafinta a kafaɗarta ta ɗauki jakarta da trolley bag ɗinta ta fito ta ishe Granny zaune bisa sallaya ta rusuna s gabanta ta dafa kanta tare da sanya mata albarka ba tare da tayi furuci ba ta haɗe hannunta alamar fatan alkhairi ta mike ta fito janye da trolley bag, can nesa da farfajiyar gidan nasu ta hangi motar da Dr Junaid yake ciki ta ƙarasa ya fito ya buɗe mata motar ta shiga shikuma yaja trolleyn yasa a but yaja motar suka tafi.
Suna tafe suna yar hirarsu har suka je filin jirgin saman suka zauna a mazauninsu babu jan lokaci jirgi ya ɗaga zuwa Rabat, zuciyar Samha cike zullumin da ta kasa sanin dalilinsa, takas da rabi suka sauka motar asibitin tazo ta ɗaukesu haɗuwa da tsaruwar asibitin shine yafi komai ɗaukar hankalinta ta sauke ajiyar zuciya a hankali lokacin da shugaban asibitin ya miƙo mata hannu sukayi musabiha tare da nuna farin cikinsa da samun ƙwararriya kuma jajirtacciyar ma'aikaciya irinta, wadda ta sadaukar da rayuwarta da lokacin don rayuwar al'umma, da wannan suka rankaya suka isa katafaren office ɗin nata ta kalli office ɗin ta kuma Kallonsa ta ƙara kallo a ranta tace “Barakallah" files files ya ɗebo daga ma'ajiyarsu ya kawo mata gabanta ya zare guda ɗaya ya mayar dashi gurin daya ɗebo waɗancan ya zauna yana mata bayanin komai dalla dalla duk ta gane me yake cewa abinda takeson sani meye dalilin zare wancan file ɗin meshi ya mutu ne ko kuwa akwai wani bayani ne na Musamman a kansa" tambayar da tayiwa Zuciyarta kenan tana me kallon sashen da file ɗin yake.
Dr Razeen ne ya fahimci inda hankalinta ya karkata ya koma ya ɗauko files ɗin yace “Kullum zuciya tana inda aka kangeta da zuwa Dr Samha wannan file ɗin ba na kowa bane face na wani babban mutum a garin nan wanda yake da matuƙar daraja, shi wannan mutumin ya kasance yana fama da wani irin ciwo bauɗaɗɗe kuma ɓoyayye, yana ɓoye ciwonsa a cikin izzarsa yana bayyana ƙarfinsa a cikin rauninsa saidai kuma abin kullum ƙara cin tura yakeyi, wannan mutum Mai daraja ya kasance lamba ɗaya a babbar masarautar nan ta ZIRKAN wato mai Martaba Sarki Rashid Ibn Fayyad Al Zirkan"
Ɗagowa tayi da sauri ƙirjinta na bugawa tace “Sultan Rashid Ibn Fayyad Al Zirkan?" Jinjina kai yayi yace “Ko kinada labarin matsalarsa ne?" Girgiza kai tayi tace “Bansan komai game da duk wani abu daya shafi Rabat da Qasr al-Malik ta Zirkan ba, Ni mutum ce me son bincike akan tarihin masarautu da abinda ya shafi masu madafin ikonta, shin zan iya samun ƙarin sani a wajenka Yallaɓai?"
Numfasawa yayi yace "Ok ki bi a hankali zakisan komai Samha" da wannan ya fice bayan ya maida File ɗinnan gurin daya ɗaukoshi cike da rashin kuzari ta fara duba tulin files ɗin dake gabanta, kowacce damuwa dai irin wacce ta baro a Fess ce babu wata sabuwa, kwantar da kanta tayi bisa kujerar tace “Ya Allah!" Lumshe manyan idanunta tayi taci gaba da juyawa bisa kujerar, sabon gurin aiki sabon bincike sabon labari, tabbas Zuciyarta ta kwaɗaitu da son sanin wani abu game da wannan file da akace mata na Sultan Rashid ne zataso sanin meye abinda yake damunsa wanda yake ɓoyeshi a cikin ikonsa yake lulluɓw rauninsa da isarsa tabbas sai tasan meye wannan.
Da wannan ta tashi tayiwa kofar office ɗin nata key ta zagaya inda file ɗin yake takai hannu ta ɗaukoshi ta koma bisa kujerar ta ta zauna, ruhinta na gargaɗinta buɗe wannan file Zuciyarta na umartarta da buɗewa haka tayi ƙarfin halin yarda da shawarar Zuciyarta ta buɗe file ɗin ta kuwa zabura ta miƙe da sauri ganin wani irin jan haske ya fita daga jikin takardar farko dake bisa file ɗin take taji wata murya tana cewa da ita, "Barka da shigowa Masarautar Zirkan ƙarƙashin mulkin Sultan Rashid Ibn Fayyad Al Zirkan, tunda kika buɗe wannan kundi dole sai kin kai kanki gareshi yake wannan ƙwararriyar likita me karambani, kar kiyi tambaya ki tafi kai tsaye, Masarautar ZIRKAN tana hsmadargudu maso gabashin Morocco, inda rana ke da zafi kuma iska ke kaɗawa da ƙura me ɗauke da danƙo na turare.
Masarautar ta samo asali daga zuriyar Idrisawa, amma yanzu ana mulke da ita da sabon sarki wanda ya fito daga reshen zuriyar da aka manta da ita shekaru aru-aru, Qasr al-Malik ta Zirkan tana tsakiyar birnin Amzir, ta cika da Marmara fitilun zinariya, da fale-falen Andalusian blue tiles.
A cikin fadar akwai zauren manyan baki (Majlis al-kabir) inda akewa mutane jawabi. Gidan Sarki inda iyalansa ke rayuwa fadar Harem wurin matan Sarki da ƴaƴan sarauta, yake wannan Ƙwararriyar likita kiyi sani wannan bayani ina miki shine don haska Miki hanyar tunkarar shafin ƙaddarar da kika buɗo da hannunki, dole Zakije fadar Zirkan zaki haɗu da kaddarori masu kyau da marasa kyau, tunda kika buɗe wannan kundin ƙaddara kin shirya"...........
*👑 HARIJIN SARKI 👑*
*Oum Hairan*
*Regular 500, VIP 1k, V-VIP 2k via 9031307566 Fauziyya Tasiu Umar Opay Evidence of payment 09031307566*
*Ga masu son a tallata musu hajojinsu ƙofa a buɗe take zamu tallata muku kasuwancinku cikin aminci da rahusa, kudai ku tuntuɓi wannan number 09031307566.*
https://arewabooks.com/u/oumhairan1
*Page 7-8*
Shuuuu...... Kamar ɗaukewar ruwan sama taji wannan murya me amon sauti irin na sadaukai ta ɗauke, Zuciyarta taci gaba dayi mata luguden dukan data fara tun farkon buɗe file ɗin, jikinta na rawa irin ta wanda ya haɗu da bazata ta rashin tsammani tare da juyawar kai da tunani a lokaci guda. Daƙyar kamar wacce aka jonawa shorck aka cire ta iya jan jikinta ta ɗaga hannunta cike da firgici ta rufe wannan File ta kai hannu ta ɗaukeshi a ɗan karfafe ta nufi inda yake ajiye tun farko ta ɗorashi ta koma ta zauna bisa kujerarta tayi tsaiii cike da zullumi fargaba da tashin hankalin wannan abu da aka sanar da ita daga buɗe File, ta kasa taɓuka komai duk lakar jikinta ta tsinke haka ta yini a wannan office hatta petiant ɗinta yau gani take musu na wanda yake bukatar a ganshi shima.
Fahimtar idan ta cika takurawa gangar jikinta wani ciwon zai iya ratsa garkuwarta ya sabbaba mata kai juriyarta ƙasa yasata Miƙewa daidai lokacin da agogo ke buga huɗu da kwata, ƙofar ta buɗe tana shirin fitowa ana turo ƙofar tayi baya da sauri jikinta na ɗaukar wata rawa saboda shigar idanunta cikin na wani ƙasaitaccen mutum me fuskar mazan fama wanda yake sanye da kaya irin na Mafarauta fuskarsa a ɗaure tamau kamar tasowar hadari, ta ratse ta bashi hanya ya shiga yana ƙarewa office ɗin kallo Tsaf ya sauke idanunsa a kan Samha da yanayin mutumin ya firgitata, amma ta dake don nuna jarumtarta, takowa yayi a sannu a hankali ya iso gabanta yace “Gaisuwa da fatan alkhairi yake wannan ƙwararriyar likita tabbas ɗazu muna zaman fada Sultan ya ganki cikin idanunsa saƙo yazo masa kamar yanda yazo masa, an tabbatar masa warakarsa na hannunki kamar yanda kema duk ƙasar Morocco shi kaɗai ne zaki samu sakamakon bincikenki a tattare dashi, ya umarceni da na taho dake Amzir yanzu domin ki bashi maganin matsalarsa"
Ja tayi da baya da sauri, wannan mutum yayi murmushi me nuna izza ya shafa gashin bakinsa yace “Sunana Yadam babban hadimin Sultan Rashid muna bukatarki tabbas muna buƙatarki sannan zamu ninka Miki albashinki" janyewa tayi, wasu siraran hawaye na shirin zubo mata tayi saurin tarewa a gun ta kuka rauni ne bata son sakar rauninta ga kowa, da wannan tace “Zan.... Zan iya neman izini a wajen shugabanni na?" Jinjina mata kai yayi ta kuwa fice da sauri yabi bayanta.
Office ɗin Dr Razeen suka shiga yana ganinta ya miƙe idanunsa yayi ja ya nunata da yatsa yace “Meyesa kike da taurin kai da rashin bin umarni? Saida nace Miki Karki buɗe wannan kundin bayanai amma Saida kika buɗe, me zan iya yi Miki Samha? Banda abinyi a gareki, hatsarin dake tattare da wannan file yasa ban haɗa Miki dashi ba ke kuma kikaga hakan baiyi Miki ba tabbas kinyi ganganci kinyi kuskure" rikicewa tayi da kalaman Dr Razeen tace “Wlh banyi tsammanin akwai wani ɓoyayyen duhu cikin wannan file ba, na ɗauka shima Normal rashin lafiya ce, don Allah Yallaɓai....." Ɗaga mata hannu yayi yana kallon fuskar Yadam da ke kallon agogon hannunsa yace “Lokacinki ya ƙare Likita Sultan baison jira" kallon Dr Razeen tayi da yayi ƙasa da kanta hawaye ya shirin zubo mata tace “Dama haka aiki A babban Asibitin ƙasa yake rayuwa da rashin ƴanci rashin zaɓi da rashin makoma, indai hakane Yallaɓai na haƙura da aikin gabaɗaya zan cike takardar barin aiki...."
Murmushi Yadam yayi yace “Idan kikayi hakan zamuji daɗi kuma zamu gasƙata kinsan aikinki dama aiki biyu a lokaci guda bazai yiwu gareki ba" kallon Yadam tayi ta kuma kallon Razeen cike da sallamawa ta juya ta fita da sauri, Yadam ya riƙo hannunta ya nufi wata mota ya buɗe ya sanyata a ciki ya shiga, yana shirin tada motar Dr Razeen ya iso ɗauke da wannan File ya ɗora mata a cinyarta ta ɗago suka haɗa idanu ya ɗaga mata hannu cike da tausayin wannan aiki me wahala data ɗaukowa kanta, koda yake zataji daɗi a lokacin da tsoro ya saketa ta gane ɓangaren da takeson yin bincike akai ne, da wannan Yadam yaja mota suka lula titi Zuciyarta cike da saƙe saƙe tare da kudurcewa a ranta zatayi aikin ne kawai in taga zata iya idan bazata iya ba kuma zata barshi ta kama harkar gabanta.
A hankali sautin Muryar ɗazu ya fara dawo mata cikin ƙwaƙwalwa, zata je ta tunkari ƙaddarar data buɗota da hannunta, zata haɗu da kaddarori mai kyau da mara kyau, to wacce irin ƙaddara ce a cikin duba mara lafiya? Gabanta ne yabada wani dam lokacin da Muryar ta dawo mata tana sanar da ita Yanada matan aure uku yanada Kwarkwara huɗu daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana yana kwanciya da dukkanin matan nan nasa guda bakwai kuma kowacce mace saita fita daga hayyacinta sannan ake fitowa da ita wata ta shiga, yanzu haka matarsa ta aure ɗaya ta mutu hakama Kwarkwara ɗaya saboda wahalar da sukesha wajen kusanci dashi".........
Shigarsu Emirates Road ya dawo da ita hayyacinta gurin iyakar hasashe bazai fasalta haɗuwarsa ba an ƙawata gefe da gefe da tsakiyar titin da manyan bishiyun dabino masu kyau waɗanda akayiwa kwalliya da fenti kala kala masu burge ido da ƙawata zuciya An zuba shimfiɗun carpert don takawar me tafiyar kafa ga wasu manyan fitilun zinariya da Andalusian tiles sai ɗaukar idanu sukeyi kamar a masallacin Alhambra, iya wannan titi aka Barka da kallo to shakka babu zaka nemi damuwa a zuciyarka ka rasa domin duk wata nau'i na damuwa zai ɗauketa.
Kowacce kusurwa ta wannan Titi soji ne da dukkan wani nau'i na jami'an tsaro suke gadin wannan Daula, wata katafariyar ƙofa da iya bayani bazai wassafawa mai karatu haɗuwarta ba, nan Yadam yayi Horn Sarakan ƙofa suka buɗe suka shiga nan Samha ta tabbatar da ita yar ƙauye ce haihuwarta a Fes ba yana nufin itan wayayyiya bace domin kuwa kanta juyewa yayi saboda kallon wannan alatu da ke narke cikin wannan gida na sarauta.
Sunyi tafiya me tsayin gaske daga farkon wannan get aka kuma buɗe wani suka shiga aka kuma buɗe wani suka kuma shiga, cikin na ƙarshen harda Roundabout haɗaɗɗe wanda aka ƙawatashi da wata haɗaɗiyar takobi, sukayi wani shataletale suka kuma nausawa sannan suka shiga Fadar Harem wadda anan ne Sultan da iyalansa suke zaune, tunda suka shigo wannan area ta Iyalan Sultan suka fara cin karo da Barori bayi da kuyangi sunata kai kawo gashinan gini ne sashi sashi a wajen bayan an wangame musu ƙaton get ɗin sun shiga kenan, nan ma basu tsaya ko ina ba Saida suka dangana da wani ɓangare aka sake buɗe musu get suka shiga wayyoh Allah aljannar duniya.
Tuni Dr Samha ta manta da wata damuwa ta dolen da akayi mata na zuwa wannan fada ta farajin a ranta lallai itan zaɓaɓɓiya ce cikin zaɓaɓɓun bayin Allah da ta kasance a wannan guri, parking Yadam yayi ya kalleta yace “Ma iya shiga likita, babu musu kuwa ta fito domin ta matsu taje ƙarshen gidan. Takawa suka farayi tana rungume da file ɗin da Dr Razeen ya bata da kuma system ɗinta suka fara tattaki abinda ya bata mamaki babu kowa a harabar wannan guri, wata haɗaɗɗiyar ƙofa da aka ƙawata adonta da zallar ruwan gold da Azurfa suka nufa suna zuwa Yadam ya taɓa Bell sau ɗaya ƙofar ta buɗe suka shiga ciki wani irin haske ne me saukarwa da zuciya nutsuwa da kasala haɗe da wani sirrintaccen ƙamshi me kashe zuciya da sanyi me sanya bacci suka ratsa gangar jiki da ruhin Samha ashe ba nan kallo yake ba Saida suka ratsa suka shiga wani parlourn shima yana yafi na baya a haka Saida suka ratsa parlour uku a na huɗun ne Samha ta daidaita nutsuwarta jiyo Muryar wata mace tana ihun neman agaji tana kuka tana faɗin wallahi tallahi na gama auren nan Sultan Na gama aurenka wayyoh Allah Pupsy na wayyoh shikenan yau ma ya farkamin Pupsy........"
*👑 HARIJIN SARKI 👑*
*Oum Hairan*
*Regular 500, VIP 1k, V-VIP 2k via 9031307566 Fauziyya Tasiu Umar Opay Evidence of payment 09031307566*
*Ga masu son a tallata musu hajojinsu ƙofa a buɗe take zamu tallata muku kasuwancinku cikin aminci da rahusa, kudai ku tuntuɓi wannan number 09031307566.*
https://arewabooks.com/u/oumhairan1
*Page 9-10*
Cik tunanin Samha ya tsaya Zuciyarta ta buga da ƙarfi ta ƙame ƙam a inda take jiyo yanda ihun yake ƙaruwa a wannan parlour matar tana wani irin kuka tana roƙon a barta ta gaji ƙarfinta ya ƙare amma babu alamun an barta ɗin tun Muryarta na fita Saida ta daina furuci ta koma wani gunji da shassheƙa me sanya zuciya karaya, guri Yadam ya nuna mata yace ta zauna, ta zauna a ɗan tsorace tana kallon duk wata kusurwa ta parlourn Yadam ya danna wata na'ura can sai ga wasu mutane nan ɗauke da kayan ciye ciye suka sanya bisa table ɗin daya kawo kansa gaban Samha da Yadam, so take ta ɗauki wani abun ta sanya a cikinta amma tunanin halin da wannan matar me kuka take ciki da tunano irin wacce azaba ce tasa take furucin ta gama rayuwa a wannan Daula, shin me akeyi mata? Bata kai ga samun amsa ba wasu ƙartan mata suka shigo parlourn rirriƙe da wata mace tana kuka tana ihu harda barin wasiyyar idan ta mutu a kaita Casablanca a binneta a kusa da kabarin mahaifinta domin shine ya jefata a wannan masifa. Kan Samha ƙara kullewa yayi musamman lokacin da aka shiga da wannan mata tana kuka tana ihu waɗannan mata majiya ƙarfi suka ɗauko wannan me ihun jini yana zuba a jikinta suka wuce da ita, ta ƙarshen da alama ta nuna itace shugabar su ta tsaya tace “Likita Samha Sultan yace kiyi treatment Lalla Jalila......"
Wata muguwar kartawa cikinta yayi ta dafeshi da sauri ta kalli Yadam, shima Kallonta yayi da fuska mara annuri yace “Yana cikin ayyukanki" tsam ta miƙe jikinta babu wani duk nau'i na ƙwari ta bi bayansu zuwa wani ɗaki da taga sun shiga da wannan mata, Saida ta kawar dakai ganin yanda suka bajeta a saman wani gado jikinta babu komai sai wani towel da suka lulluɓawa al'aurarta, cike da rauni.
Samha tace “Bansan ta ina zan fara ba kuyimin bayani bansan damuwarta ba" sauran Hadiman duk ficewa sukayi ya rage daga Samha sai wacce tayi magana a parlourn, matar tace “Sunana Basrah Nice babbar hadimar Sultan Rashid mai kula da shige da ficen matansa, wannan itace Lalla Jalila Amaryar Mai martaba ce watan ta biyu a wannan masarauta, wannan ɗinkin da zakiyi mata shine ɗinki na uku kenan da za'ayi mata, ta kasance mara juriya gata da gautsi duk sanda Sultan ya kusanceta sai ta yage" cikin tashin hankali Samha tace “Saikace tsumma tayita yagewa ana ɗinketa wanne irin zalumci ne wannan, idan ta gaza a haƙura da ita mana ta koma gidan iyayenta" tunda ta fara maganar Hadima Basrah ta zuba mata idanu tana mata murmushin rashin sani yafi dare duhu irin na da Kinsan meye a gabanki da baki furucin nan ba.
Fara duba Matar tayi tana rintse idanu jikinta na rawa ta fara duba kayan aiki abin mamaki ɓangare kamar asibiti haka yake komai na amfani akwai, haka tana hawaye da taimakon Basrah ta ɗinke Lalla Jalila ta zauna tayi zugum Zuciyarta ta cika da duhu wannan rashin imanin yayi yawa koda batasan Sultan ba taji ta cika da tsananin tsanarsa, wannan wacce irin rayuwa ce ta kama karya da rashin tausayin na ƙasansa, har yanzu tana jiyo ihu ta ɗago ta kalli Basrah tace “Nifa na kasa gane komai waccan da take ihu fah ita meye tata damuwar?" Ɗagowa Basrah tayi tayi murmushi tace “Lalla Najjisa kenan ita ce babbar matar Sultan Jiya ma a nan ta ƙarasa kwana saboda doguwar sumar da tayi a lokacin da Sultan ke tarawa da ita......"
Zaro ido Samha tayi tare da dafe ƙirji tace “Na shiga uku suma kuma? Wai wahala ce da sex har haka dama?" Da mugun mamaki Basrah take Kallonta tace “Ke bakisan yanda sex yake ba?" Cikin tausayin kai tace “Ni ban taɓa yin aure ba" jinjina kai Basrah tayi tace “Kuma ko Saurayin da zaki bawa dama ya kaiki wannan duniyar mai daɗi baki taɓa yi ba? Likita Samha Jima'i nada matuƙar daɗi da haskaka zuciya musamman idan kikayishi da wanda kikeso kuma wanda ya iya kama sitiyarin abin, saidai su a wannan gida matan Sultan basu taɓa sanin daɗin jima'i ba saboda wata jarabta da Allah yayi musu da HARIJIN SARKI mafi ƙaranci a rana Sultan yana kwanciya da mace biyar a tsayin wayewar gari kuma kowacce yana mata cin sama da 2 hours idan kuwa abin ya juyo yakan ƙara ma akan biyar ɗin da biyu ko uku kuma kowacce sai ta fita a hayyacinta yake ƙyaleta, ke a takaice dai a yanda naji gurin Kasirsh Sultan yakan ɗauki wata guda ne baiyi release ba kuma Joystick ɗinsa bata kwanta ba"
Ji sukayi an Turo ɗakin da ƙarfi suka ɗago a tare, zubar da Lalla Najjisa akayi a wani gadon itama Samha ta miƙe cike da tashin hankali itanma taimakon gaggawa take buƙata, wata likita ce tazo ta cajeta tsaf ta sauke ajiyar zuciya tace wannan karon bata ƙaru ba" cikin rashin sanin furucin ya kufce mata tace “Au su kullum a yage suke kenan abin ma ya zama jiki a garesu?" Kafin akai ga bata amsa wata Hadima ta shigo tace “Wai likita Samha taje inji Sultan" gaban Samha ne ya faɗi ta kalli Basrah, tayi ƙas da kanta cikin rashin abinyi ta ɗauki kayan aikinta ta fice daga ɗakin takawa takeyi ba tare da yasan inda take saka ƙafarta ba har ta isa parlourn da suka zauna ɗazun, har yanzu Yadam yana gurin kamar gunki. Kallonta yayi tare da nuna mata wata ƙofa ta tsaya cik tana kallon ƙofar tana Kallonsa ya jinjina mata kai yace “Sultan Baison jira yana buƙatar taimakon gaggawa kije kiganshi" wani yawu ta haɗiye muƙut ta ƙara jan siraran ƙafafunta ta danna bottle na ƙofar ta buɗe, Innanillahi nan Samha ta manta da tashin hankalin baya ta shagala da kallon wannan parlour a ranta tana tambayar kanta wai parlour nawa ne a wannan sashi ne? Batasan da mutum a gurin ba Saida taji anyi gyaran murya tayi wani firgigit ta dawo hayyacinta tare da sauke idanunta kan mutumin dake zaune da mugun sauri ta haɗe da jikin bango tanajin wani fitsari na neman ƙwace mata.
Ƙasa tayi da idanunta tanajin yanda Zuciyarta ke harbawa fiye da aikinta, a fili tace "wannan wacce irin duniyar masifa na shigo Ni Samha ƙato a tuɓe....." Maganar ce ta maƙale lokacin da taji hucin mutum a kusa da ita, ta ɗauke numfashinta cak jin ya sanya hannu ya ɗago fuskarta yace “Barka da zuwa Daulata Likita Samha El-Fahri."
Hatta iskar da take saƙa saida ta tsaya mata cak,
Sarki Rashid Ibn Fayyad Al-Zirkan.
Yana tsaye a cikin duhun hasken fitila, rigar sarauta mai baki da zinariya a jikinsa buɗaɗɗiya da bata rufe sirrin ƙirjinsa da ƙirarsa ta sadaukan gaske ba, idanunsa suna kallonta kai tsaye kamar suna binciken zuciyarta, Ta ji sanyi ya ratsata Ba tsoro ba ne, wani irin nauyi ne da ta kasa fassarawa ,Ta sunkuyar da kai cikin ladabi, tace cikin murya mai rauni
“Ya mai girma, ni ce likitar da aka ɗauko daga Fes. An ce ina da alhakin kula da lafiyar Mai Martaba…”
Tsayawa yayi kusa da ita, har ta ji ƙamshin turarensa mai matuƙar daɗi Ya ɗan murmusa amma idonsa bai nuna murmushi ba yace “Kin san dalilin da yasa aka kiraki?” Girgiza kai tayi tace “A’a, Mai Martaba. Na zo ne da niyyar yin aikin da aka ɗora min kawai” Ya yi shiru tare da maida idanunsa ga kallon hasken glub ɗin ɗakin idanunsa suka yi wata irin walƙiya kamar wuta, Sannan ya ce cikin sanyi “To, likita… ki shirya don yin maganin ciwon da babu likitan ya taɓa ganin irinsa.”
Ta kalle shi a hankali, tana ganin wani yanayi mai zurfi a cikin idonsa haɗin azaba, iko, da sirri.
A cikin zuciyarta, wata murya ta ce:
“Wannan ba kawai majinyaci bane… akwai wani abu da ya fi jiki.”
Amma ta share
Ta lumshe idonta, ta ce cikin nutsuwa
“Insha Allah, zan yi iyakar ƙoƙarina.”
Ya ɗan matsa kusa sosai, har muryarsa ta zama kamar sirri a kunnenta ya ɗora hannunsa a kuncinta ya zagaya zuwa kan laɓɓanta yace “Samha… a nan, iyakar ƙoƙari na iya zama haɗari”
Sai ya wuce cikin duhu yabar ƙamshin turare da nauyin tunani a bayansa Ta tsaya, tana kallon ƙofar da ya ɓace ta ciki, tana jin zuciyarta tana bugawa kamar tambaya
“Me yasa nake jin kamar na san wannan mutumin tun kafin na same shi?"..........
*👑 HARIJIN SARKI 👑*
*Oum Hairan*
*Regular 500, VIP 1k, V-VIP 2k via 9031307566 Fauziyya Tasiu Umar Opay Evidence of payment 09031307566*
*Ga masu son a tallata musu hajojinsu ƙofa a buɗe take zamu tallata muku kasuwancinku cikin aminci da rahusa, kudai ku tuntuɓi wannan number 09031307566.*
https://arewabooks.com/u/oumhairan1
*Page 11-12*
Taɓe baki tayi tana gwada yanda taga yana wani bubbuɗawa yana tafiya cikin iko ta juya zata fita taji an kira sunanta ta tsaya cik ya tako cikin sabuwar shiga yace “Zaki dubani ki faɗamin matsala ta" juyowa tayi