Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 7
fita ya dawo dauke da kayan abincin ya ajiye a gabanta yace “Mamee tace kunyarta kikeji kinqi fita" murmushi kawai tayi ya cire kayansa ya shiga wanka ya dawo sukaci abincin sannan sukayi La'asar yajata bayan part din nasa suka zauna a qasan wata bishiyar mangoro Yana aiki da System dinsa lkc zuwa lkc yana janta da hira. Sai gafda magrib suka koma gda yayi alwala ya fita masallaci itama tayi tata sallar tayi wanka ta canza kayanta ta zauna a parlourn tana kallo sai bayan Isha ya shigo suka fita parlourn akaci abincin dare Mamee ce kawai sai Humaida saisu Abba bayanan suna gaf da gama cin abincin sukaji an bankado qofar parlourn an shigo ana cewa “ina kike baqar munafuka hankakiya maida dan wani naki to kisani kinyi kadan kiyimin qwacen yata aure ne ban yarda ba ban lamunceshi da danki ba waima banda tsabar munafurci Ina ruwanku da rayuwarmu a gdanmu ne munafukai annamimai...." Miqewa Janah tayi ta Isa gaban Mom tace “haba Mom meye haka don Allah meye laifin bayin Allan nan meye sukayi naga taimak...." Dauketa tayi da mari tace “taimakon durun uwarki sukayi Miki shegiya butulu mara sirri ke yanzu bakiji kunyar daukar videon ubanki tsirara ki yadawa duniya ba?" Dagowa Janah tayi cikin hawaye tace “meye aibuna danna aikata hakan shi meyesa baiji kunya wulaqantani ba saini zanji kunyar tona Masa asiri sake daga hannu Mom tayi zata mareta Bashir ya janyeta tare da cewa “haba Mom meye abin tada hankalin?Akan abinda yariga yabar hanunki muma yabar hannunmu ya koma hannun hukuma kawai kije kiyi baccinki gaskiya zatayi halita very soon" janye matarsa yayi Mom nata zage zage babu Wanda ya qara kulata suka shige part dinsu itakam Mamee dama ta rigasu barin gurin. Ganin sun shanyata sun massheta yar iska yasa ta dauki qafarta sumsum ta fita Lkc ya rinqa tafiya sosai Janah ta samu kwanciyar hankali da farko Mom taso dagansu hankali Amma da Bashir yayi Mata kyakkyawan kashedi saita shiga hankalinta ta dainayi musu zarya a gida qarshe ma dauke matarsa yayi suka wucce Lagos kasancewar aikinsa yabar dashi Abuja ya koma Lagos watansu biyu a Lagos Janah ta fara rashin lfy sosai zazzabi amai da ciwon ciki dole sukaje asibiti suna zuwa aka sanar dasu ciki ke gareta wayyoh murna gurin Bashir kamar ya goyata haka suka dawo gida cikin tattali da kulawa ya Kira iyayensa ya fada musu suma sukayi musu murna da fatan alkhairi bayan ya gama wayar ya dawo kusa da ita ya zauna tare da sanya hannu ya dago kanta hawaye takeyi sosai mamaki da tsoro suka cikashi ya dagota jikinsa sosai yace. “Meye Kuma dalilin kukan?" Cikin sanyin jiki tace “inaso ace Nima inada Wanda zan Kira na fada masa abin farin ciki ya sameni Amma banidasu mahaifiyar da zan iya sanarwa damuwata tayi fushi dani akan abinda nasan banida laifin komai akansa [05/05 9:53 pm] Yar Mkrnt: *_NKU_* *_39-40_* Shafa sumarta yayi yana murmushi yace “shine kikemin asarar hawayenki my life ok naji kinaso ki fada musu kinsamu ciki to me kikeso suyi miki?" Shiru tayi saikuma abin yabata kunya ta rufe idonta tana dariya shima dariyar yayi yace “jibi zamuje Kano akwai wani Abu daya taso na gaggawa akan case dinki da Dad naso mu qyale mgnr ta tafi a haka tunda abin yariga ya wucce so shi yakasa ganewa yanata yimin barazana da rayuwata dole na daukaka qara a cikin hakanne Mom take sanarwa sudin basune mahaifanki ba wai....? A tsorace ta dago ya sake fadada murmushinsa yace. Wannan mgnr da Mom ta fada ita ta qara hargitsa komai alqalin yace dole sai kinje anyi gwajin qwayoyin halitta idan suka tabbatar da kedin ba yarsu bace to daganan Kuma zaa matsasu su Fadi yanda akayi suka sameki" Dafe kanta tayi cikin sanyin jiki tace “ya Allah" kwantar da kansa yayi a jikinta yace “kada ki wani damu kanki Babu abinda zai faru sai alkhairi" da wadannan kalaman ya mantar da ita komai Saida yaga ta samu nutsuwar zuciya sannan ya shirya ya fice daga gdan ya nufi office dinsa. Kamar yanda ya tsara din hakance ta faru kwanaki biyu suka dauki hanyar Kano a gdansu Mamee suka sauka an gyara musu part din nasu tsaf Mamee ta tareta da fara'arta tana tambayarta ya jikanta Amsawa tayi cike da kunya ta dan zauna ta huta a parlourn sannan ta nufi part dinsu ta kwanta domin hutawa Saida ya shigo sannan sukayi wanka sukayi azahar ta fita ta tarar da Mamee a kitchen ta Kama Mata aikin sunayi suna hirarsu Nan mamee take Bata lbrn irin badaqalar da aketa tukawa da dad shi yace ita yarsace Mom tace ba yarsu bace ita yanzu haka kotu tabada adadin kwanakin da zaa qara zama inda aka buqaci Mom ta gabatar da shedarta. Jikin Janah ya qara sanyi tace “a gdan marayu suka daukoni ko Mamee? Ni dama rayuwata tayi Kama data mara gata Allah dama...." Rufe Mata baki Mamee tayi tace “koma dai mene Murjanah qaddararki ce Kuma kinsan Babu mutumin da yake qetarewa qaddararsa yanzu Rana da lkc kawai zai bayyana Mana koma" mirgina Kai tayi cikin sanyin jiki a haka suka gama aikin Janah ta shige dakinta ta rungume pillow tana hawayen tausayin kanta Koda yake wani bangare na zuciyarta tanajin dadi da addu'ar Allah ya tabbatar Dad ba mahaifinta bane. ********* Ranar litinin 3/3/ kotun ta qara zama ranar dole Janah Saida ta halacci zaman kotun inda duk take a darare tana zaune ne kusa da mijinta da surukarta inda gabadayanta batada kuzari musamman lkcn da taga an shigo da Dad ya kalleta yayi qwafa ta sunkuyar da kanta daidai lkcn Mom itama ta shigo ita da lauyanta tare da wasu mutane guda uku dukkanninsu zama sukayi kowa da abinda yake tunani kotun ta dauki Shiru na Dan wani dogon lkc kafin a fara gabatar da shari'ar wata Mata da miji sannan akazo kan tasu tashin farko Murjanah aka fara Kira gabanta ya bada wani ras har saida Bashir ya tallafota tare dayi Mata murmushin qarfafa gwiwa ya miqar da ita ta fito Saida ya rakata har gurin da aka nuna Mata sannan ya juya ya koma ya zauna itadai gabanta cigaba yake da faduwa ta jiyo muryar me gabatarwa Yana cewa “baiwar Allah munason jin cikakken sunanki da alaqarki da wadannan mutane guda biyu Gen Habib da Hajiya Bara'ah" Cikin rawar murya tace “Murjanah Habib Macchido" kallonta kowa yayi kafin me gabatarwar yace “nasabarki dasu fah?" Shiru tayi na dan lkc kafin ta dago idanunta da suka ciko da qwallah ta saukesu akan Bashir Jinjina Mata Kai yayi hakan yasa Mata qwarin gwiwa tace “iyayena ne" sake dubanta yayi yace “iyaye koko mahaifa?" Sake bashi amsa tayi da cewa “mahaifa" duba takardar yayi yace “waye Bashir Mu'az a gurinki Kuma meye alaqarki dashi?" Dubanshi tayi ya kanne Mata ido tace “mijina ne rayuwata tane shidin" take gurin ya dauki ihu Saida Mai shari'a yayi tsawa sannan aka nutsu akaci gaba da karanto Mata qunshin tambayoyi tana amsawa ciki harda tambayar meye asalin abinda ya kawo baraka tsakaninta da iyayenta har ta yanke shawarar barinsu ta koma hannun aminin mahaifinta inda har takai ga sunyi Mata aure batare da sahalewar iyayenta ba?" Kamar yanda Bashir ya karanta Mata haka ta rinqa bada amsa abinda ya kada zuciyar lauyan Dad ya tashi domin dakatar da lauyan da yake kare bangaren Bashir din inda alqalin ya hana faruwar hakan daga bisani ne bayan abubuwa sun lafa lauyan yace “Hajiya Bara'ah takasance mahaifiya a gareki inda Gen Habib Macchido ya kasance mahaifi so yanzu kuma wata ta bullo mahaifiyarki tayi da'awar basune mahaifanki ba meye kika sani game da hakan?" Girgiza kai tayi tare da share hawaye tace “bansan komai game da hakan ba Kuma bazan iya cewa komai ba sune suke da baki magana Nima su nake sauraro" gdy lauyan yayi ya koma ya zauna me shari'a yabawa lauyan Dad damar yimata tambayoyi Amma yace bashida abin cewa. Nan aka sallameta ta koma mazauninta inda aka Kira sunan wata Mata ta fito da alamun matar taga gararin rayuwa ta hau saman gurin tsayawar alqalin da kansa yace ta gabatar da kanta da abinda ya kawota. Cikin kuka ta fara da cewa “Sunana Dr Abidat Solomon Asalina Ni mutuniyar Ibadan ce aiki ya kawoni Abuja Inda nake aiki da wani babban asibiti me zaman kansa ranar wata Litinin Dana manta date din wasu Mata da miji sukazo asibitinmu lkcn nice akan aiki da fari nayi tunanin petiant ne Saida muka zauna suke zayyanemin qudurinsu ba wani Abu mijin ya fadamin ba sai cemin da yayi suna buqatar jariri namiji sabuwar haihuwa daga naira million daya zuwa million goma zai iya bayarwa domin cikar burinsa. _*NKU*_ _Last page_ _And ina me matuqar baku hqr na dakatar da rubutunnan da nayi batare da neman uzuri a gurinku ba wannan ya fsrune sakamakon wasu qwararan dalilai ina fatan zaku fahimceni kuyimin uzuri banyi don wulaqanci gareku ba._ _41-42_ Numfashi Abidat Solomon ta sauke kana taci gaba da cewa “Da farko naqi aminta da qudurinsu duk da kasancewar ba sabon abu bane a gurina amma ganin cewa da gaske sukeyi matar da qaton cikinta na tsumma tana roqona na taimakesu na basu baby kada asirinsu ya tonu, so sai tabani tausayi na yanka musu kudi masu tsoka suka bani advance suka tafi akan cewa muna samun baby zan kirasu. Haka kuwa akayi kwanaki uku da faruwar lamarin matar wani Minister tazo haihuwa cikin ikon Allah ta haifi yara biyu duka mata saidai bata cikin hayyaci, taimako daya na samu abokin aikina ya fita dauko jini nayi sauri na sace yarinya daya nakai bayi na bude abin flushing nasata a ciki, mukaci gaba da kula da petient dinmu har tasamu dama muka kaita dakin hutu ita da babynta sannan muka fadawa danginta sukayita zuwa ganin mejego da yarinyarta, koda aka kira minister akace masa matarsa Aysha ta haihu baby girl sai yace ai sunje Egypt ance musu yara biyu ne mata, Qwarai zufa ta rinqa ketomin domin itama mejegon yara biyu tace tana gani idan sunje scanning Cikina ya duri ruwa sosai na shiga rudu ganin asiri na yana shirin tonuwa domin da gasken gaske wadannan mutane sun kafe akan yaransu biyu ne koda naga abin ya dan lafa saina sulale dama lkcn tashina ya kusa naje nasa jaririyar a cikin jakkar kayana nayi sallama da kowa na fuce. Ina zuwa gda nayi mata wanka nasa mata kaya na dauki waya na kirayi Gen Habib Macchido na fada masa an samu baby amma baa samu namiji ba mace aka samu, da farko Hajiya Bara'ah taso taqi yarda ta amshi macen amma da sukazo sukaga yarinyar fine girl sai suka cikamin kudina harda qari suka karbi yarinyar nan sukace sunason muje dasu gdansu azuwan nice na karbi haihuwar cikin dare akayita. Haka akayi muka tafi na kwana a gidansu nidai bacci na kwana inayi amma asubar fari sai naji gdan ya fara cika da mutane nan mukayi sallama na tafi nabar Hajiya bara'ah nata narkewa ita a dole me jego sai liqawa babyn nono takeyi taqi amsa hakan yasa suka sake nemana na rubuta musu magani da madara, nidai daga wannan lkc ban qarabi takansu ba sune dai suke bibiyata sunamin Ihsani haka rayuwa taci gaba da tafiya bamusan ya akayi ba nidai naga an sallameni daga aiki a asibitin da nake wannan dalilin yasani komawa Ibadan naci gaba da rayuwata acan cikin qunci abubuwa sun qara lalacewa nakasa samun aiki sai wahalar neman abinda zaa kula da kai kasancewata marainiya babu uba balle uwa kwatsam kwana uku da suka wucce naga dirar motoci a qofar shagona sukayo wuff dani wannan shine abinda na sani game da wadannan bayin Allah" Shiru kotu tayi tsayin lkc kafin daga bisani alqali ya magantu ta hanyar bada umarnin abawa shaida na gaba dama ya fito ya fadi abinda zai fada, nan take shaidun Momy suka rinqa fitowa daki daki suna bayani inda shikuma lauyan Dad ya kafe kaida fata a qarshe dai saida likitoci suka shiga cikin lamarin domin shari'ar tazo qarshe amma ankasa gane me gsky tsakanin mom da Dad dole tasa aka shiga bincike na qwaqqwafin records na abubuwan da suka faru shekarun baya a asibitin da aka saci jaririyar anan aka gano cikakken sunan matar ministern dashi kansa aka fara bibiyarsu tashin farko da Alh Mahmoud Abbas ya bawa Bashir damar zuwa su gana a lkcn da yabada umarnin a kawowa baqinsa ruwa wata matashiyar budurwa ta shigo dauke da tire din kayan motsa bakin ba bashir ba hatta Mahaifinsa da suke tare da lauyan gwamnati saida sukayi kamar su dige don tsananin mamakin kamar da take tsakanin budurwar da sukaji an ambata da Maryam lauyan ya kasa jurewa ya magantu da cewa “Dr Bashir wannan ai matarka ce ko?" Girgiza kai yayi yace “Janah batakai wannan haske ba kuma tafi wannan jiki kadan sannan da ciki a jikinta" Jinjina kai sukayi nan suka zayyanewa Alh Mahmoud Abbas abinda ke tafe dasu yayi jim yana tunani kafin daga bisani ya dago yace “ina yarinyar take?" Dagowa Bashir yayi yace “tana nan cikin garin abuja suma suspect din suna hannu dukkansu idan babu damuwa zamu iya zuwa ayi duk abinda ya dace tabbas Murjanah yar'uwar Maryam ce" Miqewa sukayi dukkansu suka dunguma suka nufi gdan Bashir dake nan qasan inda suka samu Alh Mahmoud Abbas harda Hajiya Hafsa da maryam da Khamal da Jamal qannensu itadai Murjanah tana dakinta a kwance abin duniya yayi mata zafi tajiyo hayaniya a parlour ta miqe ta dauki hijjab dinta tasa zuwa yanzu cikinta yayi nauyi sosai daqyar take daga qafarta ta fita parlourn ja tayi tayi turus lkcn da sukayi ido biyu da Maryam gabanta ya bada wani ras suka zubawa juna ido suna kallon kallo bata hango bambamcin dake tsakaninta Maryam din ba saida taji Hajiya Hafsa tace Alhmdllh tagwai na sun dawo" sai suka nufeta da gudu suka rungumeta Hajiya Hafsa ta fashe da kuka tana cewa wlh Alh basai anyi wani gwajin jini ba wannan yatace ta cikina lkcn dana haifesu tabbas biyu na haifa amma aka sace daya akace bana cikin hayyacinane shiyasa naji kamar biyu" Shi kansa Alh Jikinsa yayi sanyi share hawaye kawai yakeyi ya matsa ya kamo hannun Murjanah yace "taho yata" sai kuwa ta fada jikinsa ta rushe da kuka tana cewa “tabbas qaunar jini a ruhi take ahli basa buya zuri'ah inta hadu da zuri'ah jini ke amsar saqo an cutar dani an rabani da gatana an gurbatamin rayuwa saboda son zuciya Allah ya Isana bazan taba yafewa duk me hannu cikin lalacewar rayuwata ba....." Rufe mata baki Alh Mahmoud Abbas yayi yace “yi shirunki yata nima bazan yafe ba" daqyar Bashir ya rarrasheta yajata suka fita babban asibitin qasa na National hospital Abuja suka nufa inda akayiwa ma'aikatan inda Dad yake tsare waya suka fito dasu nan akayi musu duk wani abu na gwaje² tsakanin Dad da Abba kawai kallon kallo akeyi yama rasa irin matakin dazai dauka tun baimaji asalin abinda ya faru tsakaninsa da yarsa ba. Kwana uku aka basu na result suka koma gda nan fah Maryam ta tubure ita gurin yar uwarta zata zauna itama ta kafe saidai su tafi tare shi kansa Abba yanason ya gana da yar tasa amma yakana irintasa tasa yace suyi zamansu idan sun huta sazo ita da Maryam din Mahaifin Bashir ne yace baza'ayi hakaba su tafi itama taji dumin iyayenta Bashir baiso ba saidai bazai iya cewa komai ba da kunya hakanan ta kama hannun yar'uwarta suka shiga hada kaya yana kallonsu saida suka gama Maryam tace “amma Yaya Bashir saita haihu zata dawo ko?" Harararta yayi tayi dariya taja trolly din ta fita Janah ta miqe ta matsa gabansa ta ruqo hannunsa saita fashe da kuka ta rungumeshi shima ya rungumeta tace “bazan taba mantawa da halaccinka gareni ba Yaya Bashir kasoni tun lkcn da ban cancanci asoni ba ka qaunace ni ka nunamin qauna inasonka mijina Allah yabarmu tare yabani ikon faranta maka" matseta yayi yana sunsunar wuyanta yace “tun kina cikin tsumman goyo nake sonki Janah da sonki zan mutu nidai burina kada ki canzamin saboda ganinki tsakanin danginki kinji, ki kulamin da kanki zan tafi kano yau nima akwai wani aiki da zanyi na sati daya a Aminu kano idan na gama lkcn kinsha nonon da bakisha ba kinqoshi sai mu dawo ko?" Lakace masa hanci tayi ya zaro kudi ya bata me yawa yace “ki kulamin da babyna" da haka suka fita suka koma parlour sukayi sallama suka tafi suma suka dauki hanyar kano, Tunda taje gdan iyayen nata take samun gata qauna sosai Hussainanta da yan uwanta suke nuna mata ga iyayenta komai Janah, abin har kuka yake sanyata, kwananta biyar a gdan da yamma suna taya Hajiya aiki a kitchen ta tsugunna zata dauko flat bayanta ya riqe tayi qasa da sauri tana kiran sunan Allah dukkansu sukayo kanta da sauri suna riqeta ta sake dafe mararta tana riqe da hannun Hajiya tace “wayyoh Hajiya kiramin Yaya Bashir mutuwa zan...." Rufe mata baki tayi tace “aa ba mutuwa zakiyi ba ina tunanin haihuwa ce" nan sukayi ciki da ita Abba suka kira suka fada masa abinda ke faruwa nandanan ya juyo gda lkcn abun yaci tura yana zuwa yace su tafi asibiti suna zuwa dake ansan matar waye a asibitin babu bata lkc sukayi mata duk abinda ya dace aikuwa kamar sun janyo ciwon nandanan sai haihuwar tazo da gaske ta haifi yarta mace kyakkyawa me kama da Bashir qatuwa da ita nurse din na zuwa ta fada musu Abba ya kira Mahaifin Bashir ya sanar dashi haihuwar kafin wane wannan haihuwar ta cika dangi Ai Bashar kasa jiran satin yayi ya dauko mota ya nufo abuja gani yake idan ya jira jirgi ma bazaije da wuri ba bakwai na dare sai gashi a asibitin lkcn janah na baccin hutu saboda tasha dinki babyn tanada girma saida aka qarata, Yana shiga Maryam da Hajjah kakarsu Janah ta wajen uwa suka haushi da tsiya shidai dake ba mai surutu bane dariya kawai yakeyi ya matsa ya duba Janah ya gyara mata allurar ruwan dake jikinta ya dauki jaririyar a gadonta ya zuba mata ido hawayen farin ciki suka zubo masa yace “Alhmdllh ya Allah" Washegari Mamee da zugarta suka dira a Abuja sunzo ganin baby Bashar yaso yima yarsa Huduba da Hafsa sunan mahaifiyar Janah amma janah tace aa Fatima zaasa mata sunan Mamee murmushi yayi yace “shikenan na hqr nanda one year zan qara baki wani babyn kinga saimu samu Hajiya" duka takai masa ya goce daidai lkcn da wayarsa tayi ring sunan Abbansa yagani ya kara a kunnensa suka gaisa yace “Yanzu aka kirani daga Prison din da Gen Habeeb yake wai ya zuciyarsa ta buga ya mutu bayan tabbatar masa da akayi yanada HIV dagashi har matarsa yanzu haka mun dauki gawarsa mun tafi Mambila acan zaayi masa sutura" Allah ya jiqansa kawai yace ya aje wayarsa yaci gaba da wasa da babynsa. Kwana bakwai akayi suna na bijinta abinka da jikar fari ta kowanne bangare a sunan ne Nasir Abokin Bashar yaga Maryam ya nace akan yana sonta to dama matarsa ta mutu cikin ikon Allah suka daidaita kansu wata biyu akasha biki amarya ta tare a gidanta itama anan Abuja rayuwa tanata albarka abubuwa duk sun shude sai tarihi inda Momy ciwo yaketa cinta a tsaye taqi yarda cewa tanada HIV sai yawonta takeyi janah nason taimaka mata amma iyayenta da mijinta sun hanata ga rashin miji ga rashin aikinyi tun lkcn shari'ar nan aka koreta a aiki ga ciwo duk wani abu da take dashi ta siyar a gurin yawonta taqi ta daina fita qasashe harkar lesbian dinta wata tafiya dai da tayi bata dawo ba. Tunma ana nemanta har an hqr a cikin shekara ta biyu da haihuwar Janah ta qara sullubo danta namiji wanda yaci sunan mahaifinta Mahmoud wata daya tsakani Maryam ma ta haifi diyarta mace akasha suna rayuwa taci gaba da tafiya cikin jin dadi wadata da kwanciyar hankali zuri'ah nata qaruwa soyayya na bunqasa komai yana tafiya daidai cikin hukuncin Allah. _Tammat Bi hamdullah_ _A qarshe dai ina qara baku hqr na tsayawata cik da rubutun wannan littafi sakamakon laluri daya addabi rayuwata watannin baya lkcn da naji sauqi kuma nayi loosing phone dina da fatan duk wanda na batawa zaiyi hqr, me qafa hudu ma yakan fadi balle me biyu am sorry please my luvly Fan's sai mun hade bayan sallah insha Allah a sabbin littafaina guda biyu *ZARRAH* da *DAN MAFIYA(to the world)* tabbas wannan rayuwa tana cike da sammatsi da qalubale shin bakwaso jin meye asalin dalilin da yasa ya zama *DAN MAFIYA* ba? Akwai rikici da rudani cikin wannan cakwalkwallan labari mai sanya zuciya cikin zullumi tabbas an dade baayi tamkarsa ba koma nace baayin ba._ _Takun dai Oum Hairan_ *_Oum Hairan_* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 7 of 7