An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Zinariya
SUNANMU DAYANaja'atu Harüna Saleh
Da
Nura Sada Nasimat
SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
UNANMU DAYA
(Hakki na bibiya)
1
Na
NAJAʼATU HARUNA SAIE
Da
NURA SADA NASIMAT КГ
2 SUNAN MU DAYA-1 ANAJNOOR
HAKKIN MALLAКА (Н)
Nura Sada Nasimat Kt
COPYRIGHT (c)H
Nura Sada Nasimat Kt
SHEKARAR BUGU
2014
GODIYA
Ina mika godiyata ga Ubangina,
mahaliccin kowa da komai, wanda Ya ba ni
dama da ikon rubuta wannan littafi nawa ba
don iyawata ba, sai don kudirarsa na
tabbatuwar rubutuna alkali a cikin al'umma.
GODIYA TA MUSAMMAN
Ga Mijina abin tinkahona, wanda ba ya
gajiya da bukatuna, ina fatan Allah Ubangiji
Ya saka masa da gidan aljanna Firdausi, Ya
daukaka, Ya kiyaye shi daga dukkan sharri,
Allahumma Amin.
3 SUNAN MU DAYA-1
SADAUKARWA
NAJNOOR
Wannan littafi nawa SADAUKARWA
ne ga mahaifiyata Marigayiya Rukayya
Na'iya, ina fatan Allah Ya kai haske a
kabarinta, Ya sa aljanna Firdausi се
makomarta.
JINJINA GA:-
Alhaji Haruna Sale (Abbana)
Alhaji Sada Isah Mani (Babana)
Alhaji Ibrahim Na'iya (Kawuna).
TA'AZIYYA
Muna taya Sadiya Garba Yakasai
ta'aziyyar rashin mahaifiyarta da ta yi mai
suna Hajiya Hauwa'u Ahmad (Umma). Allah
ya kai haske a kabarinta, ya ba wa 'ya'yanta
hakurin juriyar rashin, amin.
TSOKA DAYA A MIYA
Ban manta da farin cikin nawa ba, wato
dana Yusuf Nura Sada (Faanah) Allah ya raya
mana shi bisa tafarki madaidaici.
4 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI
Aisha Aliyu Zamfara
Amina S/Unguwa
Aminatu Jos
Bilaratu Kebbi State
Fatima Mainasara
Fatima Ahmad Gwale
Hadiza Daki Tara
Hadiza Sama'ila
Hafsat F/Samji
Hafsat Katsina
Hafsat S/Unguwa
Halima K/Marusa
Hassana Adamawa
Hussaina Zaria
Khadija Sadi Sidi Sharifai
Malama Hindatu Zaria
Malama Hindatu Kcbbi
Maryam Bomo Zaria
Maryam Lawal Isma'i2
wHauwa Adam CRO
Fatima Umar Maiduguri
Maimunatu Azarc (Munari)
5 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
Naja'atu Nura (Najnoor)
Nasima Dorayi
Lubabatu Abubakar (Maman Ummi)
Rabi Yahya
Rukayya Maiduguri
Rukayya Ahmad (Maman Zuhra Sharada)
Rukayya Yola
Sa'adatu Umar Abubakar
Sadiya Usman Zaria
Zahra'u Zaria
Zainab Yusuf Sulaiman
Haj. Asma'u Shchu Shanono
Hadiza Zamfara
Asiya Zamfara
An buga a Karkashin kungiyar Zinariya
Writter Assocition Katsina (ZWAК).
6 SUNAN MUDAYA-1 NAJNOOR
Ka ribaci Kuruciyarka kafin tsufanka
Ka ribaci lokacinka kafin mutuwarka
Ka nibaci arzikinka kafin talaucinka
Ka ribaci lafiyarka kafin rashin lafiyarka
Typesetting:
Nura Sada Nasimat Kt
MANAWA BUSINESS CENTER.
Link Anis Bookshop
08131994808
BUGAWA DA YADAWA
FANCY PUBLISHER
S/unguwa Kwabren Dorawa Katsina.
08131994808
7 SUNAN MU DAYA-I NAJNOOR
SUNANMU DAYA!
asu mutane sukan yi kulli Wa cikin DUHU, wanda a
tunaninsu su kadai ne suka
san Küllin da suka kulla, ba sa tunanin
akwai wasu halittu da duhun shi ne
HASKENSU, da ke haskake musu u kullin
masu kulli Firit! Za su yi a cikin küllin
komai ya warware, sai dai ba su samun
damar kutsa kai cikin sha'anin masu kulti,
har sai SHUGABA, SARKI ya fuwace
musu.
Hakika zuciya tana kusantar
shaidan, kusantar shaidan kuma taбewa ce,
rashin tsarkake zuciya na kusanta bawa
halaka.
Rashin hakuri yana kawo aikin da na
sanin da za a jima ana cizon yatsa
Hakika kuma ba karya ba ne,
HAKKI NA BIBIYA kamar yadda dan
kwikwiyo ke bin ubangidansa.
8 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
Yana sanye da farar jallabiyya mai
wando, ya saka hular dara a kansa,
hannunsa rike da carbi ya fito daga
makeken gidan da ya gaji da haduwa,
saboda kyau da tsarin fasali. Kallo daya za
ka yi wa fuskarsa ka san yana cike da
nutsuwa da cikar kamala.
Kai tsayc wani masallaci da ke cikin
layin ya nufa, tafiyarsa kanta abar so da
sha'awa ce, musamman shigar tasa da ta
saje da launin fatar jikinsa, abin sai ya ba
da sha'awa.
Wankan tarwada ne mai silki da jaja,
dogo, kuma tsayayyen namiji, ingarman
gaske na hakika. Idan yana tafiya sai ka
dauka toron giwa ne, wannan kasaita tasa
tun yana yaro haka yake da ita, har abin ya
zame masa jiki.
9 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
Yammaci nc sosai a lokacin, domirn
karfc biyar ta gota, haka yakc yi duk iri n
wannan lokacin ya ke shiga masallaci idaın
ba shi da yawaitar aiki a wajen aiki. Ba z ai
fito daga masallacin ba har sai an yi sal lar
isha'i da shi, sai ko idan wani babban uz uri
garc shi.
Sannu a hankali ya iso c'ikin
masallacin, sabanin kullum da shi kadi ke
fara halartar masallacin kafin daga bisani
gab da magriba kenan masu kula da
hidimar masallacin su karaso. Yau kaım ya
tarar da wani matashin saurayi zaune..
Jin motsin shigowa cikin mas allacin
ya sa matashin dago da kai, ya dubi mai
shigowar.
Kallo daya suka yi wa juna, ABIDU
ya ji gabansa ya fadi, hakan kuwa ba ya
rasa nasaba da abubuwa biyu da suka shige
shi a lokaci guda. Na farko, mamakin
ganin matashin a cikin masallaci a wannan
10 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
lokacin. Na biyu, tunanin kamar ya taba
gani da sanin fuskar matashin.
Kasancewar ya san hira a cikin
masallaci ba abu ne mai kyau ba, addini ya
haramta sai in ya zama dole, don haka ya
boyc abubuwa biyun da suka damu ransa
tunda ba su zama dolen da hira za ta
wakana a tsakaninsu a lokacin ba.
Kai tsayc ya nufi lokar da ake ajiye alkur'ani, ya dauko Tafsccrul-Kur'an ya
samu guri daga nesa da matashin ya auna.
Ya budo Suratul Ankabut inda ya
tsaya a saukar da yake kokarin hattamawa
ta wannan makon kc nen,
Ya soma karatun nasa a cikin
zuciyarsa, yayin da shi kuma matashin ya
kc kwararo Kira'arsa cikin Suratul
Ali'imrana, tamkar Baralaben asali
mazaunin Madinatul Munawwara.
Kasa jurewa Abidu ya yi da jin
yadda matashin ke lailayo kira'ar cikin
11 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
salon burgewa, sai da ya dago kai cike da
tsananin mamaki ya dube shi.
Abin da ya lura da matashin ma shi
ne, ashe ba alkur'anin yake dubawa ba, da
ka yake kawo duk abin da yake kawowa.
Wannan na nuna cewa, shi din saukakke
ne da ya yi tilawa sau ba adadi, har ya san
ba wa kowanne harafi hakkinsa yayin
karantawa ba rubutawa ba.
Koda yake bai kamata ya yi
mamakin ba alkur'ani matashin yake
dubawa yayin karatun ba, domin lokacin
da ya shigo cikin masallacin bai ga littafi
ko daya a hannunsa ko a gabansa ba, illa
carbi wanda da farko ya dauka lazimi yake
yi. To amma abin al'ajabinsa bai wuce ta
ya aka yi matashin yana da wannan
dumbin ilimin ya taba riskarsa a wani
bigire da bai dace ba?
Saurin korar shaidan ya yi daga
gurbin zuciyarsa da ambaton.
12 SONAN MU DAYA-1 NAJNOOR
sbonnslillahi wa'inna ilaihi raji'un
Ganin shaidan yana neman assasa
masa tunanin da zai dauke hankalinsa daga
bautar Ubangijisisy n
swowWani abu da ya kara daure masa kai
shi nc, kamar matashin. ya san ko yana
hangen shafin surar da yake karantawa, sai kawai ya ji ya saki surar Ali'imrana da
yake karantawa ya koma surar Ankabut,
kuma daidai ayar da yake karantawa ya
datsa, wato aya ta talatin da daya.
rKin mayar da kai ya yi a kansa, ya yi namijin kokarin ci gaba da karatunsa, har
tsayin lokacin da masu kula da masallacin
suka 70ival skusq sy ost ab sbnsw IdIS
at a mike zuwa waje don ba su damar
da za su share cikin, kamar yaddalyake
idan suka zo kowa fita ya keaımili nidmuk
A jikin wata bishiyarbdalbejiyaya
jingina bayansa yana mail duban? kofar
masallaci don ganin fitowar matashin.dYa
II SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
salon burgewa, sai da ya dago kai cike da
tsananin mamaki ya dube shi.
Abin da ya lura da matashin ma shi
ne, ashe ba alkur'anin yake dubawa ba, da
ka yake kawo duk abin da yake kawowa.
Wannan na nuna cewa, shi din saukakke
ne da ya yi tilawa sau ba adadi, har ya san
ba wa kowanne harafi hakkinsa yayin
karantawa ba rubutawa ba.
Koda yake bai kamata ya yi
mamakin ba alkur'ani matashin yake
dubawa yayin karatun ba, domin lokacin
da ya shigo cikin masallacin bai ga littafi
ko daya a hannunsa ko a gabansa ba, illa
carbi wanda da farko ya dauka lazimi yake
yia To amma abin al'ajabinsa bai wuce ta
ya aka yi matashin yana da wannan
dumbin ilimin ya taba riskarsa a wani
bigire da bai dace ba?
Saurin korar shaidan ya yi daga
gurbin zuciyarsa da ambaton.
12 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
б ож Тпрalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
Ganin shaidan yana neman assasa
masa tunanin da zai dauke hankalinsa daga
bautar Ubangiji.
swow.Wani abu da ya kara daure masa kai
shi nc, kamar matashin ya san ko yana
hangen shafin surar da yake karantawa, sai
kawai ya ji ya saki surar Ali'imrana da
yake karantawa ya koma surar Ankabut,
kuma daidai ayar da yake karantawa ya
datsa, wato aya ta talatin da daya.
Kin mayar da kai ya yi a kansa, ya yi
namijin kokarin ci gaba dai karatunsa, har
tsayin lokacin da masu kula da masallacin
suka zo.ixal sknab sy oal b sbne
sta mike zuwa waje don ba su damar
da za su sharc cikin, kamar yadda yake
idan suka zo kowa fita ya kemili mdmоb
A jikin wata bishiyar dalbejiya ya
jingina bayansa yana maik duban kofar
masallaci don ganin fitowar matashin. Ya
13 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
ayyana tambayoyi kwarara da zai gabatar
da su a gare shi, sai dai har lokacin da
masu sharar suka kammala matashin bai
fito ba, ko me ya sa shi bai fito ba?
Suna gama sharar kai tsaye Abidu ya
koma cikin masallacin, yana nan zaune a
inda ya barshi, da alama ma ratse shi masu
sharar suka yi, domin zaman nasa babu
alamar ya tashi tsaye.
Har dai aka gabatar da sallar
magriba, ana gamawa kuma matashin ya sa
kai ya fice, shi ma Abidu da ya hango
fitarsa ya biyo bayansa. Sai me?
Kamar walkiya ko rufa ido! Babu
matashin babu alamarsa, duk kuwa tsawon
da layin yake da shi kafin ka riski kwana.
Ina ya yi layar zana?
Cike da tsananin mamaki ya yi tsaye
yana baza idanunsa ko zai samu nasarar
hango matashin ko da a cikin mutanen da
suke wake da shinkafa a kan layin, ma'ana
14 SUNAN MU DAYA-I NAJNOOR
maza da mata masu wuccwa da wadanda
kc zaunc zaman jiran magrubar ta nuna.
Yanzu kam mamakinsa ya lunka na
dazun linkin ba linkin. Ya dade a tsayсn
yana walainiya da kwayoyin idanunsa,
shiru makatau babu amo babu labari, dole
tasa ya koma cikin masallaci ya ci gaba da
laziminsa har aka sallaci isha'i. Ya gama
addu'a kamar yadda ya sabar wa kansa, ya
fito ya nufi gida.
Daidai lokacin da yakc kokarin
shigowa cikin harabar gidan ya ci karo da
mahaifinsa, Alhaji Nasir Barhim yana
kokarin fitowa daga cikin gida. Fuskarsa
yalwace da fara'a ya се.
ya cc.
"Abidu har ka shigo?"
Abidu ya dan rusuna cike da ladabi,
"Eh Abba".
Alhaji Nasir ya jinjina kai, yana
fadin.
15 SUNAN MU DAYA-I NAJNOOR
"Masha Allah, ni ma zan je gidan
Goggo ne".
amsa.
Abidu ya ce masa.
"Ah, to bari na zo na kai ka".
Cike da jin dadi Alhaji Nasir ya
"Da kuwa ka kyauta, don da ma ina
jin wuyar tukin. Ban san me ya sa ba a 'yan
kwanakin nan sam bana son tuki, ga
Mashkur da yake dan kokarin ma ya
daina".
Abidu ya се.
"Bari dai na sauyo kayan na zo".
Kai tsayc ya shiga bangarcnsa ya
sauyo dogaycn kaya na danyar shadda da
ta sha aikin sama, ya fesa turaren 'Hotice
ya fito zuwa harabar gidan, har Abban
nasa ya shiga gidan gaba na motar mai
zaman banza.
A sukwanc cikin takun nasa na
mazantaka ya budc mazaunin dircba ya
16 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
shiga ya zauna, makullin na makale a
mazauninsa, don haka kai tsayc ya tayar
suka nufi Sabuwar Unguwa, Tudun
Matawalle inda gidan Goggo yake.
Suna tafe cikin nutsuwa, Alhaji
Nasir yana matukar jin dadin tukin Abidu,
saboda ba ya tukin ganganci, shi ya sa duk
lokacin da tafiya wata unguwa ta kama shi
in dai Abidun nc zai kai shi, to kuwa za ka
same shi cike da nishadfi.
A hankali Alhaji Nasir ya juya
dubansa ga Abidu, ya сс.
"Abidu, ina so ka ba ni shawara
yadda zan yi da kanncaka Mashkur da
Haidar. Na rantsc maka da giman Allah
na soma Kosawa da halayensu, kullum ni
kenan cikin karbar korafin da ya shaf
Abidu ya dan juyo a kaikaicc ya се.
ка yi hakuri Abba, komai lokaci
nc. Kuma akwai launin Kuruciya da kan zo
17 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
wa yara kala-kala, ka dauka haka tasu
kuruciyar ta ke".
Alhaji Nasir ya yi murmushin
takaici, ya се.
"Daga Mashkur har Haidar wane ne
yaron da za a kira masa kuruciya?
Kowannensu fa ya haura wa shekaru
ashirin, idan ba su nutsu ba yanzu sai
yaushe? Mhm..."
Abin ya tare shi.
"Haka ne kam Abba. Addu'a ita ce
abar da ya dace da su, insha Allah zan
dinga kwatanta musu".
Daidai lokacin da suka iso wajen
gidan Amadi Kurfi, wanda za su shiga
kwanar sabuwar unguwa firamare, suka
tarar da jerin gwanon motoci kusan goma
sha, wadanda ke faman neman damar yin
kwana. Dole Abidu ya ja tunga shi ma ya
jera layi har zuwa lokacin da zai samu
damar shan kwanar.
18 SUNAN MU DAYA-I NAJNOOR
Su biyun babu wanda ya kuma yin
magana, illa Abidu da ke mamakin abin da
ya haddasa wannan cunkoson ababen hawa
da daddare ba yammaci ko safiya ba.
Kamar an ce ya kai dubansa gefen
gidan Amadi Kurfi, karaf! Idanunsa suka
hango masa wasu matasa guda biyu sanye
da T.Shirt da wandon jins da suma sosai a
kawunnansu, kowannensu ya cika baki da
hayakin abin da ya zuka daga abin da yake
hannunsa.
Cikin 'yan sakanni Abidu ya tsura
musu idanu cike daa tausayin halin da suka
sanya kansu a ciki, domin a dan
takaitaccen lokacin da ya dube su ya gane
ba sigari ce suke sha ba, duba da yadda
hayakin ke hada gajimare yana watsewa
sama, cikin biyu za a samu daya, ko dai
wani ganye ne aka yi wa nadin mandula ko
kuma kacokam tabar wiwi cc.
19 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
AAbin har ya so ya ba shi mamaki,
yadda suke fesar da dunkulen hayakin ba
tare da shakkun komai ko ga lafiyarsu ba,
ballantana mutanen da za su cutar.
Daram! gaban Abidu ya fadı yayin
da ya lura da daya daga cikin & matasan
biyu, ba wani ba ne illa matashin da suka
hadu a masallaci.
Dazun ya riske shi yana karatun
alkur'ani mai girma cikin kira'ar da ke nuni
shi mai zurfin ilimin addini ne! Yanzu
kuma ga shi ya gan shi a wani gurbataccen
yanayi, koda yake da ma ya sanshi a wani
lokaci can da ya wuce yana aikata abin da
ya fi wanda ya riske shi yanzu a ciki.
Sai dai daga lokacin da ya ganshi a
masallaci ya dauka ya bar wannan
gurbatacciyar rayuwar ne, ashe baya na
suka gaba na kaikayi ne, wato mai fuskа
biyu, fuskar farko ta kamala, fuska ta biyu
20 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
kuma ta munana, lallai FAHIMTА
FUSKA...
Yana cikin wannan nazarin ya hango
matashin ya kura masa idanu cikin wani
irin yanayi da ke nuni akwai tsoro a tare da
shi, sai kokarin boye abin da ke hannunsa
yake.
Girgiza kai kawai Abidu ya yi yana
hailala a cikin zuciyarsa da fatan Allah ya
shiryi al'ummar musulmi a duk inda suke.
A hankali ya kawar da dubansa daga
matashin saurayim ya mayar da shi a
gabansa yana ci gaba da silalawa da motar
cikin nutsuwa, har ya karya kwanar da za
ta sada shi da Sabuwar Unguwa firamare
inda daga nan ne zai shiga layin har zuwa
gidan Goggo.
A takaicc har suka shiga gidan
Abidu bai cikin hayyacinsa, wanda zai taka
muhimmiyar rawa daga cikin zantukan da
mahaifinsa kc yi.
21 S1NANE D4Y 4-1 UNOOR
Ya kasa hankalinsa biyu, dayaa kan
hanya, daya a kan matashin saurayin da
sunansa ya kwanta masa, bai san inda yake
ba, illa saninsa da ya yi a wani bigire mai
kama da muzanci da tozarci!
"Rukayya, sanin kanki ne ina
kaunarki". In ji Abidu
"Don haka ki kwantar da hankalinki,
bana so mu yi gaggawa".
Rukayya ta dago kai ta dube shi a
raunane, ta cc.
"Ba gaggawa nake nufi ba Abidu,
ina gudun kada jinkirinka ya haifar mana
da matsala... Wallahi ka ji na rantse maka
kai ne farin cikina, kai ne burina, kuma..."
Ya tare ta da fadin.
"Ba sai kin rantse ba, ni kaina na
sani Rukayya. To amma abin da za ki duba
shi ne, duka watana biyar fa da soma aiki,
22 SUUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
kina ganin yanzu idan na kawo maganar
aurc ba zan samu tsaiko ba? Albashina fa
bai soma kashe min kwarnafi ba".
Ta сc, "Wallahi har yanzu ba ka gane
inda na dosa ba... Ni fa ba ina nufin lallai a
wannan lokacin za mu yi aure ba, ina dai
so ne ka kawo kudin aurenka, a san da
maganar da gaske ka ke yi, ka ga ko da
wani zai yi magana za a sanar da shi an
karbi maganar wani".
Ya tsare ta da idanu, kaifin hankali
da dogon lissafin Rukayyan na daga cikin
abin da ke armasa soyayyar tasu.
Ba zai manta ba, ko a haduwarsu ta
farko a kan hanyarsa ta dawowa gida
bayan ya je dubiya a asibitin Medical
center, da karamtattun kalamanta ta sace
masa zuciya. Tunda shi da farko a wasa ya
dauki lamarin nasu, daga nesa kadan da
asibitin ya ganta ya tsayar da ita, kuma ta
23 SUNAN ME DAYA-I NAJNOOR
amsa gayyatar tasa ta tsaya, har da
tukwicin gaishe da shi.
A wasandare ya gabatar da kansa a
gare ta a zuwan ya gani ya yaba, sai aka yi
sa'a so gamon jini, ita ma ta yaba din, ta
kuma karbi tayin soyayyarsa cikin aminci
ta hada da kwatanta masa gidansu.
Kamar wasa ya yi zuwa na farko, na
biyu, na uku, na hudu soyayya mai karfi da
motsa zuciya ta yi awon gaba da su, ta
yadda kowa a gidan su Rukayya in ka cire
mahaifinta suka san da soyayyar tasu.
Kyawawan halayen Rukayya suke
alamta masa ya yi dace da IRI NA GARI
wanda ake fatan samu, wato mai cikar
haiba gaba da baya.
Ya sauke ganinsa a kan kyakkyawan
zoben da ke a karamin yatsanta, ya ce.
"Rukayya ki amince da ni a kowanne
hali ba zan guje ki ko na yi wasa da damar
mallakar junanmu a matsayin ma'aurata ba.
24 SUUNAN MU DAYA-I NAJNOOR
Ba ni da wani buri a 5angaren
zamantakewar aure irin wadda Allah ya
zaba mana, don haka mu yi hakuri da ci
gaba da addu'ar Allah ya jagoranci
lamarinmu, Ya sa mu zamo a inwa daya".
Ta rausayar da kwayar idonta, ta ce.
"Na amince da kai Abidu, wallahi na
amince ka zamo mijina. Amma ina tsoron
abin nan da Hausawa kan ce, a bari ya
huce shi ke kawo da rabon wani".
ta ce.
Ya shashantar da maganar da fadin.
"Ina son wannan zoben na yatsanki".
Ta dubi yatsan, sannan ta ciro zoben
"Ai ka wuce ka tambayi wani abu a
gurina na kasa ba ka shi, ballantana ni
kaina wata rana mallakinka ce. Ga shi".
ta mika masa. Ya karba yana juya
zoben a hannunsa, da murmushi a fuskarsa
ya ce.
25 SUNAN MU DAYA-I NAJNOOR
"Amma ki ganczoben nan ya
matukar kayatar da ni, sannan a kallo daya
da na yi masa na ayyana ya fito ne daga
hannu mai daraja, hala wani saurayin ya
ba..."
Kafin ya karasa ta katse shi.
"Subhanallahi Da bakinka ka kc
ambaton wannan furucin a kan
harshenka?"
Yadda ta yi maganar kamar wanda
ya aikata wani gagarumin 'laifi, sai jikinsa
ya yi sanyi, shi kansa ya ga rashin dacewar
yi mata wannan hasashen. Idan zai duba
irin yadda ta sadaukar da rayuwarta a gare
shi, ko sau daya ba zai ce ya taba ganin
wani saurayiya zo gurinta zance ba.
Fuskarta a daure ta ci gaba da cowa.
"Abidu, ni kaifi daya ce! Idan na ce
ina so ba na sauyawa, koda yakc na lura
har yanzu ba ka aminta da dumbin son da
26 SUNAN MU DAYA-I NAJNOOR
nakc maka wanda ke hana ni sukuni ba,
kuma..."
Da sauri ya katse ta.
"Ba tunanina ke nan ba, wallahi na
yarda da dumbin son da kike min, zuciya
ce ba ta da kashi, kuma kin san Hausawa
sun ce, idan an ciza ya kamata a hura. Ba
na shakku a kanki".
Ta cc, "Idan haka ne don Allah ina
rokonka alfarma ka daina kawo min
zancen wani, don ba ka san yadda zuciyata
ke tafasa ba a duk lokacin da aka kawo
min zancen wani namiji bayan kai".
Ya yi murmushi, ya cс.
"Shi kenan, na daina".
Ya karashe maganar yana duba
agogon da ke daure a tsintsiyar hannunsa,
ya cc.
"Kai ashe lokaci ya ja haka ba mu
sani ba... Ya kamata na wuce, sai yaushe
kc nan zan dawo?"
27 SUNAN MU DAYA-I
Ta cc, "An jima"
Ya yi dariya, ya ce.
NAJNOOR
"Kin ganki ko? Wato don kin san ina
da shamaki an jiman ko? To shakuruminki
daga yau Baba zai janye min wannan
shamaki, duk lokacin da na yi galarin
ganinki za ki gan ni a kofar gidanku".
Ta ce, "Uhm! Ba shi ya sa na ce ka
turo magabatanka ba..."
Yana zura hannu aljihu ya ce.
"Me kike ci na baka na zuba? Kc dai
ci gaba da koya wa zuciyarki hakuri da ni".
Ta ce, "Mhm! Ai zuciyata ta dade da
koyon hakuri da kai, don zuciyar da ke so
ai ba za a shawarce ta yin hakuri da wanda
ta ke so ba".
Ya mika mata zoben yana fadin.
"Ga zobenki, na gode".
Та се, "Haba dai! Wallahi na bar
maka shi, da ma kwacensa na yi gurin
Kakarmu".
28 SUNAN MU DAYA-I NAJNOOR
Ya ce, "Lalalah! Ashe kin fara fashi
da makami Rukayya?"
Ta yi dariya har kumatunta ya lotsa,
wanda hakan ya kara bayyanar da
kyawunta, ta ce.
"Allah ba fashi da makami ba ne,
taimakonta na yi, wai fa tun tana budurwa
kakanmu ya ba ta shi ta ke ta ajiyarsa, ba ta
taba sanya shi a hannunta ba, sai bayan
rasuwarsa ma fa ta fiddo shi, shi ma ba
sanyawa ta ke ba illa ta saka shi a gaba
tana alhini".
Ya ce, "Ba wani taimako, ta'addanci
kika yi a soyayya! Tunda ki ka ga tana
muhimmanta zoben bai kamata ki raba ta
da shi ba, ai ko ba komai wannan ya isa
zama darasi a gare ki, ki ganc yadda karfin
so ya ke tasiri ga wanda ke son. Saboda
haka ni ba azzalumin soyayya ba ne, ba
zan karba ba".
29 SUNAN MI DDAYA- NAJNOOR
Ta marairaice kamar za ta yi kuka, ta
cc.
"Kar ka yi min haka..
:
tamYatare tam
A'ah kar ki marairaice min ki karya
lagona. Kawai ki mayar mata da zobenta".
Ba ta son yin jayayya da shi, saboda
haka ta sa hannu ta karba, sannan suka yi
bankwana ya tafi cike da farin ciki. Lallai
ya zamto mai sa'a a rayuwarsa, don Rukayya kyauta co daga Rabbi, wadda
kowannc namiji zai yi fatan ta zamanto
uwar 'ya'yansa sola id
YauwaAbidube nasoji dadin
shigowarka, tun dazu na ke jiran Haidar na
aike shi kasuwa, amna ka ga shiru har
yanzu bai dawo ba".g
Hajiya Jummai mahaifiyar Abidu ta
fada lokacin da ya shigo falon.
30 SUNAN MU DAY A-1 NAJNOOR
Ya zauna a kan kujcra, sannan ya ce.
"O.K, me za a sayo miki?"
Ta cc, "Atamfa ce ta ankon diyar
Hajiya Zuwaira da za mu yi mako mai
zuwa, wai ta kare a gurinsu, amma bari na
dauko maka kyallen wata kifa idan aka
bincika a kasuwar a samu".
Ta nufi dakinta, jim kadan ta dawo
hannunta rike da kyallen atamfar ta mika
masa.
"Ina jin ba za ta wuce dubu uku ba,
don Allah ka bincika sosai".
fadin.
Ya karbi kyallen da kudin yana
"Insha Allah za a samu".
bsb Mintoci kadan suka sada shi da
babbar kasuwar Katsina (central market),
ya fara shiga shaguna yana nuna kyallen
atamfar, amma ko ina ya bincika, ba ya
samu. Har ya fara sarewa, yana tunanin
komawa gida, a shagon da ya shiga na
29SUNAN MU DAYA-17NAJNOOR
се.
Ta marairaice kamar za ta yi kuka, ta
lm oye
"Kar ka yi min haka.."
Ya tare ta.n
n nedA'ah kar ki marairaice min ki karya
lagona, Kawai ki mayar mata da zobenta".
Ba ta son yin jayayya da shi, saboda
haka ta sa hannu ta karba, sannan suka yi
bankwana ya tafi cike da farin ciki. Lallai
ya zamto mai sa'a a rayuwarsa, don
Rukayya kyauta ce daga Rabbi, wadda
kowannc namiji zai yi fatan ta zamanto
uwar 'ya'yansa.
*** *** ***
"Yauwa Abidu na ji dadin
shigowarka, tun dazu na ke jiran Haidar na
aike shi kasuwa, amma ka ga shiru har
yanzu bai dawo ba".
Hajiya Jummai mahaifiyar Abidu ta
fada lokacin da ya shigo falon.
30 SUNAN MU DAY A-1 NAJNOOR
Ya zauna a kan kujcra, sannan ya ce.
"O.K, mc za a sayo miki?"
Ta cc, "Atamfa ce ta ankon diyar
Hajiya Zuwaira da za mu yi mako mai
zuwa, wai ta kare a gurinsu, amma bari na
dauko maka kyallen wata kila idan aka
bincika a kasuwar a samu".
Ta nufi dakinta, jim kadan ta dawo
hannunta rike da