ma yi ttunanin
yana gida tunda na ga yaullahadi cе?"
Abdulmalik ya ce.
"Ai ka san aikinmu shiftin-shiftin ne,
an kai shi Zcnith bank".
Abidu ya cc, "To don Allah ka fada
masa na zo, kwana biyu ba ma haduwa".
Abdulmalik ya ce.
"Insha Allah zan fada masa".
Suka yi sallama, Abidu ya bar
unguwar.
Kwana biyu Abidu yana cikin
ayyukan ofis saboda kusantowar zaben
66SUNAN MI DAYA-| NAJNOOR
shugabannin kananan hukumomi ba ya
samun lokacin kansa, idan ya tafi ofis tun
safe ba ya dawowa sai bayan Magriba, don
haka ba shi da sukuni, ko wajen Rukayya
ba ya samun sararin zuwa, illa waya da ke
shiga tsakaninsu.
Yau ya dawoh da yamma, yana
kokarin shiga da mota cikin harabar gidan
ya hango ana tsayar da shi da hannu ta
jikin madubin motar.ge sn sb
Bai karasa shiga da motar ba ya ja ya
tsaya, yayin da Salman abokinsa ya karaso.
Ya bude motar ya fito yana murmushi.s
"Haji Salman ashe ka dawo?" In ji
Abidu bayan ya iso,
Salman ya yatsina fuska, ya ce.
"Ya hausar na dawo, da ma ba na ce
maka kan hanya nake ba, kai kuma ka ce
sai gobe za ka dawo, ai kai zan tambaya
ko?"
Dariya Abidu ya yi, ya ce.
a
67 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
"Ina na je har muka hadu da kai?"
Shi ma Salman sai ya yi dariya, ya
се.
"To raina min hankali. Ka manta
dazun mun hadu da kai a Kaduna, daidai
Gamji gate na je karbo hotuna, ina sauri
zan dawo Katsina?"
Yanzu yanayin fuskar Abidu ya
sauya daga fara'a zuwa al'ajabi, ya ce.
"Ni din kuwa, ko dai mafarki ka yi
mun hadu a Kadunan ne?"
Kallon rainin hankali Salman ya
watsa masa, ya cc.
"Kai fa matsalata da kai akwai son
wasa. Kana nufin rudewata har ta kai na
hadu da mutum a mafarki na zahirantar da
shi?"
Abidu ya tamke fuska jin abin na
zahiri ne, yana kuma mamakin faruwar
zuwansa Kaduna har suka hadu da Salman
ba tare da ya sani ba.
68 SUNAN ME DAYA-I NAJNOOR
"Ka ga Salman kada ka ruda ni
mana, ni ba inda na je, hasalima ba ni da
kowa a Kaduna bare wani abu ya kai ni".
Salman ya ci gaba da kallonsa а
shckc, yana kuma murmushin rainin
hankali, yа сс.
"Shi kenan, tunda haka ka ce mu tafi
a haka, duk lokacin da ka amince mun
hadu da kai a Kaduna ma tattauna maganar
aikin da ka cc za ka yi min hanya da muka
faro a can Kadunan".
Yana karashe fadar haka bai jira jin
ta cewar Abidun ba ya bar shi a nan tsayc
cike da tsanani mamakin lamarin.
Labiba ta fara fado masa a rai, ta ba
shi labarin Abid da abin da ya baro a
Borno, wato masoyiyar da ke suma a
kansa. Sannan matashin da suke haduwa a
masallaci wanda ya kira kansa da suna
ABID NASIR BARHIM.
69 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
Yanzu kuma ga wani rikitaccen
labari a bakin abokinsa Salman, shin mene
ne alakar Abid din Borno da wanda suka
hadu a masallaci, da kuma wanda Salman
ya hadu da shi a Kaduna?
Tabbas a bakin matashin masallaci
ya ji cewar, shi dan Kaduna ne, kenan shi
ne ya je Kadunan har suka hadu da
Salman? Amma kuma ta ina kamanninsa
suka jirkice zuwa nasa kamannin? Mene
ne dalili?
*** *** ***
Yana kwance a kan gadonsa cikin
mayalwacin dakinsa, da misalin karfe
goma na daren ranar juma'a, wayarsa ta yi
kara.
Ya kai hannu ya janyo ta, tare da
duba fuskar wayar ya tarar da sunan
Nazcer L. Abdul na yawo a kai.
70 SUNAN MUDAYA-1 MAJNOOR
Ya danna malatsin amsa kira, sannan
ya kai wayar a kunnensa.
Dan sanda abokin kowa".
Abinodayya fara fada konan, sannan
ya dora da cewa.
"Sai yau na ke jin ka a waya?"
Nazeer ya ce da shi.
"Kai ba dogon turanci za ka yimin
ba, ina wajen da ka ce za mu hadu ina
jiranka, ka taho min da bluctooth".
Abidu ya tashi zaune, ya ce.
"Ban gane kana inda na ce zamu
hadu ba?"
Nazeer ya ce,
"A'ah, kada ka raina min hankali
mana, ba dazun ka zo gidanmu na ce maka
ina aikin dare ba, ka cc mu hadu a Luna
Hotel da misalin karfe goma na dare?"
Da sauri Abidu ya ce.
"Gaskiya ba ni ba ne, tun ranar
lahadi fa na zo gidanku kuma ban tarar da
Πt:afSSC
73 SUNAN MUDAYA-I NAJNOOR
"Zan jc allura ne, saboda zazzabi ya
matsa min".
ka?"
Alhaji Nasir ya ce.
"To me zai hana Mashkur ya kai
Da sauri ya ce.
"Zan iya tukin da kaina".
Alhaji Nasir ya jinjina kai, ya ce.
"To shi kenan, Allah ya kara lafiya".
Wannan tsayarwar tasa ya samu
tsaikon isa Luna a kan kari. Yana isa ya
dinga dube-duben inda zai ga Nazcer,
amma bai ganshi ba. Saboda haka ya koma
gida musamman da ya ji Nazeer din ya
fada masa yana aikin dare ne a wayar da
suka yi dazun, ya san ba zai tarar da shi a
gida ba, wannan ya sa ya koma gida da
shan alwashin zai je unguwar su Nazeer
din gobe.
Ai ko da safen ya je unguwar su
Nazcer, bayan ya kwashi mintina goma a
74 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
tsaye Nazcer ya fito duk da yanayin bacci
da ke tare da shi, fuskarsa a sake ya iso
gurin Abidun, ya ba shi hannu suka yi
musabiha. Abidu ya dora da cewa.
"Jiya na je Lunan ban tarar da kai ba,
kuma ka kama waya ka kashe".
Nazeer ya hararc shi da gefen ido, ya
се.
"Wallahi ka raina min hankali
Abidu, wato bayan artabun da muka yi da
kai a waya ka ji ba lasa ka zo Lunan muka
hadu, shi ne yanzu kuma za ka zo min da
wani salon rainin hankalin, wai ka je ba ka
tarar da ni ba?"
cC.
Cikin nuna rashin damuwa, Abidu ya
"O.K ya zo kenan?"
"Waye?" In ji Nazeer.
"Takwara, wanda kuka yi za ku
hadu".
Nazcer ya ja tsaki, yа се.
73 S111N MUDAYA-I NAJNOOR
"Zan jc allura ne, saboda zazzabi ya
matsa min".
ka?"
Alhaji Nasir ya ce.
"To me zai hana Mashkur ya kai
Da sauri ya ce.
"Zan iya tukin da kaina".
Alhaji Nasir ya jinjina kai, ya ce.
"To shi kenan, Allah ya kara lafiya".
Wannan tsayarwar tasa ya samu
tsaikon isa Luna a kan kari. Yana isa ya
dinga dube-duben inda zai ga Nazeer,
amma bai ganshi ba. Saboda haka ya koma
gida musamman da ya ji Nazeer din ya
fada masa yana aikin dare ne a wayar da
suka yi dazun, ya san ba zai tarar da shi a
gida ba, wannan ya sa ya koma gida da
shan alwashin zai je unguwar su Nazeer
din gobe.
Ai ko da safen ya je unguwar su
Nazcer, bayan ya kwashi mintina goma a
74 SUNAN ML DAYA-1 NAJNOOR
tsaye Nazeer ya fito duk da yanayin bacci
da ke tare da shi, fuskarsa a sake ya iso
gurin Abidun, ya ba shi hannu suka yi
musabiha. Abidu ya dora da cewa.
"Jiya na je Lunan ban tarar da kai ba,
kuma ka kama waya ka kashe".
сe.
Nazeer ya harare shi da gefen ido, ya
"Wallahi ka raina min hankali
Abidu, wato bayan artabun da muka yi da
kai a waya ka ji ba lasa ka zo Lunan muka
hadu, shi ne yanzu kuma za ka zo min da
wani salon rainin hankalin, wai ka je ba ka
tarar da ni ba?"
сc.
Cikin nuna rashin damuwa, Abidu ya
"O.K ya zo kenan?"
"Waye?" In ji Nazeer.
"Takwara, wanda kuka yi za ku
hadu".
Nazcer ya ja tsaki, ya се.
755 SUNAN M DAYA-1 NAJNOOR
"Ka ga Malam bacci nake aka taso
ni, kada kanshiga hakkina da shirme!"
Ya juya zai koma cikin gida. Abidu
ya yicaraf ya riko hannunsaz
"Don Allah ka tsaya naafahimtar da
kais. Wallahi ba ni ba ne, wani ne da
SUNANMU DAYA. amma mutanec suko
ganinsa a matsayinni".
"Sünanku dáya sai kuma
kamanninku su zamo daya? Kawai dai ka
faukiamutanc gwangwanaye, don haka ka
jeda fahimtar taka ba ma so
Duk yadda Abidu ya so Nazeer ya
saurare shi, amma ya Rij ya shigeroikinya
bar shi baki a sako.
Aiki yaarufaremasa a ofis, amma da
yako yana da burin ganin Abid a yau dons
ya ji yaddaaka mutu a ragaya, don haka ya
tsallake ayyukan karfe biyar saura ya nufo
gida.
76 SUNANMU DAYAA AD AAVOOR 2
021 Tun biyaredakwata lya akczaunc a
masallacinnummia har aká yidshali bailgan
ko máái káma dai Abidodajsdotejashakura
da cikar burinsaßenunaσ ολίτ εγσISO İY BV
ab sTunisjiya yake ssonslzuwaTudun
Matawallc gaidonGoggoy kai tsayd y nuf
gidan nataysuka sha hira, bai baro gidan b
sai karfc goma da mintociashi mardong
kansalke ciwe. Bvab пкавпи2"
E iвDasya láwotbaisamia zahtawandal
Abbans nasab da yyastararvayfalo ubamikab
tsayc ya wucc säshensad slel slraidst sb ot
BY TOWashcgari yastashi dabworiha lgurin
aiki,i Ummarisasta ba shi sakon katbomata
dinki a gurin telanta, donshakalsyla dnufid
gurin.
sb snYana, isa gurin maidinkin yatarar da
Lahibasvita bta Afaraustararsad da gaisuway
sannah sukabzantajda mai dinkinsýa ce baiv
karasasbaşsai dai yal däwol gobervs с
sbig
78 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
iya haduwa da ku har ya rasa ya aka samu
haka?
Sai dai abin lura a nan shi ne INA
HUJJAR TA KE da idan SUNANKU
DAYA da mutum, a ce kamanninku daya?
Wannan bai fi daure maka kai ba?"
Ta saurara idanunta a kansa.
Ya girgiza kai, tukunna ya ce.
"Abin da ke ba ni mamaki kenan
Labiba, SUNANMU DAYA da Abid,
amma ni ban taßa ganin kamannina a tare
da shi ba ga wanda na ke hasashen shi ne
kuke nufi. Sai dai duk wanda zai ba ni
labarin ya ga Abid abin da zai fada kenan,
wai kamanninmu daya, har a dinga tunanin
ni ne shi..."
cе.
Ta yi murmushi, tana narke idanu, ta
"Ka gani ko? Shi ya sa na yi
tsammanin kana da matsala a kwalwarka,
79 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
watakila dalilin haka ne ya sa ka ke
bayyana a guri ka ce ba kai ba ne...'
Da sauri ya katse ta da fadin.
"Ko kuma ku ke ruda kanku ko?"
Yadda ya yi maganar kamar ya
shaka, sai ya ba ta dariya, ta kuwa dara
tukunna ta ce.
"Kwantar da hankalinka Abidu, ba fa
ni na kar zomon ba, rataya aka ba ni...
Koda yake ka ce min kana son sanin
gidanmu ko?"
Shi ma sai ya dan washe fuska cikin
nuna komai ba komai ba ne, ya ce.
"Kwarai kuwa".
Ta yi far da idanu, ta ce.
"Ko za ka iya fada min dalilinka na
son sanin gidanmu?"
Ya yi jim na wani lokaci kafin daga
bisani ya се.
"Shi zumunci ai ba a tuhumar dalilin
yin sa ko?"
80 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
Ta ce, "Lallai kam... To amma
gidanmu ba a barina fita, saboda tuni an
fitar min da miji, shi kuma marikin nawa
yana da akidar idan ya tsayar da magana a
kan yarinya babu mai sake tsayawa da ita"
ni..."
Abidu ya jinjina kai yana fadin.
"Amma tsarin gidan naku ya burge
Ta tare shi da fadin.
"Kamar yadda tsarin gidan su
Rukayyah ya ke?"
Ya yi mata kallon tuhuma, ya ce.
"Kin ce ba ki santa ba...?"
"Yanzu kuma sanadinka na nemo
gidansu ba". Ta fada.
ם
"Kenan kun gaisa da ita?" Ya ce.
Ta girgiza kai, ta ce.
"Wasa na ke, ta ya zan gano gidansu
bayan ba ka fada min unguwar da ta ke
ba?"
Ya yi dariya, ya cc.
8210 SINYA MU DAYA u UYDOR
162 udKwasa d kuipisabgasvabibpts fado
rayuwarsa, yandubi bocuin
kamanninsu daya? Mene saihi dm xa
ngsdaska KA 00 Y
Yana shiga gidaninsisb
sfamarin d:5 T karda
al'ajabi. Mahaifinsa ya tarahsbisdgi
7月 200 a fako
kowanne fuskarsa babu a "Yirisdas
пітало а в за на amsa
sannan ya rusuna yana gaishe ia
kokarin wucewa dakin st
Alhaji Nasir ya kira suy dalA"
swulu a ind master a lio A Al
ENARIEYANI Babaska minste ad
owed thidam ashoes ab ana
mun buwa Pab anbeeagide sy пNиBA
83 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
Kirjin Abidu ya buga da karfi, ya
dago kai da sauri ya dubi mahaifin nasa ba
tare da ya yi magana ba, sai dai bakinsa na
motsi alamar yana son tofawa jijiyoyin bayar da damar maganar sun Ki tallafa
masa, illa tsananin firgici da fuskarsa ke nunawa.
Alhaji Nasir ya ja tsaki, ya ce. "Wallahi ka bata wayonka, tunda ka zamo asharari mai ci da addini. Duk kamewar da ka kc nunawa kana da ita, ashe GORAN DUMA ne sai an fafe za a
san abin da ke ciki? To ka kyauta, sai dai ka sani ba ni ka batawa ba, Mahaliccinka
ka batawa, kuma mutumcinka ka zubar ba
na..."
Saboda kuwwar da maganganun ke yi wa Abidu a dodon kunne ya kasa jure
saurare, sai da ya samu mazantakar
tsinkawa.
84 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
"Abba don Allah ka yi hakuri,
wallahi ban san laifin da na yi ba..."
Alhaji Sani Kafinta ya cabe da cewa.
"Iyc Abidu! Da ma dai ka tabbata
mara kunya ko? In ganka jiya da daddare
ka dawo a buge kana tangadi, na yi maka
magana har kana cewa ka je ka yi, shi ne
yanzu za ka karyata ni?
Ba mamaki, watakila buduwar da ka
yi ce jiyan ya sa ba ka shaida mun hadu
ba".
Abidu zai yi magana, Alhaji Nasir ya
riga shi da cewa.
"Rabu da mutumin banza, idan bai
ganka ba zai ce ya ganka ne? Ko ka manta
yanayin da ka dawo jiya ka ce wai kanka
ne kc ciwo? Ashe da ma abin da ka shawo
ne ya sauya ka?"
Abid ya yi wuri-wuri da shi, ya tuna
jiya bayan sallar isha'i yana Tudun
Matawalle, bai baro unguwar ba sai gima
85 SUNAN MUDAYA-1 NAJNOOR
da rabi. Ya dawo kansa na masa ciwo
sosai, don har idanunsa sun kada sun yi ja,
shi ya sa ko da suka hadu da Abban nasa
bai samu đamar tsayawa sun zanta ba, ya
sanar masa kansa ke ciwo ya shige Gangarensa...
Alhaji Nasir ya katse masa tunani da
cewa.
"Rayuwa ce, idan haka ka zabar wa kanka bismillah".
Abidu ya buda baki a karo na biyu
zai yi magana, mahaifin nasa ya katse shi
ta hanyar daga masa hannu.
"Tashi ka ba ni guri, ja'iri kawai!"
Ba shi da zabin da ya wuce bin
umarninsa, don haka ya mike jiki a sabule
ya shiga dakin Ummansa. Ya tarar da ita a
zaune tana amsa waya, ya nemi guri yа
zauna, sai da ta gama amsa wayar sannan
ta dago ta dube shi, ta ce.
86 SUNAN MU DAYA- NAJNOOR
"Lafiya dai na ga ka shigo da
damuwa a fuskarka?"
Duk da jar zuciyar da yake da ita, sai
da ya ji kwalla na shirin zubo masa,
muryarsa a raunane ya ce.
"Umma ina cikin damuwa da
firgici..."
Da sauri ta katse shi.
"Wace irin damuwa Abidu?"
Ya ce, "Jiya da daddare na je gidan
Goggo, na dawo da tsananin ciwon kai, shi
ya sa ba mu zauna da Abba ba na shiga
sashena. To yanzu na dawo na tarar da
Alhaji Sani Kafinta da Abba yana sanar da
shi, wai ya ganni jiya na shawo barasa...
Wallahi Umma na rantse miki da, girman
Allah ba ni ba ne ya gani".
Ya karashe maganar lokacin da
hawayen suka samu damar zubo masa.
87 SUNAN MUDAYA-I NAJNOOR
Umma ta yi shiru tana al'ajabin
wannan bakon al'amari. Ta ci gaba da tsura
masa idanu don nazartarsa.
Tunda har ta ga Abidu na zubar da hawayc a kan wannan maganar, to lallai bai aikata abin da ake zarginsa da shi ba. Amma haka kawai Alhaji Sani Kafinta zai
ce ya ganshi a make?
Ko dai sun hadu da Abidun ne lokacin da yake cikin halin ciwon kai, sai ya yi tsammanin barasar ya shawo? Cikin kwantar da murya ta ce masa.
"na ji, daina zubar da hawayen. Bari
za mu tattauna da Alhajin".
Muryarsa a raunane ya сe. "Wallahi Umma rabon da na ga ma Alhaji Sani har na manta".
Та се, "Кar ka damu... Ya maganar dinki?"
Ya ce, "Bai karasa ba, wai sai gobe". Ta ce, "Shi kenan".
88 SUNAN MU 1DAYA-1 NAJNOOR
Haka ya fito daga dakin nata har
lokacin Alhaji Sani Kafinta bai tafi ba. Ya
wuce su zuwa sashensa abin na ci gaba da
daure masa kai.
Lallai lamarin Takwara ya ta'azzara,
domin ya tabbata shi ne Alhaji Sani
Kafinta ya gani a buge ya ce Abidun ne.
Abidu ya kasance cikin rashin sukuni
saboda fushin da mahaifinsa ke yi da shi a
kan abin da bai aikata ba, sam ko
gaisuwarsa yadaina amsawa, ballantana ya
yi masa duban mutumci.
Duk yadda Umma ta so fahimtar da
Alhaji nasir gaskiya ya ki saurarenta, sai
ma fada da ya kan rufe ta da shi, wai ita ke
daurewa yaran gindi suna abin da suka ga
dama.
Wannan ya sa ta zare hannunta a ba
shi hakuri, don sarai ta san halinsa, mutum
ne mai wuyar sha'ani.
89 SUNAN MUDAYA-1 NAJNOOR
A cikin kwanakin babu abin da
Abidu ya ke fata da buri irin haduwa da
Takwara don ya ji shin me ya yi sama ya
kc bibiyarsa da sharri, to amma kamar an
yi ruwa an dauke, ko inwar Abid bai kuma
gani ba!
*** *** ***
Abidu yana zaunė a karkashin wata
bishiyar durumi da ke can bayan layinsu,
shi da wani abokinsa Tukur, suna hirar
duniya game da yadda ake murdiyya da
babakere a lokacin zabe.
Daga nesa da su wani dattijo ne ya
taso 'yarsa a gaba, da alama su duka cikin
tsananin firgici suke.
Har sun kusa gota inda su Abidu
suke macen ta dora idanunta a kan Abidu,
da sauri ta ja ta tsaya. Dattijon ya се.
90 StNAN ME DAYA-I VAJNOOR
"Ya ki ka tsaya a nan mutuniyar banza?
Ta nuna masa inda su Abidu ke
zaune, ta ce..
ya ce.
"Ga shi can gurin".
Kai tsayc suka karasa gurin, Dattijon
"Kai nc Abid Nasir Barhim?"
Abid ya tsura wa Dattijon idanu yana
gyada kаi.
"Eh ni ne".
Dattijon ya kalle shi cike da takaici,
ya cc.
"Da ma game da maganar wannan
yarinyar ne 'yar wajena ta ce kai ka yi
mata ciki, shi ne muka zo jin baʼasi".
A firigice ya fiddə idanu wajc, yana
duban budurwar, ya се.
"Ke kin san ni? Kin taba ganina tunda ki kc rayuwarki?"
91 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
Ta daga gira ba tarc da ta yi magana
ba, idanunta har lokacin hawaye suke
zubarwa. Yayin da shi kuma ya ci gaba da
cewa.
"Wallahi ban taba ganinta ba sai
yanzu, ba ni ne na yi mata cikin ba".
Dattijon ya kara harzuka ya ce.
"To idan ba kai ba ne waye? Kar ka
manta na tambaye ka sunanka ka fada min,
kuma yarinya ta tabbatar da kai ne".
Hankali a tashe, duk ya rikice ya ce.
"Na rantse da wanda ya busa min
numfashi ba ni ba ne, SUNANMU DAYA
da wanda ya aikata mata wannan aikaaikar, ya dade yana aikata munanan
ayyuka ana cewa ni nc. An gan shi gidan
giya yana sha, an zo an cc ni nc. Yanzu
kuma kun zo da wannan fatawar! Wayyo
Allah, ni Abidu na ga ta kaina, daga
SUNANMU DAYA da mutum sai komai
92 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
namu na halitta su zo daya, har ya aikata
abu acc ni ne?"
Dattijon ya kada kai, ya ce.
"Babu abin da zan ce da kai sai Allah
ya isar mana cutar da ka yi mana, na bata
mata tarbiyyar 'ya da muka dauki lokaci
mai tsawo muna tattali.
Da ma cikin ya zube sanadin dukan
da ta sha a hannun yayanta, mun zo ne don
mu tabbatar da mugun da ya cutar da mu,
to ba za mu hada ka da hukuma ba, saboda
tonon asirinmu ne. Kuma tunda cikin ya
zube fahadas! Allah ya yi mana sakayya!"
Dattijon ya maida kallonsa ga Tukur
yana fadin.
"Idan abokinka ne sai ka yi hattara
kada ya lalata maka tarbiyya, ko da yakc
sai hali ya zo daya akc abota".
Da sauri Tukur ya girgiza kai, ya сe.
"Kada ka yi mana kudin goro Baba,
shi ya aikata laifi ni ko sani ban yi ba".
93 SUNAN MU DAY INAJNOOR
Dattijon ya dubi budurwartare da
daka mata tsawa.
"Kin wuce mun tafi ko sai na karya
ki, munafuka, ai duk ke ce sanadi da ba ki
ba shi kanki ba ya zo ya bata miki rayuwa,
ina ce har gida an zo mana da maganar
mayaudari nc, ya yaudaro wata yarinyar a
Borno ya gudo nan, amma da yake kunnen
kashi ne da ke sai da kika janyo mana abin
kunya..."
Ya karashe maganar yana kokarin
kai mata duka, ita kuma ta daka tsalle ta yi
gaba, ya bi ta a baya.
Tukur ya cika da tsananin mamakin
wannan al'amari, wai Abodu mutumin da
kowa yake ganinsa da kima, mai kuma
riko da addini, amma ya yi wa 'yar mutane
ciki! Lallai mugun mutum ba shi da kama.
Ya dinga kallon Abidu bayan
bacewar dattijon mutumin kenan da 'yarsa,
94 SUNAN M DAYA-I NAJNOOR
yana jin kyamar Abidun na shiga
zuciyarsa.
Abidu ya cire tagumin da ya rafka,
idanunsa sun fada sun yi jawur, ya се.
"Wallahi Tukur ban taba ganin
yarinyar nan ba sai yau, amma ka ji
kazafin da suka yi min?"
Tukur ya girgiza kai, ya ce.
"Haba Abidu, kazafi ko gaskiya? Ba
su sanka ba saboda Allah a wane dalili za
su ce kai ka yi mata cikin? Ai ka ma godc
wa Allah da ya sa suka salwantar da cikin
ba tare da ta haife maka shegen da zai
buwayi rayuwarka! Sannan kana da damar
tuba ga Allah a kan kuskuren da ka aikata,
ka kuma yi tuba ta gaske ba tuban muzuru
ba!"
Cikin yanayin damuwa Abidu ya се.
"Tukur kai ma yanzu ka yarda da
wannan kazafin da aka yi min?"
Tukur ya cс.
95 SUNAN MI DAYA-1 NAJNOOR
"Ka daina wahalar da kanka, ni ba
zan tona maka asiri ba, yadda Allah ya rufa
maka zan ci gaba da rufa maka".
Bai san lokacin da kwalla suka zubo
masa ba, takaici goma da ashirin ya hana
shi magana.
Tabbas ya gode wa Allah da ya sa ba
a gidansu aka yi case din nan ba, saboda
har yanzu mahaifinsa na fushi da shi, to ina
kuma ga an ce wai ya yi wa wata ciki?
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".
Ya samu kansa da ambato a cikin
zuciyarsa.
Tukur ya girgiza kai, ya ce.
"Wallahi Abidu yanzu ba lokacin da
idanu za su koka ba ne, yanzu ba lokacin
damuwa ba ne a gare ka. Lokaci ne da ya
kamata ka yi gaggawar tuba tun kafin
lokaci ya kurc maka, ka girbi abin da ka
shuka".
96 St NAN MU DAYA-1 NAJNOOR
Har yanzu ya kasa cewa wani abu,
ba don ma kar ya tashi afujajan ya bar
gurin ba, Tukur ya fasa rufa masa asirin da
ya alkawarta zai rufa masa mugunyan
kwai ya fashi ba, ai da tuni ya bace wa
gurin.
Tukur ya yunkura yana fadin.
"Bari na shiga gida, amma ka
kwantar da hankalinka, ba zan taba tona
maka abin da ka binne ba. Sai dai ina
tunasar da kai, muddin ba ka tuba da
tsarkakkiyar zuciya ba, Allah zai iya
jaraftarka ta wasu hanyoyin da ba ka taba
tsammani ba, ka girbi abin da ka shuka tun
a duniya!".
Yana Karashe fadar haka bai jira
cewarsa ba, ya bar gurin don ya san ba
cewar zai yi ba.
Sam Abidu ya kasa motsi, yana
zaunc a gurin cikin tsananin firgici da
kaicon rayuwa!
97 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
a
Kalmar da Tukur ya yi amfani da ita
ta karshe, 'ka girbi abin da ka shuka tun
duniya! ta tsaya masa a rai matuka, ta
dinga amsa amo a zuciyarsa tana yi kamar
za ta faso kirjinsa ta fito waje.
Yana zaune a gurin wayarsa ta yi
kara, yana dubawa ya ga lambar Nazeer
cc. Ya dauka tare da sallama, Nazeer ya
се.
"Kana ina?"
Abidu ya amsa masa da cewa.
"Ina cikin unguwarmu".
Nazeer ya се.
"To ka zo ka same ni a Katsina
Motel ina son yin muhimmiyar tattaunawa
da kai".
Gaban Abidu ya fadi, kada a ce
dattijon mutumin nan ya kai shi ga hukuma
a kan ya yi wa diyarsa ciki?
To amma idan haka ne me zai sa
Nazeer din ya zabi kadaicewa da shi a
98 SUNAN MU DAYA-| NAINOOR
Katsina Motel maimakon ya zo gida ya
kama shi?
Zumbur ya mike tsaye ya shiga
motarsa ya nufi Katsina Motc/don kada ya
bata wa kansa lokaci har Nazeer ya hasala
ya zo ya kama shi cikin tozarci.
Mashin din Inspecter Abdulmalik ya
soma gani, su din ma suna tsaye su biyu
Nazeer da Abdulmalik, kowanne fuskarsa
babu annuri.
Ya yi parking din motar, sannan ya
iso gare su. Nazeer ya сe.
"Mu je daga ciki".
Bai musa ba ya bi su a baya har
zuwa dakin da suka kama.
Nazeer da Abdulmalik suka zauna a
gado, yayin da shi kuma Abidu ya zauna a
kan stool yana zuba musu idanu de
sauraren abin da za su fada.
Abdulmalik ne ya soma cewa.
99 SUNAN MU DAYA-I NAJNOOR
"Abidu muna tuhumarka ne da laifin
kashe wasu mutanc guda biyu a kan bangar
siyasa!"
Zumbur kuma cikin kaduwa Abidu
ya mike tsayc, yana motsa la66ansa amma
ya kasa magana. Abdulmalik ya ce.
"Eh mana, an tabbatar da kai ka yi
kisan nasu, saboda kun yi hatsaniya da su a
ofis dinka sun cc idan ba ka sanya hannu
an yi magudi yayin gudanar da zae ba, za
su yi sanadin sauke ka aiki, shi ne ka bi
daren jiya ka kashe su!"
Idanun Abidu a waje ya ce.
"Wallahi ba ni ba nc, sam ba mu yi
wata rigima da wasu mutane ba a wajen
aikina ko a gida".
Abdulmalik ya yi takaitaccen
murmushi, ya ce.
"Hmm, idan ba kai ba ne, to wane
ne?"
100 SUNAN MUDAYA-I
се.
NAJNOOR
Da sauri cikin rawar baki Abidu ya
"Ta...kwara... ne!!!"
Suka dubi juna Nazeer Abdulmalik, Abidu ya ci gaba da cewa.
da
"Ban taba sanin haka Takwara yake
ba sai yau, shi ya sa na ke mamaki, wai shi ya kashe mutanen nan kuma a ce ni daga kawai SUNANMU DAYA? Haba sai ka ce
a mafarki ko garin marasa hankali?"
Nazeer ya ce cikin kakkausar murya.
"Ba a garin marasa hankalin ba ne, a
garin masu hankali ne fiye da hankalin da
kifi yake da shi yayin da yake cikin ruwa..."
Bai tsaya ba ya ci gaba da cewa.
"Na yarda da hujjojin da aka kawo
cewar kai ka yi kisan nan, saboda haka ina shawartarka kada ka wahalar da kanka da shari'a, ka ba wa hukuma damar samun
101 SUNAN MUDAYA-1 NAJNOOR
saukin yanke maka hukunci daidai da
laifinka".
Abidu ya marairaice, ya се.
"Wallahi ba zan amsa laifin da ko a
mafarki ban gaskata faruwarsa ba, sai dai
idan za a yanke min hukunci bisa zalunci,
wannan na yarda, ai ba yau aka fara
zalunci a Najeriya ba".
Abdulmalik ya girgiza kai, ya cc.
"Idan ka ce ba kai ka aikata wannan
ta'adin ba, shin ya aka samu I.D card dinka
a gurin gawarwakin yayin gudanar da
bincike?"
Cike da tsananin mamaki da rudani
Abidu ya laluba aljihunsa, sai ya ji wayam
ba I.D card ba alamarsa, cikin takaitaccen
lokaci ya tuna tun jiya juma'a da ya dawo
aiki ya dora I.D card din a saman talabijin
dinsa bai sake bi ta kansa ba.
Murya a raunanc ya се,
102 SUNAN MU DAYA-1 NAJNOOR
"I.D card dina kuma? To ai ni tun
jiya na dora shi a kan talabijin din dakina,
yanzu haka yana can gida idan aka je za a
ganshi".
Cikin tsananin bacin rai Abdulmalik
ya fiddo I.D card ya wulla masa yana
fadin.
"Yanzu sai ka musa idan ka isa! Ko
don ka ga mun yi maka gata mun keбe ka a
keba66en guri don mu kare ka tozarcin
jama'a?"
A matukar razana Abidu ya dauki
I.D card din yana warc ido a kansa!
Tabbas hotonsa ne radau a kai! Maimakon
suffar wanda yakc hasashen shi ne
Takwara da