Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels PIAZA SAI SANNGBINTAA WALI (Mirs Auwal G. Danborno) MAZA SAI SANNU 2 S un share kusan awa guda suna tafka masha"a da Jamila kala. Lallai dole masu kudi da "yan siyasa su likcwa Jamila kala. Tsawon shekaru sha biyu da fara neman matan Isma"il, ma"ana tun lokacin da ya balaga bai taßa nema da wacce ta kai Jamila kala ba. "Isma"il " Jamila kira sunan sa a hankali ga dukkan alamu itama ta jigata. Jamila" shima ya kira sunan ta daga kwancc. "Ya kamata ka shirya ka tafi dare ya-farayi" "a nan nakc son kwana" : "A'a bai dace ba saboda iyalanka" ta fadi haka ne don burinta ya gogawa matarsa alakakai. "ban sha"awar zuwa gidan nan wallahi" "Haba sweetheat gobe ma rana ce, bari in zuba ma ruwa kayi wanka. Karfe tara dai-dai Isma"il yasa kayansa bayan gama wanka da yayi. "Bari in fesa ma turare" Jamila ta fada tana murmushin farin ciki samun abokin tafiya. "Na gode ya fada dai-dai lokacin da ta gama fesa masa turaren. "Gobe fa da wuri zaka shigo Isma"il" "Kamar karfe nawa?" ya tambaya yana murmushin banza ta fadi "Kamat karfe goma" "Lokacin ina kasuwa" Ka zo ba komai zan dauke nauyin ka. "Ba komai sweety Allah ya kaimu. Har wajc ta rako shi, ba ta koma gida ba sai da taga bacewar marigayin, kamar yadda ta kira shi. 8 ya isa gida cikin farin ciki da annushuwa, sai dai abinda ke ba Isma"il mamakin lokaci guda sha"awar Hajara ta fada masa duk da cewasun gajiyar da juna shida Jamila kala. gidan bude yake, sauran abokan hayarsa zaunc a kofar gidan suna hirar matan makota. "Sannunkiü ya ſada a gajarcc. "Yawwa barka da zuwa suka amsa baki daya.. "Yau ma a abuge yake" Malan Lawan mijin ta Salla ya fada bayan shigewar Isma il gida. "Gashi Allah ya bashi kyakkyawar mace mai biyayya, "haba Malam Musa baka ganin yanzu duk ta jema saboda wahala da takeyi. "laka yake Malama Lawan a da in dai mutum ya kalle ta dole ya kyasa amma yanzu duk ta kode kamar wacce ta haifi "ya ya ashirin. "duk da haka da sauranta don yanzu in ka....." "ina wuninku wata mata dake rike da yaro a hannu ta fada dai-dai lokacin da zata gifta ta kusa da su. "lafiya" suka amsa gaba daya. "Mhm masu layya suke da kayan nama" Malam Lawan ya fada. "Tanko dai yayi dacen mata" a cewar Malam Sani. "don ma Hijabi ta sa, amma da dan gajeren mayali tasa da kaga sura" Malam Iawan ya fadi yana dariyar shakiyanci. Amma bata kai matar Alhaji Yahaya ba?. "A wannan ai karshe ce na ji ma ance ya saki uwar gidan" "Kai kuwa ai dole ya sake ta irin wannan daula da ya sannu" "Ba wannan ne yasa ya sake ta ba". Malam Musa Tada. "Me yasa? "Yawwa Malam Lawan kayi tambaya a wajen dan gari. 9 to bar gamin Alhaji Yahaya nada kudi gidan sa ba wadatar binci kuma... "Kai Musa kamar Alhaji Yahaya ace gidan sa ba abinci zabga-zabgan yan "yammatan dake gidan sa kai kace ci dasu" "Gaskiyar ka Malam Sani, baka sani ba dama auri saki ke gareshi, duk wayan nan "yammatan da kake gani gidan kowacce da uwar ta" "Mc yasa har yanzu ba"ayi masu aure bane" "Wai karatu suke" a cewar Malam Sani. "Yo karatun boko wani karatune" "In banda iskaci me suke a makarantun" laka suka yi ta gulma kamar yadda suke yi kullum har dare ya raba, sannan suka shiga wajen kazaman matan su. *** Zaune take gefen gado sanye da doguwar rigar fakistan mai ado tun daga wuya har kasa, kanta tsefe yake ta daura wani baki.dan kwali mai adon jar fulawa tayi tagumi da hannun ta na hagu wanda zane yake tsab da kunshi irin na Sudan. Ta fiyar da taji bata kawo a ranta cewa Isma il ne ba, don tasan lokacin dawowar sa bai yi ba.ya shigo dakin kamar wanda aka jeho, bata san lokacin da murmushi ya kubce mata ba, ta saki hannun ta daga tagumin da take, kai tsaye ta tashi ta taro Isma"il gami da rungume shi, dawowar sa da wuri tayi matukar burgeta, kuma yau kwata-kwata ya canza mata kamar ya kara kyau. Isma"il naji dadin dawowarka da wuri. "Ni ma naji dadin kwalliyar da kikayi don ni "kana nufin kwalliyar ta burgeka?" "Kwarai ma kunta" har yanzu rungume suke da juna kamar yadda ya fada kwalliyar ta bargeshi, yaji sha"awar ta ta kwaranyo zuciyar sa, kamar ya hadiye ta. 10 "Wane irin kamshi nake ji a jikin ka?" "Turare ne wani aboki na ya fesa min. "Kamar turaren mata" "A turare a kwai na mata a kwai na maza?" "Kwarai makuwa Darling". A hankali ta fara cire maballan rigar Isma"il cikin nutsuwa, dai-dai ta circ masa kayan dake jikin sa ta barshin daga shi ai gajcren wando, maballayc uku kadai ta cire a jikin daguwar rigarta, rigar ta rabu da jikin ta cikin sauri ya rage daga ita sai jar shimi, ta saki Isma"il ta nuli makunnin wutar dakin, Isma"il ya kalli bayan ta ya hadiyi yawu gami da yin tsaki cikin zuciya. "Ina da irin wannan matar nake tafiya wurin wasu "yan iska" ya fadi haka cikin zuciyarsa. *** Yau kusan kimanin shekaru biyu kenan Alhaji lawan na neman Jamila kala ya kashe mata kudin da ko zaa yankashi baisan adadin su ba, sarkoki da yan kunna yen gwal bazai iya misalta yawan wanda ya saya ba, shadda leshi atamla duk masu tsada ba irin wanda baya sayowa Jamila reza yanki ba kyauye, kudin da yake kashewa Jamila ko mahaifiyar da ta tsugunna ta haife shi baya kashewa, amma abin bakin cikin ko siket dinta bai taba gani ba,hana rantsuwa ya taba taradda ita tana canza kaya, ya kuma taba yin rawa da ita ta mintin uku fatin wani abokinsa, shima sai da yayi mata alkawarin makudan kudi. a Tafe yake cikin motar kirar jeep chiroki mai ruwan gwal. farar shadda da farar hula muhadu a baki gami da bakin tabarau sanye a fuskar sa. Yau ne bokan ya bashi rana don sauraron matsalar sa da biya masa bukatun sa kamar yadda yayi alkawari. Daidai kauyen BAGADAWA ya saki hanya, hanyar da 11 yabi hanya ce mara kyau hade da rairayi gami da busassun itatuwa a gefen hanyar dajin. Ya sami kusan mintina arba"in yana tafiya bisa wannan mummunar hanyar a hankali ya fara hango "yar kewayayyiyar bukkar bokan da shi ya kira malami, minti biyar da hango bukkar ya isa, ya tadda bokan zaune bisa wani yagalgalalallan buzun da bai gane ko na wace irin dabba ba ne, sai dai abinda ya ba Alhaji Lawan mamaki bokan magana ya ke ba tarc da wani na kusa da shi ba, bil asalima kamar yadda ya lura ko a cikin bukkar bai ga alamun motsin mutum ba. "Eh ka gaya musu an samu" a cewar bokan. "IH"a hahaha dariya, mai karfi ta biyo bayan maganar. "Na riga na gaya muku wannan kashe shi za a yi" ya fada bayan gama dariyar, gaban Alhaji Lawan ya fadi, wato daman wannan bokan har kisa ya ke, "To har an gama da shi madalla da ku bayina, na san ba zaku bani kunya ba, nima har abada ba zani baku kunya ba. salla dai ko? to na daina". Yana gama magana wanı curarren hayakı ya fito daga bakinsa ya nufi wata bishiyar kuka dake kusa da wajen. "Me ke tafe da kai?" Boka ya tambaya har ya buda baki zai fara zuba boka ya daga mai hannu. "Na san matsalarka", ya fadi yana zare ido, Alhaji Lawan shiru ya yi yana kallon bokan. "Matsalar ka Jamila Kala" Bokan ya fadi kamar yadda dan koren sa ya fada masa. "Kwarai kuwa Malam", Alhaji Lawan ya fada a mamakin ce. "Kar ka kira ni malam nan gaba" "To Ma...." "Aa!" ya daka masa tsawa. "To! To! na ji" 12 "Ka kira ni Boka kai tsayc" "To" Alhaji Lawan ya fada a gajarce fuskarsa na kwararar da gumi, kamar wanda kunama ta harba a kan gyambonsa. "Me kake son samu wajenta?" Bokan ya lambaya. "Na dade ina yi mata hasara har yanzu shiru ba wani bayani kamar an aika bawa garin su". "Fadi bukatarka kai tsayc" "Bukatata yadda na kashe kudi na samu makamako" "Har yanzu baka fadi ba, ka sani mu nan ba wani boyeboye ko alkunya, ban kira kai na da malami ba, Boka fa na ce ma ka kira ni, ni ba kura ba ce lulluße da fatar akuya, ban shi ga rigar malanta ba bokanci na ke yi SAK! in kashe mutum ka ke so mu yi fadi za ka yi in arzikinsa ka ke so mu karaya fadı za kayi, in jini ka kake so mu sakar mata, ko mu sata cutar tusa duk wanda ya zo wurinta daga buda baki zai yi magana sai tusa ta barko mata, wane ne ka kě so ciki?t "So nake na sadu da ita" ya fadi da gaggawa kamar subuce masa maganar ta yi. "An gama" Ya dau tsawon minti goma yana hade-haden daga karshe ya hada wani gari-gari kamar kwalli, ba za kice ga kalar abin ba, ya cakuda ya daura cikin wata karamar kwalbar turare. "Karbi wannan " ya fadi yana zazzare ido kamar barawon da mata suka kama. Alhaji Iawan ya miko hannu ya karba ya dan dubi tsakin maganin dake cikin kwalbar, gaskiya ya rena shi a zuciyarsa, ya zaa ce wannan dan garin shi zai biya masa bukata, duk da irin kudin da ya kashe a banza. "Kar ka rana garin maganin" Bokan ya fada kamar ya shiga zuciyar Alhajin, hakan kuma shi ya ba Alhajin mamaki da amincewa da Bokan, abin da Alhaji bai sani ba, Bokaye sau 13 tari kan karanci fuskar mutum su fadi yanayin da suka ganshi cikin farin ciki ko saßanin haka, kuma kowane mutun mai hankali na iya yin hakan. "Nawa ne abin sadakar?" Alhaji Lawan ya tambaya. "Nawa nc kudin zaka cc" Boka ya gyara masa. "To nawa ne kudin?" "Dubu hamsin!" ya fadi da karfi gami da zarc ido kamar beran da tarko ya kama wai shi kar a kawo wasa ko ai ragi. Gogan naki cusa hannu kawai ya yi a aljihu ya debo kudi. Bako irgawa ya dai tabbatar sun haura dubu hamasin. Boka ya miko hannu ya karfe kudin dan kar wani sabanin fasawa ya gifta "Shi wannan kwalli shi ake kira da Kifil in ka sa, duk macen da ta ganka sai ta yi sha"awa, yadda za ka yi amfani da shi, in kajc kofar gidan yarinyar sai ka samu waje ko cikin motarka ka shafa, da kun hada ido an gama, ko me ka ke so zaka samu "Na godc kwarai" ya fada gami da farin cikin kamar an bashi tsaleliyar budurwa. "Shegun masu kudi in banda haka ba zaka ci kudinsu ba" Bokan ya fada bayan fitar Alhaji Lawan. "Duk karya muke ba mu da wani magani, canki fadi ne kawai, ni wannan kwallin ma ban san dame da me na hada ba, ni dai na san akwai garin batir a ciki" ya tintsire da dariya gami da buga kafa har da hawaye. Ya ci gaba da cewa aka yi su bada zakka ko su yi sadaka, sai su dinga goce-goce yanzu idan Allah ya sa maganin ya yi to ni kakata ta yanke saka. Ya isa gida da gaggawa kamar wanda aka koro da ga wajc. "Dannan kaje rasuwar da na fadama" mahaifiyar Alhaji Lawan ta tambaya dai-dai lokacin day a shiga gida. "Banje ba" ya amsa a gajar ce 14 r 1 daidai lokacin ya fara taka matattakalar benen da za ta sada shi da turakarsa. "Me ya sa baka son zumunci ne dannan?" ta ſada cikin kunan rai da bakin cikin wulakancin da ya ke yi mata, wannan karon bai amsa ba, don tuni ya haye sama. Shi kadai ne danta ta kuma sha matukar wahala da fadinta bata baki ne, ta fi jin dadinsa kafin ya samu kudi, amma kudi na zauna masa ya canja sabuwar rayuwa. ya kwashi kusan minti arba"in yana kwalliya zuwa wajen Jamila Kala, Hausawa sun ce in kana da kyau ka kara da wanka, wannan dalilin ne ya sa Alhaji Lawan yin kwalliya da yake ganin zata firgita Jamila, duk da ya san ta saba ganin "yan birmi. Kamar yadda ya shiga bai saurari kowa ba, haka ya fita bai saurari kowa a gidan ba har mahaifiyarsa. Kai tsaye ya wuce farfajiyar da yake ajiye motocinsa, motoci jere birjik kamar a Akija ta Katsina road. Mota ya dauka dunkulalliyä sabon yayin boksuwaja wacce ba kowane Bello da Mudi ne ke shiga irin ta ba a birni. ga Tukin minti ashirin ya sada shi da Burma road inda gidan Jamila kala yake ya kuma yi sa a kofar gidan bude yake dukkan alamu ba wanda yazo, dan da wani na cikin da yaga mota yasan duk masu zuwa gidan Jamila ba talaka. Hannu ya sa a aljihun rigar sa ya dauko "yar kwalbar da ke cike da kwallin da bai san dame akayi shiba. Ya turmutsa dan tsinken da ya siya wajen wani dan koli ya gwale idon sa na dama ya turmutsa tsinke, "wash" ya yi "yar kara gami da yamutsa fuska saboda tsabar zafi da yaji, bai hakura ba don karfin hali ya kara danna tsinken dan sawa daya idan, ya kara gwale daya idon ya dankara masa kwalli da boka yake zancen akwai garin batir a cikin "wash" wannan karon ma kara, ya kara yi ya dade cikin motar kafin radadin ya huce ya 15 dubi dan madubin da a ka tana da don duba baya, idon yayi jawur kamar yadda ya gani yasa wani farin hankici ya goge hawayen daya Gata masa fuska, ya bude motar a han kali ya ziro kafarsa abinda ya ba Alhaji Lawan mamaki gaban sa yayi faduwar da bai taba yiba, faduwar gaban da sai da ya yi jim kafin ya tsallaka kwatar dake ga bansa, "Alhaji Lawan" yaji an kira sunan sa ya daga kai, wayyo Jamila kala ce sanye da riga da wando na jins baki kanta ya sha shamfo sai sheki yakeyi har yanzu kirar na nan kamar yadda take duk ba wannan ne ke burge Alhaji Lawan ba, murmushin da take shi ke burgeshi da kuma mamaki tunda yanke kashe mata makudan kudade bata taba yi masa murmushi ba ko da sau daya ya dada gwale idon sa wai don kwallin ya kara aiki kamar wasa murmushi Jamila kara fadada zuwa dariya. A bangaren Jamila ita murmushi da take yi murmushi ne na ta tabbatar yauma ta kara samun abokin tafiya a gida basai taje nema ba. "Ya ka tsaya a nan?" Ta tamtaya gami da karasowa kusa da shi, hannun sa ta rike izuwa gidan kamar rakumi da akala binta kawai yayi yana da da zarc ido. Har cikin daki ta kaishi suna shiga ta cire masa hula gami da babbar riga da yake sanye da ita. Zaunar da shi tai bisa gado gami da sumbatar kumatunsa. Bari in kullo kofar gidan T'a fada gami da tashi tsaye ta nufi kofar dakin. "Dole tsafi gaskiyar mai shi" Alhaji ya fada bayan fitarta. "T'suntsu daga sama gashasshe" ita ma ta fada dalidai lokacin da take kulle kofar gidan. Rigar dake jikin ta ta fara cirewa daga ita sai yar Bez ta zauna kusa da Alhaji Lawan. Ilankalinsa yayi matukar tashi tashin da bai tabayi ba yaji dadi gami da yin godiya ga boka a zuciyarsa sai dai wata 16 faduwar gaba dake damunsa ca acikin zuciyarsa. wasanni ta kama yi masa har hankalin sa ya gushe ta na lura da gushewar hankalin ta fara ciremasa kaya daya bayan daya cikin gaggawa da dauki gamin da zumudin samun abokin tafiya. *** A gidan su Hajara kuma gardama ce mai karfi ta turnike tsakanin mahaifin IHajara da mahaifiyar ta Hajiya Ladi. "Haba Alhaji yanzu na fada maka matsalar da "yar nan ke ciki kace a rabu da ita "me kike so ayi mata?" "Aje a taho da ita" a cewar Hajiya "Ke kinsan meyc aure kuwa?" "Haba Alhaji ko mai sanin darajar aure ai ba ma kyaleta yunwa da wahala su kashe ta ba" "ita ta saya" "Ni dai gaskiya zanje in taho da ita ko da karfi ne, don ina ji ina gani ba zan bari "yata ta halaka ba" "Ban amince miki ki fita ba in kuma ki ka fita karki dawo min gida" Alhaji ya fada a fusace. "Kar na dawo ma gida?" Ta tambaya a mamakince a zaman su na sama da shekaru ashirin bai faba fada mata haka ba. "Haka na fada kuma haka nake mufi" Zura masa ido kawai tayi cikin mamaki Ki fita harka tsakanin miji da mata in ba so kike ki fada cikin fushin Ubangiji ba" To yanzu Alhaji ya za a yi?" Ta tambaya cikin sanyin murya mai nuna alamun ta amince da gajeriyar nasihar da yayi mata amincewar dole. "Zubawa sarautar Allah ido don duk wanda ya sabawa iyayen sa sai yaga sakamako" 17 tayi" yanzu Alhaji baka yafe mata ba?" "Na yafe mata amma dole taga sakamakon sabawar da "Kai na shiga uku yanzu ni ya zanyi da raina wayyo.." T'a ſada gami da yin kukan bakin cikin halin da yarta ke ciki. Ai sai kiyi ni kinga fitata" ya fada gamida nufar kofar gida abinda Hajiya Ladi bata sani ba dauriya ce yake irin ta maza da zaa tsaga zuciyar sa yafi kowa bakin ciki da takaici. *** Tun daga kwanan farko da Isma"il ya yi a dakin Jamila kala wanda ta kora shi gida saboda iyalin sa kamar yadda tace Isma il bai kara kwana a gida ba kullum da irin karyar da yake shirga wa kwata-kwata bama ya san ganin ta, kullum sai karfe goma na safe ya ke dawowa gida abinci da dan kudin kashewa kullum Jamila ke bashi ba ruwan sa ya wanke goma ya tsoma biyar ga dan tabi da yakeyi da dare : "Wai yanzu Isma"il ina kake kwana ne?" Hajara ta tambaya "Ke ina ruwanki da in da nake kwana nafa gaji wadannan tambayoyin naki na remin wayo" "Amma ya kamata na tambayeka a matsayina na matar ka" Ta fada muryar ta na rawa kamar zata yi kuka, shiru kawai tayi tana kallo sa cikin mamaki kamar bashi ne Isma"il din nan mai dadin zance da yake zuwa gidan su ba gwanin iya kwalliya sarkin iya zance. Can a tsakar gida su Tasalla sun sa hira kamar yadda suka saba kullum. "Oh ni Tasalla wannan yarinya tana ganin tasku sai kace marainiyar dake hannun kishiya". "Ke ma dai kya fada yanzu fa ya dai na dawowa da dare sai iyanzu zaki ga shege ya shigo" a cewar Saude. "Tun da a fara wankau ko kwanon shinkafa da ya bai 18 : sayo mata ba" Larai dake gefe guda ta fada "Kuma daga ganin yarinyar daga gidan gata ta fito in kika yi la"akarin da irin kayan dakinta da shegen ya cefanar" A cewar Saude. To ai baki sani ba tunda ta zo fa bai taba yi mata dinki ba kuma walla..." "Kc Larai karki rantsc." Ta salla ta tari numfashinta,. sanna ta ci gaba "Mahaifiyar sa ta kawo mata super print irin "yar dari uku da hamsin kwanaki." amsa. "Yaushe wacce super print?" Larai ta tambaya. "Wata koriya mai alamar ganyen rogo." T'a salla ta bata ""T'o ai wannan sawar ta biyu." A cewar Saude. "Kwarai ma kuwa ta sa ran wata alhamis ta kuma Kara sawa ran wata talata, yau sati biyu kenan da kwana uku." Larai ta fada daidai lokacin data kamo kwarkwata a kanta ta rabon sa da wanke wa sama da wata biyu in ka dauke wankan tsarki da take yi, wannan kuwa ba sabulu. "Dama ni tun daga tsarin zaman nan nasan ana zaman karya." Saude ta fada. "Gaskiya ya za a ce namiji ya sai da kayan daki na kakaf ina kallonsa." "Ai yarinya ce bata san ILLAR MAZA ba, kuma ba ta san MAZA SAI SANNU ba, har yanzu ba ta tabbatar da MAZA BA SU DA TABBAS ba, kuma,a ta yi hankali ba sai ranar da ta tabbatar da NAMIJI BA DAN GOYO bane..." "Ahayye ayuuriri." Suka bushe da dariya jin irin kalmomin da Tasalla ke fada kan maza kamar ba namiji ne ya haifeta ba. "Allah da gaske nake Saude ba za ta yi hankali ba sai ta tabbatar da NAMII TABARMAR KASHI ne ta kuma hakkake da NAMIJI KWANDON ZAWO ne.." 19 "Suka kara bushewa da dariya karo na biyu, jin Tasalla na sakin baki. "Amma dai har da mazajen wajen Katsina ko?" Saude ta tambaya tana dariya. "Ke ban son iskanci kina nufin iyaycna." "Ai namiji kika ce." "Ban da iyayena." "Mu da namu iyayen kenan?" suka kara bushe da dariya ganin zare ido da Tasalla ta fara yi tun ba a je ko ina ba maganganun na neman faddawa kan iyayenta. A cikin dakin Hajara kuwa hirar da ta biyo baya "Yanzu kana nufin a matsayina na matarka ba zan tambayeka ba?" Hajara ta kara maimaita tambayar. "Kina ban ci da sha ne?" Bai san-lokacin da kalmar ta subuce daga bakinsa ba. "Ina dai ciyar da kai na, wanda kai ya kamata ka ci da ni." Ta fadi haka ganin Isma"il bai san kunya da kara ba, gori na farko da ta fara yi masa kuma shi ya ja, duk da haka bata ji dadi a zuciyarta ba. "Na gode." ya fada a gajarce don bashi da abin cewa. "Ai kai ka ja." Ta fada a nadamance. Banza ya yi da ita, sai dai abinda ya kudurce a zuciyarsa ba zai kara dawowa ya kwana a gida ba har lokacin da zata gaji ta bar gidan don ya gaji da ita, inin ya so ya koma wajen Jamila ya tare tunda tana son sa ga kuma kudi, ya yi godiya a zuciyarsa rashin haihuwa dake tsakaninsu in suka rabu sun rabu kenan, dama shi ya san aurc abu ne mai wahala gwara zaman bariki in ka gaji ka gudu ko ku bata ba mai tuhumarka, tunda baku tara shaidu ba, a hanya kuka tsinci juna a hanya zaku yarda juna. *** BAYAN WATA BIYU 20 Bakin cikin halin da Isma"il ya jefa Hajara ya fara sa ta ramewa ga tari da Hajara ke yi, wanda bata san abinda ya haddasa shi ba, magani ba irin wanda bata sha ba, amma tari kullum kara gaba yake yi, kamar maganind a take sha na kara tarin ne. Wankin da take ma dai nawa ta yi saboda tarin, kudin da ta tara, shi take ci, da kuma magani, Isma"il kuwa ba ruwansa, shi barikinsa ya sa gaba. Kuma kullum kara tsananta yake уi. "Kuf.... kuf.... kuf.." Tari ya turnuke lajara kamar yadda ya saba kullum duk lokacin da ta bude baki don yin magana, sannan ne lokacin da shi kuma tarin zai fara aikinsa. Isma "il dake zaune gefen gado ya harareta ya matsa gefe guda gami da toshe bakinsa da hannu da wani dan hankici mai ruwan kasa da ke hannunsa, Hajara na son yi masa magana amma tarin da take fama da shi ya hana. "Isma.....kuf.....kuf... ""Tarin ya kara turmuketa. Ya karа kallonta kallo irin na wulakanci. "Wai Hajara wacce irin rashin lafiya ke damunki haka? Ni fa gaskiya ba zan iya zama dake kina irin wannan tarin ba, don tun muna firamare ake gaya mana irin wannan tarin communicable disease" "IHaba....kuf.... kuf.... Isma"il ai Allah...yake dorawa mutum cuta shi kuma ke yaye masa, ka yi hakuri tund ina shan maganiczan samu sauki in Allah ya yarda." Hajara ta yi sa"ar fada, wannan karon tarin bai yi sa"a a kanta ba. "Ba wanı sauki yau watanki nawa kina tarin gashi kullum sai ramewa kike, in ba dama kawai ki tafi gidanku ni ba zan iya zama dake haka ba, in kin sami

Chapter 1 of 4