An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
GARARI
VIBB PUBLISHERS
GARARIHADIZA ADAMU SHITU (Matar Muhd.Nuhu Namarwa)
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
GARARI
2
NA
HADIZA ADAMU SHITU
(MATAR NUHU MUHAMMAD NAMARWA)
1
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Garari part 2
aba daya jikin Harira ya Ggama mutuwa hankalinta
ya yi matukar tashi
zuciyarta ta duguznuma,
tunaninta ya rarraba akan wannan bakin
albishir din da matan suka zo mata da
shi, shin da gaske ne mutumin nan da
zai auri Hansa'u yana da cutar Aids, ko
kuwa makirci ne irin na mata ina zata
sami wadannan tambayoyin wacce
hanya za ta bi ta gano kan al'amarin to
in ma da gaske suke ya zata yi ta raba
wannan auren da Lawai ya dora burinsa
kacokan a kai, suma ya zame musu wata
madafa a rayuwa.
Domin ban da wannan gidan da ya
zama mallakar mutumin ne da suke ciki
ya zama duk motsin da ta yi sai ta ga
wani abun da ya zamo shi ya sai musu.
3
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Yanzu matsalar kayan abinci ta
kau store dinsu cike yake da kayan
abincin da ya sai musu banda kudaden
da yake dankara musu, duk kwana biyu
idan ya zo zance wajen Hansa'u. To
amma wannan alkairin da yake musu zai
iya sa zuciyarta ta danne wannan
maganar da ta ji wadda barinta tamkar
salwantar da rayuwar 'yarta ne, sam
bata jin cikin zuciyarta zata iya wannan
dauriyar.
Tana son 'ya'yanta tana son
inganta rayuwarsu da farin cikinsu.
Wannan tunanin. ya hana idanuwanta
rintsawa kafin wayewar gari zuciyarta ta
Karfafa da shawarar da ta yanke na fara
zuwa bincike.
Washe gari ya kasance ranar
Lahadi ne ta bi kwatancen da Lawai ya
taba yi na gidan Alhaji Ahmad Ahuta.
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Unguwar shiru bata cika da yawan
jama'a ba amma hakan bai hana ta gano
gidan Alhaji Ahmad ba, saboda
shahararshi, a unguwar.
Gidane katon gaske fiye da
zatonta ma aikata na ta fenti daga ciki
ga katon get din gidan a rufe ta sauke
ajiyar zuciya tana karantar makwabtan
gidan da take ta tunanin shiga.
Daya daga cikin gidajen ta yi
tambaya game da shi, duk yawancinsu a
rufe kofofinsu suke.
Daga can ta hango kofar wani gida
a bude wata budurwar yarinyar ta fito ta
tsaya tana rike da kofar da alama wani
take jira ta nufi gidan ta yiwa yarinyar
sallama, ita kuwa ta amsa da fara'arta ta
gaishe ta sannan ta bata hanyar shigewa
a take ta samu karfin gwiwar shiga daga
ainihin gidan zuciyarta cike da addu'ar
5
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
samun nasara a kan abin da ta shiga
nema.
Ta yi sallama matar gidan ta fito
daga kiching da ga ni ba tambaya
mahaifin budurwar yarinyarce saboda
kamanin. Ita ma da fara'a ta karbeta
sannan tai mata ta yin shigowa daga
cikin falo, bata musu mata ba, ta bi
bayanta zuwa cikin wani katafaen falo
wanda yasha kayan alfarma sai kamshin
turaren wuta dan maiduguri ke ta shi.
Bayan sun gaisa shiru ya ratsa a
tsakani ya yin da Harira ke ta tunani ta
inda zata so ma magana har matar ta
dan Kosa ta ce.
"Baiwar Allah daga ina ban fa
gane ki ba?'
Harira ta yi murmushi. "Ba ma ki
sanni ba, ni ma kuma ban san ki ba ai. A
takaice ni ce mahaifiyar amayar da
makocinku zai aura Alhaji Ahmad
6
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Ahuta, na zo ne nan ganin ku ne
makotansa, kuma da na kowane, dan na
yi bincike a kan wani abu da ya shige
min duhu".
Take ta zayyanewa matar zancan
da aka sanar da ita a jiya da yamma,
kuma.da abin da ya kawo su.
Ta dora da cewa "Shine na shigo
nan dan yin bincike tun da dai da na
kowane, kuma za ku iya sanin wani abu
game da shi, tunda ku makotansa ne
kuma al'amarin ya hada har da mutuwar
matarsa da kuma sakin wasu matan
nasa
Nan da nan fuskar matar ta juye
zuwa kalar tausayi.
Sai dai ta kasa maganar har zuwa
'yan dakiku sannan ta nisa.
"Ni dai abinda na sani matarsa da
ta mutu ta yi doguwar jinya, amma ban
san wanne ciwo ta ke dauke da shi ba,
7
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
har zuwa lokacin da Allah ya yi ınata
rasuwa, sauran matan da yake aure ban
ma sansu ba, tunda ba shiga gidansa
muke yi ba, saboda baya son a dinga
zuwa masa gida".
Harira ta sauke ajiyar zuciya tana
godiya. Duk. da bata samu bayani sosai
yanda ta ke so ba, amma shimfidar
fuska tafi ta tabarma, inji Malam
Bahaushe.
Bayan ta fito daga gidan har ta
fara nisa sai ta ji ana cewa "Hajiya
tsaya".
Sai ta waiwaya don ta ji mai
maganar. Kamar da ita yake, sai ta ga
wani saurayi ne, wanda tun shigowarta
gidan ta kula da shi yana wanki a tsakar
gida. don haka ta tsaya cak! Tana
saurara karasowarsa.
8
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
"Hajiya na ji tattaunawar da ku kai
da Maman Fati, ganin cewa ina da
masaniya akan wasu abubuwan da ki ka
tambaya yasa na biyo bayanki, amman
mu fara barin layin nan tukun na".
Batare da ta yi masa musu ba ta
fara tafiya ya ce "Ni suna na Aminu
yaron gidan Alhaji Ahuta ne ni, ina yi
masa 'yan aikace aikace saboda na
shigo ne nan gidan danna gyara musu
injinsu daya lalace na ji hirarku tare da
Maman Fati, ita kanta tsoro ne ya hana
ta fada miki gaskiya, ni kuma na ga
lamarin ba na 6oyewa ba ne,
musamman tun da ya shafi lafiya da
barazana da rayuwa tunda ki ka zo
neman gaskiyar magana bai dace a 6oye
miki ba, tabbas akwai mun san abubuwa
a boye kamar yanda ki ka ji a kallah na
zauna da matan Alhaji Uku kuma duk
9
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Kananun yara ne da basa wuce shekaru
sha biya sha shida.
Asma'u ya aura wadda bata fi
shekara biyu ba ta fara matsananciyar
cuta wanda har sai da aka kwantar da
ita, a Asibiti kuma tana Asibiti ya
dankara mata saki har uku tun daga
ranar ban kuma jin doriyarta ba.
Sannan ya kuma auro wata
yarinyar Maimuna ita kuma shekararta
daya ya sake ta ita ma bayan tasha fama
da rashin lafiya, sannan ya auro Bahijja
ita ce ta haura shekaru biyu Allah ya yi
mata rasuwa bayan tasha fama da jinya
wata rana ina aiki na ji yana hira da
abokinsa a waya yana fada masa wai
malaminsa ne ya gaya masa zai rabu da
ciwon da yake da shi, ta dalilin auren
wata yarinya me kananun shekaru, cutar
zai samu maganinta gaba daya, amma
sai ya yi aure auren mata a cikinsu zai
10
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
auri maganin cutarsa na ji ma ina
tunanin wacce irin cuta ce wannan.
Duk da ya taba yin wata jinya mai
tsanani kamar ba zai rayuwa ba, amma a
wancan lokaci cutar typot akace ke
damunsa.
Wata rana ina sharar dakinsa na
tsinci wata takarda sakamakon cutar
kanjamau da sunansa a jiki, kuma bata
fi wata guda da yin wannan hirar ta su
da likitan ba ya auro Amina, ganin
kankantar yarinyar yasa na dinga
tunanin Allah yasa shawarar likita
ya bi ya aureta, ita ma batafi
shekara ba ta kamu da matsanancin
ciwo daga nan ya sake ta, sannnan ya
auro wannan wadda ta mutu kwanan
akanta ne na gane ciwon mutuwar
yarinyar saboda tun farko bata son
Alhaji kuma ta yi iya kokarinta ta bar
shi amma iyayenta suka dage a kan
11
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
zamanta da shi wanda daga karshe ita ma
abinda ya faru da suaran matan ya faru da
ita. sai dai ita ta samu sassauci saboda bai
saketa ba sai dai ta zauna a Asibiti tsawon
wata uku har ajali ya sauka akanta
sakamokon buguwar da zuciyarta ta yi
Ai kafin ya gama bawa Harira
labari gumi ya gama jika jikinta ya
soma rawa.
Ya ce "Ki kwantar da hankalinki
Inna tunda Allah ya sa ki ka sa ni batare
da an yi auren ba, amman duk hanyar da.
za ki bi ki bita don ki hana yarki shgowa
gidansa, don ceto rayuwarta.
Harira ta share gumi "Na gode na
gode dan nan Allah ya saka maka da
alkairi ya sa ka gama da duniya lafiya”.
Ya ce "Amin Umma ai yiwa wani
yiwa kai ne domin ina da kanne ni ma.
Sun rabu amma jikin Harira bai
daina bari ba, saboda ta ga gaskiya a
12
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
tare da shi kuma ta yarda da abin da ya
gaya mata, saboda yanda ta shigo cikin
tashin hankali gaba daya su Asiya na
tsakar gida, amma suka biyo ta aki, suna
tambayar lafiya.
Duk da ta ce musu ba komai
hankalinsu ya kasa kwanciya
musamman Asiya da ta zauna ta zuba
tagumi sai Umaima ce ta ci gaba da
lissafin kawayenta za su kaiwa katin
gayyatar biki.
Wanda dama daga ita sai Asiya
suke ta shirya shiryen ita kam ko zama
awajen bata yi ba, ta debo wankin
kayanta ta na ji domin lamarin auren
nata jinsa kawai take yi kamar tatsuniya.
Yanayin da Ummansu ke ciki ya
dami zuciyar Asiya ta kuma yi duk wata
hikima da ta gane ko Umman zata gaya
mata abin da ke damun zuciyarta amma
sai Umman ta nuna mata ba komai
13
3
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
bayan ga komai din ta na gani a
shimfide a kan fuskarta sai dai ta kasa
bayyana mata.
Tuntuni ta ke ta sake sake akan
abin da zai iya zama sanadin damuwar
Umma, babban tashin hankalinta ace
wata matsala ce game da auren Kanwarta Hansa'u wanda alamu ya
soma nuna hakan..
Tana gyara su Mahmud wajan
kwanciya. Ummansu na tsakar gida tana
dibar ruwa da za ta yi wanka wani yaro
ya shigo da sallama "Wai ana kiran
Hansa'u"
Muryar Umma ta ji ta ana amsawa
yaron "Je ka ce bata nan
Ita kanta Umman bata san lokacin
da wannan kalmar ta subuce mata ba ta
fito daga bakinta ba.
Asiya da ta tsaya cak cike da
mamaki har Hansa'u da ke kwance a
14
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
kan tabarma sai da ta mike zaune sun
hada ido da Asiya, amma babu wacce ta
iya magana da 'yar uwarta.
Bayan mamakin yanda ta iya
sharara karya lokaci daya har da
mamakin dalilin karyar.
Ita kanta Umma jikinta ne ya
dauki rawa ji take yi kamar ma ya
shafawa Hansa'unta wannan ciwon sai
gata ta zauna cikin tashin hankali sunan
shi kawai da ta ji ya gama girgiza
zuciyarta.
Asiya dake hangota ta window ta
fito da sauri "Ummana ya ya dai me ya
ke faruwa?"
"Dauki wannan ruwan ki samin a
bandaki"
Ta fada ba tare da ta bata amsar
tambayar ta ba. ta yi yanda ta ce, amma
ita ta sake tsinkewa zarginta yana son
zama gaskiya koma me yake ta da
15
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
hankalin Umma yana da alka da auren
Hansa'u, koma me Lawai zai yi yau za a
yi ta ta kare, dan ba zan kai 'ya ta ga
halaka ba.
Saboda son duniya abin da Harira
ke ta nanatawa kenan a zuciyarta. Har
zuwa lokacin da Lawan ya dawo lokaci
ne da ta ke tsammanin gaba daya yaran
sun kwanta barci.
"Yau na sha wahala wallahi.tunda
na fita nake yaron rabon katin bikin nan
manyan abokaina, ba ki ga yada suke yi
min karaba".
Ya fada ya yin da yake ajiye
hularsa ta hango tudun kudi a aljihunsa
yanda yake fara'a ta san cewa ba kanana
kudi ya samo ba ba a wajen abokansa da
kyar ta iya tattaro karfin gwiwar ta ta ce
masa "Ka kuwa yi bincike akan
mutumin nan?"
"Wa ke nan tukunna?"
16
Hadiza Ado Yalwa
ma.
Garari 2
Ya mayar mata da tambayar shi
"Alhaji Ahmad ahuta mana"
Sai ya yi dariya "Ni na ga randa
kauyenci zai barki Harira ke kin san
waye Alhaji Ahmad Ahuta kuwa? То
duk garin nan babu wanda bai san
Alhaji Ahmad ba, to wani bincike zan
yi a kan shi bayan kowa ya san shi ba
6oyayyen mutum ba ne".
Harira ta sauke ajiyar zuciya.
"Eh tabbas ba 6oyayyen mutum ba ne
shi yasa ma al'amuransa kyawawa da
munana ba za su boyu ba”.
Daga nan ne ta so ma ba shi
labarin matan da suka zo wajenta har
zuwa binciken da ta yi a kai da cewa
yana dauke da cutar kanjamau
17
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Nan da nan annurin fuskarsa ya
dauke cikin tashin hankali da
hargowa ya ce "Wato ke duk abin
alkairin da zai same ni sai kinn yi
kokarin kin haramta min shi, shi ne
za ki bullo da maganar yana da aids
to ba aids ba in ma Asibitin Zana ne a
kansa sai anyi auren nan, kuma dai
'ya dai ta wa ce ni na ke da iko a
kanta, in ma bakin ciki kike yi da
samun arziki da rufin asirin da Allah
ya yi min ta sanadinshi, to sai dai
bakin ciki ya kashe ki, domin ko za a
kaita yau gobe ta mutu sai an yi
wannan auren babu fashi tunda
Lawan ya soma daga murya da
hargowa duk maganganun da yake yi
daga Hansa'u har Asiya duk suna
18
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
jiyowa, domin babu wacce ta rintsa a
cikinsu.
Dukkaninsu suka mike zaune
cikin tashin hankali Hansa'u har ta
fara kuka tana cewa mutumin da ya
ke da ciwo zai aura min yana cewa ko
da za a kai ni yayo gobe na mutu sai
an kai ni, wannan wane irin rashin
adalci'ne.
Asiya ta yi saurin rufe mata baki
ita ma cikin muryar kuka ta ce "Ka da
ki fadi munanan kalamai a kan
mahaifinmu domin bai isa yin komai
a kanmu ba, sai abin da ubangiji ya
zartar a kanmu ki yi shiru mu yi
addu'a daga nan ita ma kuka ya ci
karfinta, har lokacin basu daina jin
hayaniya a kan maganar ba.
19
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Kamar yanda Ummansu bata
rintsa ba haka su ma su ka yi kwanan
zaune ba tare da sun rintsa ba, domin
sun san halin mahaifinsu, sun kuma yi
alkashin daya dauka a kan maganar
auren, na cewa ko gawata ce sai ya
kai gidan Alhaji Ahmad ita kuma
Harira in dai ta sake yi masa magana
a kan auren to a bakin aurenta.
Kwanaki shidan da suka rage
Hansa'u ta tare a dakin mijinta sun
zame musu tamkar zaman makoki
babu wani me kuzari kowa ni me
kakkafar maganar a cikinsu, hatta da
rabon goron biki sun dakatar da yinsa.
Ya ga gurin lawan kuwa ba abin da ya
sanja kullum cikin hidimar raba katin
daurin auren yake.
20
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Ana saura kwana uku daurin
aure Alhaji Ahmad ya aiko a ai masa
kiran Hansa'u
Ummansu da take shara a tsakar
gida ta ce "Ace bata nan ashe Lawan
ya biyo bayan dan aiken kafar ya ji
amsar da Harira ta baya, ya karasa
shigowa afusace. Gabanta ya yi
mummunar faduwa don bata taba
tsammanin dawowarsa a wannan
lokacin ba.
Ya dubi Hansa u da take zaune
ya daka mata tsawa "Ke ta shi ki
fita".
Cikin kankanin lokaci ta rame,
idanuwanta duk sun kumbura sbaoda
kuka, ya saka daga mata tsawa "Та
shi ki je mutuniyar banza ni na ke da
iko a kanki ko ita? kuma daga yau
21
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
idan ya kara kiranki ki ka ki zuwa ni
da ke ne a gidan nan, saboda tsabar
rikicewar da tsawar da ya buga mata
ko takalmi bata saba bare mayafi, ta
yi hanyar soro tana kuka, ya sake
daka mata tsawa "A haka za ki fita sai
kace hauka sabon kamu".
Ya kalli kayan jikinta wani
soshasshen lesi ne da wata
kodaddiyar atamfa wadda ya manta
tsawon tun kwanakin da yake ganinta
a jikinta.
"Maza ki je ki canza wadannan
kayan ki wanko fuskarki"
Ya juya ya dubi Harira wadda ke
tsaye da tsintsiya a hannunta jikinta a
sanyaye yanayinf uskarta kamar zata
rushe da ihu.
22
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
"Ke kuma dama na dade da
sanin ke ce ke nuna musu ni din ba
komai ba ne a idonsu, har su ke yi
min kallon raini, to ni din nan da ki
ke gani ba irin mazajen da za'a dinga
karyawa doka ba ne a zaune lafiya, ba
kuma na cikin mutanan da za su
dauki raini da tozarcin mace a idon
duniya, in dan kina takamar ganinsu a
gabanki, kina tare da su, to ki je na
sake ki bana bukatar na sake ganin
kafarki a gidan nan".
Gaba dayan masu hankalin sai
suka rushe da kuka.
Ita kuma kalmar Innalillahi wa
inna ilayyi raj'un da ta fada ta sa ta
karfin zuciya.
Ya daka musu tsawa mutuwa a k
ayi da za ku sa mutane a gaban kuna
23
Hadiza Ado Yalwа Garari 2
kuka za ku taramin makota toh duk
wadda na kuma jin bakinta sai jikinta
ya ga ya mata kowa ya yi mai dalili.
Ya shiga daki ya tuso Hansa'au
a gaba, tana kuka har suka fita, sai a
lokacin kuka ya zowa Harira ya yin
da ta ke ta nanata wa Hansa'u
Addu'ar kariya daga Ubangijin,
sannan ta cewa su Asiya ku yi shiru
dama ko da bai sake ni ba, zan bar
gidan domin ba zan iya ganin ranar da
za a fitar da Hansa'u a gidan nan
ba,gwara bana gani, gwara ba na ckin
gidan ku kwantar da hankalinku in dai
da ragowar zamana zan dawo mu ci
gaba da zama tare idan kuma babu ya
zama dole mu yi hakuri zan yi ta
binku da addu'a a duk in kuke na san
24
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
za ta same ku kuma Allah zai
kareku".
Ganin hankalinsu ya ki
kwanciya yasa ta dinga nuna musu
kamar ta fasa tafiyar, sannan ne fa
bacci ya debe su ita kuma wannan ne
ya bata damar yin shirin ta a nutse.
Ana idar da sallar Asuba ta saci
jiki ta tafi babu wanda ya ganta a
cikinsu.
Dukkaninsu sai wayar gari su ka
yi suka ga Ummansu ta barsu barin da
basu san lokacin dawowarta ba, sun
shiga tashin hankali kamar wanda
dayansu ne ya mutu, sun kasa aiwatar
da komai a gidan sai kuka.
Tun jiya Umaima ta ke ta saka
wani abu a ranta ganin har wayewar
yau da Ummansu ta tafi babu wanda
25
Hadiza Ado. Yalwa Garari 2
ya kawo mafita da za a raba ta da
wannan auren ya bata karfn guiwar
kawo tata shawara.
Bayan da ta ji babansu ya fita
yana cewa duk yarinyar da ba za ta bi
umarnin sa ba to ta dauki haramar
bar min gida donn ni ba zan dauki
halin raini da Harira ta dora ku a kai
ba, ta dubi yayarsu Asiya da ke ta
sheshshka da ajiyar zuciya.
"Yaya ni ina ganin yaya
Hansa'u ta gudu ta bar gidan nan in
ba yaga bata nan ba dole ya hakura da
maganar auren.
Asiya ta ce "Ni kuma ina ganin
ni ya dace na fuskanci wannan
rayuwar ni ya dace da shiga wannan
ramin mutuwar domin bakin cikin da
nake ciki a yanzu nafi zabar mutuwa
26
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
da rayuwa zan fadawa Baba ya mai
da auren nan kaina, maimakon
kanwata Hansa'u me Karancin
shekaru.
Hansa'u ta yi saurin rike Asiya
ta ce, duk ba zai ai haka ba yaya ni
baba ya fi sha'awa da na shiga
wannan rayuwar kuma ni ma da na
rayu batare da Ummata ba gwara
mutuwa da rayuwa. duk abin da zamu
yi yanzu harzuka zuciyar Baba zai yi
in dai ba amince aurena da Alhaji ba
harzuka zuciyar Baba kawai zai yi.
Mu yi addu'ar Allah ya kawo
mana dauki shine kawai abin da yafi.
Kamar daga sama sai ji su kai an
shigo hade da sallama Dan Baba suka
gani a tsaye Baban wansu. Ba laifi
yau yana tare da tsafta kuma babu
27
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
tsumman shaye shaye a hannunsa, da
alama yana cikin nutsuwarsa.
· Abin da ya fara cewa musu shi
ne "Ina Umma?"
Asiya ce ta yi saurin ba shi amsa
"Ta tafi unguwa
Sai a lokacin ya kula da
fuskokinsu ya dubi Hansa'u "Ke
kuma me ya sa ki kuka?"
Ba wanda ya ba shi amsa. Ganin
haka ya sa shi cewa "Na zo ne na
yiwa Umma sallama zan je Lagas ku
ce mata don Allah ta yafe min"
Ya lalubi aljihunsa ya dauko
dari biyu ya mikawa Asiya "Ungo
wannan ku bawa Umma in ta dawo
ku kuma ku raba wannan ku yi min
addu'a.
28
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Dubu daya ya basu. Sai ya jin
muryar Babansu su ka yi yana сеа
"Zo ka fita rmin daga gida ban ce kar
ka sake shigo min gida ba, daga yau
karka sake shigo min gidan in ma dan
uwarka ka ke zuwa gidan nan to yau
ta fita ka je can ka neme ta"
Kalmar ba karamin girgiza dan
Baba ta yi ba, sannan ya dubi
kannensa ya ga dukkansu kuka suke
yi. Hankalinsa ya yi matukar ta shi
yana so ya tambaye su me ke faruaw,
amma babansu ya ki bari sai tura shi
yake waje yake tare da cewa "Karya
sake shigo masa gida.
Shi kuwa Lawan a Gangarensa
hadimar aure ma ta zame masa guda
biyo domin tunda ya ga ya samu gida
mai dan sararin dakuna ya karbi ta
29
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
yin tsohuwar bazawarsa da ke sayar
da abinci a kasuwa da zummar zai
toshe daki da rumfa ya zama daki da
rumfa ya zame daki dai dai barin
Harira gidan yasa ya je da bukatar a
daura aure ta tare kafin bikin domin
baya son a yi dauren aure batare da
mace a gidan ba.
Dama Asabe shi kawai take jira
don haka bata yi wani musu ba ta
amincewa bukatarsa.
Ta fadawa yayanta da ta ke
zaune a gidansa nan da nan shi ma ya
amince a ka daura aure.
A gobe dauren aure da daddare
su Asiya sai jin mata suka yi nata
shigowa suna rangwada guda sun
shigo dakin Ummansu suna jin shewa
da maganganu mata adakin.
30
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
A maganganun na su ne suka
fahimci cewa amarya a ka kawo,
amma sun kasa ganewa haya aka
kawo ko kuma amaryar babansu ce.
Basu gasgata abin da suke zargi
ba sai da su ka ga babansu ya shigo
da leda a hannunsa yana ta zabga
kamshin turare sai bayan da ya yi
kamar rabin awa a cikin dakin sannan
ya kira wo ya ce "Kun ga wannan ita
ce matar dana aura, ku dauketa kamar
ita ta haife ku, dukkansu suka bi ta da
kallo.
Asabe gajeriya ce baka sol
saboda mayukan da take shafawa
akwai jabun hakoron makka a
bakinta, ta na da kirki sosai ta dinga
tambayar sunayensu, daya bayan
daya sannan ta janyo ledar daya shigo
31
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
da ita gasasshen nama ne da Kabeji
da tumatir ta raba shi biyu ta basu
rabi.
Sannan ya ce da Asiya dukw ani
abu da kki ka san naku ne na
amfaninku a nan dakin gobe ki zo ki
daukar musu Asiya ta ce to.
Daga nan suka koma nasu dakin
cike da mamakin wannan aure na
gaggawa na Babansu abin da ya ma fi
basu yanda a ka yi idanun Babansu ya
rufe ya iya auran wannan matar da
suke ganin ko Ummansu ta girmewa
in bata yi sa'arshi ba, to ko zai girme
mata da kadan ne, sun dai ji dadin
yanda take da fara'a.
Daren ya zame musu daren
bakin ciki domin washe gari ne aka
32
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
aura auren Hansa'u da Alhaji Ahmad
Ahuta.
Su na jin hayaniyar mutane
Abbansu nata shiga da fita a tsakar
gida, amma babu wacce ta fito tsakar
gidan a cikinsu hatta Sayyada da take
karama bata san abin da yake faruwa
ba, ganin yayyanta na takore a daki
yasa itama take fitowa.
Asabe ce ta shigo da kwano a
hannunta ta ajiye musu ta ci kwalliya
sosai da koriyar atamfa ta ce "Wai ni
'yan mata me ku ke yi a daki har
yanzu ba ku fito ba, ba ku yi wanka
ba har da amaryar ma, ni ma da
nake tsohuwar amarya ga shi na ta shi
na shirya, to ku yi maza ku ta shi ku
yi wanka ku shirya kafin mutane su
fara shigowa, ga wannan kuma ku ci"
33
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Yanda su ka ga Asabe nata
lallashinsu yasa' su ka ji baza su iya
bata kunya ba haka suka ta shi
kowacce ta yi wanka.
Kuka na zahiri ya dauke daga
idanuwansu sai dai na zuci.
Gidan ya cika makil da jama'a
ainun biki sosai ake yi amma duk
cikar mutanen basu wuce na kawayen
Asabe da danginta ba, sai daidaíku
kawayen Umman su da suke shigowa
daga makota.
Asabe da yake wayayyiyar
macece duk wanda ya shigo ta na
karbarsa da fara'a ta kuma ce ai
Harira ta dan fita ne wasu shirye
shirye,