mata murmushi ita kuwa kai ta ɗauke,tana mai jawo wayarta ta kunna data so take ta yi bincike don gano shin abubuwan da suke faruwa zai iya kasancewa ko kuwa ƴarta ce kawai ke da shi.
Tunanin ta watsar ta shiga WhatsApp ta fara duba saƙonnin mutane masu yi mata barka kafin kwatsam ta ganta cikin wani group.A hankali ta soma biyayar abubuwan da ke faruwa sai ta ga amsoshin tambayoyinta kan wani posting.
```“M” CIKIN TAFIN HANNU,MAUME HAND/PAUME DE MAIN
Chiromancy wata daɗaɗiyar hanya ce ta hango makomar mutum da kuma fassarar halayyar mutum daga dalilin layukan hannu. Wani lokaci waɗannan layuka na iya samar da lambobi da haruffa. Ɗaya daga cikin waɗannan wasiƙun na iya zama wasiƙar M, ma'anar wacce mystics da dama suka yi nazari a kanta.
Kamar yadda mutane da yawa suka yi imani, layukan da ke kan tafin hannunmu suna bayyana halinmu da ƙaddararmu. La lettre M est attribuée à des personnes vraiment spéciales(The letter M is assigned to truly special people). An ba su kyakkyawar fahimta kuma suna wakiltar abokan haɗin gwiwa akan dukkan wasu kasuwanci.
Idan mutanen da kake so suna da wasiƙa ta musamman M a cikin tafin hannu ya kamata ka sani cewa ba za ka iya raina masa hankali ba kuma ta wata hanyar ba za ka iya yin ƙarya ko yaudarar wannan mutumin ba. Kasancewar shi mai dubara da hankali da tsantsar lura sosai, mutamin da ke da harafin M a tafin hannu cikin sauƙi zai fahimci cewa ana yi masa ƙarya ne ko yaudara.
``Matan da suke da harafin M a tafin hannunsu suna da zurfin tunani fiye da maza, har ma da waɗanda suke da wannan wasiƙar. Ana yi musu baiwa da ikon sarrafawa da shawo kan duk wani cikas a rayuwa, kuma sun san yadda ake amfani da albarkatu da damar da ake da su.
Harafin "M" a kan tafin hannu ma na iya nufin:
• Ƙwarewar shugabanci
• Iko wato power/pouvoir```
Zuciyar Safeenatu banda bugawa babu abin da take yi har sai da ta ajiye wayar ta je ta ɗauki ruwa masu sanyi ta sha .Ta dawo ta zauna don ƙara duba saƙon sai dai hatta shi kansa group ɗin ya ɓata a wayarta babu shi sam .Kamar mahaukaciya haka ta miƙe ta je ta yi wani gurwanau a gaban net ɗin da aka saka Baseerat,ta zuge zip ɗin ta kalli ƙofar toilet inda motsin ruwa ke ta zuba da alamu Habibah wanka ta shiga ba tare da ita ta san yaushe ta shiga ba .
Murya a ɗan kasalance ta ce “ Baseerat ni ce mahaifiyarki,ni na haife ki.Duk wani wanda bai son ganin kin cutu to tabbas sai dai ya biyo bayana,don haka kar ki ga kamar ban son ki a'a wallahi zuciyata raunk ne da ita.Magana nake son yi miki game da abin da na gani cikin wayata,shin kina da masaniya? In dai tabbas ke ƴar baiwa ce kamar yadda saƙon nan ya bayyana to ki buɗe idonki ki kalle ni” ko rufe baki ba ta yi ba kuwa Baseerat ta buɗe idon sai da Safeenatu ta dafe ƙirji saboda tsoro.
“Mine ne wai?” daga bayanta Habibah ta tambaya ,zip ɗin net ɗin ta mayar tana mai cewa “ babu komai Gwaggo Habibah,na yarda na aminta da lamarin nan gaske ne ana samun ƴan baiwa to Allah bata ikon yin amfani da ita ta hanyar ƙwarai” ruwan sama ne suka fara sauka a daidai lokacin da Safeenatu ta rufe bakinta.
Gwaggo Habibah ta yi wani ɗan ihun murna tare da rungume Safeenatu ta ce “ kin ga ko? Ƴarki ta musamman ce ancestor/ ancêtre suna tare da ita”
A wannan daren cike da zullumi da tunani Safeenatu ta yi shi,da ta samu bacci ya ɗauke ta mafarkai ta yi barkatai akan goben Baseerat.
Washegari tun da safe kukan jaririn Murjanatu ya cika gidan kamar wanda ake cirewa rai.
“Jaririn can ba dai kuka ba” Safeenatu ta faɗa .
Habibah ta ja baki ta yi shiru tana tuna jiya irin gumurzun da suka yi ita da Hajara akan kurwar yaron.Dakyar ta yi nasara ta tone ta tare da saka Hajara don doli ta mayar masa abarsa wacce tuni ita kanta kurwar ta yi rauni,kukan da yake yi kuma saboda ciwon jiki ne.
★A kwana a tashi babu wuya wurin Allah yau ne sunan Twins ɗin Safeenatu waɗanda dangin Bashir suka yi bajinta sosai wurin yankan manyan raguna uku biyu na BASHEER ɗaya kuma na BASEERAT .A wannan rana ta farin ciki Safeenatu ta rakuɓe wuri guda tana ta yin kuka,ga shi dai ta sha ƙunshi da kitso ga kuma gizner ta gani ta faɗa amma rashin masoyinta ya dawo mata daram musamman yadda ake ta faɗar an yi masa madadi da kuma addu'o'in da mutane ke yi.
Da wannan damar Gwaggo Hajara ta shirya mugunta wacce take kambacin fansar da ta yi niyyar ɗauka akan Habibah da hana ta rawar gaban hantsi.Sai da ta bari duk hankalin mutane ya ɗauku,sannan jarirai duk an fitar da su can tsakar gida saboda zafin da ɗakin ya ɗauka sannan ta nufi ɗakin Safeenatu.Duk da akwai mutane hakan bai hana ta gwada sa'arta ba,“ ungo Safeena Gwaggonki Habibah ta ce ki ci abincin nan kafin ta zo ta yi miki ta ƙarfi tun da dai ke ba ki jin magana kina jego amma kin ƙi cin abinci ” Hajara ta faɗa tare da miƙa mata plate mai cike da nama ya sha jar miya,ta karɓa tana turo baki tare da soma ci don ita duk a tunaninta gaske dai Habibar ta bata.Cike da murna Hajara ta bar ɗakin ta je ta kasa kunne tana jiran sakamako.
Da rana mutanen arziki sun cika gida, Safeenatu ta shiga Toilet ta yi wanka da canza kaya daga shadda zuwa less.Kamar wacce aka yi wa wankin ido haka take ganin ƴan biki tsirara tamkar babu kaya jikinsu,zuciyarta ta yi wani mugun bugawa ganin ta soma ganin hanjin cikin mutane yayin da kuma take jin wani abu a bakinta da ba ta san mine ne ba.A daidai nan free page ya ida,duk mai son ci gaba za ta biya kuɗi domin shiga PAID GROUP.
*FREE PAGE/ PAGE NA KYAUTA YA IDA*
Detail 500 via 6042551755
Hassana ibrahim
Keystone bank DM +22795045822
In kin san ba ki shirya saya ba kar ki min magana,ga detail nan kawai ki tura kuɗin ki turo min evidence ta WhatsApp.
*NB:* daga lokacin da ya kammala ya zama complete zai koma 1000.
01 octoba 2024
#CHAMSIYA LAOUALI RABO
MRS SADAUKI 💫
```MRS SADAUKI💫✍️```
My book is only 500 via
6042551755
Hassana ibrahim
Keystone bank,ko kuma katin MTN na 500₦ ƴan Nijar kuma carte airtel ko Moov ta 500f sai a turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822,in kin san ba ki biya kuɗin karatu ba kar ki karanta min littafi domin mallakina ne .
___________________
03/10/24
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels