cikin masai ne zan zubar da ku ke da ruwan” Gwaggo Habibah ta faɗa tana wani murmushin jin daɗi.
Kamar daga sama tsakaka ta soma magana wacce ta kasance Gwaggo Hajara ,“ ki taimaka min Habibah na yi miki alƙawarin daga yau na zubar da makaman yaƙi”
“Kar ma ki zubar ki yi ta riƙon su har sai Mahadi ya bayyana,ba dai maita ita ce jarinki ba? Ki ci gaba da yi wata rana mutuwarki za ki ci” tana gama faɗar haka ta fito daga toilet ɗin,sai kuma ta tuna duk wanda ya mutu a ruwa yayi shahada da sauri ta koma ba tare da ta ce komai ba ta ɗauko robar ta fito da ita tsakar gida tare da juye ruwan ga ƙasa.
Tamkar acid haka turɓayar ta soma yin bori tana fitar da kumfa tsabar bala'in da ke tattare da ruwan,a kunyace Gwoggo Hajara tsakaka ta soma jan ciki ta nufi hanyar ɗaki.
Ita kuwa Gwaggo Habibah ji ta yi kamar ta sa ƙafa ta laɓe shegiya kowa ya huta.Tana komawa ciki ta cewa Safeenatu “Ki shiga toilet to kafin na juye ruwan yi miki wankan” sai kuma ta fita ta ciko ƙaton bokiti da ruwan zafi,da ɗan ƙaramin towel ta soma yi wa Safeenatu wankan jego ita kuma tana ihu kamar wata ƙaramar yarinya.
Macijin jiya ne ya sake bayyana a jikin macen yana wani naɗe jikinta,ita kuma ta buɗe ido taram tana kallonsa kamar mai wayo.Tsawon lokaci ya ɗauka tare da ita yana yi mata wasa kafin ɓace jin motsin su Safeenatu za su fito.Gefen gado ta zauna ta soma shayar da yaran kafin ta kimtsa cikin riga da zane,sai da Gwaggo Habibah ta gama wanka ita ma ta fito ta shirya sannan ta je ta kawo masu abinci suka ci daga nan suka wuce asibiti bayan sun karɓi kuɗi wurin Daddy.Lafiyarta da ta babys aka duba kafin su dawo gida,tuni kuma ƴan Barka suka fara zuwa in waɗannan sun fita wasu sai su shigo.
SAKEENATU
Tana rungume jikin Abbas ta ce “ Yau tana ɗaya daga cikin ranakun ovulation ɗina,yau na gama period ” cikin tsokana ya ce “ period ɗin ɗaya rana ” ta ja hancinsa ta ce “ eh na dai ji,inda ina jimawa kafin ta ɗauke ai da yanzu ba ka kasance da ni ba don jiya ne na gan ta”
Ya gyara mata kwanciya kan ƙirjin nasa yana mai cewa “ Keent don Allah ki dinga bin Mamuh a hankali kin san ta tsufa,ban so kina yin abin da zai ɓata ranta ki guji ɓata mata don farincikina.Ina yi miki wani mugun so ne wanda na san ke ko rabin shi ba ki yi min”
“To in sha Allah na yi ma alƙawari zan kiyaye,ai Ma'idar ma an tafi da ita”
“A'a za ta dawo,sanin kan ki ne yadda nake mugun sonta ba zan iya yin nesa da ita ba”
Wani daɗi ne ya luluɓe zuciyar Sakeenatu,ita ce shaida kan son da yake yi wa ƴarta duk da ta fito ba ta hanyar aure ba.Za ta iya cewa halarcin bai nuna mata ƙyama ba ne ya ɗunguza ta ga aurensa,soyayyarsa ma ba ta jima da samun gurbi a zuciyarta ba.
“Ina son ki Keenat!” furucinsa ya katse mata tunani,ta yi murmushi mai ɗan sauti ta ce “ na gode”
“Ke ba za ki faɗa kina sona ba? Keenat sai yaushe zan ji furicin so daga bakinki?”
Ta laƙace masa hanci ta ce “ sai ranar da na haifo ma kyakkyawan Prince mai kama da kai” sai kuma ta miƙe ta je ta shiga toilet,shower ta sakarwa kanta tana tunanin saurayinta mahaifin Ma'idah.Ruwan hawayenta haɗi da na pampo suka haɗu wuri ɗaya suna zuba.Daga bayanta ta ji an rungume ta,da sauri ta juyo suna fuskantar juna kallo guda yayi mata ya hango damuwa a shimfiɗe a ƙwayar idonta.Zuciyarsa kuma ta basa ta yi kuka,bai tsaya tambayar ta ba ya ɗora bakinsa kan nata a wannan rana a kuma daidai lokacin nan Abbas ya shayar da ita zumar ƙauna mai haɗe da yayafin kalaman soyayya masu nuni da sadaukarwa.Ba tare da ta shirya ba ta ce “ I love You Abbas!” numfashinsa ne ya kusan tsaya wa tsabar murna da farin ciki,kamar wani ƙaramin yaro ya soma yi mata kuka saboda kawai ta ce tana sonsa.
Shi yayi musu wanka ya shirya su,a ranar a gida ya ja su sallah har ta isha'i .Bayan sun salamce sun yi dogayen addu'o'i ya dube ta da kyau ya ce “ Keenat fatan bayan tafiyata duk salloli kin yi su kan lokaci kuma kin tsare su?”
Da sauri ta sunne kai ba tare da ta basa amsa ba,yatsun ƙafarta ya soma ja mata tare da soma yi mata nasihar da ya saba game da mai wasa da sallah a ƙarshe yake cewa “ in kuma na ga kin ƙi yi zan kawo miki ƙanwa ustaziya” a shagwaɓe ta faɗa jikinsa ta ce “ to ai ina yi ko”
“Kina yi ko za ki dinga yi?”
“Duka biyun! Ba za ka koma asibiti ba?”
“Tare za mu koma tashi ki shirya” da “ to” ta amsa kafin ta canza kaya suka fito,sai da ya tsaya ya saya musu fruits sannan suka isa asibitin.Da sallama suka shiga ɗakin Gwaggo Rahamu ce ta amsa yayin da Mamuh ta juya musu baya tana jin wani irin baƙin ciki ya turnuƙe ta saboda a yadda ta gansu cikin farin ciki suna nishaɗi ta san sun keɓe da junansu.Abbas ya ƙarasa yana mai cewa “ Mamuh ya jikin naki?”
“Ka damu da ni ne ka sa ƙafa ka yi tafiyar ka? Wato Abbasi matarka ta fi ni ko?” ta faɗa cike da masifa tana juyowa.
“Ki yi haƙuri Mamuh Allah dai ya baki lafiya ” ya faɗa kansa ƙasa.
Tsabar fitina ta Mamuh sai cewa ta yi “ ina wakena?” Abbas ya ɗago da sauri yana kallon ta yana mai cewa “ wane irin wake kuma Mamuh yanzu da daren nan? Ga ayaba nan da lemu da apple na sayo ”
“Na yi da kai na ce ka sayo? Ita waccar abar ai ta san wake nake ci mi yasa ba ta dafo ba?”
“Yi haƙuri Mamuh gobe sai a daf....” bai rufe baki ba Mamuh ta saka kuka yana cewa “ shinenan tun da mata ta fi uwa”
Da mugun sauri Sakeenatu ta ce “ bari na koma gida sai na dafo mata”
Abbas ya ce “ to ki yi sauri” ta yi tunanin shi zai kai ta amma sai kuɗin ɗan sawu ya bata,tana zaune tana hawaye har suka iso gida ta biya shi kuɗin kafin ta wuce ciki.
A gaggauce ta soma aikin tana mita “ an yi tsohuwa kamar mayya kullum wake yanzu nan in ban wanke shi ba sai ta sani mtsww ” ta ja tsuki tana dirje waken amma jin ita ma an ja mata tsuki yasa ta zabura tana dube-dube sai dai babu kowa.Watsar da tunanin ta yi ta ci gaba da aikinta wani tsukin ta kuma ji sannan ana magana ƙus-ƙus,gabanta ya faɗi jin tamkar ana tafiya cikin falo.Tana shirin fitowa aka ɗauke wuta,lalubo ta soma yi cikin duhu ko Allah yasa ta ɗauko wayarta ta kuwa yi sa'a ta samu jakarta hannunta har rawa yake ta zuge zip ta ciro wayar sai ta ga saura ƙiris batirin ya mutu alhalin a cike ta bar ta.Tana ƙoƙarin ganin ta kunna fitilar ta ji tamkar saukar huci kusa da ita,ta wani juyo da sauri ta inda take jin abin tare da haska hasken screen babu kowa sai ƙafafuwan ƙofato da ta yi arba da su babu kuma gangar jiki.......
*ZAWARCI*
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman
_____________________
26/09/24
9
Babu shiri Sakeenatu ta saki wayar ta arta a guje,sai dai ta nemi ƙofar fita ta rasa saboda mugun duhun da ya mamaye gidan baki ɗaya.Cikin ƙanƙanan lokaci duk ta firgice,dakyar ta iya samu ta fito tsakar gida da lalabe zuciyarta sai ƙara tsananta gudu Waige-waige ta fara sai ta ga ashe kaf unguwar ne babu wuta,ba ta gama daidaita numfashinta ba wata baƙar mage baƙa ƙirin ta soma yin kuka miyau!miyau! Kukanta duk ya cika gidan.
Ta ɗaga kai dakyar ta dubi inda sautin kukan ke fitowa,ido huɗu suka yi da magen wacce hasken idonta yake kamar na lantarki sai canza kaza suke.A hankali ta sauko daga katangar ta soma nufo inda Sakeenatu ke tsaye da gajiyayun ƙafafunta,Allah ya gani ba ta wani ba wai karatun addini muhimmanci ba dukkan lokacinta da hazaƙarta ta zuba su ne a harakar boko wannan ya sa ba ta iya wasu addu'o'i ba .A halin yanzu da take tsaye ta yarda kuma ta aminta rayuwarta na cikin haɗari,tabbas ta san wannan magen ba normal ba ce muguwa ce cutar da ita za ta yi.
Ta na dab da ta kawo kusa da ita ta samu bakinta na furta “ la haula wala ƙuwata illa billah!!!” ƙiiii magen ta wani ci burki tana mai canza salon kuka zuwa na jarirai amma sam Sakeenatu ba ta yi gigin yin shiru da bakinta ba sai ma ƙaimi da ta fara wurin maimaita addu'ar.A gaban idonta magen ta soma mayar da idonta kamar na mutane kafin ta ruga a guje ta yi tsalle ɗaya ta haye katanga,daidai nan kuma aka maido wuta yaran unguwa suka hau ihun murna.Sakeenatu ta ja ajiyar zuciya tana mai yin hamdala ga Ubangiji,bakinta bai gushe ba yana ta furta lahaula wala ƙuwata illa billah a haka ta koma can ciki.Gas ɗin ta kashe saboda muguwar gajiya da ta saukar mata wacce ba ta san dalili ba,wayarta ta ɗauka Allah yayi sa'a babu abin da ya same ta abun mamaki kuma yanzu cajin wayar a cike yake saɓnin ɗazu da aka nuna mata ta kusa mutuwa.
Lambar Nafisa ta kira,tana ɗauka babu wani tsaya wa gaisuwa ta ce “ Nafi ki turo min karatun nan da kike saurare don Allah duk dare”
“Anty Sakeena lafiyar ki kuwa?”
“Ki turo min karatun dai don Allah ina son saurare ”
“Ok to bari na hauda data yanzu zan turo miki”
“Yawwa ina jira” ta faɗa tare da kashe kiran,ita ma datar ta kunna babu jimawa kuwa karatun ya shigo suratul Baƙara ce ta turo mata sai Yasin .Tamkar abun tsiya network ɗin ya ɗauke ɗif ko ɗaya babu wanda ya buɗe,juyin duniya ta yi amma sun ƙi buɗewa har wayar ta kashe ta kunna amma network ɗin ya ƙi yi.Cike da damuwa ta sake kiran wayar ƙanwarta,tana ɗauka sai ta rasa abin da za ta ce mata kawai ta fashe da kuka.Daga can ɓangaren Nafisa ta ce “ subahanallah! Anty Sakeena don Allah mike faruwa? Mike damun ki?”
Cikin muryar kuka take cewa “ Nafisa tsoro nake ji! A tsorace nake ji nake kamar ba ni ɗaya ba ce cikin gidan nan tamkar ina ....inaaa” ta kasa ida maganar saboda motsin da ta gani ana yi can cikin labule wanda ta tabbata kuma ba ɓera ne ba saboda girman halittar.Ihu ta fasa ganin ƙatuwar gafiya ta faɗo timmm da ƙasa,yayin da kuma wata ta biyu ita ma ta sake fitowa a guje ya kama waccan wacce ta faɗo a gaban idonta suka soma faɗa suna cizon junansu.Babu shiri Sakeenatu ta haye ɗaram kan bed ta na kuka,Nafisa na jin haka ta ziri hijabi ta fito ko Mamarsu ba ta sanar ma ba ta fito ta samu ɗan sahu.Allah yayi sa'a ba wani nisa ne sosai a tsakaninsu ba,da gudu ta shigo gidan tana ambaton sunan Allah daidai nan gafiyoyin suka yi ɓatan dabo hatta.
Nafisa ta je ta rungume ƴar uwarta wacce da ace tana da cutar asuma da tuni numfashinta ya fita,“ yi shiru don Allah ya isa yi min bayanin mike faruwa? Ina shi Abbas ɗin?”
“Yana asibiti wurin Mamuh,na dawo na dafa mata wake da shinkafa ne shi ne ake ta firgita ni” nan ta kwashe duk abin da ya faru ta shaida wa ƙanwarta.
Nafisa ta ja dogon numfashi bayan ta saurare ta,sannan ta ce “ wannan duk sharrin miyagu ne shi yasa a kullum ake son bawa ya keɓe wani lokaci don nemawa kansa kariyar ruhi da gangar jiki ba wai gyaran duniyarka ba kawai.Ni wallahi na fara zargin Mamuh ɗin nan,kina dai ganin yadda Ma'idah ta caka mata cokali da dukkan alamu ta hango abin da idanunmu basu gani.In ba masifa ba cikin daren nan za ki dafa mata wake kamar mayya,ke ƙila ma ita ce.Tashi mu je ki yi alwala ai zama bai gan ki ba tun da kin ji kin gani aure a inda ba a ƙaunar ki”
Da taimakon Nafisa ta yo alwala dama ita Nafisar kusan kowanne lokaci tana da alwala mace ce mai riƙo da addini ba ta da sake,hasali ma malamar makaranta ce a wata islamiyya.
Karatun Alkur'ani ta soma koya wa Sakeenatu kamar wata ƴar yarinya haka take biyawa inda ta yi kuskure kuma ta gyara mata.
“ Ki kasance kullum cikin tsarki bima'ana alwala saboda tana da muhimmanci sosai wurin bada kariya,ko sheɗanu suna shakkar mutum mai zama da alwala a koyaushe,ke ko period kike to ki yi abarki sannan ki riƙe azkhar na safe da maraice”
“Amma ai kin san ban iya su ba ko?”
“Ki koya mana anty Sakeena ,shi ilimi ai bai da ƙa'ida shekaru ko tsoho ɗan shekara ɗari zai iya shiga makaranta ballantana ke da ko talatin ba ki kai ba”
“ Ni rubutun larabcin ne ke bani wuya ”
“Zan nemo miki littafi mai fassarar Hausa ,sai na dinga koya miki yanzu bari na tura miki app ɗin Alkur'ani sai ki dinga saurare ”
Ta karɓi wayarta ta tura mata tare da saita mata komai ta kunna sautin ya soma tashi,ta ce “ to ni zan tafi gida ko Mama ban sanar ma ba”
“ Don Allah Nafisa kar ki tafi ki bar ni ki jira har Abbas ya dawo,bari na kira Mamar na shaida mata” haka suka yi kuwa,tun suna jiran Abbas har ƙarfe sha biyun dare bai zo ba a tare suka fito suka rufe gida da ko ina sannan suka je suka kwanta.
A can asibiti kuwa bayan fitar Sakeenatu,Gwaggo Rahamu ta yi wani kishingiɗa ga kujera kamar mai bacci nan kuwa ruhinta ne ta soma fitar wa daga gangar jikinta.Sawun Sakeenatu ta bi,hasali ma ta rige ta zuwa gidan duk abin da take yi akan idonta hanyar farko da ta soma bi shi ne tafiya ta shiga tunanin mai kula da nepa na unguwar ya ɗauke wuta ba tare da shi kansa ya san dalili ba a cikin wannan duhun ne ta yi ta yi wa Sakeenatu mugunta.Da ta koro ta da addu'a shine ta biya wurin wasu miyagun ƙawayenta ta basu address suka je a siffar gafiya,su ma ba su bar gidan ba sai zuwan Nafisa.
Abbas na daga can gefe Mamuh na yi masa hira tana murmushi saboda duk abin da ke faruwa ita tana gani saɓanin shi Abbas ɗin.Bayyanar esprits biyun yasa yanayin shaƙar iskan ɗakin ta sauya saboda tsabar muguntar su, wannan karon hatta Abbas sai da ya ji wani iri.Har yanzu Gwoggo Rahamu ba ta farka daga baccin ƙaryar da take ba,cikin hirarsu ta ƴan duniyar ɓoye suke bata labarin yadda suka firgita Sakeenatu tana ta yin kuka.
“Na gode sosai ƙawayena,kar ku manta in kun gama yawon Maitar dare ku biyo ta nan mu sake komawa mu uku mu haɗa ƙarfi mu shayar da ita mamaki” baƙin ruhin Gwaggo Rahamu ya faɗa ,suka yi dariyar mugunta tare da ɗaukar mata alƙawari kafin su bar wurin.Cikin ƙwarewa ta dawo da ruhinta a gangar jikinta,ta dubi Abbas tana mai cewa “ bacci ya ɗauke ni duk yau ban rintsa ba,ina sauran waken ni ma na ci yunwa nake ji”
Shi Abbas sam ya manta da wani zancen wake saboda yadda Mamuh ke masa hira,sai yanzu ya tuna Sakeenatu ta je gida dafawa.Da ya duba agogon hannunsa ransa ne yayi mugun ɓaci,“ uwar tamu ai ba ta dafo ba tana can tana gantalin da ta saba,ah to dama su likitoci ba su da kamun kai tsakaninsu da abokan aikinsu suke neman juna in aka ce miki tana can asibiti wani ƙato ya taushe kar ki yi gardama” Mamuh ta faɗa ,yayin da Gwaggo ta karɓe “ i sosai ita ma wannan shegiyarta ta ai shugabansu ne ya ɗirka mata cikin ya bar yaronmu da wahala,wai Abbasi wai ya ƙaƙaba maka aurenta?”
Kasa cewa komai yayi,haushi goma da gomiya tara ya rasa da wane zai ji abin ka kuma da zuciyar namiji sai ya ji zargi ya ɗarsu a ransa.Da ya nuna zai je gida Mamuh ta hana shi tafiya ta hanyar amfani da tsafinta,haka suka dinga kwaso sharri iri-iri suna yaɓa ma Sakeenatu sosai kuma suke samun gurbi a zuciyarsa.Can waje ya koma ya kwanta kan wani banci yana ta tunanin rayuwa baya yadda neman aurensa ya kasance yadda sam Sakeenatu ba ta samu shaidar ƙwarai ba ga mutanen unguwa amma ya rumtse ido ya ce sai ita .
Ƙarfe biyu da rabi na dare ƙawayen Gwaggo Rahamu suka biyo mata,kafin su yi tsinke gidan Sakeenatu.Sai da suka shiga kitchen suka cinye kaf abincin da ta dafa sannan suka dawo falo suka fara shawarar abin da za su yi mata,suna dariyar mugunta suka tura ƙofar falon sai dai da zarar sun yi niyyar ɗora ƙafarsu a tile ɗin bedroom sai su ji tamkar cikin garwashin wuta ne suke ɗora su.Gwaggo Rahamu ta ƙanƙance ido tana kallon gefen Nafisa inda kusan kanta ta ɗora wayarta ne sautin karatun Alqur'ani na tashi a hankali wanda ba ma a jinsa sosai,kamar ta san suna nan kuwa sai ta kai hannu ta ƙara volume a tare suka saki wani ihu wanda sai da gidan ya girgiza a firgice Sakeenatu ta farka tana zarar ido
My book is only 500 via 6042551755
Hassana ibrahim
Keystone bank DM +22795045822
My book is only 500 via 6042551755
Hassana ibrahim
Keystone bank,DM +22795045822
*ZAWARCI*
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman
_____________________
28/09/24
10
A wahalce Gwaggo Hajara ke bin bango don isa ɗakinta,fatar nan tata ta tsakaka duk ta yi wani taushi ta fara fitar da wani fanko.A yadda bango ke zuzar fatar cikinta ji take kamar ta yi ta ƙurma ihu sai dai ba dama sata lahira! Tana isa ɗakinta ta ɗauki siffa ta mutum nan ne fa ta yi tozali da yadda duk jikinta ya kumbura yayi ja kamar wacce aka soya,mai ta ɗauko ta shafe jikinta da shi tana matsar ƙwalla tare da jin tsanar Safeenatu na sake feso mata daga can ƙasan zuciyarta.
A fili ta furta “ sai na wulaƙanta rayuwarki,sai na saka kin tozarta a duniya,sai na shayar da ke gubar azaba wacce sai kin gwammaci mutuwa akan rayuwarki. Ke kan ki Habibah ba zan bar ki ba zan ɗora miki karatu da alamu har yanzu ba ki ji jiki ba shi yasa kike taimaka wa wata wurin ruguje plan ɗina” shiru ta yi jin an turo ƙofa.Daddy ne ya shigo da sallama a bakinsa,ba ta amsa ba sai ma saurin jawo hijabi da ta yi ta saka duk ta luluɓe jikinta.
“Ni kam Hajara lafiya kike? Kin ga yadda fuskarki ta yi suntum sai huci take kamar ƙullun wainar da ya ji yis?” Daddy ya faɗa yana ƙare mata kallo.Wani ƙululun baƙin ciki ne ya ƙara turnuƙe Hajara ta ce “ uwar waina ce....” ba ta ida kai aya ba ta ji yatsun Daddy biyar kan kuncinta,shaye da mamaki take kallonsa nan ta hango wani baƙin tauraro tsakiyar goshinsa wanda ko shakka babu aikin Habiba ne ta tura masa shi.
Ba ta gama dawowa daga duniyar mamakin da ta je ba Daddy ya soma magana cikin masifa,“ wato abun naki ya fara zama iskanci,daga tambaya shine za ki zagin uwata saboda kin san yau za ta zo.To tsaya ki ji Hajara duk wata tijararki ki tattara ta ki ajiye wuri guda muddin Hajiya ta koma da baƙin cikinki gida to wallahi akan aurenki.Ki tashi ki ɗora girki tsabar lalaci muna da mai jego a gida amma kin zo kin shige ɗaki kin haye gado tare da saka hijabi kamar matar liman kowacce za ta yi aikin ƙwarai” yana gama faɗa ya nufi ƙofa,sai kuma ya juyo ya ce “ Murjanatu na kan hanya sai ki fara shirin tarben ta” kawai ya fice.
Gwaggo Habibah da ke zaune kan kujera a falo ta saki wani irin murmushin nasara,tun da uwarta ta haife ta yau ce ranar farko da ta juya taurarinta na baiwa ta yi aiki da su.Tun bayan da ta yi wa Twins wanka ta shirya su sannan ta bai wa uwarsu abin da za ta ci kawai ta fito falo ta zauna,Daddy na fitowa ta soma yi masa transfer ɗin tauraron ta hanyar kallonsa tsakiyar ido da farko har ya tambaye ta lafiya sai kuma yayi shiru jin sabon abu a tattare da shi.
Duk abin da yake faɗa wa Gwaggo Hajara sarai ta ji alamun aikinta yayi kyau,ta saki murmushin nasara tana mai cewa ‘ mijinki zai zame miki kumurci,da haka zan raunata muguwar zuciyarki’
“Habibah karɓi wannan ko kuna da buƙatar wani abu sai a ɗauka ciki” Daddy ya faɗa yana mai katse mata tunanin zuci.Ta karɓa tana mai cewa “ Yaya Ɗayyabu na ce bayan biki sai Safeenatu ta koma can gida wurin Hajiya ko?”
“Saboda me? Ba a nan za ki zauna ba?”
“Eh to ni ma da haka na ce ɗin amma sai na ga kamar anty Hajara ba ta son zamana tun da na zo idonta kamar za su faɗo tsabar yadda take jifana da mugun kallo”
Ran daɗi ya ɓace, yanayin fuskarsa ya canza tuni tauraron goshinsa ya ƙara yin baƙi ba tare da ya ce komai ba ya ƙara komawa ɗakin Gwaggo Hajara ita kuwa Habibah har da wata dariyar mugunta ta yi tare da tashi tana taka rawar murna.
Daddy na shiga ɗaki ya yi wa Hajara wankin babban bargo,ko ina ana jin muryarsa yadda yake yi mata masifa in ta je yin magana kuma sai ya gwaɓe bakin.Da wannan baƙin cikin ya fita ya bar ta,sai da ta sha kuka wiwi sannan ta fito ta ɗora girki babu jimawa kuwa sai ga Hajiya ta zo .A ladabce Gwoggo Hajara ta gaishe ta wanda sosai ita hajiyar ta yi mamaki don rabon da ta yi mata irin wannan ladabin tun ranar da Ɗayyabu ya kawo mata ita a matsayin matar da zai aura.Cikin sakin fuska ta amsa tare da cewa “ to barkarmu Safeena an sauka Allah raya kan sunnah,kin samu mai taya ki aiki da kuma miji” Hajiya ta faɗa tana murmushi a doli ita ma ta yi murmushin yaƙen a can ƙasar zuciyarta tana cewa ‘ an haifo mana masifa dai aljanar jaririya muguwa wacce ta yi gadon jaraba ’
“Zan shiga daga ciki” hajiyar ta faɗa tare da nufar ɗakin Safeenatu,cike da murna ta zauna tana kallon jariran Gwaggo Habibah ta ɗauki namijin ta bai wa Hajiya ta karɓa tana mai kai masa sumba haɗi da yi masa addu'a sannan ta miƙa shi.Ana ɗora mata macen jikin Hajiya ya ɗau kyarma kamar mazari,murya na ɗan rawa ta ce “ wane suna za a saka musu?”
“Basheer da Baseerat ” Habibah ta bata amsa tana murmushi tana kallon mahaifiyarta wacce kambun muguntar Gwaggo Hajara duk ya dabaibaye ta yanzu kuma ya fara barazanar tarwatsewa.
Hajiya ta ce “ karɓar ta” tana mai miƙo Baseerat don ruhinta ya soma yin rauni, Habibah ta ce “ Hajiya don Allah ki riƙe t...” ba ta kai ƙarshe ba Hajiya ta miƙe ta je ta shimfiɗe Baseerat a shimfiɗa,sai aka yi rashin sa'a safar da aka saka ma hannunta na hagu ta fita wani mugun haske ya fito ya shiga ƙirjin Hajiya saura ƙiris ta faɗi saboda yadda fitilun idonta suka rufe jiri kuma ya ɗebe ta.
Safeenatu dai na daga gefe tana kallon abubuwan ban al'ajabi , Gwaggo Habibah ce ta kamo Hajiya ta taimaka mata ta zauna.Kamar mai cutar huka haka numfashinta ke fita,ruwan sanyi ta nema da sauri aka bata ta shanye ƙatuwar gora.
“Habibah bani pilow bacci nake ji” cewar Hajiya ,da sauri ta ɗauko ta miƙa mata ita kuma ta kwanta babu jimawa bacci mai nauyi ya