yanzu, shin
ko soyayya dole ce? Kc kuwa ke mayya cc wai? To
na rantse da darajar iyayena idan baki fita daga
sha'anina ba duk ranar da kika shiga hannuna sai kin
gane kurenki".
Koda gimbiya Shahriya taji haka sai tayi
murmushi ta matso daf da shi sannan ta cc, "Ya kai
masoyina kayi sani cewa ba komai yasa na ziyarceka
ba a yanzu sai domin in ga fuskarka saboda idan ban
ganta ba ba zan iya bacci ba, kuma kayi sani cewa
21
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
shi so ba dole banc, amma daga gareni za ka fara
soyayyar dolc. Kuma ba komai ni ke so gareka ba
illa ka bani aron zuciyarka domin ta zamowa tawa
zuciyar jagora wurin ci gaba da rayuwarta. Hakan ne
yasa na sa aka dauko min littafinka wanda ka fifita
akaina, kuma ba zan baka shi ba har sai ka amince
da bukatata".
Tana kawowa nan a zancenta sai ta kai baki da
niyyar ta sumbaceshi. Cikin sauri Affan ya kauda
kansa, abinda ya sa gimbiya Shahriya tayi murmushi
ke nan ta juya ta fice ta barshi nan yana hucin bakin
ciki
*
*
Haka dai ya kasance cıkın kurkukun har tsawon
kwanaki bakwai. Lokacin ya yi kuka, ya yi bakin
ciki sannan ya yi nadamar zuwa ceton Kasim da ya
yi har gimbiya Shahriya ta ganshi har ma idan ya
tuno cewa bai gama karatun littafin hikaya ba kuma
gashi lokacin da aka basu ya kare ko yanzu ya koma
ba za a bari ya shiga gasar ba, wannan ne yasa tuni
ya debe 1ansa da tunaninsa a cikin masu gasar.
Abinda kawai yake tunani yanzu shi ne, hanyar da
zai kubuta ya shiga gidan sarautar ya kamo gimbiya
Shahriya ya yi ma ta kisan wulakancin da ko a tarihi
22
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
a a taba yiwa wani mahaluki irin sa ba, domin ya
wanke takaicin bakin cikin da ta cusa masa.
Kansa sunkuyc yana wannan tunanin kawai sai
yaji an bude kofa da karfi. Koda ya daga kai ya
duba sai ya ganshi. Cikin mamaki Affan ya ce, "Ya
kai Malam Basiru ya aka yi ka samu damar shigowa
wannan wurin?"
Koda Malam Basiru yaji haka sai ya се,
"Yanzu ba lokacin wani zance bane". Cikin sauri ya
sa makulli ya kwanceshi suka fita. Fitowarsu ke da
wuya sai Affan ya kama hanya da niyyar shiga gidan
sarautar. Cikin sauri Malam Basiru ya rikoshi ya ce,
"Ina kuma za ka?" Ya amsa da cewa, "Zan je wurin
gimbiya in amso littafina na hikaya".
Koda Malam Basiru yaji haka sai ya dauko
littafin ya mika masa ya ce, "Gashi na dauko maka".
Cikin matukar mamaki da murna ya karbi littafin ya
rungumeshi sannan Malam Basiru ya ja hannunsa
suka rika sanda gare da tsallake masu gadin da ke
kwance suna ta sharar bacci. Duhun dare ya
suturtasu, har suka fito gidan ba wanda ya gansu.
Suna fitowa suka iske sadauki Kasim na jiransu da
dawakai guda uku. Nan da nan suka kama dawakan
suka haye suka zaburesu cikin matsanaicin gudu
suka rika tafiya har suka fita daga kasar Zururi suka
kama daji.
23
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
Sai da suka kwana suka wuni suna tafiya da
wani azababben gudu tamkar wadanda za su bar
duniya baki daya. Suka wanzu suna cikin kcta
kwazazzabai, duhuwowi, koguna, tudu da gangare,
sai da suka kwana uku suna tafiya ba tare da cin
zango ba, kuma ba su haďu da wani abu, mai cutarwa
ba. A rana ta uku ne da la'asar likis sai suka fahimci
cewa dawakanku sun galabaita kamar yadda suma
suka galabaita musamman Malam Basiru wanda bai
da jimirin wahala. Nan da nan ya yi umarnin da a
yada zango domin hutawa.
Koda Affan yaji haka sai hankalinsa ya tashi ya
dubi Malam Basiru ya ce, "Haba Malam ya za ka ce
mu yada zango tun yanzu bayan ka san tafiyar da ke
gabanmu bata wasa bace?"
Cikin fushi Malam Basiru ya dubeshi ya се,
"Kai Affan shin ko baka da hankali ne? Kwanaki
uku muna tafiya ba cin zango sannan ka ce kada mu
tsaya? Shin ko bamu da jini a jiki ne? To ka yi sani
cewa duk mai rai dole ne ya ba ransa hakkinta wato
(hutu) kuma zafin nema baya kawo samu. Kuma ka
yi sani cewa in dai ba sihiri garemu ba ba yadda za a
yi mu iya isa kasar Mahbub cikin lokacin da muke
so, sai idan mun isa duk bala'in da za a yi sai ka
shige wannan gasar saboda haka mu kan sai mun
huta".
24
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
Yana kawowa nan a zancensa sai suka fara
sauke kaya shi da Kasim suka bar Affan a tsaye yana
tunani, can shima sai ya sa hannu suka sauke kayan
tare da kafa tanti.
Bayan sun gama kafa tantin ne sai suka dauko
guzurinsu suka shiga ba Ciki hakkinsa. Haka suka
kasance wurin har rana ta fadi duhu ya shigo, Kasim
da Affan suka je suka samo Itace suka hada wuta
domin jin dumi sakamakon sanyin dake bugawa
awurin, suna cikin hakane sai Affan ya dubi
Mallam Basiru ya ce "Ya kai Mallam ka yi min
alkawarin cewa idan muka samu nutsuwa za ka
fadamin yadda kayi ka samu damar kubutar dani da
yadda ka samu nasarar dauko littafin hikaya a
hannun Gimbiya Shahriya."
Koda Mallam yaji haka sai ya yi murmushi ya
ce, "Wato wani lokaci Affan taurin kai ne da kai,
Lokacin dana bukaci ka bari mu bi abin a hankali, da
ka bari da bai kai ga haka ba." Ya ci gaba da cewa,
"Lokacin da na ga ka wuni ka kwana ba ka dawo ba,
sai na san ba shakka Gimbiya tasa an kama ka. To
daga wannan lokacin ne na shiga tunanin hanyar da
zan bi in kubutar da kai. Da yake ina da wani aboki
mai suna Sami'u. Sami'u ya kasance shi ke dafa ma
masu gadin gidan Sarki Fikihu giya, kuma lokaci
zuwa lokaci ina ma kai masa ziyara gidan Sarki,
25
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
wani lokacin ma ina tayashi aikin wurin dafa giyar.
Wannan ne yasa ko masu tsoron kofar gidan Sarki
sun ganni basa hanani shiga saboda sun san wurin
Sami'u ni ke zuwa.
Ranar da ka cika kwana bakwai ne na kaima
Sami'u ziyara gidan Sarki, kuma na umarci Kasim da
ya yi shiri domin zamu bar garin da daddare. Ina isa
gidan Sarki sai na iske Sami'u yana cikin aikin
dahuwar giya, mamaki ya kamani saboda na ga
kullum ana dafa duro uku ne amma yau na ga sama
da diro shida.
Bayan mun gaisa da Sami'u sai ya ce, "Kai
Malam Basiru amma ka zo dai-dai lokacin da nike
bukatarka saboda yau kan aiki ya yi min yawa ina so
ka taimaka min".
Koda na ji haka sai na yi murmushi na ce, "Ai
na ga alama saboda yau kan na ga diro shida ne.
Shin wai mi za a yi da su ne haka, ko har da
dawakan gidan sun fara shan giyar ne?"
Sami'u ya yi murmushi ya ce, "Ba kowa ya sa a
kara yawan giyar ba face gimbiya Shahriya, saboda
gobe za a yi ma ta bikin baiko da wani bakon
sadauki wanda ya samu nasarar - kashe Kwadon
Rijiya, shi ya sa ta ce in dafa mata duro uku na gobe,
ukun kuwa na yau ne za a sha su."
26
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
Koda naji haka sai hankalina ya tashi don na
san ba kowa bane face kai. Cikin yaudara na fara
bugun cikinsa da cewa, "Shin ba ance sadaukin ya
gudu ba? Ya aka yi ya dawo?". Sami'u ya ce, "Ban
san da wannan ba, abinda na sani shi ne kwanakin
bakwai da suka wuce gimbiya Shahriya ta tara
dukkan masu gadin gidan nan ta ce da su idan sun ga
wani sadauki mai siffa ka za-da-ka za kada a hanashi
shigowa, kuma kada wani ya ce da shi kala. Ai ko ba
ta jima da yin wannan maganar ba sai ga wanıan
sadaukin ya shigo yana cikin tafiya ne kwatsam s.
na ga an sako raga an kamashi an yi kurkuku da shi".
Koda naji haka sai na cewa Sami'u, "Kai baka
zaton akwai abinda gimbiya ta daukar ma wannan
sadaukin har tasa ya dawo dole?" Sami'u ya ce, "Б.
shakka akwai lokacin da na je kaima wasu Askarawa
giya na ji wani cikin su na cewa, "Ai ba don gimbiya
ta sa mun dauko mai littafin ba da ba zai kawo
kanshi ba, kuma ta ce ba shakka idan bai yarda an yi
musu baiko ba ba za ta bashi littafin ba."
Koda naji haka sai hankalina ya dada tashi don
na san al'adar kasar mu idan aka yiwa namiji baiko
da mace to ba a bari yaje ko ina sai an daura musu
aure. Kawai sai na kudurci yaudara a zuciyata na
fakaici idon Sami'u na rika jefa kololon Banju a
27
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
cikin diron giyar sai da na saka banju a kowanne
diron sannan muka ci gaba da matsa giyar.
Bayan giyar ta dafu sai muka shiga aikin
rabawa masu gadi ita. A lokacin da dare ya yi sai da
na tabbatar da cewa na shayar da dukkan wadanda
za su kawo min matsala wajen kubutar da kai ciki ko
har da Sami'u bai tsira ba giya mai banju,.
Bayan dan wani lokaci sai na tashi na shiga
zagayen lungu-lungu, sako-sako na gidan duk inda
na bi sai in yi arba da dakaru sun zube kasa suna
sharar barci. Sai da na tabbatar da kowa ya yi bacci a
gidan sannan na shiga sanda da labebe duhun dare
ya suturta ni har na isa inda dakin gimbiya yake. Ina
zuwa sai na leka wata 'yar karamar taga kawia sai na
yi arba da ita zaune saman gadonta ta tasa littafin
hikaya gaba tayi tagumi. Nan ne naji tana cewa,
"Sadauki Affan ina sonka kuma ba shakka gobe za a
yi mana baiko da kai ko kana so ko baka so. Kamar
yadda Abbana ya alkawarta min."
Koda naji haka sai na fada tunanin yadda zan
rabata da littafin. Can sai na dauko garin banju na
hura cikin tagar na koma gefe na make.
Bayan 'yan dakiku sai na leka na ganta tuni
banju ya gama ma ta aiki, wato ta bingire da bacci,
ina ganin haka sai na sadada na bude kofar dakin na
shiga na dauko littafin hikaya. Ai ko da fitowata sai
28
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
sako-sako tamkar farin dango suna cewa, "Affan
oyoyo! oyoyo!!'
Kafin ka ce kwabo tuni wurin ya cika da
al'umma ba masaka tsinke. Malam Basiru da Kasimu
kuwa mamaki suke ashe haka ake son Affan a
kasarsu? To wai mi ya hana a bashi sarautar a huta.
Ana cikin haka ne sai Affan ya daga hannu alamar
kowa ya saurara, wurin ya yi tamkar ruwa ya ci su,
ya fara magana da cewa.
"Ya ku al'ummar kasata ina mai yi muku
godiya bisa wannan tarba da kuka yi ba, amma sai
dai ban ji dadi ba kamar yadda na ga alamar kuna
ciki wani hali na tashin hankali, ko mine dalilin
hakan?"
Koda jama'a suka ji wannan tambayar sai suka
yi shiru. Can sai wani tsohon mai yalwar furfura ya
ce, "Ya kai Affan ka yi sani cewa dole ne mu shiga
cikin tashin hankali saboda tunda mahaifinka ya
mutu kai al'ummar wannan kasa ke son ya gajeshi,
sai gashi ace sai kun je neman ilimin hikaya."
Tsohon ya ci gaba da cewa, "Tun ranar da kuka
bar garin nan mutane ke kidayar ranaku tare da fatan
ka ri ga kowa dawowa, saboda kada ka zarce
kwanakin da-aka dibar muku amma sai gashi kowa
ya dawo kuma har ka wuce kwanaki sittin baka
dawo ba, kuma kowa ya san cewa ba za a barka ka
31
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
shiga gasar ba saboda ka keta doka. Wannan shi ne
ya samu cikin tashin hankali don mun san in ba kai
ka ci wannan gasar ba to duk wanda ya ci talakawa
na cikin matsanaicin bala'i".
Kalaman wannan tsoho sai da suka sa Affan
zub da hawaye. Cikin tattausar murya ya fara
magana da cewa, "Ya ku masoyana mutanen kasata,
ina mai baku hakuri akan wannan tsako da na samu.
I na wannan tsaikon ya faru ne ba bisa sona ba, sai
bisa wani dalili wanda ba zan iya fada muku shi ba
anan, amma ina so ku kwantar hankalinku zan je
fada yanzu kuma duk yadda zaa yi zan shiga wannan
gasar, kuma ba makawa ni zan lashe gasar, saboda
haka kowa ya koma ya ci gaba da harkokinsa kamar
kullum".
Yana kawowa nan a zancensa sai jama'a suka
Garke da tafi da shewa suna cewa, "Sai ka yi! Sai ka
yi!!"
Lokacin da suka isa bakin fadar sai suka iske
fadar cikin tsauraran matakan tsaro, duk inda ka
duba dakaru ne cikin shirin ko ta kwana. Sannan an
kara kawata fadar tayi matsanaicin kyau fiye da
tunanin mai tunani. Abinda ya sa Malam basiru da
Kasim suka saki baki suna kallo da mamakin yadda
fadar ta kawatu haka, saboda tunda suke ba su taba
ganin fada mai girma da kyawu kamar wannan ba.
32
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
sako-sako tamkar farin dango suna cewa, "Affan
oyoyo! oyoyo!!!
Kafin ka ce kwabo tuni wurin ya cika da
al'umma ba masaka tsinke. Malam Basiru da Kasimu
kuwa mamaki suke ashe haka ake son Affan a
Kasarsu? To wai mi ya hana a bashi sarautar a huta.
Ana cikin haka ne sai Affan ya daga hannu alamar
kowa ya saurara, wurin ya yi tamkar ruwa ya ci su,
ya fara magana da cewa.
"Ya ku al'ummar kasata ina mai yi muku
godiya bisa wannan tarba da kuka yi ba, amma sai
dai ban ji dadi ba kamar yadda na ga alamar kuna
ciki wani hali na tashin hankali, ko mine dalilin
hakan?"
Koda jama'a suka ji wannan tambayar sai suka
yi shiru. Can sai wani tsohon mai yalwar furfura ya
ce, "Ya kai Affan ka yi sani cewa dole ne mu shiga
cikin tashin hankali saboda tunda mahaifinka ya
mutu kai al'ummar wannan kasa ke son ya gajeshi,
sai gashi ace sai kun je neman ilimin hikaya."
Tsohon ya ci gaba da cewa, "Tun ranar da kuka
bar garin nan mutane ke kidayar ranaku tare da fatan
ka ri ga kowa dawowa, saboda kada ka zarce
kwanakin da aka dibar muku amma sai gashi kowa
ya dawo kuma har ka wuce kwanaki sittin baka
dawo ba, kuma kowa ya san cewa ba za a barka ka
31
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
shiga gasar ba saboda ka keta doka. Wannan shi ne
ya samu cikin tashin hankali don mun san in ba kai
ka ci wannan gasar ba to duk wanda ya ci talakawa
na cikin matsanaicin bala'i".
Kalaman wannan tsoho sai da suka sa Affan
zub da hawaye. Cikin tattausar murya ya fara
magana da ccwa, "Ya ku masoyana mutanen kasata,
in mai baku hakuri akan wannan tsako da na samu.
I na wannan tsaikon ya faru ne ba bisa sona ba, sai
bisa wani dalili wanda ba zan iya fada muku shi ba
anan, amma ina so ku kwantar hankalinku zan je
fada yanzu kuma duk yadda zaa yi zan shiga wannan
gasar, kuma ba makawa ni zan lashe gasar, saboda
haka kowa ya koma ya ci gaba da harkokinsa kamar
kullum".
Yana kawowa nan a zancensa sai jama'a suka
Garke da tafi da shewa suna cewa, "Sai ka yi! Sai ka
yi!!"
Lokacin da suka isa bakin fadar sai suka iske
fadar cikin tsauraran matakan tsaro, duk inda ka
duba dakaru ne cikin shirin ko ta kwana. Sannan an
kara kawata fadar tayi matsanaicin kyau fiye da
tunanin mai tunani. Abinda ya sa Malam basiru da
Kasim suka saki baki suna kallo da mamakin yadda
fadar ta kawatu haka, saboda tunda suke ba su taba
ganin fada mai girma da kyawu kamar wannan ba.
32
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
Bai wuce saura taku kadan su isa bakin kofar
ba sai wani sadauki mai suna Kausar ya sha
gabansu. Koda Affan ya ga haka sai ya dubeshi ya
ce, "Shin mine ne dalilin ka na tare mana hanya?"
Kausar ya amsa da cewa, "Ya shugabana kayi sani
cewa tuni Shugaba Waziri Kwabis ya bamu umarnin
da kada mu bari kowa ya shiga fadar sai da izininsa
saboda bada cikakken tsaro da kariya ga manyamanyan-baki da Malaman Hikaya da kuma dubunan
'yan kallo da suka fito kowanne sako na duniya
wadanda yanzu wannan fadar ke karbar bakunci
domin shedar wannan gagarumar gasa da za a fara.
Koda Affan yaji haka sai ya ce, "Kana nufin
dama ba a fara wannan gasar ba?". Kausar ya ce,
"Ba a fara ba saboda wasu 'yan matsaloli, amma ko
shakka yau za a fara saboda cikin 'ya'yan Sarki kowa
ya dawo wurin neman ilimin Hikaya, kai kadai ka
rage, kuma tuni alkalan gasar sun halarta.
Koda Affan yai cewa ba a fara wannan gasar ba
sai murna ta kamashi. Cikin murmushi ya ce, "Ya
kai Kausar na umarceka da ka je ka sanar da Waziri
cewa gani na iso".
Cikin sauri Kausar ya tafi domin cika umarnin
Affan. Bayan wani dan lokaci da wucewar Kausar
sai ga shi tafe tare da Waziri Kwabis cikin wata irin
33
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
shiga ta alfarma tamkar ma shi ne Sarkin kasar
Mahbub gaba daya.
Tunda suka yi arba da juna sai zuciyar Waziri
ta buga, ransa ya 6aci sosai ya fara zancen zuci da
ccwa.
"Ashe wannan tsinannen yaron da nike zaton
ya hallaka yana nan? To yanzu kamata ya yi tunda
ya wuce wa'adin da aka dībar musu in yi amfani da
wannan damar in kareshi cikin wannan gasar
kawai."
Can kuma wani 6angare na zuciyarsa ya ce,
"Kai ka manta irin makircin da ka kulla masa na
turashi wurin Malamin da bai san komai ba? Saboda
haka ko ya shiga gasar ba zai iya tabuka komai ba,
gara ma ka kyaleshi".
Waziri Kwabis na kawowa nan a zancen
zucinsa sai ya kyalkyale da dariyar mugunta kuma
lokacin ne ya iso daf da su Affan cikin murmushin
munafunci, Waziri ya rungume Affan tare da yi mai
kalamai irin na dadewa ba a ga juna ba.
Bayan sun nutsu ne sai Affan ya gabatar da
Malam Basiru da Kasimu wurin Waziri suka gaisa.
Bayan sun gama gaisawa ne sai Waziri ya ce, "Ya
kai dana ka yi sani cewa bamu da wani isasshen
lokaci yanzu saboda ni kadai ake jira a fara wannan
34
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
gasar, saboda haka ku shigo mu je fada domin
gabatar da ku wurin Alkalan Gasar kafin a fara.
Wohoho! Ai lokacin da suka shiga cikin fadar
sai Malam Basiru ya saki baki yana kallon irin yadda
aka kawata fadar da wasu irin kayan alatu wadanda
bai taba gani ko jin labarin su ba. Wannan ne yasa
ya zama tamkar wanda ke rayuwa cikin rijiya ya
shigo birni. Fadar an kasata zuwa bangaroti uku,
bangare na farko shi ne bangaren dubun-dubatar
'yan kallo na ciki da wajen kasar.
Bangare na biyu kuwa shi ke dauke da wasu
irin kujeru na alfarma wadanda aka sana'anta da
ruwan farin zinare aka yi musu ado da farin dimon,
kujeru guda hamsin ne kuma 'ya'yan Sarki Gulam su
arba'in da tara suna saman kujerun cikin shiga ta
alfarma sai sheki, suka yi tamkar taurari kujerar
Sadauki Affan kawai ta rage wanda sai yanzu ya iso.
Bangare ma uku kuwa, shi ne ke dauke da
wasu kujeru wadanda aka kera da ruwan zallan jan
zınare, aka yi musu ado da farin zinare, wadannan
kujeru guda hamsin ne kuma ba kowa ke zaune
kansu ba face manya-manyan mashahuran fitattun
Malaman hikaya na duniya su arba'in da tara cikin
shiga irin ta alfarma.
Bangaren yamma na fadar kuwa wani dan tudu
ne mai dauke da matattakala goma wanda ke dauke
35
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
da karagar sarautar Kasar Mahbub. Karagar sai
Kyalli da walwali kawai take, gefen karagar kuwa
wani dan mumbari ne aka samar saboda masu
gudanar da gasar.
Kai ganin yadda wannan fadar ta kawatu ne
yasa Malam Basiru ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ba
shakka tafiya mabudin ilimi ce, wanda bai tafiya ba
bai sha kallo ba".
Bayan Waziri Kwabis ya gabatar da su Affan
gaban 'yan kallo da Alkalin Gasar ne sai ya yi musu
umarnin da su je su zauna domin fara gasar ne sai ya
yi musu umarni da su je su zauna domin fara gasar
kai tsaye. Sadauki Affan ya zarce Gangaren da 'yan
uwansa suke ya zauna saman kujerarsa abinda yasa
suka cika su hamsin dai-dai. Ai ko zamansa ke da
wuya sai gaba daya ya dusashe hasken van uwansa
ya zame musu tamkar Wata a cikin tadra, wao shi
dai ake gani, shima Kasim ya samu wuri cikin 'yan
kallo ya zauna.
Shi ko Malam Basiru tuni hankalinsa ya tashi
jikinsa ya kama kyarma sakamakon nuna masa
wurin zamansa inda ya yi arba da manya-manya
gawurtattun Malaman Hikaya wadanda duniyar
marubuta ke takama da su, kamar su, Abdul'aziz
ibini Sani Al-Madaks, Shehu ibini Usman,
Abdullahi ibni Mukhtar Al-Yaron Malam, Ibini
36
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
Shitu Al-Bature, Hassan Ibini Shu'aibu Al-Harande,
Mubarak Ibini Hamza Al-Gadon Kaya, Ibn Isa AlKwalisa, Rabi'u Ibn Abubakar Al-Sharfadi,
Abubakar Ibn Tanko, Ibni Tajeri mai Dodo. Da dai
sauransu.
Nan da nan ya fara maganar zuci da cewa,
"Kai, yau asiri na ya tono, da na sani da na yi
zamana gidanmu. Kai! Ina ni ina goga kafada da
wadannan manyan Malamai a matsayina na karamin
Almajiri?"
Yana cikin wannan tunani ne har ya iso wurin
su yana zuwa sai ya yi zaune dabas a kasa. Koda
Malaman suka ga haka sai suka dubi juna, sannan
cikin murmushi Malam Abdul'aziz Sani ya ce,
"Haba Malam ya za ka zauna a kasa bayan ga kujeru
wadanda aka tanadar domin ka?" Cikin rawar murya
Malam Basiru ya amsa da cewa, "Haba maigida,
kuna saman kujera ina sama ai na yi rashin kunya, a
matsayina na almajiri". Cikin murmushi Abdul'aziz
ya ce, "Kai ko Malam ai ita baiwa daga Allah ta ke,
kuma duk yadda ya baka ita bai kamata ka rainata
ba, saboda haka ka zo ka zauna saman kujera duk
mun zama daya".
Nan dai ta kaddama ta kaure tsakaninsu. Da
kyar Abdul'aziz ya shawo kan Malam Basiru sannan
37
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
ya zauna saman kujerar suka cika Malamai hamsin
ke nan dai-dai.
Lokacin da ya tsinci kansa cikin tsakiyar
manyan marubutan duniya sai ya yi godiya ga Allah
don acewarsa ko zama cikin su ma wani abin
alfahari ne".
Can kuma Gangaren waziri cikin murya mai
karfi ya fara magana da cewa, "Ya ku al'ummar na
ciki da wajen kasar, tare da manyan Malaman
Hikaya, kuma alkalan wannan gasar, kamar yadda
muka tsara dan dan Sarki na farko shi zai fito yanzu
ya fara gabatar da nasa hikayoyin, wato babban
saboda haka mun zabi Malam Abdulsalam ibini
Bature da Abdul'aziz su kasance manyan Alkalan
wannan gasar, in ya so M. Shehu ibini Muhammad
da M. Mukhtar Al-Yaron Malam su kasance masu
kula da maki, sauran Malamai kuwa su kasance
masu naziri waziri Kwabis ya kara da cewa, "Da
fatan kowa zai yi aikinsa bisa adalci ba tare da son
zuciya ba, saboda haka Bakar ga mai fili ga mai
doki.
BAKAR ya taso cikin 'yan uwansa a natse yana
tafiya cikin takama da izza fuskarsa cike da alamun
samun nasara. Ganin cewa Malamin da ya koyar da
shi wato M. Abdul'aziz Sani ya koyar da shi sosai,
38
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
kuma vashu yana bugun gaban shi nc babban dan
Sarkı
Da haka har ya iso saman mumbarin da aka
tanada domin su, ya dubi karagar muikin kasarsu ya
dan nisa ya luskanci jama'a wadanda tuni suz vi tsit!
shi dai ake sauraro, ya yi gyaran murya ya ce, "Ni ne
Bakar daya daga cikin 'ya'yan Sarki Gulam mai
burin lashe wannan gasar, saboda haka kowa ya bani
aron kunnensa zan fara daga cikin taskar Malamina".
Ya fara bada labari da cewa.
Kash! mai karatu sai sai a kara hakuri dani, ku
nemi littafi na uku domin jin yadda za ta kasance.
Shin waziri Kwabis zai samu damar cimma
burinsa kuwa na rashin son Affan ya hau karagar
mulki?
Ku biyoni a HIKAYA HAMSIN kashi na uku.
Daga mai kaunarku.
BASIRU ALIYU HARANDЕ
(Zuru)
07087325348-08163531398.
1
39
ود
Rikaya Hamsin
DANDANO
Basiru Aliyu Harande
Har ya juya da niyar wucewa sai ya yı ta riko
masa riga ta baya sai ya tsaya. Cikin wata siriryar
murya ta fara magana da ccwa, "Haba Samir ina so ka
san cewa tun lokacin da na fada ma sirrin zuciyata ka
barni cikin wani mawuyacin hali na zullumi saboda
rashin amsa min bukatata...."
Cikin sauri ya juya ya katseta da cewa, "Don
Allah ki yi hakuri ki kyaleni banda lokacin soyayya
yanzu, ki barni da irin masifar da mahaifinki ke son
jefa rayuwata ita ta isheni. Daga littafin mai suna
(MAKOMАTА)
BASIRU ALIYU HARANDE ZURU.
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!
Shahararren matashi mawakin Hausan nan
wato Ibrahim O.C. Sokoto na farin cikin sanar da
ma'abota sauraren wakokin Hausa sabon Album
dinsa na gab da fitowa, wanda yake dauke da
dadaden, zakakan wakokin tsantsagwaron soyayya
da sanyaya zukata da sanya shauki ga ma'abota
soyayya. Akwai wakokin fadakarwa, ilimintarwa da
nishadantarwa, ma za ka nemeshi a kasuwa don
wanke kwarkwatar kunnenka. Sunansa 'LAUNIN
SOYYAYA ALBUM'.Daga,
Ibrahim O/C Sokoto.
finaioianint icrorit!
40
AKARA CITY
BOOKSHOP
LITTATTAFAN MARUBUCIN HIKAYA HAMSIN
RUNDUNAR DAUKAR FANSA
FARMAKIN
ABOKAN GABA KOGON HALAKA
ABDULSALAM ADAM SHITU
(BATURE) G/KAYA
ABDULSALAM ADAM SHITO
(BATURE) G/KAYA
A.A. BATURE PUBLISHERS
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it