An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
HIKAYA HAMSIN2BASIRU ALIYU HARANDE ZURÜ
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
HIKAYA HAMSIN => 2
ta
da
OKACIN DA GIMBIYA Shahriya L OKACT kwalla kara ta fadi sumammiya sai
hankalin jama'a ya dada dugunzuma musamman
Sarki Fihru wanda bai san lokacin da ya rugo
gudu ya zo inda gimbiya ke kwance sama
kuyanginta hamsin na kanta suna kokarin ceto
rayuwarta ba
da
Cikin tsananin tashin hankali Sarki ya duka ya
tallafota yana jijjigata tare da kiran sunanta yana mai
żubda hawaye saboda ganin halin da 'yarsa wanda
yake tsananin so fiye da komai a duniya ta shiga.
Su kuwa jama'ar gari abin sai ya zame musu
biyu, ga tashin hankali da zullumin halin da sadauki
Affan ke ciki sannan ga gimbiya Shahariya kwance
sumammiya. Wannan yasa jama'a suka yi tsaye
cirko-cirko suka gaza motsi saboda rudewa.
Ana cikin haka ne sai kwatsám aka ga
hannayen sadauki Affan ya kamo bakin rijiyar. Koda
jama'ar da ke gurin suka ga haka sai kowa ya saki
baki ya tsurama bakin rijiyar ido. Ai ko ana cikin
haka sai gashi ya yunkuro da kyar ya fito jikinsa
faca-faca da jini. Dogon wandonsa ya yi kaca-kaca
tamkar tsohon mahaukaci. Duk da jikinsa babu wasu
4
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
raunika amma kallo daya za ka yi masa ka san yana
cikin matsanaiciyar gajiya.
Mamaki da al'ajabin wannan lamari ya sa Sarki
Fihru da al'umma suka shiga tunaniń wai shin
wannan sadauki ko mutum ne? Saboda tun a tarihin
wannan rijiyar ba a taba samun mahalukin da ya
taba shiga rijiyar ya fito ba.
'Tunaninsu ya katse ne lokacin da suka ji
sadauki Affan ya fara magana a galabaice da cewa,
"Ya ku mutanen kasar Zururi, kuyi sani cewa yau
ina muku albishir da na hallaka wanann tsohon
Kwadon da ya hana musu sakat a garin nan, kuma
kamar yadda na fada da farko wato idan na ci
wannan gasar gimbiya ta zama mallakin wannan
sadaukin saboda ni bana daga cikin masú neman
aurenta iyaka dai taimako kawai na yi..,"
Yana kawo nan a zancensa sai ya fadı saman
guiwowinsa saboda galabaita.
Farat! Kawai sai gani aka yi gimbiya Shahriya
ta tashi kamar wadda aka tsikara da allura idonta
kuri a bakin rijiyar. Wohoho! Ai ko da tayi ido hudu
da shi sai ta zabura da karfi ta mike tamkar ba ita
aka gama neman ranta ba. Har za ta ruga bakin
rijiyar da niyar ta rungumeshi sai ta tuna cewa cikin
mutane take kada a gane al'amarinta girmanta ya
fadi. Haka dai ta koma ta zauna zuciyarta cike da
5
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
tsan anin farin ciki tamkar wadda aka damkawa
muha lin aljanna.
Mu'lane kuwa tuni suka gurbata wurin da tafi da
shewa suna masu yiwa sadauki Affan jinjina akan
wannan gag rarumin aiki da ya yi wanda ko a tarihi ba
za a manta shi ba.
Cikin sauri sadauki Kasim yazo ya rungume
Affan yana sumıbatarsa sannan ya dubeshi ya ce, "Ya
kai wannan bakon sadauki shin kai wane, kuma daga
ina kake, mi ya kawoka kasarmu har ka zo ka ceci
rayuwata daga hallaka?"
Koda Affan yaji wadannan tambayoyi sai ya
ce, "Ni sunana Affan ibni Gulam kuma ba komai ya
kawoni Kasar nan ba face neman wani malami mai
suna Basiru ibini Aliyu Al-Harande, wanda kuma
har kawo yanzu ban gane gidansu ba."
Koda Kasim ya ji haka sai ya yi murmushi ya
ce, "In dfai wannan ne to kukanka ya kare domin shi
wannan Malamin yayana ne gidanmu daya da shi".
Suna cikin haka ne sai suka ji Raizu ya fara
sanarwa yana cewa Gimbiya Shahriya ta ce a sanar
da wannan bakon sadaukin cewa ya shirya aurenta
saboda shi ne ya samu nasarar lashe gasar da ta aza.
Koda Sadauki Affan yaji haka sai ya ga in ya
tsaya wannan gimbiyar za ta bata lokaci akan abinda
ya zo nema, kawai sai ya ja hannun sadauki Kasim
6
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
suką bi ta çikin dandazon mutane suka sulale suka
gudu.
Ba su zame a ko ina ba sai a gidan Malam
Basiru wanda ke can wajen garin Zururi ta baryar
yamma gidan dan karami ne mai dauke uku an
zagayeshi da ciyayi kai da gani ka san tsohon fakiri
ne.
Suna shigowa sai suka iske shi saman buzunsa zaune
kansa a sunkuye sai faman rubuce-rubuce kawai
yake yi domin bai da aiki sai rubutu.
Koda yaji alamun mutane sun shigo sai ya dago
kai domin ganin ko su waye, kawai sai ya yi arba da
su. Cikin mamaki Malam Basiru ya dubi Kasim ya
ce, "Ya kai Kasim shin wai ina ka shiga ne kwana
biyu ina ta nemanka ban ganka ba, kuma ina ka
samo mana wannan bakon Sadaukin?
Koda Kasimu ya ji haka sai ya kwashe labarin
tun lokacin da ya shiga gasar neman auren gimbiya
da irin taimakon da Affan ya yi masa ya ba Malam
Basiru, ya kare da cewa, "Shi wannan sadaukin
sunansa Affan, kuma ya ce kai ya zo nema".
Koda Malam Basiru yaji haka sai ransa ya bаcі
ya dubi Kasimu ya ce, "Kai in banda kana shashasha
ai ka san wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, kai ina
kai ina shiga gasar neman auren gfimbiya Shahriya
wadda tafi kowacce mace kyawu a duniyar wannan
7
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
karni? To ai gashi nan ka jefa kanka cikin masifar
domin numfashinka dai ke gaba da ka hallaka,
saboda haka kada in kara jin ka sa kanka cikin irin
wannan lamari.
Bayan Malam Basiru ya gama yiwa Kasim fada
sai ya dubi Affan ya yi masa godiya akan kubutar da
rayuwar kaninsa da ya yi sannan ya ce masa, "Yanzu
ina so ka je ka yi wanka ka kintsa sannan ka zo in ji
abinda ke tafe da kai."
Har Affan ya tashi sai Malam Basiru ya сe,
"Amma fa sai ka yi hakuri da yanayin gidan don ka
san gidan gauraye sai a hankali". Affan ya yi
murmushi sannan ya wuce.
* *
Bayan Sadauki Affan ya kimtsa sai suka
fuskanci juna. Malam Basiru ya dubeshi ya ce, "Ya
kai wannan sadauki shin mi ke tafe da kai wurina?"
Sadauki Affan ya yi gyaran murya sannan ya ce, "Ya
kai wannan malami, ka yi sani cewa na kasance daya
daga cikin 'ya'yan Sarki Gulam, wato Sarki mai
cikakken iko bisa yankin kasar Mahbub baki daya.
Lokacin da mahaifinmu zai rasu sai ya bar wasiyya
wurin Wazirinsa wato Baffanmu cewa duk wanda
yake so ya gajeshi sai ya bada daddadar hikiya guda
hamsin. Lokacin da Baffan namu ya sanar damu
8
Hikaya Hạmsin Basiru Aliyu Harande
hakan sai muka ce mu bamu da wata masaniya akan
hikayoyi, to shi ne aka bamu kwanaki sittin da
niyyar mu shiga duniya wurin Malaman Hikiya su
koyar damu tare da sharadin cewa duk wanda ya
wuce kwanaki sittin din za a fitar da shi daga gasar.
Wannan ne yasa Baffana ya turoni wurinka ka koyar
da ni domin in samu damar lashe wannan gasa.
Koda Malam basiru yaji haka sai hankalinsa ya
tashi idanunsa suka zazzago ya dafe kirji ya ce, "Kai
amma ba shakka wannan Baffa naka da ya turoka
wurina bai sonka ya ci amanarka kumá bai burinka
da ka lashe wannan gasa, domin kuwa da yana sonka
da ba zai turoka wurin almajiri ba ya ce wai Malami
ne ba, ga dai manyan Malaman hikiyu nan a duniya
irin su Ibn Adamu Shitu Al-bature da irin su Ibni
Sani Al-Madaks, mi yasa bai turaka wurin su ba?"
Koda Sadauki Affan yaji haka sai hankalinsa ya
tashi ransa ya baci har kyalla suka zubo masa. Cikin
sanyin jiki ya dubi Malam Basiru ya ce, "Ba shakka
wannan Bafdfan namu baya kaunata, amma sai na yi
zaton ko ya sauya halinsa ne". Malam Basiru ya ce,
"To mi yasa baka yi bincike akaina ba kafin ka zo?"
Takaici da bakin ciki yasa Affan bai ce kala ba.
Bayan wani dan dogon tunani sai Malam Basiru ya
dubi Affan ya ce, "Ka kwantar da hankalinka na yi
9
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
maka alkawarin muddin ina raye zan taimaka maka
sai ka cimma burinka".
Yana kawo wa nan a zancensa sai ya fada
bukkarsa ya bar Affan nan zaune yana bakin ciki.
Can bayan wani dan lokaci sai gashi ya fito
hannunsa rike da wani tsohon Kundin littafi wanda
aka yiwa bango da fatar Kada a jikin littafin an yi
wani rubutu cikin manyan haruffa kamar haka
"HIKIYA HAMSIN" littafin ya yi kura kai da gani
ka san tsohuwar ajiya ne. Malam Basiru na zuwa sai
ya mikawa Affan littafin sannan ya ce, "Wannan shi
ne Kundin HIKAYA HAMSIN wanda na gada
wurin Kakana Harande. Da yake kwanaki sittin ka
ce an baku ka ga ke nan kana da sauran kwanaki
arba'in kafin ka wuce, yanzu sai ka yi kokari kullum
ka karanta hikaya biyu. Na rantse da darajar iyayena
muddin ka tsaya ka yi ma wadannan hikayoyi
karatun kyau ka haddacesu to ba kasar ku ba kо
duniya gaba daya ake gasar hikayoyi sai ka lashe ta.
Kuma na yi ma alkawarin duk lokacin da za ka
koma tare zamu, domin in shiga cikin alkalan
wannan gasar. Sadauki Affan ya karbi littafin cike
da farin ciki sannan ya yi ma Malam Basiru
alkawarin muddin ya lashe wannan gasar shi zai
zama Wazirin sa". Ai koda Mallam Basiru ya yi an
10
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
hakan sai muka ce mu bamu da wata masaniya akan
hikayoyi, to shi ne aka bamu kwanaki sittin da
niyyar mu shiga duniya wurin Malaman Hikiya su
koyar damu tare da sharadin cewa duk wanda ya
wuce kwanaki sittin din za a fitar da shi daga gasar.
Wannan ne yasa Baffana ya turoni wurinka ka koyar
da ni domin in samu damar lashe wannan gasa.
Koda Malam basiru yaji haka sai hankalinsa ya
tashi idanunsa suka zazzago ya dafe kirji ya ce, "Kai
amma ba shakka wannan Baffa naka da ya turoka
wurina bai sonka ya ci amanarka kuma bai burinka
da ka lashe wannan gasa, domin kuwa da yana sonka
da ba zai turoka wurin almajiri ba ya ce wai Malami
ne ba, ga dai manyan Malaman hikiyu nan a duniya
irin su Ibn Adamu Shitu Al-bature da irin su Ibni
Sani Al-Madaks, mi yasa bai turaka wurin su ba?"
Koda Sadauki Affan yaji haka sai hankalinsa ya
tashi ransa ya baci har kyalla suka zubo masa. Cikin
sanyin jiki ya dubi Malam Basiru ya ce, "Ba shakka
wannan Bafdfan namu vaya kaunata, amma sai na yi
zaton ko ya sauya halinsa ne" Malam Basiru ya ceе,
"To mi yasa baka yi bincike akaina ba kafin ka zo?"
Takaici da bakin ciki yasa Affan bai ce kala ba.
Bayan wani dan dogon tunani sai Malam Basiru ya
dubi Affan ya ce, "Ka kwantar da hankalinka na yi
9
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
maka alkawarin muddin ina raye zan taimaka maka
sai ka cimma burinka".
Yana kawo wa nan a zancensa sai ya fada
bukkarsa ya bar Affan nan zaunc yana bakin ciki.
Can bayan wani dan lokaci sai gashi ya fito
hannunsa rike da wani tsohon Kundin littafi wanda
aka yiwa bango da fatar Kada a jikin littafin an yi
wani rubutu cikin manyan haruffa kamar haka
"HIKIYA HAMSIN" littafin ya yi kura kai da gani
ka san tsohuwar ajiya ne. Malam Basiru na zuwa sai
ya mikawa Affan littafin sannan ya ce, "Wannan shi
Kundin HIKAYA HAMSIN wanda na gada
Kakana Harande. Da yake kwanaki sittin ka
an baku ka ga ke nan kana da sauran kwanaki
arbe'in kafin ka wuce, yanzu sai ka yi kokari kullum
ka karanta hikaya biyu. Na rantse da darajar iyayena
muddin ka tsaya ka yi ma wadannan hikayoyi
karatun kyau ka haddacesy to ba kasar ku ba ko
duniya gaba daya akergasor hikayoyi sai ka lashe ta.
Kuma na yi ma alkawarin duk lokacin da za ka
koma tare zamu, domin in shiga cikin alkalan
baan gasar. Sadauki Affan ya karbi littafin cike
in ciki sannan ya yi ma Malam Basiru
alkawarin muddin ya lashe wannan gasar shi zai
zama Wazirin sa". Ai koda Mallam Basiru ya yi an
10
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
kan yaye bakin cikin shekara dari ga wanda aka
yiwa shi, sanana ta fara magana cikin muryarta mai
kama da ana busa sarewa da cewa;
"Ya kai sadauki Affan ka yi sani cewa idanuna
sun yi min ganin abinda yasa suka tausasa zuciyata
ware masa wani fage na musamman a cikinta, kuma
zuciyata tana buri da muradin ta gayyaci wannan
abun cikin wannan fagea da ba mahalukin da zai iya
cikashi sai shi. Zuciyata tuni ta nutse cikin kogin
Kaunarsa har ta gaza ninkaya bare ta ceci rayuwarta
daga hallaka. Wannan abu kuwa ba komai bane face
kai, tua lokacin da na fara ganinka a wurin gasar
shiga rijiya.
Koda Affan yaji haka sai ya dubeta ya ce, "Ya
ke wannan gimbiya shin wa ya fada miki sunana?
Kuma yá ya aka yi kika san inda nake?" Cikin
murmushi ta amsa da ccwa, "Yawan mafarkin ka shi
ya sa a san sunanka da inda kake, domin
mafarkinka ya zamc min tamkar wata sana'a da
nikeyi duk dare, tsananin so da kaunarka ne da suka
yi awon gaba da zuciyata shi ya sa na ce bara na zo
da kokon barar soyayyata garcka ko za ka taimaka
ka amsa.
Koda Affaa yaji haka sai ya ce, "Ya ke wannan
gimbiya ki yi sani cewa ni ba wai soyayya ko ncman
aurc ya kawoni Kasarku ba, na zo ne domin acman
13
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
ilimin hikiya domin samun damar lashe karagar
mulkin mahaifinmu saboda haka sai ki yi kokari
banda lokacin aurenki yanzu".
Koda gimbiya Shahriya taji haka sai hankalinsa
ya tashi ta dubeshi ta ce, "Haba ya kai abin kaunata
shin ka manta cewa kaine ka lashe gasar neman
aurena? To mi zai sa yanzu ka ce ba za ka aureni
ba?"
Koda Affan yaji haka sai ya ce, "To lokacin da
na shiga gasar cewa na yi na shiga ne domin neman
aurenki? ai cewa na yi idan na yi nasara kin zama
mallakin Sadauki Kasim, saboda haka yanzu ke
zaman Kasim kike, in kuwa wurinsa kika zo sai ki
cimmasa a daki, amma ba dai ni ba".
Duk da wadannan kalamai nasa sun dan sosa
ranta amma sai ta kanne ta dubeshi ta ce, "Ya kai
masoyina kayi sani cewa mahaifina ya kasance mai
tsananin tarin mayaka masu tsananin karfi da
sadaukantaka, wadanda ko shi bai san adadinsu ba,
kuma duk fadin duniya ba abinda yake so da kauna
sama da ni, saboda haka idan sarauta kake so ka bari
zan yi masa magana ya bamu sadaukai mu je can
kasarkui mu azaka saman mulki ko ta karfin tsiya in
ya so sai mu yi aure bayan ka zama Sarki.
Koda Affan ya yi haka sai ya ce, "Ai wanann
abin kunya ne a gareni ga 'ya'yana ace ta karfin na
14
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
amshi karagar mahaifin mu wurin yan uwana.
Kuma kin sani cewa nima ina da karfin da zan
tarwalsa 'yan uwana in amshe mulki amma sai ban
yi haka ba saboda gudun kada duniya ta aibatani.
Don haka yanzu banda lokacin komai a gabana face
wannan littafin hikaya saboda haka kiyi hakuri".
Koda gimbiya Shahriya taji haka, sai ranta ya
6aci, zuciyarta ta harzuka, cikin fushi ta mike ta fara
magana cikin fushi da cewa, "Kai karya ka ke yi! To
bari ka ji, tunda na zo duniya ban taßa neman abu na
rasa shi ba, kaima ba zan rasa ka ba, yanzu zanje in
hadaka da mahaifina, za ka ga abinda zai biyo baya".
Tana kawo wannan a zancenta sai ta juya ta
fice. Tuni idanun ta sunyi shabe-shabe da kwalla.
Fitarta ke da wuya sai ga Mallam Bashiru ya fito
daga kicin niki-niki da abinci idanunsa sunyi jawur
saboda hayaki.
Bayan ya ajiye abincin gaban Affan sai ya
tambayenshi cewa, "Shin ya ku ka yi da gimbiya
ne?"
Affan ya kwashe labarin abinda ya gudana
tsakaninsa da ita ya gaya masa.
Koda Mallam Bashiru yaji haka, sai ya ce "Kai
amma Affan da shi ne ka ke irin wadannan suce
suna sonka ai sai ka tsaya ka ci arziki, sannan ba ka
15
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
tsoron wannan wulakancin da ka yi ma ta ya janyo
ma wata matsala?"
Koda Affan yaji haka sai ya ce, "Kai Mallam
ka sani cewa idan tana kurin ita 'yar sarautace to
nima fa dan sarautane in kuwa karfin mulki ko
dukiya ta ke yi da su nima ina da su, har ma na ninka
ta,saboda haka bana tsoronta.
Mallam ya sosa keya sannan ya ce "To ka dai
bi ta a hankali, domin halin mahaifintą ba shi da
sauki a kanta, karka janyo mana wutar da ba ma iya
kashe ta".
* *
Wata rana sädauki Affan da Kasim sun dawo
daga faurata,a hanyarsu ta dawowa ne sai fira da
karke tsakanin su inda Kasim ya dubi Affan ya ce,
"Amma fa gaskiya ka bani mamaki da za a ce
sarauniya kyawawan duniya ta kawo ma kokon
barar soyayyarta har gida amma ka yi ma ta
wulakanci. Ai tsayawa za ka yi ka ja kaya."
Koda Affan ya ji haka, sai ya yi murmushi ya
ce, "To ai lokaci da na lashe gasar neman aurenta
cewa na yi ta zama mallakinka, mi.ya sa lokacin da
ta zo baka fito kun gana ba?"
Koda Kasim yaji haka sai ya dafe kirji yа се
"Ai lokacin da na leko na ganku tare, sai na koma na
16
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
dunkule cikin mayafi saboda ban son ma ta ganní
don na san gimbiya Shahriya tafi karfina, ba aji na
ba ce, karambani da kaddara kawai suka sa na shiga
gasar neman aurenta, kuma na rantse da darajar
iyayena duk fadin duniya ba wani da namijin da ya
dace da Gimbiya Shahriya fa ce kai.
Koda Affan yaji haka sai ya yi murmushi ya ce,
"A gaskiya nima ba wai bana sonta bane saboda abin
alfahari ne a gareni ace na auri Sarauniya kyawawan
duniya kamarta, to amma ba zan so hada soyayyarta
da abinda ya kawoni nan ba, ka ga yau kwanaki
biyar kacal suka yage min a garin nan kuma gashi
ban kammala karatun littafin hikayoyi ba, amma da
za tayi hakuri ta bari har in cika ma burina dani da
kaina zan dawo neman aurenta ....."
Suna cikin haka ne sai suka ji kuwwar Mallam
Bashiru yana neman kawo masa dauki cikin sauri
suka zare takobinsu suka ruga domin ganin abin ke
faruwa. Suna isa kofar gidan sai suka iske shi an yi
masa daurin buhun goro idanunsa sun yi jawur kai
da gani ka ksan ya wahala. Cikin sauri suka zo suka
kwanceshi, yana tashi sai ya rufe Affan da fada yana
mai cewa, "Ka ga abinda ni ke yi maka maka gudu
ke nan, sai da na ce ka bi a hankali da gimbiya
Shuhriya amma ka ki, na rantse da darajar iyaycna
da sadaukan da ta turo sun iske ka da ko gunduwa17
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
gunduwa suka yi da namanka ba za ka ishe su rabo
ba, yanzu sai ka shiga ka ga yadda suka yamutse min
gida duk da babu komai ciki sai tsummokara.
Koda Sadauki Affan yaji haka sai hankalinsa ya
tashi nan da nan tunanin littafin Hikayoyi ya fado
masa, cikin sauri ya fada cikin gidan ya siek gidan
yamutse, kawai sai ya zarce fakinsa ya iske dakin
kaca-kaca kawai sai ya shiga neman littafin hikaya,
sai da ya dauki sa'o'i yana bincike amma bai ganshi
ba, yana cikin haka ne sai ya yi arba da wata takarda
a kasa. Cikin sauri ya duka ya dauki takardar ya
warware ya fara karantawa kamar haka.
Daga masoyiyarka wadda tsananin kaunarka ya
raunata zuciyarta ka yi sani cewa kwana uku ke nan
rabona da ganin kyakkyawar fuskarka amma sun
zame min tamkar shekaru uku, saboda tunani,
mafarki da shaukin begenka sunsa na rasa sukuni,
saboda haka kada ka zargi kowa akan wannan abun
da ya faru ni ce na turo a dauko min wannan littafin
don haka idan kana son littafinka sai ka iskeni gida
kafin faduwar rana idan kuwa baka zo ba to ni na zo.
Daga mai kaunarka gimbiya Shahriya.
Wani irin bakin ciki da takaici suka daki
zuciyarsa ta rika tafarfasa kamar za ta tsage kirjinsa
ta fito. Tsikar jikinsa ta mimmike, idanunsa suka yi
jawur kamar gauta jikinsa ya kama rawa saboda
18
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
harzuka, kawai sai ya zare takobinsa ya fito cikin
fishi hawaycn takaici na zuba a idanunsa. Yana
fitowa sai ya yi kicibus da su Malam Basiru da
Kasim sun shigo cikin kaduwa, Malam ya
tambayeshi, "Ya kai Affan shin ina za ka na ga ka
zare takobi?" Cikin fushi ya amsa da cewa, "Ta sa an
dauke min littafina shi zan je wurinta in amso
yanzu". Koda Malam Basiru yaji haka sai ya rikeshi
cikin razani ya ce, "Kai rufawa kanka asiri na rantse
da girman iyayena shiga gidan sarki gareka dai-dai
yake da a saki Zomo ace gurgu yaje ya kamoshi,
saboda haka ka bari mu bi abin a hankali".
Koda Affan yaji haka sai ya ce, "Ka bari kawai
in je in amso littafin, kuma in yi ma ta iyaka dani,
idan ba haka ba kuwa za ta ji daci na".
Yana kawowa nan a zancensa sai ya fisge
hannunsa ya wuce. Malam Basiru na kira amma ina
tuni ya hau doki ya zabureshi ya yi gaba. Har
Sadauki Kasim ya kamo doki zai hau sai Malam
Basiru ya daka mai tsawa da cewa, "Kai ina za ka?"
Kasim ya ce, "Zan je ne in taimaka masa". Malam
Basiru ya ce, "To rufawa kanka asiri kada ka debo
mana ruwan dafa kanmu, idan a wancan lokacin ya
kubutar da kai, to wannan lokacin ko kansa ba zai
iya cetowa ba bare wani".
19
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
Jikin Sadauki Kasim ya yi sanyi da jin
wadannan kalamai sai kawai ya samu wuri ya zauna
abin shi.
Shi ko sadauki Affan, koda ya isa kofar gidan
sarautar sai ya iske dandazon Dakarun cikin shigar
yaki sai faman kai komo suk yi suna muzurai tamkar
sa ci babu. Har ya kawo kofar shiga gidan ba wanda
ya ce da shi kala bare a tsai da shi. Kai tsayc ya
shige gidan inda ya iske sadaukai da barori sai
faman sha'anin gaban su kawai suke yi bama wanda
ya kulashi.
Wannan ne yasa Affan ya cika da mamaki yana
mai tunanin cewa shin ba Malam Basiru ya ce shiga
gidan zai yi masa wahala ba to shi ya aka yi ya shiga
gidan ba wanda ya ce da shi kala barc a tarcshi?
Tunaninsa ya katsc ne lokacin da ya tsinci
kanse tsamo-tsamo a cikin raga shi da dokinsa, kafin
ya yi wani yunkuri tuni wasu Dakaru sun yi ca
akansa sun yi masa kamun kazar kuku suka daurcshi
tamau, can sai ga Raizu ya zo ya ce,
"Ma za ku kaishi kurkuku kamar yadda gimbiya
Shahriya ta umarta". Haka aka daukeshi aka kai
kurkukun da ke cikin gidan Sarki aka daďdaureshi
cikin sarka.
20
Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande
Ilaka ya kasance cikin kurkukun har dare ya yi
yana hangen ana azabtar da wasu fursunoni amma
shi ba a taba shi ba sai ma kokarin kula da shi kawai
ake yi.
Kansa sunkuyc yana tunanin wannan hali da ya
shiga kawai sai yaji an turo kyauren dakin da yake
an shigo. Koda ya duba sai ya yi arba da
kyakkyawar fuskarta, tana cikin shigar kayan bacci
masu shara-shara.
Tun kafin ta iso ta jcfeshi da wani murmushi
mai juyar da hankalin duk wani da namiji. Shi ko
Affan lokacin ne wani bakin ciki da takaici ya
yunkuro masa har ya wujijjiga sarkar da aka
daureshi ko zai iya kwaccwa amma ina sai ma ji ya
yi tamkar sarkar ta dada daureshi. Cikin tsananin
fushi ya fara magana da cewa, "Shin wai ke mi ne
kike so gareni ne? Na ce banda lokacinki