Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels HIKAYA HAMSIN2BASIRU ALIYU HARANDE ZURÜ Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande HIKAYA HAMSIN => 2 ta da OKACIN DA GIMBIYA Shahriya L OKACT kwalla kara ta fadi sumammiya sai hankalin jama'a ya dada dugunzuma musamman Sarki Fihru wanda bai san lokacin da ya rugo gudu ya zo inda gimbiya ke kwance sama kuyanginta hamsin na kanta suna kokarin ceto rayuwarta ba da Cikin tsananin tashin hankali Sarki ya duka ya tallafota yana jijjigata tare da kiran sunanta yana mai żubda hawaye saboda ganin halin da 'yarsa wanda yake tsananin so fiye da komai a duniya ta shiga. Su kuwa jama'ar gari abin sai ya zame musu biyu, ga tashin hankali da zullumin halin da sadauki Affan ke ciki sannan ga gimbiya Shahariya kwance sumammiya. Wannan yasa jama'a suka yi tsaye cirko-cirko suka gaza motsi saboda rudewa. Ana cikin haka ne sai kwatsám aka ga hannayen sadauki Affan ya kamo bakin rijiyar. Koda jama'ar da ke gurin suka ga haka sai kowa ya saki baki ya tsurama bakin rijiyar ido. Ai ko ana cikin haka sai gashi ya yunkuro da kyar ya fito jikinsa faca-faca da jini. Dogon wandonsa ya yi kaca-kaca tamkar tsohon mahaukaci. Duk da jikinsa babu wasu 4 Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande raunika amma kallo daya za ka yi masa ka san yana cikin matsanaiciyar gajiya. Mamaki da al'ajabin wannan lamari ya sa Sarki Fihru da al'umma suka shiga tunaniń wai shin wannan sadauki ko mutum ne? Saboda tun a tarihin wannan rijiyar ba a taba samun mahalukin da ya taba shiga rijiyar ya fito ba. 'Tunaninsu ya katse ne lokacin da suka ji sadauki Affan ya fara magana a galabaice da cewa, "Ya ku mutanen kasar Zururi, kuyi sani cewa yau ina muku albishir da na hallaka wanann tsohon Kwadon da ya hana musu sakat a garin nan, kuma kamar yadda na fada da farko wato idan na ci wannan gasar gimbiya ta zama mallakin wannan sadaukin saboda ni bana daga cikin masú neman aurenta iyaka dai taimako kawai na yi..," Yana kawo nan a zancensa sai ya fadı saman guiwowinsa saboda galabaita. Farat! Kawai sai gani aka yi gimbiya Shahriya ta tashi kamar wadda aka tsikara da allura idonta kuri a bakin rijiyar. Wohoho! Ai ko da tayi ido hudu da shi sai ta zabura da karfi ta mike tamkar ba ita aka gama neman ranta ba. Har za ta ruga bakin rijiyar da niyar ta rungumeshi sai ta tuna cewa cikin mutane take kada a gane al'amarinta girmanta ya fadi. Haka dai ta koma ta zauna zuciyarta cike da 5 Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande tsan anin farin ciki tamkar wadda aka damkawa muha lin aljanna. Mu'lane kuwa tuni suka gurbata wurin da tafi da shewa suna masu yiwa sadauki Affan jinjina akan wannan gag rarumin aiki da ya yi wanda ko a tarihi ba za a manta shi ba. Cikin sauri sadauki Kasim yazo ya rungume Affan yana sumıbatarsa sannan ya dubeshi ya ce, "Ya kai wannan bakon sadauki shin kai wane, kuma daga ina kake, mi ya kawoka kasarmu har ka zo ka ceci rayuwata daga hallaka?" Koda Affan yaji wadannan tambayoyi sai ya ce, "Ni sunana Affan ibni Gulam kuma ba komai ya kawoni Kasar nan ba face neman wani malami mai suna Basiru ibini Aliyu Al-Harande, wanda kuma har kawo yanzu ban gane gidansu ba." Koda Kasim ya ji haka sai ya yi murmushi ya ce, "In dfai wannan ne to kukanka ya kare domin shi wannan Malamin yayana ne gidanmu daya da shi". Suna cikin haka ne sai suka ji Raizu ya fara sanarwa yana cewa Gimbiya Shahriya ta ce a sanar da wannan bakon sadaukin cewa ya shirya aurenta saboda shi ne ya samu nasarar lashe gasar da ta aza. Koda Sadauki Affan yaji haka sai ya ga in ya tsaya wannan gimbiyar za ta bata lokaci akan abinda ya zo nema, kawai sai ya ja hannun sadauki Kasim 6 Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande suką bi ta çikin dandazon mutane suka sulale suka gudu. Ba su zame a ko ina ba sai a gidan Malam Basiru wanda ke can wajen garin Zururi ta baryar yamma gidan dan karami ne mai dauke uku an zagayeshi da ciyayi kai da gani ka san tsohon fakiri ne. Suna shigowa sai suka iske shi saman buzunsa zaune kansa a sunkuye sai faman rubuce-rubuce kawai yake yi domin bai da aiki sai rubutu. Koda yaji alamun mutane sun shigo sai ya dago kai domin ganin ko su waye, kawai sai ya yi arba da su. Cikin mamaki Malam Basiru ya dubi Kasim ya ce, "Ya kai Kasim shin wai ina ka shiga ne kwana biyu ina ta nemanka ban ganka ba, kuma ina ka samo mana wannan bakon Sadaukin? Koda Kasimu ya ji haka sai ya kwashe labarin tun lokacin da ya shiga gasar neman auren gimbiya da irin taimakon da Affan ya yi masa ya ba Malam Basiru, ya kare da cewa, "Shi wannan sadaukin sunansa Affan, kuma ya ce kai ya zo nema". Koda Malam Basiru yaji haka sai ransa ya bаcі ya dubi Kasimu ya ce, "Kai in banda kana shashasha ai ka san wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, kai ina kai ina shiga gasar neman auren gfimbiya Shahriya wadda tafi kowacce mace kyawu a duniyar wannan 7 Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande karni? To ai gashi nan ka jefa kanka cikin masifar domin numfashinka dai ke gaba da ka hallaka, saboda haka kada in kara jin ka sa kanka cikin irin wannan lamari. Bayan Malam Basiru ya gama yiwa Kasim fada sai ya dubi Affan ya yi masa godiya akan kubutar da rayuwar kaninsa da ya yi sannan ya ce masa, "Yanzu ina so ka je ka yi wanka ka kintsa sannan ka zo in ji abinda ke tafe da kai." Har Affan ya tashi sai Malam Basiru ya сe, "Amma fa sai ka yi hakuri da yanayin gidan don ka san gidan gauraye sai a hankali". Affan ya yi murmushi sannan ya wuce. * * Bayan Sadauki Affan ya kimtsa sai suka fuskanci juna. Malam Basiru ya dubeshi ya ce, "Ya kai wannan sadauki shin mi ke tafe da kai wurina?" Sadauki Affan ya yi gyaran murya sannan ya ce, "Ya kai wannan malami, ka yi sani cewa na kasance daya daga cikin 'ya'yan Sarki Gulam, wato Sarki mai cikakken iko bisa yankin kasar Mahbub baki daya. Lokacin da mahaifinmu zai rasu sai ya bar wasiyya wurin Wazirinsa wato Baffanmu cewa duk wanda yake so ya gajeshi sai ya bada daddadar hikiya guda hamsin. Lokacin da Baffan namu ya sanar damu 8 Hikaya Hạmsin Basiru Aliyu Harande hakan sai muka ce mu bamu da wata masaniya akan hikayoyi, to shi ne aka bamu kwanaki sittin da niyyar mu shiga duniya wurin Malaman Hikiya su koyar damu tare da sharadin cewa duk wanda ya wuce kwanaki sittin din za a fitar da shi daga gasar. Wannan ne yasa Baffana ya turoni wurinka ka koyar da ni domin in samu damar lashe wannan gasa. Koda Malam basiru yaji haka sai hankalinsa ya tashi idanunsa suka zazzago ya dafe kirji ya ce, "Kai amma ba shakka wannan Baffa naka da ya turoka wurina bai sonka ya ci amanarka kumá bai burinka da ka lashe wannan gasa, domin kuwa da yana sonka da ba zai turoka wurin almajiri ba ya ce wai Malami ne ba, ga dai manyan Malaman hikiyu nan a duniya irin su Ibn Adamu Shitu Al-bature da irin su Ibni Sani Al-Madaks, mi yasa bai turaka wurin su ba?" Koda Sadauki Affan yaji haka sai hankalinsa ya tashi ransa ya baci har kyalla suka zubo masa. Cikin sanyin jiki ya dubi Malam Basiru ya ce, "Ba shakka wannan Bafdfan namu baya kaunata, amma sai na yi zaton ko ya sauya halinsa ne". Malam Basiru ya ce, "To mi yasa baka yi bincike akaina ba kafin ka zo?" Takaici da bakin ciki yasa Affan bai ce kala ba. Bayan wani dan dogon tunani sai Malam Basiru ya dubi Affan ya ce, "Ka kwantar da hankalinka na yi 9 Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande maka alkawarin muddin ina raye zan taimaka maka sai ka cimma burinka". Yana kawo wa nan a zancensa sai ya fada bukkarsa ya bar Affan nan zaune yana bakin ciki. Can bayan wani dan lokaci sai gashi ya fito hannunsa rike da wani tsohon Kundin littafi wanda aka yiwa bango da fatar Kada a jikin littafin an yi wani rubutu cikin manyan haruffa kamar haka "HIKIYA HAMSIN" littafin ya yi kura kai da gani ka san tsohuwar ajiya ne. Malam Basiru na zuwa sai ya mikawa Affan littafin sannan ya ce, "Wannan shi ne Kundin HIKAYA HAMSIN wanda na gada wurin Kakana Harande. Da yake kwanaki sittin ka ce an baku ka ga ke nan kana da sauran kwanaki arba'in kafin ka wuce, yanzu sai ka yi kokari kullum ka karanta hikaya biyu. Na rantse da darajar iyayena muddin ka tsaya ka yi ma wadannan hikayoyi karatun kyau ka haddacesu to ba kasar ku ba kо duniya gaba daya ake gasar hikayoyi sai ka lashe ta. Kuma na yi ma alkawarin duk lokacin da za ka koma tare zamu, domin in shiga cikin alkalan wannan gasar. Sadauki Affan ya karbi littafin cike da farin ciki sannan ya yi ma Malam Basiru alkawarin muddin ya lashe wannan gasar shi zai zama Wazirin sa". Ai koda Mallam Basiru ya yi an 10 Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande hakan sai muka ce mu bamu da wata masaniya akan hikayoyi, to shi ne aka bamu kwanaki sittin da niyyar mu shiga duniya wurin Malaman Hikiya su koyar damu tare da sharadin cewa duk wanda ya wuce kwanaki sittin din za a fitar da shi daga gasar. Wannan ne yasa Baffana ya turoni wurinka ka koyar da ni domin in samu damar lashe wannan gasa. Koda Malam basiru yaji haka sai hankalinsa ya tashi idanunsa suka zazzago ya dafe kirji ya ce, "Kai amma ba shakka wannan Baffa naka da ya turoka wurina bai sonka ya ci amanarka kuma bai burinka da ka lashe wannan gasa, domin kuwa da yana sonka da ba zai turoka wurin almajiri ba ya ce wai Malami ne ba, ga dai manyan Malaman hikiyu nan a duniya irin su Ibn Adamu Shitu Al-bature da irin su Ibni Sani Al-Madaks, mi yasa bai turaka wurin su ba?" Koda Sadauki Affan yaji haka sai hankalinsa ya tashi ransa ya baci har kyalla suka zubo masa. Cikin sanyin jiki ya dubi Malam Basiru ya ce, "Ba shakka wannan Bafdfan namu vaya kaunata, amma sai na yi zaton ko ya sauya halinsa ne" Malam Basiru ya ceе, "To mi yasa baka yi bincike akaina ba kafin ka zo?" Takaici da bakin ciki yasa Affan bai ce kala ba. Bayan wani dan dogon tunani sai Malam Basiru ya dubi Affan ya ce, "Ka kwantar da hankalinka na yi 9 Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande maka alkawarin muddin ina raye zan taimaka maka sai ka cimma burinka". Yana kawo wa nan a zancensa sai ya fada bukkarsa ya bar Affan nan zaunc yana bakin ciki. Can bayan wani dan lokaci sai gashi ya fito hannunsa rike da wani tsohon Kundin littafi wanda aka yiwa bango da fatar Kada a jikin littafin an yi wani rubutu cikin manyan haruffa kamar haka "HIKIYA HAMSIN" littafin ya yi kura kai da gani ka san tsohuwar ajiya ne. Malam Basiru na zuwa sai ya mikawa Affan littafin sannan ya ce, "Wannan shi Kundin HIKAYA HAMSIN wanda na gada Kakana Harande. Da yake kwanaki sittin ka an baku ka ga ke nan kana da sauran kwanaki arbe'in kafin ka wuce, yanzu sai ka yi kokari kullum ka karanta hikaya biyu. Na rantse da darajar iyayena muddin ka tsaya ka yi ma wadannan hikayoyi karatun kyau ka haddacesy to ba kasar ku ba ko duniya gaba daya akergasor hikayoyi sai ka lashe ta. Kuma na yi ma alkawarin duk lokacin da za ka koma tare zamu, domin in shiga cikin alkalan baan gasar. Sadauki Affan ya karbi littafin cike in ciki sannan ya yi ma Malam Basiru alkawarin muddin ya lashe wannan gasar shi zai zama Wazirin sa". Ai koda Mallam Basiru ya yi an 10 Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande kan yaye bakin cikin shekara dari ga wanda aka yiwa shi, sanana ta fara magana cikin muryarta mai kama da ana busa sarewa da cewa; "Ya kai sadauki Affan ka yi sani cewa idanuna sun yi min ganin abinda yasa suka tausasa zuciyata ware masa wani fage na musamman a cikinta, kuma zuciyata tana buri da muradin ta gayyaci wannan abun cikin wannan fagea da ba mahalukin da zai iya cikashi sai shi. Zuciyata tuni ta nutse cikin kogin Kaunarsa har ta gaza ninkaya bare ta ceci rayuwarta daga hallaka. Wannan abu kuwa ba komai bane face kai, tua lokacin da na fara ganinka a wurin gasar shiga rijiya. Koda Affan yaji haka sai ya dubeta ya ce, "Ya ke wannan gimbiya shin wa ya fada miki sunana? Kuma yá ya aka yi kika san inda nake?" Cikin murmushi ta amsa da ccwa, "Yawan mafarkin ka shi ya sa a san sunanka da inda kake, domin mafarkinka ya zamc min tamkar wata sana'a da nikeyi duk dare, tsananin so da kaunarka ne da suka yi awon gaba da zuciyata shi ya sa na ce bara na zo da kokon barar soyayyata garcka ko za ka taimaka ka amsa. Koda Affaa yaji haka sai ya ce, "Ya ke wannan gimbiya ki yi sani cewa ni ba wai soyayya ko ncman aurc ya kawoni Kasarku ba, na zo ne domin acman 13 Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande ilimin hikiya domin samun damar lashe karagar mulkin mahaifinmu saboda haka sai ki yi kokari banda lokacin aurenki yanzu". Koda gimbiya Shahriya taji haka sai hankalinsa ya tashi ta dubeshi ta ce, "Haba ya kai abin kaunata shin ka manta cewa kaine ka lashe gasar neman aurena? To mi zai sa yanzu ka ce ba za ka aureni ba?" Koda Affan yaji haka sai ya ce, "To lokacin da na shiga gasar cewa na yi na shiga ne domin neman aurenki? ai cewa na yi idan na yi nasara kin zama mallakin Sadauki Kasim, saboda haka yanzu ke zaman Kasim kike, in kuwa wurinsa kika zo sai ki cimmasa a daki, amma ba dai ni ba". Duk da wadannan kalamai nasa sun dan sosa ranta amma sai ta kanne ta dubeshi ta ce, "Ya kai masoyina kayi sani cewa mahaifina ya kasance mai tsananin tarin mayaka masu tsananin karfi da sadaukantaka, wadanda ko shi bai san adadinsu ba, kuma duk fadin duniya ba abinda yake so da kauna sama da ni, saboda haka idan sarauta kake so ka bari zan yi masa magana ya bamu sadaukai mu je can kasarkui mu azaka saman mulki ko ta karfin tsiya in ya so sai mu yi aure bayan ka zama Sarki. Koda Affan ya yi haka sai ya ce, "Ai wanann abin kunya ne a gareni ga 'ya'yana ace ta karfin na 14 Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande amshi karagar mahaifin mu wurin yan uwana. Kuma kin sani cewa nima ina da karfin da zan tarwalsa 'yan uwana in amshe mulki amma sai ban yi haka ba saboda gudun kada duniya ta aibatani. Don haka yanzu banda lokacin komai a gabana face wannan littafin hikaya saboda haka kiyi hakuri". Koda gimbiya Shahriya taji haka, sai ranta ya 6aci, zuciyarta ta harzuka, cikin fushi ta mike ta fara magana cikin fushi da cewa, "Kai karya ka ke yi! To bari ka ji, tunda na zo duniya ban taßa neman abu na rasa shi ba, kaima ba zan rasa ka ba, yanzu zanje in hadaka da mahaifina, za ka ga abinda zai biyo baya". Tana kawo wannan a zancenta sai ta juya ta fice. Tuni idanun ta sunyi shabe-shabe da kwalla. Fitarta ke da wuya sai ga Mallam Bashiru ya fito daga kicin niki-niki da abinci idanunsa sunyi jawur saboda hayaki. Bayan ya ajiye abincin gaban Affan sai ya tambayenshi cewa, "Shin ya ku ka yi da gimbiya ne?" Affan ya kwashe labarin abinda ya gudana tsakaninsa da ita ya gaya masa. Koda Mallam Bashiru yaji haka, sai ya ce "Kai amma Affan da shi ne ka ke irin wadannan suce suna sonka ai sai ka tsaya ka ci arziki, sannan ba ka 15 Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande tsoron wannan wulakancin da ka yi ma ta ya janyo ma wata matsala?" Koda Affan yaji haka sai ya ce, "Kai Mallam ka sani cewa idan tana kurin ita 'yar sarautace to nima fa dan sarautane in kuwa karfin mulki ko dukiya ta ke yi da su nima ina da su, har ma na ninka ta,saboda haka bana tsoronta. Mallam ya sosa keya sannan ya ce "To ka dai bi ta a hankali, domin halin mahaifintą ba shi da sauki a kanta, karka janyo mana wutar da ba ma iya kashe ta". * * Wata rana sädauki Affan da Kasim sun dawo daga faurata,a hanyarsu ta dawowa ne sai fira da karke tsakanin su inda Kasim ya dubi Affan ya ce, "Amma fa gaskiya ka bani mamaki da za a ce sarauniya kyawawan duniya ta kawo ma kokon barar soyayyarta har gida amma ka yi ma ta wulakanci. Ai tsayawa za ka yi ka ja kaya." Koda Affan ya ji haka, sai ya yi murmushi ya ce, "To ai lokaci da na lashe gasar neman aurenta cewa na yi ta zama mallakinka, mi.ya sa lokacin da ta zo baka fito kun gana ba?" Koda Kasim yaji haka sai ya dafe kirji yа се "Ai lokacin da na leko na ganku tare, sai na koma na 16 Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande dunkule cikin mayafi saboda ban son ma ta ganní don na san gimbiya Shahriya tafi karfina, ba aji na ba ce, karambani da kaddara kawai suka sa na shiga gasar neman aurenta, kuma na rantse da darajar iyayena duk fadin duniya ba wani da namijin da ya dace da Gimbiya Shahriya fa ce kai. Koda Affan yaji haka sai ya yi murmushi ya ce, "A gaskiya nima ba wai bana sonta bane saboda abin alfahari ne a gareni ace na auri Sarauniya kyawawan duniya kamarta, to amma ba zan so hada soyayyarta da abinda ya kawoni nan ba, ka ga yau kwanaki biyar kacal suka yage min a garin nan kuma gashi ban kammala karatun littafin hikayoyi ba, amma da za tayi hakuri ta bari har in cika ma burina dani da kaina zan dawo neman aurenta ....." Suna cikin haka ne sai suka ji kuwwar Mallam Bashiru yana neman kawo masa dauki cikin sauri suka zare takobinsu suka ruga domin ganin abin ke faruwa. Suna isa kofar gidan sai suka iske shi an yi masa daurin buhun goro idanunsa sun yi jawur kai da gani ka ksan ya wahala. Cikin sauri suka zo suka kwanceshi, yana tashi sai ya rufe Affan da fada yana mai cewa, "Ka ga abinda ni ke yi maka maka gudu ke nan, sai da na ce ka bi a hankali da gimbiya Shuhriya amma ka ki, na rantse da darajar iyaycna da sadaukan da ta turo sun iske ka da ko gunduwa17 Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande gunduwa suka yi da namanka ba za ka ishe su rabo ba, yanzu sai ka shiga ka ga yadda suka yamutse min gida duk da babu komai ciki sai tsummokara. Koda Sadauki Affan yaji haka sai hankalinsa ya tashi nan da nan tunanin littafin Hikayoyi ya fado masa, cikin sauri ya fada cikin gidan ya siek gidan yamutse, kawai sai ya zarce fakinsa ya iske dakin kaca-kaca kawai sai ya shiga neman littafin hikaya, sai da ya dauki sa'o'i yana bincike amma bai ganshi ba, yana cikin haka ne sai ya yi arba da wata takarda a kasa. Cikin sauri ya duka ya dauki takardar ya warware ya fara karantawa kamar haka. Daga masoyiyarka wadda tsananin kaunarka ya raunata zuciyarta ka yi sani cewa kwana uku ke nan rabona da ganin kyakkyawar fuskarka amma sun zame min tamkar shekaru uku, saboda tunani, mafarki da shaukin begenka sunsa na rasa sukuni, saboda haka kada ka zargi kowa akan wannan abun da ya faru ni ce na turo a dauko min wannan littafin don haka idan kana son littafinka sai ka iskeni gida kafin faduwar rana idan kuwa baka zo ba to ni na zo. Daga mai kaunarka gimbiya Shahriya. Wani irin bakin ciki da takaici suka daki zuciyarsa ta rika tafarfasa kamar za ta tsage kirjinsa ta fito. Tsikar jikinsa ta mimmike, idanunsa suka yi jawur kamar gauta jikinsa ya kama rawa saboda 18 Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande harzuka, kawai sai ya zare takobinsa ya fito cikin fishi hawaycn takaici na zuba a idanunsa. Yana fitowa sai ya yi kicibus da su Malam Basiru da Kasim sun shigo cikin kaduwa, Malam ya tambayeshi, "Ya kai Affan shin ina za ka na ga ka zare takobi?" Cikin fushi ya amsa da cewa, "Ta sa an dauke min littafina shi zan je wurinta in amso yanzu". Koda Malam Basiru yaji haka sai ya rikeshi cikin razani ya ce, "Kai rufawa kanka asiri na rantse da girman iyayena shiga gidan sarki gareka dai-dai yake da a saki Zomo ace gurgu yaje ya kamoshi, saboda haka ka bari mu bi abin a hankali". Koda Affan yaji haka sai ya ce, "Ka bari kawai in je in amso littafin, kuma in yi ma ta iyaka dani, idan ba haka ba kuwa za ta ji daci na". Yana kawowa nan a zancensa sai ya fisge hannunsa ya wuce. Malam Basiru na kira amma ina tuni ya hau doki ya zabureshi ya yi gaba. Har Sadauki Kasim ya kamo doki zai hau sai Malam Basiru ya daka mai tsawa da cewa, "Kai ina za ka?" Kasim ya ce, "Zan je ne in taimaka masa". Malam Basiru ya ce, "To rufawa kanka asiri kada ka debo mana ruwan dafa kanmu, idan a wancan lokacin ya kubutar da kai, to wannan lokacin ko kansa ba zai iya cetowa ba bare wani". 19 Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande Jikin Sadauki Kasim ya yi sanyi da jin wadannan kalamai sai kawai ya samu wuri ya zauna abin shi. Shi ko sadauki Affan, koda ya isa kofar gidan sarautar sai ya iske dandazon Dakarun cikin shigar yaki sai faman kai komo suk yi suna muzurai tamkar sa ci babu. Har ya kawo kofar shiga gidan ba wanda ya ce da shi kala bare a tsai da shi. Kai tsayc ya shige gidan inda ya iske sadaukai da barori sai faman sha'anin gaban su kawai suke yi bama wanda ya kulashi. Wannan ne yasa Affan ya cika da mamaki yana mai tunanin cewa shin ba Malam Basiru ya ce shiga gidan zai yi masa wahala ba to shi ya aka yi ya shiga gidan ba wanda ya ce da shi kala barc a tarcshi? Tunaninsa ya katsc ne lokacin da ya tsinci kanse tsamo-tsamo a cikin raga shi da dokinsa, kafin ya yi wani yunkuri tuni wasu Dakaru sun yi ca akansa sun yi masa kamun kazar kuku suka daurcshi tamau, can sai ga Raizu ya zo ya ce, "Ma za ku kaishi kurkuku kamar yadda gimbiya Shahriya ta umarta". Haka aka daukeshi aka kai kurkukun da ke cikin gidan Sarki aka daďdaureshi cikin sarka. 20 Hikaya Hamsin Basiru Aliyu Harande Ilaka ya kasance cikin kurkukun har dare ya yi yana hangen ana azabtar da wasu fursunoni amma shi ba a taba shi ba sai ma kokarin kula da shi kawai ake yi. Kansa sunkuyc yana tunanin wannan hali da ya shiga kawai sai yaji an turo kyauren dakin da yake an shigo. Koda ya duba sai ya yi arba da kyakkyawar fuskarta, tana cikin shigar kayan bacci masu shara-shara. Tun kafin ta iso ta jcfeshi da wani murmushi mai juyar da hankalin duk wani da namiji. Shi ko Affan lokacin ne wani bakin ciki da takaici ya yunkuro masa har ya wujijjiga sarkar da aka daureshi ko zai iya kwaccwa amma ina sai ma ji ya yi tamkar sarkar ta dada daureshi. Cikin tsananin fushi ya fara magana da cewa, "Shin wai ke mi ne kike so gareni ne? Na ce banda lokacinki

Chapter 1 of 3