gabansa.
A daren ranar da za su yi tafiyar ne, Waziri ya
kira su Bakar su goma. Bayan sun gaisa ne sai Waziris
ya dubesu ya ce, "Ku yi sani cewa ba komai ne ya sa
na taraku nan ba sai don in taimaka muku akan
wannan tafiya da za ku yi gobe. Taimakon kuwa shi
ne, ina so ne in turaku wajen wasu manya-manyan
Malaman hikaya wadanda duniya ta yarda da
kwarewarsu a sha'anin sanin hikayoyi. Ina mai
tabbatar muku da cewa idan kuka sadu da wadannan
Malaman hikaya zaku buge kowa a wannan gasa.
Abin da yasa na ce muku haka, na san duk wanda
ya lashe gasar daga cikinku wani ba zai yi bakin ciki
ba". Suka amsa da cewa, "Haka ne". Waziri ya ci gaba
da cewa, "Ku saurareni da kyau zan fara sanar da ku
sunan malaman hikayoyin da inda za ku riskesu.
Wadannan Malaman hikayoyin duk sun kasance
mabiya addinin Musulunci, kuma' suna nahiyar
Kasashen bakaken fata.
Malami na farko wani fasihin Malami ne mai
suna Abdullahi Ibni Mukhtar Al-Yaron Malam, wanda
shi babban malami nc masanin hikaya wanda ya yi
23
Hikaya Hamsin Basiru Harande
hikayar (Bajakadc). Ya kai Bakar wannan Malami shi
na ke so kaje garcshi. Daga wannan nahaiya tamu
zuwa nahiyarsu tafiya ce ta kwanaki ashirin ba cin
zango. Dan haka sai ka bada himma za ka je ka samu
abin da ka je bida ka dawo.
Malami na biyu shi ne Abdul-aziz Ibni Sani AlMadaks wanda shi ma babban Malami ne wanda ya yi
hikayar Kundin Tsatsuba. Zalum kai ne za ka je
wurinsa. Daga nan zuwa kasarsu tafiya ce ta kwana
bakwai. Sai malami na uku shi ne Rabi'u ibn Abukakar
Al-Sharfadi, wanda hikayoyinsa sun shahara a duniya,
cikinsu kuwa har da Hikayar Fairuzasshaha. Ina
tabbatar maka da cewa ko wannan hikaya ka koya ta
isa ta sa ka lashe wannan gasar. Da'uf kaine wanda za
ka je gareshi. Sai Malami na hudu, wani babban
Malami ne masanin hikaya mai suna Mukhtar Ibni Isah
Al-Kwalisa, wanda wanda ya yi hikayar Gimbiya
Zahrà. Itama wannan hikayar ta shahara sosai a
duniya. Shafir kai za ka je wurinsa. Malami na biyar
shi ne Shehu ibni Usman ibni Muhammad, wanda ya
yi hikayar Mazan Fama. Shima masani ne sosai.
Hamzi kaine wanda za ka ziyarceshi. Malami na shida
shi ne Mubarak Ibni Hamza Al-Gadon Kaya wanda ya
yi hikayar Jihadi, shia babban mai ilimi ne. Sagar kai
ne za ka je wurinsa. Malami na bakwai kuwa shi ne
Abubakar Ibni Tanko Al-lliyas, wanda ya yi hikayar
24
Hikaya Hamsin Basiru Harande
Bautar Bayi. Shiam masanin hikaya ne. Samar kaine
za ka je wajensa. Malami na takwas shi ne Umar Ibni
Lawan Al-Abdul wanda ya yi hikayar Jarmai Sha
Yaki. Shima masani ne sosai. Masul kai za ka je
wurinsa. Malami na tara shia ne Hassan Ibni Shu'aibu
Al-Harande, wanda ya yi wata kasaitacciyar hikiya,
wadda ake kira Dan Sarauta. Shima babban masani ne.
Gubur kai ne za ka je wurinsa. Malami na cikon
goman shi ne Abdul-Salam ibni Shitu Al-Bature,
wanda ya yi hikayar Gawurta, shima duniya ta sanshi.
Sakar kai nake so kaje wurinsa".
Waziri ya kare da cewa, "Na rantse da wuta da
zarar kuka isa wurin wadannan manyan masana
hikayoyin na duniya ba shakka sai daya daga cikinku
ya lashe wannan gasar. Sabo da haka daga yanzu na
gama daku, kowa tasa ta fishsheshi". Suka yi godiya
kowa ya watse.
A cikin daren ne kuma Waziri ya shiga laluben
hanyar da zai bi ya cutattama Affan. Duk da ko ko bai
san wurin Malamin da Affan din za shi ba.
Bayan wani dogon tunani da Waziri ya yi sai
kawai ya kyalkyale da wata irin dariyar mugunta, sabo
da ya samu hanyar da zai kau da Affan cikin sauki.
Nan da nan yasa aka yi masa kiran Affan. Bayan
Affan ya shigo cikin turakar da yake zaunc ya gaishe
shi, sai Waziri ya dubeshi ya ce, "Ya kai Affan na
25
Hikaya Hamsin Basiru Harande
kiraka ne sabo da in taimakeka akan wannan gasa ta
HAKAYA HAMSIN, sabo da na ga duk cikinku ka
fisu hankali da nutsuwa. Taimakon kuwa shi ne, zan
turaka wurin wani Malami masanin hikayoyi. Wannan
malami sunansa Basiru Ibni Aliyu Al-Harande. Kuma
yana Zaune ne a nahiyar kasashen bakaken fata
ma'abota addinin Musulunci a wani birni mai suna
Zururi. Daga nan zuwa birnin tafiyar kwanaki goma
ce. Ba shakka idan kaje wurinsa zai koyar da kai
dadadan hikayoyi wadanda za su kai ka ga lashe
wannan gasa. Amma ina so wannan magana da mukai
tsakanin ni da kai ta zamo sirri kada ka sanar da wani a
cikin 'yan uwanka har ya rigaka zuwa wajen wannan
masanin hikayoyi ya lashe gasar".
Koda Affan yaji haka sai mamaki ya kamashi
sabo da ya san dai Waziri ba kaunarsa yake ba, amma
kuma sai ya yi tunanin ko Waziri ya canja halinsa ne.
Cikin murmushi Affan ya yi godiya, sannan ya
cc, "Na yi alkawari ba zan afdawa kaowa ba. Kuma
komai wuya zan je birnin Zururi dan saduwa da
wannan ma'abocin hikayoyi." Daga nan Affan ya mike
ya shige cikin gida.
Affan na shigewa Waziri Kwabis ya rinka
kyalkyala wata irin dariyar mugunta, sabo da ya san ya
tura Affan wurin Malamin da bai da wata kwarcwa ta
fuskar sanin hikayoyi. Kuma ya san ba abin da zai iya
26
Hikaya Hamsin Basiru Harande
koyawa Affan sai shirme kawai, sabo da ko shi bai
kware ba barc ya koyar da wani. Kai hasalima bai taba
rubuta wata shahararriyar hikaya ba bare duniya ta
sanshi. Wannan shai ne yasa. Waziri ya yi ta. murna
don yana tunanin ya gama da A ffan.
Gari na waycwa Affan ya gama shirinsa tsaf yaje
ya sallami mahaifiyarsa Zawira, tayi mai fatan samun
nasara.
Yana fitowa ya kama dokinsa ya hau ya yi masa
kaimi ya bi sahun 'yan uwansa wadanda tuni wasu sun
yi nisa a daji.
Haka yarima Affan ya yi ta tafiya cikin daji yana
keta kwazazzabai, koramu da duhuwowi. Kai akan
sauri ko zango bai tsayawa ci. Bai gushe ba yana
wannan tafiyar ba sai da ya kwashe kwanaki goma cіcif, kuma bai hadu da wani abin tsoro ba.
A rana ta goma ne yana cikin tafiya saiai ya hango wata
irin ganuwa mai tsananin tsawo. Nan da nan Affan ya
yi wa dokinsa kaimi domin cimma ganuwar. Yana isa
kofar ganuwar sai ya ga an rubuta 'BIRNIN ZURURI'
cikin manyan harrufa. Wannan ne yasa Affan ya gano
cewa ya iso birnin da malamin da zai sanar da shi
hikayoyi yakc. Murna ta kamashi sabo da ganin ya
kusa cimma burinsa.
Lokacin da Affan ya shiga cikin kasar Zururi sai
ya kasancc cikin mamakin ganin garin yadda bai zata
27
Hikaya Hamsin Basiru Harande
ba, ya ga manyan ginc-ginc kawatattu, ga yawan
al'umma, ga ya komi na garin cikin tsari yake. Haka
dai ya ci gaba da mamakin ganin birnin Zururu kamar
an tsaga kara da birninsu na Mahbub.
Su kuwa jama'ar birnin duk inda Affan ya bi sai
kallonsa kawai suke sabo da basu taba ganin
kyakkyawan balaraben mutum kamarsa ba.
Musamman ma matan birnin, wadanda sun fi sa masa
ido.
Koda Affan ya ga rana ta tassama yamma, sai ya
fara tambayar mutanen birnin gidan Malam Basiru
Ibni Aliyu Al-Harande. Amma duk wanda ya tambaya
sai ya ce bai sanshi ba. Saboda dama ba wani sannane
bane.
Haka dai ya yi ta tambaya wuri-wuri, sai da ya
tambayi sama da wuri ashirin amma bai dace ba. Haka
ya yi ta aywo cikin garin har ya tsige boni.
A cikin yawonsa ne yabi wata hanya inda ya iske
cincirindon mutane sun yi da'ira suna shewa, da gani
kasan wani abu suke kallo. Nan da nan Affan ya doshi
wurin domin ganin irin wainar da ake toyawa. Yana
isa sai ya ga wasu mutane ne daddaure cikin śarkoki
gabansu kuwa wani basamuden kato ne rike da takobi
tsirara, gefensu kuwa wani mutum ne cikin kayan
Sarki. Da ganinsa ka san yana da mutunci a garin.
Mutumin ya fara magana cikin kakkarfar murya
28
Hikaya Hamsin Basiru Harande
da cewa, "Ya ku mutanen birnin Zururi, kuyi sani
cewa wadannan mutanc sun kasance daga cikin
masoyan mai girma gimbiya Shahriya, kuma suna
daga cikin wadanda suka shiga gasar neman aurenta."
Mutumin ya ci gaba da cewa, "Dama kun san
cewa duk wanda ya shiga wannan gasar an bashi
sharadin cewa idan bai ci gasar ba za a kashe shi?
Sabo da haka wadannan mutane ba su yi nasara ba,
kuma shi yasa gimbiya ta bamu damar kashesu. Kuma
yanzu zamu kashe su domin cika umarninta."
Mutumin na kawowa nan a zancensa sai ya bawa
Hauni umarni ya cika aikinsa. Haunin ya gabata garesu
ya daga takobinsa ya sare kan dayan. Koda dayan ya
ga haka sai hankalinsa ya tashi ya rika kuka yana
kucce-kucce.
Da yake Affan ya kasance mutum ne mai tausayi
sai abin ya bata masa rai, har ya kai shi ga zubda
kwalla.
Lokacin da Affana ya ga hauni ya daga takobinsa
zai sake sare kan na biyun, sai ya ga ba zai iya bari ayi
hakan ba sabo da tausayi. Cikin tsananin zafin nama ya
baiyana a gaban haunin ya tunkudeshi. Hakan yasa
saran da haunin ya kawo ya sari iska.
Wannan lamari ba karamin mamaki ya baiwa duk
ilahirin mutanen da ke wajen ba, saboda tun da suke ba
a taba zuwa kashe wani ba wani yazi ya kareshi sai
29
yau.
Hikaya Hamsin, Basiru Harande
Cikin fushi mutumin da ya sa hauni aikinsa mai
suna Raizu ya ce, "Ya kai wannan bakon saurayi shin
kai wane daga cikin tsageran duniya da za ka hanamu
cika umarnin shugabarmu? Ko kana son fushinta ya
tabbata a kanka?"
Koda Affan yaji haka sai ya ce. "Ni bako ne,
kuma ba wai na hanaku cika umarnin shugabarku
bane, sai dai tausayin wannan mutumin da ake shirin
kashewa ne ya kamani, wannan yasa na ga zan iya
sadaukar da rayuwata domin in kubutar da tasa. Sabo
da haka na umarceku da ku fada min gasar da ya gaza
ci ni zanyi, idan na samu nasara sai ku sakeshi ya tafi,
idan kuma ban samu ba sai ku zartar da hukuncin a
kaina a madadinsa".
Koda Raizu yaji haka sai ya yi murmushi ya ce,
"Ya kai wannan bakon saurayi ma'abocin shisshigi,
shawarar da zan baka ita ce kada ka sa kanka a cikin
wannan lamari, domin ba shakka ba za ka ci nasara
akan gasar ba, sabo da haka ka kubutar da wannan
kyakkyawar halitta taka kayi tafiyarka".
"Koda Affau yaji haka sai ya ce, "Kayi sani cewa
ni na sa kaina a wannan lamari, saboda haka na
umarceka da kaje ka shaidawa Sarkinku ko ita
gimbiyar, idan sun amince zan yi komai rintsi da
tsanani".
30
Hikaya Hamsin Basiru Harande
Koda Raizu yaji haka sai ya ce, "To shi ke nan,
wanda baiji bari ba zai ji hoho! Abind a nake so da kai
shi ne, kazo muje wurin Sarki kayi bayani da kanka".
Lokacin da Raizu ya kai Affan wurin Sarkinsu
mai suna Fakihu sai ya kwashe labarin duk yadda suka
yi da shi ya sanar da Sarkin. Koda Sarkin yaji haka zai
ya yiwa yarima Affan duban nutsuwa, ya ce, "Ya kai
wannan bakon Sadauki, kayi sani cewa masu hasashe
sun tabbatar da cewa duk fadin duniya ba mace mai
kyau da cikar zati kamar 'yata gimbiya Shahriya.
Wannan ne yasa masoya suka yi ma ta ca. Koda na ga
haka sai na bukaceta da ta fitar da wanda take so
domin in yi ma ta aure, amma sai ta ce ba wanda take
so sai wanda ya shiga rijiyar da ke tsakiyar garinnan ya
kashe wani tsohon kwado wanda ke hana mutane
dcibar ruwan cikin rijiyar sai sati-sati kawai. Kuma shi
wannan kwado ya dade a cikin rijiyar, kuma ya
hallaka manyan bokaye da manyan Sadauki sama da
dari-dari". Sarki Fakihu ya ci gaba da cewa, "Lokacin
da gimbiya tayi wannan shawarar sai wasu daga cikin
masoyanta suka ce ba za su iya ba, sun janye, wasu
kuwa suka ce sunji sun gani. Koda taga haka sai ta се,
"Duk wanda ya shiga rijiyar yaji tsoro ya fito ba
shakka za a kashe shi". Suka ce "Sun amince". Sarki
ya kare da cewa, "Wannan yaron da ka gani yana daya
daga cikin wadanda suka shiga rijiyar suka ji tsoro
31
Hikaya Hamsin Basiru Harande
suka fito, shi yasa abasu halaka ba. Amma sauran da
suka shiga duk sun halaka. Kaji wannan shi ne dalilin
sanyawa a hallakasu".
Koda Sarki ya kawo dai-dai nan a zancensa sai
abin Affan ya ce, "To idan kun amince ni zan shiga
rijiyar in kashe kwadon sai aba wannan Sadaukin
auren gimbiya. Idan kwadon ya hallakani kuwa shi ke
nan na fanshi jininsa".
Koda Sarki yaji haka sai ya yi murmushi ya ce,
"Ya kai wannan sadauki kar ka jefa wannan
kyakkyawar siffa taka cikin bala'i, gwara kayi
tafiyarka, ko ka more kyawunka". Affan ya ce, "Shi
yaji ya gani".
Koda Sarki ya ga alamar bashi da niyyar bari sai
ya ce, "To yanzu ka ga rana tana gab da faduwa, sabo
da haka zamu baka wuri ka kwana gobe zamu kaika
bakin rijiyar ka shiga. Amma idan ka tsorata ka fito ba
shakka sai mun kasheka". Affan ya ce, "Na amince da
hakan".
Gari na wayewa Sarki yasa aka yi shela. Aiko nan
da nan jama'a suka yi cincirindo a bakin rijiyar domin
kaseh kwarkwatar ido. In kayi duba saman wani
mumbari za ka ga Sarki Fakihu da sauran
mukarrabansa zaune saman kujeru na kasaita. Gefensa
kuwa gimbiya Shahriya ce zaune saman kujera cikin
wata shiga irin ta kasaita sai sheki take tamkar rana ya
32
Hikaya Hamsin Basiru Harande
yin da tayi tsaka. A gaskiya hankali, tunani, nutsuwa
ba za su iya misalta irin tsabagen kyau da cikar zatin
da Allah ya yi ma ta ba, sabo da duk da namijin da ya
yi arba da fuskarta ba zai sake son kallon wata 'ya
mace ba a duniya.
Raizu ne ya mike ya fara magana da cewa, "Ya
ku jama'ar kasar Zururi da yake dai kowa ya riga ya
san abin da ya sake taramu bakin wannan rijiyar.. Ba
tare da 6ata lokaci ba muna bukatar wannan bakon
Sadaukin ya fito domin cika alkawarinsa na shiga,wannan rijiyar".
Koda Jama'a suka ji haka sai kow aya nutsu yana
sauraren fitowarsa.
Ana cikin haka ne sai gashi ya faso taro ya fito,
ya tsaya bakin rijiyar. Tsananin kayu da kwarjininsa
tare da cikar zatinsa yasa duk jama'a suka yi shiru suna
kallonsa, daga shi sai dogon wanda na fatar damisa, ga
alamubn karfi na baiyane a jikinsa. Hannunsa rike
yake da takobi tsiraraa kugunsa kuwa akwai igiya ta
kai kamu dari. Sadauki Affan ya fara magana da cewa,
"Ya mutanen kasar Zururi kuyi sani cewa ni bako ne,
kuma na shiga wannan gasa ne ba don ina daga cikin
masu neman auren gimbiya ba, a'a sai don in ceci!rayuwar wani wanda tausayinsa ya kamani, sannan
idan na ci nasara ba shakka gimbiya za ta zama
mallakin wannan jarumi da zan canja".
33
Hikaya Hamsin Basiru Harande
Ita ko gimbiya Shahriya tunda ta kyalla ido ta ga
Sadauki Affan sai tsananin kyau da kwarjininsa suka
daki zuciyarta, ta kura mai ido zuciyarta ta rinka
bugawa: Nan da nan ta fara maganar zuci da cewa,
"Ashe a duniya akwai da namiji mai kyau kamar
wannan? Amma da na sani da ban ce sai an yi gasar
neman aurena ba, da sai dai in shiga gasar neman
wannan sadaukin ya aureni".
Tana cikin haka ne sai ta ga Sadauki Affan ya yi
alkafura ya fada cikin rijiyar. Hankalinta ya tashi, ta
shiga wasi-wasin ko zai fito ko zai halaka a ciki?
Amma ta san idan matukar ya hallaka a ciki ba shakka
itama za ta hallaka, saboda tuni kaunarsa ta raunata
zuciyarta, kuma ta yanke cewa ko bai ci wannan gasar
ba shi za ta aura.
Jarumi Kasim shi ne wanda Affan ke wannan
fafafutuka sabo da kubutar da rayuwarsa. Shima haka
ya kasance cikin wannan wasi-wasi ko Affan zai samu
nasara ko zai ji tsoro ya fito a kashesu gaba daya, sabo
da ya san bala'in da ke rijiyar.
Bayan sa'a biyu da shigar Affan rijiyar sai aka
rinka jin wani irin gurnani, ruwan rijiyar suka rika
hautsinawa.
Ana cikin haka ne sai kasar wurin ta fara girgiza
tamkar za ta tsage. Hankalin jama'a ya dugunzuma,
musamman gimbiya Shahriya wadda tuni ta fara kukan
34
Hikaya Hamsin Basiru Harande
zuci sabo da rashin sanin halin da masoyinta ke ciki.
Ana cikin haka ne sai aka ga ruwan cikin rijiyar
ya yo tsiri zuwa wajen rijiyar samansa jini ne a malale
tare da wani 6angare na jikin dogon wandon da ke
jikin Affan. Hakan shi ya dugunzuma hankalin jama'ar
gari, kowa jikinsa ya yi sanyi. Gimbiya Shahriya ta
rintse ido tare da kwalla kara tayi kasa ta fadi
sumammiya domin ta baiwa kanta tabbacin tabbas
wannan bakon saurayi da ta kamu da kaunarsa ya
hallaka. Jikin dubban jama'ar da ke wajen gaba daya
ya yi sanyi.
Nima ajiye birona nayi ina jimamin faruwar
wannan lamari.
INA LABARIN 'YAN UWAN YARIMА
AFFAN WADANDA SUKA NUFI
SHAHARARRUN MALAMAI MASANA
HIKAYOYI?
A CIKINSU WAYE ZAI SAMU NASARAR
ZAMA SARKIN BIRNIN MAHBUB?
A WANNE HALI ZAWIRA MAHAIFIYAR
AFFAN DA KISHIYOYINTA KE CIKІ?
SHIN AFFAN YA HALLAKA NE KO KUWA
YANA RAYE?
YA YA RAYUWAR GIMBIYA SHAHRIYA
ZA TA KASANCE TUN DA BAKON SAURAYIN
DA TA KAMU DÅ KAUNARSA YA HALLAKAА
35
Hikaya Hamsin
CIKIN RIJIYA?
Basiru Harande
Ba a shiga komai a cikin labarin ba, yanzu aka
fara.
Mu hadu a littafin HIKAYA HAMSIN kashi na
biyu dan jin ci gaban wannan kayataccen labari.
Mai debe muku kewa, da fatan nishadantar da ku,
BASIRU ALIYU HARANDE
(ZURU) 08087325348-07066006764.
Don Allah ina neman shawarwarinku ko
gyarrarrakinku akan wannan littafi, dan adam ne ni
ajizi ba abin mamaki bane aga tarin kura-kurai.
Littattafan Marubucin:
Hikaya Hamsin
Bakar Damara
Rundunar Daukar Fansa
Makomata
Harbin zuma
Hucin zuciya
Kulli
Duk daga taskar,
BASHIR ALIYU HARANDE
ZURU
36
Hikaya Hamsin Basiru Harande
Albishirinku Makaranta littattafan Yaki? Ku
ce min goro. G
awurtaccen shahararren matashin marubucin nan,
wanda tauraruwarsa ta fara haske a sararin samaniya,
marubucin Azabtarwa, Gasar Ajali, Izaya, Gawurta, Fargabar Bayi, ya kara gwangwajewa, ya baje basirarsa, ya tsara ya shirya, ya rubuta kasaitaccen littafi daya tamkar da dubu, mai
suna 'HALAKA! HALAKA!! HALAKA!!!" Labari ne kasaitacce kayatacce, wanda ya zamo bakandamiya a cikin littattafan yaki da suka taba wanzuwa a duniya. Babban abin farin ciki kuma shi
ne, wannan littafi babba ne, ma'ana mai yawan shafuka. Káma guda daya-ne jal. Haka zalika akwai babbar garabasa a cikin littafin, ma'ana akwai gagarumar Gasa da aka sanya a cikin littafi domin auna fahimtar makaranta.
Littafin Halaka, littafi ne mai dauke da labari mai tsananin kayatarwa, kama daga jarumtaka, soyayya, tsafi, al'ajab da kuma rikitarwa.
Abdul-Salam 'Adam Shitu Bature G/Kaya, ba baya bane wajen tsara kayattattun labari ga duk wani ma'abocin karanta littafi ya san yanda yake tsara littafansa cikin tsari da salo mai Kayatarwa.
Dole a jinjinawa wannan matshin hazikin fasihin marubuci bisa yanda ya baje hikimarsa ya rubuta wannan littafi, kuma ya kayata aikinsa da aikin mai kyau, kama daga kayataccen bango mai santsi, da hoto mai matukar kyau, farar takarda karanta ka barwa jikokinka tare da tsararrren rubutu kamar a Ingila. Kai dai nemi wannan littafi da zarar va fito. Tuna da sunansa, "Halaka! Halaka!! Halaka!!!"
Yana nan tafe!
37
Hikaya Hamsin Basiru Harande
KARANTA WANNAN
K
oda Gimbiya Umla taji haka sai ta dubi Sarki ta се,
"Ya kai Abbana shin ka manta da alkawarin da na
daukarwa kaina cewa ba zan taba son wani da namiji
ba bare har in aurcshi? Kai! ni ina ganin ma So karya ne! In ko
ba karya bane me yasa har yanzu ban ji son wani da namiji ya
shigeni ba? Sabo da haka ya Abbana ina so duk wanda ya kara
cewa yana sona kasa a kamashi a kulleshi a cikin kurkukun duhu
ayi ta gana masa nau'ikan azabobi har kala dari tara da casa'in da
tara, har sai ya mutu sabo da tsananin ukuba. Matukar ka yi
hakan na tabbata kai mai kaunata ne, idan kuwa ba ka aikata
hakan ba lallai kai makiyi ne a gareni. Kuma na rantse da
darajar karagar mulkinka sai na kashe kaina!!".
Koda Sarki yaji haka sai ya yi murmushi ya ce, "Ya ke
'yata, ba wai na mance da wannan alkawari da kika ďaukarwa
kanki bane, sai dai ina ganin har yanzu kuruciya na cinki. Kuma
ita kalmar "So" da kika ji ana ambata har kike karyatata, wata
shu'umar kalmace mai shammatar zuciya, wadda babu wata
halitta da ke rayc a ban kasa da zai ce ya san lokacin da take
shammatarsa ta shigeshi ba. Ina tabbatar miki da cewa matukar
baki bi a sannu ba, kin hanu ga aibata kalmar So da karyatata, sai
kin tsinto zuciyarki a cikin kuncin matsanaiciyar soyayya mai
wajigarwa....Ki tsinto kanki a cikin yanayin kaskantar da kai ga
wanda kika kamu da soyayyarsa, ya yin da shi kuma zai nuna
halin ko-in-kula a garcki....Lallai zuciyarki za ta yi soyayyar da
ba a taba yin irinta ba a tarihin duniya..."
Wannan kadan ke nan daga cikin littafin RUNDUNAR
DAUKAR FANSA, wanda ke tafe nan ba da jimawa ba. Daga
Taskar,
Basiru Aliyu Harande.
38
bnsa6H inias8
Hikaya Hamsin
nlzmeH Gужн
Baslru Harande
TRY ABANIEW E ab B 18W srinis gts 7628M
adabbs ab sinc
sy sanads IS
Kadan daga littafin
Kwan Sihiri
ATEW E 8182
em my t
СTES PIaloQ Labari ne akan wata yar Sarki, Ita wannan "yar Sarki
kyakkyawa ce ta gaban kwatance, domin har wasu na ganim
ccwa ba mutum bace aljana ce ke siffantuwa da siffar mutane,
sabo da tsananin tsabagen tsubin kyawunta. Kyawu ne da
idanuwa basu taba ganin koda kwatankwacinsa ba. Kyawu ne da
ke saurin fuskar zukata izuwa ga shagaltuwa da kaunar
ma'abociyar kyawun. Hakan yasa labarin kyanta ya watsu a
lardinan duniya. Fatake suka rinka yadashi ga manyan dauloli da
manyan Sarakuna da Attajirai, bokaye suka ringa kwadaitawa
'ya'yansu da 'ya'yayen isassun Sarakuna.
Sai dai kash! Duk da tsananin wannan kyawu na ban
mamaki da wannan 'yar Sarki ke da shi, tana da wata lalura mai
abin mamaki, lalurar da manyan bokaye da masana magunguna
suka gaza gano takamaimai wacce irin cuta ce. Ta kai cewa
wannan 'yar Sarki ko kofar dakinta bata iya zuwa sabo da
tsananin lalurar, An yi magani da tsatsube-tsatsuben, amma abin
ya ci tura.
Ana cikin wannan yanayi ne wani ani shahararren boka ya
baiyana daga wata nahiya daga cikin nahiyoyn da suke wanze a
duniya da labarin hanyar da za a bi a samu maganin da zai
warkar da wannan lalura ta wannan kyakkyawar 'yar Sarki.
Hanyar kuwa ita ce, sai an je wani kungurmin bakin daji
mai dauke da miyagun hadarurruka, an dauko wani katafaren
Kwai wanda ake kiransa da suna 'KWAN SIHIRI'.
Wannan KWAN SIHIRI yana bangon duniya barin
yamma karkashin tsaron wadansu miyagun maridan aljanu
wadanda tsafi da kaifi baya tasiri a kansu. Ba su san komai ba
39
Hikaya Hamsin Basiru Harande
face hallakar da bakuwar halittar da ta ziyarci nahiyar da suke.
Matukar aka samo wannan Kwai aka dafawa wannan 'yar
Sarki ta ci za ta warke daga wannan muguwar cuta da ke addabar
rayuwarta".
Ya yin da mahaifinta yaji wannan batu sai hankalinsa ya
dugunzuma, har sai da ya zubar da hawaye, domin yana ganin
cewa babu wata halitta da za ta iya dauko wannan kwai. Yana
cikin halin tsananin bakin ciki wannan boka da ya kawo labarin
Kwan ya shawarceshi da cewa ya tura sadaukan kasarsa ya turasu
dauko wannan Kwai, idan aka taki sa'a sai wani daga cikinsu ya
SAI nasara.
Nan take ya tarasu ya sanar da su bukatarsa, tare da yi
musu alkawarin duk wanda ya dauko wannan kwan sihiri za a
aura masa wanann 'yar Sarki tare da raba kasarsa biyu ya bashi
rabi ya mulka.
Runduna guda ce tayi gagarumin shiri ta nufi bangon
duniya dauko wannan kwai. Gaba dayansu sun rasa rayukansu,
da kyar da sidin goshi wani matashin jarumi mai karancin
shekaru ya sau pasarar dauko wannan kwai bayan ya rasa
raytuwarsa, ya samu nasarar tsira da miyagun raunika. Ya yin da
ya kawo wannan Kwai aka dafawa wannan 'yar Sarki ta ci, sai ta
mike tamkar ma bata taba yin wata lalura ba. Wani babban abin
aľajabi shi ne, irin tsananin kiyayyar da wannan 'yar Sarki ta
nuna ga wannan jarumi da ya sai da rayuwarsa ya dauko wannan
Kwai....
Dan jin yadda za ta kasance, nemi wannan Kayataccen littafi mai
suna 'KWAN SIHIRI da yake gab da fitowa. Yana dauke da
labari mai tsananin nishadantarwa da ban al'ajabi.
Daga,
Hassan Shu'afbu Harande.
40
AKARA CITY
BOOKSHOP
LITTATTAFAN MARUBUCIN
HIKAYA HAMSIN
RUNDUNAR DAUKAR FANSA
FARMAKIN
ABOKAN GABА
KOGON HALAКА
ABDULSALAM ADAM SHI
(BATURE) G/KAYA
A.A.
ABDULSALAM ADAM SHITU (BATURE) G/KAYA
BATURE PUBLISHERS
G/KAYA KANO
07041591141 08162707231, 08124173211
Cover illustration: Anka-Graphics Fagge. 07030319787
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking