An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
HIKAYA HAWSINBASIRU ALIYU HARANDE ZURU
Hikaya Hamsin Basiru Harande
HIKAYA HAMSIN-1
A da can bayan wani zamani mai tsawo da ya
shude, an yi wata kasa ca yankin larbawa
mai suna Mahbub. Kasa Mahbub ta kasance
babbar kasa ce mai yawan al'umma da tarin dukiya tare da
manyan ginc-gine wadanda suka sa kasar ta shiga cikin
manyan kasashen da suka shahara wurin kyau da
Kawatuwa a wannan zamani.
Sarki Gulam shi ne Sarkin kasar Mahbub, kuma ya
kasance Sarki ne mai tsananin adalci ga al'ummar kasarsa,
ba abin da Sarki ya sama gaba sai tabbatar da adalci
tsakanin al'ummarsa. Wannan ne ya sa jama'ara kasarsa ke
matukar sonsa tare da biyayya gareshi.
a
Sarki Gulam ya kasance yana da matan aure hamsin,
kuma kowacce daga cikinsu ta kasance ba baiwa bace 'ya
ce a wurin wani babban Sarki ko wani attajiri. Sai daya
daga cikinsu wadda ya taba ribatowa a wurin yaki. Ita dai
wannan baiwar sunanta Zawira. Ta kasance baiwa ce amma
Sarki Gulam yafi sonta daga cikin matansa. Sabo da Zawira
ta kasance mace ce mai gaskiya da rikon amana ga tausayi
da son taimakawa talaka. Ga uwa uba kyakkyawa ce ta gani
ta fada. Wadannan abubuwa ne yasa Sarki Gulam ya fi
sonta kuma yake yawan neman shawararta a duk lamarin
da ya kuduri aiwatarwa.
Wannan nc yasa sauran matan Sarki arba'in da tafa
suke tsananin kishinta tarc da tsangwamarta. Kuma suna yi
ma ta gorin cewa kowa daga cikinsu tana da asali amma
ban da ita, sbao da ita kammar baiwace. Ba a san asalinta
6
Hikaya Hamsin Basiru Marnde
ba. Da yake Zawira ta kasance mai hakuri ce ko taji
suna maganganunsu sai dai tayi murmushi ta wuce.
Da yake ance mutum tara ne bai cika goma ba,
wata rana matan Sarki suka taru suka rinka jifar
Zawira da munanan kalamai na 6atanci. Tun Zawira na
kannewa har ta gaza hakuri ta mayar musu da martani.
Abin da yasa suka taru suka yi ma ta dukan tsiya suka
barta kwance. Koda labari ya iske Sarki sai ya shigo
gida cikin sauri ya zo ya iske Zawira cikin dakinta
kwance tana jinya. Bayan ya zauna kusa da ita sai ya
dubeta cikin sanyin jiki ya ce, "Ya ke matata kiyi sani
cewa duk abin da ya faru tsakaninki da abokan
zamanki ina sane, kuma abin da na ke so da ke shi ne,
ki ci gaba da hakuri kamar yadda kika saba. Me hakuri
shi kan dafa dutse, kuma da sannu za ki ga nasara cikin
lamuranki." Sarki Gulam na kawowa nan a zancensa
sai ya sumbaci goshinta sanann ya fice.
* * *
Waziri Kwabis shi ne Wazirin Sarki Gulam,
kuma ya kasance dan uwa ne na jini ga Sarki, amma
sai dai Waziri Kwabis ya kasancc mutum mai son abin
duniya da sona gadara da girman kai. Kuma mutum ne
mai kokarin ba Sarki shawarwarin shimfida mulkin
kama karya da cin zarafin talakawa.
Lokacin da Sarki ya fuskanci hali da irin manufar
7
Hikaya Hamsin Basiru Harande
Waziri Kwabis sai gaba daya ya daina neman
shawararsa ta fannin mulki, sai ya koma neman
shawarar Zawira.
Waziri Kwabis ya kasance Waziri ne kawai,
amma Sarki bai neman shawararsa. Wannan lamari
ashe ba karamin yima Waziri Kwabis ciwo ya yi ba.
Ganin cewa gashi namiji kuma kullum shi ne a fada
amma ace Sarki sai ya shiga gida ya nemo shawarar
mace. Ko Cikin matan ma baiwa, to mene ne
amfaninsa ke nan? Wannan ne yasa shima Waziri
shiga cikin jerin masu bakin ciki da Zawira tare da
neman hanyar da zai yi maganinta.
Ana cikin haka ne sai matan Sarki gaba daya
suka samu juna biyu, wato ciki. Cikinsu har da Zawira.
Lamarin da ya sa Sarki Gulam cikin tsananin farin ciki
da bai misaltuwa ganin matansa hamsin sun sami ciki
lokaci guda. Kuma yana ganin za su haihu lokaci guda.
Haka dai matan Sarki suka ci gaba da renon
cikinsu cikin kwanciyar hankali amma banda Zawira,
domin ita kullum sai tayi kuka sabo da irin kalaman da
kishiyoyinta ke fada mata. Kai hara ce ma ta suke yi
cikinta ba na Sarki bane cikin kasuwa ne. Amma da
yake Sarki na sonta sai ya rinka kwantar ma ta da
hankali. Da haka har cikin matan Sarki ya isa haihuwa.
Wata rana Sarki na zaunc ana fadanci sai ga
Jakadiya ta shigo tana guda tana cewa, "Yau ranar
8
Hikaya Hamsin. Basiru Harande
1
farin ciki, matar Sarki ta farko ta sauka lafiya."
Koda Sarki yaji haka sai murna ta kamashi, tun
kafin ya gama murnar na farko sai ga albishir na biyu
cewa wata ta kara haihuwa. Ana cikin haka sai ga na
uku da na huďu lokaci daya. Kai haka dai aka tafiyar
da wannan ranar ba a yi fadanci ba domin kuwa a
ranar fada ta koma tambar wani asibitin haihuwa sabo
da duk inda ka duba jarirai ne. Sai da aka kawowa
Sarki Gulam 'ya'yansa su arba'in da tara dukkansu
maza wadanda aka haifa rana daya.
Koda aka gama kawowa Sarki jinjiran baiji ance
ga dan Zawira ba, sai ya tambaya ya ce, "Shin ina dan
da Zawira ta haifa ne?".
Koda Waziri Kwabis yaji haka sai ya ce, "Ya
shugabana dama tuni na shaida ma cewa cikin Zawira
ba naka bane domin tuni bokana ya shaida mani cewa
matanka za su haihu rana daya lokaci daya, duk wadda
bata haihu a cikinsu ba to ba shakka cikin ba naka
bane. Sabo da haka ka gasgata maganata ka dauki
tsattsauran mataki akanta..."
Cikin tsawa Sarki Gulam ya katse shi da cewa, "Kai
Kwabis, na san matata kuma na san halinta ba za ta
taba cin amanata ba, sabo da haka karya bokanka ya
fada maka. Kuma idan gaskiya ne bokanka yake to ya
zo ya sameni".
Sarki na kawowa nan a zancensa sai ya juya ya
9
Hikaya Hamsin Basiru Harande
shige gida ya bar Waziri Kwabis nan yana jimamin
Karyar da ya shara bata yi ba.
Haka dai Sarki da al'ummar kasar Mahbub suka
kasance cikin murna tare da kawata garin domin bikin
murnar suna. Mako na zagayowa aka barke da murnar
bayan Sarki ya radawa 'ya'yansa suna su arba'in da
tara. Duk inda ka duba makada ne da mawaka tare da
masu bushe-bushe. Abinci kuwa wurin ba a magana
domin sai da aka rasa inda za a sa shi. Sarki kuwa ya
kasance cikin farantama tallakawan kasarsa rai ta
hanyar raba musu dukiya, tufafi, dabbobi da sauransu.
Sai da aka shafe kwanaki bakwai ana wannan shagali
sannan kowa ya watse ya koma inda ya fito.
Ita ko Zawira sai ta kasance cikin tsananin tashin
hankali sabo da ganin duk kishiyoyinta sun haihu
amma ita ba ta haihu ba. Kuma gashi dama ana cewa
cikin ta bana Sarki bane. Nan da nan ta shiga tunanin
shin wannan tsaikon da ta samu bai sa Sarki ya yi
zargin kazafin da ake yi mata gaskiya ne? Amma duk
lokacin da ta tuna irin so da yardar da ke tsakaninsu da
Sarki sai hankalinta ya dan kwanta.
Haka shima Sarki abin ya dameshi, domin tun
lokacin da matansa suka samu ciki yafi kaguwa ya ga
dan Zawira bisa dana kwance, amma gashi kowaccе
matarsa ta haihu banda Zawira.
Sai da aka yi kwana hamsin dai-dai da haihuwar
ΙΟ
Hikaya Hamsin Basiru Harande
matan Sarki sannan Zawira ta haifi santalelen danta.
Sarki ya kasance cikin tsananin farin ciki sabo da
ganin 'ya'yansa sun cika hamsin, kuma dan Zawira ya
kasance kyakkyawa wanda baki bai iya bayanin
kyawunsa gaba daya. Gaba daya 'ya'yan da Sarki ya
haifa sai dai su biyo bayansa fagen kyau. Wannan ne
yasa masu zuwa barka suke cewa ko dai wannan yaron
aljani ne? In ka dauke Sark da ita Zawira da wasu
tsirarun kuyanginta duk gidan ba wanda ya yi murna
da wannan haihuwa, kowa ka gani fuskarsa murtute
take, musamman Waziri Kwabis wanda bakin ciki
yasa ya rasa inda zai sa kam don ya san an haifi
yaron da Sarki zai fi so fiye da komai a duniya.
Mako na zagayowa aka radawa yaro suna Affan.
da yake dama ba wani farin ciki ake yi da haihuwar
yarin ba shi yasa ba a yi wani shagalin biki ba.
Lokacin da 'ya'yan Sarki suka kai shekaru gomagoma, sai Affan ya kasance tamkar farin wata a cikin
taurari cikin yaran. Sabo da yafi su kyau nesa ba kusa
ba, ya fisu kwarjini ga fara'a, bai da girman kai, sannan
ba ruwansa da mai kudi da talaka, duk daya nc a
wurinsa. Idan aka dawo maganar jarumtaka, wato abun
sai dai ayi shiru, sabo da duk matashin da ke Kasar
Mahbub tsoronsa yake a fagen fama. Kai har mai
koyar da shi dabarun yaki ya fara tsorata da lamarin Affan.
Hikaya Hamsin Baslru Harande
Wadannan halaiye na Affan yasa jama'ar garin ke
matukar kaunarsa, yara da manya, maza da mata kowa
sonsa yake. Kai har wasu na cewa "Kai za ka gaji
ubanka".
Su ko sauran 'yan uwansa sun kasance yara ne
'masu tsananin girman kai da son nuna su 'ya'yan
sarauta ne ga wulakanta talakawa da cin zarafinsu. Kai
ba don Sarki na hana musu yin yadda suke so ba da sai
sun ce mutane su kwanta su rika takinsu suna tafiya
samansu. Wadannan halayya anasu ne ya sa Sarki ya fi
son Affan sabo da ya bambanta da su.
Lokacin da suka kai shekaru ashirin, kowannensu
ya mallaki hankalin kansa, kuma kowa ya kawo karfi
cikinsu. Sadauki Affan ya cika sadauki mai tsananin
karfin damtse da sanin dabarun yaki ya zamo duk
sadaukin da ke wannan yanki tsoronsa yake a fagen
fama. Kyawu da kwarjininsa suka kara baiyana.
Jama'ar kasar kuwa sai kara sonsa suke yi sabo da
karuwar kyawawan dabi'unsa.
Haka shima Sarki Gulam yake kaunar Sadauki
Affan sama da sauran 'ya'yansa bakid aya sabo da yana
ganin duk cikinsu ba wanda zai gado halinsa sai Affan,
shi yasa koda yaushe suna tare da Sarki, bacci kawai
ke rabasи.
Wannan yasa gaba dayan sauran 'yan uwansa
suka tsangwameshi, kuma suke tsananin bakin ciki da
12
Hikaya Hamsin Basiru Harande
shi tare da neman hanyar da za su hallakar da shi su
huta. Amma da yake sun san ba yadda za su yi da shi
dan ya fi su karfi da jarumta, kuma zai iya watsasu
gaba daya shi yasa suka hakura.
Haka shima waziri Kwabis ya kasance cikin
tsananin bakin ciki da Sadauki Affan, domin duk
shawarar da Sarki zai nema wurin Waziri sai ta koma
wurin Affan, idan ya ce ayi abu, to ba makawa sai
Sarki ya yi shi. Haka kuma idan ya ce kar ayi ba
wanda ya isa ayi shi. Wannan yasa koda yaushe Waziri
Kwabis ke tasa 'ya'yan Sarki yana karanta musu
muguwar shawara akan Affan.
Wata rana Waziri Kwabis ya kira wasu yara
goma daga cikin 'ya'yan Sarki wadanda yafi shiri da
su. Yaran sun hada da Da'uf Zalum, Safir, Bakar,
Hamzi, Sagar, Samar, Masul, Gubu da Shafir.
Bayan sun zo sun zauna sai Waziri Kwabis ya
fara magana da cewa, 'Ya ku 'ya'yana ba komai yasa na
taraku anan ba sai don in sakaku a hanyar da nike
zaton kun kauce mata." Ya ci gaba da cewa, "Ina ganin
bai dace ace gaku maza majiya karfi, ga ku da yawa
amma ace mutum daya daga cikin ku wanda ya
kasance kani daga ckinku ya hana muku sakal, ya hana muku walwalwa da sakewa a cikin gidan nan. Wannan
ne yasa na ce bari in yi kiranku domin ku san matakin
da za ku dauka, nima zan taimaka muku kuma na ga
13
Hikaya Hamsin Basiru Harande
kamar kun fi sauran hankali ne shi yasa na nemeku".
Koda Waziri Kwabis ya kawo nan a zancensa sai
daya daga cikin yaran mai suna Bakar ya dubi Waziri
ya cc, "Ya shugabana gaskiyace wannan magana da
kayi, ta dade tana damunmu. Kai bama Affan din
kadai ya damemu ba har da Sarki sabo da bai dace a ce
kamar mu 'ya'yan Sarki muna aiki kamar yadda kowa
kc yi ba, in mun yi laifi a hukuntamu. Kai har gidan
kurkukui ya sha yasa a kullemu, ya hana mu jin dadin
rayuwa, ya hana mu nuna mu 'yan sarauta ne. Kuma
ina zaton ba kowa ke sa yana yi mana haka ba illa
Affan. Ba don komai ba sai don ya kara farin jini ga
idanun al'umma. Sabo da haka ba Affan kadai ya dace
mu dauki mataki akai ba har mahaifinmu Sarki".
Koda Bakar ya kawo nan a zancensa sai sauran
suka ce, "Wannan gaskiya ne".
Koda Waziri Kwarbis yaji haka sai ya се,
"Maganar daukan mataki akan Sarki ya rage gareku,
sabo da Sarki dai ubanku ne, kuma ni dan uwana në,
sabo da haka yanzu sai ku yankc shawarar abin yi da
kanku".
Waziri Kwarbis na kawowa nan a zancensa sai
wani daya daga cikin su mai suna Da'uf ya cc, "Ya ku
'yan uwana, shawarata anan ita cc, kun ga dai tsufa ya
riski mahaifinmu, kuma har yanzu bai bamu cikakken
'yancin mu ba, sabo da haka abin da ya fi kawai mu
14
Hikaya Hamsin Basiru Harande
hallakar da shi ta hanyar shayar da shi guba. Kun ga
idan ya mutu sai mu kama Affan mu kulleshi a
kurkuku har abada ba zai fito ba, ya kasance cikin
nau'ikan azabobi. Daga bisani sai ayi mana kuri'a duk
wanda ya ta fada kansa sai a bashi sarauta. Mu kuma
mu goya masa baya, ya zamo mun samu 'yanci mu
fantama mu wala a cikin kasar nan".
Koda suka ji haka sai gaba dayansu suka hada
baki suka ce, "Mun amince da wannan shawara taka".
Haka shima Waziri Kwabis ya amince da wannan
bakar shawara ta Da'uf.
Hakan kuwa aka yi, domin sai da suka yi kokari
suka sawa Sarki guba a cikin ruwan shansa. Tun ranar
da Sarki ya sha ruwan gubar ya kwanta ciwo. A
kullum sai ya yi aman jini, abin da ya matukar
dugunzuma hankalin mutanen garin ke nan,
musamman ma Affan da mahaifiyarsa Zawira,
wadanda ko yaushe suna kusa da Sarki suna zubar da
hawaye, sakamakon ganin irin mugun halin da yake
ciki. Kuma suna tunanin cewa idan Sarki ya mutu za
su shiga wani hali na matsi a gidan sarautar.
* *
Koda Sarki Gulam ya ga alamar wannan cuta ba
ta tashi bace, sai ya aika aka kira masa Waziri Kwabis
domin ya bar masa wasiyya.
15
Hikaya Hamsin Basiru Harande
Waziri Kwabis ya shigo ya zauna kusa da Sarki
fuskarsa na nuna damuwa da jimamin rashin lafiyar
Sarki.
Sarki ya dago cikin dauriya da kyar ya dubeshi
ya ce, "Ya kai dan uwana abin da yasa na yi kiranka
shi ne, zan bar maka wata wasiyya. Wasiyyar kuwa ita
cc, bayan na mutu ina so a bawa Affan karagar
mulkina, sabo da duk cikin 'ya'yana hamsin ba wanda
zai iya mulkin adalci da gaskiya kamarsa. Kuma na
horeka da kada ka yi sakaci da wannan wasiyyar,
kuma kada ka canja ra'ayi sabo da tuni ka san cewa a
al'adar wannan masarauta tamu duk wanda Sarki ya ce
a ba mulki kafin ya mutu to shi ake ba. Idan kuwa ba a
bashi ba to duk wanda ya hau karagar mulkin zai
mutu, kuma zai jefa kasar cikin rudanin da zai yi
sanadiyyar rushewarta. Sabo da haka ka kula da
wannan wasiyya".
Sarki Gulam na kawowa nan a zancensa sai
idanunsa suka kakkafe alamar ya mutu. Koda Waziri
ya ga haka sai ya tabbatar Sarki ya mutu. Maimakon
ya yi murna sai abin ya zame masa wani babban abin
bakin ciki. Ba wai sabo da mutuwar Sarkin ce ba, a'a
sai don ya san abin da Sarki ya fada gaskiya ne,
muddin ba a baiwa Affan sarautar kasar ba to kuwa
duk.wanda ya hau karagar mulkin sai ya.halaka.
Lokacin da al'ummar kasar Mahbub suka ji
16
Hikaya Hamsin Basiru Harande
sanarwar mutuwar Sarki sai suka kasance cikin
mummunan tashin hankali tare da bakin ciki mai
tsanani, sabo da sun san cewa duk wanda za a bawa
sarautar Kasar in dai ba Affan ba to ba shakka sai
mutanc sun ga ba dai-dai ba, sabo da sanin halin
'ya'yan Sarki, kuma gashi suna zaton ba za a baiwa
Affan sarautara ba kasancewarsa kani garesu. Wannan
shi ne ya kara tayar da hankalin al'ummar kasar.
Affan da mahaifiyarsa Zawira kauwa, suka
kasance cikin bakin ciki mara misaltuwa, domin har
Sarki ya yi kwana uku da rasuwa basu daina kuka da
jimamin rashinsa ba, sabo da sanin za su fada cikin
wani hali. Amma sauran matan Sarki da 'ya'yansu ba
wani bakin ciki da suka yi. Kai wasu ma har nuna farin
cikinsu suke yi suna cewa, "Yanzu dai zamu san mu
'ya'yan Sarauta ne, zamu sakata mu yi yadda muke so
cikin kasar nan ba wanda ya isa ya hanamu".
A daren rana ta bakwai da mutuwar Sarki sai su
Bakar da 'yan uwansa su goma suka iske Wazu
Kwabis suka nufi gidan Waziri Kwabis.
Bayan sun kwashi gaisuwa a gareshi sai Вака
ya nisa ya fara magana da cewa, "Ya kai Baffanmu,
abin da ya kawomu shi ne, ka ga mun riga mun kask.
mahaifinmu, to yanzu mene ne abin vi"
Koda Waziri Kwabis yaji wannan batu ya yi
ajiyar numfashi cikin takaici gamı da girgiza
17
Hikaya Hamsin Basiru Harande
jikinsa a sanyaye ya ce da su ya kwashe labarin
wasiyyar da Sarki ya yi masa na cewa Affan ne wanda
zai gajeshi ya sanar da su. Ya kare da cewa, "Wannan
ne yasa ku ka ga na kyaleku". R
Koda suka ji haka sai hankalinsu gaba daya ya
dugunzuma. Cikin matukar tashin hankali Da'uf ya ce,
"Ashe inda aka tona nan aka fada ke nan?".
Ya dubi Waziri Kwabis ya ce, "To yanzu ba wata
hanya da zamu bi, shi ke nan sai mu zauna karkashin
mulkin kaninmu, irin mulkin da zai hanamu sakat.
Kuma ka san sabo da irin hakane ya kaimu ga hallakar
da mahaifinmu".
Koda Waziri yaji haka sai ya daga kai yana
tunani. Can sai ya dubesu ya ce, "Abin da nake so da
ku shi ne, ku kwantar da hankalinku gobe zanje wurin
wani sanannen boka nawa. Na rantse da wuta
ma'abociyar boruwa zai iya shawo mana kan wannan
matsalar komai wuyarta. Kuma na rantse da furfurar
Babana in dai ina numfashi a doron kasa Affan ba zai
taba hawa karagar mulkin wannan kasar ba. Sabo da
haka ku tashi ku je na sallameku".
Suka tashi kowa ya kama gabansa.
Run da farar safiya Waziri Kwabis ya yai hawa
da niyyar zuwa kogon bokansa, wato boka Larhat Ibni
Khushubul Mannaf.
Boka Larhat Ibni Khushubul Mannaf ya kasance
18
Hikaya Hamsin Basiru Harande
bokane masani a cikin sha'anin bokanci, kuma yana
zaune ne a cikin wani kogon dutse da ke bayan garin
Mahbub.
Haka Waziri Kwabis ya yi ta tafiya, bai zame ko
ina ba sai bakin kogon boka Larhat Ibni Khushubul
Mannaf. Da yake ya saba zuwa wurin, shi yasa ya
kunna kai cikin kogon kai tsaye.
Shigarsa ake da wuya sai ya iske boka Larhat Ibni
Khushubul Mannaf saman buzunsa na tsafi yana
tsatsube-tsatsubensa. Koda Waziri Kwabis ya ga haka
sai ya samu wuri ya zauna yana jiran bokan ya gama
ya yi mai bayanin abin da ke tafe da shi.
Bayan bokan ya gama surkullensa sai ya dubi
Kwabis ya ce, "Barka da zuwa ya kai Waziri Kwabis,
na riga na san abin da ke tafe da kai. Kuma ba shakka
wasiyyar da Sarki ya bari ma haka take. Bakin
alkalami ya riga ya bushe, muddin kuwa kouka nada
wani ba wannan yaro ba, to zai halaka. Kuma kasarku
za ta shiga wani bala'i da zai kai ta ga rushewa".
Koda Waziri yaji haka sai hankalinsa ya tashi,
hantar cikinsa ta kada. Cikin rawar murya ya fara
magana da cewa, "Ya kai shugaban bokayen duniya,
kayi sani cewa muddin wannan yaron ya hau sarautar
kasar nan zamu kasance cikin kunci da danniya. Kuma
yanzu shi ke nan kana nufin ba wata hanya da zamu
6ulloma wannan lamarin?".
19
Hikaya Hamsin Basiru Harande
Koda boka Larhat Ibni Khushubul Mannaf yaji
haka sai ya dauko jakar tsafinsa ya baje ya shiga
bincike tare da wasu irin sambatu. Sai da ya dauki
sa'o'i yana yi sai kawai ya kyalkyale da wata irin
mummunar dariya, sannan ya dubi Waziri ya ce, "Ya
kai Waziri kayai sani cewa na samo mafita daya
wadda daga ita ba wata".
Cikin zakuwa Waziri ya ce, "Maza sanar da ni
wannan mafita da ka samo".
Boka Larhat Ibni Khushubul Mannaf ya ce,
"Mafitar da na samo ita ce, za ka tara 'ya'yan Sarki
baki dayansu kace musu duk mai son hawa karagar
mulkin kasarku sai ya bada dadadana HIKAYOYI
HAMSIN. Idan suka gaza sai ka basu kwanaki hamsin
su shiga duniya wurin Malaman Hikayoyin da suka fi
na kowa dadi su samo su zo su karanta ma. Muddin
duk wanda ya samu nasarar yin hakan a cikinsu zai
hau karagar mulkin ba tare da ya hallaka ba, kuma ya
gudanar da mulki son ransa.
Lallai wannan ita ce kawai hanya daya da za a bi,
kuma makarin wannan sirri na sarautar kasarku.
Amma idan ba ta wannan hanya ba, ina mai tabbatar
maka cewa duk wanda ya hau sarautar a cikinsu sai ya
rasa rayuwarsa kamar yadda ka sani face mutum daya,
wato Affan".
Koda Waziri Kwabis yaji haka sai murna ta
20
Hikaya Hamsin Basiru Harande
kamashi, domin ya san ya samu hanyar da zai cimma
burinsa.
Waziri Kwabis ya duka gaban bokan ya yi
godiya, sannan ya tashi ya tafi cike da farin ciki.
Fadar ta cika makil kamar za ta tsage. In kayi
duba izuwa 6angaren dama za ka gansu zazzaune su
hamsin dai-dai akan wadansu kujeru na alfarma,
kowannensu sanye cikin kayatattun suturu na sarauta,
kowanne yana shan kamshi da nuna isa da izza, idan
ka dauke Affan wanda yake karamin cikinsu, bai damu
da girman kai ba.
Waziri Kwabis ya mike ya fara magana da murya
mai karfi da cewa.
"Ya ku mutanen wannan birni na Mahbub! A
matsayina na wazirin kasar nan, kuma Sarki mai rikon
kwarya tun bayan rasuwar dan uwana Sarkinmu mai
adalci. Ku yi sani cewa aba kaomai ne yasa na taraku a
nan ba sai face sai don ku shaidi wata wasiyya da
Sarki ya umarci in sanar da 'ya'yansa kafin ya bar
duniya".
Waziri Kwabis ya ci gaba da bayaninsa cikin
farin ciki da mummunan kuduri a zuciyarsa.
"Wannan wasiyya kuwa ita ce, Sarki ya sanar da
ni cewa duk wanda yake son ya gajeshi, ma'ana ya hau
21
Hikaya Hamsin Basiru Harande
kan karagar mulkin wannan kasa tamu mai albarka ya
mulki jama'arta, ya zamo dole a gareshi sai ya bada
dadadan HIKAYOYI HAMSIN. Sabo da haka yanzu
zamu baku dama ku fara gabatar mana da hikayoyin ga
duk wanda yake bukatar hawa mulki. Kuma duk
wanda ta sa tafi dadi da kayatarwa shi zamu nada
Sarkin wannan kasa. In kuwa ba za ku iya ba, to zamu
baku kwanaki sittin ku shiga duniya wajen masana
hikayoyi ku samo labaran hikayoyi masu dadi".
Waziri Kwabis na kawowa nan a zancensa sai yai
duba izuwa ga 'ya'yan Sarki ya ce, "Yanzu mene ne
ra'ayinku akan hakan?"
Su kuwa 'ya'yan Sarki da sauran al'ummar gari sai
hankalinsu ya dugunzuma sabo da basu taba zaton
hakan zai faru ba, kuma gashi cikin 'ya'yan Sarki babu
daya da yake da masaniya ko kwarewa akan hikaya.
Cikin sanyin jiki Bakar ya mike ya ce, "Ya
Baffanmu, da yake dai an san cewa duk cikinmu ba
wanda ya iya hikaya koda daya ce balle hamsin, sabo
da haka mun yarda da a bamu kwanaki sittin mu shiga
duniya neman ilimn HIKAYA."
Koda Waziri yaji haka sai ya dubi sauran 'ya'yan
Sarki ya ce, "Ku kun yarda da wannan shawara ta
Bakar?". Gaba dayansu suka hada baki suka ce, "Mun
amince".
Waziri ya gyada kai cikin gamsuwa ya ce, "То
22
Hikaya Hamsin Basiru Harande
daga gobe- za ku tafi. Kuma duk wanda ya wuce
kwanaki sittin ya fita daga cikin wannan gasar".
Yana kawowa nan a zancensa sai ya sallami kowa
ya kama