Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels HIKAYA HAWSINBASIRU ALIYU HARANDE ZURU Hikaya Hamsin Basiru Harande HIKAYA HAMSIN-1 A da can bayan wani zamani mai tsawo da ya shude, an yi wata kasa ca yankin larbawa mai suna Mahbub. Kasa Mahbub ta kasance babbar kasa ce mai yawan al'umma da tarin dukiya tare da manyan ginc-gine wadanda suka sa kasar ta shiga cikin manyan kasashen da suka shahara wurin kyau da Kawatuwa a wannan zamani. Sarki Gulam shi ne Sarkin kasar Mahbub, kuma ya kasance Sarki ne mai tsananin adalci ga al'ummar kasarsa, ba abin da Sarki ya sama gaba sai tabbatar da adalci tsakanin al'ummarsa. Wannan ne ya sa jama'ara kasarsa ke matukar sonsa tare da biyayya gareshi. a Sarki Gulam ya kasance yana da matan aure hamsin, kuma kowacce daga cikinsu ta kasance ba baiwa bace 'ya ce a wurin wani babban Sarki ko wani attajiri. Sai daya daga cikinsu wadda ya taba ribatowa a wurin yaki. Ita dai wannan baiwar sunanta Zawira. Ta kasance baiwa ce amma Sarki Gulam yafi sonta daga cikin matansa. Sabo da Zawira ta kasance mace ce mai gaskiya da rikon amana ga tausayi da son taimakawa talaka. Ga uwa uba kyakkyawa ce ta gani ta fada. Wadannan abubuwa ne yasa Sarki Gulam ya fi sonta kuma yake yawan neman shawararta a duk lamarin da ya kuduri aiwatarwa. Wannan nc yasa sauran matan Sarki arba'in da tafa suke tsananin kishinta tarc da tsangwamarta. Kuma suna yi ma ta gorin cewa kowa daga cikinsu tana da asali amma ban da ita, sbao da ita kammar baiwace. Ba a san asalinta 6 Hikaya Hamsin Basiru Marnde ba. Da yake Zawira ta kasance mai hakuri ce ko taji suna maganganunsu sai dai tayi murmushi ta wuce. Da yake ance mutum tara ne bai cika goma ba, wata rana matan Sarki suka taru suka rinka jifar Zawira da munanan kalamai na 6atanci. Tun Zawira na kannewa har ta gaza hakuri ta mayar musu da martani. Abin da yasa suka taru suka yi ma ta dukan tsiya suka barta kwance. Koda labari ya iske Sarki sai ya shigo gida cikin sauri ya zo ya iske Zawira cikin dakinta kwance tana jinya. Bayan ya zauna kusa da ita sai ya dubeta cikin sanyin jiki ya ce, "Ya ke matata kiyi sani cewa duk abin da ya faru tsakaninki da abokan zamanki ina sane, kuma abin da na ke so da ke shi ne, ki ci gaba da hakuri kamar yadda kika saba. Me hakuri shi kan dafa dutse, kuma da sannu za ki ga nasara cikin lamuranki." Sarki Gulam na kawowa nan a zancensa sai ya sumbaci goshinta sanann ya fice. * * * Waziri Kwabis shi ne Wazirin Sarki Gulam, kuma ya kasance dan uwa ne na jini ga Sarki, amma sai dai Waziri Kwabis ya kasancc mutum mai son abin duniya da sona gadara da girman kai. Kuma mutum ne mai kokarin ba Sarki shawarwarin shimfida mulkin kama karya da cin zarafin talakawa. Lokacin da Sarki ya fuskanci hali da irin manufar 7 Hikaya Hamsin Basiru Harande Waziri Kwabis sai gaba daya ya daina neman shawararsa ta fannin mulki, sai ya koma neman shawarar Zawira. Waziri Kwabis ya kasance Waziri ne kawai, amma Sarki bai neman shawararsa. Wannan lamari ashe ba karamin yima Waziri Kwabis ciwo ya yi ba. Ganin cewa gashi namiji kuma kullum shi ne a fada amma ace Sarki sai ya shiga gida ya nemo shawarar mace. Ko Cikin matan ma baiwa, to mene ne amfaninsa ke nan? Wannan ne yasa shima Waziri shiga cikin jerin masu bakin ciki da Zawira tare da neman hanyar da zai yi maganinta. Ana cikin haka ne sai matan Sarki gaba daya suka samu juna biyu, wato ciki. Cikinsu har da Zawira. Lamarin da ya sa Sarki Gulam cikin tsananin farin ciki da bai misaltuwa ganin matansa hamsin sun sami ciki lokaci guda. Kuma yana ganin za su haihu lokaci guda. Haka dai matan Sarki suka ci gaba da renon cikinsu cikin kwanciyar hankali amma banda Zawira, domin ita kullum sai tayi kuka sabo da irin kalaman da kishiyoyinta ke fada mata. Kai hara ce ma ta suke yi cikinta ba na Sarki bane cikin kasuwa ne. Amma da yake Sarki na sonta sai ya rinka kwantar ma ta da hankali. Da haka har cikin matan Sarki ya isa haihuwa. Wata rana Sarki na zaunc ana fadanci sai ga Jakadiya ta shigo tana guda tana cewa, "Yau ranar 8 Hikaya Hamsin. Basiru Harande 1 farin ciki, matar Sarki ta farko ta sauka lafiya." Koda Sarki yaji haka sai murna ta kamashi, tun kafin ya gama murnar na farko sai ga albishir na biyu cewa wata ta kara haihuwa. Ana cikin haka sai ga na uku da na huďu lokaci daya. Kai haka dai aka tafiyar da wannan ranar ba a yi fadanci ba domin kuwa a ranar fada ta koma tambar wani asibitin haihuwa sabo da duk inda ka duba jarirai ne. Sai da aka kawowa Sarki Gulam 'ya'yansa su arba'in da tara dukkansu maza wadanda aka haifa rana daya. Koda aka gama kawowa Sarki jinjiran baiji ance ga dan Zawira ba, sai ya tambaya ya ce, "Shin ina dan da Zawira ta haifa ne?". Koda Waziri Kwabis yaji haka sai ya ce, "Ya shugabana dama tuni na shaida ma cewa cikin Zawira ba naka bane domin tuni bokana ya shaida mani cewa matanka za su haihu rana daya lokaci daya, duk wadda bata haihu a cikinsu ba to ba shakka cikin ba naka bane. Sabo da haka ka gasgata maganata ka dauki tsattsauran mataki akanta..." Cikin tsawa Sarki Gulam ya katse shi da cewa, "Kai Kwabis, na san matata kuma na san halinta ba za ta taba cin amanata ba, sabo da haka karya bokanka ya fada maka. Kuma idan gaskiya ne bokanka yake to ya zo ya sameni". Sarki na kawowa nan a zancensa sai ya juya ya 9 Hikaya Hamsin Basiru Harande shige gida ya bar Waziri Kwabis nan yana jimamin Karyar da ya shara bata yi ba. Haka dai Sarki da al'ummar kasar Mahbub suka kasance cikin murna tare da kawata garin domin bikin murnar suna. Mako na zagayowa aka barke da murnar bayan Sarki ya radawa 'ya'yansa suna su arba'in da tara. Duk inda ka duba makada ne da mawaka tare da masu bushe-bushe. Abinci kuwa wurin ba a magana domin sai da aka rasa inda za a sa shi. Sarki kuwa ya kasance cikin farantama tallakawan kasarsa rai ta hanyar raba musu dukiya, tufafi, dabbobi da sauransu. Sai da aka shafe kwanaki bakwai ana wannan shagali sannan kowa ya watse ya koma inda ya fito. Ita ko Zawira sai ta kasance cikin tsananin tashin hankali sabo da ganin duk kishiyoyinta sun haihu amma ita ba ta haihu ba. Kuma gashi dama ana cewa cikin ta bana Sarki bane. Nan da nan ta shiga tunanin shin wannan tsaikon da ta samu bai sa Sarki ya yi zargin kazafin da ake yi mata gaskiya ne? Amma duk lokacin da ta tuna irin so da yardar da ke tsakaninsu da Sarki sai hankalinta ya dan kwanta. Haka shima Sarki abin ya dameshi, domin tun lokacin da matansa suka samu ciki yafi kaguwa ya ga dan Zawira bisa dana kwance, amma gashi kowaccе matarsa ta haihu banda Zawira. Sai da aka yi kwana hamsin dai-dai da haihuwar ΙΟ Hikaya Hamsin Basiru Harande matan Sarki sannan Zawira ta haifi santalelen danta. Sarki ya kasance cikin tsananin farin ciki sabo da ganin 'ya'yansa sun cika hamsin, kuma dan Zawira ya kasance kyakkyawa wanda baki bai iya bayanin kyawunsa gaba daya. Gaba daya 'ya'yan da Sarki ya haifa sai dai su biyo bayansa fagen kyau. Wannan ne yasa masu zuwa barka suke cewa ko dai wannan yaron aljani ne? In ka dauke Sark da ita Zawira da wasu tsirarun kuyanginta duk gidan ba wanda ya yi murna da wannan haihuwa, kowa ka gani fuskarsa murtute take, musamman Waziri Kwabis wanda bakin ciki yasa ya rasa inda zai sa kam don ya san an haifi yaron da Sarki zai fi so fiye da komai a duniya. Mako na zagayowa aka radawa yaro suna Affan. da yake dama ba wani farin ciki ake yi da haihuwar yarin ba shi yasa ba a yi wani shagalin biki ba. Lokacin da 'ya'yan Sarki suka kai shekaru gomagoma, sai Affan ya kasance tamkar farin wata a cikin taurari cikin yaran. Sabo da yafi su kyau nesa ba kusa ba, ya fisu kwarjini ga fara'a, bai da girman kai, sannan ba ruwansa da mai kudi da talaka, duk daya nc a wurinsa. Idan aka dawo maganar jarumtaka, wato abun sai dai ayi shiru, sabo da duk matashin da ke Kasar Mahbub tsoronsa yake a fagen fama. Kai har mai koyar da shi dabarun yaki ya fara tsorata da lamarin Affan. Hikaya Hamsin Baslru Harande Wadannan halaiye na Affan yasa jama'ar garin ke matukar kaunarsa, yara da manya, maza da mata kowa sonsa yake. Kai har wasu na cewa "Kai za ka gaji ubanka". Su ko sauran 'yan uwansa sun kasance yara ne 'masu tsananin girman kai da son nuna su 'ya'yan sarauta ne ga wulakanta talakawa da cin zarafinsu. Kai ba don Sarki na hana musu yin yadda suke so ba da sai sun ce mutane su kwanta su rika takinsu suna tafiya samansu. Wadannan halayya anasu ne ya sa Sarki ya fi son Affan sabo da ya bambanta da su. Lokacin da suka kai shekaru ashirin, kowannensu ya mallaki hankalin kansa, kuma kowa ya kawo karfi cikinsu. Sadauki Affan ya cika sadauki mai tsananin karfin damtse da sanin dabarun yaki ya zamo duk sadaukin da ke wannan yanki tsoronsa yake a fagen fama. Kyawu da kwarjininsa suka kara baiyana. Jama'ar kasar kuwa sai kara sonsa suke yi sabo da karuwar kyawawan dabi'unsa. Haka shima Sarki Gulam yake kaunar Sadauki Affan sama da sauran 'ya'yansa bakid aya sabo da yana ganin duk cikinsu ba wanda zai gado halinsa sai Affan, shi yasa koda yaushe suna tare da Sarki, bacci kawai ke rabasи. Wannan yasa gaba dayan sauran 'yan uwansa suka tsangwameshi, kuma suke tsananin bakin ciki da 12 Hikaya Hamsin Basiru Harande shi tare da neman hanyar da za su hallakar da shi su huta. Amma da yake sun san ba yadda za su yi da shi dan ya fi su karfi da jarumta, kuma zai iya watsasu gaba daya shi yasa suka hakura. Haka shima waziri Kwabis ya kasance cikin tsananin bakin ciki da Sadauki Affan, domin duk shawarar da Sarki zai nema wurin Waziri sai ta koma wurin Affan, idan ya ce ayi abu, to ba makawa sai Sarki ya yi shi. Haka kuma idan ya ce kar ayi ba wanda ya isa ayi shi. Wannan yasa koda yaushe Waziri Kwabis ke tasa 'ya'yan Sarki yana karanta musu muguwar shawara akan Affan. Wata rana Waziri Kwabis ya kira wasu yara goma daga cikin 'ya'yan Sarki wadanda yafi shiri da su. Yaran sun hada da Da'uf Zalum, Safir, Bakar, Hamzi, Sagar, Samar, Masul, Gubu da Shafir. Bayan sun zo sun zauna sai Waziri Kwabis ya fara magana da cewa, 'Ya ku 'ya'yana ba komai yasa na taraku anan ba sai don in sakaku a hanyar da nike zaton kun kauce mata." Ya ci gaba da cewa, "Ina ganin bai dace ace gaku maza majiya karfi, ga ku da yawa amma ace mutum daya daga cikin ku wanda ya kasance kani daga ckinku ya hana muku sakal, ya hana muku walwalwa da sakewa a cikin gidan nan. Wannan ne yasa na ce bari in yi kiranku domin ku san matakin da za ku dauka, nima zan taimaka muku kuma na ga 13 Hikaya Hamsin Basiru Harande kamar kun fi sauran hankali ne shi yasa na nemeku". Koda Waziri Kwabis ya kawo nan a zancensa sai daya daga cikin yaran mai suna Bakar ya dubi Waziri ya cc, "Ya shugabana gaskiyace wannan magana da kayi, ta dade tana damunmu. Kai bama Affan din kadai ya damemu ba har da Sarki sabo da bai dace a ce kamar mu 'ya'yan Sarki muna aiki kamar yadda kowa kc yi ba, in mun yi laifi a hukuntamu. Kai har gidan kurkukui ya sha yasa a kullemu, ya hana mu jin dadin rayuwa, ya hana mu nuna mu 'yan sarauta ne. Kuma ina zaton ba kowa ke sa yana yi mana haka ba illa Affan. Ba don komai ba sai don ya kara farin jini ga idanun al'umma. Sabo da haka ba Affan kadai ya dace mu dauki mataki akai ba har mahaifinmu Sarki". Koda Bakar ya kawo nan a zancensa sai sauran suka ce, "Wannan gaskiya ne". Koda Waziri Kwarbis yaji haka sai ya се, "Maganar daukan mataki akan Sarki ya rage gareku, sabo da Sarki dai ubanku ne, kuma ni dan uwana në, sabo da haka yanzu sai ku yankc shawarar abin yi da kanku". Waziri Kwarbis na kawowa nan a zancensa sai wani daya daga cikin su mai suna Da'uf ya cc, "Ya ku 'yan uwana, shawarata anan ita cc, kun ga dai tsufa ya riski mahaifinmu, kuma har yanzu bai bamu cikakken 'yancin mu ba, sabo da haka abin da ya fi kawai mu 14 Hikaya Hamsin Basiru Harande hallakar da shi ta hanyar shayar da shi guba. Kun ga idan ya mutu sai mu kama Affan mu kulleshi a kurkuku har abada ba zai fito ba, ya kasance cikin nau'ikan azabobi. Daga bisani sai ayi mana kuri'a duk wanda ya ta fada kansa sai a bashi sarauta. Mu kuma mu goya masa baya, ya zamo mun samu 'yanci mu fantama mu wala a cikin kasar nan". Koda suka ji haka sai gaba dayansu suka hada baki suka ce, "Mun amince da wannan shawara taka". Haka shima Waziri Kwabis ya amince da wannan bakar shawara ta Da'uf. Hakan kuwa aka yi, domin sai da suka yi kokari suka sawa Sarki guba a cikin ruwan shansa. Tun ranar da Sarki ya sha ruwan gubar ya kwanta ciwo. A kullum sai ya yi aman jini, abin da ya matukar dugunzuma hankalin mutanen garin ke nan, musamman ma Affan da mahaifiyarsa Zawira, wadanda ko yaushe suna kusa da Sarki suna zubar da hawaye, sakamakon ganin irin mugun halin da yake ciki. Kuma suna tunanin cewa idan Sarki ya mutu za su shiga wani hali na matsi a gidan sarautar. * * Koda Sarki Gulam ya ga alamar wannan cuta ba ta tashi bace, sai ya aika aka kira masa Waziri Kwabis domin ya bar masa wasiyya. 15 Hikaya Hamsin Basiru Harande Waziri Kwabis ya shigo ya zauna kusa da Sarki fuskarsa na nuna damuwa da jimamin rashin lafiyar Sarki. Sarki ya dago cikin dauriya da kyar ya dubeshi ya ce, "Ya kai dan uwana abin da yasa na yi kiranka shi ne, zan bar maka wata wasiyya. Wasiyyar kuwa ita cc, bayan na mutu ina so a bawa Affan karagar mulkina, sabo da duk cikin 'ya'yana hamsin ba wanda zai iya mulkin adalci da gaskiya kamarsa. Kuma na horeka da kada ka yi sakaci da wannan wasiyyar, kuma kada ka canja ra'ayi sabo da tuni ka san cewa a al'adar wannan masarauta tamu duk wanda Sarki ya ce a ba mulki kafin ya mutu to shi ake ba. Idan kuwa ba a bashi ba to duk wanda ya hau karagar mulkin zai mutu, kuma zai jefa kasar cikin rudanin da zai yi sanadiyyar rushewarta. Sabo da haka ka kula da wannan wasiyya". Sarki Gulam na kawowa nan a zancensa sai idanunsa suka kakkafe alamar ya mutu. Koda Waziri ya ga haka sai ya tabbatar Sarki ya mutu. Maimakon ya yi murna sai abin ya zame masa wani babban abin bakin ciki. Ba wai sabo da mutuwar Sarkin ce ba, a'a sai don ya san abin da Sarki ya fada gaskiya ne, muddin ba a baiwa Affan sarautar kasar ba to kuwa duk.wanda ya hau karagar mulkin sai ya.halaka. Lokacin da al'ummar kasar Mahbub suka ji 16 Hikaya Hamsin Basiru Harande sanarwar mutuwar Sarki sai suka kasance cikin mummunan tashin hankali tare da bakin ciki mai tsanani, sabo da sun san cewa duk wanda za a bawa sarautar Kasar in dai ba Affan ba to ba shakka sai mutanc sun ga ba dai-dai ba, sabo da sanin halin 'ya'yan Sarki, kuma gashi suna zaton ba za a baiwa Affan sarautara ba kasancewarsa kani garesu. Wannan shi ne ya kara tayar da hankalin al'ummar kasar. Affan da mahaifiyarsa Zawira kauwa, suka kasance cikin bakin ciki mara misaltuwa, domin har Sarki ya yi kwana uku da rasuwa basu daina kuka da jimamin rashinsa ba, sabo da sanin za su fada cikin wani hali. Amma sauran matan Sarki da 'ya'yansu ba wani bakin ciki da suka yi. Kai wasu ma har nuna farin cikinsu suke yi suna cewa, "Yanzu dai zamu san mu 'ya'yan Sarauta ne, zamu sakata mu yi yadda muke so cikin kasar nan ba wanda ya isa ya hanamu". A daren rana ta bakwai da mutuwar Sarki sai su Bakar da 'yan uwansa su goma suka iske Wazu Kwabis suka nufi gidan Waziri Kwabis. Bayan sun kwashi gaisuwa a gareshi sai Вака ya nisa ya fara magana da cewa, "Ya kai Baffanmu, abin da ya kawomu shi ne, ka ga mun riga mun kask. mahaifinmu, to yanzu mene ne abin vi" Koda Waziri Kwabis yaji wannan batu ya yi ajiyar numfashi cikin takaici gamı da girgiza 17 Hikaya Hamsin Basiru Harande jikinsa a sanyaye ya ce da su ya kwashe labarin wasiyyar da Sarki ya yi masa na cewa Affan ne wanda zai gajeshi ya sanar da su. Ya kare da cewa, "Wannan ne yasa ku ka ga na kyaleku". R Koda suka ji haka sai hankalinsu gaba daya ya dugunzuma. Cikin matukar tashin hankali Da'uf ya ce, "Ashe inda aka tona nan aka fada ke nan?". Ya dubi Waziri Kwabis ya ce, "To yanzu ba wata hanya da zamu bi, shi ke nan sai mu zauna karkashin mulkin kaninmu, irin mulkin da zai hanamu sakat. Kuma ka san sabo da irin hakane ya kaimu ga hallakar da mahaifinmu". Koda Waziri yaji haka sai ya daga kai yana tunani. Can sai ya dubesu ya ce, "Abin da nake so da ku shi ne, ku kwantar da hankalinku gobe zanje wurin wani sanannen boka nawa. Na rantse da wuta ma'abociyar boruwa zai iya shawo mana kan wannan matsalar komai wuyarta. Kuma na rantse da furfurar Babana in dai ina numfashi a doron kasa Affan ba zai taba hawa karagar mulkin wannan kasar ba. Sabo da haka ku tashi ku je na sallameku". Suka tashi kowa ya kama gabansa. Run da farar safiya Waziri Kwabis ya yai hawa da niyyar zuwa kogon bokansa, wato boka Larhat Ibni Khushubul Mannaf. Boka Larhat Ibni Khushubul Mannaf ya kasance 18 Hikaya Hamsin Basiru Harande bokane masani a cikin sha'anin bokanci, kuma yana zaune ne a cikin wani kogon dutse da ke bayan garin Mahbub. Haka Waziri Kwabis ya yi ta tafiya, bai zame ko ina ba sai bakin kogon boka Larhat Ibni Khushubul Mannaf. Da yake ya saba zuwa wurin, shi yasa ya kunna kai cikin kogon kai tsaye. Shigarsa ake da wuya sai ya iske boka Larhat Ibni Khushubul Mannaf saman buzunsa na tsafi yana tsatsube-tsatsubensa. Koda Waziri Kwabis ya ga haka sai ya samu wuri ya zauna yana jiran bokan ya gama ya yi mai bayanin abin da ke tafe da shi. Bayan bokan ya gama surkullensa sai ya dubi Kwabis ya ce, "Barka da zuwa ya kai Waziri Kwabis, na riga na san abin da ke tafe da kai. Kuma ba shakka wasiyyar da Sarki ya bari ma haka take. Bakin alkalami ya riga ya bushe, muddin kuwa kouka nada wani ba wannan yaro ba, to zai halaka. Kuma kasarku za ta shiga wani bala'i da zai kai ta ga rushewa". Koda Waziri yaji haka sai hankalinsa ya tashi, hantar cikinsa ta kada. Cikin rawar murya ya fara magana da cewa, "Ya kai shugaban bokayen duniya, kayi sani cewa muddin wannan yaron ya hau sarautar kasar nan zamu kasance cikin kunci da danniya. Kuma yanzu shi ke nan kana nufin ba wata hanya da zamu 6ulloma wannan lamarin?". 19 Hikaya Hamsin Basiru Harande Koda boka Larhat Ibni Khushubul Mannaf yaji haka sai ya dauko jakar tsafinsa ya baje ya shiga bincike tare da wasu irin sambatu. Sai da ya dauki sa'o'i yana yi sai kawai ya kyalkyale da wata irin mummunar dariya, sannan ya dubi Waziri ya ce, "Ya kai Waziri kayai sani cewa na samo mafita daya wadda daga ita ba wata". Cikin zakuwa Waziri ya ce, "Maza sanar da ni wannan mafita da ka samo". Boka Larhat Ibni Khushubul Mannaf ya ce, "Mafitar da na samo ita ce, za ka tara 'ya'yan Sarki baki dayansu kace musu duk mai son hawa karagar mulkin kasarku sai ya bada dadadana HIKAYOYI HAMSIN. Idan suka gaza sai ka basu kwanaki hamsin su shiga duniya wurin Malaman Hikayoyin da suka fi na kowa dadi su samo su zo su karanta ma. Muddin duk wanda ya samu nasarar yin hakan a cikinsu zai hau karagar mulkin ba tare da ya hallaka ba, kuma ya gudanar da mulki son ransa. Lallai wannan ita ce kawai hanya daya da za a bi, kuma makarin wannan sirri na sarautar kasarku. Amma idan ba ta wannan hanya ba, ina mai tabbatar maka cewa duk wanda ya hau sarautar a cikinsu sai ya rasa rayuwarsa kamar yadda ka sani face mutum daya, wato Affan". Koda Waziri Kwabis yaji haka sai murna ta 20 Hikaya Hamsin Basiru Harande kamashi, domin ya san ya samu hanyar da zai cimma burinsa. Waziri Kwabis ya duka gaban bokan ya yi godiya, sannan ya tashi ya tafi cike da farin ciki. Fadar ta cika makil kamar za ta tsage. In kayi duba izuwa 6angaren dama za ka gansu zazzaune su hamsin dai-dai akan wadansu kujeru na alfarma, kowannensu sanye cikin kayatattun suturu na sarauta, kowanne yana shan kamshi da nuna isa da izza, idan ka dauke Affan wanda yake karamin cikinsu, bai damu da girman kai ba. Waziri Kwabis ya mike ya fara magana da murya mai karfi da cewa. "Ya ku mutanen wannan birni na Mahbub! A matsayina na wazirin kasar nan, kuma Sarki mai rikon kwarya tun bayan rasuwar dan uwana Sarkinmu mai adalci. Ku yi sani cewa aba kaomai ne yasa na taraku a nan ba sai face sai don ku shaidi wata wasiyya da Sarki ya umarci in sanar da 'ya'yansa kafin ya bar duniya". Waziri Kwabis ya ci gaba da bayaninsa cikin farin ciki da mummunan kuduri a zuciyarsa. "Wannan wasiyya kuwa ita ce, Sarki ya sanar da ni cewa duk wanda yake son ya gajeshi, ma'ana ya hau 21 Hikaya Hamsin Basiru Harande kan karagar mulkin wannan kasa tamu mai albarka ya mulki jama'arta, ya zamo dole a gareshi sai ya bada dadadan HIKAYOYI HAMSIN. Sabo da haka yanzu zamu baku dama ku fara gabatar mana da hikayoyin ga duk wanda yake bukatar hawa mulki. Kuma duk wanda ta sa tafi dadi da kayatarwa shi zamu nada Sarkin wannan kasa. In kuwa ba za ku iya ba, to zamu baku kwanaki sittin ku shiga duniya wajen masana hikayoyi ku samo labaran hikayoyi masu dadi". Waziri Kwabis na kawowa nan a zancensa sai yai duba izuwa ga 'ya'yan Sarki ya ce, "Yanzu mene ne ra'ayinku akan hakan?" Su kuwa 'ya'yan Sarki da sauran al'ummar gari sai hankalinsu ya dugunzuma sabo da basu taba zaton hakan zai faru ba, kuma gashi cikin 'ya'yan Sarki babu daya da yake da masaniya ko kwarewa akan hikaya. Cikin sanyin jiki Bakar ya mike ya ce, "Ya Baffanmu, da yake dai an san cewa duk cikinmu ba wanda ya iya hikaya koda daya ce balle hamsin, sabo da haka mun yarda da a bamu kwanaki sittin mu shiga duniya neman ilimn HIKAYA." Koda Waziri yaji haka sai ya dubi sauran 'ya'yan Sarki ya ce, "Ku kun yarda da wannan shawara ta Bakar?". Gaba dayansu suka hada baki suka ce, "Mun amince". Waziri ya gyada kai cikin gamsuwa ya ce, "То 22 Hikaya Hamsin Basiru Harande daga gobe- za ku tafi. Kuma duk wanda ya wuce kwanaki sittin ya fita daga cikin wannan gasar". Yana kawowa nan a zancensa sai ya sallami kowa ya kama

Chapter 1 of 3