ya cije, yaki ya jawo
shi kuwa Sadauki sai kokarin janshi yake
a cikin wannan lokaci ne aka ga jikin Sarki
ya saki nan take ya fara yin amai, aikuwa
nan Sarki Yaki Safwan da kuma Yarima
Yazid suka kamo da tsananin firgici har ya
zama sun yi rige rigen tasowa amma Sarki
na ankarewa da su sai ya daka musu tsawa
da su dakata, shi kuwa wannan Sadaukin
55
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
koda ya jawo Sarki Gaban Sarakan Sai ya
cire wani katon gatare daga jikinsa ya daga shi zai sare kan Sarki, har idanuwan jama'a ya rufewa kawai sai gani akai
Yarima Yażid ya taho cikin iska ya doki
wannan Sadauki ya fadi kaka ya fada kan
gatarin ya cire masa makogaro cikin sauri
ya dauke Mahaifinsa da yake ta faman a
man jini ya kaishi sansaninsu. Kafin ya dawo filin dagar kuma sai suka ji wani irin nishi mai karfi ya karade filin gurin baki daya, wannan al'amari sai ya dugunzuma
hankalin duka jama'ar da suke wannan
gun, suka saka idanuwan sosai.
Aikuwa kafin kiftawar idanuwa Sai
ga Macijiya Burukul Kursum ta bayyna cikin tsananin tashin hankali.
A nan take Yarima Zaiyan ya dakata da yunkurinsa domin daga zuwanta har ta yabcari kadan daga cikin al'ummarsu ta yi
musu loma daya.
56
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
Daga Abdul aziz sani madakin gini
mai debe muku kewa akowane lokaci sai
mun hadu a cikin littafi na biyar dan jin ci
gaban wannan labari na TURBAR
GASKIYА
SHIN SARKI ABU ZAIYAN ZAI
SAMU LAFIYA?
WAYE ZAI KARASA KARAWA
DA WADANNAN ADAWAN DA SU
SARKI HUSAKA SUKA ZO DA SU?
SU WAYE ZA SU NASARA A
CIKIN WANNAN GAWURTACCEN
YAKI A TSAKANIN RUNDUNAR
MUSULUNCIN DA KUMA
RUNDUNAR KAFURCI?
YA YA ZA AKWASHE DA
MACIJIYA BURUKUL KURSUM A
CIKIN WANNAN HALI.
A TSAKANIN SHADILAT DA
GIMBIYA LUMSHAIRA WACECE
TAFI KAUNAR YARIMA YAZID.?
57
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
WANE NAMJIN КОKARI
GIMBIYA LUSHMAIRA ZA TA YI
HAR TA ZAMO YARIMA YAZID ZAI
AMINTA DA JARUMTAKARTА.
Sai mun hadu a littafi na biyu
58
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
TALLLA! TALLA!! TALLA!!!
A wani zamani can baya mai tsawo da ya
shude bayan shudewar mulkin fir'auna na birnin
misra an yi wata azzalumar sarauniya mai suna
Zuhaira bin Masrud.
Sarauniya zahuira tana mulkin wata
babbar kasa ce dake bakin gabar tekun bahar
sufiya kuma ta gaji sarautar ne a wajen
mahaifinta sarki masrud bin Zaurid
Sarki masrud ya kasance gawurtaccen
mayaki wanda yai shuhura zamaninsa kuma shi
a rayuwarsa babu abinda ya tsana sama da
ma'abota addinin musulunci ba komai ne ya
haddasa mummunar gaba tsakaninsa da
ma'abota addinin musulunci ba face akwai
watarana da wadansu fatake ma'abota addinin
musulunci da suka zo giftawa ta birninsa, sai
suka yada zango a gefen garin domin su yada
zango.
A wannan lokaci akwai wani takadirin
aljani a cikin birni na Sufras wanda muatena ke
59
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
bautawa a matsayin ubangijinsu. A kullum sai an
yankawa wannan aljani raguna uku, shanu, uku
da rakuma uku, kuma Sarki masrud ne da kansa
yake jagorantar wannan hadaya da ake yiwa aljanin mai suna burrata.
A ranar da wadannan fatake suka ya da
zango a bakin birnin Sufaras ne wata annoba ta
zo birnin ya zamana cewa gaba daya dabbobin garin da tsuntsayensu sun kamu da wata irin cuta
ta gudawa don haka sai suka rinka mutuwa wasu
kuma suka lafke ya zamana cewa ko ta shi basa
iya yi.
Bisa ka'idar hadayar da ake yiwa aljani burrata ana yanka masa lafiyayyun dabbobi ida
kuwa aka kuskura aka yanka masa mara lafiya
koda guda daya ne kacal a ranar babu wanda ya isa ya yi barci a garin kuma duk kanannan yar dake garin sai sun kamu da cutar da zasu yi ta
mutuwa haka kuma idan aka saba lokaci na yin
wannan hadaya to fa sai wannan bala'i ya afko. Sarki marud. yana samun dukkan biyan bukatarsa a wajen aljani Burrata bisa wannan
dalili ne baya yarda a sami matsala a ko kadan akan yi masa hadaya.
60
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
Lokacin da ake yin wannan hadaiya ga
aljani Burrata da yammaci ne sakaliya daf da
magruba tun da rana wannan annoba ta afku a
cikin birnin na Sufras al'amarin da ya
dugunzuma hankalin Sarki masrud ke nan ya
baza dakarunsa ko ina a cikin birane da kauyuka
na kusa a kan a nemo lafiyayyun dabbobin da
za'a yankawa aljani Burruta kafin rana ta fadi.
Ai kuwa har gefen la'asar ba'a sama
dabbobinba sai ga Dakarun da aka tura sun dawo
cikin gigita da dimauta, shugabansu ya zube
kasa a gaban Sarki masrud ya ce, Ya shugaba
mun duba ko ina a cikin biranc da kauyuka dake
kusa da wannan kasa tamu babu inda wannan
annonba bata je ba, mun rasa lafiyayyun dabbobi
amma akan hanyarmu ta dawowa mun ga
wadansu bakin fatake kuma suna da dabbobi
lafiyayyu fiye da adadin da muke bukata.
Koda Sarki jin wannan batu sai farin ciki
ya lullube Sarki Masrud ya ce, "Maza ku koma
wajen wadannan fatake ku siyo daddbobin da
muke bukata a wajensu komai tsadarsu kuwa,
idan suka ki siyar muku ko kwato su da karfin
tsiya ku zo mini da su, domin mu hanzarta zuwa
61
TURBAR GASKIYA --4
dakin bauta.
_MADAKIN GINI
Koda jin wannan batu sai Shugaban
dakaru ya mike tsaye da sauri yana mai cewa an
gama ya shugabana, nan take ya jagoranci
dakarunsa kimanin su dari biyu suka hau
dawakansu suka zaburesu da gudu izuwa gfen
gari
Su dai wadannan fatake da suka ya da
zango a gefen birnin sufras gaba dayansu basu fi
su ashirin ba kuma duk zur'a dayane na wani
attajiri da ake kira Abu Salhaif.
Acikin wannan Zuri'a akwai matarsa guda
daya da kuma dansa shima guda daya jal wani
matashin saurayii wanda baisfi shekara goma sha
hudu ba, shi ake kira da suna Salhif, sauran
mutane goma sha bakwan daga kannensa sai
matansu, da 'yayansu.
Abu Salhif na tsaye tare da dansa Salhif
yana koya masa yadda ake yaki wato suna kaiwa
junansu sara da suka cikin gwaninta a gefe daya
kuma matarsa da sauran abokan tafiyar na tsaye
suna kallonsu sai kawai suka hango kura daga
can nesa ta turnuke sama, sannu a hankali suka
hango dakaru bisa dawakai a sukwane sun
62
TURBAR GASKIYA --4
durfafosu.
MADAKIN GINI
A zaton su Abu Salhif yanfashi ne suka
kawo musu hari, har mazajen cikinsu sun
yunkura zasu zare makamansu su tari mahayan
sai Abu Salhif ya daka musu tsawa, ya hana su,
don haka sai kowa ya tsaya a inda yake har
mahayan suka kara so daf da su suka yi turjiya
suna sanye cikin kayan yakin dakarun birnin
Sufras.
Koda Abu Salhif da jama'arsa suka ga
cewa ashe dakarun birnin Sufra ne sai hankalinsu
ya kwanta suka mayar da takubbansu cikin kufe.
Cikin biyayya Abu Salhif ya risina ga
shugaban dakarun ya yi gaisuwa sannan ya се,
"Ya ku Dakarun Sarki Masrud me kuke bukata
daga garemu har da zaku kawo mana ziyarar
bazato a irin wannan lokaci alhalin ko shigowa
cikin birnin naku ba mu yi ba?
Koda jin wannan tambaya sai Shugaban
Dakarun ya sauko daga kan dokinsa ya matso
daf da Abu Salhif ya ce, "Ya kai wannan attajiri
tsohon abokin cini kinmu ka yi sani cewa Sarki
ne ya tro mu gareku domin ku siyar mana da
raguna uku, shanu uku rakuma daga cikin
63
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
dabbobinkudomin mu bayar da jinin su ga abin bautarmu gunku Burrata."
Koda jin wannan ba tu sai hankalin Abu Salhif ya dugunzuma ya ce, "Subhanallahi ya kai
wannan badakare ka yi sani cewa mu musulmai
ne wadanda suka yi imani da bautar Allah Sarki guda daya wanda shi ne ya halicci komai da kowa har da shi gunkun da kuke bautawa, ta yaya zamu bayar da dabbobinmu kuje ku aikata
wannan mummunan sabo da su, ai idan muka
baku tamkar muma mun yi imani da abin da kuke bautawar ke nan, ku koma ku gayawa Sarki Marud cewa ni attajiri Abu Salhif nace ya yi hakuri ba zamu iya siyar masa da dabbobinmu a,
koda jin wannan ba tu sai shugaban dakarun ya tari numfashin Abu Salhif yana mai daka masa
tsawa ya ce, "Sarki ya bamu umarni idan har baza ku bamu wadannan dabobbi ba lallai mu
karbe su da karfin tsiya koda jin haka sai Mazajen ayarin na Abu Salhif suka zare takubbansu da nufin su yaki dakrun Sarki Masrud, amma sai Abu salhif ya sake daka musu
tsawa a karo na biyu ya ce, "Baku da hankali ne ta yaya zaku iya yakar dakarun kimanin dari
64
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
biyu alhalin gaba dayanmu bamu wuce mu goma
sha ba."
Nan take mazajen suka sake mayar da
takubbansu cikin kufe suka koma bayan Abu
Salhif suka tsaya a wannan lokacin ne bakin ciki
ya lullube Salhif har zuciyarsa ta kama tafarfasa
kamar zata kone jikinsa ya kama tsuma koda
shugaban dakarun ya lura da halin da Salhif ke
ciki sai ya bushe da dariya mugunta sannan ya
dafa kafadar Salhif ya се.
"Yaro ka yayyafawa zuciyarka uwan sanyi
idan ba so kake yanzun nan jini zuri'arku gaba
daya ya zube anan ba."
Koda jin wannan ba tu sai Saihif ya sake
fusata ya yunkura zai kaiwa badakaren Sara da
takobin hannunsa amma sai Saihif ya yi wuf ya
ruke hannunsa kuma ya zabga masa mari har ya
fadi kasa, cikin tsananin mamaki Salhif ya shafe
kuncinsa sa'adda hawaye ya zubo masa ya
kurawa mahaifinnasa idanu saboda wannane
karo na farko da ya taba marinsa amma ko bakar
magana bai taba gaya masa ba, nan take Abu
Salhif ya dubi Shugaban dakarun ya се.
"Za mu baku dabbobin da kuke bukata
65
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
amma ka gayawa Sarki cewa bukatarku ba zata
biya ba ta hanyar amfani da da dabbobin
ma'abota addinin musulunci koda gama fadin
hakan sai Abu Salhif yasa aka kwanto raguna
uku shanu uku da rakuma uku aka baiwa
dakarun suka tafi da su.
Bayan tafiyars ue Abu Salhif ya mikawa
Salhif hannunsa ya kama ya tashe shi tsaye
sannan ya dube shi ya ce, "Ka yi hakuri ya kai dana inda ban mareka ba bisa kuskuren da ka
aikata da tuni an kasheka a gaban idanuna kasani
cewa kai ne ka dai a gareni ni da mahaifiyarka don haka ba ma son mu rasaka ku ta shi mu kimtsa mu
bar garin nan domin abin da zai biyo baya ba mai kyau bane,."
Koda jin haka sai kowa ya ta shi aka hau
kimtswa nan da nan kowa aka gama shiri aka kama
hanya domin ci gaba da tafiya izuwa birnin na
gaba.inda za'a gudanar da harkokin fatauci.
Al'amarin Sarki Masurd ana kai masa
wadannan dabbobi sai yai shiri ya tafi izuwa dakin
bauta aka yanka dabbobin aka bayar a jininsu ga aljani Burrrata kamar yada aka saba
Faruwar hakan ke da wuya sai suka ji aljani Burrata ya kwarara uban ihu al'amarin da ya janyo
66
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
dakin bautar ya kama rugujewa, mutane dake ciki
suka dimauce suka rinka zubewa kasa sumammu,
Cikin firgici Sarki Masrud ya zube kasa
gaban gunki Burrata yana tuba.
Nan take gunki ya bude baki ya ce, "Maza ka
tura dakaru su je su kashe wadannan bakin fatake
domin jinin dabbobinsu bai magance mini
kishirwata ba face Karuwata kuma ka sani cewa
lallai sai an yi asarar dubban rayuwaka a cikin
Kasarka saboda fishina idan baka hanzartaa samomin
jinin da na saba sha ba ko wa sai ya dandana
kudarsa."
Koda jin wannan batu sai Sarki masrud ya
sake dimaucewa ya mike tsaye zumbur yana mai
kwalawa Sarkin yakinsa kira ya fice da gudu.
Kadan ke nan daga cikin littafin
JAHADI wanda zai zo nan bada jimawa ba.
Naku har kullum Abdul'aziz sani madakin gini
Dukkan mai son wannan labari da kuma
sabon labarina WASIKAR JINI SAI KU SAME SHI
A SABON BRANCH NA JAKRA CITY BOOK
SHOP DAKE KASUWAR SABON GARI
MARKET KUSA DA MADAKIN GINI BOOК
SHOP ДБЕМ
Sai mun ji daga gareku za a iya samunmu a
wannan numer kamar haka
67
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
08162707231-08069524699
TALLA! TALLA!! TALLA!!!
SAKON MUTUWA
A tsakar dajin mai yalwar korayen
ganyayyaki suke tsaye su biyu a tsakiyar
koraye ganyayyaki wasu jibgajibga aljanu
suna tsaye a gefensu kowane su rike yake
da jariri a hannunsa cikin tsananin farin
ciki da ganin juna.
Sarakuna ne masu ji da sarauta
suturun dake jikinsu kawai zai tabbatar
maka da haka kowane yana rike da jariri a
hannunsa
Sarki
2
Madhan shi ne Sarki kasar
Arfat, sai Sarki Azkam shi ne Sarkin kasar
Yuhud abokane ne su wadanda aka yi
68
L
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
shelar a duk duniya babu abokai masu
kaunar juna da amincin sama da su,
sannan babu wasu sarakai masu girman
masarauta da tumbatsar arziki face su,
kuma duk da sun kasance abokan gugayya
a bangaren sarauta dukiya gami da jin kai,
basu zame masu yiwa juna bakin ciki ba
haka ma shi yafi musu dadi a rayuwa
domin basa so ace a cikinsu wane yafi
wani, sun fi son su zama suna tafiya daidai da juna.
Abu guda ne ya banbanta wadannan
Sarakai Sarki Madhan yana mutukar son
ganin ya haifi 'ya mace ya yin shi kuma
Sarki Azkam kuma ba shi da burin da ya
wuce ace ya samu haihuwar da namiji,
amma sai aka samu akasi a shekarar da
matarsa zata haihu sai ta haifi 'ya mace shi
kuma Sarki madhan sai matarshi ta haifi
da namiji, wannan dalili ne yasa suka yi
wa juna alkawarin musayar yaran ta yanda
69
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
babu wanda ya san da haka, face aljanunsu
guda biyu kuma masa rike sirrikansu.
Ranar daya lokaci guda aka samu
wannan haihuwa a lokaci da matan suka
haihu sai Sarki Madhan da Sari Azkam
suka badawa matansu hodar banjo sukа
kama barci ta wannan yasa suka saka
aljanunsu suka kwashe su zuwa wannan
daji.
Koda Sarki madham da Sarki Azkam
suka dubi juna sai farin ciki ya baibaye su,
Sarki Madhan ya ce, "Ya kai Aminina hakika
godiya ba zata kare ba bisa yanda muke
mututta juna kuma muke daraja juna lallai
daukakarmu da boyayaryamu ba zata taba
rugujewa face an samu ranar da dayanmu zai
ji bazai iya rufe sirrin dayanmu ba, dan haka
ina mai horonka da ka yi yaki da zuciyarka
wajen gujewa wannan, sannan ina mai kara
jadda maka akan ka tsare wannan sirrin
kamar yanda zaka tsare rayuwaka dana ya
zamai naka 'yarka ta zama tawa, har abada
70
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
babu wata rana da zamu saka ido akan wani
daukaka da zata biyo baya a lokacin da yaran
nan suka girma, in har mun kawar da wannan
to babu shakka amincinmu zai cika gaba da
daurewa har abada."
Koda Azkam ya ji wannan ba tu sai ya
mika jaririyar dake hannunsa ga amininsa shi
ma amininsa ya mika masa jaririn. Sannan
Sarki Azkam ya ce, "Babu wata rana da
zuciya ta isa ta kawo mana sukar junamu
halas malak na bar maka wannan yarinya
kamar yanda halas malak ka barmin wannan
yaron, dan haka koda masifar wuta da ruwa
zasu cudu a cikin kasata ya zamana bani da
maganin wannan masifar face ďanka to ina
mai tabbata ba zan taba bukatar shi daga
gareka.
Da jin haka sai Sarki Madhan ya yi
murmushi ya rungume Sarki Azkam suna
masu murmushi. Da haka kowannensu ya
koma ya haye kan aljaninsa.
Suka Bace daga cikin dajin cikin
tsananin farin ciki da nishadi.
71
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
n
Tirka shi, kirarren labari ne da na
ratattako muku shi mai suna
SAKON MUTUWA yana nan tafe
daga ni Abdulsalam Adam shitu bature gadon
kaya
D
A
08162707231
Ni Abdulsalam ina kara yiwa makarantana
tuni da fitowar littafin DAKARU KASHI NA
HUDU SANNAN NA BIYAR SHI MA YA
FITO TARE DA WANNAN LABARI IN
BAKA SAMU GARAZAYA KA NEMI NAКА.
MUNA KARIN SANAR DA
SHAHARARREN MARUBUCIN YAKIN NAN
MARUBUCIN GIMBIYA ZAHRA DA
ADDININA WATO MUKTAR KWALISA YA
ZO MUKU DA SABON LITTAFI MAI SUNA
RANAR GAMO YANA NAN A
KASUWA
72
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels