Sarki kowane Sarki akwai
gawurtaccen Sadauki ashirin a cikin ashirin
kuma aka zabi goma wanda suka fi kwarewa ya
zamana sun kai su talatin kowannensu ba sai an
fada ba da gani kasan maye zai ci mutum.
Lokacin da aka fito da da Wadannan
samudawan Dakarun kowa dakc gurin sai da
gabansa ya yanke ya fadi da ganinsu domin
kuwa mamaki ne ya kama su suka rasa ta ina aka
fito da wadannan samudawan abinda jama'a
basu sani ba shi ne kebantattu ne da aka boye su
ake kuma kula da lafiyarsu ake saboda kada
ciwo ya kama su su mutu, irin mutuwar cuta ba a
filin daga ba. Domin a ganinsu wannan ba
Karamar asara bace.
Acan kuma sansanin Sarki Abu zaiyan
lokacin da dan aiki ya baro sansanin sai Sarki ya
tara manyan kasar da dukkanin jama'ar da ake
tafe dasu.
Koda kowa ya nutsu sai Sarki ya
numfasa ya ce, "Ya ku jama'ata ku yi sani
cewa wannan shiri ne abokan gabarmu
suka zo mana da shi, domin sun san cewar
idan har muka yi yakin mamaya da su
25
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
suna ganin za mu samu nasara a kan su, sai
suka yi dabara suka bukaci da mu yi yakin
daidaiku za su iya samun nasara a kanmu,
shi ne dalilin da ya sa suka bukaci da ayi
wannan yakin.
Sarki ya ja numfashi yana kallon
jama'arsa sannan ya ci gaba da cewa.
"Hakikanin gaskiya suna da manyan
sadaukai masu kumari, da za su iya samun
nasara a irin wannan yakin, amma ni zan
nuna musu cewar ba ma dogara da wani a
cikin gogaiya da juna, zan nuna musu da
Allah muke takama dan haka na hutar da
kowa a cikin mayakana, ni da Sarkin yaki
Safwan da kuma Yarima Zaiyan mu kadai
ne zamu dinga karawa da wadannan
dakaru har sai mun ga karshensu, in har
kuma sun sauya mana yarjejeniyar da
muka Kulla a tsakani to babu shakka za mu
tarc su mu yi yaki da su babu ji babu gani"
Koda Sadauki Zaiyan da Sarkin yaki
26
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
Safwan suka ji wannnan Sanarwa sai
kawai murna ta kama su, ka ji maza,
maimakon su ji tsoron wannan gumu da za
su yi amma su farin cikin suke.
Lokacin da wasu daga cikin manyan
mayakan kasar Birnin Baitul haural suka ji
wannan sanarwa sai bakin ciki ya kama su,
domin kuwa ba haka suka so ba tuni sun
fara wasa makamansu saboda kawai suna
ganin lokacin da za su wasa jininsu ya yi,
amma jin wannan sanarwa sai yasa
wasunsu har zubar da kwalla su kai.
A cikin masu kuka kuwa har da
Gimbiya Lushmaira hankalinta ya yi
mutukar dugunzuma ainun da kyar ta iya
cin abincin da aka rarraba musu, ita kuwa
Shadilat sai ta danne duk da ta so a ce ta yi
wani a bu a cikin wannan yaki.
A wannan lokaci da Sarki Abu
Zaiyan da Yarima Zaiyan da kuma Sarkin
yaki Safwan suna tsakar filin gurin da
27
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
suka yada sansani su uku suna tattaunawa,
fuskar Yarima Zaiyan da ka gani kasan
cewar yana cikin tsananin bakin ciki.
Aikuwa suna nan tsaye sai ga Kora ta
tokare sararin samaniya lokaci guda kuma hargowar kafurai ta cika kunnawansu ta batse.
Koda Sarki Abu zaiyan ya ga
wannan sai ya yi murmushi ya cе.
"Matsoratan sun fito ya kamata ace
دو mu shirya dan a fara gwagwarmaya.
Koda jin wannan batu sai Yarima
Zaiyan ya ce, "ai kuwa in haka ne bari na
isa gare su na sanar da su cewar su shirya."
Sarki Abu Zaiyan ya ce "Ka zama
cikin shiri kawai ai sun fi ka gaggawa domin suna ganin cewar akwai nasara.
Aikuwa Sarki bai yi aune ba ya ga
alamun sun fara kewaye filin gurin har ya
zamana an ajiyewa shugabanninsu kujerun alfarma da za su zauna. nan take shi ma
28
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
Sarki ya fara sa jama'arsa da su kewaye
filin nan da nan ya zama ankewaye filin
gurin baki daya.
Sarki da Yarima da' Sarkin yaki
kuwa sai suka kara kebancewa da fara
shiri.
Daya daga cikin Manyan Adawan Su
Sarki Madham sai ya fito tsakar fili da
wani garjejiyar gudma a hannunsa wanda
tsaye da kauri Gudumar zata iya yin
girman garjejen kato, sannan hannunsa na
dama kuma rike yake da wata karkuwa,
katon sai faman ihu yake yana dokan
jikinsa yana huce yana aibata addinin
musulunci.
A wannan lokacin su Sarki Abu
Zaiyan ba su ma fitar da wanda zai fara
karo na farko ba.
Koda ganin wannan kato yana ta ihu
da wadai ga musulunci sai ran Yarima
Zaiyan ya baci ya dane dokinsa da alamar
29
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
zai hau ya tunkari wannan sadauki.
Sarki abu Zaiyan sai ya yi tsawa a
gare shi ya dakatar da shi, ya ce, "Bana
bukatar ka tunkari wannan wannn aikina
ne, kafin wani ya yi yunkuri sai Sarki ya
zaburi doki ya nufi filin cikin kuwa da
kabbara.
Daukacin abokan gaba ganin Sarki a
cikin wannan fili sai suka cika da mamaki
Sarki Tarmas da sauran sakaran sai suka
fara murna suna masu kara yiwa Wannan
kara sadaukin karfin gwiwa. Saboda ya
yiwa Sarki farad daya wanda yin hakan
tamkar samun gawurtacciyar nasąrarsu ce.
Shi kuwa Sarki sai ya yake ji kamar
shi suke kara karfin gwiwa ya kara yiwa
dokinsa kaimisabin da ya kara basu
mamaki lokacin da Sarki ya isu kusa sosai
su suka lura a she babu makami ko
garkuwa a hannunsa.
Wannan abu ya kara sawa suka saka
30
TURBAR GASKIYA--4
rai na samun nasara.
MADAKIN GINI
Lokcin da Sarki Abu Zaiyan ya isa
ga wannan Sadauki batare da wani
makami ba, sai doka tsalle tun saura baifi
taku goma a tsakaninsu ba ya dira a
gabansa.
Taron 'yan kallo suka mai da kansu
sama suna ganin yanda Sarki abu Zaiyan
ya wulwula a sararin samaniya.
Shi kansa Sadaukin dake ta faman
jijjiga jikinsa yana kurari ganin irin shillon
da Sarkiya yi sai abin ya ba shi mamaki
amma kuma da yaga Sarki Abu Zaiyan a
gabansa kamar giwa da 'yar karamar
'yarta sai ya 6ace da wata shu'umar
dariya.
Yana dariyar yana nuna Sarki da
hannunsa yana kara kyakyacewa, wannan
dariya da wannan Sadauki ke yi sai ta
fusata ran Sarki Abu Zaiyan ya dunkule
hannunsa da niyar ya dankarawa wanna
31
TURBAR GASKIYA--4 MADAKIN GINI
basamuden Sadauki duka, sai aka daka
masa tsawa daga bayansa, wannan dalili
ne yasa ya fasa aniyarsa ya juya don ganin
mai aikata wannan sako a gareshi. nekan
sKoda ya waiga sai yaga Sarki
madhan Sarki Husaka, tare da Sarki
Tarman suna nufowa inda yake tsaye.
iB Koda ganinsu sai Sarki Abu Zaiyan
ya yi murmushiya kuma dubesu Pa
wufakance ya yi kaki ya tofa a tsakaninsu.
nollinyin wannan kaki a garesu yasa
sauran dakarun suka fashi dawani
hargitsantsan ihu na kai Bara suna masu
gyara makamansu suna kokarin yin kan
Sarki abu Zaiyan a fusace, sai Sarki
Tarmas ya daka musu tsawa suka
tsaitsaya. OUN RORY avish S
asA can ma gefe sansanin su Sarki
kuwa sai Yarima Zaiyan da Sarkin yaki
Safwan suka nufo su a fusace. Sarki Abu
Zaiyan ya yi saurin dakatar da s ed
132
TURBAR GASKIYA-4 MADAKIN GINI
Koda akaa samu nustuwa na dan
lokaci kuwaa na yi dan uwansa kallon
banza, sai Sarki Abu Zaiyan ya dubi
dukkan Sarakan uku a wulakance ya ce,
"Ina mai bukatar ku bamu fili domin fara
gugaiya da abokan gaba a sanina daku
banda Karfin baki da surutun cece kuce
babu wani abu da kuka fi kwarewa akai
nan fili ba gurinku bane dan haka ku koma
mazauninku ku kalli yanda jini zai tsiyaya
a kan kasa, yanda harshe zai karci kasa,
lallai ba zan gusheba ina gidadddaba
wadannan Samudawa face na ga bayansu
dan haka ku koma ku yi saurare ku kuma
zuba idanuwan."
Koda Sarki Tarmas da kuma sauran
sarakan suka ji wannan umarni daga Sarki
Abu Zaiyan sai suka hada baki suka bushe
da wata shu'umar dariya keta.
Wannan dariya ce ta fusata ran Sarki
ya daddage ya doka musu tsawa wacce ta
33
TURBAR GASKIYA--4
MASAU
MADAKIN GINI
yi sanadin tsayar da dariyar ta su, sannan
ya nuna su daya bayan daya ya cе.
Dukkanin wanda ya kara yin sakaci a
cikinku yanzu take zan tsaida numfashinsa
ya zamana na yi masa bakin ciki da ganin
gagarumar bajinta da za a yi a wannan filin
daga."
Saboda iirin kakkarfar lafazi gami
da budaddiyar muryar da da Sarki Abu
zaıyan yayi amfani da ita sai dukkaninsu
jikinsu ya yi sanyi suna ganin zai iya
aikata abinda ya fada sai suka yi gum.
Da kyar Sarki Madhman ya maso
kusa da Sarki ya ce, "Ya kai abokin
gabarmu muna so mu san yawan Dakaru
da za a yi wannan kwafsawar da su domin
sanin adadin zai amfanar da mu da ku, mu
gane dawa-dawa za a kara.?"
Koda jin wannan ba tu sai Sarki Abu
Zaiyan ya ji wannan ba tu sai ya yi
murmushi ya ce, Bana bukatar sanin
34
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
Π
yawan dakarunku daga gareku domin na
riga na 'yarga yawansu su kimanin talatin
ne, wadanda aka tace daga manyan
Zakarun a cikin kasashenku, kamar yanda
dukkanin giman wadannan adawa naku
suke kuma rike da manyan manyana
makamai masu tsananin girma da bantsro
to ina mai sanar da ku cewa yawa
Dakarun da zasu fito filin da mutum uku
ne kacal, NI Sarkin yaki sai kuma Yarima
Zaiyan kuma a dukkaninsu babu wanda zai
fito filin daga da makami ko garkuwar
kare kai, sai a ciki a filin ne zai kwace na
Makami kare kai da na barautar rayuwa
mu yi gutsi-gutsi da sassan jikin
Sadaukanku sannan a kowanenmu zai kara
da mutum goma daga cikin talatin din da
kuka tanada duk wuya duk rintsi wannan
ba zata canza ba, da yardar Sarki Allah
mai iko mai yin yanda ya so daga garcshi
nasara take kuma daga gareshi muke nema
35
CADA TURBAR GASKIVA --4 MADARKIN GINTUT
cikin natunsasdi yartarsa suka Kaure аa kab8aLoaein aa sarakan uky daskuma
m
mamayes(fbaomina gaiin
nasara sun gani da naka lm sa
SwSXOREaka natsa da iha da kabafaina kbwane Sansaf? liSadhu
TSAMukane
jikinsa yand dagamanfib sgsb nilil otil
Nan
SarkiTamagrda BSdki ipusinh inеM
madhman suka kölha KelHan
zauna suna RanoH Wan ekh2 da rath cikr ikdmidisuh san Hasara tasdm
nanngh kuwa SavAbulZa!Sgush!skKk
dubi gabas ya i sújfada ga A ad ya mikë va daga hkrfiry yiadugraKaiean ya shafa ya dubi Sadaukst glgegU
TURBARUNGRAVA --4 A-MADAKIN GINUT
S MAoiqaskiya ibanda Sarki Abu
Zasi daesbrovkumalbai san tsovo ba
daswobu sthaeksisay ydlijis tsoron Makanu
ddhnskuskunburejilimsSadauki makamu
abussaisdaduwat ugaba neшрasкyanda
desAsengokeanawa16u26alakaisikacels
wata bijimar Mesa demakelkwamto raka
nuvfdrfasi, obwarwans kardaid Adolesyasa
Babnugighdakisal sladowaryid igabaşb
müsammansrii makami näakaresdangi sdav
yaale bulimumsay sanithal list
Amma shi Sarki AbuZaiyan kó ldra2
dakh dayilba fataasa kawal stbja daga
aikyw adiTadaninoVkaton uyadsshamamnales
Sa Zalyint yadwdbulmasaukatuwar
garkwarsaundalshiyanutaiy GallawalAbud
Zalyan bayangut BY TaVin sb slisri ses
Koda SarkiAbplaiyasyauba gahowaak
wannan garkowa uamkaMansbakaubwari an
habotavsaboda isananin gudon dahake ares
waki ithskinakara nakeniammas kafini kuw2
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
ya ankara tuniSarki Abu Zaiyan ya tafi ga
garkuwar nan sai da ya kusa isa gareta
sannan ya daka tsalle ya takata ta kowa
kara masa karfin ta shi sama koda ya tafi
cikin iska tamkar an har ba shi bai sauka
ako ina ba da kafafuwansa biyu ya doki
kirjin Sadauki Makanu.
Sarki Abu zaiyan ya fado kasa baya
da taku biyar saboda tsananin bugun da ya
yiwa Makanu shi kuma Makanu ya yi
amfani da karfin kirijinsa ya yi cille da
Sarki Abu Zaiyan.
Koda Sarki ya gansa a kasa ga kuma
Sadauki Makanu a tsaye tamkar ba shi ya
yiwa wannan dukan ba, sai ran Sarki ya
6aci, kafin ya yi aune Makanu ya ta so
masa haikan da niyar ya rugaza shi da
katuwar gudumar dake hannunsa.
Gudun da Makanu yake shi ya
tsorotar da zuciyar su Yarima Zaiyan da
sauran jama'a domin tun kafin Sarki ya
38
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
farga ga shi kuma ya fargar amma bai yi
wani yunkuri ba duk da cewar saura kiris
Makanu ya isa gare shi abinda basu sani ba
kofar ragowa ya yi masa sai da Makanu ya
gama bada karfinsa guri guda sannanne
Sarki Abu zaiya ya yi katantanwa ya fille
kafafuwansa.
Aikuwa sai ga Makanu ya tashi sama
tamkar wanda aka saka kugiya ta shilla
sama da shi, kana ga gudumarsa ita ta yi
sama. Ganin haka Sarki ya yi sufa ya
dauki Gudumar kafin Su iso kasa, sai ya
saita tsakiyar kan Makanu ya buga masa
ita ai kuwa ID DCsai jini aka gani ya yi tsartuwa
a filin gurin, gawar Makanu ta silalo kasa
sai ga shi jini sai zuba yake ta ko'ina yana
shuri-shiru mutuwa.
Nan take Hangaren Sarki Abu Zaiyan
aka hau tafi da shewa ana kabbara da kiran
sunan Allah, shi kuwa Sarki Abu Zaiyan
sai ya shiga zarya yana jiran wani mai
39
TURBAR GASKIYA--4
karar kwanan a tsakiyar fili
MADAKIN GINI
Wannan al'amari ba karami mamaki
ya bawa kowa ba a cikin sahun sahun
kafurai da manyan adawan da aka tanada
dan maganance musulunci da kautar da
TURBAR GASKIYA.
Amma sai suka sauri suka turo wani
Narkeken kato wanda ake masa lakabi da
suna Jaura, shi dai wannan Sadauki an
haife shi a na lokacin da ake muku-mukun
sanyi wanda kuma saboda tsabar
haihuwarsa da a ka yi da abubuwan
al'ajabi a wannan lokaci haka ya kasance
har sai da Lokaci ya wuce sannan aka saka
masa riga da wando kai sannan ne ma aka
fara gasa masa cibiya, wannan dalili ne
aka saka masa suna Jaura, kuma a duk
lokacin da wannan Sadauki ya fi saukaka
al'amuran al'umma shi ne lokacin Jaura,
baya fada ko mai ka yi masa.
Dan haka Sai Jaura ya fito a cikin
40
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
hargitsantsan gudu da niyar ta take Sarki
ya yi tamole da shi. Kowa dake filin sai da
ya ji faduwar gaba da fitowar Jaura domin
girmansa ya yi Makanu sai biyu sannan
kumarinsa ya ninka na Makanu ga shi baki
wuluk ko dan haske rahma babu a fuskarsa
uwa uba ga irin makamin da yake rike da
shi, wani dogon mashi ne amma bakinsa
mai tsini ne da shi wani fataitane mai baki
shi da wanda idan aka su ke ka da shi babu
mamaki sai ya zaftaro duk wani abu da
yake cikin cikinka.
Koda ya nufo Sarki Abu Zaiyan da
wannan makami cikin tsananin gudu
wanda yasa kasa girgiza, koda ya rufo
Sarki sai Sarki abu Zaiyan ya juya da baya
ya fita da gudu kamar ya ji tsoro wannan
al'amari ya saka su Sarki Tarmas dariya
suna ganin Sarki tsorata ya yi, koda Suka
zuba tsare tsakanin Sarki Abu Zaiyan da
Jaura sai suka ci gaba da falfalawa Sarki
41
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
yana zagayawa da Jaura a fili har kusan
rabin sa'a a wannan lokaci kuwa sai Jaura
ya tsaya yana haki, shi kuwa Sarki Abu
zaiyan sai ya tsaya a gabansa ya ce.
"Yanzu ne ya kamata mu yaki juna
ni da kai."
Kafin Jaura ya yi wata magana tuni
Sarki ya yi kansa nan take suka kauri da
hargitsantsan yaki suna kai sara da suka
babu ji babu gani, dukka wani sara da
jaura ya ke kaiwa Sarki sai Sarki Abu
zaiyan ya kauce, a haka nan ma Sarki ya
Kara wahalar da Jaura har ya zamana jaura
ya fara yin laushi da kai sara da suka,
amma saboda tsananin taurin rai da karfin
hali bai fasa ba, shi kuwa Sarki Abu
Zaiyan sai ya tikirkire ya dunkule hannu
ya shammace Jaura ya dokan masa
mukamuki da hannun nasa.
Sadauki jaura ya shamye dukan
tamkar sauro ne ya cije shi ya kawowa
42
TURBAR GASKIYA -4 MADAKIN GINI
Sarki cafka da niyar ya daga shi sama ya
jefar da shi sannan ya bi shi da suka,
aikuwa sai Sarki ya kauce jaura ya kara
kai hannu nan take ya yi sa'ar damkar
Sarki Abu Zaiyan ya daga shi sama sai ya
daga shi ya dankara Sarki da kasa,
maimakon Sarki Abu zaiyan ya fadi kasa
ya ji ciwo ko ya karkarye sai kawai aka ga
Sarki ya dirga akan kafafuwansa daram,
ganin haka Jaura ya kawo suka, Sarki ya rike mashi da hannunsa tamau.
Jaura ya ja mashi da iyaka karfinsa
mma sai ya ji ya kasa kwace, dan haka sai
ya kawo mangari da Garkuwarsa, shi kuwa
Sarki Abu zaiyan sai ya yi matattakala da
Garukuwa ya tafi a sama ya doke Jaura a
fuska, wannan dalili ne yasa Jaura sakin
Mashin ya tafi taga taga zai fadi nan take Sarki Abu zaiyan ya loma masa wannan
mashin a ciki, ya kuma zaro Mashi lokaci
guda, Sai ga Jaura yana ihu,'ya'yan
43
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
hancinsa hanta kuda da sauran kayan ciki
sun yi fitar burgo
Koda faruwar Wannan al'amari sai
kuwa da ihu ya cika gurin baki daya aka
kama Kabbara, mamaki irin
Sadaukantakar Sarki Abu Zaiyan ta cika
zuciyar Yarima Zaiyan da Sarkin yaki
Safwan da Kuma Lushmaira da kuma
Shadilat da sauran jama'ar da suka taho
dan yi jahadi.
Su Sarki Tarmas kuwa sai suka ji
kamar su fashe da matsanancin kuka
saboda ganin 6arnar da Sarki ya yi musu a
dan kankanin lokaci ya karar musu da
sadaukan da idan da fadan Yamutse akai
da tuni sun kashe ya kai Dubu goma amma
sun salwanta batare da sun ji gabata Sarki
ba, nan take Sarki tarmas ya dubi Sarki
Madham ya ce, "Ai kuwa ba wuka muka
dauka muka dabawa kanmu ba ya ya kuke
ganin zamu samu nasara alhalin a cikin
44
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
majiya karfin talatin da muke ji da su, biyu
sun tafi, ta hanyar Sarkinsu kadai. Kada ku
manta a kwai Sarkin yaki Safwan mun san
kwazonshi ba tun yau ba, ga kuma Yarima
Zaiyan wanda labari ya zo mana cewar shima tsakwakurine."
Koda ya kawo nan a cikin batunsa
sai Sarki Husaka ya ce, "Haba ya kai Sarki
Tarmas kada ka manta, da waye Sarki abu
Zaiyan ai ku da za a samu lagonsa ba
yanzu ba, kai da ka zuba ido akwai ribar a
nan gaba.
Kafin su ankara sai suka ji ihu wani
Barden ya fito ganin wannan katon da ake
Kira Rislalu sai hankalinsu ya kwanta
domin kuwa shi kuma bai da wani lokaci
da aka taba nasara akansa, duk irin yaki da
ya yi a duniya wanda a kalla ya yi yakukuwa dari biyar, ba'a taba samun
lokacin da aka lakuci koda yatsansa ba,
saboda tsananin masifarsa a filin daga ko
45
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
jinin makiya bai taba wanke masa fuska,
saboda zafin namansa kuwa sai ya kashe
mutum biyar a sa'ili daya
Dan haka ko da ya fito sai suka kara
mai da hankali a fili, bai Kai Jaura tsaho
ba amma dai ya fi Jaura kauri shi a cure
yake guri gudu, ya kware wajen raba hanta
da jini, sannan ya kware wajen sarrafa
masana iya yaki, takobi ce guda biyu a
hannunsa dukkaninsu basu fi kamu uku
uku ba, yana tafiya yana jijjiga kwanjinsa
yana motsa ga66ansa dan karamin bante
ne a jikinsa kawai dan haka surorin jikinsa
duka a waje.
Sarki Abu Zaiyan ya na rike da
mashin da Ya hallakar da Jaura, sai ya
wullar da shi gefe, a wannan karon sai ya
tsaya yana murmushi, shi kuwa Risalu sai
ya tsaya yana hararar Sarki. Wannan
al'amarin ne ya fusata Sarki Abu Zaiyan
ya kukan kura ya yi kan Risalu, aikuwa
46
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
yana isa gare shi sai Risalu ya daga
kafarsa cikin a zaba ya doki Sarki a kirji,
Sarki ya tafi da baya ya fadi kasa.
Cikin fushi Sarki ya mike tsaye ya
fursa da yawu, ya kara yin kan Risalu da
gudun koda ya isa kan Risalu sai Risalu ya
soke Takobin ta shi guda biyu a jikin
bantansa ya kama Sarki ya daga shi yasa
ya wujijjiga shi ya cilla shi can gefe daya.
Abin da Sarki ya fara lura da shi ga
wannan Sadauki ba a yi masa shigar burgo
domin a kasa yake, yana iya fahintar duk
da irin yunkurin da ka zo masa da shi, dan
haka sai ya daina binsa, shi kuwa sokon
sai yake tsammanin Sarki tsoro ya ji dan
haka sai ya nufo Sarki yana mai kiran
Sarki da hannu wato yazo Sai Sarki yake
ja da baya har ya zamana Ya takure Sarki
Abu Zaiyan ya kai shi karshen inda jama'a
su ka yi musu da'ira, Sarki na ja da baya
shi kuma na kusanto Sarki, ai kuwa sai ya
47
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
yi sufa ya kamo Sarki da hannu daya ya
daga shi sama, koda Ya daga Sarki sama
ya kama jijjiga shi yana kokarin ganin ya
runtuma shi da kasa, shi kuwa Sarki a she
ya dauke takobi daya daga jikin bantai din
Risalu aikuwa nan take Sarki ya
shammace ya soka masa takobin a cikin
hammatarsa.
Wani abin mamaki sai Risalu ya yi
cilli da Sarki ya kuma kama kotar Takobin
ya cirota daga hammatarsa ya kurma wani
uban ihu na fusata yabi Sarki da niyar ya
danne Sarki ya ja daga ya daina ja da baya
lokacin da ya iso gaban Sarki sai Sarki ya
kama kai masa duka da hannu da kafa
aikuwa sai salon fadan ya sauya nan suka
shiga kaiwa junansa duka da hannun da
Kafa suna karewa a wannan lokacin ne
kowa ya samu naushi a baki har sau uku.
A sannane suka ja da baya, kamar
wasu Zakaru, wannan al'amarin ba
48
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
karamin yiwa Sarakan uku dadi ya yi ba
domin ganin yanda Risalu kawai ke walar
da Sarki.
Shi kansa Sarki ya yi mamakin
yanda Risalu yake fahintar dukka irin
abinda ya yi niya, amma sai ya sauya
dabara, cikin zafin nama Sarki Abu
Zaiyan ya yi kansa, shi kuma Risalu sai ya
tsaya yana tunanin ya tare shi, amma me a
lokacin da Sarki ya isa gare shi sai ya zabe
daga waftar da ya kawo masa ya kuma
sace wukar ta daya kubin ya soka masa a
dokin wuya.
Lokaci guda Su Sarki suka ga Sarki
ya wuce salin alan shi kuma Risalu ya yi
tsaye, ya kuma daina motsi, suna tunanin
wani karfin shifin yake sai kawai suka ga
Risalu ya fadi riga ji a kasa ku shurawa
bai yi ba sai a sannnne suka ga ashe soka
masa wuka Sarki ya yi ta dokin wuya.
Wannan al'amarin ne ya jawo
49
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
hankulan Sarakan domin a tsai da fadan
haka kowa ya kuma ya kara shirin.
Nan da nan suka bukaci haka Sarki
ya yi farin ciki da haka domin dama
lokacin Sallah ya yi, dan haka kowanenesu
sai suka koma nasu sansanin.
Lokacin da Sarki Tarmas da kuma
Sarki Husaka da Madhman suka kebance
sai Sarki Madham ya dubi Sarki Husaka
ya ce, "Hakikanin gaskiya akwai gyara a
cikin wannan yaki, saboda haka ku saura
shawara, ni dai ina da ita in ma baku da ita
abin nan dole a samu a bi ta karkashin
kasa, ba komai nake nufi ba face, a cikin
Sadaukin da zasu kara da Sarki Abu
zaiyan akaro na hudu ya kamata a ce, An
samu wata guba da za'a yi amfani da ita a
shakawa Sarki, idan ya so shi Sadaukin sai
ya yi farat daya ya kashc shi, ka ga dai ku
dai fili ya hautsine mun samu babbar
nasara.
50
TURBAR GASKIYA--4 MADAKIN GINI
Koda jin wannan shawara ta Sarki
madham Sarki Husaka da Sarki Tarmas sai
suka hada baki suka ce, "Kai da kana da
wannan dabara amma baka yi sauri zuwan
mana da ita ba.
Da jin haka sai Sarki Madham ya yi
murmushi ya ce, "Hakika a baya bani da
wannan dabara amma a yanzu da wahala
ta kai wahala (sai ta fado min dan haka
yanzu abinda za ayi shi ne mi yi umarni
da ahada huda da gumar da zai shaka, ya
mutu.ua
LHAikuwa nan take su Sarki suka yi
umarni da aka hada wannan abu, Sadaukin
da Za'a yi wannan fafatawa da shi, aka ba
shi aka kumà sanar da shi yanda zai yi aiki
da ita, nan take sai suka ci abinci suka
samu hutu, sannan suka komafili пто0
wwed Avcan kuwa 6angaren Su Sarki Abu
Zaiyan an yi sallah an ci abinci, dan haka
Sarki ya karayin bayanit dan Karawa
251
TURBAR GASKIYA --4 WMADAKIN GINI
jama'ar imani da tsoron Allah sannan ya
Kara yin shirin yaki, aka fito filin daga
Koda fitowarsu sai suka ga ashe tuni
Sadaukin da za a yi karawar da shi ya fito
yana tsaye a filin daga yaña ta dage dagen
hannu ana tafa masa.ie aled ni Д
ab ing Shi kuwa Sarki sai yayi sallama da
jama'arsa ya shiga tsakiyar filin batare da
shakka ba, Yarima zaiyan a wannan
lokacin suna zaune da Shadilat suna hira
mai dadi ita kuma Lushmaira tana can
bayansu kishi duk ya hanata sukuni, banda
harara babu abinda take aiko musu da ita.
Amma lokacin da aka fara kwafsawa sai
hankalin. kowaya koma kanfilin
fafatawar. busy ide eb tausz sok eks ida
sduAna shiga fili sai aka fara fafatawa
domin kuwa kowa a huce yake, lokacin da
suka fara artabu sai fadan ya fara bawa
kowa mamaki domin yanda suka kasance
cikin kaiwa juna bara hannu da kafa suna
1252
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
shillo tare da kaucewa dukan juna, tun da
aka fara wannan karafkiya babu wanda aka
taba Sarki shi kansa wannan fadan yafi
burgeshi da yakin da su ka yi a baya
domin kuwa a wannan yakin yafi zagin
damtse a dirji juna abinda ya fahinta da
sabon Sadauki shi ne masani ne wajen iya
yaki da hannu ga takubba a hannunsa
amma bai damu da ya kai suka da ita ba, a
na cikin haka Sarki ya yi sa'ar naushinsa a
fuska.
Ya tafi daga taga zai fadi sai ta tirje
ya gyara rikon Banjo din da aka ba shi a
hannunsa ya kusanto Sarki Sarki ya yi
alkafira ya doke shi a kirji sadauki ya kara
yin baya, amma saboda naci ya kara
dawowa nan suka kara kaurewa da sabon
yaki, domin ya sanja salon fadan ganin
Sarki ya fahinci inda ya dosa anan ne ya
samu lagun Sarki har ya naushi a fuska sau
biyu kuma a cikin naushin ne ya yi sa'ar
53
TURBAR GASKIYA --4
shaka masa wannan Banjo din.
MADAKIN GINI
Aka ci gaba da yakin kamar Sarki
bai ji komai ba, suna cikin yaki Sarki ya
shammace Sadauki ya karya masa wuya
6aras.
Ai kuwa kafin ya sake shi wani
Sadauki da ake kira Hirnanu ya fusato ya
fito da karfi ya taka Sarki, Sarki Abu
Zaiyan ya mirgina kasa ya mike cikin
dauriya, kafin ya kara yin wani yunkuri
Hirnanu ya kara yin dirango a bayan Sarki
ya kirbawa Sarki naushi a mukamuke ya
kuma zare takobi da niyar ya sare masa kai
amma sai Sarki ya baje a kasa ya kuma
kwashe kafafuwan Hirnanu.
Nan take Hirnanu ya zube kasa,
Sarki ya ya kama kansa ya danna a cikin
kasa, aduk girman Hirananu sai ga shi ya
kasa kwacewa ga shi kuma sai tirjjiya yake
saboda tsananin walaha babu damar
shakkar numfashi sai dai kasa da yake
54
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
shaka Sarki Bai daga shi ba sai da ya ga ya
daina motsi.
Nan ma Sarki bai daga Mataccen ba
wani sadauki ya kara yo sufa ya dake shi
ta baya Sarki Abu zaiyan sai ya fadi kasa
kuma ya kasa ta shi. A wannan yakin da
(aka yi su Sarki tarmas suna ganin cewar
gubar bata samu shiga Sarki ba amma
ganin ya kasa ta shi sai suka kama murna
domin sun san aikinta ne.
Koda Wannan Sadauki ya kara yo
tsalle sai ya kama Sarki da niyar ya jashi a
kasa, amma sai Sarki