An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
TugiarCaakiya
ABDUL'AZIZ SANI
MADAKIN GINI
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
TURBAR GASKIYA 4
okacin da Gimbiya Lushmaira take duban
wadannan Zakuna miji da mata sun yi
mata kawanya sai nan take ta shiga cikin
tsananin ta shi hankali
Cikin 'yar sarsarfa suka dinga matsuwa
inda take, tana masu wani hargitsantsan gurnani mai zaranar da zukatan maʼabota saurare.
Nan ta tsaya ita ba abin ta zura da gudu ba, ba kuma abin ta yi yaki dasu ba domin ko ba
gwadaba linzami ya fi karfin bakin kaza, amma
lokacin da ta ga sun yo kanta cikin fushi sai ita
ma hankalinta ya dugunzuma domin ta aiyana a
ranta cewa, idan ta tsaya tabbas za su sami
nasara akanta idan kuma ta ta shi tsaye ta kare kanta, watakila ta samu ta yi nasara akanta.
Nan take tunanin irin jarumtakar da mahaifinta
ya yi a lokacin da macijiyar Burukul Kursum ta shi go birninsu ya fado mata a lokacin da mahaifiyarta take bata labarin irin namijin kokarin da ya yi har ya soke idon macijiya a
yanda aka siffanta mata macijiyar loma guda
4
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
zata yi wa wadannan Zakuna ta gama da su,
tabbas idan ta kasa karo da wadannan Zakuna
babu shakka ko inda ake yaki da Macijiya ba za
ta iya zuwa ba, in kuwa hakane kudirinta ba zai
taba cika ba.
Wannan tunanin shi ya yi tsananin karawa
Gimbiya Lushmaira Karfin ta ji wani sabon karfi
ya shigeta bata san lokacin da ta kwarara
Kabbara ba. Ta tunkari Zakunan kamar yanda
suke tunkarota.
A tare suka yi sufa kanta, ita ma sai ta
daka tsalle ta yi kansu a ka wata bahagoyar
haduwa a cikin sararin iska, su duka suka gauro,
wani taimako da Allah ya yi mata, a lokacin da
aka ta shi sama da niyar ta yi karo da wadannan
Zakuna sai suka fita ta shi sama, dan haka su
biyu suka gauro suka zube kasa bisa faduwar
rashin tsammanin domin dukkanin su basu fadi
akan kafafunsu ba kamar yanda ita ta fadi a kan
nata kafafun.
Kafin su yi yunkuri mikewa sai ta yi
azama ta yi kan Namijin Zakin da yake kokarin
mikewa a cikin tsananin fushi.
Tun daga inda take ta yi alkafira ta fada
5
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
kan Zakin ta mai da shi, ya kara wani yunkuri
zai mike ta saka kafa ta taka wuyansa iyaka
Karfinta.
Nan take ya kama kakarin mutuwa ita
kuwa sai ta kara dagewa tana cikin haka bata
ankara ba ta ji an sureta an doka ta da kasa.
Cikin rashin bazata ta dubi wannan
Zakanyar ce ta kara yunkuruwa cikin ta shin
hankali ta kara biyota zata kara turmesheta.
A wannan lokacin karfin Gimbiya ya
gama karewa amma ta ta kwala wata Kabbara
domin ta riga ta san idan wannan Zakanyar ta
turme sheta to sai dan Buzunta, ai kuwa yin
wannan kabbara sai ta yi sama tamkar wacce aka
saka kugiya aka shillata, koda ta ta shi fadowa
sai ta sauko a kan Kafafuwanta.
Ai kuwa tana faduwa Zakanyar nan ta
Kara yin kukan kura ta yo kanta. Irin mahaukacin
gudun da take yi yasa Gimbiya Lushmaira ta
fahinci idan ta sameta za su yi muguwar
ragwabza, ai kuwa sai ta falfala da gudu. Ita ma
Zakanyar ta bi bayanta suka kasa tsire cikin
tsananin gudu, wata dabara ta fadowa Gimbiya
Lushmaira lokacin da ta ga Zakanyar ta kara
6
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
tsananta, wajen ne man ranta, dabarar da ta fado
mata ita ce wata dogowar bishiya ta take
gabanta, suna cikin gudun sai kawai Gimbiya
Lushmaira ta kara azama dan ta nufi jikin
bishiya tana kuwa isa sai ta kama tattaka bishiyar
tamkar wata 'yar biri, sai da ta yi nisa a saman
bishiya a lokacin da Zakanyar ta dako tsalle da
niyar ta cafkota sai kawai Gimbiyar Lushmaira
ta wultsila da baya, Zakanyar ta dake bishiyar.
Saboda karfin da Zakanyar ta yi wajen
dokan bishiyar sai da Bishiyar ta karya biyu rabi
ya zubi kasan jijjigen bishiyar ya kuma ya
tumboko amma bai gama tumbukcwa ba, amma
rabin bishiyar ya cire sun yi tafiyar ruwa da
zakanyar, Zakanyar ta fadi kasa ko shuruwa bata
yi ba.
Aikuwa ganin wannan nasara da Gimbiya
Lushmaira ta yi sai ta yi sauri zuwa inda jaririn
Zakin nan yake ta dauke shi ta kara falfalawa da
gudu domin kuwa duk Zakunan ta lura basu
mutu ba, domin kuwa sai motsi suke.
Koda ta yi nisa sai ta fara tafiya a hankali
domin wata shu'umar gajiya ta sarketa haka nan
bata san lokacin da ta zube kasa ba amma saboda
7
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
tsananin naci irin na gimbiya Lushmaira bata
saki wannan jaririyar Zakin ba.
Al'amarin su Yarima Zaiyan da sauran
tawagar su Sarki kuwa lokacin da suka kara nisa
a cikin tafiyarsu, har ya zamana sun shigo cikin
dajin da 'yan sumamen daga 6angaren Su Sarki
Madham suka boye cikin ciyayi sukc. Koda
Suka shi go wannan gurin sai tafiyarsu ta koma
sassarfa kuma da yawa daga cikin mayakan da
suke kan gaba sun zare makamansu.
Ba komai ya sa haka face, kawai sun lura
cèwar akwai alamar wasu halitton a gun, ba dan
komai suka gane haka sai ganin da yawan
Tsunsayen dajin sun ta shi sama, sannan
kananun namun dawa sun komo wajen dajin
idanuwansu na kallon cikin korayen ganyayyarki
Lokacin da suka isa tsakiyar dajin basu
gushe ba suna kara falfalawa da gudu suna
kabbara tare da daga makamansu sama.
Haka nan suka wuce wannan dajin batare
da maboyan Dakarun sun yi illar komai a gare su
ba.
Lokacin da Ayarin Dakarun suka gama
wucewa sahu-sahu, su ka yi nisa sai Dakarun
8
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
suka firfito suka tsaya su ka yi cirko cirko suna
numfarfashi. Domin wani irin tsuro ne ya cika
musu zuciya har ya haifar musu da kasa aiwatar
da komai.
Su ka fito daga cikin maboyar Sadauki
Aksar ya tsaki gami da doka kafarsa a kasa, ya
cе.
"Tir da wannan jarumtakarmu da har kwarjinin wasu zai hanamu mu aiwatar da
abinda shugabanmu ya umarcemu, yanzu mai
kuke zaton za mu je mu sanar da Sarki. Wani mai bi masa da ake wa lakabi da
Kuffuru, ya numfasa ya cc, "Ya shugaba ni kaina abinda yake raina ke nan, kuma na tabbata idan har muka komawa Sarki da labarin wannan
ragwanta da mu kai ba mu da hukunci da ya
wuce harshensu ya karce kasa, ma'ana kaifin takobinsu ta datsa wuyanmu, sai dai ba za mu taba barin haka ta faru kuma aikata hakan ba ya
na nufin mun gama asarar aikinmu bane, yanzu
ma akwai dama tunda a yanzu muna bayan
wadannan Dakaru abu na farko da za mu yi
saurin yi yanzu shi ne mu bi bayansu tun kafin
su Isa Sansanin da za a yi wannan gumürzun mu
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
bi su da tsananin harbin kibiyoyi yanda za mu
rage yawansu idan ya so kafin su ankara damu
sai mu juya da baya mu gudo"
Koda Sadauki Askam ya ji wannan
shawara daga yaronsa Kuffura sai ya yi aminci
da wannan shawara nan take ya yi umarni da a ci
gaba da bin bayansu, sannan ya yi umarni kowa
ya fitar da masunsa.
Nan take dakarun suka bi umarninsa suka
aikata abinda ya umarce su da su yi.
Koda suka dunguma zasu fara tafiya sai
suka ga mutum a bayansu, su duka suka waiga.
Suna waigawa sai su ka yi ido biyu da gimbiya
Shadilat, suna ganinta suka ganeta kamar yanda
ita ma ta ganc su, ba komai yasa suka shaidata
sai ganin kamanin da su ka yi da Sarki Abu
Zaiyan, nan take sai Askam ya kyalkyale da
dariyar mugunta. Sakamakon dariyar da yake
yasa daukacin jama'arsa su ma suka kaurc da
wannan shu'aumar dariya.
Gimbiya Lushmaira tana tsaye da jaririn
Zakinta a hannunta tana binsu da kallo cikin
tsananin mamakinsu
Nan suka kuma daina dariya da kansa
10
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
Sadauki Askam ya yi kanta da niyar ya kamata,
amma kafin ya isa gareta sai kawai ya ji wani
irin ihu yana ta shi daga bayansa, kukan fitar rai
ko da ya waiga sai yaga ai tuni an ci karfin sama
da mutum duba a cikin dakarunsu.
Yana duban Dakarun nasa suna sulalewa
kasa suna faduwa, amma ya kasa ganin wanda
yakc musu wannan 6arnar saboda tsananin zafin
namar mai aikata kisan, bai ankara ba ya ga gaba
daya dakarun duk an karkashesu, ya zama dan
kauye sai waige yakc yana son ganin wani
mala'ikan daukar rai ne ya zo yake girbar masa
Dakaru.
Ba shi ba hatta Gimbiya Lushmaira kallon
mamaki take, cikin tsananin faduwar gaba
Yarima Zaiyan ya bayyana a daf da shi, wanda
saboda tsananin firgici Sadauki Askam sai da ya
saki fitsari a wandonsa.
Gimbiya Lushmaira tsananin mamaki ya
hana bakinta rufawa saboda irin jarumtakar da
Yarima zaiyan ya yi amfani da ita wacce bata
taba ganin ya yi irinta ba.
Sadauki Askam ya dubi Yarima yana
kirma ya zuba giwowinsa a kas, yana neman
11
TURBAR GASKIYA --4
yafewa.
MADAKIN GINI
Koda Yarima ya dube shi sai ya tsar ta
masa yawo a fuskarsa.
"Ahir dinka da a ke kiranka da gwarzon
Sadauki kuma har yake jagoranta wadansu
Dakaru dan aiwatar da wani shiri na karkashin
kasa, ina son ka sani duk kan shirin ku mun fara
saninsa daga fara shigowa cikin wannan dajin
haka zalika ko da aka fita daga cikin dajin nan ni
ban fita ba ina nan ina son na ga sabon shirin da zaku kulla.
Dajin wannan batu sai jikin Sadauki
Askam ya Rara rawa, yana makyakkyata, shi
kuwa sai Yarima Zaiyan ya dube shi cikin fushi
ya ce, ka dauki daya bayan daya ka dora dukkan
dakarun da na salwantar akan dokinsa ina nan
ina jiranka.
Aikuwa nan da nan Sadauki Askam ya
fara aikin cikin sauri-sauri gudu-gudu, kafin
wani lokaci har ya kwashe su duka, ya na gama
dora su a bisa dawakan kowannensu sai Yarima
Zaiyan ya dube shi ya ce..
Ya kai wannan sakaran jarumi kasan
abinda ya sa na sa ka aikata haka,?"
12
TURBAR GASKİYA --4 MADAKIN GINI
Cikin rawar jiki Sadauki Askam ya ce, "ya
shugabana ban da masaniya akan hakan.?"
Da jin haka sai Yarima Zaiyad ya yi
murmushi ya cc, "Abinda hakan ke nufi shi ne za
ka jagoranci gawarwakin izuwa sansaninku ka
labartawa sakaran Sarakanku yanda aka yi aka
salwantar da rayuwakan wadannan dakaru, ka
basu labari ni ne Yarima Zaiyan daya daga cikin
dakarun cikin birnin Baitul Haural ina so ka
sanar dasu cewa guguwar bala'i tana daf da
isarsu kuma duk irin shirin da suke tunanin za su
yi a kanmu mun riga mun gama da ku, fatanmu
mu hadu a fili daga mu gidaddabaku in har ba
zaku bi TURBAR GASKIYA BA.
Koda Yarima Zaiyan ya gaba sanar da
Sadauki Askam wannan sako sai ya juya da
niyar ya yi gaba ya barsu a nan da Gimbiya
Lushmaira.
Nan take gimbiya Lushmaira ita ma ta yi
gaba batare da damuwa da shi ba. Yana tafiya
kawai ya ga ta zo ta wuce shi ranta kuma a басе
bata ko kallonsa, ga jaririn Zakinta a hannu.
Koda Yarima Zaiyan ya dubeta sai ya yi
sauri ya ya sha kanta, ita ma ta tsaya su ka yi
13
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
cirko cirko suna kallon juna na tsawan lokaci a
farko kallon kurillar da sukewa junansu, basu
san a irin matsayin da suke ba, domin kuwa
kowannensu wani tunanin ya tafi na daban.
Yarima Zaiyan ya dawo haiyacinsa ya yi
saurin dubanta kamar bai shiga wani hali na
tsawon lokacin da ya yi yana dubanta ba, ya се
cikin kakkarfar murya kamar yana doka mata
tsawa.
Take ita ma ta dawo haiyacinta ta dube shi
da shakka, tana saurarensa.
"Yake wannan karamar yarinyar mai
shirin zama jaruma, hakika a yanzu na tabbatar
da cewar kin yi kokarin da idanuwanki za su iya
jure ganin irin gagarumin gumurzun da zamu
kwafsa tsakaninmu da makiyanmu, tabbas, bana
da haufi ba zaki tsorota ba a yayin da
idanuwanki suke kallon wannan gumurzu,
sakamakon wannan bajintar da kike na dauko
jariririyar dabba."
Yana zuwa nan a cikin zancensa sai ya
juya da niyar ya wuce gaba, da ganin haka sai
Gimbiya Lushmaira ta dakatar da shi da cewa.
"Kai kuma a yau ne na fara tunanin dinbin
14
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
shckaru da ka dauka kana kowan yaki, duka ka
yi su nc a banza, domin kuwa ka bani mamaki da
har kake fada na shammata, duk wani jarumi mai
ji da tumbatsarsa jarumtarsa, baya yaki da wanda
bai shirya ba, dan haka akwai saura rina a
gabanka."
Tana zuwa nan a jawabinta sai ta cilla
masa jaririn Zakin ta yi gaba cikin gudu kafin ya
dawo daga mamaki kalamanta tuni ta yi nisa.
Cikin sanyi jiki ya baro cikin dajin Shi
kuwa Askam tuni ya dauke hanya yabi wata
siririyar hanya wacce ta zagaya ce ya tura
dawakan da matattun dakarun da suke kai
Koda Gimbiya Lushmaira ta isa cikin
tawagarsu ta yi sauri karasa inda sahunsu yake ta
tarar da Shadilat a cikin sahu tana tafiya, koda
Shadilat ta ganta sai mamaki ya rufeta har ta
kasa yin hakuri ta kamo hannun gimbiya
Lushmaira ta ce.
"Ya ke 'yar uwata shin yaya a ka yi kika
kamo a cikin wannan tafiya, da tuni na cire rai
dake.?"
Da jin haka sai Gimbiya Lushmaira ta yi
murmushi tun daga lokacin da tafi kawo irin
15
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
gwaggwarmayar da ta yi da Zakunan zuwa
lokacin da Yarima Zaiyan ya iso ya yi yaki da
Dakaru sama da dubu goma da irin bajintar da ya
yi, ta kuma dora irin yanda Yariman ya
gwasalcta a cikin tafiyarta da kwazonta sannan ta
karc da ita ma irin gwasale shin da ta yi, duk ta
sanar da ita.
Da jin wannan bayani sai Shadilat ta ce,
"A gaskiya kin yi kokari kuma na yaba da irin
kwazonki domin kuwa ban yi tsammanin samun
nasararki ba, ni kuwa yanzu a hali da nake ciki
na fara tsanar jarumtakata, kai in takai ce miki na
saduda da duk wani kudiri nawa.
Cikin tsananin mamaki
Lushmaira ta dubi Shadilat ta ce.
"Ke kuwa akan me yasa.?"
Gimbiya
Shadilat ta yi wani kayataccen murmushi
ta dubi Gimbiya Lushmaira ta ce.
"Kc kuwa mai kike tunanin zai saka ni a
cikin irin wannan hali in ba soyayya ba, ya ke
aminiyata ina so ki sani a cikin 'yar gajcriyar
tafiyar da muke, sakamakon rashinki a tare da ni,
sai Yarima ya ke zuwan min lokaci lokaci yana
taya ni hira, a wannan lokaci ban yi aunc ba
16
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
tsananin soyayyarsa ta shiga cikin raina."
Kafin Shadilat ta gama zuwa karshen
maganarta gaban Gimbiya Lushmaira ya yanke
ya fadı wani irin kishi ya turnukcta, da kyar ta
iya kawar da damuwarta ta dubi Shadilat cikin
nuna rashin damuwa ta ce.
"Amma dai kc kuwa kin yi asara a kan
soyayya ki zubar da irin burukanki tabbas na yi
dana sanin kulla kawance dakc, domin kuwa a
tafiyata bana son sakarci ni kuwa ban dauki
soyayyar komai face sakarci in har zaki yi
soyayya to babu shakka ke sakaryacс."
Wannan magana ba Karami bakantawa
Shadilat rai ya yi amma sai ta yi murmushi ta cс,
"Ko da zaki rabu dani, ba zan ji takaici ba tun da
dai ina tare da gwarzon namijin duniya kuma
shugaba ga wannan tafiya ina so kuma ki yi sani, Yarima Zaiyan nc kadai zai iya yin nasara akan
dukkanin kudirinki domin kuwa a yanzu a kaf cikin wannan nahiyar babu sadauki mai karfinsa
da kwarjinsa dan haka kada ki taba tunanin kcсе zaki iya sokc daya idaniyar Maciyar Burukul
Kursum, kuma shi ne zai zama gwarzon karni a
cikin wannan gagarumin yaki da za a kwafsa,
TURBAR GASKIYA--4 MADAKIN GINI
tabbas idan ya zamo abin gabarki a yanzu zai
zamo abin son ki a nan da wani dan lokaci mai
zuwa, ina mai shawartarki da ki yi biyayya a
garc shi domin ki samu saukin bakin cikin
rugaza miki kudiri da zai yi.
Koda gimbiya Lushmaira ta ji wannan ba
tu sai ta fusata ta cire hannu daga rikon da
Shadila ta yi mata ta bar gun cikin tsananin
fushi, tana barin gun kuwa ta shiga wani sahu a
na ci gaba da tafiya.
A dai-dai wannan lokacin kuwa aka tsaya
yin sallar Azahar, wannan damar ce ta sa
Gimbiya Lushamaira ta samu guri ta zauna
dukkanin abubuwan da Shadilat take sanar da ita
nan take ya dinga dawo mata, wani tsananin
kishinta ta ji, tabbas a yanayin jarumtakar da
Yarima yake nunawa zai iya zamowa gwarzon
karninmu dan haka abinda ya kamata ta yi shi
ne ta ta yi kokarin da zata zamo itama-za a
yabeta tana da masaniya ko da bata kai
kokarinsa in har ta zamo masa na biyu to bai isa
ya yi mata wani kuri ba, da wannan tunanin
Gimbiya Lushmaira ta ta shi ta tafi ta yi alwala,
sai dai lokacin da ta dawo daga yin tsarki sai ta
18
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
hango Shadilat da yarima Zaiyan suna hira har
da kyalkyalewa da dariya, wannan abu ba
karamin yi mata ciwo ya yi nan take wani
tukokin kishi ya rufeta.
Koda aka idar da sallah za'a ci abinci bata
bari ta je inda Shadilat take ba saboda yanzu
haushinta ma take ji, a haka aka ci gaba da
tafiya.
****
A can kuma san sanin su Sarki Madhan
lokacin da suka iso bakin filin da za yi wannan
yaki sai suka tsaya da tafiya nan take kuma aka
kama kafa tantun domin a samu huccwa kafin su
samu sako daga jama'ar Sarki Abu Zaiyan.
Koda aka kammala da kafatuntunan su
Sarki sai Sarki Madham Sarki Tarma da kuma
Sarki Husaka suka kadaice a cikin nasu tantin da
dubu da irin abubuwan da yake gabansu.
Koda yin shiru na dan wani lokaci
kowannensu yana tunanin abin da zai faru, sai
Sarki madhan ya yi ajiyar zuciya ya dubi
Sarakan gudu biyu ya се.
"Ya ku Sarakai 'yan uwana yanzu ya kuke
tunanin jama'armu da muka turo don yin
19
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
kwantan 6auna don su hallakar da wasu daga
cikin jaruman Sarki Abu Zaiyan ta hanyar yi
musu ruwan kibiyo.
Da jin wannan ba tu sai Sarki Huzuka da
Sarki Tarmas su ka ajiye zuciya a tare sannan
suka tsai da kallon su ga Sarki Madham Sarki
tarmas yа сс.
"Lallai kam akwai abin duba a cikin
tafiyar tasu dole muna bukatar mu san abin da ya
faru ko sun samu nasara ko kuma basu samu ba
domin mu yi yunkuri yin wani tunanin tun kafin
su Sarki su iso wannan fili a fara yin yaki dasu."
Shi kuma Sarki Husuka sai ya ce,
"Wannan haka yake, amma kuma ta yaya kuke
ganin zamu san samun nasararsu, tun da dai kun
sani ba mu tura su dan su je su yi nasara su dawo
ba, mun tabbatar da cewar konar bakin wake su
kai, domin kuwa babu wanda zai sha a cikinsu,
fatanmu dai su yi barma ko yaya take."
Sarki Madhan cikin karfin gwiwa ya cc,
"Babú ko kokwanto za su samu nasara abin da
ya kamata yanzu mu yi shi ne mu kara nemo
wata hanyar da zamu yi amfani da ita dan samun
biyan bukatarmu."
20
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
e Kafin wani daga cikinsu ya yi wata
magana sai Shugaban dakaru na birnin Sarki
Husuka ya shigo cikin tanti cikin rissanawa ya
cc.BIBWB "Ya shugabana Sadauki Askam ya iso cikin
mawuyacin hali tare da gawarwakin duka
dakarun da ya tafi da su.M ihs2 sbo isaKoda suka ji wannan ba tu sai dukkaninsu
suka cika da firgici ainu, har sai da aka samu dan
lokacin sannan suka dawo hayyacinsu, Sarki
Husuka ya yi saurin duban Sadaukin Rauwal ya
сe, "Ka koma ku duka ku saurari fitowarmu.
Sannan ina so kafin nan ka tura Dan leken asiri
dan gano mana a halin yanzu a ina abokan gabar
mu suke."
swogse Koda jin wannan ba tu sai Sadauki
Bhan Rauwal ya yi sujjada ga Sarakan sannan ya fice.
UR Fitarsa ke da wuya sai Sarki Tarmas ya cc,
"Tirkashi lallai sai mun yi da gaske domin kuwa
jama'ar nan sun gano mu, kuma ba za su tabа
yarda da duk wani shirin da za mu zo mu su da
shi ba domin kuwa za su cc yaudara cc, kuma
sanin kanku ne gaba da gaba da su ba karamin
ta'adi za su yi mana domin Kasar Baitul Haural
sun kware wajen iya yaki mamaya a duk duniya
21
TURBAR GASKIYA --4 A-AY MADAKIN GIN
duk wanda zai yi gaba da gaba da su a fafataa
filin daga babu shakka sai sun sha jininsa sai sun
samu nasara akan ku, don haka yanzu sauya shir
ya zama dole, mai kuke tunani wata shawara za
ku zo mana da ita?"
Koda Sarki Husaka da Sarki Madhan suka
ji wannan jawabai na Sarki Tarmas sai
dukkaninsu suka yi shiru na rabin lokaci. Daga
R
bisani Sarki Madham ya ce "Ai kuwa in haka ne
tusa ta Karewa budari domin kuwa ni ban ga ta
yanda za a yi mu samu nasara akan Sarki Abu
Zaiyan ba in har ya zama dole yin gaba da gaba
da su babu nasara. AATey nild s Bisir
Da jin haka sai Sarki Husuka ya yi saur
dagowa ya cc, "Bai kamata mu dinga sagewa
kanmu gwiwa ba, kamata ya yi mu samu hanya
mafi dacewa damu domin yin gaba da gaba da su
koda za'a samu nakasu. A yanzu a cikin
tafiyarmu muna da manyan Dakaru da ko a
duniya za a sasu a cikin sahun manyan dakarum
duniya, abinda ya kamata da a yi shi ne, a yanzu
takc mu jarraba tura dan sako da mun tabbatar
da i sowar su mu shailanta musu cewa za'a yi
yaki amma ba na mamaya ba, za a yi yaki irin
:22
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
yakin na gasa, ma'ana jarumi da jarumi, ni na
tabbata idan suka aminta da haka to babu shakka
za mu iya yi musu a sarar manyan dakarunsu."
Da Sarki Husaka ya zo nan a cikin batunsa
sai dukkaninsu suka yi shiru na tsawon lokaci
kana suka dubi juna. Sarki Madham
"Ai kuwa in har za su amince da wannan
ni kaina ina kallon samun nasara amma kuma
amincewarsu shi ne badakalar."
Da jin haka sai Sarki Husaka ya сc, "Ai
sai mun jarraba, kumaishi mai nema ai yana tare
da samu."
Nan take su ka yi na'am da wannan ba tu
suka nemo Sadauki Rauwal ya shigo ya sanar
dasu gabatowar rundunonin kasar Baitul Haural
har sun kafa tantuna sun fara fito da kayan
makamansu.
Koda suka gama jin wannan batu sai suka
sanar da shi sakon a sanar da dan aiki ya je zuwa
ga sansaninsu domin isar da sakon da suka
tanadar musu.
Nan take ya karbi sakon ya bayar aka kai
ba dauki tsawan rabin sa'a ba dan aikin ya
dawo.
23
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
Cikin girmamawa ya mikawa Sarki
Husaka Sarki Husaka ya mikawa Madham nan
take sai Sarki Madhan ya warwareta ya fara
karantawa suka kasa kunnc cikin doki sun jin
abinda yake kushe a ciki
Zuwa ga azzaluman Sarakai marasa son
gaskiya ba su bawa Turbawa gaskiya baya,
hakika, tabbas ko yanzu mun gano cewa tsoro ne
yake bibiyarku har yasa kuke neman sassauci
daga irin azabobin da za ku riska, ina son ku sani
babu tudun da a ba hawansa ake ba, abinda zai
hana kasar Baitul Haural su sassaraku su mai da
jininku abin shan Kasa, shi ne karbar addinin mu
na gaskiya, wato addininmu, ina son ku yi sani
mun yarda da dükkan irin zabin yaki da zaku zo
mana da shi, sai dai ina so ku sani duk wanda
kuka zaba ba za a daina yinsa har sai an ga
wanda ya ci nasara.
Daga Sarki Abu Zaiyan dodon kafurai.
koda ya zo nan a cikin karatunsa sai su
duka suka dubi juna daga bisani kuma sai suka
kece da wata shu'umar dariya mai firgita mai
saurarc, koda kammala wannan dariya sai suka
fito suka sa a ka kira manyan jarumin na kowace
24
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
kasa daga kowanc