biyu suna kwance, uwarsa tana nesa da
su tana sharar barci.
Koda gimbiya Lushmaira ta ga wannan
al'amari sai farin cikin ya cika mata zuciya
ainu nan take ta yi farin ciki ta tabbatar da
cewa zata yi abinda Yarima ya umarceta,
muddin kuwa ta samu nasara, to zata hada shi
da gagarumi aikin da ba zai iya ba. Domin ta
haka ne zata nuna duniya cewar ita jaruma ce,
kuma ta haka ne karfin da yake takama da shi, zai dusashe a cikin birninsu.
Koda yin wannan tunanin sai ta zura
hannu ta dauki daya daga cikin jariran
zakunan, a cikin sanda. Amma me ta na dago
kai ta hango Namjin Zakin nan ya na dawowa da cikin matsanancin gudu.
Ganin haka yasa Lushmaira yunkurin mikewa da sauri ta falfala da gudu tana rike
da wannan jaririn Zakin.
Zakin ya kurma wani uban ihu
mai tsananin firgici ya bi bayanta. Ita kanta
60
TURABAR GASKIYA 3 APМАDAKI
Gimbiya bata san tana da irin wannan gudun
da takeiyi ba, sai dai duk irin gudun da itake
Zakinınan ya ninka nata domin sau tari yaná
kamota saita zille ta sauya hanyal na нег
16 ms Warnan (alamari yariyin mutu kar tayar
da hankalire Lushmairagdomin Zakin namya
kuntäta inga i shiogajiyansta farassarkartasta
sedudustana ganin ba zatuliya samun hasara
ba. ilsy malaiseligist
nsasnKoda ta fara layrjuwa na dibarta sai ta
dake ta di igabal da gudun tañarrike da jaririn
Zakin, a hannuntasy sbug issdol nimob syset
smul Av hakahar tlisol indainsukanyada
sansaninnaslokaci hankulintasba Rararhinta
shìyal yi da ganin yanda gurin yasyi shira ba
kowa da alamar sun ji ma da yin gabastana
tsaye cikin tsoro da fargaba Zakin yakara so
fitinıgurin ayana gurmanins hiskansanyaugaji
likes su kø yi gaba da gabasdarita bab halin
gup sq kdub avea elim smuk st នigm
ainswOimbiyduLushmairaz tarcird dankwdlin
kantwdagd sauti faures Rarari jaririn Zakin
sannan ta yi zafinohamanpe daurerijshisrda
jikin swatatsiririyer sbashlyawol in2
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
Aikuwa kafin ta kara wani Yunkuri
Zakin nan ya yi sufa kanta da niyar ya
turmusheta, amma sai ta azama ta bar gun ta
sauka akan kasa, gurin ya'cika da kura.
Da ganin haka sai ta ja daga kamar
yanda shima ya dago yana fuskantarta da
Kara damara. A wannan lokaci sai ita ta
nufeshi cikin fushi zuciya suka kauri da
hargitsatsten yaki.
Gimbiya Lushmaira ta yi danasan
kaiwa wannan Zakin bara a karon farko kai
tsaye domin lokaci guda ya yagar mata fatar
bayanta gurin ya kwalane ya yi fari ya kuma
saka hakuransa akan kafarta yana neman ya
cisgeta, da kyar Lushmaira ta iya kwace
kanta.
Ba tare da ya jira ta samu sukuni ba
zakin nan ya kara nufarta da niyar ya
turmesheta amma sai ta yi ta 'yan maza ta
murgina ta kuma mike tsaye duk da jini na
zuba daga jikinsa sai ta dunkule hannuwanta
cikin karfin halin ta tsaya kan Kafafuwanta
tana jiran isowar Zakin.
Shi kuwa sai ya saka kafarsa a kasa
62
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
gami da tona kasa ya/yi kuka mai cikc da
amon ya yi kanta koda ya iso gare sai ta
daddage ta kai masa naushi a fuska
Ta yi kuwa sa'ar samunsa a idonsa nan
take sai ya kauri da wani hargitsantsan ihu
mara dadin ji. UCAH UM
Lokacin da ya kife kasa kafin ya kara
samun wani karfin halin ta sauri juya da niyar
daukar jaririn zakin nan da ta daure shi. KP
Abinda ta gani shi ya yi mutukar
razanata ta ji gabanta ya yanke ya fadi ba
komai ta gani face, uwar Zakin tana
shinshinar jikin dan.
Wani hargitsantsan kuka ta ji, a bayan
tana waigawa taga daya Zakin ya mike ya yo
kanta.
WANI IRIN GAGARUMIN YAКІ
ZA'A KWAFSA TSAKANIN GUNGIYAR
MUSULUNCI DA TA KAFURCI.
WANE IRIN GUMURZU SADAUKI
ZAIYAN ZA SU KWAFSA TSAKANINSU
DA MASU KIBIYO DA SUKA BOYE A
CIKIN CIYAYI
63
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
INA LABARIN MACIJIYA
BURUKUL KURSUM.
YAYA GIMBIYA LUSHMAIRA
ZATA KARE DA WADANNAN
ZAKUNAN.
MU HADU A CIKIN LITTAFI NA
HUDU GA MAI SON JIN CI GABAN
WANNAN LABARI NAKU HAR
KULLUM
ADBUL'AZIZ SANI MADAKIN
GINI
64
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
KADAN DAGA
BA TSIRA
A wani zamani can baya lokacin
jahiliya kimanin shkaru dubu biyu kafin
daukakar birnin Misra an yi wata babbar
daula da ta kunshi manya birane guda uku.
Birni na farko ana kiransa da suna
Darul Husuk, na biyu kuma Baitul Lazima
na ku kuwa shi ne Nurul Amsar.
Gaba daya wadannan birane uku
suna da girman kasa, arzikin noma da
kasuwanci amma kuma suna cikin wata
babbar masifa ta rashin zaman lafiya
saboda ko yaushe acikin yake-yake suke,
ga yawan kawo hari na 'yan fashin, an rasa
sarki guda daya wanda zai ia kare Kasarsa
da jama'arsa daga wannan masifa saboda
mutanen kowane birni basu da adalci da
tausayi, rayuwa ake yi kawai irin ta
dabbobi.
Wanda duk yafi karfin wani zai iya
kashe shi, ko ya yi masa fin karfi ya
65
TURABAR GASKIYA-3
kwace masa gida, mata da gona.
MADAKI
Bisa wannan dalili ne mutanen
wannan daula suka fara kokarin yin hijira
domin su gudu daga nahiyar gaba daya,
amma sai gudun nasu ya zamo na banza,
tunda basa samun tsira saboda a kokarin
guduwa ne kuma suka rinka haduwa da
masifu ta ajalinsu.
Asararar dukiyoyinsu da kuma
iyalansu. Nan fa rayuwa ta yi tsananin
mutuka a cikin wannan daula ga shi dare
da rana kasashen a cikin yake yake suke, a
koyaushe za'a iya kawo har, idan ma
mutum a cikin daji yake rayuwarsa kamar
ta kiyashi take.
Sarkin dake mulkin a birnin Nurul
Amsar shi ne mafi adalci a cikin sarakunan
ukun amma kuma ya tsufa ainun baya iya
yin komai kuma ciwo ya ci karfinsa, yana
da matar aure guda daya jal mai suna
Lahira sai kuma da guda daya wani
matashin saurayi dan shekara goma sha
€99
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
takwas ana kiransa da suna Huzainu.
Huzainu ya taso da gagarumar
jarumtaka ta iya yaki da kuma kwarewa
wajen iya farauta a daji, a rayuwar Hizanu
babu abin da yake so sama da ganin ya
kawo karshen rashin zaman lafiya a
wannan daula tasu, amma sai yaga abin
yafi karfinsa, domin a haka ake rayuwa a
nahiyar tun kafin ma a haife iyayensa.
Watarana da yammaci sai ciwo yai
itsananin ga Sarki Saiham wato mahaifin
Yarima Huzaini har ta kai cewa yana suma
a wannan lokaci Huzainu da mahafiyarsa
tare da dukkanin fadawan Sarki Saiham na
zaune a gabansa suna ta faman shara kuka.
Kwatsam sai aka ji Sarki Saiham ya
bude baki ya ce,
"Kowa ya fita ya barsu shi da
99 iyalinsa."
Nan take kuwa fadawa da duk
hadimai suka fice daga cikin dakin, aka
bar Huzuinu da mahaifiyarsa, su biyu
67
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
kacal, duk da haka sai Sarki ya dubi
Huzainu ya ce ya rufe tagogin da kofofin.
Cikin sauri Huzainu ya cika umarni
sannan ya zo ya zauna daf da Sarkin suka
kurawa juna idanu, suna masu zubar da
hawaye: Sarki ya bude baki da kyar ya ce,
"Ya kai dana ka yi sani cewa gaba dayan
kasashen nan uku dake cikin wannan daula
zasu rushe nan da cikar kwanaki kadan,
zała zubar da jini mai yawan gaske za'a yi
asarar miliyoyin rayuka da dukiya mai
yawan gaske.
Abinda nake so da kai shi ne ka
dauki mahaifiyarka da sauran amintattun
jama'ata ku sulale ku bar nahiyar nan gaba
daya in ba haka ba kuwa gaba dayanku
mutuwa za ku yi."
Kodaujin wannan batu sai hankalin
Yarima Huzainu da na mahaifiyarsa ya dugunzuma ainun Huzainu ya dbi Sarki
yace, "Ya kai Abbana ina amfanin mu yi
tagudun da babu tsira ka sani cewa
68
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
muna cikin mugun yanayi na gaba tsini
baya siyaki, muna gidan bamu tsira ba
haka ma muna dawa."
Sarki ya yi tari har da aman jini
sannan yace, "Ya kai dana na yarda da
jarumtakarka da kuma sa'arka, lallai kada
ka sare domin ina ji a jikina cewar zaka
iya kubotar da kanka da kuma dukkan
.masoyana י,
DAGA MADAKIN GINI YANA
NAN TAFE BA DA JIMAWA BA
eZINA MASU YIWA MAKARANTA
NA TUNI TA SABON LITTAFINA DA
YA FITA MAI SUNA WASIKAR JINI.
mTSARARREN LABARI NE DA
AKA KWAFSA GAGARUMAR
SOYAYY ALS DA HARGITSANTSEN
YAKIE? ewind s
CIN AMANA MUNAFURCI
GAGARUMAR BAJINTA YANA NAN
A KASUWA IN BAKA NEMA KA
69
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
NEMI SHI A KASUWA. YANA NAN A
KASUWA
Kadan daga KARAGAR MULKI
A wani zaman can baya mai tsawo
da ya shude a kasar Hindu an yi wani
gawurtaccen Sarki wanda ya shahara akan
karfin mulki da kuma karfin sihirin tsafi
wanda masana da masu bincike suka
tabbatar da cewa a wannan zamani babu
wani matsafi da ya kaishe karfin sihiri a
duk fadin duniya komai na jin dadin
duniya Allah ya baiwa wannan Sarki
wanda ake kira da suna Kanzal, face rashin
haihuwa.
A wajen mahaifinsu su tara ne kuma
gaba dayansu maza ne babu mace ko daya
Sarki Kanzal shi ne dan auta a gidan
sarautar kuma shi Allah ya baiwa Sarautar.
Lokacin da mahaifinsu ya kwanta
ciwo sai gaba dayansu su taran kowa ya
kwallafa ransa akan sarautar har ya
zamana cewa suna ta kaiwa junansu har
70
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
domin su hallaka junansu, bisa dole
kowannensu ya nemo hayar dakaru na
waje, domin tsare lafiyarsa, amma duk da
haka sai da kowannensu ya sha bakar
wahala ya kusan rasa rayuwarsa saboda
mugun tanadin da sukewa juna.
Wadannan 'yan uwa guda tara suna
yin tsananin gaba, babu wanda yake son
yaga wani a raye.
Babu wanda yafi shan wahala acikin
su sama da Sarki Kanzal domin awannan
lokaci shi ne mafi kankanta a cikinsu.
Sau uku ana sassarashi ayi masa
dukan kawo wuka ana zaton ya mutu, kai
akwai lokacin ma da aka daddaure shi
tamau da igiya aka sashi a cikin buhu aka
kulle buhun kuma aka jefashi a cikin teku
amma bayan sati biyu sai ga shi ya dawo
fada a raye duk jikinsa yasha dinki na
saran takobi.
Daga wannan rana ne Kanzal ya
hada nasa inasa yabar Rasar ya
71
KATSIRK BOSTNESS ON
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
bazama a duniya neman sihirin tsafi, ba'a
sake jin duriyar Kanzal ba sai bayan wata
shida.
A fada ya tarar da ana shirin yin gasa
kala takawai a tsakanin 'yan uwansa
domin a baiwa wanda ya lashe gasar
karagar mulki nan take Kanzal ya ce, ai sai
a kara gasar ta zama gudu tara tunda ga shi
ya dawo.
Nan fa mamaki ya turnuke gaba
dayan jama'ar dake fadar aka kurawa
Kanzala idanu bisa ganin kankambarsa da
kuma gangancin da yake shirin yi na shiga
wannan gasa.
DAGA MADAKIN GINI YANA
NAN TAFE.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels