ko, kuma
bana son dayarku ta yi min karya ku sanar
da ni iyaka gaskiyarku.
KodaShadilatda Gimbiya
Lushmaira suka ji wannan batu daga
Sarkin sai suka durkusa bisa gwiwoinsa
sannan suka ce, "Ya shugabana muna
rokanka alfarma a bisa kyata maka doka
da muka yi ka yi sani ba mu yi haka dan
komai ba sai dan mu je zuwa wannan filin
daga domin idanuwanmu ya gane mana
irin jarumtakar da Jarumi Zaiyan da
30
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
kuma kai zaku nuna, a wannan gurin.
Koda Sarki ya ji su da wannan ba tu
sai ransa ya yi mutukar faci ya dube su ya
כ
ce, "Amma dai kun cika sakarai a wanne
dalili ne kuna mata ma'abota rauni zaku
biyo sawunmu zuwa wannan bakin
yamutsin da ko a tarihin ban taba jin irin
azababbin yakin da zamu yi mu da
wadannan Sakarai uku da suka hadu a
kanmu, tabbas sai kun koma gida domin
kuwa bazan taba lamunta na yi tafiya daku
36
zuwa wannan yaki ba.
Koda yazo nan a batunsa sai su duka
suka sauke kawunansu Kasa suna masu
nadama zuwa dan su taimakawa masa
hakan ya jawo masa asarar tafiyarsu.
Sim sim suka juya suka sauka daga
kan tsaunin, cikin rashin kwarini jiki.
Sarki ya biyo bayan su, duk jikinsa
yakushe ne gaa jini koda Sarkin yaki
Safwan ya ga kyawawan 'yan mata daga
saman tsaunin sun sauko kafin ya gane
31
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
su waye sai ya zare makami koda suka yi
kasa ya gano su Lushmaira ne sai ya yi sak
ya kuma cika da tsananin mamaki, kafin su
iso kasa sai ga Sarki shima ya nufo su
koda ya hango Sarki cikin mawuyacin
halin sai ya nufo shi.
"Ya shugabana lafiya mai ya faru da
kai haka.?"
Sarki Abu zaiyan ya dube shi batare
da ya tsaya bata lokaci ko inda inda ba ya
kwashe duk abinda ya faru a tsakaninsa da
zakuna da kuma taimakon da su Shadilat
da Lushmaira suka kawo masa, amma sai
ya rufe Sarkin yaki da fadan yanda a ka
bar su Shadilat da Lushmaira suka biyo
bayansu.
Nan da nan Sarkin yaki ya kama
rantsuwa yana nuna rashin saninsa da
wannan al'amari ana wannan abu sai ga
Zaiyanu ya iso gurin ganin su Lushmaira
da Shadilat ya yi mutukar ba shi mamaki
32
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
kai tsaye ya dubi Sarki ganin halin da yake
ciki ya ce.
"Ya mahaifina shin mai yake faruwa
da kai haka ina dalilin ganin raunika a
jikinka, kuma wadannan daga ina suke.?"
Koda Sarki ya ji wannan ba tu sai ya
ce, "Bana son Su Shadilat su kara koda
sa'a daya anan lallai a shiryasu su koma
can gida domin kuwa ba zamu yi wannan
tafiya da su.
Koda jin wannan ba tu sai yarima ya
dube shi cikin tsawa ya ce, "Mai yasa kuka
biyo mu, ta wace hanya kuka biyo
bayanmu, koda ya kurawa Shadilat idanu
sai ya ce, "Tabba na gane ki ba ta ko wace
hanya ko ka biyo ba face ta hanyar Likita
Zauwad ba kuma na nufin shi ya yi muku
hanyar biyo mu ba kun bata cikin
jama'arsa kun biyo mu.'
Su dai basu iya cewa komai domin
dukkanin zuciyoyinsu cike suke da
fargabaa, da tashin hankali muddin suka
33
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
koma cikin birnin to babu shakka cuta
damuwa zata iya sanadin haifar musu da
wata matsalar.
Sim-sim suka dinga hada
komatsansu, Sarki ya sa aka basu dawakai
biyu da 'yan rakiya mutun biyar ya yi
وو umarni da a raka su.
Koda Lushmaira da Shadilat suka ga
an hada su da 'yan rakiya sai Lushmaira ta
je gaban Sarki ta durkosa gabansa cikin
dauriya idanuwanta na zubbar da hawaye,
ta ce, "Ya Mahaifina za mu koma kamar
yanda umarninka ya zartar akanmu, sai dai
ina mai son shaida maka, zuciyarmu tana
tsananin son zuwa wannan fili na yaki da
za'a yi wanda bana tunanin akwai wani
yaki a nan gaba da za'a yi wanda yafi
girman wannan yaki, hakika wannan yaki
ne da wanda yaje kallonsa shi kansa ya
tabbata a girmamashi, a saka shi a sawon
babban jarumi a wannan duniya, ya
Abbana hakika ina mai bakin cikin
3
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
rashin zuwa na wannan yaki, sai dai ina
mai bakin cikin sanar da kai tunda har na
kasance babu ni a cikin wannan tafiya to
babu shakka ni da aure sai dai a cikin
aljanna fiddausi.
Koda Lushmaira ta zo nan a cikin
batunta sai ta mike ta ja da baya, izuwa ga
'yar uwarta da kuma abokan rakiyarsu. Shi
kuwa Sarki Abu Zaiyan sai ya nitse cikin
tunanin maganganun Lushmaira daya
bayan daya, bai gushe yana tunani ba har
sai da ya ga sun kama hanya suna shirin
tafiya sannan ya mike ya nufo inda take
abisa dokin tana mai kokarin sakar masa
linzami ya yinda suke kallon, kallon da
Yarima Zaiyan.
Sarki ya dubeta sosai kafin ya ce
komai sai daga bisani ya ce, "Ya ke
wannan 'ya tawa mai biyayya ina son ki
sanar dani dalilin da zai hanaki yin aure
alhalin kina sane da cewar da aure ne zaki
samu cikar burinki na duniya wato da, ko
35
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
'ya ina son ki sani babu mamaki dan da
zaki haifa ya zamu cikon farin cikinki ya
zamo yayewar rasa mahaifinki da ki kai
tun yarintarki, ina mai son ki gagggauta
kawar da wannan kudiri nake na kin yin
aure domin na shirya yin bikinki ta zarar
mu dawo daga wannan yaki.
Koda jin wannan batu sai Lushmaira
ta dago da idanuwanta da mamaki ta dubi
Sarki Abu zaiyan, shi ma ita yake kallo
cikin kulawa, ta sauke idanuwanta cikin
tunani, kamar yaya ayi shagalin bikina
alhali a duniya ban ta6a ganin namajin da
naji ina so ba, kada dai Sarki ya ce ya yi
min mijin, in kuwa haka ne tabbas zan
taba bijire masa domin kowa in har ban je
wannan yakin ba na hadu da jarumin da yafi kowane jarumi yin kwazo a filin daga
to babu shakka bazann taba sauyawa ba,
in kuwa naje na gani jarumin da yafi kowa jarumtaka to shakka babu shi ne zai zamo
mijina, a rashin jarumin da zai soke
36
TURABAR GASKIYA-3
idon Macijiya Burukull Kursum."
MADAKI
Koda ta kara dago da idanuwanta ya
kalli Sarki sai taga dai har a yanzu kallonta
yake kuma da dukkan alamu ya karanci
abinda zuciyarta ke saka mata, dan haka
sai ya yi murmushi, ya се
"Za ki aure bayan mun samo nasara
mun dawo gida, yake 'yata Jarumi da zai
zamo mijinki babu shi a cikin zuciyata,
amma ina da tabbacin samun shi kafin
dawowarmu."
Babu walwala akan fuskarta ta kada
linzamin dokinta kai tsaye ta fara tafiya
batare da ta bawa Sarki Amsa ba, wannan
dalili ne yasa zuciyarsa ta bugo ya ji wani
irin a ranshi, nan take ya kwala mata kira.
"Ya ke Lushmaira ina dalilin yin
biris dani alhalin ina yin magana dake.?"
Bata waigo ba ta ce, "Ya Abbana na
matsu da nabar wannan guri, bana son na
bi abinda zuciyata take kodirtamin, domin
kada na bijirewa umarninka, dan haka
37
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
ina mai baka hakuri a bisa abinda na
aikata."
Nan take suka jera tare da Shadilat
kowace fuarta na zubar da hawaye, Sarkin
yaki Safwan ya dubi Sarki shi kuwa Sarki
sai ya dubi Yarima Zaiyan, a lokacin da
Yarima ya kautar da kai ga barin kallon su
Shadilat ya ci gaba da al'amarin gabansa
domin kuwa abinda Sarki ya yi, ya yi masa
dai-dai.
Sarki yaki Safwan ya matsa kusa da
Sarki cikin girmamawa ya ce, "Ranka shi
dade kana ganin barin su su koma yafi
tafiya da su alkairi.?"
Sarki ya juyo daga barin kallon
Yarima ya dubi Sarkin yaki, ya ce, "Nima
ina barar shawara gami da hakan, hakika
na yi mutukar mamakin yanda suke da
jarumta a halin da suka taimake ni a saman
tsauni, sai dai ko kadan bana son a ce an
fita dasu filin daga domin dalilin son
zuwansu bai kwantamin ba."
38
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
Sarkin yaki ya yi murmushi ya се,
"Ba na tunanin za su yarda su wuce gida."
Sarki Abu Zaiyan ya dube shi, cikin
mamaki "Kamar yaya kake nufi zasu iya
,, dawowa ke nan.
"Ya shugaba shakka babu domin
kowa zuciyarsu bata gida bake daya sun
dauke kacokan sun kaita filin daga, ya
kake tsammanin Kura da Kare sun tafi
neman nama babu Mage?"
"A lallai fa zata ji rashin jin dadi to
amma mai kake tsammanin zasu yi idan
sun je can."
Sarkin yaki ya yi murmushi akaro na
biyu ya ce, "Ya shugaba kai za a tambaya
domin kaga gogewarsu."
Sarki ya dan sha mur kana ya ce "А
dawo da su, amma da sharadi, sharadin
kuwa kada su dinga yawo har sai an isa
filin kuma ko da an je filin dasu, kada
dayansu ya kuskura ya fito su adana kansu
kamar yanda sauran matan da
39
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
muke tafe dasu suka adana nasu kan."
Sarkin yaki Safwan ya yi murmushi
ya kwalawa wani Babban badakarensa kira
wanda shi ne zai jagoranci mai da su
gidan"
"Ku dawo ya kai Zarfun, Sarki ya
bukaci dawowarsu amma kada su sake a
cikin dakarun yaki, su mai da kansu kamar
dabbobin gida."
Gaban yarima Ya yi muguwar
faduwa ya dubi Sarkin yaki ya ce. A wane
dalili.
Da jin haka sai Sarki ya ba shi amsa
da cewa "Akwai bukatar su, amma ba a
filin yaki ba.
Shadilat da Gimbiya Lushmaira suka
zo suka fadi gaban Sarki cikin murna suna
godiya.
Da ganin haka sai Yarima Zaiyan ya
turbune fuska, ya bar gurin domin bai so
hakan ba.
Lokacin da aka cika sa'a biyar a
40
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
wannan gurin sai Runduna ta kara ta shi.
Aka ci gaba da tafiya babu ji babu gani.
A can 6angaren su Sarki Tamas
kowa tuni tafiya ta yi nisa duk kasashen
sun hadu guri guda, fushi ne mai tsananin
a fuskokinsu cikin tafiyar takama da ihu
babu ruwansu da ibadu, dan kuwa babu
abinda yake tsayar dasu face gajiya, ko cin
abinci Sarakan su uku su kwashe manyan
dakarun sun saka su a tsakiya dan kyautata
tsaro.
A wani fafffadan daji mai yalwar
korayen ganyayyaki suka Sarki Tamas ya
yi umarni dan a tsaya a kara shiri na sosai
domin kuwa sun fara jiyo kamshi abokan
gaba.
Lokacin da Rundunonin mayaka
suka kafa sansuna sai kowa ya fara aiwatar
da abinda ke gabansa a can kuwa babbar
Tanti da Sarakan uku suka kadaice sai
Sarki Tamas ya dubi Sarki Madham da
Sarki Husaka ya сe.
41
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
Ya zame mana dole mu yi shirin na
sosai kafin a ce sai da muka riske su,
tafiyarmu haka kai tsaye ga makiya bata
nufin samun nasara kuna sane shi dai yaki
dan zambo ne musamman wannan yakin
da zamu yi shi da Birnin Lautul Nusur,
suna da mayaka masu naci da dagiya
wajen ganin sun samu nasara, abinda
zuciyata take raya min tun dazu shi ne, ina
son mu kasance ciki fatancen shiri ga
abokan gabarmu, ma'anar 6atancen shiri
shi ne ina son mu ware wata Runduna ta
tafi izuwa bisa hanyar da za su nufo, kafin
zuwa filin da muke tunanin hadu, su
wadannan Dakaru su zamo sun 6oye
kawunansu cikin ciyayyai ta yanda babu
yanda za'a yi su Sarki Abu Zaiyan su
fahincesu a gun.
Idan suka wuce su, kafin su yi masu
nesa sai su zari masu da kiboyu su yi musu
ruwansu, bayan haka sai su yi rufdugu
kansu, su yi dauki badadi koda na sa'a
42
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
bakwai ne, na tabbata idan haka ta faru,
zasu samu nasarar hallakar da yawa daga
cikin Dakarun Sarkin Abu Zaiyan duk da
cewar na tabbata babu daya daga ckin
Rundunarmu da zasu tsira, ya kuke gani
shawarar nan ta yi ko kuwa akwai wanda
zai bada wacce ta fita."
Da jin hakan Sai Sarki Husaka ya yi
ajiyar zuciya ya dubi Sarki Madham ya ce,
"Ni dai wanntan shawara ta yi min sai dai
kai, ya kake gani.?"
Sarkin Madham sai ya tuntsire da
dariya ya се.
"Babu sake, wannan shawara ta yi,
kuma na yaba da kwazo wajen yin wannan
zurfin tunani sai dai yanzu kamar yaya za
a samar da dakarun da zasu iya yin
wannan aiki kasan fa dole a samu masu iya
lambo da basaja cikin korayen ciyayi.?'
Koda Madhan ya zo nan a batunsa
sai Sarki Tamas da Husauka su ka yi shiru
daga bisa sai suka dubi juna, Sarki
43
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
Tamas ya yi saurin cewa "Ai babu
Rundunar da zamu zaba dan yi mana
wannan aikin face Rundunar Sadauki
Aksar, ba dan komai ba su ne maharba,
kuma duk inda aka san maharbi an san shi
da lamfo a bayan bishiya dan haka shi ne
zai jagoranci wannan aiki."
Nan take sukai na'am da wannan ba
tu take aka kira Sadauki Aksar aka sanar
dashi abinda ya zai yi. Batare da bata
lokaci ba ya aminta cikin gaggawa suka
zame jiki daga cikin sahu-sahu na
Miliyoyin rundunonin yaki suka bace daga
sashin suka nufi hanyar da suka durfafa.
A bangaren su Sarki kuwa tun da
suka ta shi daga wannan guri sai suka ci
gaba da tafiya ba tsayawa ya da zango in
har ba sallah ba ko cin abinci, a haka suka
kwana hudu, gajiya ta riske wasu daga cikinsu da yawa, lokacin da suka kwana na biyar ne sai murna ta kama wasu su
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
domin sun san cewar yanzo ne lokacin da
za zauna domin a huce gajiya ta tsahon
sa'a shida maimakon ta rabin sa'a da suke
idan zasu yi sallah ko cin abinci.
A wannan rana da rana ta cika na
biyar kowa yana sa rai da Umarni Sarki
amma Sarki ya yi shiru ya ki ya bada
umarni tsayawa, tafiya kawai ake, aka
tsaya aka yi sallah Azahar aka ta shi aka ci
gaba da tafiya, aka la'asar nan ma aka ci
gaba da tafiya, magriba isha'i a sannane
Sarki ya yi umarni da a tsaya a nan a huta.
Kowa ya fitar da tsammanin hutawa,
a ranar irin ta yau, dan haka lokacin da
suka ji umarni sai kowa ya cika da farin
ciki, kafin ma a fara kafa tanti wasu suka
zube kasa, Yarima Zaiyan da Gimbiya
Lushmaira da Shadilat kuwa suna jin
wannan umarni sai suka cika da tsananin
bacin rai domin a san su, ba za'a tsaya ba
har sai an isa dajin da za'a fara wannan
yaki.
45
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
Dan haka babu wani annuri akan
Fuskar Yarima Zaiyan tun daga farin
tahowa har zuwa wannan umarni na Sarki
takaicensa biyu tafiya da Shadilat, da
kuma Lushmaira, ga kuma wannan
tsayawar wacce ya fitar da rai da ita.
Hadiman da suke masa hidima suka
hada masa Tanti, lokacin da suka hattama
sai ya yi saurin barin gun, ba ko ina ya
nufa ba face Inda su Gimbiya Lushmaira
da Shadilat suke.
Lokacin da ya isa sai ya şame su, a
cikin Tantinsu su biyu zaune, cikin nishadi
da walwala, akwai kuyangi biyu da suke
masu hidima gabansu kayan marmari ne,
sai ruwan inibi a cikin tambula.
Koda gabatowar bakin Tantin sai
yarima Zaiyan ya yi musu sallama ya
shiga cikin tantin koda ganinsa sai suka ci
ka da mamaki, Shadilat cikin ladabi da
biyayya ta rankwafa ta ce, "Barka da
zuwan Yarima, garemu muna fatan
46
TURABAR GASKIYA-3
samun duban goyan baya gareka."
MADAKI
Koda yarima ya ji wannan daga
Shadilat sai ya nemi guri ya zauna, ya
kuma dubeta ya ce, "Barkan ki da
warhaka, ina fatan komai lafiya.?"
Ta yi wani kayataccen murmushi ta
kara dora dara-daran idanuwanta akansa,
sannan ta ce, "Komai lafiya babu fargaba
tunda har Sarki ya ji kanmu ya barmu yin
2,
wannan tafiya."
Ita kuwa Lushmaira lokacin da ta
gan shi cikin dakin sai ranta ya yi mutukar
baci, da kyar ta iya bude baki ta ce,
"Sannu."
A sa'ilin da ya ji yanda ta yi furucin
sai da ya dago kai ya dubeta, domin duk
rashin jituwar da take tsakaninsu bata tabа
nuna masa, a koda yaushe idan zasu hacп
zata bashi girmansa amatsayinsa wanda
yake gaba da ita. Amma sai ya kanne bai
nuna fushinsa ba ya dubi Shadilat ya ce,
"Kada ku cire fargabarku, domin а
47
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
kowane lokaci zasu iya komawa gida,
domin ni ban lamunci da tafiya da mata
ma'abota rauni a cikin irin wannan bakin
yaki da zamu durfafa.
Koda jin wannan ba tu sai Shadilat ta
yi shiru ita kuwa sai Gimbiya Lushmaira
ta yamatse fuska cikin kunkuni ta ce, Babu
rauni a tare da basadaukiyar mace da zata
iya karo da karatan Sadaukai sama da
Ashiri kuma ta samu nasara dan haka, ka
cire wannan batu a ranka babu halin da
zaka mai damu gida.
Koda jin wannan batu sai Yarima
Zaiyan ya ji ransa ya 6aci da maganar
Gimbiya Lushmaira amma sai ya kanne
bai bi ta kanta ba, har da dan murmushi ya
се.
"Sadaukai ko kuma ragwaye, kada ki
yi tsammanin ganin kuna yaki a junanku
na bajinta ki yi tunanin cewar za ku iya yin
bakin yaki da wanda ya taba halarta horon
yaki koda na kwana guda ne, dan
48
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
haka ki kiyaye kada ki dauki kan ki a
bakin komai, duk bajintar da ku kai a
bakin Ruwa na sani bana bukatar ki sanar
dani."
Koda Gimbiya Lushimaira ta ji
wannan ba tu sai ta yi kayataccen
murmushi ta ce, "Bana haufi idan akwai
jarabawa da zaka auna Sadaukantakarmu,
muna saurarenka, in kuma babu abinda
zaka jarrabamu da shi, to muna son ka
bamu sarari domin mu shaki iska,"
Cikin tsawa Shaidilat ta doka mata
tsawa ta mike tsaye ta ce, "Ya ke Gimbiya
kada matsayinki ya dinga mantar dake
waye Yarima Zaiyan, kada isa da iko ki
manta da isar sa da ikonsa, lallai furucinki
haramtaccene a gareshi don haka ki yi
biyayya ga yarima Zaiyan."
Koda Shadilat ta zo anan acikin
zancenta sai ran Gimbiya Lushmaira ya
tashi ainu cikin баcin ran ta dubi Shadilat
ta nuna ta da yatsa ta ce, "Kada kwarjini
49
TURABAR GASKIY'A-3 MADAKI
mulki ya rinjiyi ra'ayinki har ki dinga son
farantawa wanda yake son bakantawa
zuciyarki, ina son ki sani Ina daukar kaina
a matsayin Jaruma Basadaukiya 'yar na
gada, dan haka babu wani namijin da
jarumtarsa bata taka kara ta karya ba da zai
nuna min isa da iko, girman Mulki, kyau,
takama basa tasiri a gareni face kawai
girman Sadaukantakaа."
Lokacin da Lushmaira take sanar da
Shadilat wadan nan maganganun sai Ran
Zaiyan ya yi mutukar baci zuciyarsa ta hau
tafarfasa, da sauri ya matsa kusa da ita ya
kai mata wani bahagon mari, cikin bajinta
Gimbiya Lushmaira ta sunkuya hannunsa
ya mari iska.
Wannan al'amarin ne ya kara jefa
zuciyar Yarima Zaiyan cikin tsananin
bakin ciki, ya saka yatsansa a baki cikin
tsananin takaici ya ma kasa cewa komai.
Ita kuwa Gimbiya Lushmaira sai ta
fashe da dariya ta се, "Ко aljani ya san
50
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
kaidin dan adam yafi nashi, haka bana ko shakka, akwai shakkar mata a zuciyar
maza, don haka ka kula da kanka, ruwa ba
sa'an kwando bane."
Da fadar haka sai Lushamaira ta
doka tsaki ta bar cikin tanti, ita kuwa
Shadilat sai mamaki ya cika mata zuciya
ita kanda bata taba tunanin rashin jituwar
Yarima Zaiyan da Gimbiya Lushmaira ya
kai haka ba. Da kyar ta samu ta daure damuwarta ta matsa kusa da shi ta сe.
Ka yi hakuri Ya kai Yarima Zaiyan
hakika zuciyar Gimbiya a kekashe take,
ba wai bata nuna biyayya akan ka bane
don rashin tarbiya a'a tana haka ne kawai
don ta nuna maka cewar ita ma jarumace
tamkar, har kullum daukar kanta take
kamar kai."
Sa'adda Shadilat ta zo nan a cikin
zancenta sai Yarima Zaiyan ya dubeta
koda ya tsura mata idanu sai kuma ya
bushe da dariya, wannan al'amari shi
51
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
ya jefa zuciyar Shadilat cikin tsananin
mamaki har sai da ta yi tsammanin Yarima
Zaiyan ya kamu da ciwon damuwa wanda
har ya haifar masa da matsala ciwon
hauka, amma kafin ta yi aune da tunaninta
sai taga ya yi shiru kuma ya kara dubanta
ya ce, "Ki je ki kirawo min Gimbiya
Lushmaira yanzu ina son zan yi magana da
ta
Batare da Shadilat ta tambaye shi
dalili ba, ta juya ta fice daga cikin Tanti,
jim kadan sai ga su sun shigo ciki Gimbiya
Lushmaira ta nemi guri ta zauna bata ko
kalle shi ba, ita ma Shadilat ta zauna a inda
take zaune.
Koda ganin haka sai Yarima Zaiyan
ya dubi Lushmaira ya matsa kusa da ita ya
dan sunkuya dan rage tsaye sannan ya ce,
"Wutar daji, tafi kama da masifar da za'a
kirata da suna KUBUBUWAR AJALI,
sunan mai tarwatsa mazaje, a filin daga
Sadauki, ya yinda sunan makashin
52
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
dabba, mafarauci, dan haka kada yaki da
dabba ya sa ki girman kai har ki dinga
daukar kanki, a matsayin jaruma, koda
ganin kashe dabbar da kukai, ban yi
tunanin dama ke jaruma ce, na yi tunani
kamar haka, ashe dama makaminki mai
وو kaifi ne.
Koda jarumi Zaiyan ya zo nan a
cikin batunsa sai tsananin fushi da takaici
ya kama Gimbiya Lushmaira kai ba ma ita
ba har Shadilat wato duk irin abin da mu
kai nasara tana daga kaifin tsinin
masukanmu da takubbanmu, tabbas, ya ma
raina musu hankali.
Lushmaira ta dago da kai cikin 6acin
rai ta ce, "Ku ido da ido da Zakanya sai na
mijin gaske, duk wannan maganganun da
kake na riga na sani kana yinsu ne domin
hassada, ina son ka sani ita hassada tana
tauye aikinka na alkari, na aminta da duk
irin gwajin da kake tunanin za ka yi min in
har haka zai tabbatar maka da
53
TURABAR GASKIYA 3 MADAKI
cewar mai hannu daya baifi gurgu ba."
Da jin wannan ba tu sai Yarima
Zaiyan ya yi murmushi domin dama
abinda yake son ke nan ya dubeta ya ce,
"Da alama za mu iya kasancewa
anan gurin har safiya abin da nake so ku
sani shi ne a baya da mu kada, na yi tozali
da wata Zakanya da take halin laulayi,
Wani bajimin zaki da ya zamo shi ne
mijinta yana kewayeta tar da shinshinar
jikinta, wannan shi ya tabbatar min shi ne mijinta.
Abin da nake so da ku aikata har ya
sa na ji cewar kin isa jaruma ki tafi daga
idar da sallar Asuba zuwa ga wannan
zakanyar ki dauko jaririyar da ta haifa."
Koda Lushmaira ta ji wannan umarni
daga Yarima Zaiyad sai hankalinta ya
dugunzuma ya tashi ainun ta yi shiru, na
dan lokaci daga bisani sai ta dago kai ta yi
murmushi hade da cewa.
Ka dauki batunka kamar ka yi
54
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
rubutu akan dutse in har da rai da lafiya
gobe kafin kafin gari ya gama wayewa zan
zo maka da jariryar kada, amma ban damu
da ka yardar da jarumtakata, ina son ka
sani ranar wanka ba'a 6oyon cibi, ranar da
zaka gano ma'anar jarumtakata ita ce ranar
da jarumtakarka zata dakushe, a idon duk
wani jarumi dake cikin kasar Lautul Barus
ya zamana ni ake gani a matsayin jarumar
da ta kaini, kamar yanda aka rasa jarumin
da ya kai mahaifina a duk wannan kasar.
Koda fadin hakan sai ta fice daga
cikin Tanti ita kuwa Shadilat sai ta cika da
tsananin mamaki, ta yaya ake Lushmaira
take daukar kanta amatsayin wata uwa a
harkar jarumtaka, alhalin ni din nan da
muka kara banga wani kumarinta ba.
Shi kuwa Yarima Zaiyan sai mamaki
ya cika shi, ba komai bane ya sa shi
mamaki face irin karfin gwiwar da
Lushmaira take da shi, bai san sa'ar da ya
55
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
fice daga cikin Tanti saboda tsananin
mamaki.
Ita kuwa ku da ta fita daga cikin tanti
sai ta nufi can wani guri da babu kowa ya
samu guri ta zauna, ta fara tunanin.
Lallai na tsokanowa kaina abinda
yafi karfina, zaki ku da makami abin lura
ne a lokacin da za ka yi yaki da shi, ta
yaya zata iya yin yaki da Zaki har ta samu
ta daukar masa da, sabuwar haihuwa, sam
wannan al'amari ba zai yiwu ba shi kansa
Yarima Zaiyan ya yi hakane kawai dan na
rasa rayuwata.
Kai ba zai so mutuwata ba duk da Kiyayyar da take tsakaninmu, ya yi hakanne dai kawai dan ya kore ni, in kuwa
hakane ko da zan salwantar da rayuwata
sai na yi shiri da asuba na tunkari gurin
wannan zakanyarmo
wiw ma 95 1
ah Aikuwa washe gari tun da asuba ana idar da Sallah ko tsayawa yin addu'a
156
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
bata yi ba kamar yanda Sarki yake a
lukutan da aka gabatar da sallah, sai ta
mike ta sulele ta cikin ciyayi ta bi ta wata
siririyar hanya. Ta nufi gurin da Yarima
Zaiyan ya sanar da ita, cikin rashin sani
kuwa tana barin gurin sai aka shafa
addu'a, daga nan sai Sarki ya yi umarni
akan a ci gaba da tafiya.
Ko yarima bai yi tsammanin hakan
ba amma da ya ji wannan sanarwa sai farin
ciki ya cika masa zuciya domin ya na
ganin lokacin da Lushmaira ta nausa da
gudu cikin dawa, ya tabbata koda ta dawO
ba zata taba samunsu a hanya ba dole ne ta
koma.
Shadilat kuwa sai hankalinta ya
dugunzuma ta shiga damuwa ainu cikin
rashin karfin haka take tafiyar duk ta
damuu.
Sai da Gim Gimbiya Lushmaira ta yi
tafiya mai nisa a sannan ta isa inda Yarima
zaiyan ya kwatanta mata sai tawyi tsaye
57
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
tana duban wajen, sai an fada da gani biri zai
ci mutum. Dajin ya zamo ma'abocin kwarjini
sannan shiru ya mamaye gurin bake daya,
dan haka sai ta fara waige waige cikin sanda.
Bata ji doriyar wata dabbar ba, dan
haka sai ta rasa abinda ya kamata ta yi, domin
ta samu ta gano inda Zakanyar take, tana
tsaye cikin dube dube sai kawai ta ji gurnani
daga can nesa kadan, ko da ta tabbatar da
wannan gurnani ba na komai bane face
gurnani zaki sai ta gyara tsayuwarta ta kuma
kurawa gurin idanu, tana tsaye sai ga wani
narkeke Zaki ya fito daga wani kogo na
bishiyar darbejiya.
Da fitowar wannan Zaki sai ya 'yi
girgiza wanda ya haddasar da korar jikinsa ta
tashi sama, ya saka kafarsa yana sosa kansa.
Da sauri Gimbiya Lushmaira ta koma
da baya ta 6oye domin ganin Zakin ya yi
mutukar ranata, tabbas ko da ita da Shadilat
da kuma Yarima Zaiyan za su hadu ba za su
iya da wannan Zakin ba.
Tana nan rabe tana son ganinya
kauce domin ta sulele ta koma can in
58
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
da ta fito domin ta san wutsiyar Rakumi ta yi
nesa da kasa, in ma ba rainin hankalin ba ta
yaya za gwada jarumtakar dan adam da Zaki
jrin wannan alhalin kuma baka rike da komai,
tabbas sai yau ta kara yarda Yarima Zaiyan
makiyinta ne kuma baya kaunarta....
Numfashinta ya dauke lokacin da ta
hango Zakin ya nufo inda take 6oye gadangadan ta yi sauri janye jikinta dan kada ya
lura da ita domin ta fuskanci ba ita ya gano
ba a kwai inda ya yi niyar nufa.
Tana makale a jikin bishiya ya zo ya
wuce, yana gurnani. Yana wucewa Gimbiya
Lushmaira ta yi ajiyar zuciya har ta dauki
hanya zata koma sai kuma ta tuna da cewa
waye mahaifinta ta tuno irin gwagwarmayar
da mahaifinta ya yi a duniya kafin ya rasa
rayuwarsa, ta tuna irin bajintar da take so ta
yi anan gaba na soke idanuwan Macijiya
Burukul Kursum.
Nan da nan wani irin karfin ya shigeta
ta koma da baya ta dubi Zakin da ya yi nesa
ya nufi wata fadama dake nesa.
Cikin sanda ya juya ta nufi inda
59
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
Zakin ya fito, koda karasawarta sai ta sunkuya ta leka cikin abin da bata zato ba shi
ya faru tana lekawa sai taga jariran zakuna
gudu