An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Lokacin da runduna ta nausa bakin birnin L
Baitul haural jama'a da suka yo musu
rakiya basu koma ba suna biye dasu suna
daga masu hannu dan yin bankwana dasu,
wasu na yin kuka wasu kuma yin kabbara dan
karawa tarin DHOG Dakarun PTRS karfin gwiwa. Shi
kuwa Yarima Zaiyan har zuwa wannan
lokacin bai daina waigen wannan mai daradaran idanuwa ba, ba komai bane yasa ya
damu da dubata sai tunanin da ya cika masa
zuciya yana ganin cewar ba yau ya fara saka
wadannan kyakyawawan idanuwa ba a cikin
nasa idanu.
Koda ya fuskanci runduna ta kara yawa
nisa tsakaninsa da wadannan matan da suka
biyo a yarin likita Zuwad sun yi masa nesa
domin tazarar dake tsakaninsu ya kai kimanin
Runduna uku, wanda yawansu ya kai kimanin
dubu goma da doriya, wannan dalili yasa
Yarima Zaiyan ya hakura da waige ya cika gaba da sa kansa gaba tare da yin kabbara
kamar yadda daukacin dandazon mayakan kasar suke yi.
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
Shi kuwa Sarki Abu Zaiyan bai lura ma
da halin da Yarima ya shiga ba, gabansa
kawai yake kallon yana kiran sunan Allah, da
haka har aka zo bakin ganuwar garin, koda
zuwa wannan bakin ganuwar sai Sarki ya
daga hannu yana mai bankwana da
al'ummarsa wannan al'amari ne yasa bake
daya jama'ar kasar Baitul Haural suka kaure
da kabbar suna masu yi masu fatan samun
nasara, da haka har aka fice daga birni aka
mai da kofar birni aka rufe jama'a suka koma
gidajensu.
A wannan lokacin 'yanfashin da suke
fakewa cikin dajijjikan da suke hanyar shiga
birnin Baitul Haural sai suka ari ta kare suka
nausa cikin maboya domin ganin yanda
Rundunonin mayaka suka durfafo hanyar,
abin da suke zargi shine yau ran Sarki ne ya
6aci da abinda suke aikatawa dan haka ya yi
wannanı gagarumar hawa ya zo domin rushe
su ya murkoshe su, aikuwa zaman
mafakarma sai ya gagari domin ganin irin
yawansu suna ganin da an nufo inda suka
boye za'a riskesu dan haka suka ta shi
5
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
suka haye dawakansu suka nausa cikin dawą
cikin tsananin firgici.
Kananun dambobi kuwa da tsuntsaye
sai hankulansu ya dugunzuma cikin tsananin
firgici suka ta shi daga gidajensu suka arci ta
kare.
Sawayan dawakai gami da kabbarar da
Dakarun kasar Baitul Haural suke yi shi yake
saka saka faduwar gaba ga dukkan wani
mugu da ya fake dan samun makafa ya cutar
da wani.
Lokacin da Aka yi sa'a hudu da rabi
ana wannan tafiya Sai Sarki Abu Zaiyan ya yi
umarni dan a tsaya a yi sallah kana a ci gaba
da tafiya.
Koda aka saurara da wannan tafiya
na kasa da dawakai da rakuma sai suka
sauko nan fa aka shiga naura alwala, cikin
kankanin lokaci aka kira sallah rashin Ibin
Haishan limamin kasar da yake ba shi aka
yi wannan tafiya yana gida, hakan ya sa
Sarki Abu Zaiyan ya ja sallah. Bayan an
6
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
idar aka thaye dawakai aka ci gaba da
tafiya.
Sai da aka kwana biyu ana wannan
tafiya babu abinda yake tsaida su face yin
sallah ko abincin ba fara girkawa ba kowa
da dan guzurin da ya taho da shi yake yin
amfani.
Lokacin da aka kwana biyar ne a
cikin dokar daji ana wannan tafiya sai
Sarki ya yi umarni da a tsaya a lokacin ba
su fi sa'a hudu ba da yin asuba bayan sun
yi ta shi daga ibarci, sun yi sallah sun ci
gaba da tafiya.
Gurin da Sarki ya yi umarni a tsaya
guri ne mai koramai da yawan sanyi, guri
ne imai kyakyawan yanayi duk da cewar
guri ne mai hatsari gaske, domin kuwa
ba'a rasa kuraye da zakuna a gun mafi
akasari gurin ne ma guri mafi son zaman
wadannan dabbobi domin su shakata su
huta, amma jin doriyar jama'ar Kasar
Baitul Haural yasa suka arce suka nemi
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
mабoya domin suna zaton tashin
alkiyamarsu ya yi, kamar yanda suka sani
daga magabatan iyayensu da kakanninsu,
akwai ranar da zasu gushe ya zamana babu
bakya daya.
Lokacin da Rudunoni suka ja dagą
suka tsaya sai aka hau kafatantuna domin
dama a duk inda aka samu kwana biyar
ana tafiya cikin irin wannan tafiya to Sarki
sai a irin lokacin yake bukatar a huta
musamman idan yaga guri mai yalwar
nutsuwa da kuma ya kwanta masa, dan
haka suka sauka daga dawakansu.
Yarima Zaiyan da Sarki aka kafa
musu tanti mafi kusanci da juna Sarkin
yaki Safwan tantinsa yana kusa da na
Sarki ya zamana sun saka Tantin Sarki a a
tsakiya.
Koda da wasu tsirarin dakarun da
suke biye da shi suka nufo tantin sai Sarki
Abu Zaiyan ya dubi Tantinsa dake tsakiya
ya kuma dubi Tantin dansa da na
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
Sarkin yakinsa a gefe da gefensa sai ya
dubi Sarkin yaki Safwan ya ce.
"Ya kai Sarkin yaki Safwan ina
dalilin saka tantina a tsakiya, alhalin kana
sane da cewar ban yi umarni da hakan
ba.?"
Da jin wannan tambaya sai Sarkin
yaki Safwan ya sadda kai kas ya dubi
Sarki ya ce, "Ya shugabana idan ban yi
dai-dai ba ina fatan hucewar zuciyarka, na
kuma aikata hakanne dan tsaron lafiyarka,
kamar yadda Yarima Zaiyanu ya tsara ni
kuma na ga daidai din hakan, ya shugaba
tsaron lafiyarka a gareni wajibi na ne,
domin ba ni da wani aiki da ya wuce
hakan."
Koda Sarki ya ji wannan ba tu daga
Sarki yaki Safwan sai ya yi murmushi ya
ce, "Kada ka manta a lokacin da aka
rantsar da kai a matsayinka na Sarkin yaki,
ba ka dau alwashin kare lafiya ta ba, ka
dauki alwarin kare al'ummata ne iyaka
9
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
gwargwadon ikon, ba ni ba, sanin kanka
ne bana bukatar tsoron kuwa face na
Ubangiji da ya halicceni, dan haka ina son
a dauke wannan tantin a kai min shi can
saman wannan tsauni ta yanda zan kasance
ni kadai,
SIKIU
kuma cikin kula da al'ummata.
Koda Sarkin yaki Safwan ya ji
wannan ba tu sai hankalinsa ya
dugunzuma domin gurin da Sarki ya nuna
guri ne da baki daya mafaka ce ta
mugayen dabbobi masu hatsarin gaske,
dan haka ya yi saurin rissana bisa
kafafuwansa ya ce.
ya shugaba ka yi sani wancan guri
da kake nunawa babu komai a bisa saman
tsauní face, dabbobi masu hatsarin gaske, BUR
ka yi hakuri ka zabi wani guri ba can ba. VSarki Abu Zaiyan sai ya dakawa
Safwan tsawa ya ce, "“Ka barni a can din
ina sane na zabi can din kuma ba dan
komai na zabi gurin ba face na yi gadin
al ummata вв na tabbata idan muka
10
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
shagala cikin hutawarmu wadannan
dabbobi zasu iya saukowa suka bi bayan
wasu daga cikin jama'ata su nemi cutar
dasu, amma muddin ina gurin da zarar
dabba ta fito ni kuma zan yi karo da ita har
sai lokacin da kowa ya gama hutuwa kafin
cikar sa'a biyar cif da na dibar mana, dan
haka bana son ka kara wata magana yanzu
take ka yi umarni a kai min tantina can.
Yarima Zaiyan dake zaune a gefe bai
iya cewa komai domin ya san in dai Sarki
ne akan jama'arsa sai Allah, zai iya cewa
yafi son su da shi kansa, dan haka ya ja
bakinsa ya yi shiru duk da bai son hatsarin
dake gurin ba amma yana iya jiyo
hargagin zakuna da kukan wasu da'ikan
dabbobin da bai san ko wane iri bane.
Shi kuwa Sarkin yaki Safwan take ya
yi umarni da wasu dakaru su je gurin su
kafawa Sarki Sansani kamar yanda ya
bukata, amma ya yi umarni da kada su bar
gurin su tsaya su yi gadinsa.
11
TURABAR GASKIYA-3 3-VAIK2V MADAKE
n kuma Bangaren Likita Zauwad
da jama arsa sat su Shadilat da Lushmaira
suka kasande elkintsanadin farin ciki
ganim har nukwashenikwanaki Biyar a'na
wannan tafnyar dasu batare da anganos
ba, ganif haka sui suka saujiki suka shiga
harkokinsu San ransu amma duk da haka
fuskkokmsarrufo sukesk ak nог вned sар
nShadilarta dubi Gimbiya Lushmaira
taka wata harika na yi mutakat farckiidand kasanee eikin
wannan tallya godiyata ba zatai kare ga
Likita Zadwad sdnnan ieAlalyasa mun
BawA?iA Rostinlaniyalazan ypa masa
kyauta ta mmusamhan, sai dai abiнаа уаkе fadaimita ngaval shi mekyanznidan
Yarimko Bansurrgano ind bakys gamin zasw łya sawaalaK 2
sai tbye mnuti shaclat te de; TabbaPidhatsurkiya ganmürzathya dagd
mana kafa safedarZai Saka tsaro akanmu
2
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
sosai amma bana jin idan yarima ya
ganmu zai barmu take batare da Sanin
Sarki ba zai sa a maidamu gida."
Da jin wannan ba tu sai gaban
Shadilat ya fadi cikin tsananin bugun
zuciya ta ce, "Ya ke 'yar uwata aikuwa in
haka ne ya zama dole na canza tufafi
domin a lokacin da yarima ya dawo kaina
domin ya kara bincikena a yayarin da
Sarki ya kira shi, ina ganin kamar ya so ya
gane ni, domin har muka baro cikin fada
muka nufo hanyar waige yake yana
dubana ganin haka yasa na sauya gurin
tsaiwa duk da haka ina kallonsa yana ci
gaba da waigen kan layin da nake, tabbas
na san har yanzu bai aminta da zuciyarsa
ba zai ci gaba da dubana, dan haka ya
zama dole na sauya kayan jikina da wata
daga cikin matan da muke tare."
Koda Shadilat ta zo nan a cikin
batunta sai Gimbiya Lushmaira ta dubeta
da kyau ta се,
13
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
"Tabbas duk wanda ya sanki bayan
6oye idanuwanki da kika yi, idan ya ganki
cikin wannan mayani na rufe fuska zai iya
shaidake ba dan komai ba saboda launin
idanuwanki ina mai goyan bayan da ki
sauya kayanki yanzu domin a wannan
lokacin Yarima zai iya zuwa wannan guri
domin ya ci gaba da bincikensa, amma
yanzu kada ki tunkari kowa daga cikin
wadannan matan bari mu nemo Likita
Zauwad."
Nan take Shadilat ta amince take
Lushmaira ta bi wata hanya ta nemo Likita
Zuwad ta zo da shi izuwa in da suke.
Batare da 6ata lokaci ba suka kadaita
acikin Tantinsu. Lokacin da suka samu
guri suka zauna sai Gimbiyar Lushmaira ta
kwashe duk abinda Shadilat ta sanar da ita
da kuma bukatarta ta sanar shi.
Koda gama jin haka sai ya yi shiru
na tsawon lokaci daga bisani sai ya dago
da kai ya dube su sannan ya ce.
14
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
"Hakika kun saka ni cikin tsaka mai
wuya, tabbas idan ban yi wasa ba sai kun
sa Sarki ya yi fushi dani, ina son kú sani
shi Yarima Zaiyan mutum ne mai tsananin
kaifin basira tunda har ya dora zargin
akanki babu shakka ko mai zaki yi sai ya
nemo ki abinda zai hana ya gano ki kuwa
hanya daya ce, wannan hanyar ba wata
hanya bace face, zaki kasance cikin tanti
daga nan har zuwa lokacin da za mu ci
gaba da tafiya muddin zaki fito to babu
shakka ko mai zaki sauya sai ya gano ki
domin ina da tabbacin zai zo nan a yanzu,
idan kina cikin tantinki ba zai taba
shigowa ciki ba, amma in har kika fita to
zai ganki kuma zai sa amai dake gida,
lkawari daya nake so ki daukar min koda
a gano ki dan Allah kada ki taba nuna
inasa cewa ni ne na sanadinki zuwa nan.
Shadilat da jin haka sai ta yi na'am
da batunsa take kuma suka mike ya koma
bakin aikinsa ita ma Lushmaira sai ta
15
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
fice tabarta cikin tanti lokacin da
Lushmaira ta fita sai idanuwanta suka kan
wata korama ta da ruwa ki zuba farin ruwa
ne fat mai sheki saboda tsananin haske dan
haka sai nan take ta ji sha'awa shiga ruwan
ta yi wanka ya kamata.
Bata tare da ta shawarce kowa ba sai
ta nufi bakin ruwan da yake ya yi baya da
inda sansanin jama'ar su suke, gadan
gadan ta nufi gurin koda zuwanta bakin
ruwa sai ta cire mayanin dake rufe da
fuskarta, ta kuma cire dogowar rigar da
take jikinta ya zamana daga ita sai wani
dan bantai da rigar da ta rufe mata mama.
Kai tsaye ta daga tsalle ta fada cikin
wannan ruwan tsundum.
Shi kuwa Yarima koda mahaifinsa ya
tafi izuwa saman wannan tsaunin sai nan
da nan tunanin wannan da ya gani ya dawo
masa nan take sai ya mike tsaye ya nufi
sansanin matan da suka taho da su dan yi
musu girke girke da kula da lafiyarsu.
16
TURABAR GASKİYA-3 MADAKI
Tun daga nesa Likita Zauwad ya
hango shi nan take sai ya nufo shi cikin
dan murmushi "Barka yarima da wannan
Nokaci.ь д
Yarima Zaiyan ya dubi likita Zauwad
da murmushi akan fuskarsa ya ce, "Barkan
babban likita da warhaka, ya jama'ar taka
sina fatan dai komai lafiya?'
Likita Zauwad ya dubi Zaiyan cikin
murmushi ya ce,
"Ranka ya dade ai kowa lafiya babu
wani abu."
Da jin haka sai Yarima Zaiyan ya
girgiza kai ya ce, "Haka ake so, amma
akwai wani bincike da nake son yi a cikin
jama'ar da ka wo dasu ba dan ina zargi ka
staho da wasu ba, a'a sai dan ina zargin
akwai wata da ta 6adda kama ta shiga
cikin jama'arka batare da saninka ba."
Dal jin wannan al'amari sai Jikin
Likita Zauwad ya kama rawa bakinsa cikin
trawa ya се. пoD aр iamo an eA
17
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
"An ya kuwa ya shugaba, amma tun
da idanuwanka sun hanga maka ba zan yi
maka musu ba, amma da wuya hakan ta
faru, domin ko yanzu na duba duk jama'ar
da muka taho dasu."
Yarima Zaiyan ya ce, "Kada ka
damu na san ba lallai ka iya gano hakan ba
domin dama a boye take kuma ba zata
taba bayyana fuskarta ba.
Da jin haka sai Likita Zauwad ya yi
shiru Zaiyan ya yi gaba yana duba yanayin
jama'ar da suke ta faman aikace aikace,
shi kuma zauwad na biye da bayansa, duk
tantin da suka nufa suka ji motsi sai
Yarima Zaiyan ya ce, "Ayi sallama da na
cikin a haka har suka wuce Tantuna kusan
goma, ana sha daya ne, Yarima Zaiyad ya
tsaya duk da babu motsin kowa a ciki
amma sai Yarima ya dubi Zauwad ya ce
"Su waye a cikin wannan Tantin.?"
Likita Zauwad ya yi shiru batare da
ya ce komai ba. Domin kuwa ya san
18
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
cewar Shadilat ce da Lushmaira a cikin,
koda Zauwad ya yi shiru sai Yarima ya
kara yi masa tambayar.
Likita ya ce, Babu mamaki su
Haisara ce matar Sarkin yaki."
Yarima Zaiyan ya dube shi cikin
rashin fahinta ya ce, "Kamar ya ya kana ji,
dama akwai wani tanti da baka san ku su
waye a ciki ba.?"
Likita ya dan yi murmushi ya ce,
"Ya shugaba abunne da yawa, amma haka
ne wannan tantin Haisara ce, mun kuma
barota tana girki a baya."
Zaiyan ya dan matsa kusa da dakin
ya ce, "Tun da babu kowa bari na leka
domin ina zargin wani abu daga cikin
wannan tanti, yanda ya zama shiru akwai
alamar sirrin 6oye a cikinsa saboda tunda
muka taho nake nazarin tantuna idan babu
mazauna cikinsa akwai dalilin akwai masu
zama, amma shi wannan ya yi kurum
kamar kurma, dan haka bari na duba.
19
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
Gadan-gadan Yarima Zaiyan ya nufi
cikin Tantin ya leka kansa, shi kuwa
Zauwad sai ya yi tsaye sak domin ya riga
ya san a sirin Shadilat da Lushmaira ya
gama tunowa, bisa mamakinsa sai yaga
Yarima ya dawo da kansa waje ya ce. "Da
mamaki ace, an kafa tanti babu kowa a
ciki haka zalika babu alamar kowa din.?'
Da jin wannan batu sai farin ciki ya
kama. Likita Zauwad domin ya fuskanci
bai yi sa'ar ganinsu ciki ba, nan ya yi
hamdala ya kuma dubi Yarima ya ce,
"Babu damuwa zan binciki masu zama a
cikin kafin mu bar gun"
Kafin Yarima ya kara cewa wani abu
sai suka ji karar ihun namun dawa daga
can bayansu, kodn juyawar Yarima sai
yaga an wani zaki ya yi sufa a sarna ya
nufi wani 6angare na da koramar nan take,
batare da ya jira komai sai ya zare
makaminsa ya nufi gurin gauan gadan. Cikin tsananin fusata koda
20
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
ya isa gurin sai ya daka tsalle ya fada
farfajiyar gurin ya yi tsaye cikin tsananin
mamaki domin koda ya isa sai yaga babu
komai a gurin sai gawar wata Kada da zaki
da aka soke shi a makoshi.
Nan take mamaki ya cika masa
zuciya ya fara waige-waige amma bai ga
kowa ba, ya isa inda zakin yake kwance
matacce sai ya lura da mashin tabbas
mashin irin mashin da aka sana'anta shi ne
daga kasar su, to waye ya yi wannan aikin.
Ga jini yana zuba daga jikin zakin ita
kanta Gadar jini ne yake malala a jikinta
alamar yanzu yanzu aka aika dasu
barzaho.
Nan take zargi ya shiga ransa ya fara
kewaya gurin sai da ya kusa rabin sa'a
yana zaga bakin ruwan nan amma bai ga
kowa ba, a sannane Likita Zauwad ya kara
so gurin shima ya taya shi dubawa. Har
yarima Zaiyan ya juya zai bar gun sai
kawai ya hango wasu suturu a makale
21
TURABAR GASKIYA-3
a jikin wata bishiya.
MADAKI
Koda ganin wadannan suturu sai
mamaki ya kama shi take ya nufi suturun
ya saka hannun ya dauka kayan mata ne
dogayen riguna irin na matan da suka fito
da su, nan take hankalinsa ya dugunzuma
ya nunawa Zauwad kayan ya се.
"Shin za ka iya shaida masu wannan
kayan.?
Zauwan ya girgiza kai cikin alamun
rashin sani ya ce, "Ya shugaba tabbas
kayan kaya ne irin na matan da muka zo
da su, amma ba zan tantance kayan wacece
ba.
Zauwad ya gane ko wane kayane ba
kayan kowa bane face kayan Lushmaira
nan da nan shima ya shiga tsananin
mamaki ya dubi Yarima ya kara da cewa
"Abinda ya kamata, yanzu ka shaida kayan
ko wacece zata zo ta dauka ka ga idan ka
gansu a jikinta zaka ganota watakila ita cе
TEWEX
22
TURABAR GASKIYA-3 MADAKІ
wacce kake zargi da satar hanya ta biyo
bayanmu."
Koda jin wannan ba tu sai Yarima
Zaiyan ya girgiza kai ya ce, "sam haka ba
zai yiyiwu ba domin kuwa idan na bar
kayan nan a nan dole zata dauka ta canza
musu kama, amma yanzu idan na tafi dasu,
koda a ce wacce ta biyo ce dolenta ta
hakura ta koma tunda ba zata ci gaba da
biyo mu tsirara ba, koda ma ta biyo mu
farat daya zamu shaidata dan haka mu
wuce mu koma cikin al'umma”
Koda gama fadan haka Sai Yarima
ya yi gaba abinsa shi kuwa Zauwad sai ya
bi bayansa cikin matsananciyar damuwa
da mamakin Lushmaira da ta iya karawa
da wannan narkekiyar dabbobin masu
hadarin gaske.
Al'amarin Sarki Abu Zaiyan kuwa
tun sa'ar da ya nufi saman tsauni ya ga
wasu dakaru da Sarkin yaki Safwan ya
barsu dan su kula da lafiyar tsaitsaye sai
23
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
ya dube su ya ce, "Ku kuma mai kuke
anan.?"
Daya daga cikinsu cikin rawar murya
ya ce, "Ya shugaba Sarkin yaki ne ya ce
mu zo don muyi tsaron lafiyarka, har ka
kwanta ka yi barci."
Da jin haka sai Sarki ya dube su ya
ce, "Kun taba ganin inda Kura tayi tsoron
lafiyar Zakin dawa.?"
Su duka suka duburburce suka kama
kallon juna.
Koda Sarki Abu Zaiyan yaga basu
fuskanci abinda yake nufi ba sai ya ce,
Ina son ku sani Kura ba zata tabа
tsoron lafiyar Zaki ba, dan haka ina mai
umartarku da ku je ku sanar da shi duk
wanda ya kara zuwa nan domin ya
tsoron lafiyata to babu shakka sai mun
gwabza yaki da shi, domin a bambancin
tsakanin aya da tsakowa."
Da jin haka sai suka yi sim-sim suka
sauka daga kan Tsaunin suka koma
24
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
kasa, koda saukar su sai Sarki ya dubi can
nesan saman tsauni sai ya lura a she wasu
gungun Zakuna ne sun kai kimanin sun
goma sun yi cirko cirko suna kallonsu,
ashe abinda ya hane su da zuwa inda
wadannan dakaru suke ganin dogayen
masu a hannunsu dan haka suna sauka sai
suka tada jijiyoyin wuya suka fara harbin
iska suna gurnani."
Shi kuwa Sarki da yaga haka sai ya
fasa shiga cikin tantin ya tsaya yana
dubansu, duk irin jarumtaka da Sarki yake
takama da shi sai da ya ji shakkar
wadannan zakuna domin Kananun cikinsu
zasu iya kai girman dan marakin jaki,
kuma su biyu ne kananun sauran manya
kuwa kowanne zai iya kai girman bajimin
Sa.
Babu abinda yafi abinda yasa ya kara
jin shakkarsu sai ganin yanda suke bude
bakunansu wasu irin tsaratan kaifafan
hakura suna haskaka masa fuska,
25
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
ga wani yawu yana dalala, koda suka kusa
kara sowa sai ya duba jikinsa ashe ya
sha'afa ko 'yar karamar wuka bai hawo da
ita ba.
Aikuwa sai suka kara kaimi suna
zagaye shi, wannan al'amari ba karama
tada hankalin Sarki ya yi ba amma saboda
tsananin jarumta sai yaki ya sauka kasa ya
nemi agajin dakarunsa, duk da cewa yasan
daga inda yake zuwa saman tsaunin akwai
nesa sosai, bare ma ko ba nisa ba zai taba
neman taimakonsu ba, nan take sai ya
sauke ajiyar zuciya ya dubesu kwanon
abincinsa da ya taho dashi sai ya ajiye shi
a gefe.
Ya murda jikinsa ya bada wani sauti
karas. Kafin ya yi aune wadannan Zakuna
sun taso masa haikan kuma su duk.
Cikin tsananin zafin nama shima ya
yi kansu, nan take suka kaceme suka
hargitse da tsananin hargitsi mai munin
gani, duk irin wannan gunji da suke
26
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
jama'ar kasa basa ji duk da,cewa Sarkin
yaki Safwan yana zaune a kasan tsaunin
domin ya tabbatar da tsaro amma komai
basa jin sai. shiru da yalwata a tunaninsu
ma yąnzu haka Sarki ya yi barci.
Abin da, basu sani ba ashe Sarki na
can yana arțabu da zakuna masu tsananin
jin yunwa da da kishirwa, dama haushinsu
suke ji sun zo sun mamaye musu guri.
Da farko Sarki ya fara kokarin wajen
kai musu bugu da hannunsa amma da
tsamari ya kai tsamari sai ya fara tsille
musu, domin koda ya doke su sai sun yage
shi a hannunsa, ko kuma su bangaje shi
wanda idan suka bangaje shi sai ya ji
kamar wani katon dutse ya bangaza, dan
haka cikin Kankanin lokaci suka dimauta
shi suka dugunzuma masa lissafi.
Ya yi danasanin rashi zuwa da
Takobi domin da akwai takobi a tare dashi
da tuni ya gama dasu, ko mai gama dasu
27
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
ba da tunanin su faman jin tsananin azaba.
Babbar cikinsu ita ce mai tsananin
dabara yaki da iya fada, domin sai
Kananun sun yunkura suna fafatawa dashi,
sai ita kuma ta ja da baya ta dako tsalle sai
dai ya ji ta bangaje shi, haka nan suka
dinga wannan dabara har Sarki ya fara fita
daga haiyacinsa.
Da kyar ya samu ya kama Wata
zakanya da ta take kokarin cafkar masa
hannun ta cinye ya yi tsalle ya dokar mata
fuska, ta yi wata kara ta kara nufo shi ya
kara yin karfin hali ya kara nausarta nan
take ta yin laushi, amma saboda tsananin
naci sai da ta kara nufo shi koda ganin irin
wannan taurin ran nata sai ya shammace ta
na zuwa ya dagata sama ya cillata can nesa
da nan take ta rikito izuwa kasa gurin
wannan koramar ruwa da Gimbiya
Lushmaira take.
A wannan lokaci Gimbiya
Lushmaira da Shadilat suna boye a
28
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
jikin katangar tsaunin nan sai kawai suka
ga wannan zakin ta rikito kasa kuma ta
fadi kasa matacciya, sai hankalinsu ya yi
sama suna daga kawunansu sai suka hango
Sarki Abu Zaiyan yana fafatawa da
Zakuna a lokacin da ya yi tsananin jigata
da kyar yake iya daga hannu ya kare
kansa, nan take suka daka tsalle suka
dauke makamansu suka haye saman
tsaunin da gudun gaske.
Koda suka isa tuni Sarki ya gama
galabaita ya zamana da kyar yake iya bude
idanuwansa, koda suka hawo saman
tsaunin sai suka farwa wadannan Zakuna
da suka da sara kafin kace meye wannan
tuni sun karar dasu, lokacin da suka gama
yakar wadannan dakaru Sai Shadilat da
Lushmaira suka nufi hanyar sauka dan
kada Sarki ya gane su domin ko a lokacin
da suke kwafsawa da wadannan Zakuna
suna yi suna rufe fuskokinsu.
Har sun bi hanyar sauka sai
29
TURABAR GASKIYA-3 MADAKI
دو Sarki ya ce "Ku dakata ya ke 'yata."
Koda suka ji maganar Sarki suka
tabbatar ya gane su sai suka tsaya suka
jiyo a hankali da yake a lokacin Shadilat ta
cire dankwalin kanta ta bawa Gimbiyar
Lushmaira ta yane jikinta dasu dan haka
ba a iya hango jikinsa dai dai kaurikanta.
Koda suka tsaya sai Sarki ya mike
tsaye da kyar ya ce, "Ku bani labarin
yanda aka yi kuka biyo bayanmu alhalin a
cikin lissafin tafiyarmu babu