Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Gyada kai tai, har suka shiga cikin gidan a ranta ta ce. "ko makabarta ana magana balle nan!" A tsakiyar Main falo suka tsaya, karar inji yasa suka juya bayansu. "Kan bura uban can................. Hhhhhh kome ta gani ga Zeenobia ga Malik..... *Assalamu alaikum......! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A'ishah. +227 84 50 64 76 500* *Idan na samu lokaci zan karo page 1 zuwa dare! In sha Allah* [01/09, 1:17 pm] usmanlauratu71: CINIKIN RAI....20 Beauty and the beast. Mai_Dambu🌚 *Wannan shafin na ku ne, Aunty Halima da Habibay ku more!* <<<<<<<|=|>>>>>>>>> Wato dukkan hankalinta ta daura akan shi, har ya fito falon baki ɗaya. *Wheelchair!* Ta furta a kasar zuciyarta. Dauke kai tayi tana dariya ƙasa ƙasa, d'ago idanu yayi ya zuba mata. Sake kallonshi tayi ta kunshe dariyarta, baki daya sai yaji ya muzanta. Jikinshi ya wani irin sanyi. "Ke meye haka?" Dake bata iya boye abin da yake ranta ba ta ce mishi. "Malik Menk Jordan! Ya kare akan keken guragu. Wai dama wannan shi ne dalilin da yasa shi nisanta kanshi da Al'umma?" Ta kuma kwashewa da dariya, sannan ta dan durkusa akan gwiwarta kamshin turaren Imperial Majesty ya daki hancinta. Sau daya ta tab'a jin kamshin nan, a rayuwarta sai yaui. "Ko a yaya nake bana kunyar haduwa da mutane, sannan maganar pmutane bata gabana. Ni mutum ce me ra'ayin kaina. Ban zo nan domin Kasuwancinmu ba, nazo na ga waye ya firgita mutane da Gwamnatin kasa baƙi daya. Ka ji da kyau, bana tsoron tunkarar kowacce matsala, amma a karon farko na rayuwata da na ga makirkirin matsala ya koma gefe yana gudun matsala, shi yasa na mishi dariya. Da nasan cewa Malik Menk Jordan ya gudu daga cikin al'umma saboda nakasarshi da ban tako nan ba!" A karon farko da yaga macen da ta saka shi ya ji ashe, shi in matsoraci h ne. Ashe tsoro ne ya saka shi boye kanshi. Kasa magana yayi ya kalli Elbashir. "Coffee take bukata ko Tea?" Wani dariyar takaici ne ya kamata, wato shi a haka har wani izza ce da shi. Haka kawai zuciya ta ingizata ta kai mishi naushi. Kafin ta idda nufinta, ya ja kekenshi. Sai da ta fadi can. "Ke baki da hankali ne?" Elbashir ya fisgota zai kifa mata mari. "Kyaleta mana, bakuwar mu ce tana buƙatar karramawa ko wacce iri ne!" Gyada kai yayi. Fita yayi kallon Malik tayi yana tafiya a keken shi har gaban wani table. Zaman shi ya gyara yana kallonta. Nuna mata kujeran da yake facing ɗinshi yayi. Hadiye yawu tayi tana me zama dakyau ta ce mishi. "Da gurgunta kake niman maza?" D'ago kai yayi ya kalleta, kasa tayi da kanta tana wasa da file din hannunta. Kwarjini ya mata lokaci guda, yadda ya kura mata idanu, tana jin ba dadi domin tsakani da Allah idanunshi na da kaifi. "Me kake so?" Ta tambaye shi muryanta a shake. Murmushi yayi yana me juya kekenshi. Shigowa aka yi da tiren tea. Elbashir yana biye dasu, duk maza ne kuma matasa. Ajiye a gabanta suka yi, Elbashir ya koma gefenshi ya tsaya a gefenshi. "Sha!" Ya fada a sassanyayye. "Ba na shan ruwa ko wani abu a inda ban yarda dasu ba!" Murmushi yayi ya ce mata. " "Sugar nawa kike so.?" "Guda bakwai!" "Bakya tsoron ciwon sugar ne?" "Waye ya damu idan na mutu? Don haka zanji dadina kafin na mutu." Duk da tarin yarintar da ya hango a tattare da ita, amma kuma ya fahimci tana fadar duk abin da ya fito daga zuciyarta ne. Sai da ya zuba mata sugar hudu, ya juya kafin ya d'an diba a cokali ya sha kaɗan, ya tura mata. Da wutsiyar ido ta kalle shi ta ce mishi. "Duk da haka ba zai saka na sha ba ""Ok" ya kai spoon zai diba Elbashir ya ce mishi. "Malik ka manta baka shan sugar!". Juyawa yayi ya kalli Elbashir ya ce mishi. "Kai haba dole mu karrama bakuwar mu" Sai da ya sha sau uku kafin ya tura mata har da cookie ɗin. A hankali ta dauka tana kallon coffee ɗin. Kurba tayi a hankali, "Idan kuma da mun saka, guba fa?" "Tunda ya sha ai zamu mutu tare ne!" Murmushi Malik yayi yana kallon ɗan bakinta yayi, yana girmama maganar da yake fitowa sam babu mara ma'ana sai dai rashin da'a. Ajiye kofin tayi tana faɗin. "Ya ishe ni" "Muje ji ga gidan!" "Tab! Ba ji ya kawo ni ba." Ta mika shi file ɗin. "Da dai kin tashi kunje!" A fusace ta kalli Elbashir. "Ban zuwa wani abu ne?" Ta tambaye shi, "ko daya" "Ok Ina file ɗin!" Mika mishi tayi ya dauki medical glass ya saka sannan ta ce mata. "Su mutanen da suka baki aikin me yasa basu, bawa Yaransu ko su kansu ba?" Shiru tayi tana kallon shi, sam bai yi kama da wanda yake dogon magana ba, amma yadda yake magana. Yana kara saka mata mamakinshi. "A Kasuwancinmu, cinikin rai yafi kome armashi da me zaki biya asarar da aka min?" Kallon shi tayi, sannan ta ce mishi, "Na sani rayuwa ita ce fansar, tsinannen dukiyarka" "Ke ki iya kalamanki!" D'aga hannu yayi alamar Elbashir yayi shiru. "Hmm! Ina jinki." Ganin babu ɓacin rai ko muzanci a kan fuskarshi yasa ta sake wani lalacin murmushi ta ce. "Ba fa ni ce ba fada ba, abin da naji mutane na fada ne, me yasa ba acin dukiyarka?" "Saboda gumina ne, babu gumin kowa a cikinshi." "Kana cire hakkin Allah kuwa a cikin gumin naka?" Rintsa idanu yayi ya ce mata. "Bana cirewa ko zaki cire min ne?". Kallon shi tayi sannan ta ce mishi. "me yasa kake jin haushi?" Nuna kanshi yayi sannan ya ce mata. "Bana jin haushin!" "Kana jin haushi mana, kokarin boye fushin zuciyarka kake, amma kafi wancan sikagon fusata!" Ta kalli Elbashir. Matse hannunshi yayi sannan ya ce mata. "bana jin haushi, baki gani ba ne!" "Kana jin haushi tunda gashi kamar zaka karya kashin hannunka, Malik" ta kira sunanshi a hankali, ta fuskance shi. "Kasan me? Nayi abubuwa dayawa a rayuwata, kama manyan laifuka zuwa kananu. Amma na iya saita kaina, kai kuma tunda nazo naga fushi da ɓacin rai a kan idanunka, idan baka manta ba kasan dalilin da yasa na kai maka duka? Domin na kara yarda da cewa kana cikin fushi ne, and saka hannu zan tafi" Ya kai tsawon shekaru sha uku a wurin zaune, amma babu me zarrar gaya mishi magana ko wacce iri sai an sunkuyar da kai amma yarinyar da yasan da yayi aure da wuri da ya haifi wadanda suka haife ta , take gaya mishi magana son ranta. "Saka min hannu?" Shiru yayi yana nazarin abun da ta fada, a fusace yake? Yes a fusace yake na tsawon shekaru arba'in yana cikin fushi da fushin wani. Amma kuma me yasa yarinyar ta zo har niman shi? Shin Ishara ce tazo ta mishi ko kuma tazo ganin sirrin shi ne ta gaywa duniya. Kamar ta san me yake tunani ta ce mishi. "Ka da ka damu, ban tab'a tsurku ba, sannan ban iya saran kowa ba, bana yin ka domin na fallasa asirinka, bana zama da kai domin dukiyarka, abu daya na sani idan kayi min halacci, zan maka biyayya kamar kare amma ba zan dauki cin mutunci ba, domin ina da saurin hannu. Abu daya nake son na gaya maka, a matsayinka na Mayor mai gari, ina son ka fito cikin al'umma ka, su san waye shugabansu ba ka zauna a tsibiri kamar wani namun daji ba." "Hmm! Kin ga?" Tab'e baki tayi tana faɗin. "Yo kwana zan yi ina surutu? Saka min hannun?" "Zan saka hannu amma da sharadi!" Tsam tayi da ranta, kafin ta ce mishi. "Hmm! Bayan ka saka hannun kenan sharadin zai biyo baya, amma yanzu ratab'a kawai." "Ki tsaya ki shi sharadina!" "Ina fa, kawai saka min sai ka faɗa min!" "Kamfanin da zan saka miki hannu akai, basu da." "Wannan daga baya zan ji da shi, saka min hannu!" "Mutanen da suka turo ki." "Malik Menk Jordan!" Tun daga tsakiyar kanshi ya ji sunan har sai da yaji tafin kafarshi tana kaikayi. ""Please saka min hannun." Kura mata idanu yayi ya ce mata. "Me yasa ba." Dan mikewa tayi ta zago bayanshi, ta dan rankwafa kadan daidai kunnenshi. "Ka saka min hannu, duk wani abin da zai faru. Zan magance shi bana son jan rai ina da wutar ciki.!" Yadda take maganar daidai kunnen shi ya haifar mishi da mutuwar jiki. Pen din hannun shi ne ya fara kokarin fadi, Elbashir ya fisgo ta, tare da dawo da ita kan kujeranta. "Ke wacce irin mutum ce?" Murgud'a mishi baki tayi, ta ce mishi.. "Dan bakinciki ina ruwanka da mu? Koma meye matsalarka da mu? Yau naga hassada. Gaskiya Uncle Malik ka gaya mishi ya daina saka min idanu." "Elbashir!" "Na'am Ubangidana!" "A kiyayye!" "An gama" "Haka ya miki?!" "Dama-dama, dan sarki akan jaki." "Kamfaninku tana da license?" "Wai duk akan saka hannun kake wannan bididdigin?" Ta fada tana kokarin kwashe file din, tunda ya kasa saka mata hannu. Rike file din yayi ya ce mata, "zan baki cheque, ki tafi ki kwashe duk yawan abin da kike so, amma ki sani da shar"Ka cinye sharadinka, na fasa." "Gashi nan ki saka iya adadin kudin da kuke so." "Kace na saka iya adadin kudin da ya mike?" "Yes!" "Ko ba Yes ba!" Ta karbi takardan cheque, sannan ya juya banki daya suke." "Golden bank?" "Kin san banki ne?" "Eh anan nake ajiye kudina!" Yadda suke jira zaka dauka sun shekara guda da sanin juna, hiran ba wai na arzikn bane, saka iya adadin kudin da suke bukata tayi, ta mika mishi. Kallon kudin yayi sannan yayi sign.. "ka duba yayi ko?" "Eh Malik na saka a cikin littafin amsar Cinikin rai ne?" "A'a" ya fada yana sign a jikin file din da ta zo da shi. "Me kike so yanzu?" Mikewa tayi tana murmushi, "me kuwa zan bukata, bayan wanda na samu? Kawai na gama sai an fara juya kome." "Idan wani abu ya samu dukiyata, sai kin biya." "Idan ban biya ba, a rataye ni. Kuma ka gayawa Awakin da suka kawo ni ahir dinsu, a kuma rufe min fuska idan ba haka ba, hukumar kare hakkin dan Adam zata shiga tsakanin mu." Karfin halinta kawai suke gani, "eyeee haka kuke barin abokin cinikayyar ku, ya tafi shi daya babu dan rakiya?" Kallon juna suka yi. "Ke dalla tafi can, tunda Malik ya dawo nan bai." "Muje a rakata ai bakuwar mu ce!" "Tow Malik!" Inji Elbashir, wani gatsina fuska tayi ta ce. "Kai wallahi baka da hali, wato aikin kwarai ba zaka saka shi yayi ba, kana nan a bayan shi kamar bindi. Wallahi ka ji tsoron Allah, ka daina hana shi aikin alkhairi ba halin musulmin kwarai ba ne." Haka suka rakota har waje. Kallon Malik tayi ta ce mishi. "Turarenka yana min kama da kamar mun tab'a haduwa, a wani wurin but i can say ga inda muka hadu ba." Ta fada tana kallon security na cikin gidan baki daya. "Kana kula da rayuwarka sosai." Ta dan dukka kaɗan. "Kamar yadda kake kula da dukiyarka, da kuma." Kasa jan numfashi yayi, domin abin da yake mugun gudu kusanci. Baya yayi da keken shi ya ce mata."ki kula da rayuwarki da mutanen da suke zagaye dake!" Sake baki tayi sannan ta d'aga kafad'arta ta cigaba da tafiya. "Malik me yasa ka amince ka saka hannu, bayan kasan ita kanta ba ra'ayin kanta ba ne?" "Babu kome, domin ko na maka bayani ba zaka gane ba ne!" "Zan gane mana, ka min bayani yadda zan fahimta. Mutanen mu suna ta bibiyar alamarinka zaku gana, kaki amma ita lokaci daya ka bata damar ku gana!" "Hmmm! Zak fahimci dalilin sai nan da yan lokaci ƙalilan." Daga haka ya juya da kekenshi. *Gudu kai saboda nakasarka?* "Elbashir yarinyar nan tayi gaskiya, a gyara min gidana na whiter town!" "Malik tunda nake da kai, tsawon shekaru arba'in baka tab'a canza maganar ka ba, yau kai kace cewa zaka koma whiter town?" "Na yanke shawarar haka, a maida ni whiter town!" ★★★ Kamar yadda suka daukota haka suka mai da ita, bata zame ko ina ba sai kamfanin Amjad. "Ajiye mishi tayi a gabanshi." "Gashi nan na samo kome!" Kallon cheque din yayi, ya ce mata. "Are you sure kin ga Malik?" "Kai baka.tab'a ganin shi ba ne?" "Ko hoton shi kuwa ban tab'a gani ba!". ."tow gashi nan, zan tafi gida." ""Da wuri haka?" "Eh ta saka kai zata fita!" "Zeenobia na gode sosai!" ""Ba kome" Ta fada tana me barin Office ɗin, ko minti biyar bata yi da barin kamfanin ba, MD da Salim suka shiga kamfanin aka shiga kwashe kome, kafin karfe shida na yamma sun kwashe kome sun sallami ma'aikata. Karfe tara na dare, ginin kamfanin ya ruguje ya zube kamar ba a tab'a ginin shi a tsaye ba..... *Zan kara muku page daya ya zama last free page in sha Allah idan na gama book one, book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three* *Assalamu alaikum......! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A'ishah. +227 84 50 64 76 500* [01/09, 9:04 pm] usmanlauratu71: CINIKIN RAI....21 Beauty and the beast. Mai_Dambu🌚 Last free page BOOK ONE <<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>> Shigowar Elbashir falon yana zaune a saman sofa, ya mike kafaffun shi yana kallon network news Elbashir ya ajiye mishi tap din a gabanshi. "Malik sun gudu daga zarrar kuɗin!" Grape ya dauka daya ya saka a bakinshi hankalin shi yana kan tv ya ce mishi. "Ita yarinyar ta sani?" "Da alamu bata sani ba!" "Rigimar shekaru arba'in ne ya dawo sabo fil." Ya fada hankalinshi yana kan tv. "Amma kamar babu ruwan, Khuldu Jahid Khan!" "Da hannun shi mana!" Ya d'ago kai yana kallon Elbashir, "ko kai ne ai zaka yi abin da ya fi haka." "Subhanalillahi, Allah ya min tsari da cin amanarka Malik gara naga mutuwata." "Hmm!" Shiru suka yi, kafin ya sake murmushi yana faɗin. "Yanzu ya zamu yi? Domin dai kasan kudina ba zai sha ruwa ba." "Duk yadda kace Malik haka zamu yi, domin nasan basu bar kasar nan ba. Idan kuma sun bar kasar tow ko suna teku ko suna bakin borda." Murmusawa yayi ya ce mishi. "Yarinyar nan ta ce, wai ina fusace!" "Sharrin kuruciya ce, baka fusace!" "Nuratu ma ta gaya min shekaru goma sha takwas baya, ta ce ina fusace amma yanayina a sanyayye yake." "Allah ya mata rahama, kasan saura kwana biyu Birthday din yan biyu?" "Na sani!" "Ka gayyato min yarinyar nan!" "An gama Malik!" "An gama kintsa min whiter town?" "An gama Malik domin kome na cikin gidan sabo ne, idan baka manta ba kome da muka bari babu abin da ya samar." "Ina son gobe Keivroto tayi sabon bakon, a gyara min gashin kaina, ina son furfuran nan su fito da kyau, fuskata ta tara kasumba a gyara min ita, ta fito shar na dan samari. Domin bayan sallah Azhar nake son na dira a cikin birnin! Domin na nuna mata ni ba matsoraci ba ne!" "Allah ya kiya shemu aikin danasani kai ba matsoraci ba ne, tsoro da kanta gudunka take!" "Hmmm! Me ya bawa yarinyar nan kwarin gwiwa, ta gasa min bakar magana haka?" "Haka take Malik, bata da kunya da d'a'a." Jinjina kai yayi yana faɗin. "Tabbas ba ga haka, naga wannan rashin da'a a cikin Idanunta. Zainabia!" Girgiza kai yayi sannan ya ce mishi. "Su shatima su same ni, a whiter town!" "An gama Malik!" Sannan ya fita, can sai gashi tare da wani saurayi, ya zo da wani akwati ya fara fidda kayan aikin, sai da ya fara mishi gyaran fuska, sannan ya rage mishi gashin kanshi. Malik baki ne asalin bahaushe wanda jinin hausawa ko nace kanawa yake gudu a jikinshi, sai dai ya biyo siffar Mahaifiyarshi dogo ne, me matsakaicin jiki. Fuskar shi doguwa ce, wacce ta badawa hancinshi damar bajewa. Domin bai da siririn hanci, hancin a baje take yana da kakkaura leb'a. Ƙwayar idanun shi sak take da ta zakuna, kasancewar uwarshi baturiya ce, Malik yana da fadin kirji, sannan a murde yake sosai, domin ko ba a gaya maka ba, kasan yana cin karfe. Dan kimanin shekaru hamsin da bakwai, yana da yawan suma sannan a tsaye yake kamar Superman ko Ironman. Idanunshi manyan ne, wani lokaci da iya su yake barazana, Malik yana da zafi wanda matukar baka kasanshi ba, zaka zata irin mutanen nan ne masu sanyin hali. Nan kuwa babban mugu ne me shegen bakin halin tsiya. Wani abun dariya shi baya boye furfuran shi. ★★★ Tun da ta koma gida, Shatima ya addabi rayuwarta da waya. Karshe turo mata text yayi. *Ki dauki kirana!* "Wannan tsohon da naci yake, da talauci ne da an shiga uku da shi!" Ɗaukr kiran tayi, ta ce mishi. "Meye zan maka?" "Baby gani a kofar gidanku!" "Eyeeee! Kace?" T "Eh gani a bakin get din Al'umma Charity House!" Ware jdanu tayi ta ce mishi. "Gani nan tow" Ta fada a sanyayye, domin bata san da gaske zai zo ba, ta shi tayi ta nufi drower ɗinta, abaya ta ciro tana sakawa akan Bom short dinta, ta fito waje yana tsaye a jikin motar. "Wai ba na gaya maka gaskiya ba, Ni fa ba zan auri tsoho ba. Gaskiya ni ko dating tsoho ba zan yi ba." "Ni kuma gani a gabanki, nazo da nufin soyayyarki." Dauke kai tayi kamar ta sake kuka, ta ce mishi. "Ni gaskiya ka tafi ka da mutane su dauka." "Muje na saya miki ice cream!" Kallon.shi tayi sannan ta ce mishi. "Ai ni Allah bai daura min kwadayin abin hannu maza ba, jeka na gode." Duk yadda yaso yarinyar nan ta bashi hadin kai, fir taki har da koranshi ma tayi, da zai tafi ne, ya riko hannunta. Ya cusa mata kudi me yawan gaske. "Ki sha ice cream!" Sannan ya bude motar ya shiga, ya ce mata. *Ina sonki!" Kallon kudin tayi a ranta ta ce mishi. "Bana sonka" Sai da ya bar gidan, sannan ta wuce dakin Inna da kawayenta, ta mika musu kuɗin. "Ke yar nan! Ina kika samu kudi haka?" "Wani tsohon najadu ne wai yana sona, ya kai shekaru sittin fa!" Ta ajiye musu tana faɗin. "gashi kuci goro." Daga haka ta bar dakin, sai Albarka sukae saka mata. ----- Tun karfe hudu na asuba, office din yan sanda ya cika makil da yan kai kara, kan Asp kamar zai fashe domin tun kiran sallah farko, aka kira ta haka suka yi ta shigar da korafin akan Kamfanin Digital art, abin mamaki dayawansu Zeenobia ta kirawo su. "Yanzu me kuke so na muku?" "So muke a kama ta, ta fitar mana da kudin mu!" "Ok sai ku bari gari ya waye!" -------- 09:30* Na safe, watsa mata ruwa aka yi ta ware idanun cikin gajiya da son yin barci. "Tashi ki bamu kudin mutane?" Tashi tayi zubur, tana kallon Sajan Barau. "Kudi wani iri?Ba yana kamfani ba" "Idan kin tafi Office din CID zaku musu bayani!" Zubur ta mike hango Asp Zulfa tsaye da wasu mata yan sanda. "Kan Uba nice za ayiwa wannan rashin mutuncin!" "Ku fita na sauya kaya!" Ban daki ta shiga ta wanke fuskarta, sannan ta fito waje, bata tab'a sanin al'amarin ya wuce haka ba, sai da ta m dauki abayarta ta saka. Sannan ta bi bayansu, haka suka sakata a motar yan sanda, suka tafi da ita. Har Office dinsu. "Ita ce.... Ita ce.... Ki bamu kudin mu!" Kai tsaye office din Zulfa aka wuce da ita. Zama tayi tana dauke kai. "Meye hadaki da mutanen can?" "Na tuna su, amma ai kudinsu yana kamfanin S..... Digital art." "Ya zaki ji idan aka ce miki, ba kamfani ba ne. Yan damfara ne?" "Kai haba, haka ma ba zai yiwu ba. Domin ni nasan inda Mr Amjad ne ba zai damfare ni ba " "Amjad Fahad Albagwi! Damfara a jinin su take, ya zaki confront mutane akan kudinsu? " "Kina nufin dama Amjad dan 419 ne? Lallai ma duk inda yake sai na zakulo shi wallahi!" Kura mata idanu Zulfa tayi ta kira Sajan Barau, ta ce mishi. "Kaita filin nan" Haka kuwa aka yi ya tisa keyarta da tare wasu yan sanda. Latsa wayar Zulfa tayi, tana jan hancinta ta saka a kunne tana faɗin. "Yasir tarihi ya maimaita kansa. Abun da ya faru shekaru goma sha ya kuma faruwa da Babysister." Ta fada tana share hawayen da yake zubo mata. "My lady, ki bar kuka ba zasu ci banza ba, In sha Allah zasu shiga hannu. Basu san wannan karon sun tab'o kusar yakin ba ne, har yanzu bata gane ki ba?" Hawaye ne sharrrrr ya zubo mata ta ce . ""She lose her memory." "God! Yanzu ki kula da ita, wasu zasu iya bibiyar rayuwarta." "Ok Yasir" "Love you!" Kashe wayar tayi, tausayin Zeenobia yana kara cika zuciyarta. Mikewa tayi ta wanke fuskarta, can suka dawo. Idanunta ya kad' a jajjur. Zulfa ta ce musu. "Sajan watsa min ita cell, dama ka mara jin magana kenan!" "Ke yar sanda, kome lalacewar gawar Giwa tafi ƙarfin Allah sarki. Kuma baki san waye ya tsaya min ba a garin nan zaku sha mamaki!" Tura keyarta aka yi cell din, kamar ta fasa ihu. Har karfe daya na rana, ana rikici kuma abu yaki ci yaƙi cinyewa, don haka suka fara shirin kaita kotu. Sannan da gayya Zulfa ta hana belinta. ★★★ _A yau dai jami'an tsaron yan sanda, na garin Keivroto city sun kama daya daga cikin yan damfarar da suka damfari mutane kudi masu yawan gaske. Daga cikin su akwai yar kunama, yar daban da ta addabi rayuwar al'umma. Ita ce wacce ake zargin da janyo mutane cikin al'amarin._ Labarin da ya karakad'e ko ina, kenan labarin abin da ya faru. Shatima yana gidan Malik da ya iso tun karfe biyu, shi kuma ya isa gidan tun karfe hudu. "Ikon Allah, yarinyar nan babu ruwanta." "Ai har da kudin Malik aka gudu da shi. Kuma munafuka ita ta zo da kanta!" "Elbashir ka yi belinta!" ""Malik!"."kayi yadda nace!" "Kudin da suka tafi da shi fa?" "Kwandilata idan suka tafi da ita zasu dawo min da hakkina." "Malik ya zamu yi da ita a kawo ta nan!" Murmushi yayi ya ce mishi. "Yanzu tana cikin alhinin abun da ya faru, ka bari a kwana biyu muga." Hankalin Shatima yayi masifar tashi, da sauri ya mike yana faɗin. "Malik zan dan fita, zan dawo an jima." "Ok!" Elbashir ya ce mishi. Da idanu suka bishi, kafin suka cigaba da abin da suke. Bai yarda ya tafi Office din yan sanda ba, sai da ya koma gida ne yayi ta Safa da Marwa dama dalilin Malik yasa taki yarda da shi,

Chapter 12 of 13