tafara kamuwa da soyayyarta.
Yau gashi Sadiq yasamu Fatima adalilin Hajiya
Murja.
Zanci gaba.....HAJIYAR BUK
PART 11
Sadiq inaso insanar dakai abinda najima ina
boyewa
azuciyata kasancewar abin yazomin ta yanda
banyi
tsammaninsaba
Sadiq Hajiyar BUK dakake ganin numberta
awayata Bawani
alaka dake tsakaninmu da ita illa Takasance cikin
Halin
jarraba daga ubangiji Allah yajarrabeta da Ciwon
So azuciya
soyayyar Dan dake sa'a da dan cikinta
Hajiyar Buk Takamu da soyayyata azuciyarta
takasa danne
zuciyarta wanda takai har ta furtamin da bakinta
cewar
zata aureni matukar zan amincemata tunda
hakan bai
sabawa Shari'aba.
Cikin tsananin Kaduwa da
razana Sadiq yamike zumbur tamkar an tsikareshi
da allura
yace Aure
Ina Sam hakam bamai yihuwabane wallahi
bazaiyihuba
bazantaba goyama baya ka auri Sa'ar mamanmu
ba
Ita batada hankali take wannan furucin sam
batamasan
abinda ke damuntaba.
Allah sarki Sadik da ka tina da yanda Allah ke
kadartawa
bawa al'amarinda baiyi zatoba da bakai saurin
rantsewaba
abinda nake sakawa kenan azuciyata
Nace Sadik kwantar da hankalinka ka tsaya
kasaurareni
sannan sai ka yanke hukunci da kake tinanin
yankewa
nakwantar dakai ina rarrashinsa amma shikam
tamkar
ankara tunzurashi yasake fusata sai babatu yake
Indai ina
tare dakai inasonka da gaskiya bazan barka kakai
kanka
inda same cutarda kankaba Tsohuwacefa kada
kadaukomana rigimar da zatazam fitina agaremu
wallahi
hajiya zanje nafadama idonsa cike da kwalla
yajuya zai
fita.
Nace Sadik tsaya kaji sadik sadik ina tuni
yakama
hanyar ficewa daga falon da muke zaune yanufi
cikin gida
Dakarfi nace Sadik Fatiman ka Ya ce awajen
hajiya murja
katsaya kasaurareni
Chakk yaja birki yatsaya Yajuyo afirgice idonsa
cike da hawaye yace mekace
Nace Fatimanka yace awajen hajiya murja
Itace yar Autanta.
HAJIYAR BUK
PART 12
Sadik Fatimanka yace awajen hajiya murja
Chakka yaja yatsaya yajuyo afirgice idanu cike da
kwalla
Yayan hajiya uku Biyu Maza suna dangin
mahaifinsu wajen
Baffansu tun bayan rasuwar abbansu
Fatimace yar auta itace ke tare da Hajiya Murja
Ka kwantar da hankalinka kazauna kafahimceni
kasani
nima wannan abu ba san raina yafaruba Allah ne
yakaddara
haka Sadik kasani bantabajin kaunar hajiya
arainaba dai
dai da kiftawar ido hajiya takansance cikin wani
mawuyacin
hali Allah ne yajarrabeta da soyayyata wanda
dagani har ita
bawanda yasan dalilin hakan hajiya tanasona
soyayya ta
gaskiya har cikin zuciyarta.
Tanada burin aurena koda zata rasa dukkan
abinda ta
mallaka
Hajiya batajin fidda kudi wajen hidimtamin tana
kashemin
konawa nabukata a yan kwanakinnan duk wanda
yasanni
inya dubeni yasan rayuwata tachanja ina kashe
kudi yanda
nakeso kayansawa kala kala tamkar dan wani
hamshakin
mai kudi agida antambayeni nace ninake siya da
kudina
kadancewar sunsan mai gidana hamshakin
dankasuwane
basu mamakin hakanba
Sadik haryau har gobe babu wani dan uwana ko
abokina
dayasan muna tare da hajiya sai kai ina mai
tabbatarmaka
bazan taba iya auren hajiyaba sbd ina kallonta
amatsayin
mahaifiyata don babu abinda Mama tafita baxan
iya auran
sa'ar mamanaba wallahi Sadik baxan iyaba
Kwalla taciko a idanuna Sadik dakansa yamatso
inda nake
yace nafahimci damuwarka abokina kada katashi
hankalinka na yarda da kai abokina i trust in you.
Sadik nayima alkawarin sada zuciyarka da
masoyiyarka
Fatima wannan shine dalilin kasancewata da
hajiya murja
nai ma alkawari dazarar ka mallaki Fatima
nikuma
zannesanta kaina da hajiya murja.HAJIYAR BUK
PART 13
Yamma tayi misalin karfe 4:30 babu jama 'a
sosai
kasancewar garin da yanayin Sanyi Sanyi
bishiyune rai rass
sai kadawa suke suna rausaya
yau Jami'ar bayero tamkar anyi yasa bakaji
sautin komai sai kukan tsintsaye da ganyen
bishiyu dake
kadawa muna tafe nida abokina Sadik gidansu
yusrah muka
nufa mintina kadan suka sadamu da quaters din
su yusrah
kanin Yusrah Dake wasa aharabar gidan ne yafara
hangomu da sauri yashiga ciki yan kiran antynsa
ga ya
Abba ga ya Abba cikin matsanin shauki yusrah na
gaba
salman na biye da ita mukai kicibus take
Wani yanayin farinciki yalullube kyakykyawar
fuskar yusrah
tai ajjiyar zuciya tana murmushi muna hada idanu
da ita
Kwarjinina yabugi fuskarta take wata bakuwar
kunya tai
saukar gaggawa cikin xuciyarta nan takasa
motsawa kanta
kasa hankalinta yadawo jikinta bata kula da
Sadik ba sai da
yaiwa Salman magana tana kallonsa takoma ciki
da gudu
yanayin ni kaina yamatukar chanja lissafina take
na
basar nace Salman oyooyo ya gida ya mum yace
mummy
batanan nace ayya ina tatafi yace suntafi unguwa
da
Mubarakh nace to muje ciki Sadik yace Abokina
Agaskiya
Yusrah na cikin wani bakon yanayi wanda yakasa
boyuwa
daga xuciyarta har idanunta sukan makance bata
ganin
kowa agabanta bayan kai nace hmm sadik kenan
ita
gayama haka ai basai ta fadaba labarin zuciya....
Nan namanta da batun Sadik muka shiga daga
ciki yusrah
tasaukemu afalonsu taimana tarba cikin
girmamawa
munjima muna hira sadik na tare da kannen
yusrah suna
lesson Yusrah tace Yayanah Umma tabani sako
wajenka
nace to inajinki tai shiru da alamun amsar bata
gamsar da
itaba duk da na fahimci wani abun sai na basary
yusrah
tace ina waje batajira amsar dazan bataba tafice
farfajiyar
gidan tabarmu a falo nakalli inda sadim yake sai
naga yana
Natashi na fita ina zuwa naga yusrah zaune kan
kujerar
roba Woww bazan iya kwatanta yanda naga
yusrah
takara kyau da haskeba kwalliyar datai
taimatakyau sosai
kallonta nai muka hada ido Masha Allah
Fatabarakallahu
ahsanil khaliqin take naji wani sinadarin yaratsa
kasan fatar
kirjina yashige direct ma'adanar so da kauna
kuzarina
yakaru namanta da tinanin komai Yusrah kawai
nake kallo
agabana.
Sannu yayanah fatan nasameka cikin koshin lfy
dafatan
kowa yana lfy nabata amsa cikin tausasa murya
kowa yana
lfy
Yayana natambayekah kwanaki bakabani amsaba
kuma
yauma zan karamaka da wata tambayar yayah
meyasa
nake yawaita tinanika azuciyata ko amakaranta
sai naji
bana jindadin komai bana bukatar kowa illah
inganka
yayanah meyasa inkazo gidanmu sau daua sai
adade sosai
kake sake zuwa yayana meyasa kake zuwarmin
amafarki
yayanah kasan ni yarinyace karama kuma
kanwarka wadda
batasan komaiba meyasa innatambayeka kan
abinda
bansaniba baka bani amsa kuma na tabbata kai
kasan
komenene ke damuna
Amma inna tambayeka baka bani amsa
Take naji tausayin yusrah ya lullube zuciyata
Yusrah
yarinya karama batasan komai game da
soyayyaba burin
mahaifinta shine tai karatu mai zurfi
Yusrah takatse tinanina da fadin Yayanah
nakaranta wani
novel yau domin insamo amsar abinda ke sanyani
yawan
tinaninka acikin labarin nasami amsar da zuciyata
takasa
ganomin ita Yayanah Menene So menene
Soyayya don Allah
kadaure kabani amsar tambayata.
Take naji
SO kuma? SOYAYYA wace irin Soyayya kuma??HAJIYAR BUK
PART 14
yusrah ke tambayata yayinda idanunta yakada ya
chanja
kala nan take
Shiru yabiyo bayan tambayarta na tsawon dakika
2
maganganun Yusrah tabbas gaskiyane amma sai
dai ina
fargabar halinda xata tsinci kanta aciki Lamarin
SO ba
abune kankaniba musamman ga Yarinya Karama
yar
makaranta wadda babanta baida burin yimata
auren wuri
Yusrah tabbas duk abinda kika fada gaskiyane
SO halittane da Allah yahalicceshi azuciyar
dukkan abin
halitta mutum da aljan dabbobi da tsuntsaye
So wani sinadarine dayake karama rayuwa
armashi dajin
dadi sannan wani matakine dake cefa rayuwar
abin halitta
ga abubuwa guda biyu
Farin ciki da bakin ciki
Idan Kakamu da son ya mace amatsayinka na da
namiji
wannan macen zatakasance agareka abar
bukatuwarka
kwatankwacin yanda kifi ke bukatar ruwa don
gudanar da
rayuwarsa zatakasace jindadinka farin ciki
nutsuwa da
walwala agareka dukkanin abinda Kasan
kishiyane ga
wadannan abubuwa to rashinta zaikasance
kishiyar
wadannan abubuwa zakazam cikin damuwa
rashim
nutsuwa bakin ciki tashin hankali wanda inyayi
yawa zai iya
zama illa ga ratuwar kowane mahaluki
Dukkanin abinda zuciyarki takamu dashi nima
nakamu
dashi inasonki yusrah Soyayya ta gaskiya inajin
sonki cikin
dukkan sassan jikina musamman bargo da
zuciyata aduk
sanda muke tare farin ciki da jindadu ke
yalwatuwa
azuciyata aduk sanda bama tare bakin ciki
damuwa da
kunci nake tsintar kaina aciki na boye hakan sbd
inabaki
dama amatsayinki na daliba bansan kihada
soyayya da
karatu ina kishinki ina tausayamiki dukkanin
abinda xai
zam damuwa agareki bana fatan inkasance nine
silar
faruwarsa wannan yasani yanke shawawar kin
bayyanawa
agareki
Yayanah kalamanka suna da matukar tasiri ga
zuciyata
sunshige kowane sakon zuciyana dawani sinadari
wanda
bansan yanayinsaba naimaka alkawarin komai
wuya komai
rintsin da zanshiga ardalilin soyayyarka bazan
taba yin
rauniba zaka sameni mai karfin guywa da juriya
Soyayyarka
ni nagani nadauka kuma zan killaceka kai kadai
azuciyata
dakai nafara dakai zankare adalilinka nafara sanin
SO
adalilin ka zan kasance cikin rayuwar farin ciki da
jindadi
Inasonka yayanah inakaunarka Har abada
Yayanah yaya
Abba
Nabaka amanar xuciyata kai zakam mai yimin
talafi kasani
akan hanya ni bakuwace asoyayya wadda
batasan komaiba
Sai dai inason sani daga hamshakin masanin
hakikanin
sirrin SO da Kauna YayanahHAJIYAR BUK
INTERMISSION
Yusrah takashemin jiki da dadadan kalaman da
tunda nake
bantabajin kwatankwacin irinsuba dani daita
muntsinci
kanmu cikin rayuwar farin ciki da jindadi bamu
rabuba
harsai da mamanta tadawo muka gaisa sannan
mukai
sallama Yusrah tarakomu bakin garden ananma
tamkar
bazamu rabuba
Allah sarki soyayya dadi idan kai dace da
masoyin gaskiya
Ahaka muka rabu muna kewar juna tunda wannan
rana
soyayyarmu tai karfi nida Yusrah kusan duk sati
sai naje
gidansu don muga juna
Sai dai kullum zuciyana cike da fargabar kada
Abbanta
yasan da wannan lamari don nayi Imanin
inyasani Lamarin
bazai mana dadiba burinsa akan Yusrah tayi
karatu tazam
babbar Likita gashi Yusrah tafada tarkon Soyayya
matsananciya
Abangaren Hajiya Murja muwa kullum wutar
soyayya dada
ruruwa take azuciyarta koda yaushe bukatarta ta
ganni
muna tare da ita yauma dai kamar yanda tasaba
ta
matsamin inje muhadu niko ban amsa mataba
yanda naji
yanayinta tana magana awaya shiyatabbatarmin
da cewa
Soyayyar ta motsa mata nace mata ganinan
zanzo da
yamma tace to yau da wuri nakeso naje gidan
hajiya
indawo da wuri sabd anjima akwai kallon ball
karfe 3pm ina
gidan hajiya sai dai kash anyi rashin sa'a hajiya
batanan
Sallamata keda wuya Aka amsa da murya
sassanya
Fatimace tabudemin kofa tana ganina tahade rai
fuska
aturbeni tace menene Makalemata mekazoyi
gidanmu yau
hajiya batanan sai ka juya kakoma inda kafito
ranta abace
taci gaba da fadin wai wani kankanin yaro dakai
kaizaka
auri mamana ai wallahi danaji kunya da duniya
tatsaneni ka
auri mamana kana Sa'ana Ai wallahi duk yanda
zanyi iya
karfin ikona da Allah yabani bazaka auri Hajitaba
Wallahi wallahi duk wata hanya dazanbi inga na
bata
wannan magana walh sai nabi sai dai adalilin
haka inrasa
numfashina Wallahi bana goyon bayan wannan
kazamin
al'amari kafice min daga gidan Ubana kakara
gaba
Sabon tashin hankali
raina yabaci kalaman Fatima sun tsoratani
matuka
Fatima nada zuciya kuma duk abinda tafada zata
iya
aikatawa batada tsoro ko kankani
Kafice nace maka wallahi ko indokama ihun
barawo yanzu
yanzunnan
Cikine yayi sanyi Fatima nada zafin rai ga zuciya
Allah
sarki Sadik alkawarin dana daukarmaine
tafadomin axuciya
Anya xan iya shawo kan Fatima tasoshi kuwa
duba da
yanda nai bakinjini wajenta
Azuciyar Fatima kaf duniya babu mahalukin data
tsana
kamar Abba besst San' auran mai neman auren
mamanta
Lamarin yasake dagulewa
INTERMISSION
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels