Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 2
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels HAJIYAR BUK (TRUE LIFESTORY) PART 1 Yauma kamar kowacce juma'a bisa al'adata dukkan juma'a ranar hutunace bana fita sai yamma, ina zaune adakina misalin karfe 4 na nakunna TV ina kallon wani film sai wayana tai ringin abokinane yakirani ina dagawa yace Abba kana inane nace gani adakina sai yace to yau munada fita ina fatan baka mantaba sai nace habba ai ina sane sai yace yaukuma ina mukayi sai nace kabiyo ta gida kasameni sai mu huce yau cikin B.U.K zamuje yace to kashirya ina kan hanya nace badamuwa na ajje waya. kamar kowace Juma'a nida abokina mukan fita yawo wajen gari kunsan zuciya akwaita dason zuwa bakon waje imzamu fita nidashi har zumudi muke duk juma'a mukan fita yawan bude idanu kunsan manyan yara akwai son bawa idanu haqqinsa. Hakan yazammana al'ada duk sati sai munfita, To yauma kamar kowace juma'a munfito nida abokina Abubakar Sadiq yadauko motar da Abbanshi yasaimasa, (THANK YOU DADDY) Sai yake tambayata Abokina yau ina muka nufane? nace yau muna kusa da gida B.U.K zamuje Staff quaters gidajen Malamai zamukaiwa lecturernmu ziyara. Sadiq yace kai mutumina wai meyasa kakeson muje wajen wannan malaminne nace walh kawai zuciyatace takeson hakan kasanni akwai son naganni cikin lambu ko waje mai shuke shuke inajin nishadi da annashuwa a irin wannan waje yace a'a abokina kodai Yusrah ce take daukar hankalinka nace a'a walh, YUSRAH yar malaminmuce Sunanta na asali shine MARYAM babanta yana matukar ji da ita takasance fara karamar yarinya yar shagwaba kyakykyawace tana da son mutane ga son karatu tana da Miskilanci inhar bakusaba da itaba YUSRAH tana matukar son taga munje gidansu mukan jima a falonsu da mommynta da abbanta muyi ta hirarmu kai kace dukkanmu family guda muke kasancewar babanta dan bokone bai dauki hakan abakin komai ba. YUSRAH tanason kasancewa tare damu kome takeyi da munje gidansu to fa wannan aiki yakare tsaida komai take har sai bayan muntafi tanajindadi kasancewa da Besst sbd besst akwai labarai kala kala ga xolaya da dadin baki. Abbansuma yanaso yagamunkai musu ziyara, muka taka mota muka nufi B.U.K road Da isarmu bakin gate kamar kowane lokaci ana cheakin point na motoci muko bamu wani bata lokaciba kasancewar Besst akwai surutu da iya zance duk masu gadin school din sun sanshi sbd zolaya da wasa da mutane muka wuce kai tsaye muka nufi staff quaters. Chakk motarnan taja ta tsaya a tsakankanin bishiyoyi da gefen yar karamar kwaltar data mike street zuwa tsakiyar jami'ar Bayero wato (BUK) mukai mukai motarnan ta tashi taki tana daukar key amma taki bada wuta nakalli manage naga mai kusan full tank muka sakko muka duba ruwa lafiya, mukai iya yan dabarunmu mota taki karbar wuta. Sadiq yabugawa mechanic dinsa waya swith-off nace Sadiq may be Capretan motarnannefa ya toshe baya hauro da mai yace to yanzu mene mafita nace kazauna inje innemo mana mechanic sadiq yana matukar respectn dina kamar ba abokinsaba kai kace ni yayansane yace a'a kai zakazauna ni zanje innemo mana akwai wani gareji anan kabuga kan titin zuwa kofar ruwa bari naje nasamo mai gyara bai jira nabada amsaba yajuya yanufi bakin gate. Niko nazauna saman mota ina kallon bishiyoyin da sukaima karamar kwaltar kawanya, ganyayyaki nata kadawa gashi yammace wajen gwanin ban sha'awa abunda nake so kenan nishadi yamamaye zuciyata. Nadauko wayata nafara chattin lokacin ma ban damu da whatsapp ba nashiga facebook muna hira a wani dandali Alokacin nine Chairman/Admin a wannan group @the year 2013 hira muke nikadai asaman mota inata dariya hira tadau dadi anata chatting... SALAMU ALAIKUM naji wata murya sautinta kamar na budurwa amma kuma ga mamakina ina dago kaina sai nai arba da mai magana, Wata macece babbar mace sanye da mayafi irinna yanmata farace doguwa tana da kiba sosai tana da kyau dai dai misali amma kanaganinta kasan ta manyanta duk data kwana biyu kwalliyarta babu bambanci da kwalliyar budurwa ga eyeshadow ga jambaki kai hardasu gyaran gira (abin yadan ban mamaki) Na amsa cikin firgici nawaiga gaba da baya banga alamun mutum awajenba sai ita kadai tsaye agabana Nan take kirjina yasara yana dukan uku uku ji kake dum dum dum tamkar ana dukan ganga akirjina natsorata matuka. Tana ta murmushi tana fara'a Tace sannu samari nace yauwa Mama..... Ina wuni, Sai naga tadaure fuska ta bata rai, Haba Samari inka kirani da wannan suna bakaimin adalciba tayaya zaka kirani Mama ai ni bawata babba bace garun jikine kawai. Nakwalalo idanuwa nasake dubanta da kyau Haba Hajiya walh ke babbace dole in girmamaki nasake durkusawa ina huni Hajiya. Taki amsawa kawai sai naga ta nufo inda nake ranta abace tana wuci..... Tuni wayata ta subuce daga hannuna hantar cikina takada nakara firgita ganin yanda naga ta tunkaroni rai abace tana xuwa sai naga ta...........???HAJIYAR BUK PART 2 Matar nan tana karasowa gabana sai naga ta kuramin ido ko kiftawa batayi sai da tai kusan minti 2 tana kallona take naga idonta ya chanja alamar ta tuna da wani abu taimin sallama na amsa tace don Allah yaro ya sunanka karka tsorata dani ni mutumce kamar ka inaso ne nasan sunanka.... Nace sunana Abba motarmuce tatsaya anan abokina yaje zaidawo yanzu tace naga lokacinda kuka tsaya ina cikin wancan quaters din tace inbazaka damuba kazo mukarasa kaga gidana can gabane kadan Nace A'a ai yanzuma Sadiq zaidawo yana kan hanya kibarshi nagode da karramawarki tace bakomai ai yazamarmin dolene inkarramaka Ni sunana hajiya murja dakazo munje gidana akwai maganar danakeso muyi dakai mai mahimmanci nace a'a Mama kifada ananma aibakomai tace Abba ina rokonka don Allah kadaina kirana da wannan suna sam bai dace daniba walh banaso nace to Hajiya nadaina in Allah ya yarda tai murmushi sannan tace kabani numberka sai nafadama tawaya nace to gata kamar haka..... Tana karba takirani special numberne numbarta tai saving tawa atinanina zanga tajuya tatafi ga mamakina kawai sai naga ta kuramin ido tana ta kallona gaba daya ta tattaro nutsuwarta takurama fuskata idanu har nafara sake sake araina anya ko wannan matar ba mayya bace kuwa nace hajiya lafiya dai ko? sai naji muryarta asanyaye lower sound tace lafiya kalau na tina wani abune amma bakomai nace to Allah yasa hakam tace ameen Hajiya gaki babbar mace da alamu kuma kinada hali to amma meyasanyaki cikin tsananin damuwa haka tace hmmmm najima banga abinda yashiga cikin zuciyata lokaci gudaba sama da yau najima banga abinda ya birgeni ya kawatar dani kamar yauba gaskiya Abba ina cikim damuwa, damuwar da zai wuya na iya furtama wani bayan kai nayi shiru ina sauraronta tacigaba da cewa Abba tinda naganka naji wani abu ya cakemin zuciya naji zuciyata ta kamu da abinda da rabon danaji irinsa tin ina yar shekara 16 bantaba tsammannin faruwar hakanba ko kadan nace hajiya shekararki nawa? Tace shekarata 16 akamin auren saurayi da budurwa nida mijina munzauna a zoo road tsawon shekara 11da mai gidana mijina yarasu sakamakon hadarin mota yayanmu uku dashi biyu maza yar autarsu mace Fatima tana tare dani suko yayyenta suna wajen kanin mahaifinta suna karatu yau shekara goma da rasuwar mijina bankara aureba bayan rabuwarmu bana muradin yin aure nasami zaurawa da dama amma ban basu damaba kawai bana sha'awar aurenne nafara harkar business na kayan mata atamfa sarkar gwal da yarirrika nasami jari mai karfi ayanzu haka dubai nake zuwa saro kaya. Abba inason fadama wata magana amma narasa ta inda zanfaro zancen nace inajinki tace idan kakoma gida zan kiraka sai infadama tawaya amma baxan iya fada agabankaba Nace to Allah yakaimu lokacin muka cigaba da hira can sai ga Sadiq da mechanic suka gaisa da hajiya mai gyara baifi minti 10 da zuwaba yatashi mota kasancewar yamma tayi sosai wajen 6:30 sai muka fasa zuwa gidan malaminmu mukai sallama da hajiya muka juya mukafice daga cikin buk Sadiq yatambayeni labarin Hajiya nafada masa komai sai naga yanata dariya nace sbd me kaketa dariya sai yace Allah sa muji alkhairi nace ban gane me kake nufiba. Yace..........??? BesstHAJIYAR BUK PART 3 Sadiq yace Agaskiya Abba matarnan Sonka take nai zumbur nai kamar antsikareni da allura nace mekace yace kayi nazari da kanka duba fa kaga yanda matarnan take kwantar da kai tana ta janka da hira kala kala gabadaya hankalinta ya tsaya cakk akanka. Nace kai Sadiq wane irin tinani kake haka matarnan fa duk tahaifemu kobaka kalletabane sosai Sadiq yace bi ahankali abokina wataran zakace nabaka labari. Nabata rai bankuma cewa dashi uffan ba rufe bakina keda wuya wayana tai ringin HAJIYAR BUK ke kira haka nai saving numberta ina dagawa naji ankwantar da murya Abba kunje gida lafiya kasancewar Sadiq na gefena nai shiru nakasa bata amsa. Dakyar nadankokarta nace a'a muna kan hanya kuma bagida muka nufaba bankarasa rufe bakiba tace ina zakuje kuma? kamata yai kuje gida ka huta kaga garinfa akwai sanyi sosai yau to yanzun ina zakuje plsss naishiru ina sake sake araina NAKASA GANE KAN WANNAN MATA. abinda nake tambayar kaina shin wai ita wannan matar meye manufarta akainane tayaya zatadungamin tambayoyin dabasu shafetaba kashe wayata nai nabata rai, Sadiq yace kaidawa kake wayane nace wani abokinane ya kirani haba wane abokinka kuma wanda bansanshiba bacin duk wanda yasanka tare ya ganmu ringin.... wayatane ya katseshi daga zancensa Hajiyar BUK again banaso Sadiq ya fahimci meke faruwa sai nadaga Hello Abba kayi hakuri inna batama rai namatsu inji kasauka lafiya kasancewar ahalin yanzu samun lafiyarka shine tawa, Allah yariga yahadani dakai Allah ya jarrabeni da ciwonda babu mai iya bani magani bayankai sonake naji kasauka gida lafiya akwai sakon da zuciyata kesan isarwa gareka. Raina yabaci matuka dajin wadannan kalaman nata nai shiru nakasa bata amsa nasake yanke wayar Sadiq yajuyo yakalleni abokina waya batama raine wannan wane irin abokine kake dashi yakeson sanyaka adamuwa menene sunansa habawa tambaya hajiya tambaya Sadiq gumi yagama taruwa ajikina Bari inzuge window naga har gumi kake hadawa gashi kuma yau gari sanyi ake ko inkunnnama AC ne nai shiru ba amsa ina sake sake cikin zcyta. Abokina baikamata kaboyemin damuwarkaba atinanina nidakai munzam daya damuwarka tawace damuwata takace mezaka boyemin ni abokine gareka har cikin zuciyarka ni abokine wanda zaka iya shawarta cikin al'amarin daya shigema duhu tindazu naganka cikin damuwa natambayeka kaki fadamin duk da ni nasan abinda ke damunka koda baka gayaminba. Maganar Sadiq gaskiyace tabbas ya fahimci komai kawai yana basarminne nace Sadiq kabari muje gida zan sanar dakai komai... Ina rufe bakina sai ga text din Hajiyar BUK awayana har guda biyu Zanci gaba....HAJIYAR BUK PART 4 Dakaina nakira Hajiya nace naga credit amma bansan kona wayeba may be kinyi mistakene kika turo phone dina KAJINI NIMA DA KARFIN HALI WAI IRIN JAN AJINNAN Tace haba wazan turama bayan kai dama nakane daniyar inturamaka nai sendin kayi hakuri wannan ne kadai yarage ajakana. Nace ni cewa nai kituromin kati ni wayana da credit zandawo miki da katinki yanzu nan da nan tamarairaice tamkar karamar yarinya Haba Abba naturo ne dominka kai nakeso kai amfani dashi plss karkamaida hannun kyauta baya bazanji dadiba ni naturo sbd kai basani akaiba ina rokonka sbd Allah karkaimin haka Bakin cikin hakan zai kasheni. Abba inaso innemi alfarma awajenka kasancewarka musulmi mai tausayi dajinkai ina rokonka daka daure ka ceci rayuwata natsinci kaina cikin yanayin da banyi tsammanin fadawa cikiba Lokacin dana fara ganin ka Allah ya jarrabi zuciyata da sonka alokaci kankani kallonka ya chanja dukkan tinanina natsinci kaina cikin kogin sonka lokaci guda inajin zafin son da rabonda naji wani abu makamancinsa tin ina yar shekara 16 nahadu dakai cikin ikon Allah inasonka cikin zuciyata banjin zan iya karasa rayuwata adoron kasa batare da sonka cikin zuciyataba Abba nibawani shekarune daniba banfi shekara 30 kai kuma nasan ayanzu zakai 25 Kaga ba wani tazarace tsakinmuba kuma hakan ba haramun bane a addinance Abba kabani dama guda daya zankebanceka tsawon rayuwata zan mallaka komai agareka ka aminta dani zanmaka hidimar tsawon rayuwata. Maganganinta abin al'ajabi kalamanta akwai ratsa zuciya bantaba ganin mace kamar hajiya murjaba ko amafarki bantaba tsammanin haduwa da irintaba kalamanta sunratsa zuciyata nan danan naji tamkar baniba Inkakalleni alokacin zakaji tausayina dana tina Hajiya murja sai naga kamannin kanwar mamana alokaci guda kuma sai intina da kalaman Maman Sadiq watarana datake cewa Allah yabaku mataye nagari yara yan dagwai dagwai muga sirikanmu tin da ranmu Nan danan kwalla tacika idanuna ta yaya zangabatar da Hajiya Murja amatsayin surukarsu tayaya matar dansu zata tsaya gabansu alhalin kansu daya tayaya mutane zasu banbance suruka da uwa Hajiya murja tayi shiru awaya tana sauraron amsata. Zanci gaba....HAJIYAR BUK PART 5 Nai dai muka gama waya da (MATAR DA ALLAH YAJARRABETA DASON SA'AN DAN CIKINTA) (GIDAN SU YUSRAH) Maman yusrah na ganinmu taimana barka da sauka fuskarta cike da fara'a kannen Yusrah Ahmad da Khadijah suka karaso cikin murna sunai mana sannu da zuwa kowa agidansu Yusrah yana murna da zuwanmu munzam tamkar yan'uwansu na dangi muka gaisheda mamansu Yusrah Abbansu yashigo falon da muke zaune muka gaidashi amma abinka da dan Ahlis sunnah hannu yamiko mana tamkar zai gaisa da abokansa Sadiq yabashi hannu amma nikam ina hada idanu da Yusrah sai naji nakasa bashi hannu sai na sunkuy da kai kasa ina cewa ina hunni Abba, Yace muyi musabaha kamar yanda addini yakoyar damu kaina asunkuye nace a'a Abba bazan iyaba nasaba gaisheda manyan mutane cikin girmamawa yace yau kuma ni zaka nunama Fulatanci gaba daya muka kwashe da dariya nace a'a Abba aini banyi zaman rugaba akasake kwashewa da dariya. maman yusrah tace harka fara halinnaka ko nace a'a momi ganinai Abban khadijah yai tsaye akaina tamkar a school anmasa laifi zaiyi punishment da reshen bishiya Hhhhaahahahaa kowa sai da yai dariya ya isheshi Sannan Yusrah tabata rai Abban nawa kake cema yana duka da reshen bishiya?? Nace aikinsan fulani ko ina sukaje sun riga sunyi sabo da rike sanda basu manta sanda suke ruga, Itama dariyarce ta kwace mata Ummansu tafita da sauri bansan meyafidda itaba ko kunyace tasa ohho, Sadiq yace to bare bari ku indai baku taba fulaniba bakwajin dadi tamkar malamine yaje makaranta bai rike Alliba, hahahahahaaha Ankuma ana wata ga wata, Agaskiya Abban Yusrah yahadu mutumne mai son barkwanci munayi shima yana tayamu hakan tasa duk yangidansu suna marmarin mukai musu ziyara. Tofa ayanda nafahimci Yusrah shine hirar danakeyi tafi birgeta fiye da komai ganin yanda gaba daya tatattara hankalinta waje guda ta nutsu sosai takuramin idanu gaba daya hankalinta nakaina nima kuma azuciyata haka abin yake idan nakalli kwayar idaniyarta hasken idanunta yaratsa nawa sai naji tamkar antsikari zuciyata, wani abu nakeji mai tsini ya sokeni akahon zuciya nakamu da son Yusrah batin yanzuba. Sai dai banda Sadiq babu wanda yasan abinda ke cikin zuciyata, tare da abbanta mukai sallar magriba cikin jam'i hakama Isha'i abbansu naja muna binsa bayan mun idarne Yusrah tashigo dauke da abinci ahannunta ahmad na biye da iya da lemon juice mai sanyi kwalin har gumi yake suka ajje mana suka fita abbansu yabude abincinnan yace muci tare Babansu mai saukin kaine matuka kunya tagama kamani amma dole na dake sbd bansan yafahimci cewa ina surukantaka dashi, Bayan mungamane mun danyi hira kadan abbansu yaimana fada sosai akan mudage da karatu komai gatanka kayi karatu katsaya da kafafunka kasancewar rayuwa mai iya chanjawace akowane lokaci abbansu yadaukemu tamkar yayan cikinsa mukai masa godiya mukai sallama da kowa nagidan Yusrah ce da Ahmad da Khadija sukai mana rakiya har muka je inda muka aje mota idanun Yusrah nakaina nima abangarena haka abin yake jikinta yayi sanyi sosai kasancewar in muntafi yanzu batasan randa zata kara hada idanu daniba, takasa jurewa tace yayana inason intambayeka akan wani assignment da aka bani nace ba damuwa tamatso kusa dani cikin sanyin jiki tana mai cewa...... HAJIYAR BUK PART 7 YUSRAH tace yayana aduk sanda kazo gidanmu nakanji cikin zuciyata babu ranar datafimin wannan rana nikadai zanji ina ta farinciki da annashuwa murna kuwa basai na kwatantaba kaima kafahimci hakan Yayana zan sanarda kai wani abu wanda nikaina bansan komenene ke faruwa daniba aduk sanda naganka sai naji farinciki ya cika zuciyata aduk sanda katafi sai najini tamkar mara lafiya inna kwanta sai na kasa bacci inta tinaninka inna rufe idona sai inga kamar kaine akusa dani yanda nake yawan tinaka bana iya tina kowa har mamana da abbana kafi komai saurin zuwa cikin raina yayana menene dalilin hakan? Nai shiru nace kinsan kece babba bakida yaya namiji to kowane da yanaso yaganshi cikin yan uwanshi to kekuma kinkasance baki da yaya bakida sister wannan yasa kike tinani tamkar yayanki kidaina sawa aranki kinga su Ahmad don suna tare dakene shiyasa basa damuwa kamar yanda ke kike damuwa. To Yayana tsakanin iyaye ko yaya da sister wanne akafi damuwa dashi cikin zuciya nace Iyaye soyayyarsu nagaba da komai Yusrah tace ba amatsayin yaya nake tinakaba domin in kana matsayin yayana bazan yawaita tinakaba fiye da mahaifaba nace to aisu kina tare dasu mutane sunfi damuwa akan abinda suka rasa fiye da wanda suke tare dashi. Yusrah tai shiru tana kallona Yayana kai kasan abinda ke damuna amma kaki ka fadamin gaskiya koda ni bansan komaiba ai ina ganin yanda mace da namiji suke damuwa da junansu a film indai daya yarasa daya damuwarsu babu bambanci da tawa. Yayana bantabajin irin hakan atare daniba sai da kafara zuwa gidanmu inada yan uwa adanginmu amma bana damuwa dasu kamar kai kalamansu basa burgeni kamar yanda kalamanka suke tasirin shiga zuciyata. Koda bansan ya ake SO ba natabbata na kamu dashi adalilinka nakamu da soyayyarka inajin dadi alokacin danake kallonka babu lokacin danafi damuwa fiye da sanda Idanuna suka rasa kallonka, yayana kaine silar fadawata cikin kogin da ban iya nutso acikinsava idan har baka kamani kaceci rayuwataba zan hallaka acikinsa walh nakamu dasonka so nagaskiya bazan taba jure rashinkaba inaso kakarbi soyayyata ni kanwar kace wadda batasan komaiba kuma bata iya komaiba kaimin jagora cikin rayuwata so da kaunarka sun narke cikin zuciyata zan iya rasa komai na cigaba da rayuwa amma inna rasaka narasa raina Ka karbeni cikin zuciyarka kabani kulawa kadamu dani yanda zuciyata ta damu dakai Yayana nabaka amanar zuciyata indai da raina da numfashina kai zan nuna amatsayin zabin zuciyata kai kadace kazam miji agareni baxan barkaba har karshen rayuwata. Yusrah ta juya taja hannun khadijah da Ahmad suka koma cikin gida nan tabarni tsaye kafafuna sunkasa daukar gangar jikina Duk yanda nai kokarin nunama Yusrah tagane amma ina abin yafi karfin zuciyarta bazata sami sukuniba inhar bata furtaba Tabarni tsaye ina Nazari cikin zuciyata... Sam baikamata Yusrah tafara soyayya tin yanzuba hakan zai chanja tsarin rayuwarta wanda mahaifanta suka dorata akai idan soyayya tai tasiri a zcyrta burin mahaifinta bazai taba cikaba. Babanta yai alkawarin bazai aurar da itaba sai tagama karatu sake-sake nake cikin zuciyata Idan har Yusrah takafe kan ra'ayinta ban kyautawa abbantaba naxo lokaci guda nasauya tsarin rayuwar yarsa. Yakamata mujinkirta komai da lokacinsa, Shekarun yusrah 16 tana SS 1 burin babanta yaga Yusrah tazama Dector. Zuciyata tashiga rudani nayi niyyar boye soyayyarta cikin zcyta har sai nan gaba sosai to gashi shakuwarmu takaita da fadawa cikin kogin soyayyar da fitarta abune mai matukar wahala. ANYA KARATU ZAI DORE GA WANDA YAFADA KOGIN SOYAYYA SOYAYYA IRIN TA YUSRAH??? jiki a sanyaye nashiga mota kaina bisa guywata navar wayana a motar Sadiq tana charge dubawata keda wuya naga miss call 17 gaba daya Hajiya Murjace takira. Tofahh..... nafada cikin zullumi YUSRAH MAI SHEKARU 16 KO HAJIYA MURJA MAI SHEKARU 37.....???HAJIYAR BUK PART 8 Hajiya takirani awaya tana tambayar meyasa banason daga mata waya hakan na wahal da zuciyarta nace tai hkr nabar wayarne a charge muka gaisa da ita sannan tafara da cewa Abba ina neman wata alfarma awajenka don Allah don Annabi inaso kaxo gidana gobe namatsu inganka kullum da tinaninka cikin raina ina kwanciya cikin fargaba kasancewar har yanzu banji daga garekaba baka bani amsar sakon da zuciyata ta umarceni inbakaba Abba kaki bani damar insoka haryanzu bansan matsayinaba don Allah kazo gobe inganka. Nace ni bazanzo gidankiba sai dai muhadu awani waje daban tace tayarda muka shirya zamu hadu da ita a Sharada kashe gari da yamma nashirya bayan munyi waya na nufi sharada ranar bansanar da Sadiq ba sbd banson yasan tsakaninmu da Hajiya murja Napep nahau kasancewar motar da muke fita ta Sadiq ce ina sauka daga napep naji ringin wayata nadaga akace kalli barin kudu tsallaken titi na hangota cikin wata bakar mota kirar companin Honda nasallami mai napep natsallaka dakanta tafito tabuden kofar motar nace a'a nibashiga zanba tace Haba dia don Allah kar ka tsinkani cikin jama'a haba don Allah kahau mubar gefen titi mana nai bismillah na shiga motar takoma barinta taja muka tsallaka phase 2 quaters wani layi muka shiga ba mutane kwata kwata sai manyan gine gine da bishiyu kala kala. Taja birki ta tsaya Sannu Abbana farin cikin dake cikin zcyta inamaka barka da zuwa tare da fatan kana cikin koshin lafiya nace lfy kalau nake bayan mungaisa tai ta lissafomin matsalolinta wadanda gaba daya akan abu daya takeyi shine SO tanaso na amince da ita muyi aure zata dauki nauyin komai hatta gidan da zamu zauna itace. Nidai sam kalmar amincewa tai nesa da harshena musamman inna tina yanda muka rabu da Yusrah da Halin da ta fada adalilina. Nacema hajiya karta damu ina tare da ita amsar dana bata bai gamsar da zcyrtaba burinta nace Inasonta amma hakan nakasa fada. Muka cigaba da hira ba yabo ba fallasa daganan tadaukeni mukaje boutique tasaimin kaya masu tsada kala kala mukaje super market tasaimin tirarika da sabulai na alfarma tasaimin Sabuwar waya kirar BB bold touch takalma kala kala takaini akasamin hakorin makkah da axurfa guda biyu a hannayena cikin kankani lokaci hajiya tahadani nafara zama babban yaro bayan kwanaki kadan mukasaba da hajiya murja tana ganina akai akai maganar soyayya kullum abu kara karfi yake a zuciyarta waya kullum ba kakkautawa ga kashemin kudi da takeyi ada inna samu 1000 sai nai sati bata kareba amma yanzu nakan kashe daya da rabinta a wuni guda kai ko Sadiq dayake dan gidan masu hali ayanzu bazai nunamin saka sutura masu kyau da tsada ba. Abin bakaramin dadi yakewa Hajiya murjaba ganin yanda ayanzu gaba daya munsaba da ita sosai abinda yarage mata kawai yaza'ai tasaci zuciyata yaza'a tamallekeni nayarda da maganar Aurenta??? Abokaina yan uwana da dangina sunga nachanja bazama big boy tunaninsu Sana'ar danakeyine shiyasa vasu damu sutambayeniba niko indai da kudi ajikina sana'ar ma ba zuwa nakeba. Duk sabon da mukai da Hajiya batasan gidanmuba nikuma banyarda naje nataba duk sanda zamu hadu sai dai muyi waya muhadu awani waje inmundawo ta ajjeni ahanya yau dai hajiya tamatsa burinta naje gidanta nikuma nagaji da magana daya yau dai na amsa zani gidan hajiya nashirya tsaff nakama hanya na nufi gidan Hajiya cikin BUK hajiya tamin kwatance nikuma banganeba bakin gate tazo tadaukeni muka shiga ciki aharabar wani kayataccen quaters muka parker muka fito daga mota hajiya na gaba ina binta abaya da shigarmu Falon gidan naga wata yarinya budurwa zaune akan kujera kanta sunkuye tana danna waya Atinani ba makawa wannan itace yar autar Hajiya datake fada to ammafa atinanina ko wannan ai zata iya aure ni banba kasancewar ahaka tafi Yusrah girman jiki munayin sallama tadago da kanta abinda nagani ya matukar girgiza tinanina... FATIMA ce zaune akan kujerar tana kallon katuwar plasmar dake falon muna hada idanu da ita tai zumbur ta mike tsaye kamar an tsikareta.... Acikin zuciyata nace Inna lillahi wa'inna ilaihi rajiun Lissafi yasake dagulewa Zanci gaba Wacece Fatima???PART 9 FATIMA ta mike zumbur tasaki baki alamun dama ta sanni tayi niyyar magana amma sanin halin mamanta yasa ta chanza salo da fadin Oyoyo Mom ur welcome back yauwa Fatima taje takawo lemo da ruwa ta ajje tajuya tafita tana mai satar kallona. To Abba wannan itace Fatima ita kadaice yata mace kuma yar auta bari inkirata kugaisa nace naganta tana da hankali sosai Ga nutsuwa hajiya tace ya isa haka naji basai ka yabetaba ai bama sai na kirataba tinda ka ganta Yauwa dia inaso intambayeka wai don Allah meyasa innakiraka da dare sai naji wayarka busy dafatan dai ba waya kake da wataba ko dia kasan bansan naga wata ya ta kusanceka kokadan inajin kishinka har cikin zuciyata. Nace a'a aikinsan bani da budurwa kwata kwata tace sai ni ko nace aukema budurwace tace to dame yan matan suka fini kaji hajiya da maganar yara. Muka cigaba da hira tsawon awa guda daganan nace ni zantafi hajiya tace aini zan maidaka nace ina tace gidamana hmm kinsan gidanmune a'a yau dai nakeso kakaini nace a'a gaskiya kinga ni tafiyama zanyi basai kinkainiba tace a'a basai naje gidanba mutafi nakaika Tal'udu muka fice daga gidan Fatima na lekenmu ta window mamaki ya cika zuciyarta. Ina zuwa gida banzame ko inaba sai gidansu Sadiq nasameshi zaune yana chattn ya akai abokina nace Sadiq yau zansanar dakai abinda najima ina boyemaka. Sadiq yau naga gidansu Fatima yarinyar da muka sha wuyar neman gidansu har muka hakura bamu samuba yau dai nagano maka gidansu Fatimarka cikin tsananin mamaki yace wace anguwane?? Nace Sadiq Fatimarka ya tace yace yarka kamar yaya kai da mukaita faman neman gidansu dakai haba don Allah yakake zolayata da abinda zuciyata ke buri Kasan irin damuwar dana shiga akan Fatima fa. Nace walh Sadiq da gaske nake Fatima budurwarka ya ce awajena Sadiq yace Bazan ganeba sai kaimin bayani....... Sadiq abokina kuma surukina hahaahhaahhah Besssst zai aurar da yaHAJIYAR BUK PART 10 Sadiq yau naga gidansu Fatima yarinyar da mukasha wuyar neman gidansu har muka fidda rai akanta yau dai naganomaka gidansu Cikin tsananin mamaki sadiq yace wace Fatimar badai Fatima BUK ba nace ita kuwa ashe haryanzu baka manta da itaba Yace haba Abba Yaza'ai namanta da fatima kasan irin damuwar danake akanta fatima tashiga raina nakamu da tsananin sonta tun randa nafara ganinta. ------------------------ Wata rana wani lokaci da yamma tun ranar da muka fara zuwa gidansu Yusrah Bayan munfito akan hanyarmu ta komawa gida muka hadu da Fatima da Uniform ajikinta da alama daga makarantar Islamiyya take domin Uniform din yayi kama da na makarantar Islamiyya. Muna cikin mota Sadiq yaja burki ya tsaya kaina nakasa ina danna waya sai naji yace sannu Baiwar Allah ina waigawa naga yarinyar karama tayi shiga ta kamala kayan makarantane jikinta tarufe ko'ina fuskarta kawai ake gani ko kallonmu bataiba tawuce abinta Sadiq yafice daga motar da sauri yabi bayanta nima nabishi muka sha kanta mukai iya bakin kokarinmu yarinyar taki tsayawa dakyar da magiya sadiq yatsai data yace kiyimin izinin tambaya daya don girman Allah Tace tambaya daya kacal daga ita bakari sadiq yamatsu take ya amsamata gaba daya yarinyar tatafi da tunaninsa yarasa mezai tambayeta tace malam sauri nake za'amin fada agida Sadiq yace don Allah meye sunanki tace Fatima tana rufe baki taigaba abinta mukai mukai taki tsayawa Sadiq yace mubita muga gidansu da sauri muka koma wajen da muka aje mota mukadauko mukabi hanyar da yarinyar tabi kosama kokasa mukanemeta muka rasa gashi arear gaba daya ba gidaje sai bishiyoyi da ciyayi Sadiq duk yabi yakidime akanta niko mamaki abin yabani kasancewar shi mutumne salihi baya kula mata amma yau shine mace tarudashi haka. Tundaga wannan lokaci muka shiga neman gidansu Fatima muka rasa duk wata islamiyya dake yankin munje lokacin tashi amma bama ganin Fatima bama ganin mai irin uniform dintama munyi har mungaji muka hakura. Amma sadiq kullum cikin zancenta da tinaninta yake Sadiq bakaramin kaunar Fatima yakeba itace mace tafarko da zuciyarsa

Chapter 1 of 2