Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
iya mantawa ko kuma na rude dan haka kumanta kawai domin innace zan fada muku komai zan iyayin karya domin bazan iya misalta kyanshiba ku kuma wasu zasu iya sumewa kai harma da masu mutuwa saboda kyanshi dan haka mutafi kai tsaye cikin labarin...... A fusace ya dago. "Aknan wannan wani irin kirane. "? tace. "Sorry uncle naga na kiraka two types baka amsaba shiyasa. ". "Hummmm. " yasaki huci. "Meya faru. "? Tace. "dama daddyne yace na kiraka. " yace. "Okey ina zuwa. " harta juya se kuma ta juyo. "Uncle zakamin waka birthday dina ya kusa. "? harara ya watsa mata. "Bazan yiba. " ta marairaice. "Saboda me uncle. "? Yace". Saboda bakijin magana yanzu kiri kiri Aknan ban hanaki yawo ba dan kwaliba...... " ta rike haba da sauri. "Sorry uncle na sha'afane shiyasa amma insha Allahu daga yau zan kiyaye. " shiru yayi tace. "To zakamin. "? Murmushi me kara bayyanar da kyanshi yayi tareda daga kai, da sauri Aknan tace. "Thank You uncle. " ta wuce da gudu tanajjn dadi. Tashi yayi cikin tafiyanshi me tsananin daukan hankali da kasaita ya nufi cikin gidan dan zuwa amsa Kiran yayanshi. Zaune ya sameshi a mainfalo shida uwar gida karisa yayi fuskarshi cikeda annuri ya zauna a kujeran da take pacing na yayanshi Alh. Sadeeq, fuskantarshi Alhaji yayi tareda fadin cikin girmamawa."barka da rana yaya, Aknan tace nazo kana nemana, " gyada kai yayi tareda cewa. "Kwarai kuwa Maheer dama ba wani abu yasa nace ina nemankaba sedai na kara maka magana akan aure, gaskiya Maheer nagaji da ganinka a haka me kake bukata baka samuba. " hajiya Asma'u da batayi maganaba tun zuwan maheer gurin tace. "Kwarai kuwa Alhaji in dukiyane Allah ya mallaka maka maheer haka in daukakane ga kwamciyar hankali ga farin jini dan haka yan mata ke bibiyanka duk inda kake to komai Allah yabaka amma kace baza kayi aureba. " Wani lallausan murmushi yayi ya dada fuskantarsu. "Aunty ba zaki gane bane Aure lokacine in Allah yayi lokacin yayi zanyi auren kudai kawai kuci gaba da tayani da addu'a Allah bani mace ta garAlhaji ya bude baki zeyi magana maheer yayi saurin dakatar dashi ta hanyar kallon tsadaddan agogon dake hannunshi yace. "Yaya lokaci yayi kacemin yau kanada ganawa da gwamna... " Alh. Yayi murmushi domin yasan halin Maheer da canxa xance yayi hakane dan avar maganan, daidai lokacin Diyam kanwar Aknan ta sauko daga sama duban su tayi tareda fadin. "Uncle next week ne zamuyi graduation na kammala secondary school please inaso kayimin waka... " dubanta yayi baki a sake. "Iye lallaima wancan birthday wannan kuma graduate to bazan yiba I have a lot work to do.... " ta marairaice. "Please uncle banaso naji kunya a cikin kawayena danna gama fada musu uncle MK zemin waka... " dariya sukayi dukkansu maheer yace. "Alright kisamu Rayyan ya rubuta miki ni kuma sena rera miki kinji dadi babyn uncle. " ta buga tsalle. "Thank You uncle. " Alh. Ya dubi maheer. "Yawwa munyi magana da me martaba sarkin bauchi akan bikin yarshi da za'ayi this Saturday yace kunyi magana zaka hallarci show din kayi musu waka.. " ya gyada kai. "Yes we al ready talk dan harna gama rera ma amarya da ango waka on Saturday Zan bi flight zuwa bauchi idan nagama dagacan zan wuce Abuja dan ana bukatana a company. " Alh yace. "Alright kunyi maganan paid ne. " maheer ya gyada kai. "Yes munyi kasan me martaba harma ya turomin. " Alh yace. "Alright yanzu inka tafi abuja se yaushe zaka dawo. "? Ya danyi shiru. "I don't think so but amma sena gama ayyukan da suke gabana zan dawo dan akwaima sababbin mawaka da za'a Wa ordition. " Alh yace. "Allah baka sa'a. " yace. "Ameen. " mikewa yayi haj. Tace. "Ina zaka. "? Yace. "Splash ward zani. " Aknan tayi saurin fadin. "Uncle please drop me at school wallahi nayi late kuma lecture two garemu kuma driver bayanan. " Yace. "Lallaima Aknan saboda kin maidani driver dinki meze hana bazaki driving da kankiba. " kallon Alhaji tayi, Alh yace. "Yes nina hanata driving saboda abunda tayi kwanaki garin tukin sakacinta. " maheer yayi kwafa. "Alright les go. " nan ta janyo tsaleliyar handbag dinta suka fice. Tunda suka isa Kasu university aketa damunsu da kira. "Mk-Mk. " kasancewarshi mawaki me farin jinii. "Har yaje yayi parking inda aka tanada dan parking kusa da faculty department dinsu Aknan. Mutane duk sunbi sun zagaye mishi mota kowa kiranshi yake masu cewa. "Maheer inasanka. na cewa masu cewa. "Mk ni fans din kane ina following dinka a media sannan inasan wakokinka. " nacewa Shidai duban Aknan yayi yace. "Daga yau ba zan kara kaiki ko inaba. " tace. "Uncle aiba laifina bane kaine kadauko motan da glass dinta anagani kaga is not my fault. " yayi tsaki. "alright fita muje. " ba musu ta fito. Nan mutane suka rufeshi cikin fara'arshi na koda yaushe ya dingi yima mutane godia, masusan yin pic dashi nan ya tsaya sukayi masusan signing dinshi ya musu amma be bada phone number dinshiba sedai ya bada complementary card dinshi ga me bukatan san ganinshi. Mutane kowa se murna yake dan ganin Mk bashida girman kai, Rayyan abokinshi dake gefe yayi murmushi karisawa mahir yayi yace. "Kai kuma yana ganka anan waka barwa aikin dake office. " yace. "Madam na kawo school. " maher yace. "Ok jeedarh sarauniya kenan. " Rayyan yace."mutane ne naga sun taru shine aka cemin Mk ne yazo. " maheer yayi kwafa Rayyan yaci gaba. "Yanzu maheer kamanka kazo ka tsaya kana selfie da wa'innan mutanen haba ai wannan zubda ajine. " Maheer yayi daria me ciwo. "Ko..... "? Ya kuma murmusawa."Allah sarki rayuwa Rayyan meye abun girman kai a ciki dan Allah ya bani daukaka dan nayi hoto dasu ba komai bane face kara musu kwarin gwiwwa akaina, Rayyan kada muyi amfani da daukakanmu dan nuna isa ko wulakanta dan Adam muyi amfani dashi ta hanyar karawa mutane kwarin gwiwwan da sukeda shi akanmu. "........ Tap.... Tap...... Tap..... Karan tafin rayyan yace. "Mutumina shiyasa nake kara sanka da masu daukaka kowa irinka yake da Al'umma sunji dadi. " rayyan ya dubeshi. "Ina zakaje yanzu. ". "Splash ward zani Zamu hadu da umar m. shareef akan wani offer. " rayyan yace. "alright dama inaso inzo in sameka jiya munyi magana da director Alfazazee Muhammad akan film dinshi daze fara zakamai waka sunanan suna jiran feed back." Juyowa yayi. "Yaushene direction din. "? Rayyan yace. "Next week. " Mk yace. "Next week am not around. " rayyan yace "to nace ya daga zuwa upper week. "? Maheer ya girgiza kai. "A'a aiki yamin yawa. " rayyan yace."yaushe zance mishi zasu samu kasan yan kannywood sunasan wakanka. "? Dan Jim Mk yayi can ya girgiza kai tareda fadin, . "kace mishi bansan da direction dinba gaskiya bazan samu yiba saboda baya plan dina.. " rayyan ze kuma magana kiran *Umar m. Shareef* ya shigo wayan maheer dan haka ya shiga mota batareda ya daga ba yayi gaba............. Bayan fitansu maheer haj. Asma'u tashi tayi ta haye samaWaya ta dauka takira kanwarta zeeza tana dagawa ta gaidata Ba tareda ta amsaba tace. "Sakarya wai yaushene zaki tahone ya kamatafa kizo. "? Zeeza tace. "Aunty inanan zuwa se end of this month. ". "Mtsssww banza kawai ki taho goban nan saboda kadafa maheer yaje yafara san wata yakamata kizo ki dauke mishi hankali. " zeeza tayi saurin fadin. "Zan taho goban nan dan banaso wata ta auri Mk in baniba kinsan yanda nake bala'in sanshi. " haj. Tace. "Yawwa kinsan dai na fada miki abubuwan da zaki dinga yi in kinzo ko. "? Tace. "Eh. " Tace. "Yawwa se kinzo ki gaidamin da umma. " nan ta katse wayan. *Tooh* Yanzu aka fara *Taku babyn........* Hmmmmmmmm *Share* *Comments* *and vote β˜‘οΈ* 8/20/21, 8:15 AM - Mimi: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *LABARINA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ Alkalamin. ✍️ *Mimi.πŸ‘Έ* Haleemart Iserh *(ummu ramlat)* *🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ* *M. W. A* *Bismillahir Rahmanir Raheem* 9&10 Alh. Sadeeq kam yana zaune yana karanta jarida wayanshi ta hau ruri ganin abokinshi ne yasa yayi saurin yin picking yakai kunni yana fadin. "Major Aliyu khaliyal se yau aka tuna damu. " bamgaren Abbah kam numfashi yaja kafin yace. "Kayi hakuri abokina wallahi ayyukane sukayi yawa." Alh yace. "Naji yanxu ya madam da yara. "? Abba yace. "Lafiya ba lafiyaba." Alhaji yace. "To me kuma ya faru major."? Abbah yace. "Dama dalilin kiranka da nayi batune akan yar gurin mariganya Rumana idan da wanda ya dace a gunka kafadamin se a hadasu aure. " Alh ya runtse ido yana kara tausayawa rumana yace. "Yanxu major rumana zakayima aure gasu raudah nan. "? Major yace. "Bazaka fahimta bane yarinyar na neman daukomin abun kunyane shiyasa na yanke wannan hukuncin..... " Alh yayi jim. "Eh inaso inyiwa maheer aure amma banaso namai zabi nafiso ya zabo da kanshi kasan kuma da wuya ya amince da ita rumanan. " Abba yace. "Ai rumana ba sa'ar shi bace kadai nema mata wani. " Alhaji yakuma yin jim. "To inba damuwa abani aurenta I aso zan aureta... " Da sauri Abbah yace. "Kasan me kake fadi kuwa Alhaji rumana fa.... "? Alh yace. "Kwarai ina matukar tausaya mata, dan Allah kada kace a'a inni amininkane ka bani auren rumana, ko kuma na maka tsufane... . "? Abba yayi saurin cewa. "A'a abokina ba haka bane kuma ni na baka ita nanda kwana bakwai se a daura auren. " Alhaji ya girgiza kai. "A'a ka bari senan da 3weeks adaura auren lokacin kanina ya dawo. " major yayi murmushi. "Nagode abokina karufamin asiri. " nan sukayi sallama. Wayan yabi da kallo yana tunanin yanda zasu kare da hajiya Asma'u, Allah yaji kuma ya sani shi yace ze aure rumanane kawai.Saboda yana tausaya mata kuma yanaso ya temaketa amma ze fadawa haj. Kuma ze auri rumana kome ze faru ya faru...!!!! ****************************************************** Cikin fada bakin ciki karara a fuskar haj. Maryam ta dubi Abba. "Dan me zakace Alh sadeeq zaka aurawa rumana bayan kasan yanda nake da matarshi. "? Yace. "To me kikeso nace mishi bayan kinsan Alfarma yanema kuma yafi karfin haka a guna. " dogon tsaki taja ta haye sama tana bakin cikin hakan domin tasan irin kudin Alhaji sadeeq khan. *Asalinsu* Asalinsu mutanen Saudi Arabia ne garin makkah nanne garinsu na gado larabawane ciki da bai dinsu su biyu tal iyayensu suka haifa bayan rasuwan su Abbakar sadeeq khan shiyaci gaba da rainon Maheer khan(Mk) cikin kulawa daso da kauna. Aiki Shiya kawo Alh sadeeq Nigeria wanda babban likitane masani dan a duniya ana alfahari dashi. Maheer khan wanda yataso a hannun yayanshi ya kasance shine komai nashi yamai gata fiyeda yayanshi na cikinshi, babban mawakine kasancewarshi mutumin saudiyya yasa har wakan larabawa yanayi amma da yike a Nigeria ya taso yasa Hausa ta goge a bakinshi shima Alh sadeeq jin yaji dadin zama a Nigeria yasa be komaba amma yana kaiwa yan uwa ziyawa wanda shima a hankali Hausa ya Kama bakinshi. Alh sadeeq ya auri haj Asma'u wacce take yar jahar katsina inda suka haifi yara guda biyu Aknan itace babba wacce ynx takai shekaru 18 se diyam da take sa'ar rumana, nan sukaci gaba da rayuwa Harda maheer da yakeda babban companoni a abuja da Kaduna na abuja global record sena nan kd white space global record Inda akwai manya manyan mawaka na gida Nigeria dama na waje, Bayada girman kai ko kadan yanxu shekarunshi 30 amma har ynx besamu wacce ze auraba acewarshi yan matan ynx duk makwadaitane koda wata Zata aureshi sedan dan daukakanshi ko dan dukiyarshi, yanada masoya da yawa wadanda yasani da wanda be saniba dan wasu a TV kawai zasu ganshi su fara sanshi wasu kuma suji wakanshi amma duk da haka be tabajin yana san ko daya ba duk da yayan manya da dama suna sanshi amma betaba jin ko san wata ba, Maheer na dawowa gida (Kaduna) duk weekend domin bayaso aikinshi ya hanashi kula da yayanshi Wanda yake matsayin mahaifi a gareshi duk da ko wani satin hakanan yake daukan hutu ya dawo gida yayishi, wanda comfanyn dakenan kd ya mallakashi a hannun Umar m. Shareef ne yayinda shikuma yake tafiyar dana abuja saboda shine babba Wanda duk duniya tafi sani. Shi mutum ne me matukar farin jini ba'a Nigeria kadaiba duniya gaba daya nake muku magana, yanada kirki sosai kuma ya iya waka dan da wuya kaji wakanshi kace be yiba..... Hummmm.... Inshort dai zance muku maheer khan gifted ne tako Ina yayi gashi dasan temako, Kai tsayawa fada muku yanda MK yake bata lokacine saboda bazaku fahimtaba dan haka mukoma cikin labarin mu...... Wannan kenan...... . har ynx baa faraba dan wallahi labarina yanada tsawo dan haka masu karatu ku gyara zama..... *Ummu ramlat ce πŸ‘Ž* 8/20/21, 8:15 AM - Mimi: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *LABARINA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ Alkalamin. ✍️ *Mimi.πŸ‘Έ* Haleemart Iserh *(ummu ramlat)* *🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ* *M. W. A* *Bismillahir Rahmanir Raheem* 11&12 Shigowan zeeza gidan kenan tareda katuwar trolley dinta tayi shigen kananun kaya kan nan yasha attachment gashi badan kwali inka ganta se kace zindikiyar arniyaniyarce, kicibuc tayi da Maheer yafito rataye da brief case dinshi da sauri ta saki trolley dinta a kasa ta ruga da gudu tana ihu da nufin yin hugging dinshi, da sauri ya kauce gefe ta taba baki. "Haba ya Mk kana abu se kace ba superstar ba. " ya danyi murmushi." Ni banasan halin yahudawan nan." ta saki baki. "Haba ya Mk kaman wanda beyi rayuwa cikin turawaba.?"? Ya taba baki. "Alright yanxu dai kinxo lpy. "? Ta shagwabe fuska. "Lapiya. " yasa hannu ya dago mata trolley din,. "Alright gashi ki karisa ciki ki huta sena dawo. " ta zaro ido. "Ina kuma zakaje ya Mk bayan kuma kasan nazone danka koyamin music. " Yayi murmushi yana duban agogo. "Inada wani show ne a fadan sarkin bauchi lokaci na tafiya danma Zanyi following train ne, bye zeeza sai na dawo. " har ya juya sai ta janyo hannun shi ya juyo da sauri tace. "to yaushe zaka dawo. " ya daure a haban shi yace. "uhmmm i think bazan wuce two weeks ba indai kuma nayi signing wani contract da aka kawomani daga touring zan iya fin months. " ta shagwabe fuska. "please kada kayi signing din ka dawo da wuri. " yayi murmushi. "all right nima ina tunanin da wuya nayi signing saboda record level ne company. "tayi murmushi. "all right sai ka dawo ya M K. " da sauri ya fice a gidan saboda private jet din shi na jiran shi. ******* ******* . "kiyi hakuri hajiya....... " cikin fada ta daka tar dashi. "Me kakeso nace maka Alhaji ina zaune dakai shekaru da dama lokaci daya kace zakamin kishiya kuma karasa dawa zaka hadani kishi se da wacce nafi yarinya karama kuma yar cikinka, shima bacin haj. Maryam da bazaka fadaminba ni ba abinda zance maka domin ko sedai ka zaba ni ko ita dan wallahi indai ita ka zaba ko sedai karabu dani ka bani takaddana.........., "ta fashe da kuka nan hankalin Alhaji yadada tashi, Nan ya shiga lallashi ganin ta kafe akan ita indai seya kara aure sedai ya saketa hakan yasa ranshi ya baci cikin kakkausan murya da kuma fada yace. "bazan fasa aureba kuma bazan sakekiba kiyi duk abinda zakiyi....... " ta sake fashewa da kuka. "to ai wallahi bada gidanka nazo duniyaba kuma sannan ba dauramin kai akai a kafaba zan iya tafiyana koba takardarka ai miji goma ba uba goma bane....... " wani mugun kallo ya bita dashi tareda daga yatsa yana nunata cikin tsawa yace. "Wallahi Asma'u kika kuskura kika tsalleke kafa kika bar gidannan to se ranki ya baci Mtsssww..... " yaja dogon tsaki ya wuce danshi tsayayyan namijine a gidanshi.... Zubewa haj. Asma'u tayi bisa three seater tafashe da kuka me cin rai, duk wannan abun da akeyi a idon zeeza, Aknan, da kuma diyam ne ganin Alhaji ya fice yasa dukkansu sukayi kanta suna lallashi, Zeeza ce ke fadin. "Aunty kiyi hakuri kada ki tafi kada kije ko ina ki zauna a gidanki ta shigo gidan mukuma zata gane aya zakine agunmu. " Aknan tace gaba daga zancen zeeza. "Eh mummy zata gane mu ba'a kishi da mummynmu.... " diyam kam babu abinda tace, hawaye haj. ta share cikeda gamsuwa da zancen su Aknan domin dama ko basu fadaba ba inda zata iya tafiya tabar mijinta farin cikin ta.. Wayan tane ta hau ruri ta sake share hawaye ganin haj. Maryam yasa tayi picking tareda kangawa a kunni. "Hello hajiya. " Acan bangaren haj. Maryam tace. "Ya dafatan dai kinyima Alhaji bala'i yafasa auren. "? Nan haj. Asma'u tafada mata yanda sukayi da Alhaji ta dora da fadin. "Hummmm ni yanxu haj. Maryam ba yanda zanyi zan barshi yayi auren...... " haj maryam tasaki huci me zafi tareda naushin iska tace. "Kai hajiya baki iya abun bane Wallahi. ". "Hummmm ya zanyi hajiya kinsan halin Alhaji Wallahi ze iya rabuwa dani kuma yayi aurensa ko a jikinsa. "haj maryam tace. "Hummm to yanxu kiyi amfani da shawaran se zeeza inta shigo kuci ubanta ku bata wahakar da da kanta seta gudu.... " dariya haj Asma'u tayi. "Shiyasa nake sanki hajiyata. " nan ta tashi tayi ciki aka ci gaba da kulle kulle. Alhaji sadeeq kam waya ya daga yakira MK hankalinshi tashe yake bashi labarin yanda sukayi da haj. Asma'u. Ijiyar zuciya maheer yasaki yace. "Yayah ai dama ni nasan haka zata faru domin kasan ko wata mace akace za'a wa kishiya dole ta nuna halinsu na mata, nidai shawarana anan shine kada ka fasa wannan auren Aunty kuma ka barni da ita. " ijiyar zuciya Alhaji yasauke yanajin dadin yanda dan uwanshi ke kara mai kwarin gwiwwa, Mk yace. "Yanxu saura kwana nawane daurin auren tunda kacemin ba za'ayi wani bukunkunaba. "? Alh yace. "Saura kwana takwas yanxu ni kin fadawa haj nayi tun farko saboda banaso ta sani se ana zan fada mata. "Mk yace. "To ai gara data sani tun yanzu duk abunda ze faru ya faru, wai wama ya fada mata."? Alh yace. "Hajiya maryam mana matar major Aliyu bello khaliyal. " Mk yasaki huci. "Okey Allah kaimu yaya. " Alh yace. "Wai yaushe zaka dawo,? ya kamata kadawo kafin ranan daurin auren dan dani dakai da Alhaji musa kawai zamuje. ". "Hummm yaya zan dawo kafin lokacin insha Allah. " Alh yace. "Meyasa ba zaka dawo yanzu ba. "? Mahir yace. "Yaya muna ordition ne yanzu amma by god grace zan samu nayi skipping nadawo before the day.... " Alh yace. "Allah kaimu kanina. "Nan sukayi sallama da naheer ze kashe yace. "Ka gaidamin aunty.......... " da sauri Alh yace. "Wata aunty kadafa ka ballomin ruwa.. ": maher ya gimtse dariyar dake shirin kufce mishi domin yasan tonon fada yayi dan yaji me yayanshi zece, nan sukayi karayin sallama kowa ya kashe, Maher dake office yayi shiru yana kallon wayan, shi yaushene zeyi aure gashi har yayanshi ze kara na biyu.? Daya tuna aure nufin Allahne se yayi murmushi. Toh rumana wannan shine badi barai anya an tsira na auren da za'a miki ko za'a koma ruwane? πŸ€”πŸ€”πŸ€”πŸ€§πŸ€§πŸ€§ . tare dani *ummu ramlat*✍️ *share* *comments* *and vote β˜‘οΈ* 8/20/21, 8:15 AM - Mimi: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *LABARINA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ Alkalamin. ✍️ *Mimi.πŸ‘Έ* Haleemart Iserh *(ummu ramlat)* *🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ* *M. W. A* *Bismillahir Rahmanir Raheem* 13&14 Tana rakube gefen famfoo se kuka take wanda tasaba kullum danya zame mata jiki tunda wannan abun yafaru na sharrin da aka mata tsakaninta da dan uwanta Faheed se wahala ya karu harma yafi wanda takesha da, dan yanzu yan aikin gidan sunfita galihu tunda yanzu a dakin karnuka take kwana tareda su ga kukan da yake zuwan mata duk lokacin data tuna aure Abbanta ze mata . "Keeee!!. " aka fadi cikin tsawa firgigit ta dago. "Na'am Aunty umaima. " "Ke dan ubanki ba aiki aka sakiba kika zauna kinata kuka. "? tasa hannu tana share hawayen tareda tashi da sauri cikin rawar murya take fadin. "ba.... kuka..... nakeba...... Aunty... " ta duka taci gaba da wankinta da tun safe tafara.,. "Mtsssww. "Umaima taja tsaki. "dama nazone ki bani gyalena zan tafi school sauri nake.. " jikin rumana yadau rawa domin yanzu ta chanya ko bushewa beyiba balle ta goge,In ina tafara umaima na hango gyalenta a waya tace. "Kutumar ubancan dama yanxu kika wanke to bari naje na fadawa mummy. " Rumana na bata hakuri tawuce. Rumana na tsaye tsuru umaima tazo ta dubeta. "Mummy na kira. "Jiki a sanyaye tabi bayan umaima. A tsaye suka tadda hajiya se girgiza take cikin tsawa tace. "Ke dan uwarki ba awa daya na bakiba ki wankesu su bushe ki gogeba amma yanxu kinyi kusan awa nawa. "? Shiru Rumana tayi kanta na kasa, hajiya ranta ya baci tasa hannu ta gaurawa rumana marida seda ta kife,. "dan uwarki fara tsallen kwado se kinyi harkin gaji sannan zaki tashi kuma kikoma ga wankin can kici gaba insun bushe ki goge, bazaki faraba ko sena karyaki,. " batada zabin daya wuce tayi abinda haj. tace. "Mtsssww wawuya, jaka, sakarya ai uwarki jaka ta haifamin yanda rahma take shaidaniya haka kike harma kinso kifita yar matsiyaciya kawai Mtsssww. " takuma jan tsaki tawuce kan cushion ta zauna, wani wahalallan kukane ya kufcewa rumana jin ana zagin mahaifiyarta tatsani a zagi mahaifiyarta a gabanta amma hakanan tadaure taci gaba da abinda aka sata, Daga farkon falon zuwa karshen falon duk da yanada tsawo sosai amma hakanan tayi tanayi tana hawaye, Tayj sosai harta gaji danse bayan magriba akace tatashi nan taje taci gaba da aikinta, bayan tagama ta jira suka bushe ta goge takaima kowa dakinshi, a takaicedai se cikin dare tagama aikin nan ta nufi dakinda take kwana (wato dakin karnuka). Kamar kullum yauma sunata haushi suna fito da harshe dan da ba'a daure sukeba tsaf zasu lasheta, abincine da aka kawo musu masu rai da lafiya sunci wasu sun barwasu dan wasu kadan suka taba domin abincin da yawa Kala kala, wanda suka barin tajanyo domin rabonta da abinci takai kwana biyar sedai taja ruwan famfoo, hannunta har rawa yake saboda yanda take tura abincin seda ta cinye tas ta kara janyo rahowan karnukan ko a jikinta burinta itadai tasamu abunda zataci domin yunwan da takeji, seda ta cinye sannan taji ta koshi tashi tayi ta gabatar da sallolin da bata yiba, Bayan ta idar kamar kullum kafin tayi bacci tafara karanto Alkur'ani tana kuka domin yawamci tasan fassararta kuma tana tausayawa kanta Ainun. Tun ranan da haj. taga megadi yana koyawa ma rumana karatu tasa Alhaji ya koreshi aka kawo wani acema Alhaji ai shine abokin iskancin Rumana, seda tayi kukanta ma'ishi tana kai kukanta ga

Chapter 2 of 14