Reading TAKOBIN DAUKAKA Chapter 6 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yaransa ke yi masa sai ya wangale bakinsa yana mai ɓaɓɓaka dariyar farin ciki,


Duk wannan abu dake wakana jarumi shamsuddin yana tsaye a gefe guda yana kallo


A lokaci guda KIRMALU ya murtke fuska tamkar an aiko masa da SAƘON MUTUWA


Kawai sai ya zare wani mashi a gadon bayan sa mai baki biyu ya daga sama da nufin ya farka cikin sarauniya lasmirat da Sunaila,














Koda ganin abinda ke shirin faruwa sai shamsuddin ya falafala da azababban gudu izuwa kan uban muridai yana mai karanto waansu addu'o'i na musamman a cikin ransa tare da maimakon Ubangijin musulunci,


Yayin da rage saura taku goma tsakanin su, sai a sannanne muridan suke iya ganin shamsuddin da idanuwan su,


Kafin aya daga cikin su yayi wani yunkuri shamsuddin ya shammace shugaban muridan ya gabza masa wani wawan naushi a fuska,


Bisa mamaki sai aka ji uban muridai KIRMALU ya kurma wawan ihu sannan ya jefar da mashin dake rie a hannun sa,


Al'amarin da ya harzua zukatan sauran muridan kenan kuma fusata ainun suka afkwa shamsuddin da azababban yai suka wanzu suna kai masa miyagun hare haren


Shamsuddin ya wanzu yana karewa tare da zillewa harin muridan tare da maida martani cikin bakin zafin nama ta hanyar amfani da hannun sa da kafa wajen kai bugu da naushi,


Tabbas ikon Ubangiji ya huce tunanin an Adam domin abinda mutum yake ganin bazai yiwu ba sai kaga Ubangiji ya samar dashi,


Domin kuwa duk wanda shamsuddin ya nausa a cikin muridan sai kaji inda ya nausa in ya ya karye yayi kara as ruus, ya kurma wawan ihu,


Nan fa ihu da kururuwur muridan ta cika dodon kunne da tsaunin baki aya,


Duk inda shamsuddin ya sanya gaba sai dai kaga muridan na zubewa kasa matattu tamkar yana sassabe a gonar auduga jini yana kwaranya,


Wohoho Hakika duk wanda ya iya ya huta inda ace mutum yana tsaye a wannan waje yaga yadda shamsuddin ke hallaka muridan dola ne ya jinjina masa ya tabbatar dacewa ya cika SARKIN SADAUKAI,


Kafin shuewar dakika ari shamsuddin ya hallaka gaba aya muridan ya zubar da gawarwakin su,


Sa'adda uban muridai KIRMALU IBN SHAMSHAN ya yi arba da gawarwakin jama'ar da sai kawai ya mie tsaye zumbur yana mai kurma wawan ihu


Take wata irin gagarumar Iska ta dunga fitowa daga hancinsa da bakinsa wacce ta sanya gashin kan shamsuddin ya mimmike ,


Kuma tayi sanadiyyar farfaowar su sarauniya lasmirat daga dogon suman da suka yi.


Sa'adda sarauniya lasmirat,boka Dayyubul-Barmas, yaslir, Sunaila,saltir, Huzmal,Barbusa, Huruful-labarus, suka yi arba da gawarwakin muridan kwance cikin jini kuma jikin shamsuddin duk ya aci da jini muridan sai suka cika da matukar mamaki,


Suka ce a cikin ransa shin taya ya akayi shamsuddin ya samu gagarumin karfin da samu nasarar hallaka muridan


Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan kawai suka zuba idanu domin suga abinda zai faru tsakanin shamsuddin da uban muridai KIRMALU,


Uban muridai KIRMALU na kammala kururuwur sai kawai ya zare wata zabgegiyar adda a ugun sa mai kaifin tsiya ya falfala da azababban gudu izuwa inda shamsuddin yake duk sa'adda ya ajiye afarsa aya sai kaga kafar wajen ta tsage ta rufta izuwa ciki,


Koda ganin hakan sai shamsuddin ya zare takobin sa ya kwala kabbara da karfi ya ruga kan uban muridai don tarar juna,


Lokacin da ya zamo saura taku goma a tsakanin su sai shamsuddin ya zamo an wada agaban uban muridai tamkar an ajiye yanwa a gaban kare,


Lokacin da aka hau sai aka ruguntsume da azababban yai mai matukar firgici daban tsoro,


Shamsuddin ya wanzu yana kare hare haren uban muridai tare da mayar da martani cikin bain zafin nama JURIYA DA BAJINTA,


Duk sa'adda uban muridai ya kai masa hari da addar sa idan ya goce duk abinda takobin ta sauka a kansa sai kaga yayi bindiga ya tarwatse yazama gari koda kuwa gini komai warinsa, nan fa shamsuddin da uban muridai suka tashin hankalin duk wata halitta dake fadar,


Gaskiyar masu iya magana da suka ce fadan da yafi karfin ka sai ka zamo an kallo,


Kuma tabbas idan gwani da gwani suka hau, juriya da naci suka ci karo da juna dole ne yai ya zamo tashin hankali daban tsoro,


Hakan ne yafaru dasu boka Dayyubul-Barmas domin koda suka lura cewa duwatsun da su shamsuddin ke rusawa a fadar suna neman danne su sai suka rarrafa da afafuwan su izuwa bayan waansu duraku a fadar suka lae suna hangen abinda ke wakana


Sai da aka shafe tsawon sa,a aya cur ana wannan bain artabu


Shamsuddin bai samu nasarar koda lakutar jikin sa ba duk kuwa da cewar yana karanta addu'a na musamman a cikin zuciyar sa


Ana cikin wannan artabu ne uban muridai ya samu nasarar make takobin dake hannun shamsuddin a lokacin da ya daka tsalle da nufin ya hau kan kafadar sa


Kawai sai uban muridai KIRMALU ya canza salon faan sa a inda ya shiga kaiwa shamsuddin hari da karfin damtse bada makami ba ,


Shamsuddin ya wanzu yana zillewa harin tare da amfani da dubaru da hikimomi, yana mai kwala kabbara gami da neman taimakon daga sunayen fiyayyan halitta annabi Muhammad s,a,w,


Nan take wani irin gagarumin karfi ya shige sa kawai sai ya daka tsalle sama ai ku wa sai gashi a saman uban muridai tamkar an janye sa da ungiya,


Kawai sai ya dunkule hannayen sa biyu ya irawa uban muridai KIRMALU naushi a wuya,


Saboda arfin naushin sai da asusuwan wuyan sukayi ara ruus as!


Uban muridai ya kurma wawan ihu, Kafin ya sake wani yunkuri shamsuddin ya sake gira masa wani naushin.


Kawai sai akaga jikin uban muridai ya sandare ya yi asa zai fao,


Koda shamsuddin ya lura cewa zai rikito daga saman uban muridai sai kawai ya dako wani wawan tsalle naban al'ajabi da mamaki ya sauka abisa turba,


A lokacin da gangar jikin uban muridai KIRMALU ta fai asa rikica, tamkar an jefar da toron Giwa ko shurawa bai yi ba


Nan fa mamaki ya turnue su sarauniya lasmirat Bisa ganin gagarumar bajintar da shamsuddin yayi na hallaka uban muridai KIRMALU da yaran sa.










Al'amrin su shamsuddin kuwa sai da suka shafe tsawon kwanaki huu a saman tsaunin Darul SHAFRAS,kowa ya warke sumul daga raunukan dake jikin sa,


Bayan shamsuddin ya samu nasarar ebo ruwan ma,ul- hayat a wani bangare a tsaunin,


Sannan su aljani Huzmal suka sake aukar su aka cigaba da tafiya,


Ana cikin wannan tafiya ne a lokacin da rana ta take sai sarauniya lasmirat ta dubi Sunaila tayi gyaran murya sannan ta kawo gwaron numfashi ta ajiye tace " ya Sunaila inyi miki wata tambaya mana idan bazaki damu ba,


Sunaila tace " ina sauraren ki fai tambayar ki,


Lasmirat ta ce" A can baya lokacin da kika samu nasarar akan wannan aljana acan birni na lokacin da na tambaye ki labarin rayuwar ki kin faa mini cewa baban Burin ki shine ki sadu da mutane ma,abota addanin Musulunci, domin aukar fansa akan wani azzalumun sarki shin


Jarumi shamsuddin baya aya daga cikin mutanen da kike nema ne?


Koda jin wannan tambaya sai sunaila tayi murmushi


Duk da kasancewar fuskar ta na rufe da rawani sai da lasmirat taga alamun loawar kumatun ta a lokacin da tayi dariyar,


Sannan ta dubi lasmirat yace" ya yar uwa ta kiyi sani cewa bawai ina tantama Game shamsuddin ba ne tabbas yana daga cikin ma, abota addanin Musulunci da nake nema sai dai ina so na kammala haa waansu hujjoji ne sannan na kari Addinin sa,


Koda jin wannan jawabi daga bakin Sunaila sai lasmirat ta gyaa kai Sannan ta bui baki akaro na uku da fara wannan tattaunawa ta ce"Amma kina ganin Ubangijin shamsuddin bashine abinda dogaro ba kuwa ki dub kiga yadda ya samu nasara akan su aljani Huruful-labarus da uban muridai wanda boka Dayyubul-Barmas yagaza kare mu,


Koda jin wannan batu daga bakin lasmirat sai sunaila tace"Tabbas duk abinda kika faa akan shamsuddin haka ne harma ya huce haka inda ace kin taa karanta jarumi Hilal da irin nasarar da ya samu a rayuwarsa da ke kunshe a cikin littafin KARSHEN ZALUNCI,


da zaki tabbatar dacewa girma da sha,anin ma,abota addanin Musulunci ya huce yadda ake tsammani,


Koda jin wannan batu sai sarauniya lasmirat tayi ajiyar zuciya sannan ta kawo gwaron numfashi ta ajiye tace" Ta ijan idan kuwa har haka ne abinda shamsuddin yayi abaya bakomai bane. Face sharar fage domin ke gaban mu yafi na baya yawa,


Tafiyar kwanaki arba'in akayi aka iso kogon Garul- barzahu inda kubar miftahul-daryal take


Sai da shamsuddin yasha gwagwarmaya dakyar da taimakon Ubangijin halitta ya samu nasarar kashe miyagun halittun dake ciki,kuma ya samu nasarar auko kubar miftahul-daryal,


Hakika su sarauniya lasmirat sun ga iko da kudirar Ubangiji a wannan rana


Bayan kwanaki biyu sai aka sake cigaba da tafiya domin isa gidan boka Daryalu domin ebo ruwan koramar sa


Yayin da aka iso cikin koramar sai aka tarar tana auke da waansu irin halittu masu auke da fuka-fukai irin na jemagu suna da kawuna irin na bil,adama, suna wani irin gurnani mai sanya firgici daban tsoro.


Nanfa aka ruguntsume da azababban yai mai matukar firgici daban tsoro yazamana cewa kowa ya gane kuren sa,


Sai da aka wuni cir ana artabu babu sassauci, sannan aka samu nasarar hallaka halittun amma kowa ya samu manyan raunuka a jikin sa


Nan fa yazamana cewa tsananin azabar dasu lasmirat suka sha tasa jikin su yayi sanyi kuma gwiwoyin su sukayi sanyi dukkanin su suka yi nadamar yin wannan tafiya domin wata buata ta jin dain duniya musamman sarauniya lasmirat,


Bisa wannan dalili ne yasanya dukkanin su suka yanke shawarar karbar addinin Musulunci


Bayan sun karbi kalar shahada ne a wajen shamsuddin


Sai shamsuddin ya bayyana wa sarauniya lasmirat cewa dukkanin bayanin da boka Dayyubul-Barmas yayi mata aiki ne. Na bokaye ma,ana sihiri shi kuma sihiri karya ne


Saboda haka imani da tayi da Ubangijin musulunci zai biya mata dukkan bukatun ta kuma muradin ta ya cika na samun aukaka a duniya da ma tsawon rayuwa


A sannanne Sunaila ta cire rawanin dake kanta fuskar ta ta bayyana a fili arara


Sa, adda kowa ya yi arba da fuskar sulaina sai mamaki ya kamashi ,


Yaslir kuwa bai san sa,adda ya ruga izuwa inda take ba ya kura mata idanu hawaye na zuba daga fuskar sa


Nan take ita ma Sunaila kwalla ta zubo mata


Bakomai ne ya sanya hakan ba sai domin a yanzu ne yaslir ya tabbatar da zargin sa cewa Sunaila ita masoyiyar sa gimbiya salimat


Kawai sai suka rungume juna cikin matukar farin ciki maral musaltuwa gami da tsantsar soyayya hade da shauin juna,


































Ana cikin wannan hali ne sai kawai akayi arba da boka Dayyubul-Barmas ya bayyana tsulum hannun sa rike da wata zabgegiyar takobi ta haske mai matukar kyawu ba wata ba ce takobin ba face TAKOBIN AUKAKA


Abinda basu sani ba shine. A lokacin da yaji dukkan su sun karbi addanin Musulunci sai ya faki idanun su ya bace yaje ya haa kai da sarki Hamras mai gidan su aljani Huruful-labarus, da tsohuwa zahira wacce sarki Hamras ya shiga gidan ta a cikin wannan daji a lokacin da ya fito farautar shamsuddin ,


Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su shamsuddin da su boka Dayyubul-Barmas,


A lokaci guda boka Dayyubul-Barmas,sarki Hamras ,tsohuwa zahira suka yi kukan kura suka afkawa shamsuddin da azababban yai mai matukar firgici da tashin hankali,


Dakyar shamsuddin ya hallaka su duka bisa taimakon Ubangiji dukkan su sukayi mutuwar hulakanci


Tabbas da ace mutum yana wannan waje zai ga yadda gawar boka Dayyubul-Barmas ta hulakanta dole ne takaici ya kamasa bisa ganin yadda duk wahalar da boka Dayyubul-Barmas yasha abaya gashi ta tashi a banza yayi mutuwar asara


Tabbas rayuwar kafirci wahala ce kuma arasa ce


Amma shamsuddin yasha wahala tamkar ransa zai fita,


Koda su aljani Huruful-labarus suka ga abinda ya faru da mai gidan su sarki Hamras da kuma irin abubuwan al,ajabi da shamsuddin yayi sai nan take suka bayar da gaskiya da Ubangiji suka amshi kalmar shahada,


Batare bata lokaci ba jarumi shamsuddin ya auki TAKOBIN AUKAKA ya tofa mata Ayatul- kursiyyu take takobin ta canza launi kuma rubutun sunayen fiyayyan halitta annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama dake jikin takobin suka fito raau,


Shamsuddin ya dubi su lasmirat yace" waannan sunaye su ne suka bawa su Boka Dayyubul-Barmas nasara akai na har nasha bakar wahala,


Haia duk wanda yayi rigo da kamun kafa da mai sunan wato annabin rahama s,a,w zai samu nasara. A komi nasa koda kuwa kafuri ne Allah zai jinkirin ta masa na wani lokaci kafin na kamashi


Koda jin wannan jawabi daga bakin shamsuddin sai kowa ya sake jin kaunar shugaban halitta ta arsu a zuciyar sa ,


Batare da wani bata lokaci ba su aljani Huzmal suka sake aukar su shamsuddin aka nufi hanyar dazata kai su birnin Misra


Bisa mamaki a wannan lokaci sai su Huzmal suka ga cewa karfin gudun nasu ya karu ainun


Abin da basu sani ba shine sirrin hasken MUSULUNCI ne a tare dasu ya basu karfin gudun


Tsawon kwanaki huu aka auka a wannan lokaci bisa taimakon Ubangijin halitta aka iso birnin Misra


Nan fa waziri ukashat da jama'ar birnin suka fito tarar su sarauniya lasmirat da tawagar ta


Bayan an sauke su an haa liyafar Abinci da abin shaye shaye nau'i daban daban,


Take kowa ya shiga kimtsa cikin sa ana fira cikin nishai


Su ma su Aljani Huzmal sai akawo musu tasu liyafar abisa wadannsu manyan tukwane dake auke da farfesun naman rakuma da shanu


Nan fa suka fara tanar baki suna rafka koma,


Al'amarin da ya sanya har dariya ta subuce wa yaslir da Sunaila kenan bisa ganin aljanu nayin kalace,


Bayan kowa ya samu nutsuwa ne waziri ukashat yakashe labarin abinda yafaru bayan tafiyar lasmirat ya zayyanewa lasmirat daga farko har karshe,


Da abinda yafaru tsakanin su da wannan dodo daya bayyana a fada


Batare da bata lokaci ita lasmirat ta shiga bawa jama'a labarin tafiyar su da abinda yafaru tsakanin su da shamsuddin da abubuwan al,ajabi da ya nuna


Sa,adda jama'a sukaji wannan labari sai suka cika da inkin al'ajabi kuma suka ce tabbas munyi imani da Ubangijin jarumi shamsuddin take sarauniya ta biya kalmar shahada


Dubban miliyoyin jama'ar ta suka amsa,


Sai da aka nako guda shamsuddin na koyar da jama'a yadda ake gudanar da ibada kuma yana jinyar raunukan dake jikin sa


Sannan aka shiga shagalin bikin aurin auren sarauniya lasmirat da shamsuddin, yaslir da Sunaila,


Bai daga sassan duniya sun halarci taron bikin


Akayi shagalin da ba,a taba yin kamar sa ba


Tun daga wannan rana HASKEN MUSULUNCI ya mamaye ko ina arzikin birnin Misra ya kara bunkasa


Bisa dole sarakunan dake nahiyar suka dunga zuwa da kansu suka karbar addinin Musulunci,


Jarumi shamsuddin yazo sabon Sarki birnin Misra,jarumi yaslir yazamo shugaban majalisar sarki,


Musulunci ya cigaba da bunasa.


Karshe
Alhamdulillah
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment