Reading TAKOBIN DAUKAKA Chapter 5 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan buzun sa ya cigaba da gudanar da ibadar sa, lasmirat ta koma wajen abokan tafiyar ta,


Sai da aka kwana biyu a wannan waje aljani Huzmal yayi jinyar Fuka fukan sa su yaslir suka samu karfin jikin su sannan aka cigaba da tafiya


A halin yanzu tafiya ta canza daga tawaga ɗaya zuwa biyu wato sarauniya lasmirat da su aljani Huruful-labarus da jarumi shamsuddin


Maimakon a wannan karon a hau bisa aljani Huzmal sai shamsuddin ya ce kowa ya hau ɗaya daga yaran aljani Huruful-labarus bisa izinin Ubangiji ɗayan su bazai saɓa daga Umarnin da aka yi masa ba,


Da yake a wannan lokaci da aka fara tafiya da hasken rana ne,


Lokacin da duhun dare yafara kawo kai sai shamsuddin yayi umarni aka yada zango


Take aljanu shida dake ɗauke da, yaslir,Sunaila, Dayyubul-Barmas, lasmirat da shamsuddin suka saki manyan fuka fukan su suka sauka a turba,


Ana sauka aka kafa tantuna bayan an kafa ne sarauniya lasmirat ta shiga tanti ɗaya tare da sunaila,


Boka Dayyubul-Barmas da yaslir, shamsuddin sai ya shiga nasa shi kaɗai


Aljani Huzmal yana tsaye bisa bakin kofar tantin su boka Dayyubul-Barmas, su aljani Huruful-labarus kuwa suka karkasu izuwa kowace kusurwa a dajin domin tabbatar da cikekken tsaro,


A cikin tantin sarauniya lasmirat kuwa bayan sun kammala kalaci ita da sunaila,


Sai lasmirat ta kwanta Bisa kan gadon ta domin ta samu rintsawa amma duk sa,adda ta rufe idanun ta sai taga babu abinda take gani face fuskar jarumi shamsuddin yana yi mata murmushi,


A wannan lokaci tuni Sunaila ta fara sharar barci har da minshari,


Haka dai lasmirat takasance a cikin wannan hali har barci yayi awon gaba da ita,


Tabbas lasmirat ta kamu da matsananciyar soyayyar wacce bata taɓa tsammanin zata shiga ba,


Tabbas da ace jarumi shamsuddin zai zaɓeni a matsayin a matsayin abokiyar rayuwar sa


Tabbas zan iya hakura da mulkina dukiya dama komai da mallaka domin na samu soyayyar sa ,


Kamar yadda ya wakana a masauki su lasmirat haka al'amarin yakasance a masaukin su yaslir


Ina da bayan sun kammala kalaci sai boka Dayyubul-Barmas ya zira hannun sa a aljihun rigar sa ya ɗauko madubin tsafin sa ya shiga gudanar da bincike bisa halarar tsafin sa.


Shi kuwa shamsuddin tun Kafin ya shiga tantin ya ɗaura alwala yana shiga ya dauko dabino da ruwan sa a cikin salka ya ɗan kimtsa cikin sa,


Sannan ya shimfida buzun sa ya shiga gudanar da Sallah, batare da kalli abincin da su lasmirat suka kawo masa ba,


Amma a ɓangaren su aljani Huruful-labarus kuwa suna cikin yin rangadi a tsakanin tantunan ne sai wani ɗaya daga cikin yaransa .mai suna Barbusa ya dubi abokin sa yace "yakai saltir wai yanzu haka zamu zauna muna ji muna gani wannan yaro shamsuddin yana juya mu tamkar yana sarrafa waina (masa) a cikin yanda


Me zai hana bazamu shammace su ba mu hallaka su mu kama gaban mu,


Baka tsoron mai girma Hamras zai aiko da wata musiba ta hallaka mu,


Koda jin wannan batu sai idanuwan saltir suka zazzaro ya dubi saltir cikin alamun tsananin tsoro yace" A kul ɗin ka yakai aboki na kayi sani cewa tun ina yaro karami mahaifina ya gargaɗeni akan irin waɗannan mutane ma'abota addinin musulunci yace a halin yanzu a duniya babu hatsabibai kamar su


Kafin saltir ya gama rufe bakin sa sai kawai su kaji wani sanyi gami daddaɗar iska ta mamaye wajen kafin kace me


Gaba ɗayan su sun bungire kasa sun fara sharar barci har da minshari,


Sarauniya lasmirat, Sunaila da yaslir suma nauyin barcin su ya karu ainun,


Kuma wani irin gurnani mai ban tsoro ya mamaye wajen baki ɗaya.


Sa'adda wannan iska mai ɗan karan daɗi ta bugar dasu aljani Huruful-labarus, tare dasu sarauniya lasmirat suka kama barci mai nauyin gaske kuma wani gurnani na mamaye wajen sai,


Kwatsam bazato babu tsammani sai aljani Hafsul-Habarus ya bayyana a wajen,


Yayin da yayi arba dasu Huruful-labarus sai ya cika da matukar farin ciki kawai sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta,


Sai da yayi dariyar ta ishe sa sannan ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa,


Kawai sai ya miƙa gabza gabzan hannayen sa domin ya ɗauko su aljani Huruful-labarus,


Yayin da rage saura kamu goma hannayen sa su isa sai wani mutum ya bayyana gaban sa tsulum,


Ba wani bane face jarumi shamsuddin,


Hafsul-Habarus ya ja hannayen sa baya ya dubi shamsuddin cikin tsananin fushi yana mai daka masa tsawa mai kama da saukar aradu


Nan take bishiyoyin dake dajin suka dunga karairayewa suna zube ƙasa, duwatsu suka dunga bindiga suna farfashewa, kuma su lasmirat suka farfaɗo daga dogon barcin da suke yi suka fito daga cikin tantunan su a firgice suna masu zare makaman su,


Sa'adda sarauniya lasmirat, Dayyubul-Barmas, yaslir, Sunaila, Huzmal, aljani Huruful-labarus da yaran sa sukayi arba da aljani Hafsul-Habarus sai suka firgice suka zube kasa,


Sunaila, yaslir,da Huzmal suna masu sakin fitsari a wando saboda tsananin firgici,


Shi kansa boka Dayyubul-Barmas a matukar firgice yake,


Nan take a lokaci guda aljani Huruful-labarus ya tsuke bakin sa ya murtuke fuska,


Take komai na dajin ya samu dai dai tuwa


Cikin Wata irin kakkausar murya mai kama da kwaran kwatsa Yace"yakai wannan bil'adama ma'abocin tsaurin idanu shin wane ne kai dazaka hanani zartar da umarnin shugaba mai duniya sarki Hamras,


Yi maza ka amsa mini waɗannan tambayoyi kafin na ganar dakai kuskuren ka,


Sa'adda shamsuddin yaji wannan batu daga bakin aljani Hafsul-Habarus sai ya yi gyaran murya yace" yakai wannan mushriki makiyin Allah kayi sani cewa babu wani mai daraja face yakasance bawan Ubangijin musulunci mahalicci


Abin da nake so dakai shi ne ka kadaina bautawa wanin Allah ka dawo izuwa TAFARKIN TSIRA,


Wato addanin Musulunci,idan kuwa kaƙi yanzun nan zan roƙi Ubangiji na ya bani nasara na hallaka ka,


Koda jin wannan batu daga bakin shamsuddin sai Hafsul-Habarus ya fusata ainun, idanuwan sa suka kaɗa sukayi jajur!


Saboda fushi har wani irin tiririn bakin hayaƙi na fita daga kofofin hancinsa,


Kawai sai Hafsul-Habarus ya zare wani makami a jikin sa,


Shi dai makamin yakasance dogo tamkar mashi, daga saman sa kawunan takobi ne guda biyu ɗaya na zarto mai cako-cako ƙasan kuma ya na da siffa irin ta lauje wanda ido bai taɓa gani ba,


Tabbas wannan makami abin tsoro ga dukkan wanda yayi arba da shi,


Sannan ya taƙarƙare ya kwarara wawan ihu ya ruga izuwa kan shamsuddin,


Koda ganin hakan sai shamsuddin ya dunkule hannayen sa ya ruga kan Hafsul-Habarus aka tari juna aka kacame da azababban yaƙi mai matukar tayar da hankali da ban tsoro,






















































Wohoho Hakika gaskiyar masu iya magana da suka ce,


Ranar bikin gwanaye sai wane da wane ne ke fitowa a taka rawa,


Kuma idan ana babbakar Giwa ba,a jin ƙaurin bera


Tabbas fadan da yafi karfin ka sai ka zamo da kallo,


Hakan ne yafaru da su sarauniya lasmirat,


Ba shiri su lasmirat suka rike tsaye suka runtuma da gudu izuwa cikin dajin , suka laɓe a bayan waɗansu bishiyoyi suka hangen artabun da akeyi tsakanin shamsuddin da Aljani Hafsul-Habarus,


Nan take su jarumi shamsuddin suka tashi hankalin duk wata halitta dake dajin ya kama girgiza kasa ta dunga tsagewa tana zaftarewa bishiyoyi na faɗa wa cikin ta, duwatsu suka dinga murginawa kan juna suna karo.


Wani abin mamaki da yafaru shine, duk yawan hare haren da Hafsul-Habarus ke kaiwa shamsuddin yana samun nasarar zillewa koda sau ɗaya makami bai taɓa jikin sa ba,


Idan kuwa shamsuddin ya naushi wata gaɓa a jikin Hafsul-Habarus sai aji ya kwalla kara,.


Bakomai ne yasanya hakan ba sai domin duk sa'adda shamsuddin ya naushe san sai yaji wajen tamakar an ƙonashi da ruwan zafi yana yi masa raɗaɗi da zugin tsiya,


Al'amarinn da yayi matukar bashi mamaki kenan bisa ganin yadda yakasa samun nasara akan shamsuddin,


Shin wannan wane irin jarumi ne da za,ace na kasa samun nasara akansa alhali koda makami bai riƙe ba , amsar tambayar da Hafsul-Habarus ya kasa bawa kansa kenan,


Kawai ya sake zage damtse yana cigaba da kai Hafsul-Habarus miyagun hare haren babu ƙaƙƙautawa,


Daga can nesa su sarauniya lasmirat na hangen artabun da ake yi tsakanin ZARATAN MAYAKAN biyu,


Sa,adda sukaga yadda Hafsul-Habarus ke yakasa samun nasara akan shamsuddin sai suka cika da matukar mamaki da al,ajabi kuma suka tabbatar da cewa shamsuddin ya cika jarumin kawarai mai karfin Allah na isa.


Nan take sarauniya lasmirat taji soyayyar jarumi shamsuddin takara shiga zuciyar ta,


Ita kanta Sunaila sai taji a cikin ranta cewa i na ma dai ace masoyin ta yana da jarumataka irin ta shamsuddin


Abin da su duka biyun basu sani ba shine tsananin taimakon Ubangiji ne,


Ke ɗawainiya dashi bayin kansa bane,


Sai da shamsuddin da Hafsul-Habarus suka shafe Tsawon sa,a ɗaya da daƙika ɗari biyar suna ɗauki ba daɗi batare Hafsul-Habarus ya samu nasarar lakutar jikin shamsuddin ba,


Nan fa Hafsul-Habarus ya sake fusata ainun ya haɗa da kai bugu da naushi hannu da kafa


Sa,adda shamsuddin ya fahimci cewa wankin hula zai kaishi dare sai ya cigaba da riƙon Allah a zuciyar sa yana mai cewa,


Ya Ubangiji ka taimaki bawan ka mai rauni akan mushirikin bawan ka. Don matsayin annabin ka,


Ai kuwa yana kammala hakan sai shamsuddin ya taƙarƙare ya ƙirɓawa Hafsul-Habarus naushi a ciki,


Saboda karfin naushin sai da cikin Hafsul-Habarus ya yi ƙara fam fam! Tamkar an daki Tanki,


Ya faɗin ƙasa yana murginawa gami da turmutsutsu Cikin sa yana murɗawa,


Kafin yayi wani yunkurin jarumi shamsuddin ya sake ƙirɓa masa wani wawan naushin a cikin sa, take. Cikin nasa yayi bindiga ya fashe tamkar an buga katuwar ganga, kayan cikin sa suka fito waje jini ya dunga tsartuwa yana feshi yana malala a ƙasa tamkar an balle ƙorama,


Sa,adda su sarauniya lasmirat suka ga irin nasarar da shamsuddin ya samu sai suka fito daga inda suke laɓe suna masu yi masa jinjina suna cewa


G ausheka GOGA SHA YAƘI,


SADAUKIN SADAUKAI


Ciwon idanun kananun kwari


JARMAI SHA YAƘI uban maza DODON MAZAJE


Amma boka Dayyubul-Barmas sai ya murtuke fuska tamkar an aiko masa Da sakon mutuwa,


Kafin su kai inda yake gangar jikin sa ta zagwanye ta narke ruwan ya tsotse a cikin ƙasa,


Suna karasowa sai shamsuddin ya dubesu yace fuskar sa cike da annuri yace " Yakamata kowannen ku yaje ya kwanta a samu ishashshan barcin saboda tafiyar dake gaban su,


Koda gama faɗin hakan sai shamsuddin ya juya ya shiga izuwa tantin sa,


Take kowa ya shiga nasa tantin a ka cigaba da barci,


















Acan birnin misra kuwa tun daga ranar da sarauniya lasmirat ta tafi izuwa ɗauko TAKOBIN ƊAUKAKA domin ta samu damar ɗebo ruwan ma'ul-diya'u,


Waziri ukashat ya cigaba da tafiyar da sha,anain mulki bisa tsari da adalci,


Wata rana waziri ukashat na zaune a fada,


Wata kyakkyawar budurwa na zaune a gefen sa na dama cikin ado na keta raini ba wata ba ce face gimbiya Hulaifat yar waziri ukashat,


A gefe guda kuma fadawa ne a zazzzaune bisa shimfiɗu na alfarma


fadar ta cika maƙil ana tafiyar da sha,anin mulki,


Kwatsam bazato babu tsammani sai kawai akaga wani waje ya zabtare a fadar ya rufta izuwa kasa


Kwatsam sai ga wani narkekeken dodo ya fito,


Shi dai wannan dodo yakasance jibgegen basamude ,fuskar sa mummuna ce babu kyan gani


Hannayen sa tafka tafka ne tamkar bishiyar kuka,tafukan kuwa su na da faɗi tamakar faranti, ƙafafuwan sa manya ne tamkar da dutse aka yi su, kirjin sa ya kumburo ya tara kwanji, kofofin hancinsa manya ne idanuwan sa jajawur tamkar garwashi girman kowanne daga cikin su yakai girman lemon zaƙi,


Tabbas wannan dodo ya cika abin tsoro domin babu wani jarumi da zai yi arba dashi face ya firgice


Nan fa yazamana cewa fadar ta kaure da guje-guje gami da ifice-ificen jama'a


Cikin matukar tashin hankali waziri ukashat ya miƙe tsaye zumbur daga kan karagar sa ta mulki yana mai zare zare takobin sa take fadawa da sauran dakarun dake fadar suka yi koyi dashi


Aka fara kallon kallo tsakanin su da dodon,


*****. *****. ****


Kashe gari tunda duku dukun safiya bayan su sarauniya lasmirat sun yi kalaci an kammala shiri tsaf!


Sai kawai kowa ya bisa kan ɗaya daga cikin yaran aljani Huruful-labarus aka cigaba da tafiya domin isa izuwa tsaunin SHAFRAS,


Tafiya kwanaki talatin kaɗai akayi aka iso tsaunin DARUL-SHAFRAS


a iya tsawon wannan tafiya babu abin da ke sanya wa atsayar da tafiya face idan jarumi shamsuddin zai gudanar da ibadar sa,


Inda aka tsaya ɗin yakasance daji ne ma,abocin kwarjini daban tsoro,


Tsakanin su sarauniya lasmirat da inda tsaunin DARUL-SHAFRAS yake ake tazara mai yawa don haka sai suka cika da tsananin mamaki bisa Ganin yadda tsaunin yakasance


Tsaunin DARUL-SHAFRAS yakasance mai matukar tsawo inda ace mutum zai kalle sa daga nesa sai yaga cewa har ya shige cikin gajimare,


Babu wani ɗan itaciya da yayi tsiro a wajen face waɗansu irin duwatsu masu ɗauke da siffofin bil,adama da dodanni masu ban tsoro


Sai da aka shafe tsawon lokaci a cikin wannan hali sai daga bisani boka Dayyubul-Barmas yayi umarni aka tashi aka nufi tsaunin gadan gadan


Nan fa jarumi shamsuddin ya dunga kallon abubuwan kudirar Ubangiji na halittun sa da tajallin sa iri daban daban,


Yayin da aka sauka a tsaunin sai kowa yasha jinin jikinsa kuma hankalin sa ya ɗugunzuma ainun,


Bakomai ne yasanya su hakan sai bisa ganin yadda tsaunin DARUL-SHAFRAS yakasance


Daga sama tsaunin yakasance mai ɗauke da manyan gine gine da aka yi su da zallar duwatsun wuta kirar mutanen farko mai ɗauke da manyan ɗakuna tamkar akwai wata halitta da ta taɓa rayuwa a wajen


Babu wani waje da mutum zai ajiye ƙafar sa face akwai ƙasusuwan bil,adama ko wasu sassa na jikin sa yana duk ta lulluɓe su,alamun dake nuna cewa wata halitta ta daɗe bata ziyarci wajen ba,


A wasu lokutan sai kaga mutum an rataye da igiya har ya zagwanye yazamana kwarangwal,


Babu abin da zai firgita Mutum shine yadda tsaunin DARUL-SHAFRAS yakasance shiru tsit tamkar babu wata halitta a cikin sa domin koda yan kananan tsuntsaye babu,


Nan fa hankalin kowa ya ɗugunzuma ainun, amma bisa mamaki sai kaga shamsuddin bai razana ba


Nan fa su duka raya a ransu cewa shin menene yasanya shamsuddin bai razana da ganin kwarjini tsaunin ba,


Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan


Boka Dayyubul-Barmas ne ya katse shirun da ya wanzu budar baki sannan yayi ajiyar zuciya ya kawo gwaron numfashi yace


"Yaku abokanan tafiyata kuyi sani cewa mun iso tsaunin DARUL-SHAFRAS inda zamu ɗauki ruwan ma'ul Daryalu,


Sai dai kafin hakan ina san na samar daku waɗansu dokoki


Da farko dole ne kowannen ku ya kiyaye amfani da dukkanin wani abu da danganci sihirin tsafi,


Abu na biyu kuwa shine dole ne kada wani ya shiga wani waje face yasanar dani na basa umarni,


























































Yana gama faɗin hakan sai ya juya ya dubi shamsuddin fuskar sa babu annuri tamkar an aiko masa da SAƘON MUTUWA cikin kakkausar murya ya ce " yakai shamsuddin kada ka manta alkawarin dake tsakanin mu dakai na fito rayuwar mu a lokacin da wata musiba ta taso mana muka kasa tseratar da kan mu idan har ka gaza ceto rayuwar mu


Tabbas zamu yanke tafiyar mu daki domin hakan ya tabbatar mana cewa Ubangijin ka ya gaza wajen taimakon ka,


Koda jin wannan batu sai jarumi shamsuddin ya yi murmushi yace"Da yardar Annabi mai daraja Annabi Sallallahu alaihi Wasallama Ubangiji na bazai bani kunya ba,


Dajin hakan sai boka Dayyubul-Barmas ya zare wani makami a jikin sa ya kunna kai izuwa cikin wani falo,


Sarauniya lasmirat, yaslir, Huzmal, Huruful-labarus da yaransa, da Sunaila tana mai gyara rawanin ta suka mara masa baya , jarumi shamsuddin a ƙarshe har yazamana sun basa tazara mai yawa,


Da shigar su izuwa cikin falon sai suka tarar yakasance makeken mai tsawo da faɗi ba'a iya hango ƙarshen sa, sai suka ci-gaba da tafiya suna kallon abubuwan ban al'ajabi iri daban daban


Yar gajeriyar tafiya suka yi suka iso wata ƙasaitacciyar fada,


Fadar an ƙawata ta da mau,ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya,


Ko ina a fadar a tsaftace yake, tunda karagar mulki har na yan majalisa babu kowa akai


Nan fa kowa ya cika da matukar mamaki bisa ganin ƙawatuwar fadar,


Musamman sarauniya lasmirat da take ganin cewa idan aka kwatanta fadar ta da wannan fadar ta tan bakomai ba ce face kango,


Koda koda a tarihi bata taɓa ganin fada mai ƙawatuwa da tsaruwa tamkar wannan fada ba,


Babu abin da yafi bawa su boka Dayyubul-Barmas mamaki kamar yadda aka shirya kayan ciye-ciye da tanɗe-tanɗe a bisa wani kayataccen teburin na azurfa, kamshin abincin ya mamaye fadar baki ɗaya, taimakar an haɗawa wani BASARAKE walima


Nan fa aljani Huzmal da Huruful-labarus suka fara tanɗar baki,har su na dalalar da yawu daga bakin su basu sani ba saboda tsananin kwaɗayi,


Kafin su farga ɗaya daga cikin yaran aljani Huruful-labarus mai suna Barbusa ya ya faki idanun su ya sunkuci wani katon faranti ɗaya mai ɗauke da wani farfesun naman tsuntsu yayi loma ɗaya dashi ya tanɗe bakin sa


Tabbas rashin sani yafi dare duhu inda ace Barbusa yasan abinda zai faru da yayi hakuri da cin wannan naman tsuntsu ya cigaba da dalarar da yawun sa saboda kwaɗayin abincin,


Domin haɗiye abincin nasa keda wuya sai kwatsam aka ga waɗansu jibga jibgan samudawan muridai suna ratsowa daga bangon fadar suna fito wa, hannayen su ɗauke da miyagun makamai, dangin gatari,al'amudi',majaujawa,takobi da mashi,


A dadin su yakai dubu hamsin da ɗoraya, Gaba ɗaya gurnanin muridan ya cika fadar baki ɗaya,


Muridan sun Kasan masu damatsa,suna rafka rafkan kawuna, suna da matukar kwarjini da muni,duk sa'adda dayan su ya ajiye lafceciyar ƙafar sa a fadar sai kaji ƙasa ta amsa saboda karfin takun,


Haƙika waɗannan muridai sun kasance ababan tsoro domin duk da irin dakewar zuciya irin ta Boka Dayyubul-Barmas, lasmirat,Sunaila , yaslir sai suka ɗimauce, tamkar ace ƙyat suka zura da gudu,aljani Huruful-labarus,saltir da Barbusa har sakin gudawa sukayi a wando saboda da firgici,


Shi kansa jarumi shamsuddin a matukar razane yake kawai saboda addu'ar da yake ne yasanya tsoro ya kau daga daga zuriyar sa ,


Nan fa nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su Dayyubul-Barmas da muridan lokacin da muridan suka kammala yi musu kawanya sai suka buɗe wata hanya a tsakiyar su ta yadda mutum goma zasu iya tsaya a jere


Take wani gurnani ya dunga bayyana a hanyar gami da karfin takun sawaye,


Sannu a hankali sautin yana ƙaruwa jim kaɗan sai ga wani narkekeken muridi ya bayyana,


Shin dai muridin yafi sauran girma da kwarjini sannan ya na ɗauke da rigar sarauta a jikin sa alamun dake nuna cewa shine shugaban muridan,


Shugaban muridan ya karewa su Boka Dayyubul-Barmas kallo, kawai sai ya bushe da dariyar mugunta mai kama da haniniyar doki,


Sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da SAKON MUTUWA


Sannan ya buɗe wawaken bakin sa daya fi kama da bakin rijiya saboda girman sa cikin kakkausar murya


" Lalle marhaban da zuwa fadar uban muridai KIRMALU IBN SHAMSHAN,


Yaku wadannan bil'adama kuyi sani cewa yau fiye da shekaru dubu shida babu wata halitta da ta taɓa zuwa tsauni na DARUL-SHAFRAS sai ayi


Na tabbata cewa abinda ya kawo ku baya rasa nasaba da Ruwan ma'ul Hayat


Ina so kuyi sani cewa kun kawo kanku gidan musiba da bala'o'i na rantse da gemun mai girma Baddadul-sihir ɗayan ku bazai sauka kasan wannan tsauni a raye ba,


Domin hakan ya zamo darasi ga bil'adama masu taurin kanki da wauta irin yaƙi,


Koda shugaban muridan duniya KIRMALU IBN SHAMSHAN yazo nan azancen sa Sai ya sake bushe da dariyar mugunta a karo na biyu


Koda can sai ya murtuke fuska kawai sai ya dakawa yaransa tsawa dake nuna su afkawa su boka Dayyubul-Barmas


Take yaran suka ɗauki kansu suna ihu da kururuwa mai firgitar wa


Nan fa ana haduwa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar muni ban tsoro gami da tashin hankali,


























Al'amarin sarki Hamras kuwa tun sa,adda da ya tura hadimin aljanin sa wato Huruful-labarus domin ya ɗauko masa gashin kan sarauniya lasmirat da boka Dayyubul-Barmas sai ya shafe tsawon kwanaki ashirin batare da yaji ɗuriyar su ba


Sai kawai ya nutsa bisa halarar tsafin sa domin yaga abinda ke wakana,


Ai kuwa nan take ya ga dukkanin abinda ya faru tsakanin Huruful-labarus da jarumi shamsuddin, tun daga inda Huruful-labarus ya rusawa su sarauniya lasmirat wannan iska sihiri suka kamu da barci mai nauyin gaske,


Har kawo inda shamsuddin ya samu galaba akan Huruful-labarus a lokacin da suka fafata artabun,


Duk daga farko har karshe ya bayyana a cikin madubin tsafin sa,


Sa,adda Sarki Hamras yaga wannan al'amari a cikin madubin tsafin sa sai ya cika da matukar bakin ciki maral musaltuwa,


Kuma yasha alwashin cewa komai daren dadewa sai ya ɗauki fansa akan jarumi shamsuddin


Kwanaki nabin kwanaki mako nabin mako sai gashi sarki Hamras ya shafe tsawon kwanaki arba'in cif yana da tafiya


A ranar kwana na casa'in ne sarki Hamras yana tafiya a sararin samaniya cikin sauri yana mai keta gajimare cikin matsanancin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya


Yana cikin wannan hali ne yaji gajiya yafara kamashi


Kawai sai ya yanke shawarar ya sauka ya huta idan yaso sai ya cigaba da tafiya,


Koda gama kammala tunanin hakan sai kawai ya shafi wani gurin shafi a damtsen sa na hagu take yayo ƙasa sulu lu lu luh!


Ya dira a bisa turaba tamakar yakasance mai fuka-fuakai


Inda ya sauka yakasance daji mai ɗauke da manyan tsaunuka da bishiyoyi, duwatsu da ƙwazazzabai,


Hakika dajin yatara dukkan wata sifa ta kwarjini


Daga can nesa sai sarki Hamras ya hangi wani kerarran gida kwarya ɗaya jal a dajin


Al'amarin da yayi matukar basa mamaki kenan kuma ya ɗaure masa kai ya ce a cikin ransa


Shin ko wane ne. Mai mallaki wannan gida kawai sai ya yanke shawarar ya shiga izuwa gidan domin yaga ko mene ne a cikin sa


Koda gama yanke shawarar hakan sai kawai ya durfafi gidan gadan gadan


Idan ka ɗauke karar takun sawaye sarki Hamras dake haddasa motsawar busassun ganyayyakin bishiyun da suke zube a ƙasa babu abinda kunne keji


Wannan shi ne a binda ya faru ga sarki Hamras na mai mulkin Daular aljanu,


*****. *****. *****










































Lokacin da aka kacame da azababban yaƙi tsakanin su boka Dayyubul-Barmas da yaran Uban muridan duniya KIRMALU IBN SHAMSHAN


Sai yaƙin yazamo mai matukar firgici daban tsoro


Karar karafniyar ƙarafa ta cika tsaunin Darul SHAFRAS baki ɗaya


Suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama JURIYA DA BAJINTA irin ta JARUMAN DUNIYA


Nan fa su boka Dayyubul-Barmas suka fara gane kuren su domin tsananin zafin naman muridan ya huce tunanin bil,dama


Kai iya hargowar muridan ta isa ta firgita duk wata halitta mai numfashi,


Abangaren jarumi shamsuddin kuwa wani abin mamaki ya faru domin dai gashi a zahiri muridan na kallonsa amma sai ya zamo basa iya ganin ballantana su tunkari inda yake,


Su kansu su boka Dayyubul-Barmas sai da suka cika da matukar mamaki da ganin hakan,


Abin da basu sani ba shine addu'o i da shamsuddin ke karantawa shine ya makantar da idanuwan muridan. Basa iya ganin sa


Sai da aka shafe tsawon dakika ɗari biyar ana fafata artabun babu sassauci


Yazamana cewa su boka Dayyubul-Barmas basa iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kansu kawai.


Al'amarin daya fusata muridan kenan kuma ya basu mamaki,


Domin a iya tsawon wanzuwar su a saman tsaunin Darul SHAFRAS basu taɓa yin gamo da halitta mai karfin damtse tamkar su sarauniya lasmirat,


Koda su kazo nan a tunaninsu sai suka sake zage damtse suna kaiwa mu hare haren bazato


Tabbas masu iya magana na cewa idan kiɗa ya canza dola ne rawa ta canza


Faruwar hakan keda wuya sai ya zama na cewa a wannan lokacin muridan sun fara samun nasarar kaftausu sara a sassan jikin su,


Duk wanda ɗaya daga cikin muridan ya kafta sara sai kaji ya tsandara ihu jini yayi tsartuwa,


Kuma ya kife a kasa yana nishin wahala,


Cikin abinda bai gaza dakika ɗari biyu ba muridan suka zubar da su boka Dayyubul-Barmas kasa babu wanda yake wani kwakkwaran motsi a cikinsu,


Sai nishi kawai suke yi numfashin su na fita sama sama


Koda samun wannan gagarumar nasara sai muridan suka bushe da dariyar mugunta suka shiga buga ƙafafuwan su a kasa,


Nan take sautin ɗariyar yayi sanadin sumewar su boka Dayyubul-Barmas,


A lokaci guda tamkar haɗin baki muridan suka tsuke bakunan su tamkar an aiko musu da WASIKAR MUTUWA kai kace basu taɓa dariya ba tunda Allah ya halicce su,


Sarkin muridan duniya KIRMALU IBN SHAMSHAN ya sake ratso wannan hanya ta tsakiyar yaran sa ya taka da kafafafun sa har izuwa inda su sarauniya lasmirat ke kwance,


Yaran sa nayi masa kirari suna cewa


Gaisheka KIRMALU mai duniya


Hadari sa gaban ka inda kake so!


Daji kake ba,a yi maka ƙyaure koda mahaukacin kafinta,


Kai gajimare mai zubar da ruwan musiba da bala'o'i


Kai ne. SARKIN SADAUKAI na duniya,


Sa,adda uban muridai KIRMALU yaji kirarin

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment