Reading JIHADI Chapter 6 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya auri wannan
yarinyar ‘yar almajiri saboda ko ni ne ba zan bari ta
wuce ni ba”.
115

jihadi
Koda jin haka sai sarki lamras ya yi
murmushi yace “Amma ba don kyaunta ya aure ta
ba an ce saboda kawai zata iya bashi labaru ne masu
daxi waxanda za su sa hankalinsa ya kwanta ya
daina hauka da shirme, abin tambaya a nan shi ne a
ina wannan yarinya zata iya samo labarai masu daxi,
kuma masu ban al’ajabin da za su iya saita wannan
mahaukacin sarki?”
Koda gama faxin hakan sai ga sarki
masrud tare da amaryarsa sun iso daf da sarki
lamras,kawai sai sarki masrud ya dubi sarki Lamras
yace.
“Na yi murna da ganinka a wannan biki a
zatona ba zaka zo ba saboda laifin da na yi maka
sa’adda muka haxu a bikin naxin sarautar birnin
sin”.
Koda jin haka sai sarki lamras ya kama
yaqe gami da murmushin dole muryarsa na rawa
yace.
“Haba ya kai sarkin sarakuna ai ban isa
na qi amsa gayyatar bikinka ba”.
Ita kuwa Muzainat sai ta dube shi tace
“Zaka sha mamaki idan ka ji irin labarum da zan
baiwa sarki daga daren yau, zaka ji daga bakinsa”.
116

jihadi
Koda jin wannan batu sai jikin sarki
lamras ya kama tsuma saboda tsananin mamaki
gami da razana.
Daga nan suka yi gaba abinsu haka dai
aka ci gaba da gudanar liyafar bikin na su.
Har tsawon wani lokaci kafin aka
kammala sarki masrud da amaryasa suka wuce cikin.
Da shigarsu sai ta fahimci kan sarki ya
fara ciwo nan da nan idanunsa suka juye ya fara
tangaxi.
Koda ganin haka sai ta fahimci cewa
lallai ciwon sarki ne zai tashi a daidai wannan
lokacin maimakon ta ji tsoro ta nisanta da shi sai ta
janyo shi jikinta ta shiga yi masa raxa a kunne tana
mai cewa.
“Ya kai wannan sarki mai daraja ka yi
sani cewa an tava yin wani gagarumin sarki a birnin
kisra wanda ya shekara xari da ashirin akan karagar
mulki batare da ya tava fuskantar wata matsala ba a
rayuwarsa amma a karon banza aka rabashi da mulki
yana ji yana gani da qarfinsa da lafiyarsa ya dawo
bawan sarkin da ya hau karagar alhalin da shi sabon
sarkin ya kasance bawansa kuma ko kaxan ba shi da
wata alaqa da gidan sarautar”.
117

jihadi
Koda jin wannan batu sai sarki masrud
ya ji kansa ya wattsake take kuma ya ji kansa ya
daina ciwo don haka sai ya dubi Muzainat cikin
tsananin zaquwa yace, ta yaya wannan al’amari ya
faru, maza ki bani wannan labari yake tauraruwar
taurari.
Sa’adda Muzainat taga sarki masrud ya
zaqu da son jin wannan labarin sai ta qyalqyale da
dariya tace.
“Ai kuwa akwai xinbin darasi a cikin
wannan labarin kuma gashi yanzu dare ya soma yi,
ina ganin har gari ya waye ba zan iya gama baka shi
ba”.
Da jin haka sai jikin sarki masrud ya
kama tsuma zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata
qone, kawai sai ya zare takobinsa ya dakawa
Muzainat tsawa yace.
“Maza ki ci gaba da ba ni labarin da kika
soma ko kuma yanzun na sare miki kai”.
Koda jin haka sai Muzainat ta dubi sarki
masrud cikin alamun tsoro tace.“Kwantar da
hankalinka ya kai mijina ai yanzu nan zan ci gaba da
baka wannan labarin” Muzainat ta yi doguwar ajiyar
numfashi sannan tace.
118

jihadi
“Wannnan abinda na karanta maka shi ba
komai bane facce hanyar tsira, wanda addinin
gaskiya ya zo da shi, ta hannun manzo mu Annabi
Muhammad (s.a.w) shi ne alqur’ani littafin daya fi
komai daraja da qima da xaukaka. Qissar dana baka
ta Anabi Musa ce da fir’auna. Ka kuma ji yadda
qarshen sa ya kasance. Don haka kaima matuqar
kana son warkewa duka daga cutarka, haka nan ka
zamo gagabadau na a cikin sarakuna to ka zamo
ma’abocin addinin”.
Koda sarki masrud ya ji haka sai ya yi
murmushi, bai ce mata komai ba ya nemi gefe guda
ya kwanta. Bai jima da kwanciya ba bacci ya xauke
shi. Washe gari da safe sarki ya tashi cikin qoshin
lafiya. Amma duk da haka sai yace Muzainat ta qara
karanta masa wani vari na littafin nan ta sake
karanta masa. Bayan ta gama yace mata zai fita fada
don haka ta shirya tare za su fita.
Nan ya shirya ya fita cikin taqama ta izza
da isa, jama’a suka cika da mamakin ganin sarki ya
fito cikin qoshin lafiya, nan aka shiga murna. Daga
nan ya saka aka tara masa mutane haka yasa aka
kirawo masa ‘Yarsa Gimbiya Zuhairat ya kwashe
labarin duk abinda ya faru ya sanar musu. Ya kuma
119

jihadi
tabbatar musu cewar shi ya aminta kuma daga yau
ya zamo ma’abocin musulunci.
Gimbiya Zuhairat ta dubi Muzainat cike
da mamaki “Wanne sihiri ki ka yiwa mahaifina?” Ta
yi murmushi kafin tace mata.
“Nima kakana ne ya bar mun littafin
hikayoyi, a bayan na gama karance shi sai a qarshe
yace mun duk wannan labarin, su zame mun tsani na
shiga addini tsira shi ne addinin musulunci. Don
haka sai na saka aka riqa mun bincike akansa har
Allah ya haxani da mujaddadi Salhif shi ya ganar
dani abinda ban sani ba” Koda jin haka sai Gimbiya
Zuhairat ta yi murmushi tace mata.
“Nima na jima da amsar addinin
musulunci, tun ranar da mahaifina ya bani labarin
Barde Barhuzu da Jarumi Nusurul Ashman da
Gimbiya Ramlatul Auliya. Daga lokacin kuma na ke
roqon Allah ya ganar da mahaifina gaskiya, na
godewa Allah daya bayyana mana gaskiya”.
Nan jama’a suma suka amsa da cewar
sun ji sun aminta sun amshi addinin gaskiya.
Masha Allahu
QARSHE

120

jihadi

121


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment