Reading JIHADI Chapter 3 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi magana sai gunki burata ya tari
numfashinta yace mata.
“Yake Gimbiya zuhaira ki koma gida cikin
kwanciyar hankali ki sa ni cewar har abada babu
wani wanda ya isa ya yi mulkin qasar nan idan ba ke
ba. Kuma babu wanda ya isa ya cutar dake matuqar
kina cikin gidan sarauta. Tabbas mafarkin da kika yi
akan yarinya muzainat gaskiya ne amman za mu yi
amfani da qarfin iko mu sauya qaddara.
Ki yi sa ni cewar bamu bar yarinyar ta zauna
da ku ba sai don yarinyar tana xauke da wata babbar
baiwa ta musamman, wanda qasar nan da jama’arta
za su amfana, kuma ita zata taimaka miki wajen
xauko bulalar tsafi wacce da ita za ki iya mulka
duniya.
Don haka bana son jin wani uzuri daga
bakin ki ko kuma wani abu kawai abinda nake so
dake ki tashi ki koma cikin gidan sarauta, ki kuma
47

jihadi
kwantar da hankalinki, don haka maza ki koma tun
kafin sarki ya kai ziyarar bazata cikin turakarki idan
ya samu bakya nan hakan zai kawo muku savani,
saboda nan da kamar rabin awa zai farka daga barci
kuma yana farkawa ke za ki faxo masa a cikin rai,
domin da fargabarki ya kwana”.
Koda ta ji abinda gunki burata yace, sai
zuciyar Gimbiya zuhaira ta xan yi sanyi ta samu
nutsuwa da kwanciyar hankali don haka ta kuma yin
sujada a gaban gunki burata tana mai yi masa godiya
akan wannan taimakon daya kawo mata, har zata
miqe sai ta ji gunki burata yace mata.
“Yana da kyau ki san dalilin daya saka
babanki sarki masrud ya kawo yarinya muzainat. Ba
komai bane sai don ci gabanki domin kwana nan zai
haxaki da ita ku yi tafiya mai muhimmanci domin
zuwa xauko bulalar tsafi wacce da ita za ki iya juya
duniya a tafin hannunki.
Ki yi sani Gimbiya zuhaira ke kaxai ba ki
isa ki xauko bulalar tsafi ba dole sai da taimakon
yarinya muzainat, hasali ma jininta za a zuba a
ramin akwatin baqin qarfe da aka rufeta idan jinin
ya shiga shi ne akwatin zai buxe. Kuma ita kaxai ce
za ta iya xauko bulalar daga cikin akwatin” Gimbiya
zuhaira ta yi jim zuwa wani lokaci sannan tace.
48

jihadi
“Wai mene ne amfanin wannan bulalar
tsafin a gare ni?”
Gunki burara ya qyalqyale da dariya.
“Yaro bai san wuta ba sai ya taka, ai
matuqar ba ki mallaki bulalar tsafi ba to tabbas ba za
ki mulki qasarki ba, ita bulalar tsafi duk wanda kika
doka da ita walau mutum ko aljani to take zai kama
da wuta ya qone, shin boka kanzul bai ba ki labarin
shu’umin matsafi marganu ba? Bokan daya samar
da wannan bulalar tsafi” Ta gyaxa kai.
“Ya ba ni labarinsa”.
“To ita bulalar akwai wani sirri da duk
duniya babu wanda ya sa ni sai ni, idan kika mallaki
bulala duk wani kangararen aljani za ki sarafa shi,
haka nan duk sanda kika jijjiga bulalar kika kai duka
da ita, to sai wani bala’in ya faru a wata qasa. Haka
nan duk sanda kika xauko bulalar tsafi to sai wani
mashahurin attajiri ko sarki ya mutu” idanun
Gimbiya zuhaira ya fito cikin kaxuwa.
“Kenan idan na mallaketa zan halaka
yarinya muzainat?”.
“Shan ruwa ya fi shi wahala”.
Wannan amsar ba qaramin daxi ta yiwa
Gimbiya zuhaira ba, nan ta koma ta qara zubewa
tana yiwa gunki burata godiya daga nan ta fito daga
49

jihadi
cikin wajen bautar tana zuwa ta kama dokinta ta
xare ta zaburi dokin ta nufi hanyar da zata kaita
cikin gidan sarauta, tana mai gaggawa tun kafin
sarki ya farka daga barcin daya xauke shi.
Cikin sa’a kuwa ta shiga cikin gidan sarauta
kai tsaye ta shiga turakarta ta haye kan gado ta
kwanta. Tana janyo mayafi da zumar rufe jikinta
saboda tsananin sanyi da yake busawa sai kawai ta ji
an turo qofar xakin nata hakan yasa ta yi saurin
runtse idanunta ta yi kamar barci take yi.
Sarki masrud ya shiga cikin xakin yana
shiga ya murxa fitila xakin ta kama xakin ya cika da
haske ya qurawa Gimbiya zuhaira idanu yana
kallonta tana kwance tana faman sharar barci, ba
komai ya saka ya qura mata idanu ba face yana son
ya gano ko yauma ta fita daga cikin turakarta domin
zuwa biyan buqatarta na kashe yarinya muzainat.
Sai daya qarewa xakin kallo tsaf sannan ya
zo ya zauna a kusa da ita a gefen gadon, ya qara
qura mata idanu yana son ganin idanunta sun motsa
ko yayane ya gane cewa ba barci take yi ba amman
sai yaga idanunta sun qi motsawa hakan ya saka
sarki masrud ya yi murmushi ya tashi da zumar ya
fita daga cikin xakin.
50

jihadi
Bisa tsautsayi sai hannunsa ya tava wani
kofin gilas dake kan wani tebur dake daf da ita take
kofin ya faxi qasa ya fashe. Qarar fashewar kofin
yasa cikin sauri ta tashi cikin tsananin zafin nama ta
zare takobinta, ko da suka haxa idanu da sarki sai
tayi qoqarin yin murmushi.
Ganin haka yasa ya koma da baya ya zauna
a kusa da ita ganin haka itama ta maida tatta takobin
cikin kubenta ta gyara zama tana mai yin hamma
alamar ya tasheta daga barci mai nauyi sarki masrud
ya kalli kayan jikinta cike da mamaki yace mata.
“Ya ke ‘yarta meye dalilinki daya saka baki
cire kayan da suke jikinki kin saka kayan barci ba?”
Koda jin haka sai Gimbiya zuhaira ta yi murmushi
saboda ta gane cewa sarki ya yi mata wannan
tambayar saboda yana zarginta akan ta fita cikin
wannan daren hakan yasa ya yi mata wannan
tambayar.
Ta kali sarki tana mai bashi amsa da cewar.
“Ya kai Abbana ka sa ni cewar saboda raina
a vace yake na kwanta a haka ba tare dana sani ba”
Jin maganar data faxa yasa ya yi murmushi kafin
yace mata.
“Nasan haka zata faru, hakan yasa nake
kuma tausasa zuciyarki kuma yake ‘yarta ina kuma
51

jihadi
neman alfarma a wajenki da ki min alfarma dana
nema a wajenki...” Kafin sarki ya rufe bakinsa sai ta
saka hannu ta rufe masa bakinsa,tana kallonsa cikin
murmushi tace.
“Na yi maka alqawari zan yi duk abinda ka
umarce ni dana yi maka, amma kuma nima ina son
ka cima min dokokin dana nema a wajenka, suna
nan ko kuma ba za su samu ba?” Koda jin haka sai
sarki ya yi murmushi tare kuma da saukar da wata
ajiyar zuciya yace mata.
“Tabbas dokokin sun yi tsauri sosai amman
saboda ki samu nutsuwa akan yarinya muzainat na
yarda zan kafa mata wannan dokokin da kika faxa”
Koda jin haka sai Gimbiya zuhaira ta rungume sarki
masrud cikin tsananin farin ciki tana mai yi masa
godiya akan haka, zuwa wani lokaci sai ta janye
jikinta daga cikin nashi tana mai cewa da shi.
“Tabbas yanzu hankalina ya kwanta saboda
haka ba ni da wata buqata yanzu a wajenka face
guda xaya jal” Cikin matuqar mamaki sarki masrud
ya dubi Gimbiya zuhaira.
“Wacce buqata ta rage miki a cikin wannan
duniyar wacce ban san da ita ba?”
“Ina son ka haxani da dakarun da za su je
nemo Abu salhif sannan kuma ka yi min izinin zuwa
52

jihadi
xauko bulalar tsafi wacce matsafi marganu ya samar
nasan kana da tarihinta” Ai kuwa sarki masrud yana
jin haka sai ya soma gyaxa kai cikin tsananin takaici
da kuma kaxuwa da damuwa data mamaye masa
fuska.
“Ba zan yi wannan ganganci ba irin wanda
barde Barhazu ya yi ba wanda yayi asara guda biyu
ya zamana bashi ga tsuntsu kuma bashi ga tarko.
Saboda tabbas idan na barki kika tafi farautar wanan
maqiyin nawa da kuma xauko bulalar tsafi, tabbas
nasan sai na yi nadama irin wacce na yi akan
sadauki Barhuza” Koda jin haka sai Gimbiya
zuhaira tace masa.
“Wane kuma sadauki Barhuza?” Sarki
masrud ya yi murmushi lokaci xaya kuma ya saukar
da murmushi.
“Wannan labari ne mai tsayi, amman kuma
zan datse shi na baki shi a gajarce, don haka ki yi sa
ni cewar koda za ki tafi nemo Abu salhif da kuma
xauko bulalar tsafi ba yanzu ba sai nan da shekaru
ashirin masu zuwa” Gimbiya zuhaira ta dubi
mahaifinta cikin tsananin kaxuwa.

53

jihadi

H

JIHADI 3
ar zuwa wani xan lokaci Gimbiya
zuhaira bata yi magana ba, sai zuwa
can ta xago kai tace wa sarki
masrud.
“Amma kuma me yasa ba zaka barni na tafi
neman su ba sai nan da shekara ashirin?” Sarki
masrud ya yi murmushi.
“Kar ki damu nan gaba zan faxa miki
daliliin faruwa hakan amma yanzu bara na baki
kaxan daga cikin labarin dana ce zan ba ki”.
‘Sadauki Barhuzu ya kasance sarkin yaqin
birnin sin wanda ya ci amanar sarki sa saboda ya
mallaki ‘yar shi ya kuma raba shi da karagar
mulkinsa bisa wannan dalilin ya sa yaje suke haxa
kai da wasu qungiyoyi ‘yan fashi suka haxa runduna
ta mayaqa ya yo gangami na dakaru suka taho qasar
sin da zumar su yaqi sarki baharu zaman.
Koda runduna guda biyu suka haxu a filin
fama sai sarki baharu zaman ya dunga daka masa
harara gami da yi masa wani mugun kallo wanda
yake nuna tsantsar qiyayya wanda nan take fuskar
sarki baharu zaman ta kama yin yatsine.
Yayin da barhuza ya kuma matsowa kusa
da sarki baharu zaman ya kuma matsowa kusa da shi
54

jihadi
hat takai tazarar da take tsakaninsu bata wuce taku
ashirin ba sai barhuza ya tsaya cak a wajen da yake
yana gyara tsayuwar sa irin tsayuwar sarkin daji
wato zaki a dabobin dawa sannan ya kalli sarki
baharu zaman ya taqarqare ya bushe da dariyar
mugunta.
Lokaci xaya kuma ya turvune fuska kamar
an aiko masa da saqo mutuwa ya daka masa tsawa
mai kaxa hantar ciki yace masa.
“Kai tsohon azzalumi ka sani na juma ina
jiran wannan rana da zan huce bautar dana yi a
qarqashin ka na tsawon shekara da shekaru domin
na cika burin zuciyata, babu irin ladabi da kuma
biyayyar haka kuma babu irin bautar da ban maka
ba amma ko kaxan baka tava saka min da alheri ba.
Sai dana kusa rasa raina saboda tsanani da
kuma begen ‘yarka wanda nake fama da shi a cikin
zuciyata amma kuma sai ka qeqashe idanu ka qyale
ni ka kuma yi min wulaqanci saboda na falasa maka
sirrin zuciyata.
To ka sa ni a yau kuma yanzu zan kashe ka
na kuma haye karagarka ta mulki na kuma aure
‘yarka Gimbiya da qarfin tsiya’ Kafin sarki yaqi
55

jihadi
Barhuzu ya kammala rufe bakinsa tuni sarki ya tari
numfashinsa cikin daka masa tsawa yace masa.
“Kai maqaryaci shugaban mayaudara na
duniya ka sa ni cewar koda giwa ta faxi tafi qarfin a
daka mata wawa, kuma ramin kura sai ‘ya ‘yanta,
kuma babban goro sai magogin qarfe ina baka
tabbacin cewar kai dai ba wani ba baka isa ka
kamani da qarfin damtse ba sai dai kuyi min taron
dangi.
Dan haka ina mai yi maka wani alqawari
idan ban kashe ka ba to zan maka wani lahani mai
muni a jikinka wanda da baqin cikinsa za ka shiga
cikin kabarinka idan kuma kana yin musu akan haka
to ka yaqe ni ka gani” A wannan lokacin daman tuni
tsurarun dakarun da suka rage na sarki Baharu
zaman sun saduda sun miqa wuya sun yarda
makamansu an kama su a matsayin fursunan yaqi an
zuba musu sarqoqi qafa da hannayensu.
Sa’ar da Barhuza ya kammala jin wannan
jawabin da sarki Baharu zaman ya yi sai ya bushe da
dariya yace masa.
“Ai wajen da babu qasa nan ake gardamar
kokawa kuma sai kuma an gwada akan san na
qwarai” Yana kammala faxin haka ya kalli dakarun
nasa gaba xayansu yace musu.
56

jihadi
“Tunda dai munci wannan yaqin yanzu
bana buqatar xayanku ya vata makaminsa ko sau
xaya da jinin wani dan haka duk wanda ya taimaka
min akan sarki Baharu zaman to da kaina zan kashe
shi da makami na don haka bana son ganin wani ya
kawo min agaji komai koda kuwa sarki Baharu
zaman zai halakar da ni” Yana kammala faxin
wannan maganar ya xaga takobinsa sama yana mai
riqeta da hannuwansa biyu sannan ya ruga kan sarki
Baharu zaman da gudu yana kwala wani uban ihu.
Ko da ganin haka sai shima sarki Baharu
zmaan shima ya yi xauki zuwa kanshi suna haxuwa
da juna a tsakiya suka kacame da wani azababben
yaqi cikin tsananin fusata.
Nan suka shiga kaiwa juna sara da suka
cikin tsananin zafin nama kamar jikin su babu jini
ko qashi a jikisu ai kuwa suna soma wannan yaqin
sarki Baharu zaman ya cika da mamaki kuma ya
firgita saboda ada sanin da ya yiwa kanshi
jarumtakarsa da kuma iya yaqinsa ya nunka na
Barhuza sau uku amma yanzu sai gashi jarumtakar
shi da kuma bajintar tasa ta kusa zuwa xaya harma
zafin naman Barhuzu yafi na shi kuma qarfin saran
shi da zafin naman shi ya nunka na sarki yakai sau
goma.
57

jihadi
Tun sarki Baharu zaman yana iya kare
saran da Barhuzu yake kai masa har takai ya gajiyar
da shi baya iya karewa har ya maida martani suna
cikin wannan azababen yaqin barhuzu ya xauki
numfashin sarki Baharu zaman ya dake shi da qafar
shi ta hagu.
Saboda qarfin duka da ya yi masa sai daya
yi sama ya faxo qsa da baya yana mai furza da aman
jini na wahala daga bakins a lokacin kuma takobinsa
da take riqe a hannunsa ta suvuce ta faxi qasa. Ya
yunqura zai tashi kafin ya tashi tuni Barhuza ya
daka tsale daga wajen d yake ya dirge a gabanshi ya
kai masa suka da takobinsa a ciki.
Cikin baqin zafin nama sarki Baharu zaman
ya yunqura zai kaucewa daya kai masa da tsini
takobin nasa amman duk da haka sai da takobin
nashi ta soki gefen cikinsa Baharu zaman ya kurma
uban ihu sakamakon mugun zafi da zogi daya ji.
A lokacin xaya jini ya yi tsartuwa daga
gefen cikin nashi amma saboda qarfin hali irin na
tsofafin jarumai sai ya yi wuf ya kama takobinsa
daga jikinsa ya yi wata alkafira daga qasa yana mai
dungurawa zuwa wajen Barhuza.
Kafin Barhuza ya yi wani yunquri tuni
sarki Baharu zaman ya yi wuf ya zaro wata
58

jihadi
sharveviyar wuqa daga cikin kubenta dake gefen
cinyar shi ta hagu yakai wa Barhuza sara a qirji
cikin tsananin zafin nama yaja da baya da zumar
kaucewa saran daya kai masa amma cikin rashin
nasara sai takobin ta sare masa babban xan yatsan
shi na hannu nan take yatsan ya guntule ya faxi qasa.
Hakan data faru ya kuma fusata Barhuza
ainun nan take ya zaro wata takobinsa daga bayan
shi ya haxa makamai guda biyu a hannunsa ya kuma
farma sarki Baharu zaman a karo na biyu yana mai
kai masa sara da suka da qarfinsa yana mai yi masa
mugun nufi.
In banda sarki Baharu zaman yana riqe da
wannan sharveviyar wuqar da tuni Barhuza ya
gididdibashi duk da haka sai da Barhuza ya yi
nasarar yankan jikin sarki Baharu zaman sau uku
wajen ya daddare ya yi rami mai zurfi jini yana
shatata daga ciki, nan take jiri ya soma xaukar sarki
Baharu zaman ya soma tangaxi.
Shi kuma Barhuza duk da babban xan
yatsan nashi ya guntule jini yana zuba amma hakan
bai saka ya nuna alamar cewar ya galabaita ba sai
ma ji daya yi kamar an qara masa qaimi akan na
baya da sarki Baharu zaman yaga jiri yana xibansa
sai ya soma tunanin mafita.
59

jihadi
Kafin ya kammala tunaninsa tuni Barhuza
ya shammace shi a karo na biyu ya kuma saka qafa
ya dake shi a qirji take sarki Baharu zaman ya yi
baya kamar an saka majajjawa an janye shi nan ya yi
sama ya faxo qasa ruf da ciki kuma cikin tsananin
galabaita domin sama-sama numfashin nasa yake
fita.
Barhuza ya rugo da gudu ya zo kanshi ya tsaya
yana kallonsa cikin tsananin wulaqanci ya tofa masa
yawu a fuska cikin wulaqanci sannan ya saka qafa ya
shure wuqar da take hannun sarki Baharu zaman cikin
wulaqanci yake kallonsa lokaci guda kuma ya qyalqyale
da wata dariya mugunta sannan ya soma cewa da shi
cikin nuna taqama da nuna isa.
‘Bana jin zan barka ka kuma ko da sa’o’i goma
numfashi yana matsawa a jikika yanzu nan zan shayar
da qasa jininka na kuma saka kanka a jikin makamina na
shiga da shi har zuwa cikin qasarka na kuma tsire shi a
jikin qofar shiga cikin fadarka har sai kowa na cikin
qasarka ya zo ya ganshi” ya ci gaba da cewa da shi.
“Yanzu ajalinka ya kusa qarewa tunda yana
hannu na kuma ‘yarka gimbiya Ramlatul auliya tana can
a hannun dakaruna a tsare a cikin tanti kaga kenan ina
kashe ka zan wuce da ita cikin gari na kawar da duk
wasu ‘yan majalisarka wanda basa goyon bayana na
kuma xane akan karagar ka na kuma aure Gimbiya
Ramlatul auliya.

60

jihadi
Koda jin haka sai sarki Baharu zaman ya miqe
cikin qarfin hali ya kalli Barhuza ya yi masa murmushin
mugunta sannan yace masa.
“Har abada wannan burin naka da kake son
cikawa ba zai tava cika ba koda bayan raina” Wannan
magana da ya faxa ta qonawa Barhuza rain an take ya
xaga takobinsa sama cikin tsananin zafin nama da zumar
zai sarewa sarki Baharu zaman kai.

Babu zato babu tsamani sai Barhuza ji ya yi
an daki qirjinsa da wani irin gaggarumin qarfi
saboda qarfin dukan sai daya yi baya kamar an
harba kibiya daga cikin baka sannan yaje ya gwara
kanshi da wata bishiya ya faxo qasa tim yana mai
yin aman jini.
Da sauri ya xago idanunsa don ganin
wanda ya yi masa wannan dukan ba kowa ya gani ba
face jarumi Nusurul Ashman wanda ya durgo daga
sama kamar tsuntsu mai fuka-fukai.
Sarki Baharu zaman koda ya xaga kai yaga
jarumi Nusurul Ashman ne ya kawo masa xauki bai
san lokacin daya soma qyalqyala dariya farin ciki ba.
Su kuma dakarun sarkin yaqi Barhuza ko
da suka ga shugabansu yana qasa ya kasa tashi
kuma yana aman jini sai suka tasowa jarumi Nusurul
ashamn gaba xayan su da zumar su yi masa rubdugu
61

jihadi
su gididiba shi yanda wani daga cikin su ba zai samu
tsokar namansa xaya ba.
Ko da jarumi Nusurul ashamn yaga wanna
runduna ta tunkaro shi kawai sai ya qwala kabara ya
tunkare su da gudu tun kafin su qaraso gare shi, ai
kuwa ana haxuwa sai ya kutsa ta cikin su da qarfin
tsiya ya hau su da sara da suka cikin wani irin zafin
nama na ban al’ajabi domin kamar guguwa ko
walqiya haka ya dunga katantanwa yana gididibasu
sai dai kaga jini yana tsiri yana fallatsi da vulvula
daga jikin sassan jikin xan adam yana malala a qasa.
Kawunan dakaru kuwa ya dunga shawagi a
sama kai kace takardu ne akai gutsu-gutsun da su
lokaci qanqani jarumi Nusubul Ashman ya yi wa
wannan dakarun mummuna varna ya kashe kimanin
mutum dubu daga cikinsu.
Don haka idan ka ji ana qi gudu to sa gudu
ne bai zo ba. Ganin irin wannan mummuna varna da
aka yi musu hakan yasa hankalin dakarun Barhuz ya
ta shi matuqa don sun san mummuna varna da ya yi
musu babu makawa idan aka ci gaba da tafiya akan
haka babu shakka zi qarar da su nan da wani xan
lokaci.

62

jihadi
Kuma sun yi imani da cewar aka ci gaba da
tafiya a haka babu shakka zai halakar da su gaba
xayansu duk da mugun yawan da suke da shi.
Shi kuma sarki Baharu zaman wanda yake
kwance ya kasa yin komai tsananin mamaki ne ya
hana shi yin komai. Yana mamakin yanda jarumi
Nusurul Ashman ya samu wannan irin qarfin tunda
yasan baya yin tsafi kuma babu makawa ubangijinsa
shi ne ya bashi wannan qarfin alhalin kuma duk
duniya babu wani addini daya tsana sama da wannan
addinin musulunci amman amman yanzu kuma ba
don ma’abocin musulunci ba da yanzu ya zama
gawa.
Wannan amsar ita sarki Baharu zaman ya
kasa baiwa kanshi hakan yasa ya saka idanu don ci
gaba da kallon yanda zata kasance tsakaninsu.
Koda dakarun Barhuza suka ga za su yi
biyu babu ba za su samu nasara akan Nusurul asham
idan suka tsaya yaqi da shi zai yi nasara akan su sai
suka ja baya suka daina yaqar shi suka koma wajen
shugaban a wajen da yake kwance suka sure shi
suka xora shi akan doki suka juya suka nausa zuwa
cikin daji suna masu yiwa dawakan nasu qaimi kai
kace duniyar za su bari gaba xaya.
63

jihadi
Har Nusurul ashamn ya yunqura zai bi su
don ya qure musu gudu ya kawo qarshen su sai sarki
Baharu zaman ya qwala masa kira yace masa.
“Maza ka je can wajen da suka yada zango
ka xauko min ‘yarta Gimbiya Ramlatul auliya tana
wurin su” Kafin sarki Baharu zaman ya kammala
rufe bakinsa tuni ya daka tsalle ya haye wani doki ya
yi masa qaimi ya nufi wajen da suka kafa sansanin
su.
Yana tunkarar wajen ya hango tsirarun
dakaru suna gadinta tun kafin ya qarasa suka soma
harbor masa kibiya amma duk kibiyar da suka
harbor masa kafin ta qarasa wajen shi sai yasa
takobi ya kaxeta.
Faruwar hakan ba qaramin mamaki ya
baiwa dakarun tsaron ba, hakan yasa cikin gagawa
suka yarda makaman su suka bazama cikin daji suka
bar wajen babu kowa kuma wajen ya yi tsit babu
komai sai tantuna da suka kakkafa sai kuma guzurin
yaqi na makamai da kuma dawakai a xaxxaure.
Cikin hanzari Nusurul asham ya qarasa
tsakiyar sansanin ya yi tirjiya ya sauka daga kan
dokin ya shiga leqawa cikin tantuna sai daya leqa
cikin tantuna bakwai amman bai ganta ba.
64

jihadi
Hakan yasa gwiwarsa ta yi sanyi ya soma
tunanin wata qila maqiya sun xauke Gimbiya
Ramlatul auliya hakan yasa ya juya da baya don
komawa kan dokinsa kawai sai ya ji motsi a wani
tanti dake can gefe xaya hakan yasa ya juya ya ruga
da gudu zuwa tantin daya ji motsin yana shiga ya
samu Ramlatul auliya su uku suna xaure da igiyoyi
a hannunsu da qafaffunsu kuma dukan su an rufe
musu bakunansu.
Cikin sauri da kuma farin ciki Nusurul
Ashman yana zuwa ya soma kwance sauran suka
rungume juna cikin murna ya qarasa wajen Gimbiya
Ramlatul auliya ya kwance mata hannu ta xaga
hannu sama tana yiwa Allah godiya sannan tace
masa.
“Ina labarin maci amana Barhuza” Nusurul
asham yace mata.
“Bani da labarin sa amman na sadu da
mahaifinki a lokacin da sarki yaqi Barhuza ke daf da
samun nasara halaka shi a halin yanzu sarki yaqi
Barhuza da duk dakarun sa sun sha kasha a hannu na
kuma sun tsere zuwa cikin daji bisa taimakon
ubangijin musulunci na baro mahaifinki a can baya
inda aka fafata qazamin yaqi tsakaninsa dana
65

jihadi
dakarun Barhuza tabas mahaifinki zai yi matuqar
farin ciki idn ya sadu dake a yanzu”.
“Wai shin ina labarin hashwan? Shin yabi
muhusin ne izuwa cikin birni don amsar dukiya a
wajen mahaifinki?” Ko dajin wannan tambayar sai
jikin su zaiyan ya yi sanyi, don haka ba tare da vata
lokaci zaiyan ya kwashe duk abinda ya faru ya
faxawa Nusubul ashaman.
Ko dajin haka sai baqin ciki ya turnuqe
Nusurul Ashman ya kalli Gimbiya Ramlatul auliya
da su zaiyan yace.
“Ai sai ki zo mu hanzarta mu koma can
wajen da muka baro sarki Baharu zaman” koda jin
haka sai zuciyar Gimbiya Ramtaul auliya ta buga da
qarfi ta kalli Nurutul ashamn cikin alamun tsoro tace
masa.
“Yazan yarda na koma wajen mahaifina
bayan nasan ya tsani addinin musulunci sama da
komai a wannan duniyar, ni kuma zai iya halakar
dani duk da tsananin qaunata da yake yi” Lokacin
da Nusurul Ashman ya ji haka sai ya yi murmushi
yace mata.
“Ki kwantar da hankalinki yake Gimbiya
Ramlatul auliya nasan mahaifinki ba zai yi yunqurin
cutar da mu ba saboda yaga yanda ubangijin
66

jihadi
musulunci ya bani qarfin kuvutar da shi da jama’ar
qasar daga halaka. Don haka yanzu ya zamar masa
dole a cikin abu biyu ya yi guda xaya kodai ya barni
na tafi dake don nasan idan na barki a hannunsa zai
iya hanaki yin addinin Allah ko kuma idan ya so ya
zauna dake shima ya amshi addinin musulunci”
lokacin da jarumi Nusurul Ashman ya zo nan a
maganar shi sai hankalin Gimbiya Ramlatul auliya
ya xan kwanta kaxan harma ta xan yi masa guntun
murmushi sannan tace masa.
“Shi kenan na yarda zan bika mu koma ga
mahaifina amma sai ka yi min alqawari cewar ba
zaka bari ya cutar da ni ba” Nusurul ashamn ya
maida wa Ramlatul auliya martanin murmushin da
ta yi masa yace mata.
“Na yi miki alqawari ba zan bari
mahaifinki ya cutar da ke ba” Nan suka xunguma
zuwa wajen da Nusurul ashamn ya baro sarki
Baharu zaman suna zuwa kuwa suka tarar da sarki
Baharu zaman a wajen daya baro shi dakaru sun
kewaye shi likitan shi kuma yana kusa da shi yana
sa masa magani a jikin raunikan da aka ji masa.
Koda sarki Baharu zaman ya hango ‘yar shi
Ramlatul auliya tare da jarumi Nusurul asham sai
fuskarsa ta faxaxa zuwa ga murmushi harma ya
67

jihadi
miqe tsaye da zumar ya tare su saboda farin cikin
sake ganinta, cikin sauri Gimbiya Ramlatul auliya ta
rakave a bayan jarumi Nusurul Ashman saboda
rshin yarda da mahaifinta ko da ganin haka sai sarki
Baharu zaman ya kalleta yace mata.
“Yake ‘yarta ki sa ni ba zan tava cutar da
Nusurul ashamn ko kuma ke ba saboda yau naga irin
qarfi da taimakon da ubangijin musulunci yake da
shi saboda ba don shi ba da yanzu sai dai gawata
kuma nasan tabbas Barhuza ba haqura ya yi ba zai
dawo kuma nasan b qaramin shiri zai kuma yo wa
ba.
Kuma zai ci gaba da tunanin hanyar da zai
kuma volo mana dani da kuma ke don ganin ya
samu cikar burinsa. Yanzu dai abinda za’a yi ku zo
mu koma cikin birni mu zaun mu huce gajiya idan
ya so sai mu kuma tattaunawa akan wannan
lamarin” Koda Nusurul Ashman ya ji wannan
maganar sai ya saukar da ajiyar zuciya yace.
“Wannan maganar daka kawo ta yi daidai
amma yanzu ya maganar abokan tafiyata su
Hashwan? Shin ka bashi wannan dukiyar da kace
idan muka kawo maka maganin ciwon hannunka za
ka ba shi?” Sarki Baharu zaman yace masaa.
68

jihadi
“Ai ban ba shi ba cewa na yi ya bari sai
zuwa gobe sakamakon tasowar wannan yaqin daga
wannan lokacin ban san halin da yake ciki ba” Ko
dajin haka sai murna ta kama Nusurul Ashman yace
masa.
“Na yi farin ciki da baka ba shi ba kaga
kenan yanzu ya yi biyu babu ya rasa dukiya ya kuma
rasa abokan tafiya, amman duk da haka akwai
matsala guda xaya, abu mai wuya ne Muhisin ya ci
gaba da zama a cikin qasarka dole ya fito yaga
yadda abu ya wakana kuma dole ya koma can wajen
daya baro su Hashwan.
Yanzu abinda nake so dakai da su Gimbiya
Ramlatul auliya ku koma cikin birni yanzu ni kuma
da Zaiyan ku qyale mu kafawa Muhisin tarko mu
kama shi a hannu domin musan irin hukunci da
zamu yi masa akan cin amanar da ya yi mana na
yunqurin halaka mu”

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment