Reading JIHADI Chapter 5 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akan
wannan farar akwatin sai akwatin ta buxe tamkar an
buxe tsakiya littafi babu komai a cikin akwatin face
wani xanqaramin jan littafi akan bangon littafin an
yi rubutu da baqar tawada mai kauri kamar haka
JIHADI shi dai wannan bango littafin an yi shi ne
daga dutsen zinare, rubutun kuwa da baqin dutsen
92

jihadi
lu’u lu’u aka yi shi sai sheqi da walwali littafin yake
yi.
Muzainat bata san sa’adda sha’awar
littafin ta kamata ba ta zura hannayenta biyu cikin
akwatin ta xauko littafin.
Koda ta fito da littafin daga cikin wannan
farar akwatin sai gaba xaya gumakan dakarun suka
kama tsattsewa suna rushewa tamkar an tsoma alli a
cikin ruwa.
Nan da nan gaba xayansu suka rugurguje
xayansu bai tsira ba.
Al’amarin da ya matuqar baiwa
Muzainat mamaki kenan ita kuwa tsohuwa jarisa sai
ta bushe da dariya farin ciki har da qyaqyatawa
kuma nan take ta rikixe ainahin sufarta ta aljana ta
buxe fukafukanta ta tashi sama tana shawagi a sama
Muzainat tana mai ci gaba da qyalqyala dariyar
murna daga can kuma sai ta sauko qasa ta fuskanci
Muzainat har a sannan bata daina kallon littafin dake
hannunta ba cikin matuqar al’ajabi.
Koda taga jarisa ta dira a gabanta sai tax
ago kai ta dubeta tace “Yake wannan aljana mene ne
dalilin wannan farin ciki naki haka? Me ximbin
yawa?”
93

jihadi
Koda jin wannan tambaya sai aljana
jarisa tace “Ba komai ne ya jefa ni cikin wannan
farin ciki ba face sai yanzun nan na sami ‘yanci da
zan daina zama tare dake, da kuma tsare wannan
littafi na tsawon shekaru ashirin tun kafin a haife
ki,kamar yadda na gaya miki da farko zan yi miki
bayanin komai yanzu.
Kakanki na wajen uwa shi ne mutumin
da yafi kowa sanin labarai na ban al’ajabi waxanda
suka faru a ko ina cikin wannan duniya, domin sai
da ya yi shekaru xari da biyar yana binciko ire-iren
waxannan labarai a cikin madubin tsafinsa.
Don haka duk inda wani abin al’ajabi ya
faru a duniya a ko ina sai ya ganshi sannan ya zauna
ya rubuce labaran da qarfin sihirin tsafi a cikin
kwanaki casa’in da tara da ya kammala wannan
aikin ne ya gyara littafin sosai ya san ya shi a cikin
wannan bangon na zinare da lu’u lu’u ya kawoshi
nan kogon dutsen ya adana a cikin akwatin nan.
Bisa binciken daya yi duk wanda ya
karance gaba xaya labaran dake cikin wannan
littafin walau a fili ko a cikin ransa sai ya samu
mulki gami da xaukaka da babu wani mahaluki da
zai iya samun kamarsa face shi xin ya bar duniya.
94

jihadi
Koda ya gano hakan sai ya sana’anta
wannan farar akwatin wacce bata da murfi ko
mabuxi yayi ta yadda babu abinda zai iya buxeta
face xigon jininsa ko na zuri’arsa.
Ya sani cewa kece kaxai kika rage a
cikin zuri’arsa don haka saboda ke kaxai ya adana
wannan littafin. Ya ke wannan yarinya me sa’a kiyi
sani cewa akwai labarai na ban al’ajabi guda dubu
biyu da xari biyu da ashirin a cikin wannan littafin
kuma a kullum za ki iya karanta kowane labari kina
gama karance labaran su zauna a cikin
qwaqwalwarki tamkar akan takarda aka rubuta da
alqalami.
Karanta sun kuwa zai xauke tsawon
daqiqa casa’in da tara ne kacal idan kina shakka ko
yanzu za ki iya jarrabawa.
Koda jin wannan batu sai Nasimat ta
qyalqyale da dariya tace, “Ai kuwa in dai haka ne
wannan kakan nawa ya cika babban matsafin da
babu kamarsa a wannan zamani.
Aljana jarisa tace “Ai dama hakanne
kuma kece kaxai za ki iya gadarsa sirrin wannan
littafi shi ne kada ki kuskura ki karanta shi a gaban
wani mahaluki face idan kin kaxaita ke kaxai a cikin
xakin ki na barci, don haka dole ne ki kasance kina
95

jihadi
mai ci gaba da voye littafi a cikin wannan akwati ya
zamana cewa kullum kina karantashi sau xaya har
sai kin shafe kwanaki xari uku da sittin kullum kina
karanta labarai bakwai sannan ki kammala shi.
Koda jin wannan batu sai hankalin
Muzainat ya dugunzuma ainun tace.
“Ta yaya zan iya voye wannan littafi da
wannan akwatin ba tare da kowa ya gani ba, kuma
yanzu kina nufin cewa kullum idan ina son na buxe
wannan akwatin sai na yanke jikina jikina na xiga
jinina a kanta?”.
Aljana jarisa tace “Shakka babu sai kin
yi haka amma akwai abin da za ki iya ki sami
babban sirri a cikin al’amarin yadda babu wani
mahaluki walau mutum ko aljan da zai tava
sirrinki,sirrin kuma shi ne za ki iya mayar da
akwatin nan ta zama xan qarami guri da zaki xaure
shi a qugunki ya kasance dare da rana yana jikin ki,
duk sa’adda kika kaxaita a cikin xakinki ya zamana
cewa kina son ki karanta littafin al’ajabi sai ki
kwance gurin ki ajiye shi a gabanki ki xiga masa jini.
Take gurin zai zama kawai sai ke kaxai
kuma akwatin zata buxe kanta ki xauko littafin ki
karanta da zarar kin kammala kin mayar da littafin
96

jihadi
cikin akwatin za ki ga ta rufe kanta, kuma ta sake
rikixewa ta zama qaramin gurin.
Haka za ki yi ta yi har ki samu nasarar
kammala karanta littafi a cikin kwanaki xari uku a
da sittin ki sani cewa daga yau ba ni da sauran alaqa
da ke koda wannan littafi domin dama nib a waiwar
kakanki ce na fi shekara saba’in ina yi masa bauta
bai ‘yanta ni ba albashir xin ‘yanta shi ne na kare
wanna littafi har izuwa lokacin da hannunki zai kai
kansa, gashi kuwa yanzu lokacin ya yi.
Da wannan furuci nake yi miki
bankwana yanzu nan zan tafi izuwa can qarshen
duniya vangaren bangon arewa zan qarasa sauran
rayuwata tare da mijina wanda tun da aka raba mu
tsawon shekaru yake zaune yana faman sharar kuka,
idan na koma gare shin a sami ‘yancina babu wani
boka da ya isa ya sake tsare ni na yi masa bauta,
kuma har izuwa qarshen rayuwata bazan sake
rabuwa da mijina ba, daidai da tsawon kwana xaya”.
Koda gama faxin hakan sai Aljana jarisa
ta yunqura zata tashi sama, amma sai Muzainat ta yi
wuf ta roqo fukafukinta guda xaya tace “Ya za ki
tafi baki gaya mini yadda zan mayar da wannan
akwati xan qaramin guru ba?”
97

jihadi
Koda jin wannan tambaya sai aljana
jarisa ta qyalqyale da dariya tace “Ai na gaya miki
tun xazu tun da dai yanzu kece kaxai a cikin wannan
kogon dutse babu wata halitta mai rai da ke ganinki
ko sauraronki,kawai ki buxe littafin ki karanta
labarai bakwai kina kammala wa sai ki mayar da
littafin cikin akwatin ki rufe za ki ga akwatin da
kanta ta rikixe ta zama gurun.
Gama faxin hakan ke da wuya sai aljana
jarisa ta buxe fukafukanta ta yi sama tana ta
qyalqyala dariya farin ciki kuma ta buxe muryarta
da qarfi tana faxin na sami ‘yanci na samu ‘yanci.
Kafin cikin daqiqa biyar aljana jarisa ta
luluqa a cikin gajimare ta vace vat tamkar bata tava
wanzuwa ba a wajen.
Koda ganin abinda ya faru sai Muzainat
ta dubi gabas da yamma kudu da arewa a cikin
kogon dutsen kuma ta kasa kunnuwa har sai data
tabbatar da cewar babu wnai mahaluki mai rai a
cikin kogon sannan ta buxe littafin na hikayoyin
aljabi ya fara karanta labarin farko.
Koda ta ji irin tsananin daxin labarin da
kuma abubuwan al’ajabin dake cikinsa sai ta ji cewa
ai idan kwana zata yi a tsaye tana karanta shi ba zata
gaji ba.
98

jihadi
Nan da nan a cikin daqiqa kaxan ta gama
karanta labaru bakwai.
Tana gama karanta labari na bakwai sai
littafin ya rufe kansa, Muzainat ta yunqura da nufin
ta sake buxe littafin domin ta ci gaba da karanta shi
amma sai ta ji littafin ya vame! Tamkar qusa aka
kafe shi.
Nan fa ta dage iya qarfinta domin ta
buxe amma sai ta kasa, bisa dole ta haqura ta mayar
da littafin cikin akwatin.
Faruwa haka keda wuya sai farar akwatin
ta rufe kanta sannan ta qanqance ta zama guru xaya
xan qarami cikin farin ciki Muzainat ta xauko gurun
sannan ta xaure shi a qugunta sannna ta ruga da
gudu ta fice daga cikin kogon dutsen.
Daga wannan rana kullum da daddare sai
Muzainat ta shiga cikin wani shago kasuwa wanda
babu wani a cikinsa ta kulle kanta ta kwance
wannan guru daga qugunta ta ajiye shi a gabanta
sannan tasa zabira ta xan yanki xanyatsanta ta
xigawa gurin jini.
Take yake zama wannan farar akwatin ya
buxe ita kuma sai ta xauko littafi hikayoyin al’ajabi
ta karance labarai bakwai a cikinsa. Tana gamawa
99

jihadi
sai ta mayar da littafin cikin akwatin kuwa sai ta
zama guru, Muzainat ta xauke abinta tax aura shi a
qugunta.
**
Yau kwana bakwai ke nan Muzainat tana
yin wannan abun cikin sirri ba tare da kowa ya gani
ba, ko ya ji hatta mahaifinta nata kuwa amma kawai
ranar daya tava hannunta ya ji alamun yanka ya
tambaye ta yadda aka yi ta sami wannan raunika sai
tace da shi ai ta je aikin aikatau ne a wani gidan
attajiri aka sata ferayar kabewa shi ne ta samu
wannan raunika.
Koda jin haka sai Sarki Yaki marhat yayi
ajiyar zuciya, cikin alamun rashin gamsuwa amma
sai ya yi shiru bai sake tanka mata ba.
A wanna rana ta bakwai ne aka je aka
xauko Muzainat da mahaifinta aka kai su cikin
wannan qerarren gida da shirin cewa kashe gari za a
yi bikin aurenta da sarki masrud.
A can gidan sarki masrud kuwa tuni an
fara shirye-shiryen bikin aurensa ana ta shirya abinci
da za a ci gobe manya baqi kuwa tuni sun fara
hallara daga sauran qasashen makwabtaka birni da
qauye, hadimai,barori da kuyangi kuwa sai kai kawo
100

jihadi
suke yi suna ta yin ayyuka nag yare-gyare ado da
shirya qawa a wurare da yake na cikin gidan
sarautar.
Su kuwa matan sarki masrud su goma
sha xaya sun taru gaba xayansu a cikin xakin
uwargidansu suna shiryawa kansu wata ‘yar
qaramar walima sai ciye-ciye da shaye-shaye suke
yi, suna ta qyalqyala dariya mugunta suna cewa za
su ga yanda wannan budurwa zata iya tsallake kaifin
takobin sarki masrud yaya suma suka kasance matan
sarki na tsawon shekaru sun haqura da zuwa
turakarsa sai kamar budurwa yar shekara sha takwas
ce zata iya da shi?
Me ta sani a rayuwar duniya ma bare ta
bashi labarum da za su kwantar masa da hankali su
hana shi hauka.
A can vangaren turakar sarki kuma a
wannan rana wani abin mamaki ne ya faru, domin a
ranar gaba xaya ciwon sarki bai tashi ba ko sau xaya
ba, kuma sai ya kasance a cikin tsananin farin ciki
ya yi ta rabon kuxi da kayayyaki ya zamana cewa
babu abinda yake son a faxa masa face a ambaci
sunan amaryarsa Muzainat, shi kansa Boka Aulad
makusancin sarki masrud sai da ya yi matuqar
mamakin yadda aka yi sarki masrud bai yi cutarsa ta
101

jihadi
hauka ba a wannan rana, kuma har sai da dare ya
raba sarki masrud bai daina nishaxi da farin ciki ba,
babu shiri a lokacin Boka Aulad yasa aka baiwa
sarki masrud maganin barci yasha sannan ya vingire
akan gado ya kama sharar barci hard a minshari
rabon da sarki masrud ya sami irin wannan barci
mai nauyi tun kafin ya haxu da lalurar wannan cuta.
Kashe gari kuwa da sassafe aka fara
shagalin biki gaba xaya birnin ya ruxe da kaxe-kaxe
gami da bushe-bushe sarakuna da ‘ya ‘yansu
attajirai da masu faxa aji suka yi ta tururwa izuwa
cikin birnin suna rinqa shiga gidan sarautar,masana
tarihin birnin said a suka tabbatar da cewa ba a tava
yin gagarumin taro da ya kai na bikin auren sarki
masrud da Muzainat ba, tun daga farkon kafuwar
qasar kuwa izuwa yanzu.
Bisa al’adar auren a qasar a wannan
lokacin dole ne ango da amarya su tsaya a gaban
masoyansu ‘yan uwansu da dukkan zuri’arsu a
kwara musu ruwan madarar shanu akansu sannan
kowannensu ya zo gaban gunkin da suke bautawa ya
yi sujjada ya dangwali wani jan zabibi da
xanyatsansa na hagu yayi fashin goshi a kansa da
goshin gunkin, sannan kuma ango ya shafawa
amaryarsa jan zabibin akan goshinta, hakan na
102

jihadi
faruwa sun tabbata miji da mata kuma sun sami
albarkar gunki.
Bayan taro y agama cika, duk inda
mutum ya hanga gabas da yamma kudu da arewa sai
dai yaga kowannan bil’adama rubutu batutu babu
masaka tsinke, a cikin tsakiyar filin gidan sarautar
ne aka yi wannan gangami sai ga sarki masrud tare
da amaryarsa sun fito daga cikin gidan sarautar sun
fito daga cikin gidan sarauta.
Dukkaninsu sun cava ado na gaban
kwatance suna tafiya a kan wani jan kishi wanda ya
nufo wajen da gunki yake, dakaru da kuyangi na
take musu baya.
Koda ganin fitowar sarki da amaryarsa
sai mutane suka ruxe da shewa suka kama yi musu
jinjina gami da kirari.
Sai da sarki masrud da amaryasa
Muzainat suka yi taku sittin sannan suka iso gaban
gunki suka tsaya tsayuwarsu keda wuya sai aka zo
da madarar guda biyu a cikin gorar ruwa aka
kwararaa sarki da Muzainat a kansu suka jiqe
sharkaf kaico, kaji wata al’adar banza duk wannan
kwalliya da ma’auratan suka yi an vatata.

103

jihadi
Nan take sarki masrud ya dangwali jan
zabibi ya yiwa kan fashin goshin kuma ya yiwa
gunki ya koma gefe xaya ya tsaya.
Ita ma Muzainat sai ta dangwali zabibin
ta shafawa kanta a goshin.
Koda ta durfafi gunki da nufin ta shafa
masa zabibin akan goshinsa sai kawai aka ji an
zabga wata irin tsawa mai qarfin gaske mai tsananin
ban tsoro wacce ta razana kowa alhalin babu alamar
hadari a garin.
Ita kanta Muzainat bata san sa’adda ta
faxi qas saboda tsananin firgita da tayi, amma sai ta
miqe tsaye zumbur taje ta shafawa gunki zabibin
sannnan ta shafawa kanta.
Koda ganin haka sai murna ta kama sarki
masrud don haka sai shima ya dangwali zabibin ya
shafawa Muzainat a goshinta suka rungume juna a
lokacin da jama’a suka kaure da shewa gami da tafi
alamar aure ya tabbata a lokacin da jama’a suka
kaure da wannan shewa ana ta murna gaba xaya
bokayen qasar kuwa hankalinsu a dugunzume yake
bisa wannan muguwar tsawa da aka tafka.
A lokacin da Nasimarat ta je zata
shafawa abin bautarsu zabibi a goshi.
104

jihadi
Hakan bai tava faruwa ba kuma yana yi
musu nuni ne da cewa lallai akwai wani babban
sauyi da yake shirin zuwa, amma ta hannu wannan
budurwa amarya sarki.
Nan da nan Bokayen suka bar filin gidan
sarautar gaba xayansu suka tafi izuwa can wani
xakin bauta dake bayan gari suka kulle qofarsa
**
Boka Aulad shi ne shugabansu don haka
sai ya dube su gaba xayansu yace da su “Abin da
nake so da ku shi ne kowannenku yayi mana bincike
yanzu a cikin madubin tsafinsa ya gano mana
ma’anar wannan tsawa mai ban tsoro da aka tafka
sakamakon zuwan Muzainat gaban abin bautarmu
da nufin shafa masa zabibi bisa al’adar aure.
Koda jin wannan umarni sai gaba xaya
bokayen suka fiddo madubinsu na tsafi suka duqufa
shima Boka Aulad xin ba a barshi a baya ba sai ya
taya su jim kaxan sai kowa ya xago kai suka rinqa
kallon-kallo a junansu cikin matuqar al’ajabi aka
rasa wanda zai ce qala har shi kansa Boka Aulad xin.
Daga can sai boka Aulad ya dube su yace.
“Na sani cewa duk abu guda muka gani a
cikin bincikenmu don haka ba sai na tambayi
xayanku ba.
105

jihadi
Tabbas wannan abin al’ajabi ne baba
kuma abin tsoro don haka ya zama wajibi musan
matakan da zamu xauka, wannan tsawa da aka tafka
ashe ba komai bace face gargaxi a gare mu gaba
xayan mutanen Hindu cewar mai girma abin
bautarmu bai yi amana da wannan auren ba na sarki
saboda ita wannan yarinya Muzainat tana da wani
babban sirri wanda nan gaba zata kai ga samun
babban matsayi da xaukaka a birninmu. Ga dukkan
alamu ma sai ta mulke mu ta zama sarauniyarmu
idan kuma hakan ta faru, mun tafka babban abin
kunya da ba a tava yin kamarsa ba.
Ko ina a duniya ace ‘yar almajiri mara
cikaken asali ta zama sarauniyar mu ya zama dole
mu hana sarki yin taraiya da wannan amarya tasa a
wannan daren na yau, kuma musan hanyar da za mu
bi mu hallakata a sirrance batare da kowa ya sani
ba”.
Koda boka Aulad ya zo nan a zancensa
sai babban Boka na birnin Kashmir ya miqe tsaye ya
dube shi cikin alamun girmamawa kuma ya risina
masa yace “Ya shugabana to yanzu ya za mu yi da
wannan cuta ta sarki tunda ka san cewa abu ne
mawuyanci mu sake samun budurwar da zata iya sai
da ranta ta aure shi?”
106

jihadi
Koda jin wannan tambaya sai Boka
Aulad ya ja numfashi ya ajiye sannan yace “Ai har
abada jarumai basa qarewa a cikin duniya sai mu
lalubo wata, ina son ku barni mini komai a hannuna
zan san abin da zan yi.
A yau xin nan zan kawar da wannan
amarya ta sarki cire silin gashi daga cikin tandun
mai yafi wannan aikin sauqi a wajena, tunda kun
sani cewa babu wani mahaluki daya fini samun
aminci a wajen sarki”.
Koda jin wannan batun sai farin ciki ya
lulluve dukanin bokayen suka kama yiwa Boka
Aulad jinjina cikin farin ciki gami da samun
nutsuwa.
A can filin gidan sarauta kuwa bayan an
gama xaura aure sarakai da manya baqi suna zuwa
su taya shi murna, kuma suna bashi kyaututtuka a
lokacin da amaryarsa ke tsaye daf da shi, sai ya lura
babu boka Aulad a filin gaba xaya. Hakan nan
‘yarsa Gimbiya Zuhaira ma bata zo ba.
Koda ya sake hangawa ko ina sai yaga
ashe gaba xaya bokayen qasar ma basa nan, nan
take hankalin sarki masrud ya dugunzuma ainun ya
aiyana a cikin ransa cewar lallai Boka Aulad yaci
107

jihadi
amanarsa kuma akwai wata maqarqashiya da yake
shirin tafka masa, shi da sauran bokayen.
Nan take sarki masrud ya kirawo sarkin
yaqinsa yace da shi, maza kasa a rakani izuwa
turakata kuma daga yau kada a sake barin kowa ya
shigo inda nake ko a inda amaryata take koda kuwa
Boka Aulad ne, kai kaxai na yarda da ka shigo
turakar mu yi magana.
Sarkin yaqi ya risina ya ce “An gama ya
shugabana”.
Nan take sarki masrud ya kama hannun
amaryasa Muzainat suka nufi cikin gidan sarauta
dakaru sama da miliyan xaya na mutane da aljanu
na take masa baya.
A daidai wannan lokacin ne Bola Aulad
da sauran bokayen suka dawo filin fadar koda Boka
Aulad ya hango sarki da amaryarsa za su shige cikin
gidan sarautar sai ya rugo da gudu ya nufi inda sarki
ya ke da nufin ya shiga.
Kwatsam sai Boka Aulad yaga sarkin
yaqi ya sha gabansa cikin fushi Boka Aulad ya dube
shi yace “Wane irin shirme ne haka zaka zo kasha
gabana alhalin kasan cewa sarki baya son na gusa
daga kusa da shi daidai da tsawon rabin sa’a”.
108

jihadi
Koda jin haka sai sarkin yaqi ya yi xan
guntun murmushi yace.
“Ai wannan da ne, yanzu nan sarki ya
bani umarnin cewa kada na sake barin kowa ya je
inda yake, koda kuwa kai ne”.
Koda jin haka sai ran Boka Aulad ya
vaci ainun ya dakawa sarkin yaqi tsawa yace “Wai
shin ni kakan ka ne har da zaka zo mini da maganar
wasa”.
Da jin haka sai sarkin yaqi ya turvune
fuskarsa yace “Na tava yi maka wasa ne? ko kuwa
zan yi wa sarki qarya ne saboda kawai biyan wata
buqata tawa? Inda sarki bai sauya ra’ayinsa ba ai
babu yadda za a yi ya tafi ya barka. Ni ina ganin
sarki yana zarginka da wani laifi don haka kasan
hanyar da zaka bi ka gyara tsakaninka da shi”.
Koda sarkin yaqi ya zo nan a zancensa
sai hankali Boka Aulad ya dugunzuma ainun fiye da
koyaushe ya dubi sarkin yaqi cikin alamun matuqar
damuwa yace.
“Dole ne naga sarki yanzu domin na
hana shi Tarawa da wannan amaryar tasa domin
kuwa akwai babbar matsala, abin da nake so da kai
shi ne ka yi min jagora izuwa ga sarki yanzu nan
kafin lokaci ya qure”.
109

jihadi
Sarkin yaqi ya girgiza kai yace.
“Ba zan iya ba, domin ni ma idan na
kaika gare shi zan iya rasa matsayina gaba xaya”.
Koda jin haka sai Boka Aulad ya dakawa
sarkin yaqi tsawa, a karo na biyu yace.
‘Shin ka manta ne cewa ni da kai duk
munyi rantsuwa da girman abin bautarmu cewa
zamu sallama rayuwarmu da komai na mu domin
mu kare wannan gidan sarauta na mu da qasar gaba
xaya.
Na rantse da girman iyayena idan ban
hana sarki taraiya da wannan amarya tasa ba sai
mulkin ya suvuce masa gaba xaya domin ita
amaryarce zata haye karagarsa kuma ajalinsa a
hannunta yake, ta yaya muna ji muna gani za mu bar
‘yar almajiri mara cikakken asali zata zo ta karvi
mulkin qasar nan dare xaya?
Sa’adda Boka Aulad ya zo nan a
zancensa sai hankalin sarkin yaqi ya dugunzuma
ainun ya yi shiru yana tunani da nazari har izuwa
tsawon yan daqiqu ya rasa abin da zai ce daga can
sai ya xago kai ya dubi Boka Aulad yace.
“Tabbas dole ne na baka haxin kai xari
bisa xari domin ganin mun ceci rayuwar sarki da
kuma darajar qasar nan ta kowane hali, amma ka
110

jihadi
sani cewa tsalle xaya shi ke jefa mutum a cikin
rijiya, gaggawa a cikin wannan al’amari a gare ni
yana da matuqar haxari, ka tuna cewa kai fa boka ne
wanda babu kamarsa a qasar nan don haka ka yi
amfani da qarfin sihirinka wajen magance wannan
matsala”.
Boka Aulad ya yi ajiyar zuciya cikin
alamun takaici yace “Ai in da zan iya yin hakan da
tuni na yi ba sai na tuntuve ka ba, ai idan ka ji Sarki
Yaki yace a yi wasan jifa to lallai ya taka hoge, ka
tuna cewa duk faxin qasar nan ba a sami budurwa
da ta amince za ta auri sarki ba a cikin wannan
larura tasa face Muzainat kasan kuma lallai akwai
abinda ta taka.
Bisa wannan binciken da na yi a kanta na
gano cewa akwai wani babban sihirin tsafi a jikinta
wanda duk wanda ya tunkareta da nufin ya hallakata
mutuwa zai yi, maganinta kawai shi ne sarki ya fasa
aurenta kuma ya nisanta da ita.
Tun da ba zamu iya tava Muzainat ba ai
za mu iya raba sarki da ita, ni yanzu ba ni da sauran
aminci sarki kai kuwa kana da shi, ka yi amfani da
wannan dama a yau xin nan kafin sarki ya shiga
xakin amaryarsa kasa a sace shi a sirrance mu fitar
111

jihadi
da daga cikin gidan sarautar gaba xaya, mu kaishi
can gidana na bayan gari mu voye shi.
A sannan ne zamu yi tunanin hanyar da
zamu bi mu fitar da Muzainat daga cikin gidan
sarautar gaba xaya a cikin ruwan sanyi”.
Lokacin da Boka Aulad ya zo nan a
zancensa sai hankalin sarkin yaqi ya qara
dugunzuma ya shiga cikin halin wasi-wasi,zullumi,
fargaba da zargi kawai sai ya xago kai ya dubi Boka
Aulad cikin alamun rashin yadda yace.
“Duk waxannan abubuwan da ka shirya
mini yanzu sunyi kama da hanyoyin da ake bi a
shirya juyin mulki, da wace hujja zan yi amfani na
gamsu cewa ba juyin mulki kake shirin yiwa sarki
ba?”
Boka Aulad ya dakawa sarkin yaqi tsawa
a karo na uku yace “Yau shekara ta arba’in ina bauta
a wannan gidan na sarauta na yi bauta ga mahaifin
sarki masrud da kakansa duk tsawon waxannan
shekarun ba a tava kamani da laifin cin amanarsu ba,
duk abinda nake nema na jin daxi duniya ina da shi
a can fada ta ina da dukiya mai tsananin yawan da
ban san iyakar adadin yawanta ba, ina da matan aure
guda tamanin da xaya, ina da ‘ya ‘ya arba’in da biyu
fadata ta ginu kuma ta qawatu fiye da wannan
112

jihadi
wacce muke ciki ina da fadawa kuyangi,barori da
dakarun tsaro waxanda suka ninka na wannan fadar
sau uku, a kan wane dalili zan yi sha’awar wannan
fada ko karagar cikinta?”.
Koda sarkin yaqi ya ji waxannan
tambayoyi da Boka Aulad ya yi masa sai jikinsa ya
yi sanyi matuqa ya rasa abin da zai ce daga can sai
ya xaga kai ya dubi Boka Aulad yace.
“Kafin dare yayi akai amarya xakin
angonta zan san abin da zan yi akai kuma zan
nemeka na sanar da kai komai”.
Koda jin haka sai Boka Aulad yayi
doguwar ajiyar zuciya, sannan yace “Lallai ka
tabbatar da cewa ka yi duk motsinka kafin a kai
amarya xakin sarki”.
Koda gama faxin haka sai Boka Aulad
ya juya ya yafito wani hadiminsa da hannu take
hadimin ya janyo dokin Boka Aulad da sauri ya
kawo masa.Cikin alamun fushi Boka Aulad ya kama
dokin nasa yah aye ya zabureshi da gudu ya nufi
hanyar fita daga cikin gidan sarautar gaba xaya,
aikuwa sai wasu dakarun Boka Aulad kimanin su
arba’in bisa dawakai suka rufa masa baya.
Koda jama’ar gari suka ga Boka Aulad
ya fice daga ciki gidan sarautar gaba xaya sai suka
113

jihadi
cika da tsananin mamaki saboda an san cewa dare
da rana yana tare da sarki baya yarda ya yi nisanta
da shi,shi ma sarkin haka fa aka fara tsegumi, kowa
ya riqa faxin albarkacin bakinsa.
Tun lokacin da Gimbiya Zuhairat ta
samu labarin mahaifinta da Muzainat hankalinta ya
gama dugunzuma. Tasan dai tunda mahaifinta ya
shiga cikin wannan mayuwanciyar cutar data
kamasa dare xaya. Kuma gashi bokaye sun kasa
warka da shi.
Don haka tabbas akwai wani abu a qasa
amma kuma abu xaya yasata farin ciki da auren ya
kuma saka duka baqin cikinta gushewa shi ne. A
yanzu tasan tabbas wannan ciwon na mahaifinta duk
lokacin daya ta shi to zai iya shaqe muzainat har sai
ya kasheta. Amman duk da haka sai ta kirawo wani
amintaccen bawanta tace ya je ya saka mata ido
akan duk abinda yake gudana.
**
Al’amarin sarki masrud kuwa lokacin
daya kama hannun amaryarsa Muzainat ya yaja ta
izuwa cikin gidan sarauta bai zame ko ina ba sai
cikin wani babban falo wanda girmansa ya kai na
fadar gidan sarautar. Babu komai a cikin wannan
114

jihadi
falo face kujeru da tebura na cin abinci birjik da
yawa iya ganin mutum.
Suna shigowa cikin wannan babban falon
sai suka yi arba da gaba xayan sarakunan nahiyar
waxanda suka zo taya sarki masrud murna wannan
aure nas kowane sarki yana tare da matarsa a zaune
ga kayan ciye-ciye dana shaye-shaye, iri-iri babu
adadi akan teburin amma a saboda girmama sarki
masrud ko ruwansha babu wanda ya xauka ya kai
bakinsa sai ya iso tukuna.
Koda sarakuna da matayensu suka ga
sarki masrud tare da amaryarsa sun shigo cikin falon
sai gaba xayansu suka miqe tsaye suna kama yi
masa tafi ya yin da waxannan sarakunan suka yi
arba da amaryar Muzainat a cikin gagarumin ado da
aka cava mata sai dukkaninsu suka ximauce bisa
ganin irin tsananin kyawun da Allah ya bata.
Nan fa wasun su suka fara munafunci da
tsegumi ga ‘yan uwansu sarakuna.
Sarkin birnin kirishna ne ya dubi sarkin
birnin lamras ya yi masa raxa a kunne yace “Tabbas
banga laifin sarki masrud ba da

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment