Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
sai yaga ita wannan yarinya wanda zai aureta farin mutum ne, kuma shine wanda zai mulki duniya, sai ya zaci ko WAHASHINFALA ne, sai ya fusata yace wa Sarki ya zama dole ya kashe wannan yaron WAHASHINFALA in kuma yaki to zai aika wa Dan uwansa Boka SAKARADUSA, ya fadawa Sarki SAIF ce wa "Sarki AFARA'U ya ajiye wani farin yaro kuma idan ya taso to duk zai halakar damu ne, sannan kuma ya mayar da wasun mu bayi. Boka SAKARAJUNA ya kare da cewa kaga kuwa idan Sarki SAIF yaji wannan batu to labudda zai halaka ka da ki da jamaaar taka baki daya." Koda Sarki AFARA'U yaji wannan magana daga bakin Boka SAKARAJUNA, sai hankalinsa yayi kololuwar tashi saboda yasan indai har wannan magana taje kunnen Sarki SAIFIRRA'ADU to kashinsa ya bushe. Koda gama wannan tunani sai yace da boka SAKARAJUNA daya bashi nan da kwana biyar zaiyi shawara, boka ya yarda da hakan. Boka yayi wa Sarki sallama ya nufi masaukinsa, yayin da shikuma a bangaren Sarki AFARA'U ya zurfufa kogin tunani na neman mafita, yana cikin wannan haline na tunani Wazirin sa mai suna HARISU ya fado masa arai. Waziri HARISU ya kasance mutum ne mai hangen nesa, saboda sanin yakamata da kuma hangen nesashi ne yasa Sarki AFARA'U ya nadashi Wazirinsa. Wanda ada yake da mukamin Sarkin gida. Koda Sarki AFARA'U yazo nan a tunaninsa, sai ya kira wani barde yace yayi maza gidan Waziri HARISU ya kirashi yanzu yanzu. Bardennan ya amsa da angama ya shugabana. Ya haye dokinsa ya sukwaneshi. Lokacin da barden nan ya dawo shida Wazirin HARISU Sarki yana cikin turakarasa. Saboda haka shima Waziri sai ya zarce inda turakarsa Sarkin take. Bayan ya nemi izini Sarki ya bashi, ya kunna kai cikin dakin. Koda shigar sa sai Sarki ya bashi labarin duk yadda sukayi Boka SAKARAJUNA akan WAHASHINFALA. Koda Waziri HARISU yaji haka sai yayi na wasu dakiku tamkar babu kowa a dakin. Daga can kuma sai ya kawo gauron numfashi ya aiye yace "abar bauta zahalu ta kareka, mafita daya garemu akan... Zamu cigaba MALUKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN littafi na daya 1 part 3 posted by Shuraih Usman @ https://dlhausanovels.com.ng Koda Waziri HARISU yaji haka sai yayi na wasu dakiku tamkar babu kowa a dakin. Daga can kuma sai ya kawo gauron numfashi ya aiye yace "abar bauta zahalu ta kareka, mafita daya garemu akan wannan lamari tunda kaidai kanason yaron nan bakason rabuwa dashi ko kadan. Mezai hana mu jewa da wannan boka kalamai masu sanyaya rai da kwantar da hankali, muyi masa alkawarin cewa Indai har wannan yaro ya girma mukaga take taken shi nason rushe mana masarauta da kuma hanamu bautar zahalu to sai mu kashehi." Koda Sarki AFARA'U yaji wannan zance sai yace "Maraba da fasihin Waziri, hakika hakan za'ayi".Da haka Waziri yayi wa Sarki sallama ya tafi gida. Bayan kwana biyar Kamar yadda Waziri HARISU yayi wa Sarki AFARA'Uu bayani, cikin sa'a kuwa suka shawo kan boka SAKARAJUNA. Sannu a hankali soyayyaya mai karti ta kullu tsakanin WAHASHINFALA da SHAMATU ba tare da Sarki AFARA'U ko boka SAKARAJUNA sun sani ba. Bayan wasu yan shekaru kowa a cikin wannan garin saida ya fahimci soyayyayar dake tsakanin WAHASHINFALA da SHAMATU saboda haka boka SAKARAJUNA ya fara kokarin rabasu ta hanyar alqalaman tsafi amman abu ya farkara. Ganin haka ya shirya mashi makirci ta qarkashin kasa. Sannu a hankali manema suka fara fitowa neman auren SHAMATU, cikinsu kuwa harda WAHASHINFALA wanda shine kan gaba. Saboda haka Sarki AFARA'U ya nemi shawarar boka SAKARAJUNA, koda boka yaji harda WAHASHINFALA sai yayi dariyar qeta yace "Inaso gobe a tattatara mani manemanta a kofar fada". Daga haka Sarki AFARA'U yasa aka rubuta takardu zuwa ga masu neman auren "Yarsa SHAMATU. Yakira wani bafadensa ya aikesa. Washe gari tunda sanyin safiya masu neman auren SHAMATU suka fara bayyana, bayan wani lokaci, suka gama bayyana a bakin fada, cikin mutanen nan kuwa harda WAHASHINFALA dashima ya shiga layin manenan SHAMATU. Bayan wani lokaci suka fara jin bugun tabura gami da busar algaita hakan ya tabbatar masu da cewa Sarki yana tafe. Haka kuwa akayi Sarki AFARA'U ne sanye cikin alkebba, daga damansa Wazirin sa ne mai suna HARISU Sannan daga hagunsa kuma boka SAKARAJUNA. Koda ya karaso bakin fadar, bayan yayi masu barka da zuwa saiya umarci boka SAKARAJUNA daya fada masu abinda ake buqata ga duk wanda yakeson SHAMATU. Boka SAKARAJUNA ya fara magana kamar haka "inayi wa bakinmu barka da zuwa, dalilin dayasa muka taraku anan shine, duk wanda yake son auren SHAMATU to sadakinta shine zai kawo mana kan Shahararren dan fashin nan wato SA'ADUNUJJANJI, koda wadannan jaruman da yayan attajirai dake neman auren SHAMATU sukaji haka sai suka fara sulalewa, cikin kankanin lokaci wajen ya zama fetal ba kowa sa WAHASHINFALA. Koda ganin haka sai boka yayi murmushin keta yace da WAHASHINFALA jarumtarka ta burgeni sai ka shirya nanda jibi ka kama hanya. Daga haka suka juya izuwa cikin gidan sarautar. Bayan kwana biyu WAHASHINFALA ya shirya cikin bakin sulke, yayi wa SHAMATU da Sarki AFARA'U sallama y kama hanya cike da kewar garinshi da kuma masoyiyarshi SHAMATU. Alamarin SHAMATU kuwa tunda masoyinta WAHASHINFALA ya tafi ta shiga damuwa kasancewar bata da tabbacin cewa ko zai dawo da rai. Ahaka ta kwana ta wuni a rana ta biyune tana bacci tayi mafarki da annabi HALLIRU alaihissasatu, yace mata ai ita taimakon WAHASHINFALA yana hannunta. Cike da mamaki ta kalleshi tace taya ya? Sai yace da ita a gidan akwai wata matattala ita wannan matattalar ta kasance idan ka taka ta farko lafiya ta biyu bazakata lafiya, yacigaba da cewa saboda haka ya zama maki dole kije ki sanar dashi. Koda SHAMATU ta farka cikin dare bata zame ko ina ba, sai bargar dawakai, cikin sanda ta kanto doki ta haye cikin sa'a kuwa ta tadda masu gadin kofar sunata sheka baccisu. Ba tare da tsoron komai ba ta bude kofar ta fice. Kasancewar WAHASHINFALA be dade da lafiya ba ita ta bi bayansa koma dokin data dauko irin na musammanne wanda ba koda wane lokaci ake fani da suba, tadauki lokaci tana tafiya cikin kurmumun daji ba tare da tsoron komai ba. Aiko cikin sa'a ta fara hango WAHASHINFALA wanda yana gab da shiga cikin gidan shahararren dan fashin nan wato SA'ADUNUJJANJI ta kwala masa kira, koda yaji ankwala masa kira sai yayi turus yaja ya tsaya ba tare daya waiwayo ba. Ganin shirun yayi yawa yasashi ya waiwayo koda ganin wadda ta kirasa sai fuskarshi ta fadada da murmushi. Ya tabayeta keko meya sa kika biyoni? SHAMATU tace Zan baka labari amman ba yanzi ba. WAHASHINFALA shida SHAMATU sukayi kokari suka shiga cikin gidan kasurgumin dan fashin nan SA'ADUNUJJANJI can suka hango wata matattakala, nan take WAHASHINFALA ya doshi inda matattalar nan take ya mika kafa ya taka ta farko ya kuma taka matattala ta biyu daga takawarshi sai ya rufta ciki wasu wukake guda biyu masu matukar kaifi, da tsini tare da suka nufoshi zasu rabashi biyu cikin azababben sauri SHAMATU ta rugo da gudu ta rikeshi sannan tayi wuf ta jawoshi waje. Ai koda ya ganta sai ya cika da matukar mamaki ya tambayeta ya akayi kikasan haka? Nan ta kwashe labari kaf ta fada masa. Da yaji haka sai yace gashi yanzu adduarki taci. Nan dai SHAMATU ta ci gaba da bashi labarin wannan matattala tace Ita wannan matattalar idan ka taka ta farko lafiya to tabiyu ta Sharri ce dan haka idan ka taka ta farko to saidai ka tsallake ta biyu ka taka ta uku. To haka sukayi har suka isa can sama da suka isa sai suka riski wata katuwar kofa ta baki karfe saboda haka sai MALUKUSSAIF ya leka ya hango wani mutum baki, kato, mai manyan idanuwa gasu jajaje tamkar garwashin wuta, gashi da katon hanci kamar gwangwani, ga katon kai Kamar mangala Sannan ga manyan labba kai kace fata aka shinfida. Daga gefen damansa mutane arbain ne haka ma bangaren hagunsa. Koda WAHASHINFALA yaga haka sai ya dawo bayan wannan kofar ya labe, koda ganin haka sai SHAMATU tace da WAHASHINFALA shi wannan mutumin na tsaki baki mummunan shine SA"'ADUNUJJANJI. Suna zaune can sai SA'ADUNUJJANJI yace da mutanensa kai kutsaya nifa kamar motsi nake ji fa? Inaga daya daga cikin mutanen da kuka kamo ya kwance, daya daga cikin ku ya tashi ya duba. Yana gama rufe bakinsa, daya daga cikin Sadaukan nan ya tashi domin ya dubo yana zuwa daidai inda kofar nan WAHASHINFALA yayi wuf ya sare masa kai, ita kuma SHAMATU ta janyeshi ta boye gawar, da aka jima sai SA'ADUNUJJANJI yaji shiru sai ya kuma turo wani barden nan ma dai WAHASHINFALA ya sare masa kai kamar yadda yayi wana farko, haka SA'ADUNUJJANJI yayi ta aiko da mutane har akazo kan na biyar nan fa kowa tsoro ya darsu a zuciyarsu aka rasa Wanda zai tashi shikuma WAHASHINFALA dayaga anjima babu wanda ya sake fitowa sai ya kutsa kai ya shiga cikin dakin ya tsaya gabansu koda SA'ADUNUJJANJI yaga WAHASHINFALA sai yace kai kuma wannan karamar halitta daga ina haka? Kuma maiya kawoka nan harka halaka mani mutane? WAHASHINFALA ya amsa masa da cewa babu ruwanka daga inda najo, kuma dalilina na zuwa na wajenka shine nazo ne na kasheka, Sannan na tafi da kanka a matsayin sadaki. Koda SA'ADUNUJJANJI yaji wannan magana sai ya bushe da dari sannan yace kai yanzu wannan yaro har MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN littafi na daya 1 part 4 post by Shuraih 99% zaka iya fada dani? Dubeka fa ka dubeni na ninka ka sau goma, yanzu kaiko wannan saurauyin wane ne ya turoka ka aikata wannan abu gareni? WAHASHINFALA cikin bacinrai yace ba'a sani ba idan zakayi shirin yaki kayi. SA'ADUNUJJANJI yace zo mu shiga cikin gidana akwai fili isasshe wanda zai ishemu ni da kai. SA'ADUNUJJANJI ya tashi yaransa suka biyoshi a baya, WAHASHINFALA ma ya biyo shi a baya, suka shige wasu manyan soraye guda uku suka riski wani fili, da suka isa wannan fili sai SA'ADUNUJJANJI ya juyo wajen mutanen sa yace idan muna yaki da wannan yaro kar wanda ya kawo mani dauki koda kuwa kunga yana kokarin samu galaba a kaina ne, ku tsaya kawai kuyi kallo. Koda yaran SA' ADUNUJJANJI sukaji haka sai su dukansu suka babbake da wata mahaukaciyar dariya, domin sun san cewa ba ta yadda za' ayi wannan karamar halittar ya iya kai shugaban nasu kasa ko yazo da matemaka bare ya zo shi kadai. Suka amsa da sunji sun yarda. Can kuma SHAMATU data ga sun shiga wannan gida, sai ta fito daga inda take boye ta hau kan wani dutse inda zata iya ganin karawar da za'ayi tsakanin SA'ADUNUJANJI da saurayinta. SA'ADUNUJJANJII ya yiwo kan WAHASHINFALA yana gurnani tamkar zakin dakejin yunwa ya hango nama, WAHASHINFALA shima ya zare tashi takobin yayi dauki kan sa suka kaure da yaki bají-ba-gani har dare yayi rana ta take. Can suna cikin wannan dauki ba dadi dine sai WAHASHINFALA ya taka wani karamin dutse ya durkushe kasa. SA'ADUNUJJANJI ya daga takobinsa ya kawo wa WAHASHINFALA wani wawan sara koda SHAMATU taga haka sai ta tabbatar da cewa indai har saran nan ya dira a kan masoyinta to saidai wani bashi ba. Sai tayi wuf! Ta zaro wani gariyo daga cikin sulkenta ta wulwuloshi ta jefi SA'ADUNUJJANJI dashi, sao gariyon ya sare shi a hannu wanda hakan yayi sanadin faduwar takobin dake hannunsa. WAHASHINFALA ya rike takobinsa a hannu yayi niyyar sarewa SA'ADUNUJJANJI kai amman sai ya fasa yace tashi ka dauki takobinka muci gaba da yaki, domin bazan kasheka ta hanyar yaudara ba, sai kuma ya juya ya fuskanci dutsen da SHAMATU take tsaye yace jinjina gareki ya ma'abociyar bege. Koda SA'ADUNUJJANJIl yaji haka sai ya tashi ya dauki takobinsa suka ci gaba da yaki, haka suka cigaba da wannan gwabzawar har tsawon kwana uku a rana ta ukun ne shuka tsaya domin su huta, ko wannensu ya samu guri ya zauna yana haki. Su kuma yaran SA'ADUNUJJANJI sun cika da mamaki ganin irin jarumta da kuma sadaukartaka ta WAHASHINFALA. Can da aka jima sai SA'ADUNUJJANJI yace "Yaro me yasa lokacin da takobina ta fadi ka samu damar kasheni amman kaki kace bazaka kasheni da yaudara ba? kuma naji kamar kana magana da wani. WAHASHINFALA yace wannan yarinyar da zan aura itace ta cillo mani wuka, kuma da ita nake magana shiyasa nace bazan kasheka da yaudara ba. WAHASHINFALA ya sakko da SHAMATU daga kan dutsen nan ya shigo da ita cikin wannan filin ta zauna kusa da shi. SA'ADUNUJJANJI yace lallai yau zan shayar da ku gidauniyar mutuwa daga kai har ita sannan naje har kasarku na kashe uban wannan yarinya na fatattaka garin gaba daya, na kwashe dukiyoyinsu sannan na koro bayi. Koda sukaji haka sai suka zabura suka cigaba da sara da suka, a takaice dai saida WAHASHINFALA da SA'ADUNUJJAN.JI suka shafe tsawon mako duga cir suna gwabza yaki amman babu wanda ya samu nasara a kan dan uwansa, har saida makamansu suka lalace nan take kowa ya yada nashi suka tsaya sukayi cirko-cirko kamar zakaru suna kallon juna suna muzurai. Can sai SA'ADUNUJJANJI yace "Kai yaro! Yanzu tunda makamanmu sun gaza yanzu sai mu fidda sharadi, WAHASHINFALA yace wane sharadi? SA' ADUNUJJANJI yace sharadin shine yanzu zamuyi kokawa nida kai duk wanda ya kada wani sau uku to shi ya cinye wannan gasar, idan kai ka kadani sau uku to kai ka cinye wannan gasa sai kayi yanda kakeso dani, haka zalika idan ni na kadakai sau uku to sai nayi yanda nakeso dakai. Koda WAHASHINFALA yaji haka sai ya yarda da wannan sharadin, suka fara kokawa kici-kici, can sai SA'ADUNUJJANJI yayi wuf! Ya suri WAHASHINFALA ya daga sama zai fyada da kasa, kawai sai WAHASHINFALA ya Kama kunnen SA'ADUNUJJANJI ya murda cikin ikon Allah sai ga SA'ADUNUJJANJI ya fadi kasa tim!. Haka dai WAHASHINFALA yayi ta kada SA'ADUNUJJANJI har sau uku, da SA'ADUNUJJANJI yaga haka sai yace yaro kayi nasara aikata abinda kakeso dani ya durkusa bisa gwiywoyinsa. Da WAHASHINFALA yaga haka sai ya dauko gariyonsa yayi niyyar sare kansa, da SA'ADUNUJJANJI yaga haka sai yace yaro amman da zaka kyaleni, da raina, ka kuma riqeni na zama bawanka domin kila wata rana zan maka amfani. Da WAHASHINFALA yaji haka sai ya ajiye wannan gariyon yace gaskiya ne na yarda da maganarka. SA'ADUNUJJANJI da kaf yaransa suka jinjina ga WAHASHINFALA sukace "Gaisuwa gareka ya shugabanmu" anan suka kwana. Da gari ya waye SA'ADUNUJJANJI da yaransa suka zo gurin WAHASHINFALA suka kwashi gaisuwa Sannan suka zauna daga gefen WAHASHINFALA. WAHASHINFALA yace da SA' ADUNUJJANJI da mutanen sa to ai saiku tashi mu tafi kasar DUWAR domin kuwa nasan Sarki AFARAU yanacan yaba jirana. Nan da nan SA'ADUNUJJANJI suka dora wa giwayensu sirdi, shi kuma WAHASHINFALA da SHAMATU suka haye kan dawakansu suka kamo kan hanyarsu ta dawowa kasar DUWAR. Bayan sun samu Kamar kwanaki uku suna tafiya sai suka fara hango katangar birnin DUWAR, anan sai shamatu ta rigasu shiga cikin birnin dankada a gane cewar tare suke, takoma gida ba tare da wani ya ganta ba. A wannan lokacin kuma sai akayi sa'a boka SAKARAJUNA yace da Sarki AFARA'U cikin gatse zomu je bayan gari muga ko wannan yaron zai dawo, Sarki, Waziri da sauran fadawa suka fito bayan gari suna diban hanya. Can sai suka hango WAHASHINFALA ga kuma SA'ADUNUJJAN.JI da yaran sa bisa giwaye, "kagani ko gashinan abinda kaja mana kasa wannan yaron ya tsokano mana SA'ADUNUJJANJI, ya matsa mashi ya sanar dashi cewa mu muka turo shi, gashinan sun sakoshi a gaba suzo su halakamu". Koda jin haka sai Sarki, boka da jama'ar gari suka ruga da gudu cikin gari suka rurrufe kofofin gari, da suka karaso sai WAHASHINFALA yasa daya daga cikin yaran nan ya bubbuga kofar amman ba'a bude ba. Koda WAHASHINFALA yaga haka sai yayi tsawa ya umarci SA'ADUNUJJANJI daya karya kofar birnin. Nan da nan SA'ADUNUJJANJI yayi wa toron giwarsa qaimi ya bangaji kofar garin ta karye, suka kutsa kai izuwa cikin MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN littafi na daya 1 kashi na daya 5 fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi rubutawa Mr Hausa Ebooks Da WAHASHINFALA yaga haka sai yace "Baba yanaji kace dani Sarki bayan ba haka bane, kuma ka kirani da wani suna wai MAALIKUS-SAIF bayan ni sunana WAHASHINFALA. Tsoho ya dubeshi yayi murmushi yace "Katahone daga garin DUWAR kuma yau kwananka sittin kana tafiya kafin kazo nan, kuma WAHASHINFALA ba sunanka bane sunan ka wanda Allah ya nufa shine MAALIKUS-SAIF, mahaifinka kuwa shine Sarki ZIYAZINUN mai mulkin kasar HAMRA'U YAMEN wanda ya rasu, kuma kaine wanda adduar Annabi Nuhu zata fada a kansa zai samu mulkin duniya baki daya, ya kuma tambayarsa ya MAALIKUS-SAIF yanzu mai kake bautawa? Ya amsa masa da cewa "Eh nidai naga mutanen nahiyar mu suna bautawa rana da wata ne, amman ni bana bauta masu sabo da nasan Allah ne ya halicceni saidai ban samu Wanda zai koya mani yadda zan bauta mashi bashiyasa ni ban bauta wa komai Tsohon yace "Ka dogara ga Allah yanzu zan musuluntar da kai. MAALIKUS-SAIF yace na dogara ga Allah, Tsohon yace kace na gasgata babu abin bauta sai Allah kuma na gasgata da Annabi Muhammadu Annabi da zaizo a karshen zamani da Annabin wannan zamanin Annabi Ibarahim alaihissasatu wassalam. MAALIKUS-SAIF ya maimaita shahada kamar yadda Tsohon nan ya fada masa. Bayan ya gama sai Tsoho yace masa ni sunana Shehu ZAJJADA, yanzu tunda ka musulunta ka zama dan uwana kuma ya zama dole na taimakeka nasan ka fito neman littafin kogin NIL zan fada maka inda yake amman inaso kafin ka tafi ka kwana a nan domin inason sanar dakai hanyoyin bautar Allah. Shehu ZAJJADA ya koya wa MAALIKUS-SAIF alwala da zikirin Allah suka zauna suna ta zikiri har cikin dare sannan shehu ZAJJADA ya mike ya daga hannu ya roki Allah ya kawo masu abinci daga arzikinsa. Nan da nan sai ga abinci da abubuwan sha iri-iri a gabansu, MAALIKUS-SAIF ya cika da dunbin mamakin ganin wannan abinci saboda baiga yadda ya kawoshi ba. Shehun ya umarceshi da yaci abinci amman kafin ya fara ci yace Bismillah. MAALIKUS-SAIF ya fadi haka ya fara dibar gara abinka da maijin yunwa. Haka yayita ci har saida yaji ya koshi sannan ya sha ruwa, sannan ya kwanta ya huta. Kwanciyarshi keda wuya bacci ya kwasheshi, shi kuma Shehun ya ci gaba da zikirinsa. Can da gari ya waye Shehun ya tada MAALIKUS-SAIF yayi masa wa'azi sannan ya kuma cewa ka dogara ga Allah, zaka kubuta da duk wani yanayi da ka samu kanka. Sannan ya zagaya da shi bayan wannan dutsen ya nuna masa yace yanzu kabar dokinka anan domin baya da amfanin tafiyar da zakayi dashi, ya nuna masa yace kabi gefen kogin nan kayi dama zakayi tafiyar kwana uku zakaga wani fili, bayan ka wuceshi zaka kuma ganin wani kogin mai matukar girma dan girmansa babu iyaka, to saika tsaya a nan. Akwai wata dabba mai suna HATSHA. Ita wannan dabba tunda Allah ya halicceta idan rana ta fito daga gabas tana daga tsakiyar wannan kogin sai tayita tsalle wai sai ta kamo rana, idan rana ta tsaya daidai a sama sai bakinciki ya kamata, sai ta fito da kanta daga bangaren gabas tayita turmutsa kanta a cikin yashi dan hushi, haka kuma idan rana ta koma gabas sai tayita tsalle da niyyar ta kamota har rana ta fadi, idan ta fadi nan ma sai ta fito da kanta a bangaren yamma ta rinka turmutsa kanta a yashi nan ma dan haushi. To idan kaga wannan dabba tana tumurmusa kanta a cikin wannan yashi to kar kaji tsoro ka kana gashin wuyan wannan dabbar ka dafeta, bazataji komai ba saboda girmanta, kai koda cikin idanunta zaka shiga bazataji komai ba. Ka zauna kana makale a kanta har ta maida kanta yamma, bayan ka sauka zakaga wani mutum, to ta dalilin wannan mutumin zaka samu wannan littafin. Daya gama wannan bayanin sai MAALIKUS-SAIF yayi godiya Sannan yabi wannan hanyar da Shehun ya nuna masa, ya shafe kwana uku yana wannan tafiyar har ya isa wannan filin da Shehun ya fada masa.... Anan zan dakata Zamu cigaba zuwa Gobe Ana yin comment yan uwa MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN littafi na daya 1 part 6 post by Shuraih 99% . Isar sa keda wuya kuwa yaga wannan dabbar tanata tumurmusa kanta a cikin yashi kamar dai yadda Shehun ya sanar dashi. Nan da nan sai yayi maza ya dane kanta har rana ta fadi,takai bakin gabar daga bangaren yamma, koda MAALIKUS-SAIF yaga haka sai ya fado daga kanta ji kake tik!. Ya tashi ya fara tafiya. Can yana cikin yafiya sai yaga wani mahayin doki a sukwane ya yi yo kanshi, koda mahayin yazo gab da MAALIKUS-SAIF da niyyar bankeshi sai MAALIKUS-SAIF yayi sauri ya banke dokin, haka suka rinka yi har sau shidda ko da mahayin dokinnan yaga haka sai ya zare takobinsa ya kaiwa MAALIKUS-SAIF Sara da suka shi kuma yana gocewa, hardai ya harzuqa MAALIKUS-SAIF, MAALIKUS-SAIF ya dubi mayin sai yace kaidai Allah wadaranka ragon banza, ai ba haka ake gwanimtar yaki ba, haka kawai mutum yana tafiya ka tasar masa dan ganin yana kasa Kai kana doki, kuma ga makami a hannunka, bari in nuna maka yadda sadaukai suke nasu sha'anin. MAALIKUS-SAIF yayi wuf! Ya damki wuyan dokinnan da hannun dama, ya kuma sake yin wif! Ya shaqo Wuyan mahayin da hannun hagu ya daga sama ya jinjina shi sannan ya saukeshi a hankalı ya ce "Kaga yadda sadaukai suke nasu lamarin". Da ganin haka sai wannan mahayim dokin ya sakko daga bisa dokinsa ya tsaya gaban MAALIKUS-SAIF ya yaye kyallen dake rufe a fuskarshi koda ya yaye sai MAALIKUS-SAIF yaga shema mace ce ba namiji ba ne ya dubeta yaga kyakkyawa ce, sai tace barka da zuwa MAALIKUS-SAIF Dan ZIYAZINUN koda yaji ta kira sunansa sai yace kekuwa yaya akayi har kika san suna na? bani labari mana. Yarinya ta fara da cewa "Suna na DAMATU, na samu labarin kane a wajen mahaifiyata wacce itace Sarauniyar bokayen birni KAIMARA, sunan ta Bokanya AKILA. Wata rana muna zaune da ita sai nace mata ta buga mani qasa taga waye wanda zai aureni, sai ta amsa mani da cewar Wanda zai aureki sunansa MAALIKUS- SAIF na ainahi amman yanzu ana kiransa da suna WAHASHINFALA, kuna asalinsa dan wani Sarki ne mai suna ZIYAZINUN Sarkin kasar hamra'u yemen amman yanzu yana qasar wani sarki mai suna AFARA'U, bayan an kwana biyu, sai tace mani shi wannan wanda zaki aura ya nemi auran wata yar Sarki aka nemi ya kawo kan wani dan fashi kuma gashi can ya dawo. To a wannan lokaci sai na rinka damunta da yaushe zai zo garin nan? Sai ta rinka ce mani ai ya kusa Zuwa, sai yau kuma dana sake tamayarta sai tace dani inyu maza ai gakacan ma ka iso, amman ta fada mani cewa inyi qoqarin yaqarka, indan naga baka da niyyar cutar dani sannan ka kama wuyan dokina sannan ya dagani daga ni har dokin, sannan ya saukemu a hankali to Wannan shine wanda zan aura, saboda haka kaji na kira sunanka kada kayi mamaki. Koda MAALIKUS-SAIF yaji wannan yarinya ta fadi wadannan batutuwa a kansa sai ya gasgata zancenta, amman a fili sai yace da ita "Ke kuwa wannan da qaryar tsiya kike, sannan kin iya shirya batu, domin wannan mutumin da ki ke fada to ni ba ni bane, kedai kawai kinyi niyyar ki yaqeni kikaga babu nasara shine kika shirya wannan zantuka". Koda 'DAMATU taji haka sai tayi murmushi sannan tace "Daman uwata ta fada mani cewa kona fada maka bazaka gasgata ba, kuma kazo wannan qasa tamu domin neman littafin tarihin NIL, kuma babata itace zata taimaka maka ka dauko wannan littafin. Tana gama wannan bayani sai ta yaye lullubin dake a fuskarta. MAALIKUS-SAIF ya dubeta ido cikin ido yace yanzu ina babar taki take? Tace tana gida, yace to mu tafi izuwa gareta. Sai DAMATU tace "A'a ai a kaidar wannan garin bako baya shiga, domin kuwa tarihi ya nuna wa mutanen wannan garin cewa wani bako ne zai zo ya sace shi wannan littafin tarihin NIL wanda ka fito nema, su kuma wadannan mutanen tun kaka da kakanni wannan littafin shine abin bautarsu, tun lokacin da suka samu labarin cewa wani bako ne zai zo ya sace wannan littafin sai suka tsafe garin, suka sana' anta wani gunki mai suna GAMMAZI wanda duk lokacin da bako ya shigo zai dinga îhu yana Ga... Bako! Ga Bako! Daga nan sai a kama bakon a yankashi wannan dalilin ne yasa bako baya shiga, amman duk da haka, babata ta fada mani cewa idan kazo qofofin shiga garinmu ka lissafa qofa ta tara sai ka duba zakaga wata bishiya a kusa da wannan qofar zakaga akwatu ka shiga ciki sannan ka girgiza igiyar sai mu jawo dakai daga cikin kwatun mu shiga dakai cikin garin. Koda DAMATU ta gama bashi wannan labarin sai ta haye dokinta ta tunkari qofar birnin nasu. Shi kuwa MAALIKUS-SAIF sai ya dinga bin sawun dokinta har ya fara hango katangar birnin KAIMARA. Daga nan sai ya juya bangaren gabas ya fara qirga qofofin shiga garin koda ya qirga ta tara, da ya hango kofa ta goma sai ya dosheta, Kamar yadda 'DAMATU ta fada masa, to daya isa bakin qofar nan sai ya boye ajikin wannan bishiyar da yake duhun dare ne ba wanda zai iya ganinsa, can yana tsaye jikin bishiyar nan sai yaga ana sako akwatu daga kan katangar, koda ya sakko qasa sai yaje ya shiga cikin wannan akwatu, sannan yaja murfin akwatin ya rufe ya girgiza igiyar sau uku. Su kuma can bokanyanya AKILA da DAMATU da sukaji an girgiza wannan igiyar sau uku sai suka jawoshi suka shiga dashi cikin birnin. Da suka isa gida, sai bokanya AKILA ta kawo masa abinci da ruwan sha, bayan ya gama sai ya kwanta, bayan ya huta sosai bokanya AKILA tace barka da zuwa MAALIKUS-SAIF Dan ZIYAZINUN.MAALIKUS-SAIF ya amsa mata da cewa yawwa, kazo wannan qasa tamu domin neman littafin tarihin kogin NIL, kuma nice zan taimakeka saka makon auren yata da zakayi. Koda MAALIKUS-SAIF yaji haka sai yace wai meye amfanin wannan littafin da har

Chapter 2 of 4