Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
jama'ar wannan gari suke bashi tsaro sosai kuma har suke bauta mashi? bokanya AKILA tace shi wannan littafin a cikinsa ne akayi bayani yadda za'a zuqo kogin NIL, kuma duk kasar data mallaki wannan littafin to fari na rashin ruwa bazata samesu ba, kuma qasar zata samu arziki da yalwa na albarkacin qasa, haka kuma duk mutumin da wannan littafin ya zamto a hannun sa to shi zai mallaki duniya. Saboda haka tin iyaye da kakanni mutanen wannan qasa suke girmamashi kuma suke bautamashi. Kuma tarihi ya nuna cewa wani baqo zaizo ya dauke shi wannan littafin, saboda haka ake bawa wannan littafin kyakkyawan tsaro. A wannan lokaci sai mutanen birnin KAIMARA sukaji gunki GAMMAZI yana cewa "Yaku mutane birnin KAIMARA ga bako ya shigo maku wannan birn?", ya fadi haka har sau uku nan da nan Sarki.. Ya fito shida tawagarsa aka rinka bincike lungu-lungu, sako-sako har dare yayi amman basuga wannan bakon ba. A can cikin gidan bokanyanya AKILA kuwa, MAALIKUS-SAIF yaji hayaniya ta yawaita sai yace da bokanya AKILA "Amman dai bazasu shigo nan ba ko?", sai bokanyanya tace "Kada ka damu bazasu shigo nan ba ya kuma tambayarta yace meyasa kikace bazasu shigo ba? bokanyanya tace ai duk manyan bokayen Sarki KABRUNU su dari uku da cittin (360) nice shugabarsu, a karkashina suke kuma su waddan nan bokaye sune suke tsaron wannan littafi dan haka ba yadda za' ayi su shigo wannan gida. MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN littafi na daya 1 part 7 post by Shuraih 99% . Da gari ya waye, Bokanya AKILA ta aika DAMATU gidan makwaftansu da yake masunci ne ta siya masu wani katon kifi, da DAMATU ta kawo sai Bokanya AKILA ta yanka kifin ta kwashe duka kayan cikin kifin ta saka qafafun MAALIKUS-SAIF a cikin kifin ta mayar da dinke cikin kifin; sannan ta dauko wani qaton tsutsu ta daura masa a wuya, sannan ta daura mashi igiya a girji, Sannan ta sakashu cikin rijiya, tace kada ka damu nayi maka wannan ne domin na bata hankalin bokaye ma' abota tsafi da Sarki zai sasu bincenka. Bokanya AKILA ta shirya ta tafi fada da zuwanta fada ta iske fada ta cika makil, ta fadi gaban Sarki tayi gaisuwa takoma mazauninta ta zauna. Zaman ta keda wuya sai Sarki KAMARUNU yace da ita daman ke muke jira, domin jiya GAMMAZI yayi mana kuwwa cewa wani bako ya shigo mana birni, to inaso ki sa yaranki su binciko mana inda wannan bako yake. Nan da nan Bokanya AKILA ta umarci wadannan bokayen dari uku da cittin (360) dasu buncika qasa su gamo inda wannan baqon yake. Bokaye suka dukufa suka zana alkalaman duba bisa rairayi suka shiga aiki, haka sukayita yu har tsawon wani lokaci, su zana su goge su sake zanawa su kuma gogewa su shafe... Can sai suka tsaya da wannan duban sukace munga wannan baqon. Koda Sarki KAMARUNU yaji wannan bokayen sunce haka sai yayi farat! Yace a ina kuka ganshi maza ku gaya mani. Can sukace shidai wannan bako gashi mun ganshi cikin duhu kuma kifi ya hadiyeshi, ga kuma wani tsuntsu ya ratayoshi, da sarki yaji haka sai yace wannan wace iriyar maganar banza ce kuke fada haka mara ma'ana. Sai Bokanya AKILA tayi farat ta rufesu da fada tace na fada maku cewa ku daina cin abinci da yawa domin yana hanaku kuyi aikin ku yanda ya kamata amman kunqiji ai ga irinta nan yanzu kun binciko wa Sarki shirme. Koda Sarki yaji haka sai ya fusata yasa hauni ya sare wa Bokaye biyar kawuna, sannan aka tashi daga fadanci. Koda Bokanya AKILA ta koma gida sai ta fito da MAALIKUS- SAIF daga cikin rijiya ta fito dashi daga cikin kifin sannan ta kwance mashi tsutsun data daura masa, kana ta kwashe duk abinda ya wakana a fada ta fada mashi. MAALIKUS-SAIF yace lallai kina da yawan hikima, badan kinyu mani haka ba da da tuni bokayen nan sun gano ni, haka sukayita fira da Bokanya AKILA tare da yarta DAMATU har dare ya raba sannan suka kwanta bacci. Da gari ya waye a rana ta biyu, Bokanya AKLA ta samo wata barewa ta daura mata fuka-fukan tsuntsu, sannan ta sa MAALIKUS-SAIF ya durkusa gaban barewar ta daura mashi ita ta kuma daura wata igiyar ta raba qafafun barewa da qasa, ta shirya ta yafi fada. Da zuwan ta fada sarki ya umarce ta data sa bokayen nan da su buga gasa su nemo inda baqo yake. Nan da nan bokayen nan suka tsundum aikı, can sai bokayen nan suka dago sukace sun ganshi. Cike da zumudi Sarki ya tambayesu yana ina? suka kada baki sukace ai gashi can wata barewa ta tashi sama dashi, nan da nan Sarki ranshi ya qara baci yace me yasa kuke kawo mani wasa ne? Kun tabajin ance yau ga barewa da fuka-fukai?, wannan ai rainin hankali ne yasa aka kuma yanka bokaye biyar nan dai fada ta tashi. Bokanya AKILA ta tafi gida tana dariya, taje ta kwance MAALIKUS-SAIF suka cigaba da hira. A rana ta uku Bokanya AKLA ta samo wata babbar tasa, ta yanka wata dabba ta juye jinin a cikin wannan tasar, ta kuma samun wata tasar da dora a cikin tasar da ta zuba jinin, Sannan ta umarci MAALIKUS-SAIF daya shiga cikin tasarnan zauna, bayan ya shiga ya zauna. Sai ta kama hanya ta nufi fada, isarta keda wuya ta umarci bokayen dake karkashinta akan su fara aiki. Nan suka dukufa, bayan wani dan lokaci suka dago sukace munga wannan baqon a cikin wani kogi na jini, sannan banda wannan kogin da yake ciki akwai wani kogin wanda shi babu komai a cikinsa, jin haka sarki ranshi ya qara baci ya umarci hauni daya kara sare kawunan bokaye goma, sannan yace da bokanya AKILA ke ya kamata ki duba mana inda wannan baqon yake tunda su sun kasa, bokanua AKILA tace to tunda yau saura kwana biyar bikin mu na shekara to a ranar zan kawo maka wannan baqo, koda jin haka sai fuskar Sarki ta fadada da murshi a haka aka tashi daga fada. Bayan kwana biyar yaune Bokanya AKLA tayiwa Sarki KAMARUNU alqawarin kawo masa baqon daya shigo wannan gari nasu. Tunda sanyin safiya MAALIKUUS- SAIF ya fara jin hayaniyar mutanen wannan gari, cikin firci ya tashi yace mekuma yake faruwa ne tace ai na manta ban fada maka ba yaune muke bikin shekarar mu kuma a cikin dakin da wannan littafin yake anan muke bikinmu, saboda haka kayi zamanka acikin gida nida hannuna zan kawo maka wannan littafin. Nan fa MAALIKUS-SAIF yanuna shi sam baiyarda ba saidai ta tafi tare dashi, dole kuwa hakan tayi tatafi tare dashi amman kafin haka saida ta bashi wani bakin ruwa na tsafi tace ya watsa qa jikinsa, watsarshi keda wuya yaga ilahirin jikinsa ya zama baki kamar yadda fatar 'yan garin suke, Bokanya AKILA ta bashi jakarta ta bokanci ya rike, tana tafe yana binta a baya har suka fito daga cikin gidan. Fitowarsu keda wuya suka tadda bokayen nan dake qarqashin Bokanya AKILA a bakin gidanta suna jiranta tana qarasawa inda suke suka dunguma sai dakin bauta, koda suka kusa shiga sai MAALIKUS-SAIF ya qarasa kusa da Bokanya AKILA ya miqa mata jakarta, ita kuma cikin rada ta qara jadda mashi kan cewa kada ya kuskura yayi yunqurin daukar littafin nan ya amsa mata da to amman badan ya yarda da shawararta ba. Koda Bokanya AKILA ta isa cikin dakin bautar sai gaba daya mutanen dake dakin bautar sukayi wa littafin sujjada bayan Sarki KAMARUNU ya fito dashi daga maboyarsa ya dorashi bisa wani taburi, ganin sunyi sujjada ga wannan littafin yasa MAALIKUS-SAIF ya taho a hankali cikin sanda, yazo inda littafin nan yake ya miqa hannu da niyyar ya dauko shi sai kawai yaga littafin ya fado qasa tim! Ya fara zagayeshi. Jin qarar fadowarshi yasa Bokanya AKILA; Sarki KAMARUNU da sauran jama'ar dake wannan dakin bautar suka dago daga sujjadar da suka yi, aiko sukayi ido biyu da MAALIKUS-SAIF, nan fa suka hau dukansa baji ba gani, MAALIKUS-SAIF shima ya hau dukansu, kasancewarsu suna da matukar yawa sai wani daga cikin.dakarun ya zagayo ta bayan MAALIKUS-SAIF ya sammaceshi ya bugesa a tsakiyar kai, nan take MAALIKUS-SAIF ya baje a kasa baiko shura ba, koda ganin haka sai Sarki KAMARUNU yayi godiya ga wannan littafi sannan ya umarci wasu dakarunsa dasu je su jefa MAALIKUS-SAIF cikin wata tsohuwar rijiya dake a bayan gari. Bayan sun dauki gawar sun jefata a wannan rijiyar ne suka dawo suka sanar da Sarki KAMARUNU. Sannan Sarki KAMARUNU yace da jama'a aci gaba da shagalin biki. Ita kuwa Bokanya AKILA koda taga an kashe MAALIKUS- SAIF sai hankalita yayi mugun tashi kasancewar tasan irin son da yarta "DAMATU takewa MAALIKUS-SAIF saboda haka ta sulale ta koma gida ba tare da sanin kowaba. Koda tafada wa DAMATU abinda ya faru a dakin bauta, kuka °DAMATU ta dinga yi da qyar Bokanya AKILA ta shawo kanta. ****** Alamarin MAALIKUS-SAIF kuwa ashe ba mutuwa yayi ba lokacin da aka MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN littafi na daya 1 part 8 post by Shuraih 99% . dokeshi a tsakiyar ka suma yayi, yana cikin wannan hali na suma wata aljana ta bayyana tsulim! A cikin wannan rijiyar koda ta daga hannunta sama sai wani ruwa ya dinga fita daga wannan hannu yana jiqa fuskar MAALIKUS-SAIF, jim kadan sai MAALIKUS-SAIF ya farfado daga suman dayayi, nan fa ya fara tariyo abinda ya faru dashi a dakin bauta, bai gama tunanin dayake ba yaji anyi sama dashi anfito dashi daga wannan rijiyar. Anan MAALIKUS-SAIF yayi godiya ga Allah madaukakin Sarki daya kubitar dashi daga cikin wannan rijiyar, to bayan ya gode ma Allah, sai ya tambayi wannan mutumin daya fito dashi yace kai kuwa wane ne kai? Mutumin ya dubi MAALIKUS- SAIF yace ni ba Namiji bane ni mace ce, kuma aljana, na kasance diyace a gurin Sarki fararen aljanu mai suna ABAYARU ni suna na AKISA, nan da nan ta juye ta koma budurwa. Kuma nazo nan ne domin wani taimako da zakayı mani. MAALIKUS-SAIF ya dubeta yace wane taimako kikace zan maki? Aljana AKISAA tace ya Dan uwana akwai wani bakin aljani mai suna MUTTADI'U. Shi wannan aljani kafiri ne mukuma musulmai ne, mun samu musuluncin mune a wajen wani bawan Allah mai suna Shehu Abdussalam. Wata rana wannan bakin aljani mai suna MUTTADrU ya sauka a Garinmu yace yazo ziyara, duk da karfin mulkin mahaifina amman yana tsanananin tsoron wannan bakin aljanin, saboda haka mahaifina ya saukeshi suka zauna afada suna fira. Can nazo wucewa da bakin aljanin nan ya dubeni sai yace yana sona, saboda tsananin tsoronsa da mahaifina yake sai yace masa ya bashi ni, ni kuma banason sa, saboda ba musulmi bane, hankalina sai ya tashi, nayi iya tunanina naga babu mai iya kubutar dani daga wannan bala'i da nake ciki, sai na yanke shawarar na tafi wajen wannan bawan Allah Shehu Abdussalam wanda ke garinmu, na fada masa halin da nake ciki na nemi ya taimaka mani. Da Shehun yaji haka sai yace Ai duk duniyar nan babu mai iya kubutar dake daga hannun wannan bakin aljanin sai wani mutum kuma Dan uwane gareki mai suna MAALIKUS-SAIF Dan ZIYAZINUN. Sai na tambayeshi inda zan sameka sai ya ce mani Inkoma wajen babata zata gaya mani inda kake. Dana koma Gida sai na tambayi uwata shine take bani labarin cewa ai yanzu wasu aljanu daga kasar KAIMARA suke bata labarin cewa gashi can a jefashi a cikin wata rijiya, maza jeki ki kubutar dashi to shine kaganni nazo to kaji abinda nakeso ka tainmakeni ka kubutar dani daga wannan baqin aljanin. Da MAALIKUS-SAIF ya gama jin wannan batu daga bakin AKISA sai ya shafa bulalarsa yaji tananan, sai yace in sha Allahu zan kubutar dake daga hannun wannan bakin aljanin. To amma kuma naji kina cewa ni Dan uwanki ne, ya akayi ni ina mutum ke kina aljana har na zama Dan uwanki?. AKISA tace uwata ta sanar dani cewa ai kaima danta ne domin tare ta shayar dani da kai nono lokacin muna jarirai. MAALIKUS-SAIF yace to ya sunan babar taki? AKISA tace DASUKATU. Koda MAALIKUS-SAIF yaji wannan suna sai yace na yarda ke yar uwata ce, to yanzu saikiyi maza ki kaini wajen wannan uwa tamu. Kafin ya rufe bakinsa sai ga DASUKATU ta dira dif! a gabansa yana ganin haka ya rungumeta, yana ce Mata mai yasa kika rabani da ku shekaru da dama. DASUKATU tace ya Dana munyi maka haka ne domin zamanka a wajenmu bazai yiwuba saboda dabi'un mu da naku na mutane sun banbanta, shiyasa ya zama mana dole muka mayar dakai ga mutane yan uwarka, yanzu maza ka hanzarta domin kubutar da yar uwarka. Da gama wannan magana sai tayi masu sallana ta tafi. MAALIKUS-SAIF ya kalli AKISA yace To yanzu sai ki daukeni ki kaini wajen wannan aljani. AKISA ta dauki MAALIKUS-SAIF ta tashi dashi izuwa qololuwar sama tayita tafiya dashi, can sai AKISA ta tsaya da tafiya ta sakko kan wani dutse, ta nuna masa wani tsauni ta ce Kaga wancan tsaunin to akansa gidan wannan aljanin yake. MAALIKUS-SAIF yace "To shiken an tsaya anan ni na shiga na fito", yakama hanya, daya isa gindin tsaunin nan yai zagaye ya rasa inda zai kama ya hau, yana cikin haka sai yaji ana kiran sunan sa daga saman tsaunin nan, ya daga kansa sai yaga wasu yan mata ne suke dago masa hannu suna kiran sunan sa. Sai suka zuro masa igiya ya kama, suka jashi harkan tsaunin nan. Da MAALIKUS-SAIF ya hau kan dutsen nan sai yaga yawan yan matan nan yakai su Arba'in,kuma dukkansu yan matane kyawawa, sai daya daga cikin su wadda kamar itace shugabarsu mai suna NAHIDA tace ai jiya a cikin baccina naga Annabi HALLIRU laihissasatu Wassalam, yace inbada Gaskiya akan addinin Annabi Tbrahim Alaihissasatu wassalam, ya musuluntar dani Sannan ya fada mani cewa yau akwai wani mutum mai suna MAALIKUS-SAIF zai zo ya kubutar damu, ya kuma fada mani cewa ni ina daya daga cikin matayen da zaka Aura, shine na fito ina baiwa wadannan yan uwa nawa labari sai muka leko muka ganka. MAALIKUS-SAIF ya tambayi yan matan nan ku kuma me ya kawoku nan? NAHIDA tace ai mu duk nan daka ganmu yayan Sarakuna ne, ganinmu da kayi anan wannan aljanı shiya kwasomu ya kawomu nan, dama shi dab1arsa shine duk inda yaga yar Sarki kyakkyawa to sai ya daukota ya kawota nan, ahaka duk ya taramu anan. Da MAALIKUS-SAIF yaji wannan bayani sai ya tuna lokacin dashi wannan aljani yaje zai dauke SHAMATU ya sare masa hannu daya, suna cikin haka sai suka ji wani rugugi da hayaqi ya tunkaro su, sai matan nan suka ce wa MAALIKUS-SAIF ya gudu ya nemi wajen buya domin ga aljanin nan ya dawo. MAALIKUS-SAIF ya ce Ku barni dashi babu inda zani, yan matan nan suka shige cikin wani daki suka bareshi tsaye a waje. Jim kadan sai ga aljanin nan ya bayyana, koda yaga MAALIKUS-SAIF sai yace yauwa daman kaine ka taba sare mani hannu yau gashi kazo har gidana, kaga sai na rama na kasheka nima. Koda gama fadin haka sai aljanin nan ya miko hannu d nufin ya kama MAALIKUS-SAIF. Cikin zafin nanma MAALIKUS-SAIF yayi wuf! Ya zaro bulalar sa ya tsula wa aljanin nan. Nan take aljani ya kama da wuta yana kururuwa yana ihu yana ya kasheni! Ya kasheni...! Cikin lokaci kankani aljanin nan ya qone kurmus, ya baje kamar turbaya. Da yan matan nan sukaga haka sai suka fito a guje suna murna, shi kuma ya yi kiran AKISA ta taho ta shigo wajen. Koda taga ya kashe wannan aljanin sai tace Ya Dan Uwana na gode wa Allah, na gode maka daka kubutar dani daga sharrin wannan aljanin, ni kuma babu abinda zanyi na saka maka illa kawai na rika maka hidima. MAALIKUS-SAIF ya umarci AKISA da ta dauki yan matan nan duk ta mayar dasu kasashensu kuma idan ta mayar dasu ta sanar da iyayensu cewa shine ya kubutar dasu. Nan da nan AKISA ta rika daukar yan matan nan tana mayar dasu qasashensu, sannan tayi bayanin kamar yadda MAALIKUS-SAIF ya fada mata, da haka har ta kwashesu kaf ya rage saura NAHIDA kadai. MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN littafi na daya 1 part 9 post by Shuraih 99% . AKISA tazo zata dauketa amman sai taqi. MAALIKUS-SAIF yace Ki tsaya mana ta daukeki ta mayar dake wajen iyayenki. Sai tace "Ai ni tunda Annabi HALLIRU ya fada mani cewa ina daya daga cikin matan da zaka aura to ba inda zani ina tare da kai duk inda zaka kuwa". Da MAALIKUS-SAIF yaji wannan magana ta NAHIDA sai ya tambayeta yace "Ke mutumiyar wace qasa ce'?" ta amsa mashi da cewa "Ita mutumiyar birnin Sin ce, kuma ubana shiyake mulkin wannan kasa". MAALIKUS- SAIF ya amsa da cewa "Naji kuma zan Aureki to ammanfa ki sani bazan aureki ba har saina auri SHAMATU DA 'DAMATU tukunan. Saboda haka yanzu ki koma qasar ku". Tayi nacim duniyar nan amman yaqi, koda ganin yaqi yarda sai tayi masa wata addua tace "To tunda kaki insha Allahu duk lokacin da zaka shiga garinmu, dagakai sai wando zaka shiga". Shikuma sai yace "Ni kuma insha Allahu lokacin kina a makance zan shiga, bazaki ganni a tube ba" Dukkansu kuwa sa aka amsa masu adduarsu. MAALIKUS-SAIF ya umarci AKISA data dauketa ta mayar da ita kasarsu. AKISA ta kaita ta dawo da AKISA ta dawo sai tace da MAALIKUS-SAIF to ya Dan Uwana in kanaso zan kaika birane bakwai mafiya kyau a Duniya?MAALIKUS-SAIF yace "Eh inaso ki kaini nayi kallo, amman kafin nan inaso ki kaini wajen Shehun nan na garinku nayi masa ziyara. AKISA ta daukeshi suka tafi. Da zuwansu, sai MAALIKUS-SAIF yaga wata hasumiya. AKISA tayi sallama sai sukaji daga ciki an amsa masu da cewa Barka dai MAALIKUS-SAIF Dan ZIYAZINUN. Suna tsaye sai wani Tsoho ya fito. MAALIKUS-SAIF ya tambayi AKISA yace Shikuma wannan Tsohon wanene shi? AKISA tace "Ai shine Shehu Abdussalam din da nake baka labari". Suka yi musabiha shida MAALIKUS-SAIF yajashi ya shiga kogon dashi yana fada wa MAALIKUS-SAIF wasu nauoi da sigogi na zikirin Allah. Bayan sun kammala ne Shehun yace ka zauna ka kwana anna ni gobe zan mutu, bayan na mutu kayi mani wanka ka daga kasan shirmfida ta zakaga likkafani sai ka lillibeni dashi. Sannan sai ka fita waje kofar hasumiyar nan kayi kira sallah, zakaga mutane ta sama da qasa sunata zuwa kar kayiwa kowa magana, kuyi zana' ida tare da mutanen nan bayan kun gama, zakaga ba kowa a cikin mutanen nan. Sai kaima ka binneni ka kama gabanka. Haka kuwa akayi gari na wayewa Shehun nan ya cika. MAALIKUS-SAIF yayi jana'idar yadda Shehun nan ya fada masa. AKISA tazo tace Ya Dan Uwana idan ka shirya to zan kaika birno na farko, MAALIKUS-SAIF yace Na shirya. AKISA ta daukeshi suka samu Kamar sa'a daya a suma suna tafiya, sai suka isa ganuwar wani birni AKISA ta sauka tace "To dan uwana gamu a qofar birni na farko, yanzu sai ka shiga ka fito ni bani da ikon shiga wannan birnin, domin akwai kafi wanda zai iya koneni idan har nayi kuskuren shiga. MAALIKUS-SAIF ya kama hanya ya shiga cikin wannan birni na farko. Da shirsa sai yaga nmanyan gine gine masu matukar kyau, sannan da Abubuwa masu balain kyau, yaita yawo yana kallo. Can sai ya iso wani fili yaga wasu mutane sunata fada. Koda suka ganshi sai duk sukayo kashi, daya daga cikin su yace "Yakai wannan baqon sai ka raba mana rikicin dake tsakanin mu. MAALIKUS-SAIF yace Wane rikici zan raba maku? babban yace nida Dan Uwana mahaifinmu ya kasance shine baban malami a wannan birni, sunansa Malam AFLADIN, ya mutu ya barmana gadon wata hula, wadda ita wannan hula ta tasance indai ka sakata to mutum ko aljan babu mai ganin ka. To shine muketa rigima akan ko wannenmu yanason ace shine ya gaji wannan hula, dama kafin kazo mun yanke shawarar duk wanda yazo ya samemu to shi zai Yanke hukunci a garemu, sai kuma gashi kazo, to muna so yanzu ka raba mana wannan rigima tamu. Da MAALIKUS-SAIF yaji haka sai yace "To zan rabamaku wannan rikici, ku bani kwari da baka zan harba ta duk wanda a cikinku ya fara dauko ta, ya kawo mani ita nan to wannan hular tazama tashi. Wadannan yan uwa biyu suka amince da abinda ya fada, suka bashi kwari da baka gami da hular ya rike a hannunsa. MAALIKUS-SAIF ya harba kibiya duk mutanen suka saki dawakansu suka bazam neman kibiya, suka barshi a tsaye da hula a hannun sa, can bayan wani lokaci sai MAALIKUS-SAIF ya hango daya daga cikin mutanen nan ya dawo a sukwane, kafin ya karaso sai MAALIKUS-SAIF ya raya a zuciya sa cewa To niko in gwada wannan hular in gani in gaskiya suka fada mani akan wannan hular, sai MAALIKUS-SAIF ya saka Wannan hular. Koda mutumin ya qaraso wajen sai ya rinka kwada kira yana yakai wannan alkali namu ina kashiga gani na dawo da kibiyar, yayita diri diri. Koda MAALIKUS-SAIF yaga mutumin baya ganinsa sai yace a zuciyarsa "To lallai na yarda da lamarin wannan hula idan kasa mutum baya iya ganinka, yanzu saura na gwadata akan aljani nagani, can sai ya tuna ai AKISA aljanace bari yaje ya gwadata akanta. MAALIKUS-SAIF yai tafiyarsa yabar wannan mutumin yanata diri-dirin neman sa, daya fito ne ya iske AKISA tana tsaye tana jiransa yazo gabanta ya tsaya amman duk bata ganshi ba, saiya kira sunan ta *Ya 'yar uwanta AKISA". AKISA tayi wani turus! "Tace kana ina ne Dan Uwana, kardai ace kasamo hular nan ta Malam AFLADIN? MAALIKUS-SAIF yace kina ganina? "Tace A'a bana ganin ka kana inane?" Koda MAALIKUS-SAIF yaji haka sai ya godema Allah daya bashi ikon mallakar wannan hula, Sannan ya cire hular da hanninsa sai AKISA ta ganshi a gabanta, ya kwashe labari kaf game da yanda akayi ya mallaki wannan hula ya fada wa AKISA. "Ai manyan sarakuna da dama na samu labarin sun rasa rayukansu akan neman wannan hula, amman kai gashi ka sameta a sama" AKISA take bashi labari, taci gaba da cewa MAALIKUS-SAIF to yanzu saika shirya na tafi dakai izuwa birni na biyu. MAALIKUS-SAIF yace to yanzu karbi hulata ki ajiye mani, tana karba yace da ita to muje na shirya. MAALIKUS-SAIF da AKISA suka kama hanyar birni na biyu nan ma dai AKISA ta saukeshi a kofar shiga gari yai mata sallama ya tinkari kofar shiga garin, da shigar MAALIKUS-SAIF garin sai jama' ar garin sukayiwo kansa suna ga bako! Ga bako...!Suka taso masa zasu kamashi sai rigima ta barke a tsakaninsu suna dukanshi shima yana dukansu, ahaka hardai sukaci karfinsa suka kamashi suka kaishi wajen Sarkin su. Shi Sarkin wannan gari sunan sa Sarki DUHANI, ita wannan qasa suna da wani zobe wanda duk wanda ya mallaki wannan zoben to shine zai zama Sarkin wannan gari, saboda shi wannan zoben shi suke bauta mawa, sannan idan aka nuna mutum da wannan zoben sai kanshi ya guntule y fadi qasa, a wannan lokaci Sarki DUHAN shiya mallaki wannan zoben, saboda haka ya zama Sarki. Sarki DUHAN ya dubi MAALIKUS-SAIF yace "Kai ko mai ya kawoka qasata?" MAALIKUS-SAIF yace "Nazo ziyara ne da kuma yawon bude idanu." Da Sarki haka sai yace Shine kuma kazo ka fara fada da mutanena harka kashe mani wasu daga ciki. Sarki yayi umarni ga wani babban bawansa da ya tafi da MAALIKUS-SAIF gida yayita gana masa azaba har sai gobe da safe a dawo bakin kogin dake gaban gidan Sarki a fito dashi a kasheshi. BULAKI ya kama MAALIKUS-SAIF ya tafi dashi ya kaishi cikin wani daki yayita azabtar dashi har dare ya raba sannan ya koma dakinsa ya kwanta. MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN littafi na daya 1 part 10 post by Shuraih 99% . Can bayan wani lokaci, MAALIKUS-SAIF yana a daure sai yaga BULAKI ya shigo dakin ya fadi gabansa yace ka gafarceni ya Sarkin Sarakuna MAALIKUS- SAIF Dan ZIYAZINUN ka gafarceni. Koda MAALIKUS-SAIF yaga haka sai yace "Ya ya haka kainefa kayita azabtar dani dazu kuma yanzu kazo mani da wannan maganar." BULAKI ya nisa yace "Ai yanzu cikin baccina naga Annabi HALLIRU ya musuluntar dani kuma yace dole na kubutar dakai. Nan da nan BULAKI ya kwance MAALIKUS-SAIF, ya kawo masa abinci yaci ya koshi sannan ya kawo masa ruwan sha, sannan ya kara jadda musuluncinsa a gaban MAALIKUS-SAIF. A wannan dare BULAKI yabi duk mutanen gidan ya musuntar dasu sai wata baiwa kwaya daya data ki musulunta, akayi akayi amman taki. Nan BULAKI ya kamata ya daure yace "Gobe Zan je ya jefata ruwa a mainakonka." MAALIKUS-SAIF yace "Tunda kai yanzu musulmine Zan canja maka suna daga yau ka koma Abdussamad." Gari na wayewa Abdussalam ya fito da wannan kuyangar lullube dan ayi tunanin MAALIKUS-SAIF ne, yazo da ita bakin kogi ya tsaya. Jim kadan sai Sarki ya leqo ta taga, yai Umarni da Abdussamad daya kashe MAALIKUS-SAIF shi a tunaninsa kenan amman baisan ba MAALIKUS-SAIF bane. Bayan Abdussamad ya kashe wannan kuyanga mai taurin kai. Sai Sarki yayi nuni da hannunsa daya jefa gawar cikin ruwa. Abdussamad ya jefa gawar cikin ruwa ya koma gidansa. A lokacin da Sarki yayi nuni da hannunsa da a jefa gawar cikin ruwa bai saniba ashe a wannan lokaci zobensa ya subuto ya fada cikin ruwan. Zoben na fadawa cikin ruwa sai wani kifi ya hadiyeshi a tinaninsa abinci ne. Da isar Abdussamad gida sai yace da MAALIKUS-SAIF "Mai kake da sha'awa yanzu na kawo maka?" **Yace kifi nakeso naci yau domin naji ina marmarinsa. Abdussamad yace Kash! Sai dai babu sauran kifi a gidan nan amman bari na fita nayi fatsa na kamo maka. Da MAALIKUS-SAIF yaji haka Sai yace kaga kuwa nima ina da sha' awar fatsa bari mu tafi tare. Abdussamad ya yarda da hakan suka tafi wannan kogin da suka jefa wannan kuyangar, can suna fatsa sai suka kamo wani katon kifi ganin kifin yana da girma sai suka hakura suka taho dashi kadai gida. Abdussamad ya yanka cikin kifin a dafa, koda ya kwaso kayan cikin

Chapter 3 of 4