Reading Fara Yar Shehu by SHATUUU Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng [3/16, 7:48 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻



_ONE_




✍🏻 *SHATUUU❤*

_Jakadiyar kainuwa_




💖Shatuuu095@ wattpad




*‫*بسم الله الرحمن الرحيم‬




*____________________________________*




*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*




Sunana Asma'u Shahada, Mahaifina Dan sanda ne Wanda ya taka Har matsayin CP that's commissioner
of police, sede yayi retire a halin Yanzun. Amma dukda haka baya zama saboda shi mutum ne me kazar
kazar, he's a patriotic citizen, never believe in zaman banza. yana da gonaki inda shi ne invest dinsa, to
kusan kullum se yaje, hakan yasa koda yayi yayi retire amma bai huta ba.



Asalinmu Yan Taura ne ta Jigawa, cikin garin Kwalam, kakanni na a Kwalam suke. Malam Aminu shi ne
kakana da ya haifi Mahaifina, manomi ne sosae, if I can say Abba anan yayi gadon noma, Don idan kaje
kofar kudu kace gidan Sarkin Noma, don't be amaze amma kowa ya sanshi. Inna Ade ita ce mahaifiyar
Abba, sunanta Sa'adatu, so se aka cire karshen Sa'ade ake kiranta Ade. Nasha ayyanawa da kuma
tunanin yadda akai har zaman Alhaji da Inna Ade Yayi wannan doruwar. Alhaji mutum ne me hakuri da
kauda kai, bazaka taba fahimtar fadanshi Ko Maganar shi ba cuz the tone is always same. Inna Ade kam!
Jarabar duniya, matar tana da fada na bugawa a Jarida, so far, zan iya cewa akwai possibility din Tasha
ruwan Atafi da ake fada saboda sunyi zaman hadejia. Lol. Amma duk wannan hayaniyar tata, bana gani
saboda muna mugun good time da ita, Tana sona kuma tana fito na fito da duk Wanda ya nemi
takurawa rayuwata, koda Abba ne ko Ummaah, Yanzu Yanzu zata wanke su tas tas, su da suka haifeni
kenan balle kuma yan uwana da ba ganinsu take da gashin Kai ba, wannan ai sede dan kansu su bar
mata gurin. I knew her Best side so far.



'Ya'yansu takwas, Hajiya Uwani ita ce babbar yayarsu Abba, Tana aure a Majia ta Taura garinsu Nanaye.
Tana da Yara wajen goma, kuma baki daya matar photocopy din Inna Ade ce plus Wasu mugayen
halayenta Wanda basuda asali bare kuma tushe. Daga ita se Abba shi ne Shahada, kuma Mahaifina, na
yadda partially da mutane su kace ana inheriting Uwar miji a gurin haihuwa, yeah akanmu Hakane. Abba
shi daya Shi ne namiji, surrounded by sisters, haka nan Ummaah, kuma haka muke a gurinta.



Daga Abba se Umma Falmata, Tana can Adamawa anan take aure, dake Inna Ade asalinta daga can take.
Asalin bafullatana ce, bansan yadda akai ta aura Alhaji ba, har ya dakko ta tun daga Uwa duniya Har
Kwalam. Mabiyar ta Anty Hauwa ce, boss kenan, se Anty Shamsiyya , Anty Mero sai Anty Rakiya da Adda
Ummiey wadda ita ce autarsu, kuma a gidanmu ta tashi, Dan Saar Adda Habiba ce, Tare akai musu aure
abinsu.



Sauda Ummaah bakanuwa ce 'yar koki, mahaifanta dukkansu yan nan cikin kanon ne. Ummaah ita kadai
ce mace a gidansu, dukkan Yan uwanta maza ne, amma Dayake Allah shi yake tsarinsa bakwai daga
cikinmu Duka mata ne se namiji daya tal. Babbar yayarmu Adda, Tana aure anan Kano, wani yaron Abba
ta aura, me bi mata Yaya Halifa, sunan Alhajin Kwalam ne dashi shiyasa sunanshi yake a boye. Shidai
baiyi aure ba se Karatu kamar zai cinye Boko, Yayi degree, Yayi Msc, banda PgD da yayi, da courses
kanana kanana. Yanzun Haka PhD yakeyi. Duk gidanmu ni ce nafi shiri dashi saboda Ina son Karatu, I find
joy and happiness in studying. Wannan yasa na zama Kamar kawarshi, I enjoyed been with him. Adda
Sa'ada ita ce takwarar Inna Ade, as we all know a gida idan kana da takwara you seems to be in the most
goodest relationship da ita, wannan karya ne when it comes to Inna Ade and Adda Sa'ada basu shiri Ko
na mintina daya, hardly ka gansu tare. Tana aure a Niger state, Adda Habiba Saar Adda Ummiey ita ce a
dutse, se Adda Meeyna, Adda Salma da Adda Maryam se ni kuma auta Kare nono as they always call me.



1995 aka haifeni, Ummaah da Inna Ade, sun bani labarin ranar da zaa haifeni, ranar kawar Inna Ade
wadda ita ce Asma'u. Kawarta ce sosae, tun suna Yanmata Har seda akai musu aure. Kunsan aikin police
federal aiki ne, so transfer Ko da yaushe ana cikinta. Amma lokacinda Ummaah ta samu cikina, shi ne
lokacin da Abba yake ASP a kano, I was lucky baayi tafiye tafiya da cikina ba.



Ranar Alhamis ce, dake Inna Ade, in har Ummaah Nada ciki to duk sati se Tazo, Har Se Ummaah ta haihu
kafin zata tattara ta tafi, wannan zaman an dinga balai da ita, musamman itada Adda Sa'ada, wani
lokacin Abba ke raba fadan. Ile kuwa ranar sun gama yinta, Adda Sa'ada tayi girki Inna Ade tace Allah ya
kasheta, ita tuwo zataci, Adda tace ita kuwa kitchen ta gama shigarshi a wannan ranar sede Inna tayi da
kanta.



"Saude Saude! Ki fito Ki raba Dani da wannan shedaniyar yar taki"



Ummaah na daki, ita kadai tasan halinda take ciki, ta jiyo kiran da Inna Ade ke yi mata, Ta sani Ko Baa
fada ba, Adda Sa'ada ce kawai Inna zata dinga ihu akanta. Gaba daya ta jike da gumi sharkaf, ta fito da
kyar, daidai karasowar Inna Ade, Tana mitar rashin amsata da Ummaah tayi, kicibis sukai, abinka da
Manya tana kallon fuskar Ummaah, tasan nakuda take, babu bata lokaci ta saka wani cousin din Abba,
kawu balarabe wanda ke zaune gidanmu Ya dakko Mota suka wuce asibiti.
Ana karbar ta, Inna ta saka a sanar da Abba, Allah Ya taimaka ya tashi a aiki, hakan yasa ya nufo asibitin,
Babu jimawa aka fito Dani cikin zani an haifeni, Inna Ade tace min kwatakwata da karbata baifi mintina
uku ba, sakon rasuwar kawarta Asma'u ya iske ta. Ta shiga Tashin hankali marar misaltuwa, Inna Ade tayi
ta kuka Abba yana lallashinta. Duk yadda akai ta hakura amma taki, se fadin



"Shahada, idan zaka saka a kaini Jimeta ka saka, idan baka sawa ka barni na tafi! "



Babu yadda ya iya haka yasa a ranar aka tafi da ita Jimeta. Seda akai kwana uku sannan ta dawo. Tana
dawowa kuwa tace lallai sunan aminiyarta Zaa maida min. Ranar da na cika kwanaki bakwai aka rada
min sunan Asma'u, Inna Ade tana cemin FARA 'YAR SHEHU!



Na tabbatar once a rayuwar Abba da Ummaah, Sunyi regretting saka min wannan sunan, ba Dan komai
ba se Dan Inna Ade. Duk weekend din duniya tana kano Tare dani, as I heard, bakina da sunanta Ya Fara
budewa, sunanta na Fara kira.



Nayi shekaru biyu aka bawa Abba commissioner of police, sannan aka masa transfer zuwa Taraba state,
inda anan ne Zaiyi commissioner din. Aka kammalla dukkan shirin tafiya, amma Inna Ade tayi tsalle tace
babu me tafiya Dani, a gurinta zan zauna. Inna Ade yar daru ce ta gaske, waye Zaiyi musu Abba ko
Ummaah? Babu. Haka aka tattara ta tafi Dani Kwalam su kuma suka wuce Taraba abinsu.



Da wannan rayuwar na tashi, babu Wanda na sani se Innata, a Haka Har na Fara Wayo nakai shekara
hudu, duk lokacinda Abba yazo da niyyar tafiya Dani Dan Ya sani a makaranta, Se Inna ta Fara kuka,



"Shahada akan yarka zaka nuna min iyakata? "



Ummaah ta lallabashi Badan ransu yaso ba, suka kyaleni a gurinta, amma seda aka kaini central primary
school dinsu. Ni mutum ce me wasa da kiriniya, I pay attention to nothing, so ko da mukai exams, it was
beyond comment, ni na dakko ajin. Abba Kamar Zaiyi kuka Dan takaici, Yaya Halifa kam Kirirkiri Ya fito
sukai ba dadi shida Inna Ade, bata kulashi ba saboda Tana yawan cewa, ita tasan darajar miji, so shi yana
cin darajar sunanshi Aminu.
A Haka rayuwa ta cigaba da gungurawa, kullum hankalin iyayena yana kaina, as for me duk tunanina
Inna ta haifeni, su ina daukarsu kawai yan uwanmu, Kamar yadda naga Sauran na zuwa. Seda nayi
shekara bakwai sannan nayi wata rashin lafiya wadda seda muka kwanta a Aminu Kano. Munfi wata
sannan na samu sauki, wannan shi ne asalin dawowata gidanmu, Inna ta hakura a cewarta kada mayu su
lashe mata kurwata. God so kind!




Surprised? Ooooo




Ayshatuuu

[3/16, 7:48 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻



_TWO_




✍🏻 *SHATUUU❤*

_Jakadiyar kainuwa_




💖Shatuuu095@ wattpad
*‫*بسم الله الرحمن الرحيم‬




*____________________________________*




*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*____________________________________*




Bayan dawowata abinda aka Fara kokarin yimin, shi ne makaranta. Dayake lokacin Ummaah ta gaji da
binshi, se sukai settling baki daya a kano, shi kuma Yana zuwa ya koma. Adda Maryam kadai ke primary
lokacin, itama kuma Tana Basic 5, a excel college. Spring aka kaini duk dan na dan farfado daga asarar da
akai, Basic 1 aka kaini, amma matsalar ko two letter words ban iya ba. Bazan taba manta wannan abin
ba.



Ranar da aka Fara kaini school din, Inata murna abuna, saboda uniform din kawai birgeni yake, ga lunch
box dina, Ummaah ta shake shi da chips, ga Caprisonne. Oolala! Yaya Halifa ne ya Fara kaini, seda ya
rakani Har class sannan Yayi min kashedi, tareda fadawa uncle din ya saka min ido sosae, Aikuwa Ya
saka, dan na amshi wuya hannun bawan Allah nan.
Abinda ya Fara sakawa na karaya nafi kowa girma a ajin, saboda Inada Girman jiki, ga yawanci duk sun
iya turanci ni kuwa daga come and go babu abinda na sani, gashi Baa vernacular a school din. Se ya
zamana idan na shiga har a tashi bana magana, saboda na taba gwada surutu da Hausa, aka fadawa
uncle Ya zaneni. Tun daga lokacin na daddara bana taba gigin yin surutu.



Idan na dawo gida bayan an tashi lesson, islamiyya ce zamu tafi nida su Adda, bazamu dawo ba se 5:30.
Da anyi Sallar Maghrib, Yaya Halifa zaizo da Belt in dakko books dina, ina kuka Haka Zamui homework
dina sannan ya koya min sabon abu, wannan belt din na gefe, bawai dukana Zaiyi ba amma ita ta
barazana ce. Karshen dukan shi ne rankwashi. Duk yadda nake son kallo musamman cartoon banayi, ana
gamawa zanyi Sallar ishai na kwanta. Cikin sati biyu gaba daya na fita a hayyacina saboda ban saba irin
wannan rayuwar ba. Rayuwar Kwalam babu sawa bare takurawa, kullum se nayi kukan zan koma gurin
Inna amma babu me kulani, se idan Boss din gidan tana nan Adda Salma ta bubbuge ni, so shirina da ita
kadan ne.



Ana haka aka kawo wani new student, Emma a class dinmu, Shi duk yafi mu, gashi azzalumi babu hasken
musulinci tattare da yaron nan, tunda yazo shikenan Sauran walwalar da nake da ita ta tafi. Ya rigada ya
gane ban iya turanci ba kuma ko yayi min abu I can't express myself hakan yasa yake cin zalina shida
gang dinsa. Ranar duka gida aka makara, so ko breakfast bamuyi ba haka muka taho se daga baya
Ummaah ta aiko driver ya kawo min Abinci, Inata murna saboda azabar yunwar da nake ji, amma ina
karbowa Emma da mutanenshi suka karbe abincin, Ina kallo suka cinye, Aikuwa Na dinga kuka na tafi
gurin uncle, it was embarrassing. Ina zuwa yace min



"Asma'u what happened? "



Gaba daya na diririce saboda bazan iya cewa "He ate my food" ba haka na gaji da tsayuwa na koma na
zauna. Shikenan suka gane lagona Har dukana suke, gashi ni kuma a gida haushin kowa nakeji, ina ganin
duk su suka jawo min, da ace Ina Kwalam waye zaimin haka? Ai babu shi idanba so yake yaga
kaddamarwar Inna Ade ba.



Da sassafe Adda Meeyna na shirya ni, Inata kuka, kallona tayi tace



"Menene Wai? Yau kwana uku kenan kullum se Kinyi kuka. Makarantar ce baki so? "
Kaina na gyada, Wasu hawayen na sakko min nace



"Ni bazanje ba Adda zazzabi nake"



Wuyana ta taba sannan tayi dariya tace



"Yar gidan Inna, babu wani zazzabi fa, kede kawai kin zama yar baci"



Muna haka Adda Sa'ada, service take anan Kano, kuma mijinta ya tafi wani official assignment a Urk, ta
shigo tana fadin



"To! Autar Ummaah me ya faru? "



Nan Adda Meeyna ta fada mata yadda mukai da ita. At this stage, iyaye ya kamata ku lura da wani abu,
bullying yafi karkata a primary school, sosae Wanda suka fi karfinsu suke zaluntar su. Shiyasa yaro zai
dinga kukan makaranta, saboda Wasu lokutan Yaran Zaa iya threatening dinsu su kasa fada, ya kamata
kowacce Uwa ta zama alert.



Shiru Adda Sa'ada tayi sannan ta kama hannuna muka fito, Ummaah ta fito dauke da bag pack dita,
ganin fuskata kacekace da hawaye yasa taja ta tsaya, fuskarta da damuwa tace



"Uwata" Kamar yadda take kiran Adda Sa'ada, da yake Baa boye mata sunanta, "Me Ya sameta? "



Inajin tayi wannan tambayar na kara kwabe fuska, Inata kuka, Inaji Adda Sa'ada nayi mata bayani, dake
Ummaah classroom teacher ce, take ta fahimci abinda yake faruwa. A ranar tare dukka mukaje school
akai complain, haka a gaban class aka Zane Emma, shikenan na samu sauki, kuma na dage na Fara
turanci, idan nayi ai tayumin dariya amma a hankali da taimakon family na, na samu nake iya hada
sentence.
Har term din ya kare babu Inna Ade babu dalilinta, haka muma bamu samu Munje Kwalam ba, in banda
Ummaah da Abba, nayi mitar nayi kukan har na hakura abuna. Ranar da akai Hutu na dawo Inata murna
Dan zan dan huta at least, Tundaga tsakar gida nake jiyo muryar Inna Ade, matar is very lousy, inhar tana
guri some miles away zaka dinga jiyo muryarta, bansan lokacinda na sake lunch box dina da school bag
ba nayi parlor a guje ina fadin



"Inna Ade! "



Kanta na fada nayi mata wata runguma me karfi, itama rungumeni tayi tana shafa jikina tareda fadin



"Fara 'yar shehu, Asma'u Sannu "



Sakinta nayi na dawo gefenta na zauna nace



"Inna Ina yini? "



"Lafiya lau, "



Tana magana Tana assessing jikina, se naga ta bata fuska ta kalla sashen da Ummaah take, zuwa lokacin
na fahimci har Abba dasu Adda suna zazzaune Kamar Wanda ake wani karamin meeting.



"Saude amma Kinsan ba haka na kawo 'yar shehu ba Ko? Ta Yaya na baku yarinya da kibarta Yanzun
Nazo Naga kashi da rai? "



Ni Kaina seda nayi dariya, balle kuma su Adda, amma Ummaah tsakani da Allah Ta Fara kokarin kare
kanta. Nanfa Inna ta hau sababi, ita kafata kafarta bazata barni anan ana cuta ta ba, Abba da Ummaah
se hakuri suke bata. Se ka rantse da Allah ita ta haifeni, basu suka haifeni ba. Inajin wannan Maganar na
Fara murna Dan tabbas a lokacin babu abinda nake adawa dashi kamar zaman gidanmu.
Halayena Wanda na aje a kofar gida lokacinda zan dawo daga Kwalam su na bude, sabon shafin rashin
mutunci, saboda I'm sure babu Wanda ya isa Ya taba ni tunda Inna Ade na nan, islamiyya na tattara na
aje, Da daddare nayi ta rigima se nayi kallo, sannan da safe se eleven nake tashi. Babu Wanda ya cemin
ci Kanki, se ana gobe Inna zata tafi, mun kammalla breakfast tace da Abba Wanda ke kokarin fita



"Shahada, gobe zan tafi Maganar Asma'u Fara da ita zan tafi."



Abba ya bude baki Zaiyi magana yaga har ta tashi ta tafi, Nima gudun abinda zai biyo baya na take mata
baya zuwa dakin da yake nata, Dan tun zuwanta na tare a can.



Adda Sa'ada ce ta mike ranta a mugun bace ta nufi dakin Yaya Halifa bansan abinda tace mishi ba, all I
know ina kwance naji sallamar Adda Maryam, amsawa nayi sannan ta shigo, tareda tambayata inda Inna
Ade take, bandaki na nuna ba tareda na furta komai ba, kanta ta gyada sannan tace min Yaya Halifa na
nemana. Wata muguwar faduwar gaba naji, saboda babu Wanda nake Tsoro, har cikin raina kamar shi
da Adda Salma. Mikewa nayi jikina a matukar sanyaye na nufi dakinshi.



Da sallama bakina na isa, yana zaune gabanshi Wasu manyan text books ne, se wata dorina me Baki biyu
a gefe. Jikina Se ya Fara rawa, naji tamkar na ruga gurin Innata amma who born me? Da kuwa Yayi min
dukan mutuwa. Tsugunnawa nayi a gabanshi bakina na rawa nace



"Yaya gani"



"Na ganki" ya furta ko kallona baiyi ba, nafi mintina goma a Haka kafin ya daura kafafunshi akan table
din yana kallona yace



"Idan Inna zata tafi gobe zaki bita? "



Shiru nayi saboda bansan right reply ba, zuciyata kowa yasan Inna Ade take son bi, amma wannan Zakin
dake gabana, I don't think zan iya fadar son raina. Ina tunani Ashe har ya dauki dorinar, sede jinta nayi a
kafafuna dana mikar, wani tsalle na buga saboda azabar radadin da naji tareda bude baki zanyi ihu,
"Idan kika bari naji Kinyi Ko tari ne, se na karkarya ki na zubar anan. Dawo ki zauna"



Its funny gaskiya, jiki na rawa na dawo na zauna inajin yadda kafafuna ke zugi, yaye skirt dina nayi,
abinka da fara tuni gurin ya tashi Yayi jawur, hawaye tamkar an bude famfo haka ya dinga zubowa, kafin
wani lokaci fuskata tayi jawur. Sakkowa yayi ya zauna gefena yace



"Kinsan idan na kara jin kince zaki koma Kwalam, wannan bulalar se ta karye a jikinki, kuma Yanzunnan
kije Kicewa Inna bazaki bita ba"



Kaina na gyada cikin sauri sannan na mike, kamar haske har na isa kofa Ya dawo Dani akan na wanke
fuskata. Ina Naga ta musu, toilet dinshi naje na wanke amma kana kallona zaka San nayi kuka, nasan
idan Inna Ade ta ganni a Haka, kilan kashe Yaya Halifa zatayi hakan yasa na wuce dakin Ummaah na
kwanta, ranar anan na kwana.




So you guys where truly waiting for me! I got it. Thank you so much for the comments and prayers! I got
you




Ayshatuuu

[3/17, 2:27 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻



_THREE_




✍🏻 *SHATUUU❤*

_Jakadiyar kainuwa_
💖Shatuuu095@ wattpad




*‫*بسم الله الرحمن الرحيم‬




*____________________________________*




*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*____________________________________*
A ka'ida tafiyar Inna da sassafe take yinta, duk inda goma take to ta kama hanya, Haka idan zuwa zatayi
da sassafe take zuwa. Tunda mukai Sallar asuba, Ummaah ke harhada min kayana, ranta a mugun bace, I
can swear cewar ban taba ganin fuskar ta a Haka ba, saboda ta kasance mutum ce me faraa, hardly kaga
ranta a bace.



Ina kwance ni kuwa Bance mata komai ba, seda ta gama sannan ta dubeni tace



"Tashi kiyi wanka"



Ban Musa ba, na tafi bandaki nayi jika jika Kamar yadda na saba na fito. Da kanta ta shafa min Mai ta
shirya ni sannan muka fita zuwa parlor, Har an hada breakfast, Yana aje an baza katuwar dining mat
anan parlor, komai an kawo se ci Ya rage. Zama nayi gefen Inna da ta gama amsa gaisuwar Ummaah
dukda an rigada an gaisa Tun asuba. Tana ta bani labarin kawayena na Kwalam, da yadda suke dokin
dawowata amma ni jinta kawai nake, muna nan Sega su Adda sun fito kusan lokaci daya gaba dayansu,
se Yaya Halifa fuskarshi a murtuke ya samu guri ya zauna yana wurga min harara, cikin rashin saa Inna ta
lura da hararar, kawai gani nayi ta dada mishi Duka a bayanshi tareda fadin



"Dan banza kawai, uban me tayi maka da safiyar nan zaka kafa hararar ta? Dole yarinya tabi ta lalace,
kun saka ta a gaba kamar mayu"



Idaanuna sukai raurau alamar kuka, su kuwa banda dariya babu abinda suke, a Haka Abba da Ummaah
suka iske mu, abincin duka babu wani armashi haka mukaci, ana gamawa Inna ta dubeni tace



"Maza Kawata tashi dakko kayanki kizo mu tafi"



Kowa a parlon zuba min idanu yayi, suna jiran ganin abinda zanyi. To everyone utmost amazement
kallonta nayi nace



"A'a Inna Ade, kije ni bazanje ba"
Wani mugun kallo Tayi min zatayi magana se kuma ta juyar da kanta zuwa inda Adda Sa'ada ke zaune
hannunta da tea mug tana kurba,



"Ahaf! Ni nasan zaayi Haka, wannan yayan suna gidannan ai na daina ganin daidai. Sa'adatu da Aminu
ba. Nagode sosae Kunyi kokari. Amma ku sani Fara 'yar shehu Ko kunso Ko kun ki tawa ce, barazanar ku
babu abinda zatayi mata! "



Tana gamawa ta Mike tareda kallon Abba tace



"Zan wuce Shahada"



Abba da Ummaah Wanda suka rasa bakin magana suka mike tareda bin bayanta, Nikam dakin Ummaah
na koma Inata kuka, wayaga samu da rashi.



A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya na hakura da zancen zuwa Kwalam na rungumi sabuwar rayuwar
dake gabana. A wannan hutun sosae nayi Karatu, Yaya Halifa ba karamin kokari Yayi a Kaina ba. Babu
Wanda yake min magana da Hausa seda turanci. Kafin Hutun ya kare har na Fara mayarwa. A bangaren
islamiyya shima sosae nake abin kirki, hakan ba karamin dadawa su Abba yayi ba, shikenan aka daina
takura min, tunda na riga nayi blending da yadda suke son na zama.



Duk Hutu idan akai Zaa kaini Kwalam nayi sati daya sannan na dawo. A Haka shekaru sukai ta ja har nakai
shekaru goma sha biyu, lokacin ake ta cukwukun kaini secondary school. Matsalata daya ce wadda kusan
kullum se anjini da Ummaah da Sauran sisters dina, bana Aikuwa, I'm very lazy, laziness dina Har ya saka
jikina kanshi na gyara se ya zama abu, wanka se Ummaah tace min naje nayi, balle gashina, se nayi sati
biu ban taje shi ba, idan aka samu nayi kitso zan iya 3 months ban tsefe ba. Kuma nafi kowa Baki idan
akace Ni kazama ce, kuma deep down inside me nasan ni kazama ce, kuma san jiki shi ne ummul aba'isin
kazantar.



Wani yammaci mun dawo daga islamiyya nida Adda Salma da Adda Maryam, tunda muka taho bakina
yake a cunne Kamar Karin kunama, saboda Adda Salma tace kaina yana wari, Bance komai ba Har muka
isa gida. Ina shiga dakinmu na tarar da kayana duka na cikin wardrobe an fito dasu an watsar a tsakiyar
dakin.
Takaici kamar zanyi me, ciki na karasa Ina bin kayan da kallo, gaba daya an cakuda wankakku, gogaggu
da masu datti. Idanuna taf da kwalla nayi kofa zan Kai Kara naji an bude kofar toilet an bude, komawa
nayi, Adda Meeyna ce hannunta rikeda face towel tana goge wet face dinta.



"Yawwa kwashe kayannan ki fitar dasu, yarinya kamar 'yar daji se shegiyar kazanta"



Tura bakina nayi na juya na tafi gurin Ummaah, Tana kitchen tana kada miyar dare,



"Ummaah kinga Adda Meeyna Gabaki daya ta Watson da kayana waje ko? "



Seda ta kashe Gas din sannan ta kalleni tace



"Ba kazanta kike ba Asma'u? Shekara goma sha biyu ace wanka se nace miki kiyi? Wallahi dama kisani ba
NTIC kike so ba? Allah Bazaa kaiki ba, Gwaram zaki tafi, yadda ko sunana kikaji se Kinyi kuka, se seniors
sun miki dukan da ko cewa akai kiyi kazanta bazakiyi marmarin hakan ba"



Ai daga jin hakan na Fara kuka ina bata hakuri amma ko kulani Batayi ba ta tafi daki, komawa nayi dakin
Inata kuka, na tsugunna na Fara tsitsince kayan, Adda Maryam ce Tazo ta tayani muka gyara kayan,
Wanda basuda guga na kaisu inda ake Tara kayan guga. Marasa wankin kuma na kaisu cikin laundry bin,
ni Kaina dana kalla wardrobe din seda naji dadi, saboda yyai kyau. Sallah mukai sannan muka zauna ta
tsefe min Kaina Dama kitson guda goma ne, ana cikin combing Adda Sa'ada ta shigo, gefenmu ta zauna
bayan ta dage curtains sannan ta kura fanka tace



"Wannan se mutum Yayi suffocating saboda warin da Kanki yake"



Ni magana Tana min wahala, amma da ina magana nasan tabbas rashin kunya zanyi, so instead of rashin
Kunyar sede na murguda Baki, bakin na murguda daidai shigowar Adda Salma, hannunta tasa ta gwabe
min bakina tace
"Zaki sani, sena fasa fitsararren bakin nan naki"



Adda Meeyna dake kwance tayi saurin cewa



"Ku kyaleta Dan Allah, kada taji Kamar an takura mata"



Dage kafada Adda Salma tayi ta kara Ficewa, wata Uwar harara nabi bayanta dashi, ribbon nasa na tufke
kan in a bun, inajin Adda Maryam na mitar gashina baida zuciya. Adda Sa'ada ta wanke min shi tas,
tayimin drying sannan tayi min kalba Manya, ta saka nayi wanka ai ji nayi kamar an sakeni, wata fresh air
tana shigata ta ko ina a Haka bacci ya daukeni.



Duk tunanina zancen zuwa Gwaram wasa Ummaah take, amma bayan sati uku lokacin Zaa shiga sabon
session Naga anata shiri, tunda naji Ni Zaa kai nake ta kuka, saboda har ga Allah bana son zuwa. Hatta
Abba dake bani goyon baya wannan Karon ban samu ba. The only person that stands for me was Yaya
Halifa, shima dalilinshi kada background dina ya lalace amma yadda Ummaah ta dage nasan babu me
juyata.



Da daddare naje dakin Abba na gaisheshi, Yana ta tsokanata yar boarding, kiran Inna Ade ya katse mana
hirar, katsewa yayi ya kira suka gaisa sannan yace mata gani a kusa. Da murnata na karba sannan na
mike na fito waje, cikeda murna na gaisheta, Tana tambayata yadda nake, nan kuma na Fara kuka ina
fada mata Ummaah bata sona, ta takura min tace Abba ya kaini Gwaram. Dariya Inna tayi tace kada na
damu karshen sati tana hanya.



Ranar asabar kuwa da sassafe se mukaji isowar ta, lokacin Inata bacci ban tashi ba, Maganar ta yasa na
fito, gaba daya

Please Login or Register in order to submit comment