Reading Fara Yar Shehu by SHATUUU Chapter 9 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan nake lallabawa Ina fita aiki amma kullum jiya i Yau, abin ya taba ni sosae da sosae.



Bayan wata daya



Anyi shuffling na koma Obstetric Team, da yamma Ina maternity dake Munada call, aka kawo wata
patient referral case ce. Tareda Nurses din mukai attending mata anan muka gane babyn ne breech,
Gata haihuwan farko so bazata iya delivering babyn, dole we need emergency CS. Nurse din tayiwa yan
uwanta bayanin akan zaayi signing consent kuma zasui donating blood. Ni Ina zaune ina Rubutu sannan
nayi notifying senior doctor na, shi kuma yayi notifying scrubs din. Ina kokarin fita naji sallama tamkar a
mafarki, cikin sauri na juyo ina kallon Wanda Yayi sallamar, shi dinne Salis ne, yana tsaye as always, Cas
dashi Dan gayu, Yau ma like usual yayi kyau, Se naga tamkar an kara Kawata shi ne. Kallon kallo muka
tsaya yi, seda nurse din tace



"Malam me ya faru?"



Kallona Yayi sannan yace



"Are you the Doctor in charge? "



Ban bashi amsa ba se kallonshi da nake kara yi, kada dai ace tunanina Ya zama gaskiya? Kada fa he's here
to sign the consent.



"Me kakeyi anan? "



Na tamabayeahi idanuna sun kasa boye tsanar da nayi mishi, kallona Yayi yace



"Asma'u! "



Hannuna na daga masa nace



"Me Ya kawo ka kawai? "



Gumin kan goshinshi ya share yace



"Matata aka kawo, Nazo nayi signing consent ne! "
Lumshe idona nayi ban kara kallon inda yake ba na dubi Sister nace



"Ina OT, Ina jiranta"



Daga Haka na juya na fita, cikin hanzari ya biyoni yana fadin



"Asma'u please listen..... "



Dan Murmushi nayi nace



"Kasan me ciki management dinta da wuya, saboda ba rayuwarta ce kadai ba, akwai abinda ke cikinta so
ka hanzarta kayi signing, ko kaga fruit of your hard work "



Daga Haka na wuce, kafata kawai nake cillawa, bawai na gama warkewa bane tun can, kawai dai naji
lokaci yayi daya kamata na dawo hankalina, se gashi ya dawo, Ashe aure yayi, a lissafina yaron cikinta is
term kenan, Tun ina Potiskum Yayi aure? Kaina na girgiza kawai na wuce OT, changing kawai nayi naji an
shigo da ita, scrubbing nayi sannan na shiga ciki. Tana kwance lifeless, Dan an rigada an makar da ita.
Itama Fara ce Kamar yadda nake Fara, tana da kyau ga gashi da ya fito ta karkashin cap din aka saka
mata. Na jima a tsaye ina Kare mata kallo, if not because of the oath I took "I'll treat everyone equally,
irrespective of gender, race, religion, ethnicity. I'll render my service to whosoever disregards to
personal affairs....... " Da Bazan mata CS dinnan ba, amma nasan it can't be. Anaesthetic din ne yace



"Dr. Shahada are you alright?"



Kaina na gyada nace



"Yeah! Scapel please"
Ana miko min na yanka ta, I was praying komai ya tafi daidai idan ba Haka ba Ina cikin matsala. God so
kind komai ya tafi yadda akeso na ciro katuwar baby girl Itakuma na dinketa aka maida ta ward. Koda
muka gama lounge na shiga na cikin theater ban ma damu da mutanen dake ciki ba, kawai na samu
cushion din gefe na zauna tareda lumshe idanuna, sosae nayi zurfi cikin tunani. Na jima a zaunen har Dr.
Lamin ya buga min hannun kujerar yace



"Dr. Shahada, kina lafiya kuwa? You have not been yourself these days "



Dan faint smile nayi tareda mikewa nace



"I'm good, kawai yau da gobe ce"



Kanshi Ya gyada yace



"A'isha Tana nemanki a ward dinsu. "



Kyaftun yake nufi, mikewa nayi nace



"Oh, ashe na kashe wayata. Lemme rush"



Handbag dita na dauka ba Wanda nayiwa magana na fice, a kofar theater na sameshi a zaune alamu
jirana yake, dauke kaina nayi saboda banga abinda ya rage tsakanina da Salis ba, komai ya kare. Bashida
bakin da Zaiyi min bayanin komai tunda lokacinda Abba yace na rabu dashi, na kirashi Ina kuka nace ya
min bayanin abinda yake faruwa se yace min na jirashi kada na damu, I didn't give up bayan sati na kara
kiranshi, Se yace min na dameshi, na rabu dashi indai bawai Anyi tying destiny dina dashi ba. nayi kuka
bana wasa ba, anan na fahimci abubuwan da Adda Sa'ada da Kyaftun suke gaya min, it took me more
than days kafin na hakura na daina kuka, na tuhumi rayuwa akan walagigi da take dani, haka na zargi
soyayya da rashin yimin adalci, sede Ina fatan zuciyata bazata kara kaini ta baroni ba.



Ganin da gaske nayi tafiyata yasa ya biyo bayana yana fadin
"Haba Asma'u, Ki saurareni mana, ko Badan ni ba"



Numfashi na da sauri yake fita saboda tsabar masifa, amma cikin raina hakuri nake bawa kaina akan
komai will be ok, kallonshi nayi nace



"Me zakace min? Godiya zakaimin? Ni da Kai bamuda Sauran magana, ga 'Yarka can na ciro maka, Bazan
mata fatan tsiya ba amma ka sani ka barmin tabon da a zuciyata bazai taba gogewa ba, kuma Inshaaa
Allah Se ka dandani bakin cikin da kasani a ciki."



Daga Haka nayi tafiyata female ward, inda nan Kyaftun take, Ina shiga taga yanayina kawai se ta dauki
excuse gurin Metron dinsu muka fita, muna fita tace min



"Ya akai? Me ya faru "



Hannunta na rike seda muka zauna sannan nace mata



"Kyaftun Kinsan Ashe Salis aure yayi? Kin sani?"



Knata ta girgiza da mamaki tace



"Inji wa ke kuma? "



Hawaye a hankali suka gangaro min nace



"Yanzun nayi mata CS... "
Tsaki tayi tace



"Kiji wata magana, hallucination kika Fara ne? "



Ganin bata yadda ba yasa na bata labarin yadda akai, ranar kakannin Salis ma seda naji tausayinsu, yasha
zagi, da tace se taje ta zagi uwarshi a gabanshi na hanata. Ilai se gashi an kirani akan Nazo babyn na
convulsing, cikin gaggawa muka tafi Harda ita, yana kofar post natal a tsaye ya zabga tagumi, ban bi ta
kanshi ba, na wuce ciki, Kyaftun ta zauna a gurinshi. Ina zuwa muka hau rescucitation, da kyar Allah yasa
akwai kwana a gaba sannan yarinya tayi responding, nayi documenting sannan na fito, har lokacin suna
zaune, fuskarsu a bace nasan zancena akeyi, hannu na mikawa Kyaftun nace



"Twin muje, Babyn tayi responding "



Zaiyi magana na dalla mishi harara, kyaftun tace



"Kai har kana da bakin magana ma "



Se yayi Shiru ni kuma na jata muka tafi. Tana ta dariya yadda ya dinga bata hakuri, ni haushi naji da ta
zauna har sukayi magana dashi, to me banda makiyi Wanda na tsana Kamar shi.




This is a Combi-three page, daga yau na gama typing Inshaaa Allah Se zuwa bayan Salla idan rai ya kai.
Allah Ya tabbatar mana da alkhairi, ya bamu Ikon yin Ibada, yasa Muna cikin 'yantattaun bayi, yasa
Munada ran witnessing na badi and many years to come. I wish u could all stay safe, May Allah bring the
end of this pandemic plaque..... Amin.




Yours Truly
Ayshatuuu!

[5/25, 9:05 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻



_TWENTY SIX_




✍🏻 *SHATUUU❤*

_Jakadiyar kainuwa_




💖Shatuuu095@ wattpad




*‫*بسم الله الرحمن الرحيم‬




*____________________________________*
*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*____________________________________*




"Hello people! Barka da sallah, howwas ramadan , May Allah accept our ibada. This is little for you ,
thank you"




Rayuwa tana zuwa mana yadda bamu expecting, wasu lokutan faruwar wasu abubuwan ke saka mutun
ya zama very strong, kamar yadda rayuwa ta Koya min lessons sosae da sosae. Bayan mun bar inda Salis
ke zaune, raina a mugun bace na nufi daki saboda aiki na na ranar ya rigada ya kare. Key na cira na bude
dakin na shiga tareda slamming kofar, yadda tayi kara har seda naji tsoron kada nazo bude kofar taki
buduwa.



Lab coat dina na cire na yar akan pink carpet din dake a dakin wanda iyakar shi gefe daya kawai yayi
occupying, dukda yawanci kayan make up dina ne a aje. Gaba daya zuciyata wata irin suya takemin
amma abin mamaki hawaye ko diso bai zuba min ba. ive cried enough akan namiji tundaga mukhtar
down to suleiman, zuwa salis nasan ban dace ba, ban kuma san har se yaushe ne zanji abunda mutane
kan fada akan soyayya ba. Mutane da yawa, kamar kyaftun kullun tana nuna min ni dace ne banyi ba in
daina kalon soyayya a worse thing amma na kasa bansani ba ko se nan gaba, when the right person
comes.



Closing chapter na mutum abu ne mawuyaci, if i can say nasha wuya kafin na fitarda salis da abinda yayi
min, saboda abinda yafi bata min rai a lissafina yayi tun muna tare amma haka ya dinga yaudarata
bayan ya rigada yayi aurensa. Luckily Allah yasan komai, na tabbatar zai saka min. Kwana biyu kawai na
kara a dutse naji baki daya garin ya isheni, babu abinda nake so kamar na ganni a kano, gashi ranar zan
fara call dole haka naje na roki Dr fadima akan tayimin covering idan na dawo se na rama mata. Dake if
you good to people dole wannan goodness din zai dawo maka, zaka tsince shi somewhere in life, ta
amince hakanyasa na baro clinic na dawo gida dan na fara shiri. Ina cikin shirin kyaftun tazo , dake ban
locking kofar ba se kawai ganinta nayi a tsaye tana kallona, kallonta nayi sannan nace



"Kano zan tafi, kiyi hakuri ban fada miki ba"



Kanta ta girgiza tareda zama gefen mattress dita tace



" hope dai lafiya?"



Rataye stethoscope din hannuna nayi nace



" kawai ina son ganin ummaah ne, garin duk babu dadi"



Kanta ta gyada tace



" Indai zakiji dadi better kije din, amma kisawa ranki no matter how badly you want something indai
Allah bai kaddara zuwan lokacin ba sede kiyi hakuri"



Na fahimci abinda take nufi hakan yasa na danyi faint smile sannan ta cigaba da bani baki, kusan duk ita
ta taya ni nayi parking sannan ta saka Dr lamin ya kaini park na tafi.
Misalin hudu na yamma na isa kano sannan na samu napep dan ya kaini gida, a gajiye naje gidan. A gate
na tarar da Abba akan wata wooden chair hannunshi da daily trust newspaper, yana karntawa, babana
is still old fashioned, duk yadda yanxun ake komi ta internet amma yafi ganewa komai ya samu
hardcopy. Tunda na turo kofar ya rufe paper yana kallona fuskarshi da murmushi akai, se naji kamar ana
yaye min dukkan damuwata har bansan lokacinda na saki murmushi ba, na isa inda yake na tsugunna
nace



"Abbana!"



"Doctor barka da zuwa"



"Barka dai , ya gida?"



Tare dashi mukaje cikin gidan, babu kowa se ummaah da inna se wata yarinya da ummaah take riko
Asiya. Da munarta taxo ta rungumeni sannan ta karbi handbag dita tana fadin



"Sannu da zuwa Anty"



"Yawwa 'yar Ummaah"



Murmushi tayi min, gefen Inna na fara zuwa dan nasan korafinta, tana zaune kan kujera tana murza goro
a magogi tana afawa a bakinta. Gefenta na zauna tareda fadin



"Kawata! Yaushe kika zo"



"Lokacinda kika tafi neman kudi"
Da rashin fahimta nace



"Neman kudi kuma?"



Na tambaya ina karbar magogin dan taya ta. Tabe baki tayi tace



"Yo neman kudi mana, kin kasa tsayawa ki nemi miji kinje kina zaman kanki, gashi gobe zaa kawo lefen
yarinyar zuwaira"



Zuwaira na maimaita a raina, ban bawa abin mahimmanci ba dan babu wata zuwaira da zan iya tunawa
a dangi. dagowa nayi lokacin na gama gogawa nace



"Inna kenan! Kowa lokacin shi daban yake"



Daga haka na tashi dan bana son bacin rai kuma, nayi tunanin zata jajanta min abinda salis yayi min,
tunda vividly tasan ba laifina bane shi ne take min wani znce kuma.



Ban ko kara kulata ba na tafi parlon ummaah bata ciki se a bedroom na sameta , tana ta waya kan
cushion na zauna ina jiran ta gama, normally zata kashe wayar ne musamman idan na jima banzo gidan
ba, amma se ta shareni ta cigaba da wayarta , nafi 30mins ina zaune sannan tayi hanging ta kalleni da
murnarta tace min



"Auta ta dawo, ya aiki?"



"Ummaah alhamdulillah, na sameku lafiya?"



"Lafiya lau"
Ta bani amsa se kuma mukai shiru kamar wanda bamu saba ba, tana ta kallona ni kuma na rasa yadda
zanyi, can nace



"Ummaah bari nayi wanka"



Ban jira amsar ta ba na fice zuwa dakina, Asiya tana ta gyara min dakin, sannu nayi mata sannan na cire
kayan na shiga wanka, abubuwa akan halinda nake ciki sunata crossing mind dina amma haka na watsar
dasu, nidai nasan iyakar addua nayi na kuma san Allah yayi alkawarin amsa adduar dukkan musilmi, no
prayer is shun away. Either a jinkirta ko kuma ka tsinta a lahira, tun muna yara ake cewa aure nufin Allah
ne amma na rasa dalilin da yasa mutane ke nuna min kamar rashin aurennan laifi nane bayan nidai
bazan auri kaina da kaina ba.



Kafin na fito kaina har ya fara min ciwo, fitowata sallah kawai nayi na fita parlor inda na samu ana kallon
wani korean movie Master Ruler zama nayi muka cigaba da kallon nida Asiya anan ummaah ta samemu.
Bata ce min komi ba se ni nace



"Ummaah babu abinda zaayi ne?"



Kanta ta girgiza amma batace uffan ba, duk se naji babu dadi hakan yasa na mike na zubo abinci amma
se naji ko taste dinma baya fita. Can na mike nace



"Ummaah zan kwanta"



"Allah ya bamu alkhairi"



Tace dani haka na tafi dakin inna nayi mata sallama, itama rai bace ta amsa , gaba daya jikina yayi sanyi
se kawai na tafi gurin abba nasan shi bazai min hakan ba. Aikuwa naji dadi dan hira sosae ya dinga min
se wajen goma da rabi kafin na kwanta.
Washegari ban tashi da wuri ba saboda na kwana biyu ban samu hutu ba, seda nayi wanka sannan na
fito anan na tarar da su Adda da kannen Ummaah se wasu daga cikin yan kwalam. Daya bayan daya
muka gaisa inata mamakin me akei. Seda na shiga kitchen naga manyan trays an ciccika da snacks, nama
dasu drinks. Zama nayi kan stool nace



"Adda Meena, me akeyi ne naga gidan a cike?"



Daidai shigowar Ummaah tace



"Jikata ake kawowa lefe?"



Juyawa nayi na gaisheta dan bamu hadu ba sannan nace



"Jika kuma? Ai ummaah jikonki babu wanda ya isa aure, sede ko early marriage zaayi"



Bakinta ta tabe tace



"Su ba irinki bane, su sunsan darajar sunnar ma'aiki, iyayenta basuyi sakacin da mukai ba, sun isa da
yarinyar su, gashi ta kawo miji zatayi aure ba kowa bace kua se Amratu:"



Tunda tafara magana na daina shan tea din dake hannuna, fuskata tayi jawur saboda tsananin yadda
raina ya baci, har mamakin ya kauce a kanta. Kallonta kawai nake inajin yadda take fada min maganganu
kamar banice auta ba. Those that mean Ummaah ma zata iya yimin haka? Anty Bintu ta taho da sauri
zuwa inda nake ta rikeni, banma san yaushe ta shigo ba . Mikewa nayi kawai na fita zuwa dakina, Anty
Bintu ta dubi Ummaah tace



"Haba Yaya Rukayya! Ya haka? Ta Yaya zaki fada mata haka, ni a ganina Asmau babu abinda take bukata
irin support. Dan kin mata gori idan Allah baiyi ba ba zatayi aure ba"
Ficewa tayi ta nufo dakina ta bar Ummaah a tsaye, Adda Meeyna ma fita kawai tayi ta cigaba da
mamaki. Ina zuwa daki nasan biyoni zaayi hakan yasa ban rufe kofar ba kawai na zauna gefen gado na
zabga uban tagumi. Na rasa yadda zanyi da rayuwata, Na rasa se yaushe ne muatane zasu fahimci idan
bakayi aure ba ba laifinka bane.



Anty Bintu da Adda Sa'ada wadda may be Anty Bintu ta fada mata sukazo suka sakani a gaba da nasihu
kalakala, I couldn't resist kawai na fara kuka ina fadin



"Na hana kaina miji ne? Idan ance ana shawara da mutum kafin a rubuta masa kaddararsa kowa will live
a life not yadda muke living yanzun. Amma me yasa kowa yake ganin laifina ne dan banyi aure ba. Har
Ummaah wadda zata lallasheni amma harda ita....."



Na jima ina kuka saboda bakin cikin dake cina, se da kaina nayi shiru sannan suka fita ni kuma na kwanta
kawai dan babu inda zanje. Kenan zuwaira da Inna tace Adda take nufi kenan, i taught i was saved daga
kaninka ya rigaka aure ashe yana nan tafe, yanxun amratu da ita zaa dinga yiman gori akan aure. Karfe
hudu dukka suka tafi nima hakanan na kwanta nayi shiru bansan abinda ke dmuna ba amma nasan
zuciyata da zaa fito da ita tabbas nasan turiri kawai ke tashi. Ina nan lwance har akai maghrib nayi sallah
na kara kwanciya, lokacin ne na samu na janyo wayata na dan kunna data na shiga instagram na fara
duba diary of a nothern woman. Shigowar Adda Maryam yasa na tashi na zauna, kallona tayi tace



"Fushi kikeyi ne?"



Dan murmushi kawai nayi bance komi ba, se ta gyara zamanta tace



"Asmau, abinda Ummaah tayi daidai ne, ke kanki a shekarunki ya dace ace kinyi settling kinyi aure, me
kike bukata? Kin gama makaranta, kin fara aiki me kike jira then? Ummaah kinsan dole hankalinta zai
tashi ace ba kiyi aure ba har yanzun."



A hankali hawaye masu dumi suka saukar min amma bance mata komai ba ta gama bababunta ta tafi.
Mikewa nayi na wuce toilet na wanke fuskata sannan na zura hijab duna na tafi parlon Ummaah, gaba
daya wani rauni ke damuna se naji bana son ganin Ummaah amma bansan shaidan ya cigaba da yimin
huduba hakan yasa na shiga da sallama, suna xaune itada 'ya'yanta masu aure, gefenta naje na zauna
nace
"Ummaah babu abinda zaayi zan kwanta?"



Kaina ta shafa tace



"Auta taje ta kwanta seda safe"



Daga haka nayiwa sauran sallama duk yadda nake son zama cikinsu muyi hira amma se naji bazan iya ba.
Haka kawai naje na kwanta dukkansu seda sukai min sallama, masu lallashi sukai sannan suka tafi. 2am
na tashi nayi alwala na fara sallah sede dukkan wata sujjada idan nazo se nace "Allahumma!" Se wani
kuka ya lwace min , I couldn't pray sede kuka wanda nasan Allah is already aware of my situation, kuma
zai daidaita al'amarin.




Ayshatuuuuu

[5/27, 5:58 PM] Shatuu Kwalam: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻



_TWENTY SEVEN_




✍🏻 *SHATUUU❤*

_Jakadiyar kainuwa_




💖Shatuuu095@ wattpad
*‫*بسم الله الرحمن الرحيم‬




*____________________________________*




*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*____________________________________*




Ban taba jin gidan mu ya isheni ba se wannan karan, seda naji inama nayi zamana a dutse ban dawo ba.
Tunda nan din dana dawo dan samun relief kwatakwata abin ya gagara, se ma karin wani tension din da
na samu.
Washegari, babu kowa gidan dukkansu sun tafi hakan yasa na fito da wurwuri na shiga kitchen dan hada
breakfast se na samu Asiya ta fara hakan yasa nayi joining dinta muka kammalla. Ina cikin wanke hannu
na cikin sink naji maganar Abba da Yaya Halifa, cikin sauri na fito dan ranar nake tunanin zuwa gidan shi.
Suna zazzaune na samesu, gaishesu na fara yi sannan na tambayeshi su anty Zannira yace min dukkansu
suna lafiya. Munata hira yawanci shi da Abba ne sede nayi ta dariya a haka Ummaah ta same mu. Gefen
Abba ta zauna suka gausa da Yaya halifa sannan na gaisheta nima, amsa min tayi normal kamar ba jiya ta
tara min jamaa ba. Nayi tunanin inama wani yayi min abinda Ummaah tayi min, inaga nida shi har abada
amma Ummaah Ummaah ce tafi gaban komai, everything she said I consider it as frustration.



Key Abba ya miko min yace



“Auta yau shekararki ashirin da shida, Allah yayi miki albarka. Ga gift dina”



Gaba daya na manta da wai yau birthday dina, tabbas girma ya hau kaina I couldn’t believe cewar I’m 26
years already. Kallon key din nayi na mota ne, ai wani ihu na buga ina fadin



“Abba mota? Abba nagode Abba Allah ya saka maka da mafificin alkhairi”



Na juya gurin Ummaah data tsira min idanu tana kallona, da murana na mika mata key din nace



“Ummaah kinga gift din Abba”



Maimakon ta karba se cewa tayi



“Haba Sir...”



Dake haka take kiranshi a matsayinshi na tsohon dan sanda



“...ta yaya zaka siya mata mota? Mu da muke son ta kawo miji tayi aure”
Gaba daya se naji murnar ta dauke min, dukkan mu muka saka mata ido muna kallonta da mamaki, nidai
inajin anya Ummaah ta ce kuwa? Is she really my mom ko wani ke zugata haka? Abba yayi murmushi
yace



“Madam, meye hadin siya mata mota da samun mijin aure? I see nothing”



“Dama baza kaga komai ba amma ai wannan maza tsoron tunkarar ta zasu dinga yi, gata likita ga mota”



Dariya sosae Abba yayi sannan ya dubi Yaya halifa kafin ya kara kallonta fuskarta a hade kamar hadari,
yace



“Halifa, kaji zancen mamanka fa. Can you imagine? What if ta dalilin motar zata samu miji. Kema mutane
sun fara miki wannan hudubar? Aure ai nufin Allah ne kuma ko shekara arba’in Asmau ta kai babu miji
bazan takura mata ba, saboda abu daya na sani everything lies on it timing!”



Daga wannan maganar abin mamaki Ummaah ta fara kuka wai Abba ya fada mata magana sannan wai
shi yake daure min wani guri shiyasa naki bada hankali nayi aure. Gaba daya hankali na yayi masifar
tashi, na dinga bata hakuri ina lallashi amma ko kallona batayi ba, se na fara kuka nima naji gaba daya
tamkar an kifar min da duniyar da nake ciki. Yaya Halifa yasa ni muka fita yana ta bani baki tareda nuna
min komai zai wuce.



Da yamma naji gidan ya isheni, kamar ana hadamin wuta haka na dinga ji, babu sauki naje nace da
Ummaah zanje gurin Adda Sa’ada, bata hanani ba se cewa tayi



“Gwara ki dinga fita ko kya samu mashinshini.”



Har na tafi ina mamakin Ummaah, mota ta kirar peugeot 206 blue na bude nayi addua sannan na tafi.
Adda Sa’ada tayimin murna sosae, da muka kebe na dinga fada mata abubuwan dake faruwa , tayi ta
bani hakuri akan lokaci ne sede I’m frustrated na gaji hakanan, bansan yaushe ne har laolacin zai zo ba.
Da daddare bayan na idar da sallar ishai na tafi parlon Abba dama seda na tabbatar Ummaah na dakinta
sannan naje. Yana zaune ya gama cin tuwo na shigo tareda zama inda ya nuna min. Shiru nayi na rasa
me zance masa saboda nauyinshi naji. Can yace



“Asmau ya akai ne?”



Kaina na girgiza nace



“Abba gobe zan koma dutse sa...”



“Saboda me? Ba kince min two weeks zakiyi ba, is just five days kawai fa”



Se na rasa me zance masa tunda ni dai I’m not used to karya amma bana son ce masa pressure Ummaah
ce ke damuna tunda dazun naga sun samu sabani akaina.



“Asmau, Rukayya ce ko? Ita take damunki akan aure ko? Kada ki damu kinji ko komai lolaci ne, kada kiji
haushinta nata salon kilawar ne. Kibar tafiya dutse ki kara hutawa kinji.”



Kaina na gyada nayi mishi godiya sannan na tafi nayiwa Ummaah sallama. Har naje bakin kofa se naji
tace



“Asmau zo nan”



Jiki a sanyaye na koma na zauna kan carpet, gaba daya mun zama sirikai nida ita , idan ina tare da ita se
naji wani irin nervousness na damuna. Drawer ta janyo ta fito da wata leda ta aje batace komai ba haka
nima se shiru nayi ina fidgeting da hannuna. Asiya babu jimawa ta shigo da wani kasko cikeda ga
garwashi, ajewa tayi a gurinda babu carpet saboda kar ya kone. Tana fita Ummaah ta mike tareda min
alamar na bita, hakanan babu yadda zanyi na bita, wasu itatuwa ta ciro a ledar ta watsa cikin garwashin
take kuwa wani mugun hayaki ya tashi, seda gabana ya fadi. Haka tasa Na tsugunna ta samu wani thick
towel ta lulluba min. Na dinga tari ga mugun gumi da ya dinga karyo min Amma Ummaah seda nayi
more than 10 minutes a haka sannan ta yayeni. Dana mike se layi har seda ta rikeni sannan ta hada min
ruwan wanka shima wasu magunguna ne a ciki amma ko uffan bance ba haka nayi, ina fitowa ta bani
mai na shafa sannnan ta sallamrni na tafi.



Seda na jera kwana biyu kullum se anyi sau biyu kafin wani lokacin na fita a hayyacina, na rame na lalace
nayi duhu. Babu arxiki na cewa Abba tafiya zanyi dan bazan iya zama ba. Shima duk abinda ake ya sani
dan tuntuni na fahimci maganin farin jini ko na samun miji akemin, i cant afford losing my iman saboda
hakan.



Da naje yiwa Ummaah sallama tace min



“Asmau akwai bikin Amratu, ina fatan zakizo”



Kaina na gyada amma deep down nasan wallahi bazan zo ba dan na rigada na rantse bana son zuwa na
zama topic of discussion.



Da motata na tafi, wannan shi ne karon farko dana fara tuki me nisa and alhamdulillhi naje lafiya. Dakin
kyaftun na wuce bayan na tsaya na zubarda magungunan da Ummaah ta bani cikin incinerator sannan
na shiga. Tana zaune ta gama girki kenan na shigo nayi wujigawujiga dani kamar an jefoni. Tace



“Twin meye hakan? Me yake damunki?”



Zama nayi nace



“Bani abinci kede”



Babu musu ta zubomin shinkafa da wake da kifi se dressed salad da zobo, nasan gandar kyaftun hakan
yasa nace
“Kinyi Bako ne?”



Fuskarta ta kwabe tace



“Dr Lamin ne yayi lunch a gurinna”



Kallonta nayi for some minutes kafin na cigaba da cin abinci na , seda na gama tas nayi wanka na dakko
zani daga cikin wardrobe dinta na daura hade da top na dawo na zauna nace



“Twin, meye tsakanin keda lamin abin yafi karfin kawance sede wani abin”



Murmushi ta fara kamar na mata albishor tace



“We’re dating har yaje Bama”



Idanuna a waje , se kuma na saki murmushi nace



“Alhamdulillah, yafi muku ai kun zauna da kuna

Please Login or Register in order to submit comment