Reading Amani 3 by SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng AMANI

3



Littafin

SUMAYYAH ABDULKADIR
(TAKORI)
takorikabara@gmail.com
07030137870
TAFIYA ZUWA DIFFA
M
asu iya magana suka ce tafiya mabudin ilmi, wasu kuma suka ce tafiya yankin azaba.
To duka dai Alhaji da iyalin sa da yan uwan sa babu wanda basu fuskanta ba a hanyar
su ta zuwa jihar Diffa ta kasar Nijar. Ga Karin ilmi suna ta samu a kan garuruwa da
Baba Idi ke musu bayani kasancewar ya taba zuwa fatauci Nguigmi daga Maiduguri tun
yana saurayi, ga kuma yanayi na wahalar zafin ranar sahara wadda tasa hatta A/c din
motar daina bada sanyi ta ke yi lokaci-lokaci saboda zafin rana da zafin rairayi
irin na sahara. A hakan ma don sun yi zagaye ne ta Maine-Soroa da Nguigmi basu bi
ta cikin Bama din Maiduguri ba.
Kasancewar sun fito tun asubah, tafiya non-stop, kuma mota lafiyayya, zuwa
yamma sai gasu a cikin Maine-Soroa, makwabtan Diffa, anan ne suka tsaya suka yi
sallah azahar da laasar da ta riske su a hanya, suka sayi gasashshen naman rakumi
da madarar rakumi mai dumi sabuwar tatsa da sabon cukui a nan cikin garin Maine-
Saroa suka ci, suka sha, Mukhy har Shayin su na Tubawa ya saya ya sha, dama kuma
dai sun yo guzurin su yadda ya dace na abinci da abin sha, wanda tun dare Rakiya ta
shirya musu suka taho da su, wadanda ba masu lalacewa ba, snacks ne da soyayyun
kaji (pepper chicken), don haka basa tare da yunwa har suka shiga jihar Diffa.
Shigar su garin ke da wuya komai ya soma kwancewa Mukhtar, (his in-born
character) ya soma aiki a kan sa, ta yadda hatta gashin jikin sa dana kan sa sai da
ya mimmike da duk wani gashi da ke jikin sa. Amani da ke gefen sa yana tuki, ta
lura da yadda Mukhtar ke canzawa a yanayin sa da halittar sa, wata irin kamala da
nutsuwa suka bayyana a tare da shi, suka lullube ainahin Mukhy saurayi nan dan gaye
suka maida shi cikakken MOUKHTAR din sa, tsigar jikin sa har wani tashi take yi
kamar mai jin sanyi. Jinin Issouffou Massaoudou ya soma circulating yana kurdawa a
cikin jikin sa, yana sauya shi daga normal Mukhtar din sa da kowa ya sani zuwa
Mainan Diffa na asali. Amani bata san me Mukhy yake kwancewa daga leda ba ta ga dai
Mukhtar ya saka hannu ya janyo wani farin kyakkyawan tsohon amawali (rawani) daga
cikin leda, ya kashe motar su a gefen titi.
Rawanin nan ya hau nannadawa cikin iyawa da kwarewa, saida ya nade kyakkyawar
fuskar sa tsaf, sai tsinin karan hancin sa da manyan idon sa ne kadai ya bayyana,
kwatankwacin yadda taga nadi a fuskar mafi yawancin jamaar garin maza, wato nadin
rawani irin na buzayen asali ko kuwa Tubawa, ko kuwa a kira su da yadda aka san su
da shi wato Larabawan Diffa. Sai bata yi mamaki ba, don kuwa ta san cewa baa
canzawa tuwo suna, Mukhtar duk dadewar sa tare dasu, idan aka taho gida, shi buzu
ne na hakika.
Ya ja motar suka cigaba da tafiya. Baba Idi na tsokanar sa wato kowa ya bar
gida-gida ya bar shi, kyawun kowanne tsuntsu yayi kukan gidan su. Mukhtar yayi dan
murmushin miskilanci ta cikin amawalin sa, bai ce komai ba. Amma ya yarda da
maganar Baba Idrisu cewa kukan gidan su har da kururuwar gidan su yake yi yanzu.
Zuwa lokacin sun shiga tsakiyar gari, Amani ta bude hanci da ido tana shan
kallon alummar wannan jiha dake cikin janhuriyyar Nijar, ta fahimci cewa sittiru,
kamanni na halitta da dukkan aladar su ta barranta da ta inda ta fito, suna ta
gudanar da harkokin su na yau da kullum cikin sukuni da godiyar Ubangiji, domin
kuwa alummar wannan yanki na Diffa mafi yawa talakawa ne likis, masu abin yi daga
kiwon dabbobi (livestock production), kasuwancin waje (export trade), jimar fatar
rakumi da sauran su. Sun kuma kasance maabota biyayya ga shuwagabannin su, wato
sarakunan yankin Diffa.
Shiga nan fita can Muktar bai manta hanya ba, bai manta koina ba, kamar wanda
ake bankado komai daga cikin kwakwalwar sa ana nuna masa, kamar jiyan nan ya tafi
daga Diffa. Haka yake ji yanzu da ya dawo cikin ta kamar ba shekara goma sha biyar
ba, haka rayuwar sa ta baya ke rewinding kamar kaset din video a cikin kan sa, tana
tuna masa duk abinda ya faru a baya.
Sai suka hau wani mikakken titi dodar mai nisa, wanda daga shi Amani ta soma
hango wani dogon kasaitaccen gini, wanda tsahon sa da fadin sa ya kai daidai da
kilomeita (2,988), wani katafaren gini suke dosa wanda daga can sama aka rubuta da
harshen larabci Al-iimaarat-al Diffa wato Diffa Emirate da harshen turanci. Suka
cigaba da tafiya Amani na cewa a ran ta wato in ka zo garin, sai ka fara kaiwa
sarki gaisuwa dole, kafin a bar ka ka tafi cikin gari inda ka zo.
Can kuma ta ce Watakila kuma Baban sa bawan sarki ne, shi yasa ya tura shi
birni neman kudi maimakon ya makale abin sa su yi bauta tare.
Ai kuwa ta kasa shiru, ta kasa barin tunanin ta a ran ta, lokacin da ta ga sun
hau titi fetal wanda ya mika har cikin fadar Diffa. Masu tsaron babbar kofar
masarauta ta farko suka tare su a kofar shiga, amma da Mukhtar ya sauke tagar sa,
suka ga wannan nadin dake kansa da wannan amawalin da kuma tambarin da ke jikin
rawanin, sai kawai suka daga musu kofa suka wuce ciki. Gasunan gasu nan har gate na
biyu, shima kamar na farko daga ya sauke glass sun ga irin nadin sa da amawalin sa
sai suka daga masa kofar masarauta suka nausa ciki.
Daga nan sai gate na karshe, wanda shine na uku kuma daga shi sai fada.
Anan ne aka dan takura da binciken bayan motar su kafin Mukhtar ya sauke glass,
Amani na cewa Daddy ashe dan naka bawan sarki ne? Ko ko dan bayi ne ka ga duk sun
san shi. Mamma Jalan ta kusa zagin ta, don ita jikin ta ya fara bata abubuwa masu
yawa, amma Amani tana haukan ta irin wanda bata san ranar shiryuwar ta ba. Baba Idi
ne ya ce mata shi dan bayi ba mutum bane? Jaira marar mutunci. Sai tayi dif!

Wani tsohon bafade tukuf, ya dogaro cikin kayan dogarai na jikin sarki sosai ya
zo bakin tagar da Muktar yake, yace Samari, na gan ka da Amawalin gidan nan,
Amawalin dana baiwa Mainan Diffa, amma ban shaida ka ba, ko zaka bude amawalin in
gan ka sosai, kafin mu yi muku iznin yin parking a kofar fada?
Sai kawai Mukhtar ya sa hannu yana warware rawanin kan sa, yanayi wa tsohon nan
murmushi idanun sa fal hawaye. A hankali ya ce Baba na Katchalla! Tsoho Bafaden nan
sai ya fadi kasa, yana fadin Allah ya taimaki Mainan Diffa, barka da dawowa hasken
Diffa!
Wannan batu da wannan tsohon bafade ke yi shi ya janyo hankalin sauran fadawa
duk suka taho da gudun gaske, wajen hannu goma ne ya budewa Mukhtar kofa a gigice,
suna faduwa suna tashi suna fadin Hasken Diffa ya dawo, barka da dawowa hasken
Diffa, barka da dawowa tauraron Diffa, Maina ka sauka lafiya ka taka a hankali.
Allah ya kare tauraron Diffa, haske maganin duhu, hadari malafar duniya.
Daga nan aka bude musu kofa a ka bazawa Mukhtar babbar riga aka kareshi ya
sauko daga motar.
Tuni har wani ya sheka labari cikin gida wai ana tsammanin Mainan Diffa ya
dawo, zancen nan nan da nan ya isa kunnen Sarki Issouffou Massaoudou, wanda ke
kwance a turakar sa a lokacin bayan ya sha magani, ya soma shirin dan mikewa ya
kwanta kafin lokacin da zai fita fada. Sai ga wayar sarkin fada wanda ya manta
shekaru nawa rabon da ya kira shi a waya, don a kaida fadawa basa kiran sa a waya.
Kamar bazai dauka ba amma sai yayi tunanin banza bata kai zomo kasuwa haka
kawai Katchalla ba zai kira shi ba, sai ya daga. Yana dagawa kuwa sarkin fada ya
fashe da kuka yana fadin nayi rantsuwa da Allah ga Maina ya dawo, ka san dai cikin
kowanne hali bazan kasa gane shi ba ko da bai zo da rawanin sa ba.
Sarki Issouffou Massaoudou a kwance yake, amma sai ganin sa yayi a bakin kofa
ya manta cewa jar hula ce da ake kira Dara da rigar shan iska mara hannu kadai a
jikin sa, ya kama hanyar kofar da zata sada shi da hanyar fada.
Fadawan da ke tsaron kofa sun kidima da ganin fitowar Sarki a haka yana ta
surfa uban sauri, aka kuma rasa wanda zai tare shi ya tuna masa babu amawali da
alkyabbar sa a tare da shi. Farin dattijo amma ba tukuf ba, kyakkyawan Balaraben
Diffa na gaske wanda yawan shekarun sa bai boye kyawun surar sa na lokacin kuruciya
da tsananin kamannin sa da Mukhtar ba.
A lokacin har an shigar dasu Mukhtar fada, baka jin komai sai tashin kirarin da
fadawa ke zubewa a kasa suna yi masa.
Hadari malafar duniya, hadari sa gaban ka inda kake so, gaba salamun, baya
salamun, haske maganin duhu Zaki dan Zaki, Majina gishirin yaro, tsawa mai ratsa
gidan arna. Kunun bagaruwa cika ciki har makogaro. Dan Sarki jikan Sarki kuma sarki
mai jiran gado.
(Wannan kirari ba da hausa suke yin sa ba, suna yin sa ne da vernacular
language din su wato Chadian Arabic daya daga cikin yaren Diffa Arab). Wani babban
bafaden kuma yace Zakin duniya makiyanka fadawan ka, ana kin ka ana rusuna maka, ba
yin kan ka bane yardar Allah ne da adduar iyaye ya dawo mana da kai. Allah Ubangaji
ga Mukhtar dan Issouffou Massaoudou ya dawo gida. Hasken Diffa ya dawo, duhu ya
yaye!.

Amani da iyayen ta da ke kallon abinda ke faruwa kamar a majigi, sun kasa ko
motsin kirki. Amani ta lura hatta tafiyar Mukhtar ta canza kan ta da kan ta, ba
irin wadda yake yi a baya bace. Me ke faruwa ne haka a gaban idon ta? Wanene wannan
Mukhtar din? Wane alamari ne tattare da shi haka?
Jalan, wadda ke tura Alhaji cikin wheelchair zamu iya cewa mamakin ta ragagge
ne, ko dama a tunanin ta tun ganin ta da shi na farko, bai yi mata kama da komai ba
sai dan sarauta maabocin kyakkyawar nasaba, duk wasu attributes na sarauta sun
bayyana kan su a tare da shi da halayen sa.
Baba Idi da Baba Sahura sai zare ido suke don kuwa Sahura har fitsari ta yi a
wando data ga wani katon Zaki mai rai a zaune, amma bai ci kowa ba, sai daga baya
ta gane zane ne da aka yi da ceramic (architect) amma kamar real image na zaki mai
rai, tambarin Issouffou Massaoudou Kenan, wato Zaki dan Zaki, zakin Diffa.
Alhaji Usman dai hawaye yake sharewa a fakaice, ba tare da ya bari an gane
kuka yake ba, Mukhtar ya shammace shi yadda baya zato, ashe dan sarkin Diffa ne mai
jiran gado yake masa bauta iya bauta shekaru kusan goma!
Dadin abun ya kyautata masa ya kaunace shi, irin yadda ko yan wan sa na jini
bai yiwa hakan ba. Allah ne ya hada shi da Mukhy amma bai taba kawowa ran sa wai
dan sarki bane mai jiran gado. Yafi dangantawa ma da cewa bashi da kowa a duniya
shiyasa baya ko so a yi masa zancen ya je ganin gida.
Karyar ku makiya da mahassada, karyar ku ta kare mahainta, yau Allah ya maido
Mainan Diffa gida (Maina na nufin Yarima mai jiran gado a Diffa, kamar yadda
Biyamaradi yake a Maradi).
Ire-iren kirarin da ake ta yi wa Mukhtar kenan har aka bashi kujera kusa data
Sarkin Diffa, amma sai ya ki zama ya zube a kasa yana kukan farin ciki da godiya ga
Allah.
A haka Sarki ya fado fadar, sarkin fada ya biyo shi da Alkyabbar sa da amawalin
sa suka rufe kofar fadar aka hana kowa shiga bayan shigewar Sarki.
Yana zuwa da Mukhtar ya fara tozali, ya ce Mon pils (Da na) Mukhtar da gaske
nake gani? Koko ire-iren mafarkai na ne? Sai yayi baya luuu! Zai fadi, kasancewar
dama yana fama da hawan jini tun tafiyar Mukhtar wanda ake treating din sa tun
lokacin, cikin zafin nama Mukhtar ya tare mahaifin sa ya rungumo shi a kirjin sa,
(for the first time) a rayuwar sa da jikin sa ya shafi na mahaifin sa, suka zube a
kasa tare.
Nan fadawa suka kare scene din da hannayen manyan rigunan su aka umarci kowa ya
fita sai manyan fada kadai. Mukhtar sai firfita yake ma sarki da rawanin sa yana
fadin ka yafe ni Ya Abiy, na dawo kenan babu inda zan kara zuwa, koda zan cigaba da
rayuwa yadda kake so.
Da kyar aka samu Sarki Issoufou ya zauna a kujerar sa, sannan ya yi umarni da
ayi wa wadanda suka kawo Mukhtar sauka ta alfarma a babban masaukin bakin sa.
Ummami na can cikin gida amma tuni labari ya kai mata ta bakin Jakadiyar Sarki
marikiya ga Mukhtar, wadda ta shiga turakar ta kai tsaye ba tareda ta jira an mata
iso ba, ta same ta tana haki, tana cewa yanzu wani bafade ya gaya mata wai Maina
yana cikin fada bata san ko da gaske bane don yace an kulle fada, an hana kowa
shiga.
Mowar Sarki, sai ta mike ba tareda rakiyar kowa ba aka ga ta kama hanyar fita,
akwai wata boyayyar kofa ta cikin turakar Sarki wadda yakan shiga fada ta cikin ta
wani lokacin, ta can Mowar Sarki ta bi ta isa fada, Mukhtar sai ganin Ummami yayi a
gaban sa, ta dubi Mukhtar shima ya dube ta ta taba shi ta tabbatar dan ta ne kwalli
daya a duniya Mukhtar dan Issouffou Massaoudou, wanda ya bar su yau shekaru goma
sha biyar! Kafin Mukhtar ya ambaci sunanta wanda ya kakare a makogaron sa ya kasa
fita, Ummami ta fado jikin sa luuu! A sume.
Mukhtar yana fadin Ummami kada ki yi min haka.. kada ki mutu bamu gana ba,
bamu fayyacewa juna zuciyar mu ba. Na yi nadamar tafiya ba tareda na fayyace muku
abinda ke rai na ba, kuma kun bani uzurin ku! Yanzu da girma ya same ni na san kuna
da uzuri fiye da nawa. Aka yayyafawa Ummami ruwa ta farfado sai ta rike Mukhtar ta
fashe da kuka.
A lokacin an fita dasu Amani da Mamma da Daddy da su Baba Idi zuwa masaukin da
Sarki yayi umarnin a kai su. Wani hamshakin gini ne na sarauta da yaji kujeru royal
chairs na alfarma, da dakunan barci da aka kawata da gadaje na kasaita, babu abinda
babu a wannan guest house din ga dakunan barci rututu. Aka shiga sauke musu kabakin
abinci har da naman Dawisu, aka ce su kintsa kafin washegari Sarki ya gama ganawa
da Maina zai neme su.
In ka ga fuskar Amani a cikin guest room dinnan ta koma kamar jikakken
tsumma, sabida yadda tayi cooling, tana ambaton Ya Salaamu sallim, a cikin ran ta,
harda su istighfari, tana neman wanda zasu hada ido ko karin bayani ne ta samu,
amma ina! Mamma Jalan ko kallon ta taki yi, sai hidima take da mara lafiyan mijin
ta. Wata irin nadama da dana sani suka zo suka lullube Amani, mutumin data raina ta
ke wulakantawa, ta cewa shege, ta cewa bawan gidan su, kai babu irin sunan
kaskancin da bata kira Mukhtar da shi ba shekara da shekaru ashe ya fi ta kyawun
nasaba, dan Sarki ne jikan sarki mai jiran gado, wanda in nasaba zaa bi ba ikon
Allah ba, da bata isa zama matar sa ba.
Ta daga ido tana kallon wannan kasaitattar hamshakiyar masarauta wadda ko
masarautar Katsina bakidaya data sani bata kama kafar ta a kasaita da shaharar
mulki ba.
Kada dai Allah ne yake yi mata talala da laifukan ta, kalaman ta marasa
Tauhidi da girman kan ta? Yanzu wace izza zata kara yiwa Mukhtar da gorin nasaba?
Dama Jalan ta ce mata ta guji ranar dana sani.
Ya Ilahal alaameena na tuba! Na tuba Ya Ubangiji na tuba, daga yau baki na ya
daina fadar abinda ba alkhairi bane a kan kowanne dan adam, na daina raina kowa, na
daina tunain nafi kowa gata!
Ita kadai take furta wadannan kalaman kamar zautatta sabon kamu, cikin
kidima, Mamma da Daddy duk suna jin ta, Sahura na yagar cinyar Dawisu ta ce ah to
ai duniya makaranta ce, ta ishi kowa riga da wando har da hula. Allah da kan sa
yayi hani da girman kai, ya bada misali da Shaidan da Annabi Adamu Alaihissalamu,
Ubangiji da ya halicci dan adam ya karrama shi akan dukkan halittun sa, kai dan
adam waye da zaka kaskanta dan adam dan uwan ka, don kawai kana tunanin ka fi shi
arziki? Ai ko hausawa sun ce rabon bawa da arziki mutuwa ce.
Baba Idrisu ya ce kwarai da gaske, baka debewa bawa tsammani da arziki sai ya
mutu! Uwa ki ji tsoron Allah ki gyara halayen ki na raina mutane, kiyi karatun ta
nutsu, nan dai kin gani gidan sarauta ne babu ta yadda zaayi su dauki halayen ki na
banza da wofi, idan ma bamu koma tare ba kenan, tunda ke din ba yar sarauta bace,
na san kuma yayan sarakuna yayan sarakuna ya uwan su kawai suke aure.
Mamma Jalan ta ce da ta fi gane shayi ruwa ne. Don in ba Mukhtar din ba sarkin
hakuri da girmama iyayen ta wa zai iya kwasar ta? Ai Amani an rako mata!
Yau dai gaki gidan sarautar Diffa, ko ki iya takun ki, ko ki ji ki a kofar
masarauta, ko kuma ki kare karkashin azaba da mulkin kishiyoyi.

Idanun Amani suka wani irin raina fata, zuciyar ta ta tsinke, wai bata san
tana da kishi ba sai yau da Mamma ta yi mata fatan kishiya, to ta Allah ba tasu ba
su duka, ta san Mukhtar yana son ta ko bai fada ba, ta ga hakan muraran ranar su ta
karshe da shi a Saliyo gidan Mamma, ta san ko saboda Alhaji ba zai wulakantata ba
balle yayi mata kishiya. Ta san ta yi kuskure ba kadan ba amma a bata dama zata
gyara. Ba wai a bita da mugun fata ba. Sai ta saka kuka tana cewa.
Mamma ke uwa ta ce, duk abinda kika fada zai iya kama ni, ki fadi alkhairi a
kaina da Mukhy ko kiyi shuru. Ta yaya zaki yi min fatan kora ko kuma na kishiya?
Baba Sahura ta fashe da dariya tana fadin yau kuma? Lallai Amale ya ga Zaki.
Yarinya wa ya gaya miki Bornu gabas take, miji irin wannan ake cewa baa so banda
wauta da hauka?
Daddy ne kawai ya ji tausayin ta, yadda suka taru suka yi mata caaa! Ganin
yadda duk ta bi ta muzanta. Yanzu kam ta gama saddaqarwa Mukhy ya fi karfin ta,
idan bata yi saa bama tare da iyayenta zata koma Katsina a matsayin sakakkiyar
bazawara. Sunan ta ya koma bazawara. Irin iskancin da ta tata masa da kaskanci da
rainin hankali da kyar zai iya yafe mata tunda ya dawo cikin gatan sa.
Na tuba Ya Ubangiji na tuba! Amani ta fada a fili tana hawaye. Alhaji daga
zaune ya mika mata hannu ya ce zo nan Uwata, rabu da su kin ji! Bakin su ya sari
danyen kashi. In dai Mukhtar dina ne dana sani wallahi zai yafe miki, kuma shi
mutum ne kaifi daya bana jin rashin hankalin ki na damun sa, tunda yace ya amshe ki
to da gaske ya amshe ki, bana jin dawowar sa gida zata sa ya canza magana. Ke dai
ki yi kokari daga rana irin ta yau ki canza halayen ki, ta hanyar komawa AMINA ba
AMANI ba.
Aminatu Mamar Manzo maaobociyar ilmi da hankali da iya zama da mutane, kin ji?
Ya shiga bubbuga bayan ta yana lallashin ta domin kukan nadama take yi tukuru.
Tana mai adduar kada Allah ya kama ta da laifukan ta a kan mijin ta Mukhtar.
Daddy kai kadai ne ka yi min fatan alkhairi, na gode Daddy har abada na san
inada kai, na san ba zaka bari a wulakantani ba, wai don nayi laifi na kuma gane na
yi laifi na tuba.
Mamma don Allah ki hyi hakuri ki sa min albarka.
Mamma ta kora ruwan tataccen inibi a tambulan na tangaran mai garai garai ta
dube ta yanzu da rahma a idanun ta, ta ce idan da gaske kike kin tuba, Shi Ubangiji
mai afuwa ne kuma yana son masu yawan tuba daga laifin da suka san sun aikata.
Ni kuma zan taya ki da adddua a kan Allah ya huwwace miki zuciyar sa, ya baki
dukkan soyayyar da ke zuciyar sa, ya kade fitina a zaman ku, ya baku zuria mai
albarka.
Amani ta ruga da gudu ta rungume Maman ta tana na gode Mamma, na gode sosai.
Sun kwana suna tattauna alamarin nan cikin tuajjibi da mamaki iri-iri, Mukhtar
dan baiwa ne hakika, wanda bai taba alaqanta kan sa da wata daukaka irin haka ba a
inda ya tabbatar baa san ko shi waye ba, amma hakika wasu attributes nasa da
yawancin personality din sa masu tsinkaye a cikin su irin Mamma, sun ce sun sha
alaqanta shi da babbar sarauta ko babbar nasaba.
Suka kwana hira da tsarkake tsarkin mulkin Ubangiji.
**** **** *****

Haka suma Uba da dan da mahaifiyar sa, sun kwana tare a turakar Sarkin Diffa,
kamar su maida dan nasu Mukhtar cikin su. Wani abu ne da Mukhtar bai taba samu tare
da su ba tun haihuwar sa, wato closeness sai yau. Don haka (he cant control his
tears).
Maina ina ka je? Maina ina ka shiga? Maina ka bar mu, shekara goma sha biyar ba
kwana goma ba Maina in ji Ummami, tana share hawaye da gefen laffayar ta.
Ummami I thought kun fi son hakan, kun fi son in yi nisa da ku din, ba kwa so
in rabe ku, kamar ba ku kuka haife ni ba.
Na yi kokari na jure hakan tun haihuwa ta amma dana fara girma sai abun yake
neman zame min ciwo a zuciya ta, dole na zabi in tafi in yi rayuwa a inda bazaku ko
samu labari na ba, tunda zamana tare da ku bai da wani amfani a gare ku.
Daga baya kuma kullum na yi kokarin juyowa gida bana iyawa sakamakon dabaibayin
dake zuciya ta.
Rana daya Allah ya yaye min wannan dabaibayi, naji hankali na ya yo gida, Im so
sorry Ummami, har aure na yi babu jimawa bada sani da yardar ku ba, but I have no
choice, saboda mahaifin ta has been my savior, my shelter for a very long time.
Nan ya gaya musu cewa bayan ya karbi kwalin kammala karatun sakandire tare da
yayan bayin gidan a makarantar gwamnatin Diffa da yayi ya kasa cigaba da zaman
kasar Nijar, ya yanke shawarar shiga duniya ya nemi ilmin

Please Login or Register in order to submit comment