Reading Amani 3 by SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da zai taimaka masa ya
dogara da kan sa. Tunda sun nuna basa bukatar shi a rayuwar su sun bar shi a
bangaren bayi yana rayuwa tare da yayan bayi, karkashin kulawar Jakadiya da mijin
ta Sarkin fada, wato Bafade Katchalla wanda shi ya fara gane shi yanzu ma da ya
dawo.
Ya ce tunda na taso na ganni a hannun jakadiyar Ummami, ita ta raine ni, saidai
lokaci lokaci ta kaini gun Ummami ta kuma dawo dani bangaren da take wato bangaren
bayi.
Dana fara girma, ma sai ta rage kai ni gun Ummami, itama ba koyaushe take wuni
da ni ba tafi wuni a cikin gida, sai dai in yi ta wasa da yaranta maza guda biyu
saanni na, sai na dauka ma su suka haife ni wato ni dan jakadiya da Baba Katchalla
ne, musamman da suka saka ni a makaranta tare da Shettima da Ari, wato yayan su,
muke zuwa tare kullum muna dawowa.
A hakan sai na fara mantawa da Ummami, wadda nake gani lokaci lokaci, kai kuwa
Maimartaba dama ba a zancen ka, don tsakani na da kai sai dai in hango ka a turakar
ka ko a fada, ko a kan Rakumi idan ana wani festivities din kamar misali bikin
sallah ko na aure ko na nadin sarauta.
A baya Baba Katchalla na zuwa da ni fada mu zauna a gefe nida shi, bazan manta
ranar da kayi masa tsawa ba, ka ce kada ya kara kawo ni fada, mai bakin baya ne ni,
tunda ga kai na ko batan wata baa kara yi a gidan ka ba.
A ranar ne ma wasu a fada suka san ni dan Sarki ne. Nan ne aka yi ta kuskus a
gari wai ashe Sarki yana da Da namiji amma baya son yaron. Ya barwa bayi shi.
Wannan zance har a makaranta an yi min gorin sa, lokacin ina karatun sakandire.
A wani dare na tsuye jakadiya ina tambayar ta da gaske ni dan sarki ne? Kuma Mowar
Sarki wato Ummami da muke zuwa wajen ta lokaci lokaci har wani lokaci ta bani apple
ita ce mahaifiya ta? Jakadiya ta tabbatar min haka ne, amma bata san dalilin ku na
ajiye ni tare da su ba, kodayake tace Sarki da Mowar gida basu da trusted servants
a cikin bayin su kamar ita da Katchalla.
Tace Sarkin Diffa ba mai yawan haihuwa bane, shiyasa yake ta aure daga kasa-
kasa don ya samu haihuwa, a irin haka ne ya auro mahaifiya ta daga wata kasa cikin
kasashen Afrika, yayan sa biyu kacal kuma duk mata ne tare da matar sa ta lalle
wato uwargidan sa da mai bi mata wato mata ta biyu. Daga kan su bai kara samun
haihuwa ba sai da ya auri Ummami, kuma tun haihuwa ta suka bata ni, shayarwa ma a
boye Ummami ta shayar da ni don sai ta bita cikin sirri ta roke ta.
Bayan ta yaye ni ma kuwa bata bukatar a kai mata ni inda take. Ni ne dai dana
yi hankali na ji ba wanda nake so a duniya irin ki Ummami, sai nake satar jiki ina
zuwa inda kuke, wani lokacin inna leka inda kuke zama da laasar zan same ku kuna
sallah tare ke da Sarki, ko kina zuba masa abinci ko kina masa yankar farce, har
rannan wani bafade ya kama ni ina leken ku ya taska min mari, shine fa ban kara
leken ku ba daga ranar.
Watarana Baba Katchalla yace muje ana bikin Yaya ta a cikin gida, nan na bishi
muka je har fada naga irin auren gata da aka yi wa yar uwata, akan taguwa aka kai
ta Tahoa inda ta auri dan sarkin Tahoa, ni kuwa inna shiga cikin gidan na hau rabe-
rabe kenan kamar mara gaskiya, hatta sittiru na tare ake din ka mana da Ari da
Shettima, babu wani banbanci tsakanina da su. A makaranta ma ajin mu daya da su.
Dana fara hankali sai nake tambayar kaina to meye dalilin hakan da sarki da
Ummami suka zabarwa rayuwa ta? Na sa a raina bakin bayan da ya taba ambata min ne
dalili, wato daga kaina ko batan wata wata matar sa bata kara yi ba har ita
Ummamin. Amma ai wannan bai isa dalilin da zasu sarayar da rayuwa ta a hannun bayin
su ba, sai ma dai yayi dalilin da zasu daukaka daraja ta fiye data kowa a
masarautar.
Bani da wata shakuwa ko kusanci da ku da zai sa na iya yi muku wannan tambayar.
Ban ma isa in je inda kuke kai tsaye ba.
Na yarda iyaye na kun haife ni ne da gaske, amma kuma baku kauna ta!
In na tuna hakan sai wani irin bakin ciki ya murde ni, har ya zame min habit,
daga baya bayan na kammala sakandire na ji bazan iya cigaba da zama a Diffa ba,
gara in tafi inda bazaku kara jin labari na ba, tunda kun haife ni bisa kuskure
amma bakwa kaunata ko miskala zarratin.
Wannan abu ya cigaba da bakanta min dare da rana, har na koma tamkar depressed,
na daina walwala, na daina shiga cikin saanni na, na yarda bakin baya na zai iya
shafar kowanne yaro iyayen sa su tsane shi.
Duk da babu abinda Baba Katchalla da Jakadiya suka raga min, suna ma kula da ni
ne har fiye da yadda suke kula da yayan su Ari da Shettima. Rana daya na yanke
shawarar barin Diffa, to amma ina zani bani da ko sisi?
A hakan ne aka ce sakamakon mu na sakandire ya fito, kuma na ci jarrabawa ta
da sakamako mai kyau wanda yafi na kowa, don haka gwannatin kasar Nijar ta dauki
nauyin karatun mu ni da wasu dalibai zakakurai iri na zuwa kasar goyon mu wato
Faransa. Aka damka min admission dina da tikitin jirgi, na so in gayawa Baba
Katchalla amma zuciya ta ta kwabe ni, kan cewa zai iya hana ni tafiya, ku kuwa dama
na san ba damuwar ku bace rayuwa ta ce, baku da matsala da wannan, hasalima na yi
amanna farin ciki zaku yi in yau aka ce na bar Diffa.
Hatta malaman makarantar mu basu san cewa ni Maina ne ba, sun dauka ni dan bawa
Katchalla ne wanda kusan kullum shi yake kawo mu makaranta ya kuma zo ya dauke mu.
Don haka da aka fara jigilar daliban da suka samu scholarship na sulale na tafi
Agadez tare da sauran dalibai yan uwa na, inda daga can jirgin mu ya daga zuwa
France. Acan ne aka rarraba mu zuwa jamioI daban daban a cikin Faransa, ni aka bar
ni a Jamiar Paris Saclay University.
***** **** ****

RAYUWA TA A FARANSA
R
ayuwa ta a matsayin dalibi a birnin Paris, rayuwa ce irin ta kowanne dalibi mara
gata sai na gwamnati, mai fafutuka da neman ilmi da gumin sa, gwamnatin kasar mu na
bamu alawus wanda da shi muke rike kan mu. Na yi wani dogon rashin lafiya bayan
tahowa ta kamar bazan rayu ba, don sai da na kwashe watanni biyu a asibiti bansan
inda kaina yake ba, bayan na farfado da kyar, na ji a cikin kaina bani da buri irin
na kara nesanta kaina da gida, kuma har Paris din ji nake ta min kusa da Nijar amma
hakika ina son samun kwalin degree dinnan, shiyasa na tsaya. Da kyar na samu na
hada karatun domin banida cikakkiyar lafiya kuma likitocin kasar duk kwarewar su
sun kasa gano takamaimai me ke damu na.
Akwai wani abokin karatuna Musulmi, Faiq, da ya zo daga kasar Masar, shi ya
bani laqanin kullum in karanta ayatul kursiiyu kafa bakwai in tofa a ruwa da safe
in sha kafin in ci komai. Da wannan lakanin na fara samun lafiya har na kammala
karatu na da kyakkyawan sakamako.
Daga wannan lokacin ne tallafin da kasar mu ke bamu ya yanke mana, wato dama
scholarship din mu iya degree ne, sai na shiga tunanin hanyar da zan bi in yi
sponsoring karatu na na gaba wato masters, duk dai don in samu damar cigaba da zama
a Paris kada in koma gida.
Ayyuka na neman rufin asirin dalibi iri-iri babu wadanda ban yi ba, tun daga
wanke-wanke da share-share a hotel, direban bus, jiran shago, zaman library da kuma
receptionist, da haka na kukkulla na kukkula na dinga biyan kudin karatun masters
dina in instalments (a rarrabe) har Allah ya taimake ni na samu shaidar kammala
degree na biyu, daga nan na dukufa neman aiki kwakkwara amma ban samu ba, ko in ce
ban dace ba, ina tunanin fallewa zuwa Hong-Kong again, don neman aikin yi, Allah ya
hada ni da Ubangida na na yanzu, wato Alhaji Usman Faskari.
Nan ya labarta musu komai na irin haduwar da suka yi da Alhaji, ya biyo shi
Najeriya ya bashi gida da aiki ya kuma ja shi jikin sa da amana irin yadda ko yan
uwan sa bai yi wa ba, duk tarin alkhairin Alhaji gare shi sai da ya fada musu har
zuwa lalurar data same shi wadda tayi sanadin bashi auren AMANI da Alhaji Usman
yayi. Yadda a rana daya yaji duk wani dabaibayi da ke zuciyar sa a kan Diffa ya
yaye, da kuma karfin zuciyar da ya samu na dawowa gida karkashin umarnin Alhaji duk
ya fada musu.
Tun kafin Mukhtar yayi nisa da labarin nan daga Maimartaba Sultan Issoffou
Massaoudou har maidakin sa Ummami kuka suke yi sosai.
Sarki Issoufoou ya janyo Mukhtar jikin sa ya rungume shi yana kuka sosai da
hawayen sa, yana rokon sa ya yafe masa, ya ce da Mukhy (cikin vernacular language
din su).
Moukhtar, duk abinda muka yi dinnnan muna sane, we did it to protect you from
envy, hatred, evil eyes, bad luck, and to save you, as the only male child that I
have, to make sure you get the throne of Diffa Emirate at an appropriate time.
Ni da kaina na hana mahaifiyar ka jan ka a jikin ta, nida kaina na ce ta fidda
kai daga ran ta, Allah zai raya mana kai. Ba zaka taba zama sarki ba idan ka samu
gatan da yayan sarakuna ke samu, kasancewar kai din daban ne, zagaye nake da makiya
haka mahaifiyar ka zagayeta ke da kaidin mata yan uwan ta iri iri musamman da ta
haife ka, kasancewar ni mutum ne mai yawan aure-aure, amma tunda muka watsar da kai
sai duk hankalin su ya bar kan ka, ya koma kan yadda zasu yi su samu nasu yayan
suma, don na nuna bana kaunar ka ban damu da rayuwar ka ba.
Mukhar dauriya iya dauriya irin wadda ba duka iyaye zasu iya ba a kan dan da
suka haifa kwalli daya muka yi a kan ka, domin mu tseratar da rayuwar ka, amma duk
halin da kake ciki a gidan Katchalla wallahi mun sani. Kuma muna kulawa da komai
naka.
Hatta tafiyar ka Farisa mun san da ita, nine kuma na sa aka baka scholarship
daga ofishin Baare Mainasara (shugaban kasar Nijar na wancan karnin).
Haka daga sanda ka bar Farisa ne muka daina samun labarin ka sannan bamu san
ina ka koma ba.
Malamai na daban-daban na cikin gida kullum gayamin suke in kwantar da hankali
na domin kana raye, kuma a kyakkyawan hannu mai tsafta, amma na kasa kwantar da
hankalin nawa.
Kullum (blaming) kaina nake yi kan ko dai hukuncin dana yi wa rayuwar ka ba
dabara bace karbabbiya? Ko dai kuskure na yi maimakon (saving life) din ka?
Wannan tunanin da wannan nadamar su suka taru suka kwantar da ni na lokaci mai
tsaho. Musamman da aka tabbatar min ka bar Farisa baa san inda ka shiga ba kuma.
Har gobe a kan treatment nake, mahaifiyar ka kuwa ka gan ta yanzu bata gani sai da
Gilashi, sabida yawan kukan tafiyar ka Maina.
In mun yi kuskure cikin abinda muka aikata muna rokon Allah ya yafe mana, kai
ma ka yafe mana. Sannan madallah da jin cewa kayi aure, lokaci ya yi da zan bayyana
ka ga duniya.
Zan maka bikin aure irin wanda baa taba yin irin sa a masarautar Diffa ba, zan
gayyato duk sarakunan jamhuriyyyar Nijar, in gabatar da kai gare su, sannan zan
baka sarautar Diffa tun ina raye. Kafin nan zan maka nadin sarautar Mainan Diffa ka
fara zama a fada tare da ni don ka koyi shaanin mulki na lokaci mai tsaho.

Duk wadannan abubuwa da ke faruwa yau, Mukhtar couldnt believe them, don ya
dauka mafarki yake yi, ire-iren mafarkan da dan adam in yana yin ba ya so ya farka,
yana rokon Allah da dai ya farka daga wannan mafarkin, gara ya zarce a cikin niimar
sa, wato ya karasa mutuwa a cikin dadin sa..
***** ***** *****

WASHEGARIN RANAR
Da wayewar gari, Sarki Issouffou Massaoudou ya aiko a tafi da su Alhaji cikin
masarauta, yasa aka kai su dakin da yake ganawa da manyan bakin sa, sannan aka
shirya musu karin kumallo tare da Sarki da Ummami. Wanda ya kai su shigifar ya ce
su jira kadan, Mai Diffa na zuwa tare da Mowa.
A lokacin Mukhtar na can yana ramuwar barcin gajiya bai ko tashi ba, don kwanan
zaune suka yi da iyayen sa, tun bayan da suka dawo masallaci sallar asubahi aka
bude masa wata shigifa da ke kusa da na mahaifin sa, yake barci har zuwa lokacin,
barci na kwanciyar hankali irin wanda bai taba samu ba.
Su Jalan sun nutsu suna kallon sarautar Allah, domin ko a cikin masarautun
Nijar Diffa na sahun farko, komai na masarautar mai ban shaawa ne da ban mamaki
kuma irin ancient dinnan amma aka zamanantar da shi, suna kalle kalle suna jiran
isowar Mai Diffa da Maidakin sa, wadda suka ji an kira Ummami (Mowa).
Can suka jiyo takun sa ya durkako inda suke. Cikin taku na haiba da kamala.
Yana shigowa duk suka mike domin girmamawa. Haske da kwarjinin addinin Musulunci ya
bayyana sosai a tare da farin balaraben dattijon. A nitse ya zauna a kujerar da ita
kadai ce kujerar mulki a dakin, wanda yafi dacewa a kira shi palace, ba jimawa da
zaman sa sai wata kofar ta kara budewa. Doguwar matar cikin kyakkyawar laffaya da
farin gilashi a idanun ta, ta shigo, ita kadai ba tare da kowa ya rako ta ba.
Ta nemi guri gefen maigidan ta ta zauna kasan kafafun sa, fuskar su fal annuri
da maraba dasu. Kafin kowannen su ya ce komai aka ji Mamma Jalan ta tsinke da
salati ta ce Yaya AISATA!
A firgice Ummami ta juyo, jin muryar kanwar ta, Jalan. Da gudu Jalan ta sheka
ta isa gareta ta rungume ta. Sai kuma ta saka kukan farin ciki. Da kyar Aisata ta
banbarota daga jikin ta. Ta ce Jalan, ke ce koko ido na ne? Aah ke zan tambaya da
gaske ke ce? Kuma Mukhtar dan ki ne kenan? Aisata (burst into tears) tace ban taba
gaya miki cewa na haihu ba, sabida bamu kara haduwa ba tun rabuwar mu sai aike ne a
tsakanin mu, sabida a kaida matan gidannan basa fita, ko asibiti bama zuwa saidai
likita mace ta zo har daki ta duba mu, sannan da matsalolin da suka biyo bayan
haihuwar tasa, da muka fara waya dake bayan kin yi aure na biyu kenan, ni ban san
meyasa na kasa gaya miki ina da Da ba, kodayake bana maganar sa sam, balle irin
wannan a muhimmiyar magana ta hada mu da wani nawa ta waya, daga baya kuma bama
tare dashi ma, daidai lokacin rasuwar Abbu sanda na aiko dan aike na wajen ku, aike
na na farko gida Kenema, lokacin Maina ya riga ya gudu.
Me ya kai ki Najeriya yanzu? Na dauka kun rabu da mijin ki na can tun su Abbu
na raye, har kin yi wani auren da Lukman kin samu yara? Daga baya kika gaya min a
waya ya rasu, ta ina kika hadu da yan Najeriya bayan na san kina Kenema?
Suka rungume juna ana ta mamakin wannan ikon Allah, Jalan ta gaya mata Alh.
Usman shine mijin ta na fari wanda aka aura mata a kasar Katsina, suka rabu bayan
ta haihu, itama rabon ta da yar tun lokacin, sai yanzu da kaddara ta sake hada su.
Ta nuna mata Amani dake ta sakin fitsari a kai-a kai daga zaune ta cikin wandon ta
a lokacin, sabida yadda ta kara firgicewa da alamarin Ubangiji, wato Mukhy Yayan ta
ne na jini kuma?! Bayan nadamar data sha jiya bata ko gama fita daga cikin ta ba,
yau ga gagarumar nadamar data fi ta jiya ta kara samun ta. Jalan ta nunowa Aisata
ita da hannun ta manuni.
Kin gan ta itace yar da na haifa na baro a Najeriya sunan ta Amina, sai da
girman ta na gan ta, kuma ita ce matar Mukhtar a halin yanzu, domin a hannun
mahaifin ta ya zauna a gidan su duk tsayin wannan lokacin.
Ummami sai ta mikawa Amani dukkan hannuwan ta tana hawaye tana fadin Ya ki nan
diya ta, ta kaina! Amma Amani ta kasa tashi sabida yadda ta jika jikin ta da
fitsari a zaune, sai da Sahura ta ciccibata, ta isa ga Aysata, ita kuma ta saka
dukkan hannuwa ta rungume ta a ciki, tana fadin dukkan godiya ta tabbata ga
Ubangijin talikai, mai rahma mai jin kai, mai yawan hikima ga rayuwar bayin sa.
Sai lokacin Sarki yayi gyaran murya ya ce hakika Ubangiji mai hikima ne,
madallah da ku, madallah da kariman mutane irin ku, masu mayar da dan kowa nasu.
Ya dubi Daddyn Amani yana murmushi ya ce yadda ka rike min Mukhtar da amana ba
tareda ka san komai a kan sa ba, haka nake fatan in rike Amina daga nan har karshen
rayuwar mu, ko da bata kasance yar uwar sa ba. Allah ya saka maka da alkhairi ya
kuma baka lafiya.
Sai ga Mukhtar ya shigo dakin daga shi sai farar jallabiyya kal da bakar hular
larabawa a kan sa, kallo ya koma gare shi suna mamakin yadda cikin kwana daya tal
ya canza ya koma tamkar ba shi ba, yayi kyau, yayi wani irin fresh tamkar balaraben
Madina. Kamar da ka latsa shi jini zai yi tsartuwa. Nan aka gaya masa ko me ke
akwai, wato Jalan kanwar Ummami ne ta jini, uwa daya uba daya.
Mukhtar sai kamar bai yi wani mamaki ba, cewa yayi ai ni naso in gane hakan
tuntuni, kawai ban san komai akan Ummami bane ko dangin ta, wanda zai karfafa
zargin nawa, amma tabbas na ga alamu, tun sanda na ga cindo Ummami a hannun ta da
wasu attributes da dama, sannan jiki na ya bani, son da na samu kaina ina ma Mamma,
kamar na Ummami ne, musamman da ita ta sake da ni sosai ba kamar Ummami ba cikin
yan kwanakin da nayi tare da ita.
Nan aka shiga mayar da zance, aka dauko tarihi tun daga farkon sa, tarihin
masarautar Diffa da yadda kakan sa Sultan Oumarou ya bada sarautar ga dan sa Sultan
Massaoudou tun yana raye, bayan rasuwar sa Sarki Issouffou ya gaji sarautar daga
hannun mahahifin sa Sarki Massaoudou. Ya ce sun kasance su masu karancin haihuwa ne
a jinin su, shiyasa suke aure-aure daga kasashen Africa daban daban daga kyawawan
matan Africa, wadanda suke saye suna sa-daka dasu (concubines) basu cika maida su
matan aure ba.
Ya ce amma ita tunda aka kawo ta gaban mahaifiya ta ta ganta da tabon sujjadah
a goshin ta, sannan aka gaya mata daga Saliyo take sai tace aure zaa daura mana
bata yarda in yi sa-daka da ita ba.
Marigayiya mahaifiya ta tace matan Saliyo mata ne na musamman, daban suke a
halitta da sauran matan Africa, Allah yayi musu baiwa ta auren manyan mutane, tace
sanda zata kwace Mowar Diffa daga hannun Ummu Aymana, bazan sani ba.
Sarki yayi murmushi yace and thats exactly what happened today, Aisata Mowar
Diffa! Kafin ita ina da matan aure guda biyu, uwargida Ummu Aymana yar sarkin
Zinder tana da ya daya; Sayluba. Sai Tarha diyar sarkin Agadaz wadda itama na samu
haihuwar diya mace da ita. Sai aka daura mana aure na Sunnah da Aisata, na bata
dakin mace ta uku a gidan sarautar Diffa.
Kasancewar duk matan da ake kawomin matsayin sa-daka nake basu, wannan ya tada
hankalin mata na; Ummu Aymana da Tarha. Musamman da ya kasance har zuwa lokacin
babu wadda ta samu haihuwar Maina cikin su. Suka daga hankalin su a kan Ummami nima
suka daga min, sanda ta samu cikin Mukhtar kuwa ina wuta su saka ta, aka hanamu
aure ta hanyar saka min tsanar ta a shimfida, aka saka mata warin gaba, aka saka
mata kurarraji kai matsaloli marassa dadin ji iri-iri a dalilin wannan ciki kamar
ba zai kai labari ba.
Don daga baya ko dokin haihuwar tata na daina. Na koma ganin abinda zata haifa
min din a matsayin matsala.
Sai malaman fada ne suka saka ta gaba da addua don kowa yana so Diffa ta samu
Maina, basa so sarautar ta bar gida na, don ina da yan uwa a raye, amma ni ko a
jiki na. Uwargida na da bakin ta ta gayamin cewa muddin Aisata ta haifi Da namiji
sai ta salwantar da rayuwar sa, na kuma san zata iya, a yadda ta cika zuciyar ta da
burin ita zata haifa mun Maina.
Sai bayan an haife shi an kawo min shi hannu na zuciyata ta cika da kaunar sa,
gashi cikin yan uwa na ma da suke da yara maza basu so na samu Maina ba, sun so ya
kasance na mutu babu magaji don sarautar Diffa ta koma hannun yayan su. Don haka na
san ta koina Mukhtar yana cikin hadarin makiya musamman da ya kasance kamar an
tsaga kara ni da shi a kamanni. Sai na shiga tunanin ta hanyar da zan bi in kare
rayuwar sa.
Nan na zaunar da Aysata, na ce wannan yaro kin haife shi dai ko? To ki godewa
Allah komin runtsi sunan sa dan ki, amma ki nema masa kariya ta hanyar rashin nuna
kauna da kulawa a gare shi.
Ta yi min kallon rashin fahimta nan na wayar mata da kai, na ce mata na barshi
karkashin kulawar bayin mahaifi na na tun tali-tali, wadanda nima gadar su nayi a
gun mahaifa na saboda amanar su, wato Katchalla sarkin fada da Jakadiyar dana bata.
Na ce ta runtse idon ta daga kan yaron nan, ta bar shi ya rayu a hannnun su. Zasu
kula da shi kamar yadda zasu kula da yayan su amma rayuwa irin ta yayan su.
Da yake Aysata mai fahimta ce, mai kuma bani hadin kai akan duk abinda na zo
mata da shi sai ta yarda. Amma ta roke ni in bar ta ta shayar da shi ko a boye ne,
ko na tsayin shekara daya ne, na amince mata. Don na san muhimmancin nonon uwa,
kuma inaso ya tsotso irin kwakwalwarta da kyawawan dabiun ta.
A takaice wannan ne dalilin da yasa muka yi wa Mukhtar rainon da muka yi masa,
yau gashi Allah ya raya shi yadda nake fata, duk wani da ya nufe shi da sharri na
tabbata ya ga abun sa a kwaryar shan sa, domin koda aka gaya min kurciya aka yi
masa daga baya ni ban damu ba, na bar shi ya je ya koyi rayuwa har zuwa lokacin da
ni da kai na nasa malaman fada suka karya sihirin, tun a daren ne kuma aka gaya min
Ummu Aymana ta fita daga gidan nan, ta tafi har Zinder a kafa, ita ba mahaukaciya
ba, ita ba mai hankali ba, ta dai koma kamar tababbiya, kuma kalamanta kullum.
Mainan Diffa dana yi wa kurciya zai

Please Login or Register in order to submit comment