Reading Jikar Mamman by Oum Yasmeen Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dawo daga niƙa
da sauri ta koma bayan katangar wani gida ta laɓe ta ɗauki wani icce tasan dole ta
wannan kwanar zaibi ai be ankara ba yana shawo kwana ta kifar da garin murguɗa baki
ta shiga yi tace




"Wana kama....ai wallahi daman nace maka sai na sa rasa kunya ta dake ka har zata
ciza akan na dake ka wato ita ga kaza uwar son ya'ya ko....,




Kuka yaron yasa yace




"Allah ya isa wallahi sai na faɗawa mamman...,




kasa ta watsa mai baki tace




"Sanini zaka faɗawa wato uban mamman....tana faɗar haka tayi gaba abin ta bata dubi
asarar da tayi mai ba tafiya take har ta zo wajejan
makarantar su ganin kofar gate ɗin a buɗe




washe baki tayi tace




"Zan sha mangwaro....,




Salallaɓawa tayi ta shiga idi be lura da ita ba haka su malam musa da suke office
har kawo iyan zu ba su fito ba
shiga tayi sun kawo kai juya idanuwanta tayi suka koma kamar hulƙilili ga uwar
hodar da tasha dan haka basu gane'ta ba tabi ta shanye hannu da kafa dafe kirji
malam ɗan ladi yayi malam musa kuwa besan lokacin da ya saki fitsari ba domin yasan
cewa




Yau kashin su ya bushe sun hi gamo maƙe murya tayi tace....✍️




*JAKAR MAMMAN*




Wattpad @ Aminaoumyasmeen


Arewa book @ oum yasmeen




*🔞`freebook`*


*Episode 5*




https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k




*Masu tambayar complete har yanzu typing ɗin'sa nake ban gama ba...*




*`ku hakuri yau inna yi posting gobe bazan ba haka za dinga yi har in kammala
wannan littafin..........`*




Ku ka sake kuka ƙaraso nan sai na shanye muku ƙafa




Chak suka tsaya kirjinsu na lugudan tara tara wata irin dariya ce ke cin ta ganin
zata ƙwaro ta kyalkyale da dariya yadda kasan ta aljannu tace




"Wato ku bil adama Allah yayi muku kunnan ƙashi to yau zan maganin ku....,




Kuka malam ɗan ladi yasa majina shaɓe shaɓe yace




"Dan girman Allah kimin rai wallahi ko auran fari ban yi ba...,




shi kuwa malam musa idonsa ne chak ya tsaya baya ko motsi ba addu'ar da bekaranto
ba ko Allah zai dube su ya kawo musu ɗauki haɗa rai tayi tace




"Dan kunga ina dariya yi ne kuka kawo min raini to kun ƙara tabka uban laifi ni
surkutiya yar gidan sarkin aljannu yau dole in kai ku gidan yari inda ake sa
aljannu masu laifi kuje can su gasa naman ku...,




Ai ƙarasa warta ke da huya malam musa ya ɗora hannu aka ya runtu mai da ihu me yake
shirin faruwa da su




Shiiiiii yi min shiru ko sai na shafe baƙin ka yaza mo babu




tsit yayi yana zare idanu malam ɗan ladi yace




"Dan girman Allah kimin afuwa wallahi ba musan laifin da mukai miki ba....wata kila
shi musa ya sani...,




duka ya kai mai yace




"A gidan uwar....ka na sani...,




Ran JIKAR MAMMAN ne yayi fari yau zara yi maganin yan iska tace




"Au a gabana kuke wannan iskan cin lallai yau lahira za tayi baƙi....ina tsaye
kuna tsaye bako risinawa lallai yau sarkin aljannu zai yi sama da iyayenku da basu
baku tarbiyyar mutunta na gaba ba....,




zube wa sukai a ƙasa haɗa baki sukai su na bata haƙuri ɗauke kanta tayi tace




"Shi ne kuka ci mutuncin JIKAR MAMMAN har da me zagin'ta to wallahi yau zan
maganin ku baku san jikar sarkin aljannu bace ina sane na ɗauke ta na kai ta faɗar
mahaifina amma saboda ku kwakwalan dusa ne daku kuka ci gaba da neman'ta.....,
"Haɗa hannye sukai suna bata hakuri amma kamar turata suke yi....,




Ku yi shiru tsit sukai tace




"Na hakura amma da sharaɗi.....,




Mun amince wata dariya tasa tace




"A'a ai baku ji ba....,




wallahi ko bamuji ba mun amince wallahi.........,




Zaku dena dukan ya'yan al'umma sannan ku faɗawa sheɗimasta.....nasa zuwan na
musamman ne




toto zamu faɗamai ku rufe idanuwanku kar in tashi da ku


rufewa sukai salallaɓawa tayi ta fuce a guje a zaton su tashi sama tayi buɗe
idanuwa
nsu sukai suna sakin ajiyar zuciya
`**********`




tana fita daga makarantar gidan ɗan dashi ba nisa bako sallama ta shiga cikin
gidan yana zaune yana jin Radio da sauri ya tashi yace




"Yau a gari.....,




Zama tayi tace




"Ni ba gunka nazo ba ina innata take....,


jarbin dake kusa da shi ya cauɗa mata tace




"ban sani ba.....,


tashi tayi ta shiga cikin gidan samin kanwar mahaifiyar'ta tana ruɗan tuwo tace




"Inna ina huni.....,




ɗagowa tayi tace
"jikar mamman kice a gidan namu......,




ehwllh inna zuwa nayi muyi sallama saboda zan koma birni gidan wan baffana




ajiye ruɗan tuwon tayi tace




"Kardai abin nesa ne ya matso kusa....,




Cikin rashin fahimta tace




"Me kenan....,




auran da aka ɗaura miki lokacin da mahaifinki ya mutu kenan tarewa zaki ba gayya




hannu ta yarfe tace
"Owo ni dai nayi nan ta fita kai inna ta girgiza tace




"Allah ya shirye ki....,




har yanzu kahu ɗan dashi yana zaune da wata hularsa yawa an kifa kwano fita tayi ba
tare da ta shiga cikin gidan ba sun gaisa




Sai yamma liƙis ta ɗauko hanyar gida Imran har ya gaji da jiran'ta dan dai yana
ganin kimar kakansa da tuni ya tafi amma bakomai zai koya mata hankali yana kofar
gida suna hira da Salisu dan gidan adamu ƙanin mahaifinsa tun daga nesa ta hango'sa
haɗa rai tayi dan kar ya raina'ta




ta canza tafiya sai harɗe kafufuwa take tana wani lanƙwasa ita ala dole ga budurwa
kafin ta ƙarsa so Mudi saurayin'ta ya taso daga inda ya zauna yana jiran'ta washe
baki tayi tace




"Me lobi lobi ( my love)....,




da sauri Imran ya ɗago ƙansa jin wani wari ya buge shi wani yaro ƙazami ya gani da
wasu koɗadɗun gwanjo ya sa p-cap saman'ta a buɗe ya riƙe wani fure zura wayar'sa
yayi a aljihu dan shi kallon mahaukaci yake mai buɗe mota yayi ya ɗauko air
freshener ya fesa dan gudin ɗaukan ciwo'ta ƙara sowa tayi tace




"Me lobi lobi...,




Washe kuɗanɗun hakoran'sa yayi ga wani wahulu a bakinsa haƙoran'sa na gaba sun zuɓe
yace
"Na'am masoyiya....me maƙon kikirani na raki shine kika tafi ke kaɗai....,




washe baki tayi tace




"Wallahi me lobi fitar ce ta zo min ba shiri lobi.....,




uhmm nidai ki dena fita ba mayafi kinsan ai ina kishinki...




ɓata rai tayi ta murguɗa baki tace




"Bayan shekaran jiya na ganka da wata a dandali kuna zance.....,




Ran Imran in yayi dubu ya ɓaci Salisu kuwa tuni ya shige gida dan faɗawa malam
Mamman tasowa yayi ya tushe hancinsa da hannunsa yace




"Kai barnan gun....,




dadine ya kama DIJE Imran na kishin'ta tace
"Ya zaka ce ya bar nan gun bayan ba gunka ya zo ba....saurayi na ne shi zan
aura...,


ai bata karasa ba ya ɗauke'ta da wani gigitatcan mari malam ya daya fito yace




"Kara mata baki da kunya ko......yana mijin kina fadama mai haka...,




zubewa mudi yayi ya dafe zuciyarsa yace




"Na shiga uku me lobi 💕💕💕 maƙiya sun yi nasarar rabani da ki shikkenan.....,




ballet Imran ya ɗauko a motarsa ya labtawa mudi a gadon baya tuni ya miƙe a zuba a
guje dan har wani taurari ya gani dan a zaton sa ba mutunne yayi mai wannan dukan
ba




ran maza ya ɓaci fuskar Imran har ja take saboda ɓacin rai yace




"Malam wannan wane yaron ne mara tarbiya ya dube ka ya faɗa maka wannan magana ya
akai kuka barta tana kula irin su har guda nawa take.....,




Salisu yace




"Ai wallahi yaya IYA ke daure mata duk abin da kaga DIJE tayi da sahannun IYA
dafa shi malam yayi yace




"Be kamata ka dake shi ba Imran a koyo tankwara zuciya....,




To yace da gudu ta shiga gida tana kuka fitowar iya kenan daga bayi butar hannun'ta
ce ta waɗi tace




"Na shiga uku me ya faru...,




Wallahi iya ba zan yarda ba wancan dan birnin ne ya korar min saurayina mudi har da
duka na




salati IYA ta saki tace




"Dan gidan inyamurar ne ya dake ki...tun kan ki tare ya fara mayar min ke jaka....,




zaman dirsan tayi tana kuka ta girgiza kanta inno ce ta fito tace




"Ke lafiya kike wannan kukan....,




Wallahi inno bazan yarda ba dan birni ne ya korar min saurayina mudi har da dukan
mu kaniyar ki KHADIJATU tsit tayi ganin mamman ya shigo tsab zai iya naɗa mata duka
be iya fushi ba ku haɗa mata kayan'ta tazo ta barmin gida




To inno tace daman ta riga ta gama haɗa mata dan haka shi ga uwar ɗaka tayi ta fito
da su a cikin wani ganah most go cikin tsawa malam yace




"Ɗauki ki bishi ku tafi....,




ba musu ta ɗauka hajibi iya ta saka ta riƙe hannun DIJE har mota a buɗe take shiga
tayi tana kuka IYA na lallashi haushine ya kama Imran dan haka be musu magan ba




cikin faɗa IYA tace




"To me kafurar zuciya a canza hali wallahi kana ganin matar ka na kuka ko dan
rarrashin ta bazaka kai ba ɗan inyamura kawai ta juya ta shiga gida daman sun hi
sallama da su malam dan haka fitowa yayi ya rufe motar'sa ba tare da yaci mata ƙala
ba ya


ɗauki hanya karatun Alkur'ani ya saki yana bi tun tana kuka har tayi shiru hanyar
cikin garin kano ya ɗauka sun bude ƙauyuka karfe 7:30 ya iso ɗaukan hanya yayi da
zata kai shi Unguwar sani me dage tun da ya shiga DIJe ta tashi daga baccin da ya
ɗauke'ta wara idanuwa ta shiga yi ganin manya manyan gidaje yawa ba a duniyar nan
take ba




gaban wani tabkeken gida ya tsaya horn yayi me gadin ya buɗe mai buzune shiga cikin
gidan yayi tashi zaune DIJE tayi tana raba idanuwa dai-dai'ta parking ɗinsa yayi ya
fito remote ya danna kofar'ta buɗe kasa fitowa DIJE tayi ɓare baki tana kuka kallon
mamaki yake mata cikin ɗaure fuska yace
"Zaki fito ko sai nayi ƙasa ƙasa dake..,




cikin tsiwa hade da tashin hankali tace




"Wallahi bazan fito ba ina taka wannan abun (interlock) lumewa ƙasa zanyi....kana
sane kakawo nan...✍️




*Muje zuwa My fan's ga DIJE abirni ya abin zai kaya ku following ɗina arewabook
watt pad channel domin iya suka dai zan dinga ɗora jikar mamman yau in nayi anan
gobe ba anan zan yi ba zama dai ku na ko wanne shafina*




*JIKAR MAMMAN*




wattpad @ Aminaoumyasmeen



Arewa book @ oumyasmeen
*`Episode 6 🔞`*




Ransa ne ya ɓaci cikin karkausar murya yace




"Zaki fito ko sai na jawo ki a ƙasa....,




kuka ta ƙara rushewa da shi tace




"Ka dubi ƙasa ka gani har da ci yayi alamin a kwai ruwa a gun ina takawa ƙasa
zanyi....,




Fin ciko'ta yayi dai dai fitowar Ihsan sanye da riga armlees blue color da three-
quarter wando White colour da adon flower blue ganin big bro da gudu ta ƙaraso gun
kallon mamaki takewa DIJE tace




"Ị dị welu, nwanne nkem..., da Ibo
barka da dawowa babban yaya




be kalle'ta ba yace




"yauwa...,
ganin ba fuskar tambaya me ya kawo jikar Mamman gidan nasu ta jiya batare da tayi
abin da ya fito da ita ba tun daga main floor take cewa




Mamy mamy mamy tsaki taja ta isa gaban tabkekiyar plasma ɗaukan remote tayi dake
kan hadaddiyar royal TV drawer ta kashe tace




"Da magaribar nan SUHAILA ta samana kiɗa... wannan kiɗan ne ya hana mamy jina




a hankali take taka stairs case ɗin yana bada wani sauki kasancewar ta sa platshoe
a kafarta me dan tudu sanya take cikin swiss lace c-green me mayan zane onion
colour an mai sirki da dar pink kafar'ta jan kunshe ne amma mara zane (kwalta) yayi
wa farar fatar kyau ta tayi dauri maryam abacha huyanta shake yake da sarkar gold
wacce ta ƙara haskata sai zabga ƙamshi take kamar su ɗaya da Imran kabo da kabo
ƙarasa saukowa tayi tace




"Ihsan besab yau she zaki girma ba.... wannan wane irin kirane....,




ƙasa tayi da idon'ta tace




"Nyemaka mamy...,




zama tayi akan luxury royal chair ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya tace
"Me ya faru kike kira na.....?,




a kujerar dake kallon'ta ta zauna tace




"Mamy bigbro naga ni da jikar mamman....,




tunani ta shiga yi ta buɗe baki za ta yi magana sai ga nasma ta tawo da saurinta
tace




"Mamy daddy na kiranki ta mika mata waya....,




amsar wayar tayi ta danna kore ta ɗaga kiran sallama yayi mata amsa wa tayi tace




"Barka da dare.....,




daga can ɓagaran yace




"Yauwa mamyn Imran.....ya kuke ya yarana...,
gyara zama tayi tace




"Lfy qalau alhmdllh....da fatan dai kana lafiya qalau.....,




lafiya qalau mamyn Imran yau Imran ya tawo da surukar'ki




cikin rashin fahimta tace




"Daddyn Imran in-law fa kace yau she Imran yayi buɗurwa har da zai kawo min
ita...,




Ajiye coffee cup ɗin dake hannun'sa yayi ya zama dole ya faɗawa Maryam komai tunda
ita bata sani ba yana fatan Allah yasa ta ɗauki abin da sauki yarda taci buri akan
matar Imran sai gashi Allah be nufa ba yace




"Mamyn Imran.....,




Cikin ɗaguwa tace
"Na'am daddyn yara.....,




Yau shekara tara da mutuwar ɗan uwana lokacin da ya mutu Imran yana ƙasar America
bayan anyi sadakar arba'in mahaifina ya ɗaurawa Imran aure da yar gidan kanina
sulaiman saboda yana ganin shi kadene zai iya tallafar maraicin'ta batare da an
sami wata matsala ba to yanzu da ya dawo shi ne ya haɗosu dashi in zai tafi ya tafi
da ita......




Gumine ya shiga karyo mata yau ne karon farko da ta ɗaga mai murya ga kuma yaron su
tashi tsaye tayi tace




"Never wallahi bazan taɓa amsar taba a matsayin suruka ka nuna iya karka a kan
Imran nima Zan nuna nawa ikon akan sa bayan kasan cewa nabeehat tana jiransa har ya
dawo shine kai min wannan yankar kaunar......,




duk wannan zance a kunan IMRAN dake shigowa DIJE da buhun'ta a hannu ta sako kafa
ba tare da ta cire ta kalmi kashe wayar mamy tayi cikin tsana ƙarara tace




"Stupid village girl maza cire min takalmi nan ba ɗakin tsohuwa bane nasma maza
kai'ta bedroom din house girl.....,




ya tsuna fuska nasma tayi tace
"Mamy daty girl...,


ta wane taɓe baki yawa wasu sababbin mutane haka DIJE ke
kallon'su harɗe hannuwa Imran yayi yana kallon su ajiyar zuciya ya saki ya shigo
bakin sa dauke da sallama kasa yayi da idon'sa ganin irin hutar kiyayyar dake
ruruwa a idon mamy yace




"Mamy Barka da dare na same ku lafiya....,




daga mai hannu tayi tace




"My son yau she ka fara boye min sirrin......? ka lallai wayan nan tsofaffi sun yi
tasiri akan....,




dafe kansa yayi da ya fara sarawa yace




"Please mamy mu ajiye maganar nan mayi daga baya...yana faɗar haka ya fita


Mamy gaskiya Imran ya raina ki kinga fita yayi kina magana cewar IHSAN




komawa tayi ta zauna tace




"In sunsan wata ba susan wata ba wallahi....,
NASMAH tace




"Zo mu yafi.....,




harara DIJE ta hurga mata cikin tsawa nasma tace




"Ke bagijiya ba zaki zo mu tafi ba .....,




sosai DIJE ta ji haushin maganar'ta dan haka ta shamma ce ta ta buga mata gana most
go ɗin ta ihu NASAMAH ta saka ta zube tana kwara amai da sauri mamy ta yo kanta a
guje DIJE ta fita ita kanta ta tsorata ganin dan dukan da tayiwa NASMAH ta zube
tana amai




kofar rabar mata tayi hanya uku zabar ta farko tayi
tabi ko ita ce zata sadata da waje ta bar musu gida turawa tayi da karfi sai kuma
tayi sa'a a buɗe take shiga tayi sakar baki da hanci tayi ashe ba waje bane wata
hadaddiyar faranda ce an kawata ta da flowers masu nau'in fure me kyau




...................wata glass door ta gani da sauri ta tura ta shiga jin muryar
mamy tana cewa SUHAILA ta faɗawa security kar wanda aka bari ya fita a gidan nan su
rufe ko wanne kofa ta gidan nan shiga tayi zare ido ta shiga yi tana kalle
kalle.......,




floor iya haɗuwa ya haɗo tsayawa fadar kyansa ɓata baki ne kofar da take kallon'ta
da sauri ta karasa saboda wani kyau da tayi tana turawa kuwa ta buɗe dai-dai cire
War towel ɗin IMRAN wata iriyar ƙara ta saki Sakamakon........✍️




*Muje zuwa my lovely fan's taku har kullum fatahiyyah nickname (oum Yasmeen) nake
cewa mu huta lafiya*




Ga me buƙatar tallata masa hajarsa ya neme ni a wannan number 09061890481




*JIKAR MAMMAN*




https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k


episode 7




ganin'sa da tayi ya cire towel yana sa wando fita tayi a guje cin burki tayi a
baranda kujerun gabion da aka kawata gun da su anan ta zauna ta zuba ya gumi a
yarda taga wannan mata me kirar tanki tsab zata zaune ta ta shiga uku.... amma
yanzu ta ina zata koma takai tana wannan tunani taji an tsulamata waya a'a wanne
dan takazar.....ai bata ƙarasa ba tayi shiru sakamakon ido hudu tayi da Imran tushe
baƙin'ta yi ta ja baya tana zare ido




Kallonsa ma wanni tashin hankali ne musamman da tagansa ba riga daga shi sai boxer
kallon ƙasan wandon'sa tayi tana tunani a ranta tab ko ina yakai mucijin da ta gani
amma Bara ta tambaye shi ciki tsoro tace
"Dan birni daman akwai farin muciji....,




Hamdala yayi ganin ba ma ta fahimce mene ba yace




"Zaki huce ko sai na karya ki....,




Ƙasa ƙasa tace




"ni da ba karaba ya za'ai ka karya ni...,




kai ya girgiza Allah ya hada shi da aiki in yace zai biye mata tofa kullum za'a
ɗebe'ta a sume yace




"Ki gaggawar barin gun nan tun kafin in fusata....,




kallon sa tayi hawaye na bin kumatun'ta tace




"Wallahi na fita zaune ni za su yi da shirga shirgan ciyoyin's...,


be kalle'ta ba ya tura kofar sa yace
"da nafi kowa jin dadi suyi maganin rashin kunyar ki....,




rasa inda zata sa kanta tayi ga yunwa tana ji komawa tayi ta zauna ta zuba ta gumi
tun kafin aje ko ina zaman gidan na neman gagarar'ta




*******




Cikin floor kuwa mamy ce sai kaiwa take tana komowa IHSAN tace




"Mamy wallahi yarinyar nan tana gidan nan dole mune muta ta bar mana gida....,




Mamy ina bigbro ance min ya dawo




Wani kallo mamy ta watsa mai tace




"Khalifa neme shi....,




Kallo yabi su NASMAH da shi ya taɓe baki ya huce cikin kuluwa NASMAH tace
"Wallahi bigbro da ya khalifa yawa ba jininki ba mamy duk wannan abin da ake yana
ji fa amma ko a jikin sa...,




zama mamy tayi ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya tace




"Barshi zan maganinsu wallahi....,




joromi joromi I want to to love me joromi baby da sauri NASMAH ta tashi ta karɓi
wayar SUHALA tace




"haba ya suhaila tun da safe kike samana kiɗa... saboda kiɗan da kika sa bama kisan
me ya faru ba....,




a fusace ta karɓi wayar ta tace




"Wallahi mamy ki rabani da yarinyar nan ina ruwana da abin da ke faruwa sarai inna
jin ku mene laifin su malam dan sun aurawa big bro Mata daman hakkin sune in shi ya
kasa samowa su zaɓamai ta gari wacce zata dauke mu matsayin yan uwa ta ɗauke ki uwa
a matsayin ki na uwa mamy sai kice Allah isa haka ya fi alkairi mamy ada kina da
hangen nesa amma yanzu duk kin koma wata daman ban taɓa tsammanin cewa zaki yarda
mom nabeehat ba a tunani na kinsan halinta so baza ki amince da zancan haɗa bigbro
da ita ba wallahi NABEEHAT yar tasha ce ai bata ƙarasa ba taji saukar mari har guda
biyu mamy tace
"Suhaila ashe rashin kishina da kike har ya kai haka....,




dafa kumcin'ta tayi tace




"Wallahi mamy gaskiya nake faɗa miki ki duba zance na....tana kaiwa nan ta koma
bedroom ɗin ta tana addu'ar Allah isa ba dana sani ke jan mamy ba kar bigbro ya
aure nabeehat karshe mamy ta shiga uku a ko da yaushe mahaifinsu me kaunar mamy ne
amma lokaci ɗaya ta juya mai baya




floor kuwa sosai IHSAN ke yiwa mamy fanfo ta hau kai kuwa ta zauna shigar khalifa
ke da huya ya ci karo da jikar Mamman cikin mamaki yace




"Jikar Mamman.....,




da sauri ta ɗago ta lula duniyar tunani tashi tayi cikin farin ciki tace




"Ya Khalifa dan Allah me dani garin mu,




da huri haka ke da bigbro kuka zo kenan...?




da sauri ta kallesa tace
"wani kuma bigi baro....?,


me khalifa zai yi inba dariya ba yace




" Ya Imran nake nufi...,




au shine kenan bigi baro ikon Allah amma wannan mutumin sunan'sa na da yawa




zama Khalifa yayi yace




"Gaskiya kam a kwai yawa...,




khalifa zaka mai dani




gaskiya ban miki alƙawari ba saboda gobe zan koma Cambridge bazan dawo ba sai
karshen shekarar nan




shiru tayi saboda bata fahimci ina za shi ba har da zai wannan dadewar ji sukai an
turo kofar da sauri DIJE ta tashi tana neman gun tsira ganin ba su nasma bane ta
koma ta zauna ta tsare wacce ta shigo da ido lallai ta yarda yau Allah ya kawo ta
gidan yan iska cikin yar fuska Khalifa yace




"Nabeehat ina huni....,
ya tsuna fuska tayi ta yarfa hannaye da suka ci farce yawa me shirin shan jini
wandon ta crazy ne duk a huje ga uban attachment da tasa har duwawu fara ce amma ta
daɗa da mai ga uban glass da ya cinye rabin fuskarta rabin kirjin'ta a waje sai
taunar chingum take tace




"Fine....,




sosai jikar Mamman take dariya tace




"Ya khalifa amma wannan mahaukaciya ce....,




tura kofar da nabeehat ba tayi ba tayi kanta ya khaleefa ya tashi yace




"Nabeehat ba girman ki bane hi hakuri ke kuma jikar mamman kar in ƙara jin wannan
magana.....,




ya Khalifa kalifa wandon ta a bule in ba mahaukaci ba wazai fita a haka




ɗauke DIJE tayi da lafiyayyan mari kama ƙa hannunta DIJE tayi ta gantsara mata cizo
wani ihu nabeehat ta saki dai-dai da fitowar Imran cikin mamaki yake kallon su yace




"Khalifa lafiya....,
dariya Khalifa ya kwashe da ita yace




"Dukan ta tayi ta rama...,


haɗa rai yayi yace




"Ke cika ta.....,




ci kata tayi ganin abin son'ta sai ta ma manta me ya faru wara hannu tayi zata
rungume shi da sauri ya ja baya yace




"Don't touch me...,




ɓata rai nabeehat tayi tace




"haba sweet nayi kewarka fa.....,


kukan takaici DIJE ta saki da sauri ya Khalifa ya kalleta yace




"Lafiya....,
fyece majina tayi da sauri nabeehat ta matsa tana ya tsuna fuska haka Imran da yake
jin kamar yayi amai cikin kuka tace




"Ni ya rabani da masoyina mudi....amma shi gashi ashe yar iska yake tare da ita
wallahi...,




zaro ido nabeehat tayi tace




"Sweet ina kuka samo wannan ƙazamar yar aiki mara hankali....?,




murguɗa baki tayi tace




"Matar sace....kuma wallahi kece mara hankali ba ni.....ba.,




da sauri nabeehat ta kalli Imran cikin tashin hankali tace




"Sweet kana jin abin da tace....,




wallahi na ƙara jin bakin ki anan sai na fasa miki baki




bayan yaya Khalifa ta ɓoya tace
"Wallahi ya Khalifa an daura mana aure tun lokacin mutuwar baffana....,




Wallahi karya kike me sweet zai yi dake gaskiya sweet kukai wannan yar aikin naku
asibitin marasa hankali




ihu DIJE tasa ta fito tana girgiza ta kama kugu tace




"Wallahi kece mara hankali bani ba ga shinan alama ta nuna duk wandon ki a
bole....,




hannu takai zata kifa mata mari Imran yace




''kar ki kuskura ki dake'ta inba haka ba zan ɓatar miki....,


sauke hannu tayi ta fita a fusace juyowa kan DIJE yayi yace




"Zo ki fita....,


marairaicewa tayi tace


"dan Allah kai hakuri na zauna a gunka wallahi in suka ganni dukana za suyi yunwa
kuma nake ji....,




be kulata ba ya fice domin yana nema ya rasa jam'i yace
"Ya khalifa zo mu tafi masallaci....,
bin bayansa Khalifa yayi ya rufo kofar ganin sun tafi sun barta ita kaɗai ta shiga
floor kurawa kayan kallo ido tayi da sauri ta tashi ganin surarta a jiki ƙara
matsawa tayi taga ita ce dariya ta sheke da ita tace




"Yau na zama yar film gani a cikin TV.....,


da sauri ta matsa kusa da ita zata kunna kallo ganin tayi tayi taƙi kunnuwa ta bar
gurin bedroom ɗinsa ta shiga kalle kalle ta tsaya yi tura wata kofa tayi da sauri
tace




la ga korama ganin Bathtub cire kayanta tayi ta shiga wata zuciyar tace mata sai
kin huce ta cikin wannan koramar kin tafi wani garin tsaki taja a fili tace




"Ina neman tsari....,




wasa ta shiga yi da ruwan yanzu da sata wanka akai da tace sannyi duk da ruwan yana
da dumi ga kamshi dake tashi......




Nabeehat kuwa da kuka ta ƙarasawa mamy tace




"Mamy wace wannan tana cewa sweet mijin'ta ne......,
dafa kai mamy tayi tace




"Kar ki kulata bata da hankali zanyi maganin'ta ne a gidan nan....




zama tayi ta share hawaye tace




"Wallahi har taban tausayi yarinyar ta da ita tana hauka a ina kuka samota....,




cikin takaici nasma tace




"Yar kanin daddy ce bigbro ya ɗauko ta dan nema mata magani....,




Wayar ta ta zaro a aljihunta ta fara charting bedroom din'ta mamy ta koma ta shiga
tunani kafin nan da sati biyu da tasa za ai auran Imran dole ya saki mahaukaciyar
yarinyar nan




isar su masallaci yayi dai-dai lokacin liman zai ta da Sallah shiga sukai


a sujjadar ƙarshe ya dade yana kaiwa Allah kukan'sa Allah ya daidaita tsakanin
mahaifan nasa ɗagowa akai ya dago shima
Bayan an idar da sallah basu tsaya a ko'ina ba sai a gidan su da yake Khalifa yana
shayin Imran tun da ya dawo ba inda ya fita daga gida sai gida shiyasa yake Allah
Allah gobe tayi yabar garin ace mutum ya dawo hutu be zagaya gari ba wannan wacce
irin rayuwa ce




ta wata kofa yabi ya koma part ɗin'sa khalifa kuma yayi cikin gida ji hamdala yayi
lokacin da yaga DIJE bata part ɗin nasa kofa ya tura ya shiga floor nanma shiru be
tsaya a ko ina ba sai a bedroom ɗinsa jin

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment