Salma ya sanya ta buɗe manya fararen idanunta wanda suka ɗan faɗa saboda damuwa da kuma rashin lafiya.
Amsa sallamar tayi tana sakarwa Salma ƙaramin murmushi, Tunda ta zo gidan daji Salma ta kwanta mata arai sosai.
"Antyah barka da safiya fatan kintashi lafiya? " Saukowa Samhad tayi tana sake mamakin halayar Salma, Sam bata da girman kai, agirma zata bawa Samhad kusan shekara 2 zuwa 3.
Katse tunanin tayi ta cewa
"Ai kece Anty ba ni ba" Samhad tayi maganar cikin yanayinta na sanyi.
"A,a naƙi wayon gaskiya da gani kin girmeni nesa ba kusa ba kuma ko babu komai aike Antyna ce tunda kina matsayin matar Yaya MUBEEN dole nabaki girmanki"
Cak numfashin Samhad ya tsaya na wucin gadi, maganar Salma tashiga yamutsawa cikin kwanyarta ta, so take mayi magana amma ta kasa.
Ganin haka yasa Salma jan hannunta ta zaunar da ita kan gado tare da bude water bottle dake ajiye kan bedside ta bata.
Amsar ruwan Samhad tayi tashiga sha babu ƙaƙautawa, Saida ta shanye tas sannan ta ajiye robar tana dauke ajiyar zuciya.
"Salma intambaye ki? "
"Ki tanbayeni Anty Samha zan baki amsa".
"Da gaske ni matar aure ce? "
Numfashi Salma ta sauke kafin cikin sanyi murya tace
"Da gaske ke matar aurece SAMHAD, ke matar Yaya Mubeen ce da aka ɗaura muku aure Shekaran Jiya ranar juma'a bayan an sauko daga sallah".
Salma wai ni miyasa rayuwa take garani kamar kwallon kafa, miyasa kullum rayuwa take sauyamin? Bana farin ciki kamar kowa, bana walwala kamar kowa, bansan miye farin ciki ba sede inga wasu Sunayi bade ni inyiba, dan Allah Salma ki gayamin idan akwai wani abu wanda nike yi ba daidai ba wallahi zan gyara, ina so inyi rayuwa kamar kowa, ina so inyi farin ciki kamar yanda kowa yakeyi.
Matsanancin kukane ya sarke ta ya hanata ƙarasa maganar da takeyi.
Kwantar da ita Salma tayi akan kafadar ta tana rarashin ta, itama zuciyarta a karye take jin irin maganganun da Samhad ke faɗi.
Banko ƙifar yayi da k'arfi yana danne abinda ke yunƙuro mishi,
Direct inda kinda Salma take ya nufa cikin tsawa yace bar nan ke.
Rikicewa Salma tayi ta ajiye Samhad dake kwance a kafadar ta ta fice tare da janyo musu ƙofar.
Cak ya dauki Samhad da ta tashi cikin yanayin firgici zata fice itama.
ɗif numfashinta ya dauke kamin ta dawo daidai yayi mata masauki a faffaɗan ƙirjinsa.
Wani yanayine wanda bata taɓa kasancewa cikin saba ta riski kanta, ji take zuciyarta na faɗa mata ta samu bango abin jingina ta samu mafaka ta samu inuwar da zata kare mata rana me tsananin zafi.
Flash back.
Tunda ya baro wajen da yaje neman Saniga ya bashi kwaya be samuba ya dawo gidan babu wanda yasan da shigowar dan bada mota ya shigo unguwar ba.
Yanzu ya shigo cikin gidan ya tarar duk an hallara za'ayi break fast, Alla-Alla yake ya wuce yayi abinda zaiyi batare da kowa ya fahimci zuwanshi ba, Amma wannan munafukar Mammy ta riga data ganshi shine ta kirashi wai yazo ayi break fast dashi.
Daddy ne yayi mishi garejen kallo tare da maida hankali ga tea da Mammy ta hada mishi.
Tsaki Muneeb yaja tare da wucewa dan ɗaukar abinda ya kawoshi sashen.
Karab kunnuwanshi suka jiyo mishi abinda Samhad ke faɗi shine ya tsaya jikin ƙofar yana saurarensu.
Zuciyarshi ce ta hau tsuma jin kalaman dake fitowa daga bakin yariyar.
Dafe kanshi dake sarawa yayi yana Ambaton sunan ALLAH. Wato bada Amincewarta suka aura mishi itaba hasalima batasan da auren ba tunda gashi tana tambayar Salma da gaske anyi mata aure,
Miyasa Daddy kullum yake goyon bayan waccan munafukar matar me fuska biyu, miyasa zata shigo da yarinyar da bataji bata gani ba cikin rayuwarsa, wannan game ɗin ita dashi suka fara bugashi miyasa zata dinga sako wanda basusan farkon yanda aka fara buga wasan ba???
Jin kukan Yarinyar yake har cin kasan zuciyarsa shiyasa yakasa daurewa ya shigo.
Numfashi yaja tare da sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya tana shafa bayan ta don tasamu nutsuwa.
Luf tayi a jikinsa tana shaƙar sanyaye ƙamshi tsadadden turarensa.
Daga alkalamin maryam star⭐✍✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
🌹RAYUWAR SAMHAD 🌹( 𝒂𝒃𝒂𝒓 𝒕𝒂𝒖𝒔𝒂𝒚𝒊 𝒄𝒆😭)
𝑾𝑹𝑰𝑻𝑬 𝑩𝒀 𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑺𝑻𝑨𝑹✍️⭐⭐⭐⭐
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K8VBORyiBdJCR61hLJ9Hq9
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page 9️⃣ To 🔟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
__________________________________________________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
Sunkai kusan mintuna biyar zuwa goma a rungume da juna kamin daga bisani yasa lallausan hannunsa ya ɗago Samhad da tayi luf tana sauke numfashi da ajiyar zuciya.
A hankali ya zaunar da ita akan gadon yana goge mata hawayen fuskarta. Kan ƙasan maƙoshi ta jiyo maganar sa.
"Mi yasa kike kuka har haka so kike ki sakawa kanki ciwon kai?" Ummm?
Yayi maganar yana gyara mata hular kanta data kusa faɗuwa.
Tsamm jikinta ya hau tsuma don yanda yayi mata maganar cikin kunne ba ƙaramin dukan zuciyarta yayi ba, Abune da tsawon rayuwar ta babu wanda yayi mata, itafa ko Abbu ba wani Janta yake ajiki ba hasalima idan magana ta haɗasu to yana nesa da ita ko kuma ita tana zaune gabanshi.
Wani guntun murmushi ne ya kwace mashi ganin yanda jikinta ke tsuma.
Miƙewa yayi ya nufi bed side ya bud'e lokokin ya ɗauki abinda zai ɗauka ya fice daga d'aki.
Kwanciya Samhad tayi yarab tana maida numfashi sama_sama a zuciyar ta take jin wani farin ciki na daban, a zahiri kuma Tsoro ne ya lulluɓeta tana tambayar kanta wannan kuma Waye ya shigo ya kori Salma ita kuma ya rungume ta?
Ganin babu me bata amsa ya saka ta tashi cikin sauri ta saka hijabin ta tafito ta manta sam da bata gaida masu gidan ba, kumafa Salma tace aikota akayi ta kirata.
Cikin takunta a hankali ta isa dinning area.
"Assalamu alaikum" tayi sallama cikin zazzakar muryarta.
Cak zuciyar Mubeen ta tsaya da aiki na wucin gadi.
Murmushi Daddy yayi yana jin wani farin ciki yana ratsa zuciyarsa.
"Fatan kintashi lafiya? "Daddy ya maida mata gaisuwar da kulawa.
"Lafiya lau Alhamdulilah"
Masha Allah.
"Ina kwana hajiya" ta maida gaisuwar ga Mamy dake binta da kallo ta wutsiyar ido.
Washe baki tayi tare da jawo Samhad kusa da ita.
Batasan yanda akayi ba sede kawai ji tayi an janyo hannuwanta da Mamy ta riƙe.
Baki ta saki tana Kallon ikon Allah, ganin da gaske yake son fita da ita yasanya togewa tana ciccijewa janyo ta yayi iya ƙarfinsa zai fice da ita suka jiyo maganar Daddy cikin tsawa da kaushin murya yace
"Karka sake ka fita da ita idan ba hakaba se ranka yayi mummunan baci"
Wani tuƙuƙin bakin ciki ne ya tokare maƙoshin Mubeen.
Har ya tsaya kamar daga sama ya jiyo maganar Mamy cikin iyayi tace. "Haba Alhaji kadena biye mishi manah kasan yana da matsala yanzu haka wani abun yaje ya shawo shiyasa yazo zai ɗaga manah hankali tunda farar safiya."
Zaunawa Daddy yayi cikin mutuwar jiki da ɗacin zuciya.
"Ka dauki matarka kawai ku tafi Mubeen tunda babu abinda ka iya se batawa mahaifinka rai, ka dauketa kawai kutafi"
Mamy tayi maganar tana kashewa Mubeen ido dayi mishi alama da hannu wai itace winner.
Fuuuuu yaja hannun Samhad da karfi tareda fice daga part din zuciyarsa na tafasa kamar wuta.
𝑬𝑵𝑫 𝑶𝑭 𝑭𝑹𝑬𝑬 𝑷𝑨𝑮𝑬.
𝑴𝑨𝑺𝑼 𝑩𝑰𝒀𝑩𝑰𝒀𝑨𝑹 𝑳𝑰𝑻𝑻𝑨𝑭𝑰𝑵 𝑹𝑨𝒀𝑼𝑾𝑨𝑹 𝑺𝑨𝑴𝑯𝑨𝑫 𝑨𝑵𝑮𝑨𝑴𝑨 𝑭𝑹𝑬𝑬 𝑷𝑨𝑮𝑬 𝒁𝑨𝑲𝑰 𝑩𝑰𝒀𝑨 𝑲𝑼𝑫𝑰 𝑲𝑨𝑭𝑰𝑵 𝑲𝑰𝑪𝑰 𝑮𝑨𝑩𝑨 𝑫𝑨 𝑲𝑨𝑹𝑨𝑵𝑻𝑨𝑾𝑨 𝒁𝑨𝑲𝑰 𝑩𝑰𝒀𝑨 200 𝑲𝑨𝑪𝑨𝑳 𝑫𝑨 𝑨𝑪𝑪𝑶𝑼𝑵𝑻
👇👇👇👇
𝑨𝑪𝑪𝑶𝑼𝑵𝑻 𝑵𝑼𝑴𝑩𝑬𝑹
9136291920
𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑼𝑴𝑨𝑹
𝑶𝑷𝑨𝒀
𝑲𝑰 𝑻𝑼𝑹𝑨 𝑺𝑯𝑬𝑫𝑨𝑹 𝑩𝑰𝒀𝑨 𝑨 𝑾𝑨𝑵𝑵𝑨𝑵 𝑳𝑨𝒀𝑰𝑵
09136291920
🌹RAYUWAR SAMHAD 🌹( 𝒂𝒃𝒂𝒓 𝒕𝒂𝒖𝒔𝒂𝒚𝒊 𝒄𝒆😭)
𝑫𝑨 𝑮𝑨 𝑨𝑳𝑲𝑨𝑳𝑨𝑴𝑰𝑵✍️ 𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑺𝑻𝑨𝑹⭐⭐⭐
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels