ce wanka na yi za ni unguwa a'a don Allah banda
yawo kar in je a kwacemin ke waye zai kwace ni kuma?
Na sani by the way yaya Hajara? Hajara na nan lafiya tana
jiran ganinka insha Allahu zan zo next week don yau zan tafi
bauhci sai karshen sati zan dawo kisa raina ranar 'talata, Allah ya
kai mu yaya su Yaya? Suna nan kalau, sai kazo ke nan?
Wahiddah don Allah ki rike min alkawari na ce kar ya ji
komai ni tasa ce ba wani bayansa. Ya ce “Love you darling, kaima haka.
Na ajiye wayar ina dariya na yi saurin shafe shafe na
dama ni bana sa kwalli, balle jagira saboda gashin gira ta da na ido
sun ishe ni illah dan nashafa janbaki, shi ma faful kasancewar yana mani kyau to in ba jan-baki faful kika ban ba ba zan karba ba.
Bayan na gama sai na yi shigar fakistan mai haďe da rigar
na dauki jakata da mayafi na fito, Inna na falo da na karasa da sauri na ce Inna ina kwana yaya gajiya?
Ta dan yi murmushi ta ce wato sai yanzu ki ka shirya ko Wahiddahh, wanne irin bacci ne yanzu mutun ya yi ta zama da
yunwa har sai ciwo ya shige ki eye?
13
Inna yi hakuri na gaji ne da yawa bara na je na gaida
Abba na mike. Ta ce wanne Abba kuma ai ya tafi gun gininsa, sai
daı in ya dawo sai agaisa ina za ki ne na gan ki da jaka? Inna gun
Hajara mana, kin manta. To amma kyaci abinci ko? Inna me akayi
ne yau a gidan? Waina ce da taushe sai koko in zakici sai ki je ga
shi can kan tebir in kuma bakyaci ga shayi can a flaks sai dai
Hanne ta soya maki wainar kwai.
Sauri nake Inna wainar ma ta isa na nufi tebur in a
gurguje na ci duk da wainar ta yi masifar dadi haka na hakura na
ce Inna kar a cinye wannan nan Inna dawo zanci amma Inna ke
kikayi miyar ko?
Inna ta yi dariya ta ce me ki ka gani? Inna miyar nan ta yi
dadi na san Hanne ba za ta iya kamar ta ba na tafi Inna sai na
dawo, karfa ki dade to Inna bazan dade ba.
Na fita da guduna na samu Manu ya gama wanke motar
na ce muje Manu don Allah. Ina ne Hajiya? Na ce masa gidansu
Hajara, banyi tsammanin Hajara na gida ba, saboda me kace haka?
dazu na gamu da direrban gidansu ya ce Hajara na asibiti a kwance
na da fa kirji, me ya faru da Hajaran? Ya dan rude ganain yadda na
rude ya ce wal wallahi ban tambaye shi ba, illah na ce zan gaya
maki kuma saina sha'afa, shiga don Allah muje nwallahi baka
kyautamin ba.
Yaja motar yana faman ban hakuri ni ko sauraransa
banyiba hankalina na gun Hajara, muna isa asibiti na fito to Hajiya
na jiraki? Manu tafi na taho ka gayama Inna kar ta ga na dade ga
dalili, an gama Hajiya.
Tani mai aikin gidansu ta ce Hajiya sun tafi mai duguri
yau da safen nan, me ya faru da Hajara ne? Uhm wallahi Hajara na
son kasha kanta saboda Yusuf, saboda wa? Yanzu saboda Yusuf ra
yi ma kanta rauni haka? Wai a ina Yusuf din nan yake ne? na fada
cikin alamun nuna tsanata gareshi, Tani ta ce mayaudari ne kawai
'yan mata na wane suka fada irin wannan halin waye bai san Yusuf
ba, wallahi Allah Wahiddah duk mace da ra yi arba dashi to fa ta
fada tarkonsa.
14
Yaudarsu yake da kyan da Allah ya bashı ua kuma iya
lafazinsa ga uwa uba Naira. Oh ni Wahiddah to tunda ta san
halinsa me ya kaita ma soyayya da dan iskak haka irnsa.?
Well kina da Lambar wayarsa? Bara na duba Jakarta
baza'a rasaba wallahi su Hajiya har gida sukak kira shi su ji yadda
za'a yi cewa ya yi shi bai mata alkawarin aure ba in ta ga zata yi
aurenta ta yi shi bai shirya yin aure yan zuba hasali ma bai ga
macen da tiyi masa ba.
Karki so kia yadda ransu Alhaji ya baci amma da akayi
mata fada shi ne bayan tafiyarsu ta dauki gilashi ta yiwa kanta
rauni Allah yasa na shiga dakin ta dauko kwanuka na ganta a sume
jinni na ta tsartuwa bansan sanda na kwalawa Auwalu direba
kiraba yazo ya taimakamin muka kawo ta nan.
ta
Na kar6I takardar lambar tarhonta na shiga duba ta
mutumin da ta kira suna Yusuf na karba na kuwa ga lambar tasa ce
biyu daga tawa sai tashi cikin kunan rai na zaro hand set di na a
jaka na daddanna lambobin da na shiga saurare da allu'ar Allah
yasa yana nan.
Jin muryarsa naji kamar ya zuban ta fasheshshen ruwan zafi don tsanarsa da nayi Hello baby ya ce min? cikin tsawa na ce
kai ni ba irin wulakantattun 'yan matan da kake yaudara bane ni na fi karfin Baby ka ji ko, wacece ke mai min magana haka gatsal? Kana so ka san ni ko wacece? To ka zo asibitin tunawa da bayajidda na kudi imajansi dfaki mai lamba 112 kazo kaga condition din da kasa Hajara daga nan kaga ko ni wacece Just I
give you 10 minute na kife layin ina huci da zage zage, Hajara ta bube idonta cikin zafin nama na karasa gunta na ce Hajara me
yasa ki kayi ma kanki haka so kike ki kasha kanki sabda mutumin da baya sonki. Ta runtse ido ta bude ta ce Wahiddah da zan iya cire ciwon son Yusuf a raina da nayi ko don maganganun da ya fada ma su Hajiya, to me yanzu ki ke nufi? Bazan iya rabuwa da shi ba, na mike to kuwa kina tare da wahala wallahi in baki rabu da
shi ba ina ga zamu 6ata akan..... ban kado kofar da akayi ba ko sallama muka juya gaba dayan mu ya salam na fada a cikin raina saboda ganin mutumin dana tabbatar shi ne Yusuf Rashida gaskiya AHah ya ce duk dan Adam tara yake bai cika goma ba, hakika
15
haka yake Yusıf ya cika goma sha daya a dauke dayan na yaudarar
'yan mata gaskiya bazan iya wassafa maki kyan Yusuf ba, amma
gashi can a Hoto kin kuma san shi ma a fili, na barwa kanki
wannan amsar.
Ban tari numfashin kiba Wahiddah mijin nan naki wanne
irin yare ne? nayi dariya na ce mahaifinsa dan Nijar ne
mahaifiyarsa indiya ce ta ta fakistan kinji inda Yusuf ya yi wo
kyau bisa kyau ina gaya maki nan na dake duk kda razanar da nayi,
na ganin kyawunsana turbune fuska ya kal lan sama da kasa ya
jijjiga kai ya wuce daya 6angaren da Hajara take ya ce me yasa ki
kayi haka? Muryar Yusif take is natural.
Na doka masa harara, ya yi murmushi ya ce mu fan bashi
guri don Allah zai yi magana da Hajara, na ce baka isa ba in
zsakayi magana kayi in bada da abin cewa hanya a bude take ba
inda zamu disiba.
Ya yi murmushi ya ce wacece ne wannan mara kunyar?
Kaine mara kunya munafikin buzu ni na rasa jarabar da kika gani
gun wannan ra motar ki ka like masa har ki ke neman kasha kanki
na bude kofar na fita a fusace.
Ya bini da kallo cikin takaici ya kalli Hajara ya ce wacece
wannan? Ya danyi murmushi ta ce kawata ce aminiyata ce
waddata mai dani 'yar uwarta Yusuf don Allah kace kana sona? Ya
danyi jim ya kuramata ido cikin alamar tausayi da kuma fargabar
gaya mat ba zai iya ba.
Ta dan dora masa hannu kana ta ce Yusuf me yasa baka
sona ta fada cikin raunanniyar murya? Ya dan dora nasa hannun
kan nata ya ce Hajara bance bana sonki ba amma tun farko na gaya
maki ni bazan yi aure yanzuba kuma bana so na yaudare ki shi
yasa na gayamaki gaskiya ta gashi kinh dau abin da mahimmanci
kowa zata zaiyi ni na ce ina sonki kuma na zo na yaudare ki kin
jifa abin da iyayanki suka ce da kawarki don Allah karki kuma
yiwa kanki illah a kaina ina labe a bayan kofa ina jinsu take na
kuma tsanar Yusuf na koma kan tebier na zauna jiki na har tsuma
yake saboda masifar da na shirya masa in ya fito.
Bai jima ba ya fito ya kalle mu ya ce kwa iya komawa
naga ya fada a gadarance na kalli Tani na ce shiga ina zuwa ta16
Kayya Inna a koshe nake ina Abban ya dawo ne? tun
yaushe yana daki amma ina ga bacci yake nima bara naje na
kwanta na huta kafin ta gama.
Inna ta ce in an gama na tasheki, na wuce dakina ina
rangaji ko kayan jikina ban cireba na fada gado na sai me fuskar
Yusuf da maganganunsa ke min zarya a kunne na na runtsa idona
na muskuta wanne mataki zan dauak akan wannan takadarin
saurayin mai cin fuskar 'yan mata.
Bara ta fito tukunna mu ga hukuncin da ya ce zai yanke
da ya ke shi ne autan maza naja tsaki ni sam baya burgeni na
lumshe idona bacci mai karfi ya daukeni.
To Rashida mu je mu yi sallah sai kuma gobe in Allah ya
kaimu maci gaba lokacin aikina ya zo.
Rashida ta doki cinyar Wahiida ta ce me yasa ki ke garani
ne surukar indiyawa.? Muka kwashe da dariya abin ma ba'a ne ko
Rashida to na bar gayamaki labarin kuma sai na gayama Yusuf.
Dan Allah yi hakuri Wahidda mu dai yi sallar muci gaba
na yadda ana sallar La'asar sai mu tashi Please.
To Rashida na saba baccin rana fa amma dalilinki kinga
har daya da rabi ra yi muna hira. Sorry mam wallahi ian son jin
labarin nan naku mai kama da Film ko almara.
Ke ki ka sani kij i komai ba ta mike ta nufi shashinta ta ce
tun da ke liman ya roka maki ni bai kosheni ba Inna da ka ta taki
Rashida sai kisa na yi sabo gun Ubangiji na.
Baki jiba Wahdda? Wai mana muyi hirar da daddare
mana kafin mu kwanta, in kai Yusuf din ina? Um shi kuwa goshi
ya ganni bakuwa ba zai barki mu sake ba? Koma sokoto in kinyi
fushi Auwal na jiranki ba matsi in shi ya yadda nii ban yarda ba.
Iye lallai yau nasan matsayina Wahiddah ta shige
bandaki tana ma Rashida dariya, Rashida ta shiga kallon Hotunan
Wahiddah da Yusuf duk da suka dauka ba marabar Wahiddah da
mutanen Yausuf don sun saje tunda Allah ya tarfa ma garinta nono
itama tana da gashin kamar nasu.
Wahiddah ta fito ta ce oh Rashidda kya gaji da kallon
hotunan mu wallahi, eh kumyi bala'in burgeni to mu ci gaba
19
Wahiddab sha mur, ta ce na gaya maki bana son sunan nan fa, to
vi hakutn matar buzu.
An kuma bara na ci abinci ko? Oh Wahiddah wanne
abınci kuma bayan wanda mukaci to kari za'ayi ki ka sani ko na
harbu, to Allah dai yaban hakuri danasa kaina wahala ta ce kin
shirya, Wahiddah ta zame daga kan kujerar ta kishin gida akan kafet ta ce kin shirya ko naje nayi bacci na.?
Na shirya yaya za'ayi da halinki na miskilanci kinga kuwa
da sai na ci yusuf da yaki ba, ai naga alama bismilla.
Wahiddah ta ce haka muka ci gaba har da jinyar Hajara
iyayenta suka dawo amma muka shirya musu kan faduwa ra yi kan
gilashi sati biyu suna cika aka salami Hajara batare da Yusuf ya
kuma ziyartattaba.
Hajara ta shiga halin damuwa wai duk yadda aka yi baya
gari shi ya sa bai zo ba saboda haka don Allah in rakata taje gidan
su ta dubo ko lafiya na ce ba da ni ba gada a ka bari ta je ita kadai
ina jiranta a gida.
Hajara ta ci uban ado abinka da farar fata sai ta dauki
haske ta karbl mukullin motar gidansu ta fara ajiyeni sannan ta
wuce ina ta faman tausaya mata.
Nan na cimma Mustafa yazo da murna ya tareni har naji
kunyar Inna shi duk ya manta na ce yaushe kazo ne? Ya ce "banjima da zuwaba."
Inna ta shige shashin Abba ta barmu don ta kula da wata
tsakaninmu da Mustafa.
Ganin Inna at tashi Mustafa ya rioni nayi saurin kwace
kaina na ce meye hakak Mustafa?
Ya shafa hannuna ya ce wallahi kin gama rudani kinga
yadda ki ka hade gaskiya bazan iya jiran har ki gama Jami'a ba, na
ce ba muyi haka da kai ba fa.
Ya ce to yava kike so na yi da sonki badama fa na tabaki
sai ki fara kawomin wasu hadisan da ayoyi. Na ce to kayi hakuri
kaban sati biyu na yanke shawara, ya yi dan tsalle ya ce are you
seriouse? Na ce sure.
20
7
Ya fakaici idona ya sumbaci kuncına, nasha mur na ce bana so in dai kana so mu shirya, to yi hakuri dama nazo ne muyi
sallama zan kos na sati uku a Abijan.
Na ce Allah sa Aslheri a dai rike alkawari kar aga 'yan
mata a manta damu.
Ya ce haba Wahiddah, don dai ba ki san yadda nake son ki bane ace san samuna ne da aurenmu zan tafi can dakin da na
huta. Na ce kar kaji komai ina jiranka ya bani tsarabar da ya kawo
min na kayan sawa ran tsatstsu da kayan adon mata na silba nayi
masa godiya.
Ya sa na kira Umma sukayi sallama ya bata Dubu goma
da kyar Inna ta karba nan yake gaya mata da shifa da Najir daya
suke dole Inna ta karba ra yi masa fatan Alheri, ta koma dakinta.
Na raka shi har gindin motarsa nan ya ka mo hannuna ya sanyamin zoben gwal mai shegen kyau ya ce na alkawari ne. Nan
na ji son Mustafa ya kuma sarkafe min zuciya har naji ya kwalla ta tahomin ya shiga rarrashina da haka muka yi sallama cike da begwen juna har motarsa ta bace.
Wato Rashida abin da ya faru da fHajara babu dadin ji haka ta shigo min wujiga - wujiga tana ta faman dure duren ashar
ban tankamata ba har ra yi mai isharta sannan na ce "What up this time?" ta ce "Wallahi sai yau nasan Yusuf baida mutunci" na ce dafa mutunci ne dashi? Ta ce kinsan abin da ya faru again? Na ce banason ji.
Ta fashe da kuka wato da najwe da wata rantsatstsiyar
yarinya tana ta faman gurza kuka.... Akan me? na tambayeta cikin
rashin kulawa na ci gaba da ninninke kayana Wahiddahhn na
yarda wannan wata baiwa ce da Allah ya bama Yusuf, tana ta
faman rokon sa wai ya aure ta, shi kuma shegen sai ma ya ce mata
ba zai yi aure yanzu ba, matarsa har gobe bata zo ba.
Na kwashe da dariya na ce “Sai kuka yi yaya?" tuninma
dana dauki jakata na zazzaga masa masifa na fito kin san abin da ya yi mana? Ina zan sani.
Dariya kawai ya yi, ya rako ni da ita har gindin mota ya
ce min in gaida tsagalgalalliyar kawata da ta koyan hankali har na iya yi masa masifa, shi ya gode maki don ya san yanzu na san
21
matsayina a gunsa. Sai 'yan'uwantaka inda hah Hajara ta sa kuka
mai tsanani, share ta na yi don na san yanzu muddin na tamka mata
zan kuma lugwigwita mata zuciya, na kyale ta ta yi mai isarta,
sannan na ce sai hakuri amma ni zan yi maganinsa na rantse da
Allah.
Nan na gaya mata zuwan Mustafa da alherin da ya yi min,
ta shiga cizon yatsa rashin ganinsa. Da yamma bayan mun ci abinci
ta tafi kan za mu hadu ranar Lahadi da yamma, zuwa fatin bikin
auren kawarmu Jamila Salisu.
Wallahi har na manta, gwara da kika gayan zan dai ba ki
Gift ki kai mata, saboda ba zan samu damar zuwa ba, ranar za mu
tafi Yola bikin Yaya Fiddausi.
Wacece haka? Na tambayeta, baki santa ba, 'yar kanwar
Hajiya ce To Allah kiyaye hanya, don Allah a rage son maso
wani. Wai, ai wallahi ni da Yusuf kuma har abada, Na yi
murmushi na ce ko da kin burge ni.
Bayan tafiyar Hajara na kuma fakin Hajiya muka cigaba
da hira, nan take gayan yaya Salima za ta zo jibi don tahowa
haihuwa, don tun da ta yi aure shekara shidda kenan ba ta taba
haihuwa ba, sai yanzu. Kuma ya zama dole ta taho goyon ciki,
murna ta kama ni na hau tsalle.
Inna na dariya ta ce "Kai Wahiddahh ba ki da dama, mai
sunanki dai ba ta da kiriniya haka, salihar mace ce wallahi."
al
Nayi dariya na ce Inna yaya sunana ne? Inna ta ce babbar
magana aikin san ba zan fada ba, saboda sunan surikata ne, amma
kin san sunan baban nan ko? Wacce Babannan? Ta gidan mai
Koko. Oh Hindatu? To haka sunanki yake, muna cewa Wahiddah
ne don sakaya sunan, na ce dama sunana Hindatu? Ba kya so ne?
Inna ta tanbaye ni
Na fada jikinta na ce Inna ina son mana suna mai dadi
haka wazai ce bai dace dani ba? Haka nan muka cigaba da hirarmu
da Inna har magariba muka tashi muka yi Sallah, Abba ya sauko
falo shi ma ya zauna muna kallon labarai. Bayan mun yi sallar
Ishai muka ci abinci, ko kallon ban koma ba na ce masu sai da
safe
**** **** * ***
22
Ranar lahadi da yamma na ci uban kwalliya, hakika ni
kaina nasan ban taba kwalliya irin ta yauba.
Duk da ba wata wai sabuwar kwalliya bace a garin
katsina amma ni a guna kwalliya ce ta cinyewa. Na gaya miki bana
sa kwalli illa na shafa hoda da janbaki na Fafaul. Doguwar riga
nasa hadaddiya ruwan madara mai ribi biyu da dan kwalinta, sam
ban yafa mayafi ba, illah wani takalmi da na sa, shi ma fari flat
mara dunduniya da farar jaka. Na feshe jikina da turaren
Diamond, nan fa kamshi ya ziyarci ko ina da ina a gidanmu.
Na dauko jakar Gift dina da ta Hajara na fito na samu
Inna a kicin. Ta kalle ni ta ce da kyau 'yar Baba, amma don Allah
ki kula da kanki, duk da na san halinki ki kuma ja motar a hankali
kar ki wuce takwas.
Na ce "To Inna na gode ni ma zan kiyaye" ta ce a dawo
lafiya ice ko da kudi a hannunki? Da akwai Inna sun ishe ni.
Manu ya riga ya wanken motata, karamar Choroki. Haka
na zuba kyautar a bayan motata na bude na shiga na yi addu'a ta
kare kai daga sharrin hadari da kuma gudun faruwar wani abu. Na
dauko cingam din Hubba-Bubba na jefa a bakina na manna
tabarauna hi-hi na ja mota.
Na hau titi a hankali, na kunna Casset din Brandy cikin
wakar CARE FOR ME ina tafe ina bin wakar sannu a hankali, har
na zo babban Hotel din garin Katsina inda za'ayi liyafar. Motoci
na gani na fada kala - kala,gun ya cika. Nan na tabbatar taro ya
cika, na koma waje kusa da wani mai nama na yi fakin na ba shi
ajiyar motar tawa. Ya ce ba komai Hajiya, insha Allahu lafiya za ki
samu motarki. Na yi masa godiya na karasa da kafa.
Tun daga barandar idanuwa suka yi min yawa, daga
matan har mazan, nan na fara dabarbarcewa, don wallahi Rashida
na tsani kallo a rayuwata, haka na dake na shige.
To fa ai har gwara wajen da ciki, wallahi kasa motsawa na
yi duk fitsarata, Allah ya taimakan Jamila da Ummi Abubakar ta
hango ni suka nufo ni da murna. Sannan na saki dariya gaba daya
hakorina na maka guda daya mai kyalkyali ya bayyana. Suna zuwa
muka rungume juna, Ummi ta ce ya na ganki ke kadai, ba Hajara?
Na ce Hajara tafiya ta same ta, amma gani madadinta.
23
Jamila ta ce lallai kam zo ki gayan sirrin leyan nan naki
Wahiddahh ban yardaba. Na yi dariya na ce wallahi ba za ki daina
halin ki ba, ina Mukhtar din naki? Ga shi can gun..... ta yanke
maganar ganin tahowarsa da babban abokin Ango. Muna ta faman
hira da Ummi, sam ba mu ga zuwan su Mukhtar ba, sai maganarsu
na ji.
To uwar yanga gani gabanki sai yanzu akaga damar zuwa
bayan ke yakamata ki zama ta dayan. zuwa. Na dago kaina da
dariyata, na ce kaina bisa wuyana, tuba nake na Jamila ba zan
kuma ba. Π
Muka kyalkyale da dariya muka shiga gaishe- gaishe,
wallahi sam ban kula wanne suke tare ba sai da Mukhtar ya ce
Wahiddahh "Meet my best friend Yusuf Saheed, babban abokina
ne" kai kuma Yusuf "Meet my wife's best and only friend
Wahiddahh Maddo
Annurın tuskata ya gushe lokaci guda, na yi bala'in daure
fuska wanda na firgita angon kansa da amaryarśa. Shi ko sai faman
kallona yake yana murmushi ya ce "Barka da zuwa miss
Wahiddahh, nice name. Na kalle shi sama da kasa na buga masa
uban harara, na ja bayan Ummi da Jamila muka wuce. Mukhtar ya
rasa bakin magana, sai kawai ya bi mu da kallo har muka 6ace. Ya
kalli Yusuf ya ce "Kai yaya me ya hada ka da Wahiddah?"
Yusuf ya soka hannayensa cikin aljihun wandonsa ya се
"Ba komai, hasali ma ban santa ba in banda yau.""A'a Yusuf, ko
dai ka yi mata halin naka?" "Allah ban santa ba, sai yau. Mu je
kawai amma fa Mukhtar ina sonta wallahi, ta burge ni. Don ni ina
son mace mai jan aji, da ganin wannan sarauniyar 'yan matan za ta
yi jan aji.
Mukhtar ya ce "Kayya, halinka nake tsoro. Wahiddahh ba
irin 'yan matan da kake latsawa bane, gaskiya muskilacе. "
Na sani wallahi ina sonta ba da wasa ba, Just na ji ta shiga
raina" "Kai ai da ma kullum 'yan mata shiga ranka suke, ba za ka
lalata mana zumuncin mu ba, tana da jan aji da ji da kai, don
Family dinsu babban gida ne, kuma ana sonta kamar yadda ake
sonka.
7
24
"I know kawai zan iya sadaukar da kaina gareta" "Amma
ka ban mamaki, ashe akwai ranar da za'a samu macen da za ta
canza maka ra'ayi haka? "
Yusuf ya yi murmushi ya ce gaskiya da wata tsakaninmu,
boye maka kawai na y, ko dayake ba da ita muka haura ba, kawai
dai tarar fadan ta yi.
Ni na san ruwa ba ya tsami banza, me ya hada ku? Wato
akwai wata kawarta da take so na, ni kuma gaskiya ban taba jin na
so yarinyar ba, har ta so hallaka kanta a kaina. To shi ne farkon
haduwarmu da Wahiddahh, ta caccaba min magana. Da na ga
tsaurin idon nata ya yi yawa na rama, to ka ji hadin mu da ita.
Wacece kawar tata? Hajara sunan ta.
Mukhtar ya dafe kai ya ce lallai ba za ka samu yin
soyayya da Wahiddah ba sam ba zai yiwu ba. Yusuf ya rude ya ce
"Why me'ya sa?" Yusuf, Hajara babbar aminiyar Wahiddahh ce,
kamar Hassana da Usaina suke, "Iam sorry count me out, zo mu
tafi"
Yusuf ya bi Mukhtar, ba waní abu da za ka iya. Wallahi
har ga Allah ina son ta. Mukhtar ya ce to gwarama ka cire son
Wahiddahh ba za ta yarda ba, ka kulal da kallon da ta yi maka
mana.
No kar kace haka wannan ba wani abu bane Just ka gayan
yadda zan yi. "Iam sorry ba zan iya ba, na san halin Wahiddahh.
Allah ya bata riko, muddin ta ga na yi Supporting dinka na kaďe.
May be ma ta yanke hurda da matata, ni kuma ba zan so haka ba
sai dai ka je da kanka, in ta sauko to, zan iya yi maka kamfen.
Dole Yusuf ya hakura, amma ya rasa yadda zai yi. Ni da
Ummi muna zaune kan wani tebir muna hirarmu muna kallon
yadda fuskar Yusuf ta shiga cikin damuwa, duk budurwar da tazo
gunsa sai ya kore ta: Ummi ta ce wallahi kin burge ni, kin ga yadda
Yusuf ke gara mata, na yi tsaki na ce su matan ne marasa aikin yi.
Me ye abin so a gunsa. A'a Wahiddahh don dai bakwa shiri ne
gaskiya guy din Classic ne..... a gunku ba.
Ke fa? Allah ya kiyaye. wallahi Ummi sai na yi
maganinsa. Uhum Wahiddah ki bi shi a hankali, yaron ya san
kammu fa, wait and so once naki ina tsoronsa.
25
Ashe haka ya yi ma Hajara, ita ma ba ta jin magana,
wallahi ta wani fannin ba shi da laifi, tunda ya gaya mata
gaskiyarsa.
Don Allah Ummi mu canza Topic please. To to uwar
fushi bara na kawo mana Snacks. Ta barni ni kadai ina shan lemo.
Ganina ni kadai ya baYusuf halin zuwa guna.
Hannayensa cikin aljihun wandonsa Jeans, fuskarsa
kunshe da murmushin yaudara ya ce "Mallama Wahida sarkin
fushi na zauna?"
Ban kalle shi ba balle na yi masa magana, hasalima sai na
ci gaba da bin wakar da ake a rediyo.
Ya tura kujerar Umma baya ya zauna ya zuban ido ya ce
"Wahiddahh don Allah ki saurare ni.... meye haka ne?" na kalle
shi a yatsine, na ce "meye tsakanin mu da kai har da zan kula ka."
Wahiddahh Allah tun ranar da na dora idona a kanki a
Asibiti, ke hasalima tun da na ji muryarki a waya na ji ina mutuwar
son ki. Wahiddahh (ME TUMSE PYAR KARTIHA) wato ya fada
da yaren babansa ma'ana yana sonaa.
Ba kalleshi sama da kasa na sheke da dariya na ce,
"Hhaba ba indiye, ba ka isa ka yaudaran ba ko kai ne Shashikafur,
nafi karfin ka ka ja can ka karata da dabbobin 'yan matanká.
Yaw lumshe ido cikin kunan rai ya ce "Na san ba za ki
yadda da abin da na ce ba, wallahi ke nake so da raina da jinina."
Wahiddahh ta ce "ni kuma ba na sonka da raina da jinina,
ka san fa kai